RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 9 BY Fateeyzah mbs✍️

RAYUWAR CAMPUS CHAPTER 9 BY Fateeyzah mbs✍️

             Www.bankinhausanovels.com.ng 

 Kwashewa suka yi da dariya,,sannan summy tace “wlh ya tafi ko dai², ga 20k yace a baki, Allah ya k’ara sauki”.

“Osheyyyy na fa gode babes, bari sai gobe in kirasa in masa godiya” cewar Hibba tana mai k’arfan  kudin a hannun summy.

Har yanzu fuskar Amatu dauke da mamaki, tace “please kun barni a duhu, kumin bayani dallah²”.

 Meena ce ta amshe da cewa “dad’i na dake Amatu gajen hakuri, to ba wani abu bane, Hibba ce muka fita karb’o ma sak’o a hannun saurayinta, shikenan”‘

Mikewa tayi tana saka nightly tana mai cewa ”  ba shikenan ba, meye amfanin saka hijabs haka?”.

Dukkansu Hibba suka zuba ma ido suna jiran amsa, hakan yasa ta zama a bakin gado tare da sauke ajiyar zuciya, sannan tace “kuyi hakuri da abinda zan fad’a muku, summy, meena, wanda kuka je wurinsa, sunansa Bukar, Ex  Husband dina ne, yanxu haka biko yake yana neman mai dani, ni kuma bana son komawa, bai san irin rayuwar da nake a school ba, shi yasa an saka ku saka Hijab, saboda kamar yanda hausawa ke cewa “kamanninka, abokanka””.

Jin abunda ta fad’i ba karamin mamaki suka yi ba, don hatta Rebeccca da ke kwance sai da ta d’ago kanta, dukkansu samun wuri suka yi suka zauna, gaba daya jikinsu yayi sanyi, meena ce ta samu kwarin gwiwar magana tace “why Hibba?, why all this?, me yasa kika boye mana kin tab’a aure?, me yasa kika biye mana muna aikata zina alhalin kin tab’a aure, may be ma har da yara, ko dai baki yadda damu bane?”.

 A sanyaye ta amsa da “ina da ‘ya d’aya dashi, sunanta Anisa, kuma wallahi ba wai ban yadda daku bane, naga duk cikinmu ba wanda ya tab’a fad’in tarihinsa, amma insha Allahu yanxu xan sanar daku wacece ni”.

Dai² nan salma Vp ta shigo daki bakinta dauke da wak’a, ganin yanda suke zaune jikinsu a sanyaye yasa ta dakatawa hade da tambayarsu “lafiya”.

Hibba ce ta mata alama da ta zauna, ganin hakan yasa ta samun wuri kusa da Amatu ta zauna, yayin da itama Rebecca ta tashi zaune sakamakon itama alama da Hibba ta mata.

Wacece Hibba?

 Sunana Muhibba, mahaifina shatima da mahaifiyata falmata ‘yan maidugurine, sannan auren zumunci akai musu, saboda iyayensu maza, uwa d’aya uba d’aya suke, neman kud’i ya kawo mahaifina garin lagos, a unguwar Agege, iyayena talakawa ne sosai, sana’ar mahaifina faaci, mahaifiyata kuma kitso, ni ce ‘yarsu ta farko, sai kannina uku duka maza, Auwal, sani, salis, dukkammu munyi karatu a makarantar gwamnati, wanda na gama secondary ina da shekara 17.

Duk karshen shekara muke ziyartar maiduguri, wanda in mun je muna yin wata d’aya ne sannan mu koma lagos, hakan ta kasance shekaran da na gama secondary, muka rankaya muka tafi, mun sauka kowa na murnar zuwanmu, sai da muka kwana biyu muka huta, sannan muka fara zagaya dangi.

Bukar d’ane ga yayan mahaifina wato baba shareef, yayin da kuma mahaifiyarsa  Aunty yakurah ta kasance yayar mahaifiyata ubansu guda, kwata² babu shiri tsakaninta da mahaifiyata, wanda hakan ya samo asali tun lokacin da mahaifina ya fara tafiya lagos, Allah ya daura ma Yakurah kaunarsa, saboda tana kaunar zaman lagos a rayuwarta, sai dai duk yadda take shisshige masa idan yazo tana nuna masa so, shi kwata² hankalinsa baya kanta, yana wurin mahaifiyata wadda lokacin ma bata isa aure ba.

Wani zuwa da yayi ne mahaifinsa ya umurcesu shi da baba shareef,  da suje gidannsu mamana su zab’i matar aure a cikin ‘yan matan gidan, sai dai ko da suka je, mahaifina ya fara zab’an mahaifiyata, yayin da Baba shareef ya zab’i Aunty yakurah, wannan ya haddasa gaba mai tsanani tsakaninsu don ba irin borin da ba tayi ba kan mahaifiyata ta bar mata babana, amma itama mamana ta nuna baza ta bar mata ba, don itama tana sonsa, abu tun suna yi tsakaninsu har yakai iyaye da sauran ‘yan uwa sun sani, inda  nan mahaifinsu ya tsawatar, aka yi biki aka gama, babana da mamana suka wuce lagos, su kuma baba shareef da Aunty yakura suka tare anan cikin garin maiduguri.

 Haka rayuwa ta kasance, shekaru suka ja,  ko zuwa su mama suka yi bata zuwa gidanta, haka ita ma domin ko had’uwa wani wurin suka yi mamana ta gaisheta  bata amsata, yaranta shidda, Bukar shine babba, sai Shatima(mai sunan babana, sai Yagana, Aisata, Rukayya da auta mahmud,  akalla bukar ya bani shekara goma saboda bayan aurensu sai da mamana ta shekara goma  sha sannan ta haifani, sab’anin Aunty Yakurah da watanta tara ta haihu, sa’ata a gidan Rukayya, mu kanmu yaran babu shiri tsakaninmu , don already mahaifiyarsu ta gama cika zuciyarsu da tsananmu.

A wannan zuwan ne kakanmu na wurin uba, ya yanke shawarar had’ani aure da bukar, don a cewarsa hakanne kad’ai zai kawar da gabar dake tsakanin iyayenmu mata, naci kuka kamar zan mutu, haka ma mahaifiyata don ta san  ba wani maslaha da za a samu, sai ma dai wasu matsalolin su shiga ciki, haka ina ji ina gani aka daura min aure da wanda bana sonsa shima kuma hakanne a wurinsa, saboda so d’aya yazo ya ganni, shima kuma baram² muka rabu, iyayena sun yi kokari wurin ganin sun min kayan d’aki masu kyau da inganci, yayin da su kuma gidansu bukar suka min wani tsinanna lefe, don babu wani abun kirki a cikinsa, haka dai akayi biki aka watse, aka kaini can kusa da gidansu bukar, don gida biyu ya rabamu dasu, yayin da iyayena da k’annina suka koma lagos cike da tausayina.

Zaman aurenmu, zamane bamai dad’i ba sai wahala da zalunci daga wurin bukar da ‘yan gidansu gaba d’aya, wurin baba Shareef ne kad’ai nake samun sauk’i, sai dai shima ba mazauni bane, don Nguru yake sana’arsa.

Idan nace zan baku labari dak’i zamu dauki kwanaki muna yi, domin kuwa ba k’aramar wahala na sha ba.

Na farko, haka yake saduwa dani kamar wata dabba, babu wasanni bbu komai, hatta first night dinmu fata² yamin, ga duka da zagi, ga rashin Abinci, ga aiki kamar jaka, domin tun daga wankin mamarsa da kanninsa ni nake yinshi, hatta su yagana da aisata da suke gidan aurensu ni nake musu wanki, ga sana’ar mamanshi ta abinci shima kusan ni nake musu komai, saboda tun karfe shida na safe nake barin d’akina in tafi gidansu ban dawo wa sai 12 na dare, haka nayi ta wannan wahalar har na samu cikin Anisa, wanda nan Babban tashin hankalin yake, domin Aunty Yakurah tace ba zata had’a jini da Mahaifiyata ba, haka zata kamani da duka saboda cikin ya zube, jik’e² da kwayoyi babu wanda bata dura min ba, amma duk a banza ciki yak’i fita, wallahi hatta tsarkin borkono Aunty yakurah tamin, haka naci azabata, har ya dena, kullun da irin muguntar da take mini, aiki kuma ko da cikina ya tsufa babu fashi, haka nake yinsa, hatta ran da zan haihu sai dana yi wankin kayansu.

Haka nak’uda ta taso min da yamma, amma matarnan ko sannu balle ta taimaka min, karshe ma sai ta kulle min baki wai na dameta da ihu, haka kuma ta kulleni a d’aki  harda mukulli ta koma parlour taci gaba da kallonta, da taimakon Allah na haifi Anisa, sai da taji kukan jaririya tukunna ta zo ta bud’eni ta yanke cibi, ta dauke yarinyar, domin kallo daya ta ma yarinya Allah ya dasa mata kaunarta, hatta suna ita ta saka mata, tun kallon dana yima Anisa dana haifeta har yau ban sata a ido ba, saboda  a daren ranar dana haihu……….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *