RAYUWAR ASMAU CHAPTER 6
Sabir kuwa a jin muryar da take magana da ita yasa nan da nan tsigar jikin sa ta mike.+
Idon sa ya kada yai ja, lumshe ido yayi ya bude, ya ce,
“In in jiya da wa na ganki?”
Yayi tambayar ba tare da yasan lokacin da ta fito ba.
Kallon sa tayi ta ga ya canja amman bata kawo komai ba. Dan haka ta ce,
“Ni da Yayanah ne!”
Kai ya gyada kawai ya dauki waya yana dane dane.
Kallon sa tayi ta kuma narke murya ta ce,
“Naje?”
Kallon ta ya tsaya yi, kafin ya ce,
“Kunyi waya da Maryam!”
Kai itama kawai ta gyada masa. A zahirin gaskiya baya son ta tafi ta bar shi amman dole ta tafi.
Dan haka ya dinga mata tambayoyi. Sannan ya bata izinin tafiya.
Tana tashi ya bita da kallo har ta fita ta rufo kofar idon sa na kan ta.
Ido ya lumshe, yana me dafe zuciyar sa.
Tana komawa ta bawa Zainab labarin abinda ya faru da yadda suka hadu jiya.
Zainab dariya tayi ta ce,
“Wai ke baki gane wani abu ba.”
Asma’u ta ce,
“Me zan gane me ya faru?”
Dariya kawai Zainab tayi ta ce,
“Allah bazan fada miki ba. In kin gano ka zo kiban labari.”
Share maganar Asma’u tayi dan ta san Zainab akwai jan rai an kana son abu.
Daga haka suka zauna aka shiga wani lecture din.
Karfe hudu dai dai Yaa Aslam yazo, kiran Asma’u yayi bata dauka ba. Yasan tana massalaci. Dan haka ya fito ya zauna daga kasan bishiya.
Yana zaune ya hango Sir Sabir ya taho a cikin motar sa.
Kallon ssa yayi ya dan saki tsaki sannan ya dauke idon sa. Ya rasa dalili shi dai kawai gayen bai masa ba.
Shima kuma ta bangaren Sir din ya ganshi sai dai shi a duk sanda suka hadu sai yaji wata faduwar gaba
Yana zaune a haka Munasha ta gano shi. Gunsa ta nufa tana canja salon takun ta.
A hankali ta karasa gun tai masa sallama. Dagowa yayi ya na kallon ta daga sama zuwa kasa.
Ita kuma sai gyara tsayuwa take. Baki ya yamutse, kamar yaga kashi ya dauke kai.
Wani iri taji amman duk da haka ta dake ta ce,
“Sannu fa!”
“Yauwah!”
Ya fada kamar bai san wanda yai maganar ba dan kansa yana can kallon gefe.
Zatai magana kenan ya daga mata hannu. Sannan ya mike ya tsaya a gaban ta.
“Me kike nema ne?”
Ya tambaye ta yana juya mata baya,
Kallon sa ta tsaya yi tana hadiyar yawu.
“Wallahi sai na dan dani zumar gayen nn.”
Ta fada a ranta. Tana kallon sa hadi da hadiyar yawu sai kace ta ga nama.
STORY CONTINUES BELOW

“Uhmm uhmm daman!”
Sai kuma tayi shiru.
Murmushi yayi mai sauti sannan ya juyo gare ta.
“Haba yan mata. Ki rike ajin ki na ‘ya mace man. Nasan irin ku nasan kalar ku muna dasu daa yawa wadan da ke bibiyar mu. Ba wai son mu kuke haka kawai ba akwai wani abu a ranku. In da ‘yar mutumci ce taga mutum tana son sa, ta san ta yadda zata tusa kanta gare shi har yasan da ita. Ba kamar ke da kikazo kika samen gaba da gaba ba. Kuma dan Allah kalli shigar ki. Wannan ba shigar ya’yan kirki bace, ko da zan so mace. Ba zan so macen da bata da kamun kai ba wacce ta gama tallata surar ta ga mazan waje ba.”
Shiru yayi sannan ya ce,
“Kalle ki dan Allah kin kalli kan ki a mudubi kuwa kafin ki fito.”
Kanta take kalla sai a lokacin taga shirga dake jikin ta ba mai kyau ba.
Kanta ya sha gashin doki har gadon baya, sannan ta saka riga da wando sun dame ta.
Sai wani dan karamin mayafi da ta yafa ta saka takalmi mai tsini.
Bilkis ce ta kara so gun ta ce,
“Kai Munasha kina wuta fa.”
Shiru Maimuna tai mata, kallon su yayi ya ce,
“Yanzu wannan dawa kikai koyi, kinsan wadan da kikai koyi dasu ko, to turawa ne, Bayan Allah madaukakin sarki ya ce,
“Kada ku rike da al’adun yahudu da nasara kuma ya ce kada ku koyi abubuwan su wajen shiga sauya suna. Duk wanda ya jibanta al amaransa zuwa ga yahudu da nasara Allah (SWT) ya ce, ka zamto daga cikin su. Wato ya zamo su.’ (Ma’ida 51)
“Kinga ko anan kinyi abu nawa irin nasu. Ji shigar ki. ji wani suna da aka kira ki dashi.
Manzon Allah (SAW) Yace,
‘Duk wanda ya kwaikwayi wasu to shima ya zama shi.’
Haka nan Manzon Allah (SAW) ya ce,
‘Mutun na tashi ranar alkiyama da wanda yake so.’
In kana son Allah da mazon sa kana yin abinda suka ce dasu zaka tashi. Haka nan in kana son wasun su, to da su zaka tashi.
Haka nan aya ta 57 a cikin suratul ma’ida. Allah madaukakin sarki yaba cewa,
“Yaku wadan da kukai imani karku riki wadan da suka rike adddinin mu da wasa da rudu’ (yahudu da nasara) su ne suka rike addinin mu da wasa. Kar mu rike kafiri a cikin masoya (mudai dai yi mu’amala) muji tsoron Allah in mun kasance mumunai.
kiji tsoron Allah ki koma ga Allah dan daga shigar ki ya nuna min ke wace, kada ki manta daman sai da shaidan ya ce,
‘Wallahi sai ya samu rabon sa.’
Wallahi ba kowa ke saka mana wadan nan ra’ayuyu kan ba in ba shi ba duk dan ya dulmiyar damu. Kiji tsoron Allah ki daina duk abinda kike. Duniya ba matabbaciyya bace, haka rayuwar mu a koda yaushe mai iya karewa ce.”
Ya juya kenan yaga Asma’u da Zainab suna tsaya suna sauraran su. Kuka Maimuna ta fashe da shi ta zube a kasa. Da sauri Asma’u ta karasa gun ta ta dago ta.
Kallon Asma’u tayi idon tana fitar da kwalla. Kuka take sosai sai da kyar Asma’u ta lallashe ta tayi shiru.
“Asma’u daman mutum kan hadu da mutum in Allah yaso. haduwa ta ga Aslam shine shiriya ta da izinin Allah. Nagode Yaa Aslam nagode insha Allahu bazan kara aikata abubuwan sabo ba.”
Sosai Yaa Aslam yaji dadi.
“Ba komai. Kiji tsoron Allah dai a duk inda kike.”
Ya kalli Asma’u ya sakar mata murmushi. Zainab ya kalla ya ce,
“A’ah In-low ashe kina nan.”
Murmushi tayi ta dan durkusa ta gaishe shi.
Gaba sukai shi da ita suna hira. Har take basa labarin yadda Maimuna ta dinga damun Asma’u akan sa.
Dariya yayi ya ce,
“Allah sarki. Ita kuma me tayi.”
Zainab ta ce,
“Ai kasan Asma’u in yan mutuncin suna nan akwai saukin kai.”
Sukai dariya gaba daya. Ya ce,
“Lallai kam. Amman dadi na da Asma’u akwai hakuri sai dai in aka kai ta karshe basan ya zata yi ba kuma,”
“Wallahi kuwa ba ruwan kowa nata ne, kowa tana iya zama da shi. Allah Asma’u bata da temper kowa sai taka ta yadda zata saka farin ciki da karatun ya. Bata da abokin fada bata da riko.”
Murmushi yayi jin halayar Asma’u wanda shima ya san da su
Asma’u tana can lallashin Maimuna har sai da ta ga ta daina kukan ta nutsu sannan sukai sallama.
Bilkis kuwa duk da abinda Aslam ya fada ya ratsa ta amman bata jin zata daina abubuwan da take yi
Gun Maimuna tayi ta ce,
“Maunas……”
Bata karasa fada ba ta dakatar da ita ta ce,
“Bana son sunan nan ki kira ni da Maimuna in zaki iya”
Ta mike tayi gun motar ta tashiga ta fita daga makarantar a guje.
Baki Bilkis ta tabe ta shiga motar da Maimuna ta tabi bayan ta.
Asma’u kam suna tsaye ita da Aslam da Zainab.
Zainab na tsokanar ta da tini an kwace mata Yaa Aslam dinta.
Duka ta kai mata ta ce,
“Ai ba mai iya kwace shi sai Allah yaso.”
Yaa Aslam ya ,
“Allah ma bazai so na ni na kine ke kadai.”
Gira ta daga ta kalli Zainab ta ce,
“Kinji ko?”
Murmushi tayi tace,
“Allah tabbatar da alheri.”
“Ameen!”
Duk suka amsa sannan sukai sallama ta shiga motar gidan su itama suka shiga ita da Yaa Aslam suka tafi.
A mota ma labarin yadda sukai da Maimuna ne yadda ya je gun ta a makaranta da lokacin da ta tambaye ta aikin sa da suna sa.
Dariya take shi kuwa ya hade rai. Kallon sa tayi ta ce,
“Me kuma nayi?”
Motar ya faka a gefen hanya ya kalle ta ya ce,
“Wai ke bakya kishi nane, daga nan baza ki gane me take nufi ba. Amman kin wani sake da ita.”
Murmushi tayi ta ce,
“To Yaa Aslam ai sai mutum bai san matsayin sa a gun masoyin sa ba zai tsaya kishi. Ni da nasan ko da duk matan duniyar nan zaka aura sona daban ne a zuciyar ka haka nan kaunar da kake min baza ta taba tafiya ba kuma bame iya samun rabin ta daga wajen ka. Kada fa ka manta mukullin zuciyar ka nice. Tayya zan bude har wata ta shiga.”
Dariya yayi ya lakace hancin ta fe,
“Ni dai ana kishi na dan baki san wasu mantan bane.”
Murmushi tayi ta ce,
“Ina kishin ka man nafi kowa kishin ka da kishin masoyin sa saboda ni kadai nasan wane irin masoyi ne dani. Ina son ka. Ina kaunar ka bazan so wata ta rabe ka ba ni kadai nasan kishin da nake maka a cikin zuciya ta.”
Watan Yaa Aslam daya ya fara shirin tafiya.
Asma’u ji tayi kamar me, dan kuka ta sha shi tinda ya ce mata zzai tafi.
Ranar Asabar ya saka tafiyar tashi. Ranar juma’a ya dauke ta ya kai ta shopping yai mata siyayya mai yawan gaske.
Amman duk jikin ta a sanyaye yake da ka kalle ta zaka san bata da walwala.
Haka suka dawo gida duk yadda yaso ta sake kasawa tayi sai dai ta dan yi masa murmushin yake.
Da dare bayan sun ci abinci ta shiga dakin sa dan taya shi hada kaya.
Shima yana kwance ya fito da kayan ya ajiye akan gado.
Tunanin shima rabuwa da ita yake. Kallon sa tayi ta wuce wajen kayan ta fara zuba masa a cikin akwatin sa.
Motsin ta da yaji shi ya sa shi bude idon sa. Kallon ta ya tsaya yi hada masa kayan take cikin sanyin jiki.
Jin idon sa akan ta yasa ta kalle shi, Murmushi ta sakar masa, ta cigaba da abinda taken.
Mikewa yayi zaune ya zura mata ido. Ko kiftawa baya yi.
Har ta gama bai dauke idon sa daga kallon ta ba.
Takalman sa ta fara hadawa ta gama ta koma gefen sa ta zauna.
Kallon sa ya dawo da shi kan ta, murmushi ta kara sakar masa.
“Yaya nah lafiya?”
Ta tambaye shi.
“Baby nah bana son ganin ki a damuwa,”
Ya fada yana kamo hannun ta.
Hannun ta. ta zare ta ce,
“Yaya nah naji sai kuma me?”
“Bansan menene ba. Amman bana son barin ki Asma’u bana son nima na tafi. Ki yadda nayi magana ai mana auren kinji.”
STORY CONTINUES BELOW

Kasa tayi da kanta sannan ta ce,
“To Yaya nah yanzu in mukai auren karatu na fa. Kaga nazo gangara ka bari nan da wata shekara sai muyi aure ko?”
Kai ya gyada ya ce,
“Haka ne, amman bana son na rasa ki bana son nayi nesa da ke.”
“Haba Yaya nah kar ka manta fa dazu kai ka gama lallashi na akan nayi hakuri muna tare ko?”
Hannun ta ya kamo ya matse shi a cikin nasa. Ido ya lumshe, sannan ya bude.
Kallon ta ya tsaya yi tin tana kallon cikin idon sa, har ta gaza kalla dan wani abu take ganin yana shiga cikin nata.
Lumshe idon tayi matsowa yayi kusa da ita. Ya ce,
“Asma’u ki riken Alkawari na kar ki taba bari na in dai ina cikin duniyar nan ina son ki yi min alkawarin ke tawa ce.”
Idon ta, ta bude wanda suka canja kala zuwa ja, ta ce,
“Wallahi Yaa Aslam na maka wannan alkawarin bazan taba barin ka ba. Sai dai in kai ka bukata.”
Ido ya lumshe samnan ya ce,
“Ni kuwa tayaya za’ai na bukaci rabuwa da rayuwa ta.”
Murmushi tayi ta ce,
“Bare kuma ni.”
Yayi murmushi.
“Bari naje na kwanta!”
Kallon ta yayi ya ce,
“Kamar mu kwana tare.”
Murmushi tayi ta ce,
“Allah kawo ranar da zamu kwana taren.”
“Ameen!”
Ya fada yana mikewa. A kofar dakin ta suka kara tsayawa sun dauki kusan minti ashirin suna tsaye sannan sukai sallama ta shiga.
Tana shiga daki ta fashe da kuka. Rasa kukan me take tayi amman ta san cewa ba zai rasa nasava da tafiyar Yaa Aslam ba.
Sai da taji kiran sa a waya sannan tai saurin shiga bayi tai wanka ta fito ta shirya sanann ta kira sa.
“Baby na kin kwanta ne?”
Ya tambaya daga can site din.
“Eh yanzu na kwanta.”
ta bashi amsa.
Ya ce,
“To kiyi addu”a sai da safe.”
Ta ce,
“Allah tashe mu lafiya.”
Ta fada tana kashe wayar.
Washe gari tin asuba ta tashi ta yi duk abinda zata yi.
Wanka tayi ta koma gado tai kwanciyyar ta.
Sai karfe sha biyu sannan ta mike ta kara watsa ruwa ta shirya cikin wani tissue pink material wanda akai mata dinkin fitetgown, batai kwalliya ba.
Hoda da man lebe kawai ta shafa sai kwalli da ta saka a idon ta.
Falo ta fito ba kowa a sama a kasa ta dinga jin maganar su.
Sauka tayi a hankali ba ta kalle su ba sai da ta shiga kkitchen.
Ruwan zafi kawai ta hada ta fito falo. Sai da ta gaishe da Yaa Aslam da Yaa Buhari sannan ta nufi daining.
Zama tayi ta kasa shan tea din ma. Yaa Aslam ne ya mike ya shiga kitchen ya dafa mata indomie sai ya soya mata kwai.
Daining ya nufa ya zauna a kujerar dake facing tata.
Kallon sa tayi ta sakar masa murmushi.
Plate din hannun sa ya tura mata gaban ta. Ya daga mata gira alamar ‘ta ci.’
Ja tayi ta saka spoon tana ta wasa da shi.
Amsar spoon din yayi ya fara bata a baki. A hankali a hankali har ta ci mai yawa sannan ta ce ta koshi.
Falo suka koma suna hira da Yaa buhari ita kuwa tai shiru sai dai ta kalli.wannan ta kalli wannan.
Kiran sallah aka yi wannan yasa kowa ya tafi dakin sa.
Alwala su Yaa Aslam sukai suka wuce massalaci.
Ita kuma a daki tai sallar tinda ta idar ta kasa tashi daga inda take har karfe biyu tana zaune.
Yaa Aslam ne ya shigo dakin cikin shirin tafiyar sa.
Yana sanye da Milk din wando sai maroon kalar riga mai dogon hannu.
Takalmin kafar sa ma maroon ne. sai tashin kamshi yake.
Tana ganin sa ta mike ta saki fara’a shima murmushin yayi ya kamo hannun ta suka fito.
Mami na falo suka tadda ta. Sallama yai mata suka fice tare.
Yaa Buhari ta gani a cikin mota yana jiran su.
Bayan mota suka shiga daga ita har shi har lokacin hannun ta na cikin nasa.
Wata zoben azurfa ya fito dashi daga cikin jakar sa. Ya zura mata a yatsan ta take hannun ya kara gaske yai mata kyau.
Sumbatar hannun yayi yana kallon cikin idon ta.
Lumshe idon tayi tana mai yin murmushi.
Suna zuwa airport din Yaa Buhari ya fita a motar.
Kallon ta yayi ya ce,
“Baby na zan tafi ki kular min da alkawari na.”
Asma’u Ta ce,
“To Yaya nah Allah kiyaye hanya, kar ka manta da alkawari na nima kaji.”
Ya ce,
“Insha Alalhu bazan manta ba!”
Yai mata kiss a goshi sannan ya fita.
Ta taga ya leko ya ce,
“Ki zauna ba sai kin ffito ba. Kai ta daga masa sai kuka kuma.
Kuka sosai take ba shiri ya koma cikin motar ya jata jikin sa yana lallashin ta. Amman kamar kara zuga ta yake.
Ya jima yana lallashin ta da kalamai masu sanyaya rai yaji ta daina kuka.
Bai daina shafa mata bayan ta ba da kwantar da hankalin ta. Sai da ya dauki minti goma a haka sannan ya dago dan ya ga me take.
Bacci yaga tana yi sai ajiyar zuciya take saukewa.
Murmushi yayi ya kwantar da ita sannan ya kara kissing nata a goshi.
Waya ya dauko ya dauki pics din ta sannan ya fita a hankali.
Yaa Buhari ya gani suka karasa ciki. Basu jina ba ya tashi. Dawowa mota Yaa Buhari yayi ya ganta tana ta baccin ta.
Motar ya tayar suka tafi gida a hankali yake tukin duk dan kar ya tashe ta.
Yana tausaya musu yana musu addu’a akan Allah ya mallaka musu juna su. Dan son da sukewa juna su shi gani yake kamar yayi yawa.
Kuma yana tausaya musu dan kar wani a bu ya faru bai san wane hali zasu shiga ba.
Har ya isa gida bata tashi ba. Daukar ta yayi ya kaita dakinta samman ya sanar da Mami sun dawo.
Sai magariba ta tashi. Tana bude ido taji idon ta a kumbure.
Taba su tayi sai kuma ta tuna da abinda ya faru dazu.
Wani kukan ta kuma saki ita kadai tayi iya yin ta sannan ta mike ta shiga ban daki.
Wanka tayi tayo alwala ta fito ta saka kayan bacci ta tada sallah tana idar wa ta kwanta anan inda take
Wani bacci ya kuma sace ta. Sai tara saura ta farka.
Bandaki ta shiga tai alwala ta fito tai sallah zata hau gado kenan sai ga Mami da Dady nan sun shigo.
Mami rike da katon tire a hannu. Gefen ta Dady ya zauna ya ce,
“Wannan shakuwar taku Asma’u tayi yawa. Yanzu inda Yayan naki yai aure ai sai Antyn ki tana jin haushi kiyi hakuri da kin gama karatu zaki je ki musu hutu kinji.”
Kai ta daga tana masa murmushi sannan tai masa sannu da zuwa.
Abinci Mami ta zuba mata sai da ta ga taci ta koshi sannan suka fita daga daki
Kan gado ta koma ta kwanta kiran sa ne ya shigo.
Dagawa tayi cikin sanyin murya. Ta ce,
“Yaya nah ka isa lafiya yasu Momy da Dady?”
“Duk suna lafiya ya na baro ku?”
“Lafiya Alhamdulilah.”
“Wallahi ina kewar Baby na.”
Murmushi tayi ta ce.
“Nima haka.”
Daga haka suka fara hirar su kamar yadda suka saba.
Sun jima suna hira sannan sukai sallama kowa ya kwanta.
*Uhmmm*