RAYUWAR ASMAU CHAPTER 8

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 8

Satin Yaa Aslam daya ya juya da shirye shiryen bikin su.

Dan yana komawa yasa Momy a gaba dole suje dubai su hadu kayan lefe.

Momy ta ce, ya bari lokaci ya kara karatowa. ‘Ki yayi ya ce shidai su tafi.

A satin da ya dawo a satin suka tafi hado lefe.

Siyayya mai yawa da tsada sukayo. Duk abinda yaga ya burge shi ya ce a dauka. Haka nan Momy itama da ta iya zabe kaya masu kyau da tsada ta dinga siya.

Kaya sai da suka hada set akwati uku amma basu isa ba.

Sosai Momy ta hado mata kayan kwalliya da english wears dan ta san irin shigar da Asma’u take kuma tasan Asma’u yar gayu ce.

Haka suka dawo gida da niki nikin kaya. Shi Dady da ya gani ma cewa yayi sunyi kadan.

Kudi ya bayar a dado kayan da gwala gwalai. Har da Mota Dady ya ce a hada mata.

Momy tace,
“Dady ai ba yanzu za akai kayan ba.”

Dady ya ce,
“Me za’a jira to. Kunga akai kaya ai sa rana kawai komai yazo daga baya.”

Momy ta ce,
“To Dady in haka ne, ai kune masu kai kayan dan na fison maza suyi komai. Mu masha biki daga baya.”

Dady ya ce,
“Zan fadawa su Alhaji Aliyu da Ahaji Abubakar da Dadyn Asma’un ma. Amman ni ban ga amfanin ajiye laifen ba akai musu kawai a huta.”

Kai Mami ta gyada ita ma dai gara akai musun kawai. Amman kuma abu kusan shekara guda.

A cikin satin akai wa su Dady magana kan za a kawo kaya.

Dady cewa yayi baiyi wuri ba tinda abinda saura.

Amman Dadyn Aslam ya ce gara a kawo ai kamar yau ne.

Rana suka saka aka kai komai da komai. Aka sa ranar auren su nan da shekara daya.

Sai kayan lefe da aka kai. Kayan sosai Mami tayi fada wai sun zubo kaya da yawa.

Momy ta ce, to in bata kashewa Asma’u kudi ba wa zata kashe wa. Ta ce,
“Amina kada ki manta fa haka kawai ma kaya nake siyawa Asma’u bare kuma yanzu. Ki daina nuna min ke kika haifi Asma’u to wallahi ji nake kamar ni na haife ta. Kinsan dai uwa daya uba daya ba wasa bane.”

Mami ta ce,
“Haka ne Yaya amman kun kashe kudi da yawa.”

Momy ta ce,
“Akwai kayan fitar bikin su ma da za a aiko dan haka ki zuba idon zuwan su. Suna gun dinki na bada a dinka mata su.”

“To Yaya angode Allah kara girma.”

“Ameen! Zancen kayan kitchen kuma na gama da komai.”

Haka suka gama wayar Mami na kara duba kayan da aka kawo.

Asma’u kuwa duk ji take kamar a mafarki wai kayan lefen ta ne.

Ji take kamar wasa kamar ba zata auri Yaa Aslam ba.

STORY CONTINUES BELOW

Tinda aka kawo kayan ta sanar da Zainab.

Zainab kuwa ranar da ta sanar mata tazo ganin kaya.

Sai zolayar ta take. Asma’u dai sai dai tayi murmushi. Bakin ta ya mutu sai dai dariya ko murmushi.

A kwana kin nan wata shakuwa ce ta kara shiga tsakanin Asma’u da Dady.
Dan yanzu wani lokacin baya zuwa office ko da yaushe tana tare da shi.

Kullum maganar sa daya ce
” *Husnah* ki rike Aslam. Aslam masoyin kine, bani da burin da ya wuce naga auren ku. To in Allah ya nuna min zanyi murna. Haka nan in Allah bai nuna min ba shima zanyi murna dan nasan na bar ki a hannun wanda zai kula dake ko ba aure a tsakanin ku.”

Yayi shiru sunan ta ya kira ya ce,
” *Asma’u* “

Da sauri ta dago kanta. dan Dady baya kiran ta da Asma’u. Murmushi ya sakar mata, ya ce,
” *Husnah* ki kasance mace ta gari a wajen mijin ki. Kiyi koyi da halin Mahaifiyar ki.  Ni Nasan wace, *Husnah* to ina fatan halin da nasan ta da shiki koyi dashi.”

Dady a ko da yaushe bai da maganar sai akan ta rike Aslam. Aslam masoyin ta ne.

Sai kuma nasiha da kullum suka zauna zai na mata kan ta.kula da mijin ta tai masa ladabi da biyayya.

In ko ba haka ba sai ya ce,
” *Husnah* ko na mutu ina son ki kasance cikin min addu’a sannan ki sawa ya’yan ki sona da min addu’a in Allah yayi ba xan ga lokacin ba. Ki kula da ya’yan ki. Ki basu tarbiyya mai kyau. Allah miki Albarka Allah yasa ki a gidan Aljanna Allah ya miki albarka.”

Kullum sai ya nanata mata wanda nan kalaman kullum.
Wani lokacin tare ya shirya musu tafiya suka je dan siyan kayan dakin ta.

In ta nuna abu ya ce, a bata irin sa wanda yafi shi tsada.

Kaya masu tsada da kyau ya siya mata.

Kaya sosai ya lodo aka kawo gida. Daki uku aka dure kayan.

Da Asma’u ta ce,
“Dady kamar an siyo kayan nan da wuri”

Sai ya ce,
” *Husnah* gara na siya tin yanzu ban sani ba ko zan kai lokacin ko bazan kai ba. In na kai Alhamdulilah ga kaya nan sai dai nagan su kamar a sama. in kuwa ban kai ba kinga Mamin ki ta huta sai dai a dauka kawai akai. *Husnah* bana son na mutu da nauyin ku ta wani abu ban muku ba. Na baku ilimi daga arabi har boko to ba abinda zance da Allah sai godiya ko a yau na mutu naci riba dan na ilimantar da ku. Bayan nan na baku tarbiyya wacce kowa yake sha’awar ku ta wannan tarbiyyar taku. To nikan me zance da Allah sai godiya da ya bani ikon daura ku akan dai dai. Gashi duk cikin ku na baku abinda zaku rike kan ku da mahaifiyar ku ko bani da rai. Asibitin can naki ne halak malak dan na rubuta a takardun suma.  Kamfani na na sharada kuma na bawa Buhari. Wadan can gidajen na kwandila na barwa Mamin ku. Ina fatan ko bayan raina kar ku shiga cikin kuncin rayuwa. Alhamdulilah da Allah ya nuna min wannan lokacin lokaci daya nake fatan Allah nuna min shine. Allah ya nunan ranar auren ki.

Kasa tayi da kan ta ta amsa da Ameen.Kalaman Dady ba karamin kashe mata jiki suke ba.
A asibiti kuwa Sosai take da kokari dan duk abinda aka daura ta akai tana yin sa bakin kokari. Ga Yaa Aslam dake kara koya mata.

Sir Sabir kuwa yana yawan zuwa ya gaida Mami ya tafi duk da duk zuwan da zai yi baya samun Asma’u a gida.

To shima yanzu ya bar Makaranta ya koma asibiti.

Son Asma’u sai daduwa yake a cikin zuciyar sa. Sako kuwa kullum sai ya tura mata amman sam ko reply.

Hoton ta shi kadai yake kalla yaji dadi a zuciyar sa.

Amman kullun da ita yake tashi da ita kuma yake kwanciyya.

Haka yau kamar kullum bayan ya koma gida yai wanka ya shirya cikin wani tissue yadi fari.

Ba karamin kyau yai masa ba. Fitowa yayi yaiwa Mamah sallama ya fita.

Kai tsaye gidan su Asma’u ya tafi. Bai da buri da ya wuce yaga Asma’u.

Asma’u tana gida yau dan ta yi targade a garin hawa sama yau duk gidan sun san Asma’u taji ciwo.

Tana jikin Mami sai raki take mata.
“Uhm wayoo Mami kafa ta.”

Mami kuwa sai lallashin take tana mata sannu. Duk ta rasa inda zata saka ‘yar tata.

Dady ya kira shima yana tambayar kafar Asma’u,

Wayar Mami ta bata yai mata sannu sannan ya ce, me take so?

Fada masa tai. Sukai sallama, tana cikin yiwa Mami shagwaba akai yo sallama kan Mami tayi bako.

Izinin shigowa Mami ta bayar. Tana kwance akan kafar Mami tana tsiyayar da hawaye ya shigo.

Da Sallama ya shigo Mami ce ta amsa masa ya shigo ya zauna.

Asma’u dake cinyar Mami tayi juyi ta gyara kwanciyya ta ce,
“Mami kafa ta.”

Shigowa yayi. Mami ta ce,
“A’a Sabir ne?”

“Eh wallahi Mami.”
Ya zauna suka gaisa, Asma’u ce ta kara juyi ta bude idon ta.

Sabir ta gani da sauri ta mike zaune tana daura kan ta a kafadar Mami.

“Ina yini?”
Ta fada tana kamo hannun Mami.

Amsawa yayi ya ce,
“Yau bakije asibitin ba.”

Mami ta kalla. Mami ta ce,
“Wai nan targade tayi shine fa take ta kuka ka ganta nan sai kace ba mace ba.”

Baki Asma’u ta turo, Sabir kuwa Murmushi yayi ya ce,
“An duba kafar?”

Kai Asma’u ta daga. Ya ce,
“Zo naga kafar.”

Kamar baza taje ba ta mike ta karasa inda yake da kyar take tafiya.

Kafar ya duba ya dan taba ta saki kara tana rike hannun sa.

Lumshe ido yayi jin hannun ta mai laushi da ya ji da ta haifar masa da kasala.

Da kyar ya ce,
“Mami gyaran ne bai ba shiyasa.”

Mami ta ce,
“Haba nifa ince tin dazu sai kukan kafar take.”

Kafar ya kama ya ce,
“Mami kuna da man zafi.”

Eh Mami ta fada ta hau sama, kallon ta Sabir yayi. Kanta a kasa ta kasa dagowa ta kalli fuskar sa.

Shi kuwa kallon ta yake kamar ya samu TV sai da yaga kamar zata dago sannan ya dauke kan sa.

Mami ce ta sauko rike da man zafi a hannu ta mika mata.

Amsa yayi yai tofi ya daura hannun sa a kan kafar ya danna ya ja.

Ihu ta saki tana kiran Mami. Kara tayi tai saurin rike hannu.

Hannun sa ya zare daga nata, ya karayin tofin yana jan kafar.

Kuka sosai Asma’u take, Sai da ya tabbatar da kafar ta gyaru sannan ya bar ta.

Akan kafet din falon ta kwanta tana kuka, hannun ta rike da kanta.

Mami ce ta mike ta kawo Sabir lemo da ruwa, sannan ta tahowa da Asma’u ruwa.

Kama Asma’u tayi ta kai ta kan kujera, ruwan ta sha, sannan ta langwabe a jikin Mami sai bacci.

Sai magariba sannan Sabir ya tafi.

Asma’u kuwa sai Magariba ta tashi. Tana tashi taji kafar ta saki.

Mikewa tayi ta haye sama tai alwala tai sallah. Tana idarwa Yaa Aslam ya kira ta.

Kafar ya tambaye ta ta ce,
“Ai Yaa Aslam sai da aka kara gyara min ashe bai gyaru ba.”

“Ayyah sorry my dear da zafi ko. Sorry.”
“Yaa Aslam ai zafi har ba’a magana.”

“Sannu toh!”
Daga haka suka cigaba da hirar su.

Yau takanas Maimuna ta wanko.kafa tazo gun Asma’u.

Dawowar Asma’u kenan daga Asibiti aka zo akace ta yi bakuwa.

Sakowa tayi. Wa zata gani in ba Maimuna ba. Cikin shigar ta, ta riga da zani sai hijab din ta iya gwiwa.

Asma’u da murna ta karasa wajen ta ce,
“Lallai yau Maimuna ce a gidan namu.”

Maimuna tai murmushi ta ce,
“To ina kewar ki ba dole na zo mu gaisa ba.”

Gaisawa sukai sannan Asma’u ta kawo musu abinci suka ci suka koshi.

Wajen Mami ta kai ta suka gaisa sannan tace tafiya zatayi.

Dubu biyar Mami ta bata tana mata godiyar ziyar da ta kawo musu.

Har waje ta rakata dan sai da ta hau Napep sannan sukai sallama ta juya gida.

Wata mota ta gani wacce kwanan nan kusan kullum sai ta ganta a layin ta rasa motar wace, ga bakin glass da take dashi.

Motar ta kuma kalla ta shige gida abinta. Sabir dake cikin motar ya yi murmushi ganin ta kallon da ta tsaya yiwa motar.

Ya tabbata ta fara gane da zaman motar a wajen.

Motar ya tayar ya bar unguwar ransa fari tas yaga abinda yake son gani.

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah. Yau gashi sauran wata uku su Asma’u su kammala karatun su.

Yau ma kamar ko da yaushe da yake asabar ce suna zaune, a falo ita da Dady

Dady ne ya kalle ta ya ce,
” *Husnah* ba abinda kike bukata a kara siya miki.”

Kallon Dady tayi ta ce,
“Dady da sauran lokaci fa.”

“Haka ne, amman na fison komai na gama shi da wuri dan bamu san me lokaci zai bayar ba “

“Haka ne Dady. Amman ni bana bukatar komai.”

“Kin tabbata?”
“Eh Dady.”

“Shikenan na miki transfer din kudi ta account din ki kingan su.”

Kai ta girgiza ta ce,
“A’ah!”

“Ki duba wayar ki, zaki gani. Dan haka ki ajiye in lokacin bikin yazo in kina bukatar kudi ki huta ba sai kin hau tambayar Mami ko Yayun naki ba.”

Murmushi tayi ta ce,
“In ban tambaye su ba ai ina da Dady ko?”

“haka ne! Kina da Ni amman in ina nan ba.”

Murmushi tayi ta ce,
“Dady tafiya zaka yi ne?”

Kai ya girgiza ya ce,
“Ko daya in na mutu nake nufi.”

STORY CONTINUES BELOW

Damuwa ce ta sauka akan fuskar Asma’u sosai har ta kasa furta komai.

Dady ya ce,
“Haba *Husnahn Dady* mene na bata rai dan na fadi abunda dole ne ya faru. Ki daina sa damuwa aranki nasan ko na mutu kina da masu rike ki amana. Amman mutuwa tana kan kowa. Kowa lokaci yake jira da tazo kuma bata jira dauka kawai take. Gara duk abinda zamu nayi muna tunawa da ita. Kuma muna sawa a ran mu a ko da yaushe zaata iya zuwa ta dauke mu. Ki daina damuwa. Allah shi ya tsara mana rayuwar mu kuma in yai niyar mutun ya rayu sai kiga ya shekara nawa ma bai mutu ba. Ina iyayen mu duk sun mutu to muma haka wata rana zamu tafi. Fatan mu da addu’ar mu Allah yasa mu cika da imani kuma Allah yasa can ta fi nan.”

“Ameen!”
Mami ta fada dan duk tana jin abinda suke fadi.

Murmushi Asma’u tayi ta ce,
“Mami kinga Dady yai ta kawo maganar mutuwa. Mami nifa bana son maganar mutuwan nan.”

Dariya Mami tayi ta ce,
“Oh su Asma’u har yau ba a girma ba. To ya zamu Allah ya bamu gadon ta kowa sai ya mutu kuma tunawa da mutuwa yana daura mu akan hanyar Allah yadda zamu gyara kura kuren mu. Ki daina damuwa dan Dady ya kawo magane mutuwa. Yana da kyau ana tinawa da ita.”

“To Mami Allah yasa mu gama da duniya lafiya. Allah ya mana makoma da gidan Aljanna in lokacin yayi.”

“Ameen *Husnah* dan Allah kar ki manta kina sa ya’yan ki suna min addu’a.”

“Insha Allahu. Dady ka daina sa wannan a ranka. Kai ma zaka rayu da su. Su sanka insha Allahu.”

Murmushi Dady kawai yayi, daga haka suka cigaba da taba hira.

Aslam fa ba zama lafiya tinda abin nan ya kara karatowa ya kara burkice ya duk wani plan nashi na auren su ne.

Bai da magana da shirye shirye in ba na auren su ba.

Katon Gidan sa da ya gama dankarawa yasa akai masa fenti aka gyare shi.

Lokaci kawai yake jira.

Preety ce kwance akan kujera gefen ta kawar ta ce, Nene, kallon ta Nene tayi ta ce,
“Haba Pretty ki hakura da yaron nan kina ganin ya kusa yai auren shi ma.”

Mikewa Pretty tayi ta ce,
“Wallahi sai Aslam ya aure ni. Kinji na rantse ko zan yawo tsirara sai na aure Aslam. Ita kuma Asma’u take ko *Husnah* zata gamu dani sai ta dandani irin yadda naji da yake son ta ni baya so na.”

Ta fada tana girgiza kafa, Nene ta ce,
“Pretty ki dai yi a hankali kinsan komai zakiyi akwai karshen sa ko?”

Kallon ta Pretty tayi ta ce,
“Ke dallah ya isa kuma daman ance makashin ka yana tare da kai. In ba haka ba duk yadda muke dake xaki ce na rabu da su ko me? To naki. Wallahi sai na samu Aslam ko da me zai faru daga baya.”

“Allah baki hakuri. Ban fada dan na bata miki rai ba.”
Tsaki Pretty tayi ta koma ta kwanta ranta a bace kamar me.

Ita fa bata da buri da ya wuce ta ganta gata ga Aslam.

Tana son Aslam ko dan gayun sa da iya shigar sa da kyan sa.

Ba abinda ya yafi rudar ta kamar kyan sa.

Ido ta lumshe tana murmushi ta ce,
“Wa ya ga Pretty amaryar Aslam!”

Ta bude ido ta yin shewa. Kallon ta Nene kawai tayi ta dauke kai.

Asma’u ce kwance akan gadon ta tana amsa wayar Aslam.

Sai murmushi take, ko magana ta kasa daga ta ce, ‘Eh’ sai kuma ta ce, ‘A’ah’ sun jima suna hira sanna sukai sallama.

Kwanciyya ta gyara tana ayano gata ga Yaa Aslam anyi auren.

Ido ta rufe da hannun ta alamar taji kunya.

Can ta bude su, ta kurawa saman dakin ido.

Tunanin yadda suka tashi tare da Yaa Asalm ta dinga yi har yanzu da suka girma har a kai maganar auren nasu.

Murmushi tayi kafin ta ce,
“Ni *Asma’u Husnah* in na rasa Yaa Aslam ya zanyi.”

Da sauri ta mike idon ta sun kawo ruwa ta ce,
“Allah na tuba Allah kada ka jarabace ni da rasa Yaa Aslam. Allah ka bani Yaa Aslam.”

Ta koma ta kwana sai kuma kuka sai kace an dake ta. Sosai take kuka. bacci ne ya dauke ta shine aka samu tayi shiru.

Tin lokacin jikin ta yai sanyi ta rasa me yake damun ta.

Karfe sha dayan dare Bayan Mami da Dady sun tafi daki.

Zama sukai Dady yana bata takardun kadarorin da ya mallaka musu.

Mami ta ce,
“Ai Dady da kabar su agunka.”

“A’ah ku rike abinku. Gara ki saba dan in bana nan yazai adana muku.”

Amsa Mami tayi ta ce,
“Alhaji kenan.”

Yai mata murmushi.
Alwala sukai suka kwanta.
Can wajen karfe ukun Dare Dady ya farka da wani irin ciwon ciki.

Ciwon ciki ne, wanda bai taba jin kamar sa ba duk da kwana biyun nan yana yin sa a dadafe a dadafe amman na yau ya banbanta.

Tin yana daurewa har ya tada Mami daga Bacci.

Mami na ganin sa a halin da yake ta mike da sauri tana tambayar sa, lafiya.

Kasa magana yayi. Da sauri Mami ta mike ta kunna fitila.

Ciki ta ganshi dafe dashi, maganin Ulcer, ta dauko ta bashi yasha.

Dan lafawa yayi dan har ya fara bacci sai ya kuma tashi.

Na wannan karan har yafi na dazu ganin wahalar da yake sha yasa Mami ta tafi dakin Buhari ta taso shi.

Da sauri ya biyo bayan ta a durkushe su ka tadda shi ya dunkule gu daya sai juyi yake.

Buhari ya ce,
“Mami bari a fito da mota mu tafi asibiti kawai.”

Ya fita da sauri shi ya kama Dady, Mami kuma ta shiga dakin Asma’u.

Zaune ta same ta akan sallaya, Asma’u na ganin Mami ta mike da sauri ta ce,
“Mami lafiya?”

Mami ta ce,
“Dady ne ba lafiya.”

Da sauri Asma’u tayi waje. Mami ce tabi bayan ta.

Mami ta ce,
“Sunyi waje.”

Kasa ta nufa ta sauka daga benen. Tana zuwa har Buhari ya shigar dashi.

Da sauri ta shiga mota ta zauna kusa da Dady. Tana rike hannun sa.

Mami ce ta shiga ta zauna. Asma’u kuwa ganin halin da Dady ya shiga duk sai ta fita daga hayacin ta.

Kuka take tana cewa,
“Sannu Dady. Sannu”

Duk bayan minti biyu sai ta kara ce masa sannu.

Suna zuwa asibiti aka amshe shi. Sun jima akan sa dan har akai sallar asuba.

Sallah Asma’u tayi ta jima tana wa Dady Addu’ar Allah ya bashi lafiya.

Dady kuwa ganin jikin sa sai wasiya yake bayar wa yana cewa,
“A kira masa *Husnah* ku kira min matata da ‘da na da Auta tah *Husnah* “

Da sauri Dr ya karasa ya kira su. Asma’u na shiga da gudu ta karasa wajen Dady ta rike hannun Dady tana jijigawa tana cewa
“Dady gani. Dady ga *Husnah* ka.”

Dady dake kwance yana fitar da numfashi sama sama, ya kalli Mami da Buhari. Ya ce
“Amina Allah miki albarka. Allah ya baki aljanna madauka. Buhari kai ma Allah maka albarka Allah ya saka a gidan aljanna Allah baka mace ta gari.”

Ya karasa maganar da kyar. Cikin sa ya kara rikewa ya kalli Asma’u ya sakar mata murmushi ya ce,
“Ga *Asma’u Husnah* nan ku kula da ita. Ita ce, yarinyar karama kar ku bar ta tai kuka. Amina Allah miki Albarka. *Husnah* Allah ya miki albarka. Allah baki zuri’a ta gari Allah ya saki a Aljanna.”

Hannun Buhari ya kamo tare da na Mami. Kallon Asma’u yayi ya sakar mata murmushi.

Kalamar shada ya dinga fadi a hankali. Mami ita take tayasa amsawa. Su Asma’u da Buhari kuwa gaba daya sun rikice da kuka.

Can Dady ya saki hannun su idon sa ya lumshe, cikin firgice, Mami ta kwadawa Dr kira.
Dr ne ya shigo ya duba shi. Kai ya girgiza kawai.

Kallon sa Asma’u tayi ta ce,
“Dr ya jikin nashi ne?”

Kallon su Dr yayi ya ce,
“Sai dai kuyi hakuri Allah ya amshi rayuwar sa.”

Asma’u dake tsaye wata juwa taji tana dibar ta. Daga nan duhu ya rufe mata idon ta.

Zubewa tayi a kasa. Mami ma faduwar tayi. Buhari kuwa ya rasa ya za yi.

Da sauri Nurse suka yi wani Daki aka kai Mami da Asma’u aka kwantar da ita. Suna kokarin ceto rayuwar su.

Buhari kuma ya buga waya ya fadawa Uncle Abubakar kanin Dady da uncle ilyasu da kanwar sa.

Sai Momyn Aslam da sauran yan uwa. Cikin minti kadan gida ya cika da jama’a.

Mami da Asma’u kuwa suna Asibiti. Momyn Aslam a lokacin suka taho a jirgi.

Karfe sha biyu aka sa za ayi jana’idar Daddy.

Momyn Aslam na zuwa, ta zarce asibiti. tana zuwa Mami ta farka.

STORY CONTINUES BELOW

Kuka Mami ta saka. Momy ta kama ta ta ce,
“Haba Amina, me yasa zaki kuka ki sani kukan ki ba abinda zai karawa Abban Asma’u. Addu’a ce kadai zaki taya shi da ita Allah yai masa rahama.dan Allah ki daure kar ki bari ki saba da zubar masa da hawaye. Allahn da ya bamu shi yafi mu son shi dan haka hakuri zamuyi muna taya shi da addu’a.”

Sosai Momy tayiwa Mami nasiha mai ratsa jiki.

Kukan ta daina amman fa zuciyar ta kamar zata fashe.

Damuwa karara akan fuskar ta. Da haka suka mike suka yi gadon da Asma’u take.

Tana kwance har lokacin bata san inda kanta yake ba.

Momy ce ta zauna da ita aka tafi da Mami gida dan ganawa da gawar Dady.

Aslam kuwa da suka taho Dadyn sa bai sanar da shi halin da Asma’u ke ciki ba.

Dan haka duk yadda yaso ya ganta ya ga a halin da take ciki bai samu ba.

Momyn sa ya kira ya ke tambayar ta ina Asma’u dan Allah ta fada masa halin da take ciki.

Dan yasan a wannan lokacin Asma’u zata fi kowa jin mutuwar Dady.

Duba da irin shakuwar dake tsakanin ta da shi.

Komai in zatayi Dady ko abu zata yi tace Dady.

Tafi yin shawara dashi akan da Mami. shiyasa yake son yasan a halin da take ciki.

Haka ta ce masa tana asibiti in ta dawo zata duba masa halin da take ciki. Amman ya kwantar da hankalin sa tana lafiya.

Suna cikin waya aka kawo Mami gida. Da sauri ya karasa gun Mami.

Duk tausayin ta ya kama shi. Shi ya kamata suka shiga cikin dakin da aka kwantar da Dady.

Addu’a Mami tai masa sosai, sannan aka zo aka dauki gawar ta shi.

Duk yadda taso kar tayi kuka sai da hawaye ya zubo a idon ta.

Kanwar Dady ita tazo ta shiga ciki da ita.

Jama’a sun cika gidan makil da mutane. kowa sai mutuwar Dady yake ji, Dady mutumin kirki me kawaici da Hakuri da taimako.
Dan haka kowa abin alherin sa yake fada da masa addu’a.

Mami karfin hali kawai take domin tasan ta rasa farin cikin ta. Ta yi asara da baza ta taba maida kamar ta ba.

Dan rashin Dady a garesu ba karamin gibi bane.

Ana ta amsar gaisuwa Mami kuwa ta yi nisa cikin tunani, ga Asma’u, ba wanda tafi ji.kamar Asma’u.

Asma’u kuwa da magariba ta farfado. Tana ta shi tasa kuka ina Dadyn ta.

Sai kuma ta kuma fashe wa da Kuka ta ce,
“Momy dan Allah ku kaini wajen Mami da Dady dan Allah Momy Dady bai mutu ba ko? Momy kada kice min ya mutu.”

Sai wani kukan Momy ma sai da tayi hawayen dan ba karamin tausaywa Asma’u tayi ba.

Allura Dr ya karai mata ganin tana neman fita daga hayyacin ta.

Sai da Dady yai kwana uku aka sallamo Asma’u, gida suka taho da Momy dake wajen ta in kaga Asma’u zaka ga ta rame sosai sai kace wacce ta dade tana jinya.

Aslam da tare suke jinya a asibiti shima duk ya rame ya yi duhu.

Tare suka dawo, Asma’u na zuwa gida tayi wajen Mami, ta rumgume ta tana wani kuka mai ban tausayi.
Kuka sosai suka yi sannan Mami ta dago ta tana kallon ta.

Ta rame har abin yai yawa.
Buhari ya ce,
“Mami ga Asma’u nan bata cin abinci ko tea taki amsa ta sha.”

Kai Mami ta girgiza ta jata jikin ta tana shafa bayan ta ahankali a hankali.

Zainab da tinda akai mutuwar take zarya daga asibi zuwa gidan yau ma tana gidan.

Dakin Asma’u suka shiga, Asma’u da ta kasa daina zubar hawaye daga idon ta.

Abinci Yaa Buhari ya dauka ya kai mata ya ce taci amman sam taki ci.

Yaa Asalm ya fadawa. Aslam da kansa ya shigo gidan ya shiga har dakin ta ya tadda ta kwance akan gado.

Zama yayi a gefen ta ya dago ta. Tana ganin shine ta fada jikinsa tana sakin wani kuka mai ban tausayi.

Rumgume ta yayi yana lalashin ta da kalamai masu nuni ga ban hakuri har tayi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa.

A hankali ya dinga bata baki har ta yadda ya dinga bata abinci a baki.

Ci take tana yamutsa fuska dan ba dadin sa take ji ba. Har wani daci yake mata a baki.

Idon ta kuwa ya kasa tsayar da hawaye, a haka ta dan ci ta ce ta koshi.

Tin daga lokacin kullum Asma’u na gefen Mami, dan ko bacci ta koma kullum tana gefen ta.

Kullun kuwa Asma’u da zazzafi take kwana ta tashi. Amman da Mami ta ce zata bata da lafiya zata ce ta ji sauki.

Ranar bakwai kuwa Asma’u kamar me kuka ta dinga yi dan har numfashin ta daukewa ya dinga yi.

Yaa Aslam da Sir Sabir su suka tsaya akan ta.

Da kyar suka samu numfashin ta ya dawo dai dai.

Bayan bakwai kowa ya watse sai Momy da Aslam.

Suma ana yin kwana goma Momy ta fara shirin tafiya. Hakuri sosai ta dinga bawa Mami.

Sannan ta zaunar dasu gaba daya, ta kara basu hakuri sannan ta bawa Mami kudi masu yawa.

Haka Momy ta tafi gidan ba dadi daga Buhari sai Aslam da Mami da Asma’u.

Asma’u da ta zama shiru shiru ko magana batayi. In anyi abu sai dai ta kalli mutum ta dauke ido.

Aslam kuwa kullum ya zauna sai ya san yadda zai sa tayi dariya.

Aslam shike sa Asma’u yin hira ta dan sauko.

In kuwa ba haka ba sai dai ta zauna tai ta zubar hawaye.

Yau ma kamar kullum tana kwance akan gado, ba abinda take sai zubar hawaye tana tunanin Rayuwar su da Dady.

Murmushi ta dan saki sai kuma, kuka da ya kwace mata.

Aslam dake tsaye a kofar ya na kallon sanda tai murmushi sannan kuka yazo ya karaso gun ta da sauri.

“Haba *Husnan Dady* yanzu haka zamu ta rayuwa kenan kullum kin ki ki sake, kina tunanin Dady zai ji dadi a halin da kike ciki. Haba *Husnah* a ko da yaushe Dady bai da magana da ya wuce yasan ko bayan ransa *Husnah* baza tai kuka ba saboda yasan damu. To menene amfanin namu da mu na nan zaki na kuka. Haba *Husnah* dady ba abinda yake nema gun ki sai addu’ar ki. Dan Allah ki daina wannan kuka. In ba haka ba ni bazan iya jurar ganin kukan ki ba zan tafi in hakan kike so.”

Hawayen ta, ta goge ta ce,
“Na daina Wallahi Yaa Aslam na daina. Kar ka tafi ka barni.”

Murmushi Aslam yayi ita kuwa duk da hawayen da take yi gogewa wani ne yake kara daduwa.

Jikin sa ya jata yana lallashin ta.

*Hmmm kulli Nafsin xa’ikatul Maut.*
*wannan haka yake*

*Karki kuce saboda na sa Dady ya mutu. Haka rayuwa take, muma wata rana sai mutuwa.*

*Hmmm kuyi hakuri haka tsarin littafin yake. In ba haka ba wani abu bazai faru ba. Nagode*

*Nusaiba S Indabawa*
Ki daure ki karanta littafin nan.

Lol wai ita indai nayi littafi wani ya mutu bata karantawa saboda tausayi.
*To sisto ki karanta dan nasan kina son karantawa. Mutu a kuma dole ce. Ke yanzu ina Dady, ya rasu. Sai dai muyi masa addu’a Allah ya kara masa rahama Ameen!*
ALLAH KA JIKAN DUKKAN MUSULMAI. KA JIKAN YAN UWAN MU, DA KAKANNIN MU, DA IYAYEN MU DA YAYUN MU DA KANNEN MU DAMU KAN MU IN TAMU. TAZO

AMEEN!

Aslam yayi na mijin kokari wajen sauyawa Asma’u rayuwa.

Dan kullum cikin daukar Asma’u ya kai ta wajen shakatawa ko ya kai ta shopping.

Banda fina finen da yake siyo mata na ban dariya.

Sai da yayi wajen wata biyu a kano sannan ya koma saboda wajen aikin sa.

Duk da tafiyar sa duk wata kulawar da yake bata bai daina ba sai daduwa dda ta karayi.

Sabir kuwa har Mamah ya kawo gida tai wa su Mami gaisuwa.

Haka Maryam ma takanas ta zo kano dan Asma’u. Asma’u ma taji dadi.

Haka nan Maimuna ma tazo tai mata ta’aziyya da yan department din su.

Da kyar Asma’u ta koma asibiti, ta cigaba da rayuwar ta.

Sabir ma yana zuwa akai akai yana duba su ya gaida Mami.

Pretty ce zaune kamar an mata allura ta mike ta dauki ATM din ta da kudi ta zuba a jaka.

Fita tayi ta tsaida mai Napep ta shiga. Tasha kai tsaye ta nufa.

Tana zuwa ta hau motar Niger.

Suna sauka Pretty ta tafi hotel.

Sai da tai bacci ta huta tai wanka sannan ta ci abinci.

Mikewa tayi sai kace wacce zata tashi sama.

Fita tayi daga hotel din ta tsaida mai napep. Yana tsayawa ta fada masa inda zata sannan ta hau suka tafi.

Yana tsayawa ta biyashi kudi sannan ta shige wajen.

Waje ne kamar jeji haka ta kutsa kai. Sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta karasa wajen

Yar bukka ce, shi kuma yana zaune a gefen ta.

Jikin sa ba komai sai ganye da yayi tufa da shi.

Kalar fatar jikin mutumin baka kirin, haka nan jikin mutumin sai tashin wari yake.

Idanun sa jajir kansa gashi ne yayi yawa dan sai a iya kitso ma akan shi.

Yana zaune gefen sa tukwane ne. Tin da Pretty ta karasa wajen yake binta da wani fiti nan nen kallo.

To kayan dake jikin ta ne kai ba zakai tunanin yar musulmi bace.

Zama tayi nesa dashi dan ita ma tana kyamar sa.

“Sannu boko na kan tudu.”

Ta fada tana kallon sa.

Bakin sa ya bude wanda hakoran dake ciki sun zama ja dasu.

“Kinji shiru ko?”

Ya tambaye ta.

Kai ta daga masa, murmushi yayi ya ce,

“Eh kamar yadda na fada miki aikin yana da wahala ne,”

“Toh! Malam……”

Tsawa ya daka mata. Ya ce,

“Kar ki kara ce min Malam.”

“Dan Allah ka taimaka min wallahi zuciya ta zata iya bugawa in ban samu Aslam ba ka taimaka min.”

Kai ya daga ya ce,

“Na fada miki aikin yana da wuta. Dan Aljannin da zai miki aikin ya ce, sai ya tara da ke tukkuna.”

STORY CONTINUES BELOW

Ido ta zaro ta ce,

“Aljannin.”

Kai ya gyada mata. Ya ce

“kar ki damu ki kwantar da hankalin ki. Ta jikina zai yi amfani dake,”

Ya fada yana lashe lebe. Kallon sa tayi a zabure ta nuna shi da yatsa, ta ce,

“Kai!”

Kai ya gyada ya ce,

“Eh ni.”

Wani kallo ta watsa masa ta mike tabar wajen.

Tana fita tayi gidan kawar ta wacce ta hada ta da bokan.

Tana zuwa ta zube mata abin da ya faru, dariya kawar tata ta hau yi ta ce,

“Amman wallahi har kin ban kunya, dan aljanni ya neme ki shine me?”

“Ke dallah shine fa zai kusance ni. Haba kinsan fa ya yake, warin jikin sa ma kadai ya ishe ni.”

Pretty ta fada tana toshe hanci sai kace a gaban sa take.

“Kinga ki ajiye duk wannan a gefe wallahi in har yayi abunda ya bukata ko to bukatar ki ta gama yi. Kin samu Aslam dan shi da wannan kwailar yarinya har abada dan nasan ko kallo baza ta ishe shi ba.”

Kallon ta Pretty tayi. Ta cigaba da magana.

“Muma duk Boka yayi abinda kike tsoron yi dashi. Kuma ya kusan ce kinki zaki ji abinda baki taba ji ba.

Kallon ta Preetty tayi a ranta tana son samun Aslam amman kuma tana kyamar ta yadda zata je wajen Boka.

A haka kawar tai ta zuga ta har taji zata je dan biyan bukatar ta.

Gida ta tafi tana tunanin taje ko kar taje.

Wata zuciyar na cewa taje wata kuma tana hanata zuwa.

A haka ta kwana da tunanin wata haryar da zata mallaki Aslam.

Ganin bata da wata hanya yasa ta amince da zata koma gun sa.

Mikewa tayi ta shiga wanka ta shirya cikin shigar banzar da ta saba yi.

Abin hawa ta hau ya kai ta inda zata je. Ya dire ta tayi cikin jejin.

Yana zaune kamar ko da yaushe, yana ganin ta ya saki fara’a.

Karasawa tayi tana jin damuwar zuwan nata. Kallon ta yayi ya ce,

“Ya kin amince ne?”

Kai ta gyda masa dariya yayi ya ce,

“To ai kin kyauta. Ki shiga daga cikin zan kira shi in zo zaki ganshi.”

Mikewa tayi tai ciki. Kallo ya bita dashi yana lashe leben sa.

Can ya mike yayi cikin dakin da ta shiga yana wata irin tafiya.

Sun dauki a kalla fin awa hudu zuwa biyar sannan Bokan ya fito yana gumi. Wajen zaman sa ya zauna.

Can kuma sai ga pretty nan ta fito. Fuskar ta tai jajir da ita.

Kallon malamin tayi ta bar wajen. Gida ta je ta dade tana dirje jikin ta sannan ta fito ta kwanta a kan gado.

Ido ta lumshe tana cewa, Amman Malamin nan yayi. Dama ace Aslam ne.

Ta yi juyi akan gado ta ce,

“Asma’u kike ko Husnah ina tausaya miki duk randa na samu Aslam kin mutu.”

Cikin ta taji yana kukan yunwa ta mike ta fita gari dan samun abunda zata ci.

Asma’u ce zaune a garden tana sanye da threequatern wando da riga karama a jikin ta. Sai hijab din ta da yake har kasa. ta rafka uban ta gumi. Ba wanda ta tino in ba Dady ba.

Hawaye taji yana bin fuskar ta da sauri ta goge hawayen tina maganar Aslam da ya ce,

” *Husnah* dan Allah kimin alkawarin ba zaki kara kukan akan Dady ba sai addu’a. wallahi kukan ki yana taba zuciya ta kamar yadda nasan ki cikin wani hali inda nima nake tsintar kai na a ciki. Ki daina kuka dan Allah ko bayan ido na kar kiyi kuka. In kuwa kikai kuka bazan taba yafewa kai na akan amanar ki da Dady ya bani ba.”

Murmushi ta dan saki na tunawa da Yaa Aslam. Tana da tabbacin Ya Aslam din ta zai rike ta amana dan tasan yana daga cikin masoyan ta na farko a duniya.

Duk abinda yasan zai sa ta farin ciki shi yake buri shi yake mata. Ko baya son abu in tana so zai san yadda zai yi ya so abin.

Sabir da yana tsaye yana kallon irin murmushin da take sai yaji wani dadi.

Hawaye kuma ya dawo zubo mata tina in kuma ta rasa Aslam fa.

Kuka sosai take yi har Sabir ya tsaya gaban ta bata ganshi ba.

Handkerchief ya mika mata. Amsa tayi tana goge hawayen fuskar ta ba tare da ta ga wanda ya bata ba.

Zama yayi daga gefe ya ce,

“Haba *Husnah* mene na kuka kuma. Ki dauki hakuri kowa hakuri yake ki na wa Dady addu’a.”

Kai ta daga tare da kallon sa. Shima kallon ta yake yana sanye cikin dark blue din wando da bakar riga. Sosai yayi kyau.

Murmushi ya sakar mata. Itama murmushin ta sakar masa.

Hira ya fara janta yana bata abin dariya. Sun jima suna tare sannan suka shiga wajen Mami.

Mami dake zaune rike da casbaha, tana ganin Asma’u ta gane tayi kuka.

Murmushi tayi ta mika mata hannu tayi gun ta. Ta ce,

” *Asma’un Dady* kukan ki kayi ko?”

Kai ta girgiza tana murmushi. Murmushin itama Mami tayi ta ce,

“Hakuri dai zamu nayi. Muma Allah bamu wucewa lafiya.”

“Ameen!”

Suka amsa.

Hira Sabir da Mami suke ita kuma tana can a whatsapp suna chat da Yaa Aslam.

Hakuri yake kara bata tare da kwantar mata da hankali.

Suna yi tana satar kallon Sabir kamar yadda shima yake satar kallon ta.

Ita dai Sir Sabir yana burgeta, akwai shi da saukin kai ga fara’a.

Haka nan nature sa na burgeta. Ido ta lumshe sai kuma fuskar Aslam ta bayyana yana mata murmurshi

Itama murmushin tayi ya zame ta kwanta akan kujera.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *