RAYUWAR ASMAU CHAPTER 10
Kuka ta kuma fashewa da shi ta ce,
“Meyasa? meyasa? Meyasa yaa Aslam? Me nayi maka da na cancanci haka.”+
Ta kuma fashe wa da kuka dan har numfashi ta na sarkewa.
Mami ce ta fito ta tadda ta a hankalin da take ciki.
Da sauri ta karassa gun ta. Ina har numfashin ta ya dauke
Da sauri Mami ta kira suka tafi da Asma’u asibiti.
Aslam kuwa ana can yau daurin aure. Duk da yau take ranar farin ciki a gunsa amman sai akasin haka.
Dan damuwa sosai ya shiga na tinawa da tini da Asma’u ake daura auren nasu.
Duk yadda yaso yai farin ciki ya kasa. Abokan sa kuwa dayawa duk basu je daurin auren ba dan ya riga ya koya musu son Amsa’u.
Dukkan su mamaki suke sosai. Wasu kuma haushin Pretty suke ji.
Wasu daga cikin abokan sa su suka hallaci daurin auren.
Bayan an gama reception ya koma gida ne ya kwanta a daki.
Ba abinda yake gani sai Asma’u da ke masa murmushi.
Ido ya lumshe, ya rasa me yake damun sa.
Gani yake kamar a mafarki wai ya auri Pretty. Mamaki yake sosai amman kuma sai wani abu ya dauke hankalin sa daga wannan.
Haka da dare aka kai amarya gidan ta. Dan Mami ta ce bazai saka kowa a gidan da ya gina dan Asma’u ba.
Wani daga cikin gidan shi yasa aka gyara akai wa Pretty kafin kayan ta.
Amarya kamar ba amarya ba dan mayafi ma a kafada ta yafa aka raka ta gidan ta.
Aslam kuwa lokacin yana gida a kwance ya rasa me zai yi.
Mami da kanta taje ta same shi a daki.
Duk da ganin yanayin da yake ya bata tausayi amman hakan bai sa ta ce,
“Ka tashi ka tafi gidan ka. Ga amaryar ka can an kai maka ita.”
Shiru yayi kamar bazai yi magana ba. Sai kuma ya sauko daga kan gadon ya durkusa a gaban ta ya ce,
“Momy dan Allah ki yafe min. Momy wallahi ban san abinda yake damu na ba.”
Kai Momy ta dauke, Kuka ya saka yana nema yafiyar Momy.
Kallon sa tayi ta tausaya masa ta ce,
“Ba komai kaje Allah bada zaman lafiya. Amman har ga Allah bana son auren nan naka.”
Kin sakin ta tayi sai da Momy ta daga sa tace,
“Kaje ka shirya dare nayi.”
Mikewa yayi ya shiga bandaki. Ya fito ya shirya cikin sky blue din shadda. Yayi masifar kyau.
Wanka da turare yayi sannan ya fita falo.
Momy bata nan dan haka yayi bangaren ta. Ko da ya taba kofar a rufe take.
Dan haka ya juya ya fice, motar sa ya dauka ya fice daga gidan.
Gidan shi ya wuce kai tsaya. Gidan ne babba wanda yake dauke da babban falo sai kofa da take kallon gabas ita ce in an bude za a shiga bangaren Pretty, Da katon falo sai bed room guda biyu da kitchen da bandaki.
STORY CONTINUES BELOW

Gidan yayi kyau sosai. Sai dayar kofar dake kallon ta Pretty shine bangaren Aslam benene.
Shima katon falo ne sai Bed room guda biyu kamar yadda bangaren Pretty yake.
Sai wajen gidan kato ne, dan bayan gidan da an shakatawa ba kamar dayan gidan da yake da komai dan har garden da swimming pool ne a shi.
Zama yayi dadi tsakanin ango da amarya sai dai sabin halaye. Da yadda ya same ta.
Ta maida Aslam kamar bawan ta dan sai abinda ttace shi yake mata.
In ta ce, kaza dole yayi shi. haka in ta aiki shi da gudun sa yake zuwa.
Duk da wani lokacin yana mamakin sa in ya kudurce a ransa bazai ba sai ya kasa.
Kamar ko da yaushe yau ma gefen karfe biyun dare ya zame jikin sa daga na Pretty.
Bandaki ya shiga yai wanka ya dauro alwala.
Sallah yazo ya dinga yi dan sai gab da asuba ya zauna yana karanta alkur’ani.
Ana kiran asuba kuma ya mike ya tafi massalaci.
Bai dawo ba sai karfe bakwai. Amman har lokacin Pretty ko mikewa batayi ba bare ta yi sallah.
Gidan dai yan aiki suna ta gyara shi. dan yan aikin da tazo dasu sunfi hudu kowa da aikin sa.
Daga mai gyara mata turaka sai mai gyara mata kitchen da girki.
Sai mai mata gyaran jiki da mai mata wanki under wears din ta.
Sai wani yaro dake mata sharar harabar gidan.
Ita ba abinda take sai dai a kawo mata taci ta koshi ta kwanta.
Dan ba abinda ttake yi. Daga zama sai kallo sai kuwa fita yawo.
Dan wani lokacin ta fice tin safe sai dare take dawowa.
Aslam kuwa da yake ba gwanin cin abincin masu aiki ba sai dai yaje gida ya ci.
Haka yake rana da dare. Duk ya rame ya zama wani iri da shi.
Ita Momy ma tausayi yake bata. Haka shi da baya son hayaniya dan gayu ya tsara yadda zai na jin dadi da matar sa.
Sai dai ya dawo ya tadda uwar lalaci a kwance yan aiki suna mata tausa.
Ko wani lokacin ya dawo ya tadda bata nan.
Bangaren Asma’u kuwa sai da tayi jinya sosai a makkah dan sai da Buhari da sir sabir suka je duba ta.
Sai da tayi sati biyu a asibiti sannan aka sallamo ta.
Ranan tana daki a kwance. Mami da Sir Sabir da Yaa Buhari suna falo suna hira.
Sir Sabir ne ya tambayi mene ya jawo wa Asma’u hawan jini haka.
Shiru Mami tayi kafin ta bashi labarin komai.
Sir Sabir sosai ya tausayawa Asma’u duk da yana mai godiya da Allah wata kila rabon sa ce shiyasa Allah yayi ba ai auren ta ba.
Daman ance, *Matar mutum kabarin sa* in Allah yayi rabon sa ce shikenan.
Sir sabir ya ce,
“Mami yanzu kina nufin Aslam yai aure?”
A kunne Asma’u kenan lokacin da ta fito daga daki.
Faduwar ta kawai suka ji. Da gudu sukayi wajen ta.
Nan da nan suka kara daukar ta sai asibiti.
Da kyar suka samo numfashin ta ya dawo dai dai.
Dr sai fada suke dan zuciyar ta da kamo da ciwo. Banda jinin ta da ya hau. Ya ce,
“Allah yasa ta tashi lafita dan ba karamin hawa jinin ta yayi ba.”
STORY CONTINUES BELOW

Kuka Mami ta dinga Sir Sabir ne mai lallashin ta dan Yaa Buhari ma ya rasa me yake masa dadi.
Abinda baya so Asma’u taji kenan ya baro ta daga kano amman dai da taji.
Wata zuciyar kuma ta ce,
“Shikenan yanzu ai komai jjuj zo da sauko tinda ta san komai.”
Sai da tai kwana uku a kwance kamar gawa.
Dan likita yai mata allurar da zata sa ta sami hutu ko nutsuwar ta zata dawo.
Kwanata hudu sannan ta farfado shima da kuka.
Dan sai a lokacin ta samu damar kuka. Ba karamin tashi hankalin ta yayi ba.
Asma’u kuka take kamar ranta zai fita. Mami ce ke lallashin ta.
Asma’u ta ce,
“Mami me nai wa Yaa Aslam? Anya Mami. Mami wallahi ba Yaa Aslam dina bane sai dai wani Yaa Aslam bazai taba yi min haka ba. Mami Yaa Aslam da ya ce min ‘yai min alkawari bazai guje min ba. Ya ce, In dai soyayyar sace na gama samu, kuma insha Allahu babu kishiya. Mami amman kuma shine yayi aure ya manta da duk alkwarin da ya sabar min dasu. Mami ce min yayi fa, ‘in bar tsoro, in sanya a rai na za ayi auren mu. In Allah ya yadda zamuyi rayuwa, matsayin ma aurata za muyi shakuwa. Ba gudu ba ja da baya sona zai tayi zai zauna dani har karshen rayuwa. Mami amman ji ya guje ni. Mami shiyasa nace miki Yaa Aslam bazai taba bari na ba.”
Sai kuma ta fashe da kuka. Dan har numfashashin ta ya fara dauke wa dan sai da aka kira Dr yai mata allurar bacci sannan aka samu tayi shiru.
Sosai Asma’u ta kuma ramewa. Ta kuma zama shiru shiru da ita dan magana ma ba sonyi take ba.
Yau kamar kullum tin da aka sallamo su a asibiti take kuka su koma gida kawai tinda abinda aake boye mata ya fito fili.
Sosai take rigima dan yanzu rigima ta dada yawa haka kawai sai ta tasa Mami a gaba tana mata shagwaba.
To yanzu ma tana kwance a falo sai tunani take, bama lokacin da suke zaune da Dadyn ta,
Dadyn ta ya fado mata da inda yake Tambayar ta abinda take bukata na bikin ta. Ta ce.
“Dady da sauran lokaci fa.”
Dadyn ya ce
“Haka ne, amman na fison komai na gama shi da wuri dan bamu san me lokaci zai bayar ba “
“Haka ne Dady. Amman ni bana bukatar komai.”
“Kin tabbata?”
“Eh Dady.”
“Shikenan na miki transfer din kudi ta account din ki kingan su.”
Kai ta girgiza ta ce,
“A’ah!”
“Ki duba wayar ki, zaki gani. Dan haka ki ajiye in lokacin bikin yazo in kina bukatar kudi ki huta ba sai kin hau tambayar Mami ko Yayun naki ba.”
Murmushi tayi ta ce,
“In ban tambaye su ba ai ina da Dady ko?”
“haka ne! Kina da Ni amman in ina nan ba.”
Murmushi tayi ta ce,
“Dady tafiya zaka yi ne?”
Kai ya girgiza ya ce,
“Ko daya in na mutu nake nufi.”
Damuwa ce ta sauka akan fuskar Asma’u sosai har ta kasa furta komai.
Dady ya ce,
‘Haba *Husnahn Dady* mene na bata rai dan na fadi abunda dole ne ya faru. Ki daina sa damuwa aranki nasan ko na mutu kina da masu rike ki amana. Amman mutuwa tana kan kowa. Kowa lokaci yake jira da tazo kuma bata jira dauka kawai take. Gara duk abinda zamu nayi muna tunawa da ita. Kuma muna sawa a ran mu a ko da yaushe zaata iya zuwa ta dauke mu. Ki daina damuwa. Allah shi ya tsara mana rayuwar mu kuma in yai nihar mutun ya rayu sai kiga ya shekara nawa ma bai mutu ba. Ina iyayen mu duk sun mutu to muma haka wata rana zamu tafi. Fatan mu da addu’ar mu Allah yasa mu cika da imani kuma Allah yasa can ta fi nan
Hawayen idon ta ta goge ta ce,
‘Allah sarki ashe Dady mutuwar kuwa zakai da gaske ke.”
Sai maganar sa ta karshe da ya ce,
‘ *Husnah* dan Allah kar ki manta kina sa ya’yan ki suna min addu’a.’
‘Insha Allahu. Dady ka daina sa wannan a ranka. Kai ma zaka rayu da su. Su sanka insha Allahu.’
Tana tunawa ta goge hawayen idon ta ta ce,
“Dady Yaa Aslam ya juyan baya bansan me nai masa ba.”
Sai wani kukan jin kanta na ciwo yasa tai shiru ta lumshe ido kawai.
*Allah sarki Husnah
Brodas nd sisters ya kk na sameku lpy. Kuyi hakuri kuci gaba da kasancewa dani.
Komai na duniya yana da darko da karshe. Ko wane tsanani yana tare da sauki.
Bawa bay gujewa kaddara ubangiji. Sai dai muyi ta addu’a Allah daura maba abibda zamu iya.
Nagode da kaunar ku. Nima ina kaunar ku.
Ina barar addu’ar ku. Kwana biyu kai na na matsamin da ciwo. Dan Allah kusani a addu’a Allah ya yayewa musulmai baki dayaTana kwance Sabir ya shigo. Zama yayi ya zuba mata ido.
Sunan ta ya kira ganin alamar ba bacci take ba.
Ido ta bude wanda sukai jajir dasu.
“Subhanallah!”
Ya fada da sauri yana matsowa wajen ta.
Kallon ta yai ya ce,
“Jikin ne?”
Kai ta girgiza. Ya ce,
“Kuka ko?”
Kasa tai da kan ta. Shiru yayi kafin ya ce,
“Haba *Husnah!* “
Da sauri ta dago kanta. Tinawa da mutum biyu ke yawan kiran ta da sunan gashi basa tare.
Daga Dadyn ta sai Yaa Aslam. to Dady ya mutu, Yaa Aslam baya tare da ita.
Ashe zata kara samun wanda zai kira ta da wannan sunan da tafi jin dadin sa akan ko wanne.
Kallon ta shima yake ido cikin ido. Kasa tai da idon ta, tana kokarin mai da kwallar da ta fito mata.
Magana ya farai mata cikin sanyi wanda taji kamar Yaa Aslam ne ke lallashin ta.
Ya ce,
“Ki daina kuka. Kina godewa Allah akan duk abinda ya faru dake. Jarrabawa d Allah ke miki in kika cinye baki san wane tukwici ne zai biyo gare ki ba. Kina sa hakuri da dangana a zuciyar ki Allah zai miki sauyi da mafi alheri da izinin Allah.
Kai ta daga. Tana jin sanyi a ranta kamar yadda Yaa Aslam ya sabai mata.
Ya ce,
“Walalhi in na gan ki cikin halin damuwa ina finki shiga damuwar.”
Da sauri ta dago ta kalle shi. Dan sai taji kamar Yaa Aslam dan shi yake fada mata wannan kalmar.
Kasa yai da kai dan baisan lokacin da ta fito daga hakin sa ba.
Hira ya dinga bata. Dan har da su dariya tana rike ciki tsabar dariya.
Mami ce ta fito ta same su a haka. Dadi taji ganin yadda Sabir ke sa mata auta tayi dariya.
Zama Mami tayi ita ma ana yi da ita har Buhari shima ya fito aka dinga yi da shi.
Sosai ta rage damuwar da take ciki.
Amman da magariba kuma sai ta sawa Mami daru kan su koma gida ta fara aiki a asibitin ta.
Sosai Mami taji dadi da taji Asma’u na son fara aiki dan da ko maganar sa batayi.
Ai kuwa cikin satin su ka daga suka yo Kano.
Gidan ssu a gyare dan masu aikin su sun gyare masu shi.
Kowa dakin sa ya shiga yai wanka suka fito suka ci abincu.
A falo suka bbaje ana hira. Can Asma’u ta ce,
“Bro saura wata nawa bikin ne?”
Murmushi yayi ya ce,
“Wata daya fa!”
Ido ta zaro ta ce,
“Wallahi da ba dan Anty zee zaka aura ba da ba inda zamu kara tafiya. Kiji fa Mami da ya fada mana muje mu hado kaya kafin mu dawo amman yaki ko?”
Murmushi Mami tayi. amsa’u ta ce,
“Mami nan da sati fa zamuje mu hado wani sati mai zuwa kuma akai kaya.”
Mami ta ce,
“Duk yadda kika ce.”
STORY CONTINUES BELOW

Asma’u ta kalli Mami ta ce,
“Na kuwa bude asibiti na hau tafiya kuma.”
Mami ta ce,
“Me zai hana.”
“Shikenan. Allah Yaya ina kara fada maka dan Anty Zee ce da ba inda zani.”
Murmushi yayi ya ce,
“Godiya nake? Nawa kuke bukata.”
Hararar sa Asma’u tayi ta ce,
“Ai ATM zaka bamu kawai sai yadda kaga saura.”
Dariya yayi ya ce,
“Mami dan Allah a dan tausya min dan naga wannan kanwar tawa so take ta sa na rasa ko na shinkafa ne.”
Dariya Amsa’u tayi ta ce,
“Ai da sauki in dai na shinka fa ne, zan dire maka kayan abincin shekara ma.”
Sukai dariya gaba daya.
Cikin ikon Allah a satin akai bikin bude asibitin.
Inda suka dauke kwararun ma’aikata.
Sosai ake aiki dan asibitin ya karbo. Sunan Dady ta saka wa asibitin aka saka masa. *Suleiman Specialist Hospital*
Taimako sosai yake a asibitin dan har ragi take na kudin marasa lafiya.
Sati daya da bude asibitin tafiyar su ta kama.
Komai ta bari a hannun Yaa Buhri. Inda suka tafi ita da Mami.
Sosai ta dinga jidowa Zee kaya masu kyau da tsada.
Set biyu suka hado mata sannan suka hado na fitar bikin su.
A lokacin ne Asma’u ta sha kuka tinawa da tai ita ma fa wai nata na nan ko.
Sai ta tuna lokacin da take gwada kayan da zasu yi fitar biki da Momy ta kawo mata.
Kuka sosai take sai da Mami ta shigo ta tadda ta. Mami tasan me ya sata kuka dan haka hakuri ta dinga bata.
Kwanan su shida suka juyo suna dawowa suka sanar da Uncle Abubakar shi ya sanar da Dadyn Aslam da uncle iliyasu akafadawa Gidansu Zainab.
Aka kai laife aka sa biki sati biyu masu zuwa.
Tinda Asma’u ta dawo ta kuma komawa shiru shiru.
Daga wajen aikin ma sai ta kulle a office tai ta kuka.
Haka biki ya dinga karatowa. Ta dibi dinkinsu takai musu.
Sir Sabir ne ya ce, zai na taya ta yin aiki.
Wanna yasa ya koma asibitin ta. Yana dan taimaka mata in bai da aiki da yawa.
Tana zaune a office din ta. Ta saka wani yellow material sai blue din mayafi da tayi rolling dinshi.
Tayi kyau sosai ta saka blue din sandal da blue din jaka.
Aiki take yana duba abu a system din ta.
Kamar kullum yau ma Yaa Aslam ne ya fado mata. Kai ta kifa kanta a benci tana ta kuka.
Da sallama ya shigo office din nata. Wanda ya haduwar kai ba zaka ce office bane.
Sai kamshi da sanyi AC ke ratsa shi gefe TV na aiki.
Sanye yake da blue din shadda yayi kyau dashi.
Kansa ya saka hula hannun sa daure da bakin agogo. Kafar sa sanye da bakin takalmi.
Yayi kyau sosai duk wacce ta kalle shi sai ta so shi.
Har ya zauna bata san da shigowar sa ba. Ganin bata san ya shigo ba yasa ya mike ya matsa kusa da bencin ta.
Dan bubbugaga table din ta take, yayi tai saurin dagowa idon ta da hawaye.
Kallon ta ya tsaya yi. Ran sa abace. Ganin sa yasa ta fara kokarin goge hawayen ta.
Zama yayi ya ce,
” *Husnah* ke fa bakya ji ko? Wai bakya son lafiyar ki ne, kita sa damuwa a ranki. To in ba ki damu da rayuwar ki ba ni na damu da ita. In bakya son cigaba da rayuwa ki ina son kici gaba da ita dan wani ne farin cikin ki ni kece farin ciki na. kece farin ciki na. Kece buri na.”
Sai kuma yai shiru. Kallon da take da mamaki a fuskar ta.
Kai ya gyada mata ya ce,
“Eh! Wallahi *Husnah* tin san da na fara ganin ki naji ina son ki. Son ki tin a lokacin ya shige ni. Na rasa ta yadda zan sanar dake ne. Ki bani dama *Husnah* zan yaye miki dukkan damuwar ki zan maye miki gurbin Aslam da yaddar Allah.”
Kai ta girgiza ta ce,
“Sir baza ka iya ba. Kasan waye Yaa Aslam a guna kuwa. Duk da abinda yai min jin sa nake har yanzu yana zuciya ta. Jin sa nake a rai na. Kasan tin ban san kai na ba Yaa Aslam ke so na. Da son sa na girma da son sa na san wace ni. Da shi kadai na taba soyayya. Sir ko ban auri Yaa Aslam ba to nasan bazan kara soyayya ba. Bazan taba daina son sa ba. Son sa ya riga ya zama jinin jiki na raba ni da shi bazai taba yiyuwa ba. Kayi hakuri nagode da soyayyar ka.”
Ta mike tana goge hawayen ta tana gogewa yana kara zubo mata.
Jakar ta, ta dauka ta fita daga office din da sauri.
Yanzu ita tasan soyayyar maso wani take.
Tinda ita take son sa shi kuma baya son ta.
A haka ta shiga motar ta, tayar da motar tayi ta nufi gidan su zee dan yin rabon kati da zasu fara.
Tana shiga ta gaida Maman Zainab sannan ta shige cikin dakin ta.
Tana kwance tana waya da Yaa Buhari sai soyayya suke yi.
Asma’u kuwa na zaune abin duniya ya isheta.
Jin hirar da Zainab take a waya shi yasa ta fara zubar da hawaye.
Wacce soyayya ce bata samu ba. Amman yanzu ita ce a halin soyayya ta juya mata baya.
Tana son Yaa Aslam baza ta taba daina son sa ba.
Dan addu’a take Allah ya cire mata son sa amman sai son sa dake daduwa.
Bata san lokacin da Zainab ta gama wayar har ta zo gaban ta ba.
Sai da ta dafa ta sannan ta dago kanta. Damuwa fal a fuskar Zainab ta ce
“Haba Asmmy mene kuma?”
Hawayen ta goge ta ce,
“Kar ki damu. Ina kati nan. Ina son zan kaiwa Maimuna yau dai naje gidan su.”
Kai Zainab ta gyada mata ta ce
“Karfe biyu ai dai kya yi sallah kici abinci sai muje ko?”
Mikewa tayi ta shiga bandakin dake cikin dakin.
Alwala tayo tazo tai sallah ta ci abinci sannan ta mike.
Mikewa Zainab tayi suka fita. Duk inda suka san da yan class dinsu sai da suka kai musu.
A hanya Asma’u ta ce,
“Wato baza ki zo ki karbi aiki ba sai kinyi aure ko?”
Kai ta gyada mata ta ce,
“Ki bari naje na gama cin amarci na tukkuna sai na fara. Yanzu haka kawai a ban hutun sati biyu mai naci.”
Kwafa Asma’u tayi ta ce,
“In ma zan baki ba.”
Dariya Zainab tayi ta ce,
“Oh sai kin bani. kinsan zan iya tafiya ta ai ba tare da an ban ba ko My husband yazo ya amsar min. Ko Mami nah ta ce na je na huta.”
Duka Asma’u ta kai mata ya ce,
“Wallahi yarinyar nan kin min wayo.”
Zainab ta ce,
“Wace yarinyar? Anty dai.”
Suka sa dariya.
Daga nan suka wuce gidan su Maimuna.
Da tambaya aka nuna musu gidan su Maimuna.
Gidan an gyara shi ya zama ginin bulo da bulo. Sannan anyi wani katon shago a jikin gidan.
Da sallama suka shiga gidan. Falo suka shiga suka tadda Baba a zaune.
Har kasa suka durkusa suka gaishe da ita.
Ta amsa cikin fara’a. Zainab ce ta ce,
“Baba Maimuna na nan.”
Baba ta ce,
“Tana nan.”
Ta kwada mata kira. Da sauri ta fito daga dakin ta.
Tana sanye da riga da zani a jikin ta. Tayi kiba tayi haske.
Tana ganin Asma’u tayi gun ta, ta rumgume ta.
Baba ta kalla ta ce,
“Baba wannan ita ce, Asma’u da nake baki labari wannan kuma kawar ta ce Zainab duk yan makarantar mune.”
Baba ta ce,
“Ayya sannu Asma’u ya karin hakuri Allah masa rahama.”
“Ameen!” Suka amsa. Maimuna ta kamo hannun su suka shiga.
Zobo aka kawo musu da ruwa. Zobon Asma’u ta sha.
Kallon ta Asma’u tayi ta ce,
“Sis makaranta kun gama ko?”
Kai ta gyada ta ce,
“Wallahi sai jiran sakamako.”
“Allah bada sa’a!”
“Ameem!”
Asma’u ta ce,
“Ya batun aure kuwa.”
Murmushi Maimuna tayi ta ce,
“Kamar kin sani sauran wata ukun biki na.”
Ta ce,
“Ina Nazir dina. Ai sis ya dawo. Wallahi ban boye masa duk halin da na shiga ba. A haka kuma ya ce zai aure ni dan shi tsakani da Allah yake so na. Kalli gidan nan shi ya gyara mana ya budewa Baba na shago yake mana cefane. Ga firij da ya siyawa Baba take lemo da ruwa. Wallahi komai Alhamdulillah dan Yaa Aslam ya taimaki rayuwa ta na koma ga Allah kuma na samu canji mai yawa.”
“Alhamdulilah!”
Asma’u ta fada.
Maimuna ta ce,
“Wallahi rannan na ce zan zo na fada miki komai ma.”
“Allah sarki sai gamu.”
“Eh!”
Kati Asma’u ta mika mata. Guda uku da na yini da dinner ita da saurayin ta sai na daurin aure.
Amsa tayi ta ce,
“Bikin kine?”
Kai Asma’u ta girgiza ta ce,
“Na zee ne da Yaya nah.”
Dagowa tayi ta ce,
“Gaskiya ne wannan amintar tayi wallahi. Allah ya kai mu. Allah sanya Alkhari Allah kawo namu.”
“Ameen!”
Suka amsa.
Maimuna ta ce,
“Ina Yaa Aslma kuwa?”
Shiru Asma’u tayi.
Zainab ce ta ce,
“Ya na nan.”
Asma’u ta ce,
“Yayi aure ma ai.”
Da sauri Maimuna ta ce,
“Ke kuma fa?”
“Allah baiyi ba.”
Kai ta dafe ta ce,
“To Allah yasa haka ne mafi alheri. Allah ya sada kowa da alherin sa.”
“Ameen!”
Suka fada.
Da zasu tafi sai da ta kira Nazir suka gaisa sannan suka tafi.
Daga nan suka cigaba da rabon kati. Sannan ta maida Zainab gida.
STORY CONTINUES BELOW

Tana komawa ta fada kan cinyar Mami ta ce,
“Mami na gaji.”
Mami ta ce,
“Sannu!”
Ta fara matsa mata kafa. Asma’u ta ce,
“Mun fara rabo fa, har mun kaiwa Maimuna ita ma saura wata uku bikin ta.’
Mami ta ce,
“Masha Allah. Allah sanya alheri.”
“Ameen!”
Ta fada. Tana mikewa.
Daki ta haye ta shiga bayi. Wanka tayi ta fito.
Ta zauna kan gado. Ba abinda ya fado mata sai lokacin da tana makaranta da a lokacin Yaa Aslma ya kira ta yaji ya ta dawo.
Sai ta tuna lokacin da safe, kafin ta tafi ya kira ta. Ta tura mada pics din ta. A hanya ya kira ta. A ckul ya kira ta. In ta dawo ya kira ta, sannan da dare ma haka.
Amman yanzu ko da wasa bai taba trying ya kira ta ba.
Hawayen idon ta ta goge ta tuna lokacin da suke hira.
Da suke zaune a garden lokacin da ta ce,
“Ya Aslam na maka alkawarin bazan taba barin ka ba zan kasance da kai a duk halin da kake ciki. Zan baka duk kan kulawa wacce ta rataya a kaina.”
Murmushi tayi ta ce
“Ni na rike maka alkawari amman kai ka manta. shiyasa na so hanaka min wannan alkawarin.”
Ido ta lumshe ta tuna abinda ya ce mata a lokacin
“Nima nayi miki alkawari….”
Asma’u ta ce,
“A’ah ni ba sai kayi ba.”
Yaa Aslam ya ce,
“Saboda me?”
Asma’u ta ce,
“Na yadda da kai zaka kula dani. Nasan ko ba aure a tsakanin mu zaka kula dani. haka kuma nasan zaka kasance dani. Wannan ma nasan zaka iya. Wanda zaka fada bana son yazo ne faru ba shine kace baza kai min kishiya ba.”
Kallon ta yayi ya ce,
” *Husnah* kenan baki yadda dani bane.”
Kai ta girgiza ta ce,
“A’ah na yadda da kai. Ai ba mu san yadda Allah ya kaddara mana ba. Su wadan can nasan ko ba aure zamu kasance tare “
Murmushi yayi ya ce,
” *Husnah* Nai miki alkawari bazan guje miki. In dai soyayya tace kin gama samu, kuma insha Allahu babu kishiya.”
Murmushi tayi jikin ta a sanyaye ta ce,
“Toh Ya Aslam. Amman ina tsoro wallahi.”
Ya ce,
“Ki bar tsoro, ki sanya a ran ki za ayi auren mu. In Allah ya yadda zamuyi rayuwa, matsayin ma aurata za muyi shakuwa. Ba gudu ba ja da baya sonki zan tayi zan zauna dake har karshen rayuwa.”
Kanta ta sunkuyar ta ce,
“Allah yasa.”
“Ameen!”
Ya fada yana dago kanta.
Murmushin yake tai masa. Fuska ya bata ya ce,
” ki fadan damuwar ki?”
Murmushi tayi ta ce,
“Ina yawan jin faduwar gaba Yaa Aslam kuma nafi alakanta haka da soyayyar mu. Ya Aslam ina tsoro. Tsoro ma ba kadan ba.”
“Kinsa dai ki kadai ce a Cikin rai na ko? Wallahi *Husnah* ke kadai ce buri na da muradi na ban da burin samun wata mace in bake ba. filin zuciyata ko ta ina kece bake, ba sauran wajen da wata zata shigo shi to kwanyar da hankalin ki.”
“Kallon ka kadai nayi da ido nishadi yake sanya ni. Kai ne muradi na. farin ciki na abin alfahari na. Dole ina tsoron rasa ka da kai kadai na yadda na aminta da kai na fara soyayya dakai nake son kare ta in har na raka ya kake zaton zan kasance.”
“Allah ma zai sa ke *tawa ce* “
“Allah yasa.”
Ya ce,
“Ameen!”
Shiru sukai ya ce,
“Kinsan me?”
Kai ta girgiza masa. Ya ce,
“Ina bude ido na farka a bacci ba wanda nake son na gani a dama na sai ke. Shi yasa da na tashi hoton ki shi nake fara kalla. Bana gajiya da kallon kyakyawar fuskar ki.”
Murmushi tayi ta ce,
“Yaa Aslam ina rasa a cikin mu wa yafi son wani.”
Ya ce,
“Kinsan me?”
Ta ce,
“A’ah!”
Ya ce,
“Ki bari sai munyi auren anan za a ga wanda yafi son wani. Ni dai nai alkwarain bazan taba saki kuka ba. zan ta faran ta miki zan kula dake insha Allahu.”
Dariya tayi ta ce,
“Nima nai maka alkwaraiin kula da kai da sauke maka duk hakkin da ya hau kai na. Zan kasance mace ta gari me son farin cikin ka mai gusar maka da bakin cikin ka.”
Hannun ta ya kamo, ya ce,
“Oya Alkawari.”
Dagowa tayi ta kalli cikin idon sa ta ce,
“Nai maka alkawarin bazan taba daina son ka ba. Kuma zan kasamce mace ta gari a tare da kai kuma bazan taba guje maka ba.”
Murmushi yayi ya ce,
“Nima na miki alkawarin bazan taba guje miki ba haka nan zan ta son ki har karshen rayuwa ta zan kasance mai saki farin cikin ki.”
“Allah yasa.”
Ya amsa da
“Ameen!”
Kuka ne ya Kwace mata ta ce,
“Me yasa zaka min alkaawari ka sabar min da son ka bayan kasan baza ka cika ba. Ji fa ji Yaa Aslam yanzu ka kyau ta kenan. Ya zanyi wallahi na yafe maka. Na yafe maka. Amman bazan taba daina son ka ba da daina tuna kalaman ka aguna ba. Ka min dashen da fitar dashi tamkar rabani da rayuwa ne.”
Sosai take kuka har bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba.
Sai da ana kiran sallah sannan ta mike Alwala tayo tai sallah.
Ta jima akan sallaya tana mika rokan ta ga Allah. Har akai isha’i sannan ta mike ta koma kan gado.
Kwanciyya tayi ta kwanta bacci ya dauke ta.
Mami ganin bata ga sakowar ta ba yasa ta hau sama dan ganin me take.
Bacci ta ganta tana yi zama tayi tana shafa kan ta.
Ajiyar zuciya taji tana saukewa. Kallon ta tayi tasan tayi kuka.
Ji tayi tana cewa
“Yaa Aslam me nai.maka?”
Sai kuma tayi shiru ta gyara kwanciyyar ta.
Addu’a Mami ta kara tofa mata sannan ta mike ta sauka.
A falon sama ta zauna Buhari ya zo ya zauna ya ce,
“Mami ina Autah ne?”
Mami ta ce,
“Tayi bacci.”
To daman batun abubuwan da kuke bukata ne.
Mami ta ce,
“Ran Dinner abinci zaka sa hotel su kawo. ran yini kuma Asma’u tace wai take away din snack zai ayi. Daurin aure ma ka saka ai mana order. Maji da lemo da ruwa kawai.”
“To Mami!”
Mami ta ce,
“Gidan sunce gobe zasu yi kafi.”
“Eh haka Asma’u ta fada min dazu.”
“To Allah nuna mana.”
“Ameen!”
Mami ta ce,
“Zaka kaiwa Momy kati na gobe.”
Kai ya gyada ya ce,
“Allah kai mu.”
“Ameen!”Sabir kuwa tinda Asma’u ta fita ta bar shi da tunani kala kala.
Allah ya sani yana son Asma’u kuma yana son ya aure ta.
Mikewa yayi ya rufe mata office din shima ya fita ya tafi gun Buhari suna shirye shiryen biki.
Washe gari da safe Buhari ya dau hanyar Abuja a mota
Asma’u yau ma daga Wajen aiki ta wuce Gidan su Zainab.
Yaa Buhari ya isa Abuja lafiya. Momy sai nan nan take da shi.
Ta cika masa gaban sa da kayan abinci kala kala.
Suna zaune suna hirar su Mami. Tana kara tambayar sa ina ‘yar ta.
Da yake haka take kiran Asma’u. Buhari ya ce,
“Tana nan ai su Asma’u an zama busy daga wajen aiki sai shirye shiryen biki.
Dan cewa tayi dama sai bayan biki aka bude. Damuwa dai ba laifi ta rage ta duk da tana cikin ta mu take nunawa ba ta cikin ta.”
Mami ta girgiza kai ta ce,
“Allah sarki. Allah kawo miji na gari. Ni ina tunanin ma na samo mata miji da kaina dan na wuce haushin da aka bamu.”
Dariya Buhari yayi ya ce,
“Haba Momy.”
Momy ta ce,
“Wallahi.”
Buhari ya ce,
“Ai kam tinda nazo naje na dubo Yaa Aslam da amarya.”
Shiru Momy tayi kawai. Momy ta ce,
“To ni me kake so nai maka ne.”
“Duk abinda Momy tayi nagode.”
“To ai shikenan. duk abinda ka gani ka godewa Allah tinda kaki zaba.”
Dariya Buhari yayi. Momy ta ce,
“Kaje ka huta ko?”
Kai ya dan sosa ya ce,
“Aah tukkuna dai zanje gidan wani aboki na daga nan zani gidan Yaa Aslam,”
Momy ta ce,
“Toh!”
Momy ya tambaya address din Aslam sannan ya fice.
Yana fita yayi gidan abokin sa anan duk ya bashi katin nan ya rabawa sauran abokan su.
Daga nan yayi gidan Aslam. Gida ne mai kyau ya hadu, yana zuwa ya ce,
“Oh ikon Allah da tini Asmmy na ce a gidan Yaa Aslam. ikon Allah ance matar mutum kabarin sa ko nan gaba zasuyi aure waya sani sai Allah.”
Yana parking ya kira number Aslam. Aslam na dagawa ya suka gaisa kamar yadda suka ssaba.
Buhari ya ce,
“Yaa Aslam gani a compound din gidan ka.”
Aslam da sauri ya mike ya ce,
“Da gaske.”
Ya ce,
“Kazo ka gani.”
Da sauri ya katse wayar ya fito. Yana ganin Buhari ya rumgume shi.
Dariya ya saki ya ce,
“Amman naji dadi mu shiga daga ciki.”
Suka shiga. A falo suka zauna. Aslam shi ya kawo masa ruwa da lemo. Sanna suka zauna hira yana tambayar sa ya Mami da Mutan gidan.
Dan sunan Asma’u ma ya kasa ambata. Duk da a cikin ransa yana son ya tambayi Ya Asma’u take amman ya kasa.
Buhari ganin bai ga Matar Aslam ba ya ,
“Yaa Aslam Ina Anty nawa.”
STORY CONTINUES BELOW

Kai Aslam ya dan sosa ya ce,
“Ta fita unguwa ne.”
Buhari ne ya mikawa Aslam katin bikin sa. Amsa Aslam yayi yana washe baki yana ta sanya albarka.
Har magariba suna tare dan a gidan sukai sallah.
Buhari ya tashi zai tafi kenan sai ga Pretty ta shigo. Cikin shigar riga da wando, kayan sun matse ta sai wani mayafi da ta yafa abin ba kyan gani.
Buhari da farko bai gane wace ba sai da ya ga Aslam ya ce,
“Madam! Barka da zuwa.”
Kallon su tayi a yatsine ta watsar ba tare da ta ce, Uffan ba ta wuce ta kwanta akan kujera tana kwallawa daya daga cikin yan aikin ta kira.
Da sauri ta karaso. Ta bata umarni ta dauko mata lemo.
Mikewa tayi da sauri ta miko mata ta dawo.
Buhari kuwa ya baki ya saka yana kallon ta.
Kallon su tayi a yatsine ta ce,
“Ina zaka ne?”
Kai Aslam ya girgiza ya ce,
“Raka shi zan yi.”
Tsaki Buhari ya saki yayi waje. Da sauri Aslam ya biyo shi a baya.
Yana karasawa ya shiga motar sa. Aslam ne ya leko ya ce,
“To bro nagode a gaida gida da su Mami. Sai munzo bikin ko?”
Kai Buhari ya daga ya ce,
“Allah kawo ku.”
Yai gaba. A ransa yana mamakin wacce irin mata Aslam ya aura.
Anya kuwa haka ta bar shi. Da wannan tunani ya karasa gida.
Yana zuwa Momy ya tadda a falo. Abinci ta bashi ya ci sannan suka tsaya hira.
Can Buhari ya ce,
“Momy daman haka Matar Yaa Aslam take?”
Momy ta ce,
“Ta maka rashin mutuncin ko?”
“Uhmm batai min komai ba. Ni ko kallo na ma batai ba. Amman Momy kinga da shigar ta take yawo. Bayan nasan Yaa Aslam ba yason shigar banza. Kuma Momy sam bata da tarbiyya kinga irin kallon da take mana kuwa.”
Ajiyar zuciya Momy ta sauke ta ce,
“Wallahi kowa complain din da yake min kenan in yaje gidan Aslam. Bansan me yake damun Aslam ba. Amman abin ba dadin ji. Ka ganni nan ban taba ganin ta ba ma bare na san ya take.”
Kai Buhari ya girgiza ya ce,
“Momy bafa kiga ba.”
Momy ta ce,
“Uhmm wallahi Buhari na rasa ya zanyi, ni yadda aka ce min ma ita ta zama mijin ma. dan sai ta ce yayi zai yi in kuwa ta ce, A’ah bazai taba yi ba. Baka ga ba duk ya zama wani iri abin tausayi. Anan fa kullum yake cin abinci dan wata rana ma ni nake aika masa har gida. Wallahi al amarin Aslam yana bani mamaki sosai.”
Buhari ya ce,
“To Momy bakya ganin ba haka suka barshi ba. In ba haka ba, abin ai yayi yawa.”
Shiru Momy tayi tana nazari ta ce,
“Kuma fa haka ne, wallahi ban taba kawo haka ba. To yanzu ya zanyi.”
Buhari ya ce,
“Zan fadawa Mami da Asma’u bama Asma’u tana da sani sosai a addini. Nasan zata san abin yi. Amman dai ya dage da addu’a muma mu dage da taya shi da addu’a.”
Mami ta ce,
“Insha Allah!”
Haka suka tashi suka tafi kowa ran sa ba dadi.
Buhari kuwa sosai yake tausayawa Aslam dan ya kasa sukuni.
A haka yai bacci. Cikin dare ma ta shi yayi ya dinga masa addu’a.
Asma’u kuwa Sai magariba ta koma gida. Tana shiga taga motar Sir Sabir.
Kai ta dauke tayi cikin gida. Yana zaune a falo yana cin tuwon da Mami ta dafa.
Tana shiga suka hada ido. Durkusawa tayi ta gaishe shi ya amsa yana binta da wani kallo wanda tasan Yaa Aslam na mata.
Ido ta dauke har zata wuce sai kuma taga Mami ta fito daga kitchen hannun ta rike da lemo da ruwa.
Karasawa tayi ta amsa, sannan ta zauna.
Mami ce ta kalle tace,
“Kun dawo?”
Kai Asma’u ta gyada. Mami ta ce,
‘Buhari ya kira ki ne?”
“A’a! Ya na ina ne banga motar sa ba.”
Mami ta ce,
“Ya tafi Abuja,”
Wata faduwar gaba taji dan tasan wajen Momy yaje, kuma zai hadu da Yaa Aslam.
Shiru kawai tayi ta jingina da kujera tana lumshe ido.
Mami ce ta lura da canjawar da tayi. Kallon Sabir tayi shima Asma’un yake kalla.
Mikewa Mami tayi ta hau sama. Yana jin shigar war Mami daki ya matso kusa da ita ya zauna.
Asma’u bata ji zaman sa ba sai kawai muryar sa da taji a dai dai kunnen ta.
Ido ta bude da sauri. Ido suka hada yana kallon ta ido cikin ido.
Duk sun kasa dauke idanun su. Shi wani kallo yake aika mata.
Ita kuma wani abu taga yana fitowa daga idon sa yana shiga nata.
Da sauri ta lumshe ido dan baza ta iya jure kallon da yake mata ba.
“Husnah!”
Ya kira sunan ta cikin sanyin murya.
Ido ta bude a hankali ta sadda kan ta kasa.
“Husnah! Wai haka kike so ki cigaba da rayuwa ba farin ciki. Ke kenan baza ki samu wanda zai sa ki farin ciki ba. Ki tattara komai naki kin bawa Yaa Aslam, husnah ba haka rayuwa take ba. A duk sanda wani ya ce baya yi da kai a lokacin wasu keyi dake, ki dauri ki ban dama zan kasance miki yadda kike so na kasance.”
Shiru Yayi yana kallon ta. Idon ta alumshe kuma daga dukkanin alamu tana jin sa. Kuma maganar ta ratsa ta.
“Husnah!”
Ya kara ambatar sunan ta.
Bude idon ta tayi da sauri jin kamar muryar Yaa Aslam.
Sai dai me ba shi bane, mikewa tayi da sauri tayi hanyar bene.
Har ta hau sai kuma ta juyo. Kallon sa tayi shima ita yake kalla.
Murmushi ta sakar masa kawai ta haye sama.
Mamaki ne ya lullube shi. Ya rasa murmushin nata me yake nufi.