RAYUWAR ASMAU CHAPTER 9

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 9

Kwanan Pretty biyu sannan ta koma gun malamin ta.

Tana zuwa ya hau mata albishir da aikin ta yayi kamar me. Murna ta farayi.

Malamin ya ce,

“Sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba. Shine ki kula sosai sannan kafin aure kiyi kokari ki dawo dan akwai wani abu da za a karayi miki.”

Godiya tayi masa, ya ce,

“Kar ki damu da kin je gida zaki tadda abin mamaki.”

Kudi masu yawa ta zube masa ta tashi tana masa godiya shi kuwa a ransa tinda ya kusan ce ta yaji a duniya ba wacce yake so kamar ta.

Yayi Alkawari da duk daren dadewa sai ya mallake ta ta zama tasa gaba daya.

Ya bata dama ne ta je wajen Aslam din amman yayi alkwarin shi da kansa zai raba su dan ya same ta.

Ita kuwa Pretty gida tayi tana ta murna.

**********************************************

Aslam ne zaune a dakin sa yana waya da Asma’u.

Duk wayar da suke kara kwantar mata da hankali yake, sosai take samun nutsuwa in tana tare da Aslam.

Sai dai kwanan nan tana yawa mafarkai akan Aslam, wanda in ta zauna ita kadai tai ta kuka ta rasa kukan mene, amman tasan tana tsoron rasa Aslam ne.

Kwanan nan ta dan rame ta kara rage walwala duk da yadda take so ta sake ko dan tana sawa Mamin ta nishadi amman kasawa take.

Bama in da dare bayan sun ci abincin dare. Ba wanda yake fado mata sai dady shi yasa da sauri take tafiya daki ta sha kuka.

In ba Aslam ne ya kira ta ya kwantar mata da hankali ba.

Dan Aslam ko ta chatting yana gane a irin mood din da take bare kuma yaji muryar ta.

Aslam dake kwance idon sa lumshe yana yiwa Asma’u tadi mai dadi da sanya ta nishadi har yaji tayi bacci.

Wayar ya bari a kunnen sa yana jin yadda numfashin ta ke sauka a hankali a hankali.

Yana kwancen nan bai tashi yayi alwala yayi shirin bacci ba bare addu’a bacci ya dauke shi.

Ya jima yana baccin can kuma sai ya mike.

Dakin ya fara kalla. Ba abinda yaji yana so ya ji ko ya gani in ba Pretty ba.

Abokin sa Mohd da Pretty tasan shi ta dalilin sa ya kira a waya.

Abokin sa dake kwance yana bacci dan lokacin wajen karfe uku ne yaga kiran sa.

Dauka yayi dan shi ya zata ma ba lafiya ba.

Aslam ne ya katse masa tunanin dalilin kiran sa ta hanyar ce masa,

“Mohd dan Allah number Pretty nake so yanzun nan.”

Mohd cire wayar yayi daga kunnen sa ya kara kallon me kiran nasa.

To kawai ya fada ya kashe wayar. Mamaaki yake me Aslam zai yi da number Pretty bayan ko sunan ta bai son ji bare wani abu da ya shafe ta.

Baki ya tabe ya ce,

“Shi yasani.”

Number ya tura masa ya koma bacci. Aslam kuwa yana ganin number yai ta kira amman a kashe.

Ranar har asuba bai kuma ba yana ta kiran wayar. Kiran sallah shi ya sa ya hakura ya mike yai wanka yai alwala ya tafi massalaci.

STORY CONTINUES BELOW

Yana fita Asma’u ta kira saboda jin bai kira ta ba.

Amman shiru bai dauka ba. Tayi tsammanin yaje masallaci shi yasa ta bar kiran nasa.

Aslam kuwa yana dawowa daga massalaci ko ta kan wayar sa bai bi ba. Ya shiga bayi ya kara wanka ya fito ya shirya cikin Wando baki sai riga ruwan kasa.

Yayi kyau dashi. Turare ya dauka ya feshe jikin sa dashi.

Falo ya fita ya tadda Momy na hada musu wajen karyawa.

Gaisawa suka sannan ya mike ya fita kamar wanda ake hankada shi.

Sauri kawai yake yaje yaga Pretty, gudu yake sosai har ya karasa gidan su,

Horn yayi aka bude masa gate din fitowa yayi bayan yai parking ya akai a kira masa Pretty

Wanda ya aika cikin gidan yazo ya ce, masa Pretty bata nan.

Cikin mota ya koma ya zauna. Wani iri yake jin sa. Ranar ji yake in har bai ga Pretty ba bazai iya rayuwa ba.

Duk ransa yana son yasan halin da Asma’u take ciki da ya fara tunanin Asma’u sai kuma Pretty ta fado masa.

Duk da Asma’un ba gushewa take a zuciyar sa ba amman ya rasa dalili.

Haka ya yini a harabar gidan su Pretty sallah ce kadai ke tayar da shi.

Da ya dawo zai tambaya ko Pretty ta dawo. Cikin lokaci kan kani ya canja ya koma wani iri.

Ranar sai karfe goma ya koma gida bayan ya tabbatar da Pretty bata nan.

Jiki a salube ya dawo gida. Momy kuwa da hankalin ta ya gama tashi na ganin tin safe basuyi waya da shi ba kuma in ta kira ba ya dauka ya daga mata hankali.

Yana dawowa ta hau tambayar ko lafiya. Ce mata yai bai da lafiya, wannan yasa ta kai shi daki ta hada masa ruwan wanka sanna ta kai masa abinci.

Wankan yayi ya ci abinci. A ransa yana tunanin yau ko a wane hali Asma’u take.

Har ya mike zai dauko waya ya kira ta kuma sai ya fasa ya koma ya kwanta.

Tunanin sa daya Pretty. Haka ya kwana ya tashi. Dan ko baccin kirki bai samu yayi ba.

Washe gari ma tin safe ya kuma dirar wa gidan su Pretty.

Pretty kuwa tana hanya dawowa ggida ana sallah la’asar aka kawo ta kofar gidan su.

Motar Aslam ta gani a cikin gidan su. Matsawa tayi wajen motar ta kalla ta kuma kalla.

Tabbas motar Aslam ce kenan da gaske dai abinda Malam ya fada mata.

Wani tsalle ta doka ta yi cikin gidan bangaren ta, ta shiga tai wanka ta fito tayi falon gidan.

Mahaifiyar ta ce zaune cikin shigar kasaita. Tana kallo.

Pretty ce ta shigo ta fada jikin ta. Kallon ta Mahaifiyar tata tayi ta ce,

“Pretty ni ai nayi fushi kwana biyu ko neme na bakya yi.”

Kai ta dan sosa ta ce,

“Sorry Mommah!”

“Shikenan waye ne tun jiya yake zaryar neman ki a gidan nan.”

Kallon mahaifiyar tayi ta ce,

“Wani ne, shine wanda nake son aura.”

Murmushi uwar tayi ta ce,

“Kai Alhamdulilah amman naji dadi amman na bar shi a waje tin jjiya yake zarya fa.”

“Kar ki damu Mommah nima nasha wahala akan sa.”

Mommahn ta ce,

“Ah ai kam kema gasa abin ki.”

Pretty ta mike ta ce,

“Kisa a kawon abinci bangare na.”

Ta fice. Dakin ta ta nufa ta zauna. Wayar ta ta dauko ta kunna.

Text din Aslam ne suka dinga shiga wayar.

Sai da ta gama karantawa taga yadda ya hauka ce sannan ta sheke da dariya.

Kiransa tayi. Lokacin yana jikin motar sa dan bai dade da dawowa daga massalaci ba.

Yana ganin kiran ta yai saurin dauka. Ya ce,

“Haba Baby na ina kika shiga ne haka?”

Murmushi tayi ta ce,

“Kana ina ne?”

Gidan ya kalla sannan ya ce,

“Ina cikin gidan ku fa.”

“Oh ai ban sani ba yanzu na dawo. Ka sa a nuna maka site dina sai ka shigo.”

Nan da nan ya tambaya aka nuna masa ya nufi wajen da sauri dan bai da abinda yake burin gani kamar Pretty.

Tana zaune a kan kujera gaban ta kayan abinci ne kala kala.

Yana shigowa ta mike ya mata masifar kyau. Yana sanye da Brown wando sai milk din riga.

Wajen sa ta nufa ta kamo hannun sa. Murmushi ya sakar mata ya karaso cikin dakin.

Zama sukai a kujera mai daya ta zauna akan cinyar sa.

Fuskar sa take shafawa a hankali kafin ta daura kan ta a kkirjin sa.

Aslam kuwa wata ajiyaar zuciya ya dinga saukewa dan ko ba komai ya samu abinda ransa ya matsa masa ya zo ya nema.

Duk da zuciyar sa tana can ga Asma’u amman wani bangaren tunanin sa yana ga Pretty ya rasa dalili.

Kallon sa ta danyi ta ce,

“Wai da gaske kai ne?”

Kallon ta yayi ya ce

“Ga alama nan kuwa.”

Kai ta gyada ta ce,

“Ya batun soyayyar mu.”

Wani murmushi ya saki ya ce,

“Sai yadda kika ce.”

“Da gaske?”

Ta tambaye shi tana wasa da sumar kan sa.

Kai ya gyada mata. Murmushi tayi ta ce,

“Aure nake so muyi nan da sati biyu.”

“Sati biyu kawai “

Ya tambaye ta.

Kai ta gyada masa, ya ce,

“An gama. Nawa ne zai ishe ki siyan kayan lefe da komai da komai.”

Kai ta dan daga ta ce,

“Ka bari zuwa gobe zan duba.”

“Shikenan! Ki fada min goben fa. Dan nima na matsu.”

murmushi tayi ta rumgume shi.

Shima rumgume tan yayi. Kiss ta fara masa, jiki da jini tini shima ya hau biye mata.

Kiran sallah da yaji ana yi shi yasa yai saurin tsayawa daga abinda yake yi.

Mikewa yayi. Kallon sa tayi ta ce,

“Lafiya?”

Nuni yai mata da waje sannan ya ce,

“Kiran Sallah ake.”

Tsaki tayi ta ce,

“Ni na zata ma wani abun ne.”

Ta koma ta zauna Kallon ta yayi yai murmushi ya ce,

“Bari naje na dawo.”

Ya fice ranar dai har goma suna tare da Pretty da kyar ta kyale shi ya tafi.

An Kar6o Daga *Aisha (ra)* Tace: Na Tambayi *Manzon Allah(ﷺ)* Game da Waige a Cikin Sallah? Sai Yace: *”Wata Fisga ce Shedan Yakeyi a Cikin Sallar Bawa”*. (Bukhari)._

_A Hadisin *Tirmizi* Kuma Ya Ingantashi: *”Kashedinka da Yin Waiwaye a Cikin Sallah, Domin Halaka ne, Idan Ya Kasance Babu Makawa Sai Kayi, To Kayi A Cikin Sallar Nafila”*._

Yana shiga gida ya tadda Momy zaune a falo.

Kallon sa tayi ya karasa gun ta.

Gaishe ta yai ya dan zauna. Kallonsa tayi ta ce,
“Aslam lafiyar ka kuwa. Kwana biyun nan ina kake zuwa da har kake kai dare haka a waje.”

Kai yayi kasa da shi. Dan ka idar sa da anyi isha’i yana gida.

“Ba magana nake maka ba. Ka fadan inda kake zuwa.”
Shiru ya karayi.

“Wallahi Aslam zan batar maka in baka fadan ina kake zuwa ba.”
kai ya dan sosa ya ce,
“Daman ina son nai miki maganar ne, wajen wata budurwa ta wacce nake son aura nake zuwa.”

Tsaki Momy tayi ta ce,
“Wai ni sa’ar ka ce da kake min wasa bayan kasan ba lokacin wasa bane yanzu.”

Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara.
“Wai ba magana nake maka bane, ko so kake na kira mahaifin ka na fada masa.”

Kai ya girgiza ya ce,
“Momy da gaske nake.”

Momy ta ce,
“Da gaske kake kamar ya?”

Kai ya sosa ya ce,
“Momy daman mun gama maganar aure da ‘yar gidan tsohon ministern man fetur ne akan nan da sati biyu zamuyi aure.”

Kallon sa Momy take tama kasa cewa komai.

Dagowa yayi ya kalle ta, ta ce,
“Eh ka dago ka kalle ni ai nifa bangane mai kake fadi ba.”

“Eh Mami yar sa Pretty ita nake so nake son muyi aure nan da sati biyu dan har nace ta fadawa Mahaifin ta ma.”

Kallon mamaki Momy kewa Aslam dan gani take kamar ba Aslam din ta ba.

Aslam din ta mai hankali da nutsuwa amman ji wannan inda yake mata wani shirmen zance.

Amman kuma fa zancen kamar akwai kamshin gaskiya.

Da kyar Momy ta iya bude baki ta ce,
“Asma’un fa?”

Kai ya girgiza ya ce,
“Momy ni yanzu ga wacce Nake son na aura.”

Kallon sa Momy tayi ta ce,
“Aslam kana cikin hayyacin ka kuwa.”

Kai ya gyada mata. Momy ta ce,
“Me ya hada ku da Asma’un taka.”

Kai ya girgiza ya ce,
“Wallahi Momy ba komai.”

“Amman saboda me zakai mata haka.”
Kallon Momy yayi ya kasa bata amsa.

Shima bai san abinda yake fadi ba. Ji yake kamar bashi yake maganar ba.

“Aslam kasan me kake fadi kuwa. Asma’un taka kake son ka ce min ka fasa aura ko kuwa.”

Kai ya gyada mata. Momy ta ce,
“Inna illahi wainna illahir rajiun.”

Sai da ta fada sau uku sannan ta dago ta kalli Aslam sosai dan taga ko ya fara shaye shaye ne.

STORY CONTINUES BELOW

Har mikewa tayi tana shinshina sa da duba sa.

Ganin ba alamar shaye shaye yasa ta kuma mike tayi wajen sa tana duba shi.

Tabbas Aslam din ne dai ‘dan ta. Komawa tayi ta zauna tana rike kan ta.

Sanna ta dago ta ce,
“Wallahi Aslam ba da yawu na ba a auren da kake son kayi. Ba ruwana kaje ka nemi wata uwar bani ba.”

Ta mike ta bar masa falon. Mikewa yayi jiki a sanyaye yayi dakinsa.

Daki ne guda kai kace dakin wata amaryar ne. Babu abinda babu a ciki.

Kan kujera ya fada, yana dafe kan sa. Ya zai yi.

Wayar sa da tin dazu take kara ya dauko ya duba.

*Soul mate* shine abinda ya bayyana akan wayar.

Ajiyewa Yayi ba tare da ya dauka ba. Dayar wayar sa ce ta hau ringing itama yana dauka naga *My* ya bayyana akai.

Shima ajiyewa yayi bai dauka ba. Haka ta gama kiransa amman bai dauka ba.

Shi kansa wani zafi yake ji, baya son damuwar Asma’u amman mai yake damun sa yake neman sa ta a damuwa.

Dan ya tabbata Asma’u tana cikin damuwa fiye da tunanin mai tunani.

Har ya dau wayar zai kira sai kuma ya fasa ya kira Pretty waya sukai sosai. Dan har sha biyu suna waya sanna sukai sallama yai wanka yazo ya fada gado.

Shi kansa yasan bai da lafiya. Dan rashin Asma’u ba karamin tashin hankaline a rayuwar sa ba.

Pretty kuwa tana can har an fara shirye shiryen aure.

Dan komai da take bukata tai masa list din su.

Haka nan kudaden da za a kashe wajen taro duk ta masa suma list
Sosai ta tsuga kudi dan komai na karya take so yayi mata.

Waya kowa tayiwa kawayen ta kan cewa nan da sati biyu bikin ta. Dan har kalar ankon da za a sak”a ta fitar dashi.
*********************************************************************
Asma’u ce kwance, akan gadon kai daga ganin ta kasan ba lafiya ba.

To rabon ta da abinci kwana biyu kenan.

Hankalin ta ya kasa kwanciyya da rashin kiran da Yaa Aslam bai mata ba gashi ta kira shima bai daga ba. Ta kira Momy ma ita ma bata daga ba.

Tana kwance idon ta jajir dan rabon ta da bacci shima yau kwana biyu ne.

Ga wata faduwar gaba da take yawan yin ta. Ta rasa ta me ce.

Ido ta lumshe hawayen da ya taru suka zubo akan fuskar ta.

Juyi tayi tana me fashewa da kuka. Ba wanda ya fado mata sai Dady.1

A duniya ta san indai Yaa Aslam ya na nan ba zatai kukan mutuwar Dady ba.

To yanzu in Yaa Aslam din ya mutu tayi yaya kenan. Ko in ya barta tayi ya kenan.

Tana tunanin taji an bude kofa. Da sauri ta goge hawayen idon ta.

Yaa Buhari ne, ya shigo hannun sa dauke da Leda.

Kan gadon ya karasa ya dan zauna kafin ya dago ta.

Jikin ta ya taba yaji har lokacin da zazzabin.

Kallon ta yayi ciki tausayawa ya ce,
“Sannu Asma’u. Ya jikin?”

Murmushi yake tai masa ta ce,
“Yaya nifa yanzu normal nake ji na.”

“Da gaske?”
Ya tambaya yana mata murmushi shima.

STORY CONTINUES BELOW

Kai ta gyada masa. Murmushi yayi ya mika mata ledar hannun sa ya ce,
“Ungo wannan to ki daure kici kinji Kanwata.”

Amsa tayi idon ta na kawo kwalla. Ta ce,
“Tnc bro.”

“Ina zuwa. Akwai wani suprise da zan miki “
Ya mike ya fita.

Bayan sa ta bi da kallo yana fita ta fashe da kuka.

Mami ce ta shigo dakin da yake Buhari bai rufe kofar ba bataji shigowar ta ba.

Mami ce ta dago da kan ta ce,
“Oh Asma’u ke haka zaki ta ciwo da kuka. Wai yaushe zaki daina kuka in baki da lafiya.”

Hawaye ta goge tana son kawar da damuwar ta.

Mami ta kalle ta sosai ta ce,
“Bayan zazzabin me yake damun ki. Dan ga damuwa nan fal a fuskar ki. In akan Dady ne, dan Allah ki rage damuwar nan Amsa’u kina masa addu’a kinji.”

Kai ta gyada.
“Yauwah koke fa, *Husnahn Dady* “
murmushi tayi.

Mami ta dauki ledar da Buhari ya kawo mata ta bude.
Murmushi tayi ta ce,
“To ai ke sai ya narke”

Ta fada tana zaro mata ice cream din daga leda. Daya ta mika mata ta mika.mata kullin naman da ya siyowa kowa nasa.

A firij ta zuba ragowar ice cream din. Sannan ta ce,
“Ina Buharin?”

“Yanzu zai daw…….”
bata karasa fadi ba sai gashi ya shigo da sallama.

“Au ina kaje?”
Mami ta tambaye shi.

Kallon Asma’u yayi ya ce,
“Daki fa naje.”

Zama yayi a gefen Asma’u ya ce,
“Sis an sa ranar aure na da Zainab fa dan kiji tare za ayi da naku.”

Yana fadar haka taji kirjin ta ya buga. Dan har sai da ta dafe shi.

A zahirin gaskiya taji dadi amman kuma bata san me ya haifar mata da faduwar gaban ba.

Murmushi tayi ta ce,
“Kai Alhamdulilah. Amman kuma shine ba a fada min ba.”

“Sorry ai kece naga bakya jin dadi.”
“Ni ba wani nan Yaya ka sani fada min zai yi sanadiyar samun sauki na. Zan hadu da Anty Zee din ne.”

Murmushi Mami tayi ta ce,
“Kaji har baki ya bude ko?”

Daga haka suka ci gaba da hira sosai suka dauke mata kewar Yaa Aslam.

Dan har sha daya suna tare. Sannan. Buhari ya tafi dakin sa. Mami kuma suka. kwana tare.

Washe gari ta dan ji dama dama amman a zuciyar ta ba sauki sai abinda yyai gaba.

Aslam kuwa sai ya tari Dadyn sa da maganar ko kallo bai ishe shi ba.

Dan haka ya tafi gun Wan Dadyn sa. wan Dady kuma ya shige masa akan maganar auren su da Pretty.

Komai da komai akai aka tsaida nan da sati uku za ai biki.

Lokacin da Dadyn Aslam ya samu labari kasa magana yayi.

Dan baisan me zai cewa, Amina ba shi har ga Allah yafiwa Aslam sha’awar Asma’u.

Ko Momyn Aslam kasa mata maganar yayi shi kadai ya dinga juya abin a ran sa.

Aslam ya kira yai masa gargadi akan ya janye batu auren yarinyar da yake son aura amman sai ga Aslam har da su kuka.

Da Dady yaki sauraron sa mma sai ya zube ya suma a gun.

Da sauri Dady ya fita dashi asibiti hankalin sa a tashe.

Allah nagode maka da ka bani ikon fara cigaba da karashen littafin *Asma’u Husnah* Allah ina rokan ka da ka bani ikon kammala shi lafiya kamar yadda na fara lafiya.

Masu korafi akan littafin kucigaba da bibiyar sa zakuyi komai.

*Mahaifiya ta farin cikin rayuwa ta. Mahaifiya ta hasken idaniya ta. Allah dada lafiya da nisan kwanan Momy Ameen*

Allah ka jikan *Mahaifina, da dukkan musulmai baki daya.

*Kannena farin ciki na. Allah bar min ku. *Nusaiba and Hauwa’u (Yasmeen)*

One love.

Ina mika gaisuwa ta ban girma gare ki yar uwa Anty nah. *Rashida Abdullahi Kardam* Allah ya dafa Allah ya karawa Mama lafiya. Allah baki miji nagari da zuri’a daiyaba. Ameen.

Sai sakon gaisuwa ta ga *Hajiya Nafisa* Momyn mu. Allah ya kara girma ya kara lafiya da arzuki ya Allah ya raya zuri’a. Ameen.

Sai gaisuwa ga Dukkan nin yan uwa marubuta musam yan kkungiyar HAJOW tare da yan uwan abokan azurki masoya. Allah ya kare mana ku Ameen.

Masoya nagode da kaunar ku a gareni nima ina kaunar ku.

Allah marasa lafiya na gida dana asibiti Allah ya basu lafiya. Allah ka daukaka musulunci da musulumai. Allah ka karya kafirci da kafirce.

*Ameen*

Bari mu shiga cikin karashen littafin dan muji abinda zai faru.

*1-5*

Ganin halin da Aslam. ya shiga ba karamin dagawa Dady hankali yai ba.

Amman duk da haka ya ce bai yadda Aslam ya auri Pretty ba.

Aslam kuwa ba karamin tashin hankali ya shiga ba. dan jinin sa ba karamin hawa yayi ba.

Momy da batasan me yake faruwa ba yasa ta shiga tashin hankali na rashin ganin Aslam ba.

Dady ta tara dan ganin bata ga Aslam ba har dare.

Dady ne ya fada mata duk abinda ya faru.

Momy mamaki ta tsaya yi yanzu abinda Aslam ya zaba kenan.

Zama Momy tayi ta dafe kan ta. Dady ne ya zauna kusa da ita ya kamo hannun ta.

Kallon sa tayi idon ta jajir ta ce,

“Dadyn Aslam ya zan yi da Asma’u. Kai kan ka shaidane akan soyayyar dake tsakanin su. Ban san me ya samu Aslam ba har haka ta faru. Amman ka min izini gobe na tafi kano naji me yake faruwa.”

“Ba komai. Ki kwantar da hanaklin ki. Na amince kije Allah ya kyauta.”

“Ameen!”

Kwana Aslam yai a asibiti dan Dady ko wajen sa bai koma ba.

Sai Pretty ya kira ya ita ta kwana a wajen sa.

Washe gari Momy ta daga zuwa Kano.

Asma’u ce kwance zazzabi ya rufe ta dan jikin ta kamar wuta.

Sai rawar sanyi take, idanun ta sunyi jajir dashi.

Mami ce ta shigo dakin rike da wani dan bowl da karamin towel a hannun ta.

Zama tayi a gefen Asma’u ta yaye bargon da ta rufa dashi.

Hijab din jikin ta ta cire mata ta matsa kusa da shi ta na tsoma towel din a cikin ruwan ta dauko ta matse sannan ta saka mata ajiki.

STORY CONTINUES BELOW

Wata ajiyar zuciya ta sauke, tana mme bude idon ta da sauri.

“Sannu!”

Mami ta fada tana cigaba da Shafa mata ruwa a jikin ta.

Sallamar Momy, Mami ta jiyo daga sama. Ajiye ruwan hannun ta Mami tayi ta mike ta fita.

Ganin Momy yasa ta saki fara’a ta ce,

“Anty nah Oyoyo.”

Ta rumgume Antyn tata.

“Mu shiga dana ciki.”

Suka shiga dakin Mami inda Asma’u ke kwance.

Momy na shiga taci karo da Asma’u kwance da sauri ta karasa wajen ta ta ce,

“Asmy na lafiya?”

Ido Asma’u ta bude jin muryar Momy. Da sauri ta mike tana sakin murmushi. Idon ta kamar zafin wuta saboda haka kanta yake sara mata dan har harbawa yake.

Zama Momy tayi agefen ta tana kamo hannun ta. Ta ce,

“Asmy bah lafiya ne?”

Murmushi Asma’u tayi ta ce,

“Dan zazzabi nake.”

Momy ta kalli Mami ta ce,

“Tin yyaushe kuma amman baki fada min ba.”

“Yi hakuri Anty, Wallahi kwana ta uku ke nan.”

Kallon ta, ta maida kan Asma’u ta ce,

“Sannu Baby nah. Kunje asibiti.”

Mami ce ta ce,

“Kinsan Amsa’u ai, tana likita amman bata son shan magani.”

“A’ah haka bazatai yiyu ba. Tashi muje.”

Ta mike tana daga Asma’u

Mikewa Mami tayi tabi bayan su. Asibitin Malam Aminu Kano suka tafi. Suna zuwa suka wuce Emergency.

Suna zuwa suka shiga ganin likita da yake suna da hanya.

BP ta ya auna, sannan ya dauki jinin ta, ya auna.

Gado ya basu ya ce, sai ana mata karin ruwa.

Buhari suka kira suka fada masa suna asibiti.

Sosai Doctor yayi musu fadan akan me jinin Asma’u da ya ga ya hau.

Mami ta rasa me yayi sanadin haka ita gani take kawai damuwar rashin Dadyn ta ce.

Momy ce ta hau tunanin ko dai sun ssamu matsala da Aslam ne shiyasa hakan ta faru.

Nan da nan sai ga Buhari yazo. Lokacin Asma’u na bacci.

Zama sukai ranar a asibiti suka yini sai gab da magariba aka ssallame su suka tafi gida.

Suna shiga gida Mami ta shiga kitchen. Asma’u kuma Momy ta hada mata ruwan wanka ta shiga tayi.

Tana fitowa ta saka kayan baccin ta sannan ta tada sallah.

Momy ma sallah tayi sannan ta zauna tana kallon duk wani mmotsin Asma’u.

Tin aa hanya take fama da kiran wayar Aslam bai dauka ba.

Yanzu ma kiran nasa ta karayi. Ganin bai dauka ba ta fara zargin ko lafiya.

Wata ta ce, lafiya kalaou da ba lafiya zai kira ya fada mata.

Wata zuciiyar kuma ta ce ko wayar sa aaka dauke. Nan ma ta ce da zai sanar da ita.

“To ko nai masa wani abun ne?”

Ta tambayi kanta. Kai ta girgiza ta ce

“In haka ne da zai sanar dani.”

Shiru tayi tana son ta gane me yake faruwa amman ta kasa.

Har akai isha’i tana zaune a inda take mikewa tayi tai sallah.

Sai da ta idar tai addu’a sannan ta kalli Momy da ta idar da sallah itama.

Ta ce,

“Momy ya Aslam kuwa lafiya ina neman wayar sa bana samu.”

STORY CONTINUES BELOW

Kallon ta Momy ta yi ta ce

“Tin yaushe kuma?”

“Yau wajen kwana biyar fa rabon da muyi waya. Bayan Yaa Aslam kullum sai munyi waya dashi.”

Kallon ta Momy tayi ta tausaya mata ta ce,

“Kuma ba abinda yya hada ku.”

Kai ta girgiza ta ce,

“Lafiya muka rabu da shi.”

Kai Momy ta jinjina ta ce,

“Kinga kar ki damu. Kin san ance jinin ki ya hau ki rage tunanii zan kira sa naji kinji. Ki kwantar da hankali ki.”

Kai ta gyada ta mike ta hau gado ta kwanta.

Zuciyar ta in banda bugawa ba abinda take.

Gaskiya tana son Yaa Aslam bata san inda zata sa kanta ba.

Tana kwance Mami ta shigo mata da kunun da ta dama mata.

Amsa tayi ta dan sha sannan ta mika mata.

Kwanciyya ta koma tayi sannan ta dasa daga inda ta tsayaa a tunanin ta.

Washe gari Mami da Momy suna zaune a falo. Momy ta dubi Mami ta ce,

“Amina wata matsala ce ta kawo nifa.”

Kallonta Momy tayi ta ce,

“Wacce irin matsala?”

Ajiyar zuciya Momy ta sauke ta ce,

“Akan Aslam da Asma’u ne.”

Kallon ta Mami tayi ba tare da ta gani me take fadi ba.

Momy ce ta gyara zama ta fada mata duk abinda yake faruwa.

Kai Mami ta jinjina tana mamaki anya Aslam ne kuwa.

Mami ce ta ce,

“Kinga Anty kuyi masa yadda yake so, Allah yasa haka ne mafi alheri ita Asma’u sai ta hakura.”

Kallon ta Momy ta yi ta ce,

“Wai ke Amina meyasa ko da yaushe kike son nuna min banbanci tsakanin ya’yan nan namu ne, kina zaton in nice Asma’u tayi ba dai dai ba zan barta ne, amman ke sai ki ce Allah yasa haka ne yafi alheri. Ai nasan daman da wannan addu’a.”

Mami dai shiru tayi fana sauraron fadam da Momy ke mata.

Sai da ta gama sannan ta ce,

“Kiyi hakuri Anty amman ni ba abinda kike nufi bane, nasan tsakanin Aslam da Asma’u ba mai shiga ne, bansani ba ko wani abun ya shiga tsakanin ne ko sun samu sabani.”

Kai Momy ta gyada, ta ce,

“Ki tuntubar min Asma’u “

Mami ta ce,

“Toh!”

Buhari da tin da Momy ta fara bawa Mami batun yana jin su har yanzu yaji jikin sa yayi mugun sanyi.

Garden yayi dan bazai iya shiga ciki ba a halin da yake ciki.

Yana zuwa ya hango Asma’u kwance a kan wata kujera. Ta kudundune jikina ta.

Idon ta a rufe kamar mai bacci. Juyawa yayi zai bar wajen ta mike tana kiran sunan sa.

Juyowa yayi yana sakar mata murmushi, ya ce,

“Ai na zata bacci kike.”

Kai ta girgiza masa ta ce,

“Ina kwance ne kawai.”

Dawowa yayi ya zauna gefen ta yana kallon ta cikin tausayawa dan yanzu da ya kara jin maganganun su Momy sai ya kara tausayawa Asma’u.

Kallon ta yayi dan ya bugi cikin ta ya ce,

“Ina Yaa Aslam kuwa? Kwana biyu bamuyi waya ba.”

Murmushi ta dan ta ce,

“Yana lafiya.”

Kallon mamakki ya bita da shi. duk yadda yaso ya bugi cikin ta bata fada masa komai ba.

Haka ya hakura ya barta sai kallon tausayi da yake mata dan yasan Asma’u ta ji Aslam zai aure ba karamin damuwa zatai ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yasan zata iya shiga wani hali. To shi da me zai taimakawa kanwar sa kar ta shiga damuwa.

Ya jima yana tunanin nan kafin ya mike ya koma cikin gida.

Asma’u kuwa har lokacin number Aslam take ya kira amman No Answer.

Aslam kuwa duk kiran da take masa yana gani dauka ne yake gagarar sa. Dan shima ba karamin sun dauka yake ba amman sai ya kasa.

Yanzu kuwa kullum yana tare da Prety daga sune can sai sune can.

Duk abinda ta lissafa tana so ya siya mata.

Buhari ne kwance ya kasa gaskata abinda yaji su Mami na fadi.

Mikewa yai zaune ya janyo wayar sa. Number Aslam ya kira.

Bugu daya ya dauka. Gaisawa sukai kamar yadda suka saba sai dai bai tambaye sa Asma’u ba kamar yadda ya saba.

Buhari ne ya ce,

“Yaa Aslam daman Asma’u ce ba lafiya naji ba ka kira ya take bane.”

Shiru Aslam yayi na dan wani lokaci kafin ya ce,

“Ai mata sannu. Yanzu ina wani aiki ne amman in na samu lokaci zan zo. kaji labarin aure na nan da sati biyu ko?”

Dif Buhari yayi jin abinda Aslam ya fada. Kai ya girgiza sannan ya ce,

“Au bikin naku har an matso dashi amman ban sani ba.”

“A’ah ba wannan ba wata xan aura anan.”

“Wata zaka aura!”

Buhari ya fada da mamaki sosai. Aslam ne ya katse masa tunani ya ce,

“Buhari kai ne dan uwana wanda kake kani a guna. Wallahi bansan me yake damuna ba. Lokaci daya naji ina son Pretty kuma ni ba son Asma’u ne bana yi ba kawai bansan me yake damuna ba.”

Sosai Aslam ya bawa Buhari tausayi. Tabbas yana tausayawa Aslam amman yafi tausayawa Asma’u ita da take haukan son sa.

Shiru yayi. Aslam ya ce,

“Dan uwana dan Allah kada hakan ya zamo sanadin yanke zumuncin mu ka fuskance ni. Momy da Dady sun kasa fahimta ta.”

Take Buhari ya gane Aslam ba acikin haiyacin sa yake ba.

Shiru yayi kafin ya ce,

“Ba komai Allah tabbatar da alherin sa.”

Wayar ya kashe yai shiru. Sai ga hawaye na zubowa daga idon Buhari.

Tabbas dole yasan abinda zai ya kubutar da Asma’u daga damuwa.

To tayaya dole ta damu in har Aslam baya kiran ta. Kuma dole ta damu in bata ganshi a wajen ta na kwanaki ba.

Ya jima yana saka da warwarar yadda zai bullowa alamarin har da sai da ya samu mafita sannan ya samu sauki a ransa.

Zainab ya fadawa duk halin da suke ciki sosai ta tausaywa kawar tata.

Asma’u ce zaune a falon Dady ta zuba tagumi, Mami ce ta shiga ta same ta.

Zama tayi a gefen ta, ta ce,

“Asma’u jikin ne, Asma’u dan Allah ki rage damuwa kinji.”

Kai Asma’u ta daga ta zare hannun ta da tai tagumi dashi.

Kallom Mami tayi ta sakar mata murmushin da bai kai zuciya ba.

Mami ta ce,

“Wai kuwa kin fadawa Aslam baki da lafiya.?”

Shiru Asma’u ta danyi ta ce a ranta.

“To ita yanzu wa zata na fadawa damuwar ta in ba Mami ba. Tinda ba Dady dole Mami ta zama kawar shawarr ta.”

Kallon Mami Tayi idon ta sun kawo da kwalla ta ce,

“Mami bansan me yake damun Yaa Aslam ba. Kwata kwata baya kira na ko na kira sa baya dagawa. Bansan laifin da nai masa har yake hukunta ni haka ba. Mami wallahi ko bacci bana iya wa saboda ya sabar min shine mutum na karshe da nake magana dashi na kwanta bacci.”

STORY CONTINUES BELOW

Sai ta fashe da kuka. Sosai Mami ta tausayawa yar ta ta. Lallashin ta tayi sannan ta ce

“Kiyi hakuri ki dage da addu’a kinsan haka na faru amman addu’a ita zata tsairatar da ke.”

Kai ta daga ta ce,

“Mami bazan iya rayuwa ba Yaa Aslam ba. Yaa Aslam ya sabar min da son sa yadda bazan iya cigaba ba tare da shi ba.”

Janta jikinta Mami ta yi ta ce,

“Ki daina fadar haka, ki sa a ranki ko da Aslam ko ba Aslam zaki rayuwa. Kina addu’a Allah zaba miki abinda yafi alheri a rayuwar ki.”

Sosai Mami ta kwantar wa da Asma’u hankali.

Suna Zaune Buhari ya shigo. Ganin idanun Asma’u da hawaye ya tada masa da hankali.

Zama yayi a gefen ta ya ce,

“Hussyn Dady menene kuma?”

Jikin sa ta fada ta fashe da kuka mikewa Mami tayi ta fita.

Asma’u ce, ta ce,

“Yaa Buhari. Yaa Aslam ne, bansan me nai masa ba.”

Ta fashe da kuka. Lallashin ta ya dinga yi. Ya ce,

“Baby nah ki kwantar da hankalin ki. Ba abinda kikai masa. Kuma insha Allahu Aslam naki ne, kinji.”

Kai ta daga ta ce,

“Yaya da Gaske.”

Kai ya daga mata ya ce,

“Kinga ki taso muje nai miki visa ki tafi saudiya. Daga nan ki yo addu’a tinda kinga kun gama karatu. in kin dawo a bude asibiti a fara aiki. Daga nan zzan zo muje wasu kasashen kar ki damu kinji.”

Kai ta daga masa. Ta mike ta wanke fuska suka fita.

Mami kuwa tana fita itama sai da ta dan zubar da hawayen

Tana tausaywa ‘yar ta. Tasan ‘yar ta bata saba da son kowa ba. Da Aslam ta bude ido ta san rayuwa gashi yanzu wani al amari na shirin faruwa.

Dakin da Momy ta ke ta shiga jiki a sanyaye.

Kallon ta Momy tayi ta ce,

“Ya kukai da ita.”

“Uhmm Anty ni a gani na kawai kibar Aslam ya aure wacce yake so. In yaso daga baya in Allah yayi Asma’u matar sa ce sai suyi auren. Yanzu dai ita ta ce, ba abinda ya hada su kawai dai baya kiran ta baya daukar number ta ne.”

“Inna illahi wainna illahir rajiun!”

Momy ta dinga nanatawa.

“Shiken Amina tinda haka kika ga yafi shikenan. Zan je zanyi iya bakin kokari na a daura auren nan da Asma’u amman ni ba yawu na a auren Aslam da wata.”

“A’ah Anty kada kiyi haka, kada ki so ma hakan ba kyau. Ki sa masa albarka kawai baki san mene alheri a rayuwar mu ba. In kika ce haka sai kiga wani abu mara dadi ya faru.”

Shiru Momy tayi ta ce,

“Shiknan dole na tafi gida yau din man.”

“A’ah Anty dan Allah ki bari gobe. Kuma dan Allah kada ki tada maganar nan.”

Shiru Momy tayi kawai.

Buhari kuwa da suka dawo gidan su Zainab ya biya da Asma’u duk dan ta samu farin ciki.

Duk da jikin ta ba kwari. Ita kanta fitar da sukai ba karamin debe mata kewa tayi ba.

Dan ya dan samu sanyi a ranta duk da da tayi shiru abin yake fado mata a rai.

Basu dawo gida ba sai dare da siyayyar da Yaa Buhari yai mata.

Kayan ta ta hau hadawa wanda za tai tafiya dasu.

Sai da ta gama ta kwanta. Tana kwance nan sai tunanin Yaa Aslan ya fado mata

Na yadda yake jaddada mata son sa da yadda yake kwantar mata da hankali.

Kuka ta fashe da shi ta jima tana kuka sannan ta mike tayo alwala sanna ta zo ta tada sallah,

Kwana tayi tana sallah tana rokar Allah ya shige mata cikin al amuransa.

Washe gari da zazzabi mai zafi ta kuma ta shi. Dan ko ‘kasa kasa sauka tayi.

Tana kwance Momy ta shigo dakin da break din ta a hannu.

Ganin ta a kwance yasa tai zaton ko bacci take wannan yasa ta fita bata tashe ta ba.

Wanka taje tayi ta shirya dan ta tafi gida.

Mami na falo Buhari na gefen ta ya zuba ta gumi.

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Mami ya ce,

“Mami munje anyiwa Asma’u visa har dake ma zaku tafi tare. Amman na je na fadawa Uncle Abubakar kan a matso da biki na kusa. In lokacin ya yi Mami ke sai ki dawo. Ki bar Asma’u acan dan ta samu nutsuwa.”

Kai Mami ta gyada masa dan gwara Asma’u bata nan za ai bikin Aslam da ace tana nan abin bazai mata ba dadi ba.

Buhari ya ce,

“To Mami jibi ne tafiyar.”

Mami ta ce,

“Allah nuna mana.”

“Ameen!”

ya asma.

Ya ce,

“Asma’u bata sauko ba ko jikin ne.”

“Jeka duba ta. Wallahi ni bana son na ganta a irin wannan halin wallahi.”

Mikewa yayi yai sama.

Yana zuwa ya tura kofar dakin. Tana kwance bata motsa ba.

Sai da ya shiga ya zauna a gefen ta sannan ya dago ta.

Idon ta ta bude wadan da sukai ja dasu. Dan wani irin ciwon kai ke damun ta wanda ya taba mata har idon ta. Dan idon ta wani zafi da nauyi yai mata.

Ido ta mayar ta lumshe saboda zafin da taji yana mata. Cikin karfin haki ta ce,

“Yaa Buhari ina kwana?”

Bai amsa ba ya jingina ta da gado. Tea ya hada mata mai kauri sai farfesun kayan cikin da aka yi ya dinga bata a baki.

Sosai taci dan rabon ta da abinci tin jiya da rana.

Sai da ta koshi duk idon ta a rufe sannan ya bata magani.

Mami dake ta taga tana ganin abinda suke hawaye ya wanke mata fuska.

Daki ta shiga tayi kuka sosai sannan ta mike ta wanke fuska tayi dakin Asma’u.

Lokacin da ya kwantar da ita kenan. Tana jin muryar Mami ta mike tana mika mata hannu.

Hannun ta Mami ta kama ta kwantar da ita akan cinyar ta tana shafa kanta.

A hankali a hankali har tayi bacci. Kallon ta Mami tayi. Asma’u ta rame ta kara gaske, sannan ta zama shiru shiru dan ko magana bata son yi.

Hawaye ne ya zubowa Mami tai saurin gogewa. Momy ce ta shigo cikin shirin ta.

Zama tayi a gefen Mami ta ce,

“Amina nifa bazan zauna ina ganin Asmaa’u a wannan halin ba sannan na kasa taimakon ta. Ko ba halin da Aslam ya canja bane yasa ta a wannan halin nasan kasance war sa da ita zata rage damuwa. Zanje nasan yadda zanyi sai munyi  waya,”

Ta mike, kallon Mami tayi ta ce,

“Na miki transfer kudi, na kayan abincin wannan watan ne. Ki kula da Asma’u sai kinji ni.”

Momy ta fita tana kwadawa Buhari kira dan zai kai ta airport.

Momy na fita Mami ta saki kuka. Su kuma tasu jarabar kenan.

Allah ya dauke musu jigon su, rumfar su. Sai kuma wannan Allah ya daukewa Asma’u Aslam.

“Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar.’

Mami ta fada tana shafa kan Asma’u.

Da yamma Mami na zaune a falo. Asma’u kwance akan cinyar ta.

Zazzabin ne ya kara zafi sai hawaye da take zubarwa. Duk da ta sha magani amman jikin nan kamar wuta.

Suna zaune ssuka jiyo sallamar Sir Sabir. Mami ce ta amsa masa ya shigo.

Sai da suka gaisa cikin girmamawa sannan ya dubi Asma’u ya ce,
“Mami yau kuma *Husnah* autan cin ne ya motsa.”

Tinda ya ambaci Husnah, Asma’u ta bude ido tana kallon sa. Shima kallon ta yake.

Mami ce, ta ce,
“Ba lafiya ne, kaga muje asibitin amman jikin kamar dada mata ciwon ake.”

“Ya Salam! Me yake damun ta?”
Ya tambaya.

“Uhmm da muka je akai mata BP sai yace jinin ta ya hau. Kaga kullum jikin da zazzabi take kwana take tashi ga ciwon kai.”

“Ya salam! Mami kar dai har yanzu Asma’u bata daina sa dumuwar rashin Dady ba.”
Mami ta ce,
“To gata nan dai.”

“Mami dan Allah ku taso muje asibiti na duba ta.”
Mami ta ce,
“To bari na kira Buhari.”

Waya ta kira shi nan da nan sai ga shi. Gaisawa sukai da Sabir sannan ya kama Asma’u suka nufi Asibiti.

Office din shi kai tsaya suka nufa. BP ya kara gwada mata. Ba karamin mamaki.ya bashi ba tesult din. Dan ya tsora ta sosai.

Ruwa ya kara juna mata sannan suka fita shi da Buhari ya ke fada masa yadda jinin ta hau.

Buhari bai yi mamamki ba dan yasan aabinda haka ma zai iya faru da Asma’u in ya tuna irin shakuwar da soyayyar dake tsakanin Asma’u da Aslam.

Magani ya kara rubuta mata. Sannan ya karbo suka dawo.

Mami tana zaune ta zubawa Asma’u ido suka dawo. Maganin suka ajiye mata.

Sabir ya kalle ta ya ce,
“Mami ki daina sa damuwa komai zai warware. Allah zai bata lafiya.”

Mami ta ce,
“Allah bata sauki.”

Tana farkawa Mami ta bata dankali ta ci. Sai magani da dakyar ta amsa ta sha.

Cikin ikon Allah kafin su koma gida jikin ta ya danyi kwari.

Suna komawa. Sabir yai musu sallama ya tafi gida da tunanin Asma’u a ransa.

Washe gari, su Mami da Asma’u suka daga kasa mai tsarki.

Momy na dira gida ta tadda Dady zaune ya zuba tagumi shima al amarin ba karamin damun sa yayi ba.

Dan Aslam sai goma ko sha daya yake dawowa gida.

Yanzu ko zaman hira basa yi. Sai Waya da Pretty duk yinin da suke tare.

Momy ce ta zauna a gefen ta cire masa tagumin da ya zuba. Kallon sa tayi ta ce,
“Dady me ya faru?”

STORY CONTINUES BELOW

Dagowa yayi ya ce,
“Komai ma. Ya su Asma’un?”

Ajiyar zuciya Mami ta sauke sannan ta masa bayani duka abinda yake faru.

Sannan ta daura da cewa,
“Dady baka ga Asma’u ba. Wallahi bata da lafiya sosai har jinin ta ya hau. Yarinya karama Dady. Kuma na tabbata har da Aslam a sanadin wallahi.”

Momy ta fada ranta a bace. Ta ce,
“Kaga yadda Asma’u ta rame kuwa.”

Dady ya ce,
“Inna illahi wainna illahir rajiun. Wallahi Aslam ban san me yake damun sa ba. Amman ko jiya da nai masa magana ko aufan bai ce min ba. Ni dai abinda za’ayi kawai a daura auren nan da yana so da baya so.”

“Nima haka nace, amman Amina ta ce, aah abi komai a hankali. Ba asan me Allah ya tsara ba.”

Kai Dady ya jinjina ya ce,
“Wallahi ba hannu na a cikin auren nan da yake so yayi. Nawa ido ne.”

Momy ma ta ce,
“Nima haka amman Aslam bansan me yake damun sa ba. Allah ya shirya shi. Nasan ba kudi ke rudar sa ba ko kyau. Dan Asma’u ba za a. fada mata kyau ko ilimi ba wallahi.”

“Nima haka baki ga yadda nake masa sha’awar auren yarinyar nan ba. Ko dan halaiyar ta. ga ilimin ta, na tabbata bazai taba samun yarinya kamar Asma’u ba.”

“Ai shikenan tinda haka ya zaba Allah ya kyauta “

“Ameen!”
Dady ya amsa. Ya ce
“Ki kira su kiji ya jikin nata.”

“Toh!”
A lokacin ne ta buga taji sun koma asibiti ma.

Sosai Momy ke tausayyawa Asma’u kuma ta dau alkawarin sai ta rama abinda Aslam yai mata.

A kwana a tashi har bikin Aslam ya rage sati daya.

Tin saura sati biyu kawar ta ta rakata asibiti akai mata wani dinki.

Yadda zata dawo kamar budurwa. Sosai take gyara kan ta.

Kamar yadda sukai da boka kan zataje in biki ya rage sati haka ce ta faru.

Da taje ce mata yayi zai mata rubutu a jiki a wanke a bawa Aslam yaci a abinci ko a lemo.

Ba kunya haka Pretty ta tube ya gamai mata rubutu daga nan kuma sukai masha’ar su.

Sosai Pretty taji haushin bata mata aiki da yayi dan ita dan Aslam tayi.

Shi kuwa bokan ta jin dadin da ta kara ya kara saukar masa da wata matsananciyar sha’awar ta.

Barin ta zai yi ta dana na dan lokaci dan ya kumai wa kan sa alkawarin bazai taba barin Pretty ba sai ta zama matar sa.

Haka ya kara hada mata wasu tsafe tsafen nasu sannan ta koma gida da murna.

Sosai take cigaba da kara gyara kanta duk dan ta burge Aslam.

A kwana a tashi har an fara shagalin bikin Aslam da Fauziyya (Pretty).

Event an tsara wajen guda biyar. Sosai Aslam ya saki kudi.

Momy da Dady kuwa kamar ba bikin dan ta ake ba dan ba abinda ta tsara zatai.

Haka nan ko su Mami bata fadawa ba dan kar Asma’u ma ta sani.

Ranta a matukar bace yake akan bikin nan dan shi kansa Aslam din tausayi yake bata.

Asma’u kuwa tinda lokacin bikin Aslam.ya kama take fama da faduwar gaba. Ga wasu mafarkai da take da Aslam.

Duk ta kara lalacewa, Ita aba ba jiki ba dama. dan ma addu’a da suke ita da Mami ba sanya.

Dan sai su kwana suna mika kukan su ga Allah.

Kullum suna waya da Buhari da Zainab haka ma Sir Sabir yana kira su gaisa.

STORY CONTINUES BELOW

Yau ma kamar kullun bayan sun dawo daga harami tayi wanka tazo falo ta zauna.

Tagumi ta saki tana tunanin Aslam lokacin da suke zaune a garden a ranar da Dadyn ta ya sanar da ita batun ya bada ita ga Aslam.

Lokacin da suke zaune ya yi murmushi ya ce da ita,
“Alhamdulilah nagodewa Allah.Zuciya ta ke kadai takewa na amince rike ta har abada.”

Asma’u ta ce,
“Ya Aslam kenan!”

Ya ce,
“Eh! Man kada ki taba zaton zan yaudare ki”

“Nasan baza ka taba bama.”
“Yauwah Love.”

Sukai murmushi a tare,
“Nima Zuciya ta kai kadai take yabawa dan tasan ka riketa ba da yaudara ba.”

“Da gaske.”
“Eh!” Ta fada tana dage masa gira.
ya ce,
“So hadi na Allah ne, Zuciyata ke kadai ta nuna min. Na riga na sanarwa da Momy da Dady da Dady da Mami, da duk wanda muke mu’amala dasu in babu ke sai dai na rasa rayuwa ta.”

Ido ta zaro,
“Su Momy,”
Eh! Mana ai kowa yasan son da nake miki in aka raba mu zan iya rasa rayuwa ta.”

“Allah ma ya kiyaye.”
“Ameen!”

“Tin da Dady ya bayyana, min son ka akan kai ne, mijina baka ji yadda naji ba. Saboda Allah yasa ga wanda nake so aka hada kaga yafi dadi ko.”

“Shiyasa nacewa Dady kar a fada miki sai na kama bakin zaren!”
“Wane zaren kuma”

Ido ya kashe mata.
“Zuciyar ki man. Hmmm *Husnah* baki san yadda na riki soyayyar ki a raina ba. Ta zama abin yi dare da rana. Soyayyar daraja ne da ita. Samun irin taki shine burin ko wane me hankali. Bana son na taba yin nesa dake. Kin shiga zuciya kinyo kafuwa. Ni dake babu rabuwa koman dadewa.”

Kallon sa ta tsaya yi.
“Kai ma kasan kaine zabin rai na. Zuciya ta, ta adana soyayyar ka ba wanda ze maye gurbin ta. Sa’a ni na sama tinda na samu gwarzon masoyi kamar ka. Kai ka ke sani addu’ar neman miji na gari, kuma nasan Allah ya amsa min da ya aikon da kai a matsayin masoyi wanda nake fatan shine miji na.”

“Gaskiya ne. Dace da masoyi shine ribar soyayya. Nasan sabon da mukayi ni dake sai dai a kira mu tagwaye, ko yaushe in na tina ki nakanyi murmushi da jin frin ciki a cikin zuciya ta.”

Murmushi tayi, ta sauke ajiyar zuciya me karfin
“Lafiya?”

Ya tambaye ta.
“Ya Aslam in na tuna da rabuwa ne sai naji zuciya ta tayi min rauni”

“Haba *Husnah ba mun kashe wannan maganar ba ne.”
“Eh!”
“To Bazamu rabu ba sai dai mutuwa itama insha Allahu tare zata dauke mu.”

“Allah yasa!”
“Ameen.”

“Yauwah kinga tin yanzu sai mu fara tsara yadda bikin mu zai kasance ko?”

****—****
Kuka ta fashe da shi tina wannan hirar tasu.

Ta ce,
“Ni na gama amince maka Yaa Aslam amman me nai maka kake min irin wannan horan. Wallahi nasan in har nan da wani lokaci Yaa Aslam bai dawo gare ni ba komai zai iya faruwa da zuciya ta.”
Ta fada tana kara fashewa sa kuka.

Dan a yadda take jin zuciyar ta ji take kamar zata fashe.

*INDABAWA*

*Asma’u Husnah*

*part 2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*

Dedicated to *My Lovelly Momy*

*11-15*

Da yamma Mami na zaune a falo. Asma’u kwance akan cinyar ta.

STORY CONTINUES BELOW

Zazzabin ne ya kara zafi sai hawaye da take zubarwa. Duk da ta sha magani amman jikin nan kamar wuta.

Suna zaune ssuka jiyo sallamar Sir Sabir. Mami ce ta amsa masa ya shigo.

Sai da suka gaisa cikin girmamawa sannan ya dubi Asma’u ya ce,
“Mami yau kuma *Husnah* autan cin ne ya motsa.”

Tinda ya ambaci Husnah, Asma’u ta bude ido tana kallon sa. Shima kallon ta yake.

Mami ce, ta ce,
“Ba lafiya ne, kaga muje asibitin amman jikin kamar dada mata ciwon ake.”

“Ya Salam! Me yake damun ta?”
Ya tambaya.

“Uhmm da muka je akai mata BP sai yace jinin ta ya hau. Kaga kullum jikin da zazzabi take kwana take tashi ga ciwon kai.”

“Ya salam! Mami kar dai har yanzu Asma’u bata daina sa dumuwar rashin Dady ba.”
Mami ta ce,
“To gata nan dai.”

“Mami dan Allah ku taso muje asibiti na duba ta.”
Mami ta ce,
“To bari na kira Buhari.”

Waya ta kira shi nan da nan sai ga shi. Gaisawa sukai da Sabir sannan ya kama Asma’u suka nufi Asibiti.

Office din shi kai tsaya suka nufa. BP ya kara gwada mata. Ba karamin mamaki.ya bashi ba tesult din. Dan ya tsora ta sosai.

Ruwa ya kara juna mata sannan suka fita shi da Buhari ya ke fada masa yadda jinin ta hau.

Buhari bai yi mamamki ba dan yasan aabinda haka ma zai iya faru da Asma’u in ya tuna irin shakuwar da soyayyar dake tsakanin Asma’u da Aslam.

Magani ya kara rubuta mata. Sannan ya karbo suka dawo.

Mami tana zaune ta zubawa Asma’u ido suka dawo. Maganin suka ajiye mata.

Sabir ya kalle ta ya ce,
“Mami ki daina sa damuwa komai zai warware. Allah zai bata lafiya.”

Mami ta ce,
“Allah bata sauki.”

Tana farkawa Mami ta bata dankali ta ci. Sai magani da dakyar ta amsa ta sha.

Cikin ikon Allah kafin su koma gida jikin ta ya danyi kwari.

Suna komawa. Sabir yai musu sallama ya tafi gida da tunanin Asma’u a ransa.

Washe gari, su Mami da Asma’u suka daga kasa mai tsarki.

Momy na dira gida ta tadda Dady zaune ya zuba tagumi shima al amarin ba karamin damun sa yayi ba.

Dan Aslam sai goma ko sha daya yake dawowa gida.

Yanzu ko zaman hira basa yi. Sai Waya da Pretty duk yinin da suke tare.

Momy ce ta zauna a gefen ta cire masa tagumin da ya zuba. Kallon sa tayi ta ce,
“Dady me ya faru?”

Dagowa yayi ya ce,
“Komai ma. Ya su Asma’un?”

Ajiyar zuciya Mami ta sauke sannan ta masa bayani duka abinda yake faru.

Sannan ta daura da cewa,
“Dady baka ga Asma’u ba. Wallahi bata da lafiya sosai har jinin ta ya hau. Yarinya karama Dady. Kuma na tabbata har da Aslam a sanadin wallahi.”

Momy ta fada ranta a bace. Ta ce,
“Kaga yadda Asma’u ta rame kuwa.”

Dady ya ce,
“Inna illahi wainna illahir rajiun. Wallahi Aslam ban san me yake damun sa ba. Amman ko jiya da nai masa magana ko aufan bai ce min ba. Ni dai abinda za’ayi kawai a daura auren nan da yana so da baya so.”

“Nima haka nace, amman Amina ta ce, aah abi komai a hankali. Ba asan me Allah ya tsara ba.”

Kai Dady ya jinjina ya ce,
“Wallahi ba hannu na a cikin auren nan da yake so yayi. Nawa ido ne.”

STORY CONTINUES BELOW

Momy ma ta ce,
“Nima haka amman Aslam bansan me yake damun sa ba. Allah ya shirya shi. Nasan ba kudi ke rudar sa ba ko kyau. Dan Asma’u ba za a. fada mata kyau ko ilimi ba wallahi.”

“Nima haka baki ga yadda nake masa sha’awar auren yarinyar nan ba. Ko dan halaiyar ta. ga ilimin ta, na tabbata bazai taba samun yarinya kamar Asma’u ba.”

“Ai shikenan tinda haka ya zaba Allah ya kyauta “

“Ameen!”
Dady ya amsa. Ya ce
“Ki kira su kiji ya jikin nata.”

“Toh!”
A lokacin ne ta buga taji sun koma asibiti ma.

Sosai Momy ke tausayyawa Asma’u kuma ta dau alkawarin sai ta rama abinda Aslam yai mata.

A kwana a tashi har bikin Aslam ya rage sati daya.

Tin saura sati biyu kawar ta ta rakata asibiti akai mata wani dinki.

Yadda zata dawo kamar budurwa. Sosai take gyara kan ta.

Kamar yadda sukai da boka kan zataje in biki ya rage sati haka ce ta faru.

Da taje ce mata yayi zai mata rubutu a jiki a wanke a bawa Aslam yaci a abinci ko a lemo.

Ba kunya haka Pretty ta tube ya gamai mata rubutu daga nan kuma sukai masha’ar su.

Sosai Pretty taji haushin bata mata aiki da yayi dan ita dan Aslam tayi.

Shi kuwa bokan ta jin dadin da ta kara ya kara saukar masa da wata matsananciyar sha’awar ta.

Barin ta zai yi ta dana na dan lokaci dan ya kumai wa kan sa alkawarin bazai taba barin Pretty ba sai ta zama matar sa.

Haka ya kara hada mata wasu tsafe tsafen nasu sannan ta koma gida da murna.

Sosai take cigaba da kara gyara kanta duk dan ta burge Aslam.

A kwana a tashi har an fara shagalin bikin Aslam da Fauziyya (Pretty).

Event an tsara wajen guda biyar. Sosai Aslam ya saki kudi.

Momy da Dady kuwa kamar ba bikin dan ta ake ba dan ba abinda ta tsara zatai.

Haka nan ko su Mami bata fadawa ba dan kar Asma’u ma ta sani.

Ranta a matukar bace yake akan bikin nan dan shi kansa Aslam din tausayi yake bata.

Asma’u kuwa tinda lokacin bikin Aslam.ya kama take fama da faduwar gaba. Ga wasu mafarkai da take da Aslam.

Duk ta kara lalacewa, Ita aba ba jiki ba dama. dan ma addu’a da suke ita da Mami ba sanya.

Dan sai su kwana suna mika kukan su ga Allah.

Kullum suna waya da Buhari da Zainab haka ma Sir Sabir yana kira su gaisa.

Yau ma kamar kullun bayan sun dawo daga harami tayi wanka tazo falo ta zauna.

Tagumi ta saki tana tunanin Aslam lokacin da suke zaune a garden a ranar da Dadyn ta ya sanar da ita batun ya bada ita ga Aslam.

Lokacin da suke zaune ya yi murmushi ya ce da ita,
“Alhamdulilah nagodewa Allah.Zuciya ta ke kadai takewa na amince rike ta har abada.”

Asma’u ta ce,
“Ya Aslam kenan!”

Ya ce,
“Eh! Man kada ki taba zaton zan yaudare ki”

“Nasan baza ka taba bama.”
“Yauwah Love.”

Sukai murmushi a tare,
“Nima Zuciya ta kai kadai take yabawa dan tasan ka riketa ba da yaudara ba.”

STORY CONTINUES BELOW

“Da gaske.”
“Eh!” Ta fada tana dage masa gira.
ya ce,
“So hadi na Allah ne, Zuciyata ke kadai ta nuna min. Na riga na sanarwa da Momy da Dady da Dady da Mami, da duk wanda muke mu’amala dasu in babu ke sai dai na rasa rayuwa ta.”

Ido ta zaro,
“Su Momy,”
Eh! Mana ai kowa yasan son da nake miki in aka raba mu zan iya rasa rayuwa ta.”

“Allah ma ya kiyaye.”
“Ameen!”

“Tin da Dady ya bayyana, min son ka akan kai ne, mijina baka ji yadda naji ba. Saboda Allah yasa ga wanda nake so aka hada kaga yafi dadi ko.”

“Shiyasa nacewa Dady kar a fada miki sai na kama bakin zaren!”
“Wane zaren kuma”

Ido ya kashe mata.
“Zuciyar ki man. Hmmm *Husnah* baki san yadda na riki soyayyar ki a raina ba. Ta zama abin yi dare da rana. Soyayyar daraja ne da ita. Samun irin taki shine burin ko wane me hankali. Bana son na taba yin nesa dake. Kin shiga zuciya kinyo kafuwa. Ni dake babu rabuwa koman dadewa.”

Kallon sa ta tsaya yi.
“Kai ma kasan kaine zabin rai na. Zuciya ta, ta adana soyayyar ka ba wanda ze maye gurbin ta. Sa’a ni na sama tinda na samu gwarzon masoyi kamar ka. Kai ka ke sani addu’ar neman miji na gari, kuma nasan Allah ya amsa min da ya aikon da kai a matsayin masoyi wanda nake fatan shine miji na.”

“Gaskiya ne. Dace da masoyi shine ribar soyayya. Nasan sabon da mukayi ni dake sai dai a kira mu tagwaye, ko yaushe in na tina ki nakanyi murmushi da jin frin ciki a cikin zuciya ta.”

Murmushi tayi, ta sauke ajiyar zuciya me karfin
“Lafiya?”

Ya tambaye ta.
“Ya Aslam in na tuna da rabuwa ne sai naji zuciya ta tayi min rauni”

“Haba *Husnah ba mun kashe wannan maganar ba ne.”
“Eh!”

“To Bazamu rabu ba sai dai mutuwa itama insha Allahu tare zata dauke mu.”

“Allah yasa!”
“Ameen.”

“Yauwah kinga tin yanzu sai mu fara tsara yadda bikin mu zai kasance ko?”

****—****
Kuka ta fashe da shi tina wannan hirar tasu.

Ta ce,
“Ni na gama amince maka Yaa Aslam amman me nai maka kake min irin wannan horan. Wallahi nasan in har nan da wani lokaci Yaa Aslam bai dawo gare ni ba komai zai iya faruwa da zuciya ta.”
Ta fada tana kara fashewa sa kuka.

Dan a yadda take jin zuciyar ta ji take kamar zata fashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *