RAYUWAR IRFAN CHAPTER 1 BY (UMMU KHAIRIYYA)

RAYUWAR IRFAN CHAPTER 1 BY (UMMU KHAIRIYYA)

Www.bankinhausanovels.com.ng 

✍️Irfan!!!! Irfan!!! wata Matashiyar mace na hango Kan wata kujerar katako tana ta kwad’a kira Wani Yaro ne da  beze Gaza Shekara 17 ba ya fito daga wani d’aki na k’asa Jikinsa Sanye da Uniform Me launin Rawaya, kusa da Matar data kirashi yazo ya Zauna gefenta Kan wata ya loluwar tabarma kana yace “Mommah nagama Shiryawafa” Dak’uwa tayi Masa Sannan Tace “Irfan Na hanaka kirana da Sunan Ya hudawan Nan Amma kak’i dainawa ko? .

Murmushi Ya yi Yace “Mommah bama wannan ba kinsan jiya A School ko Magana banyiwa Mubarak ba, Saboda na Ganshi da Su Sadi Reeza Shiyasa, Yana taimin magana Amma Ni nak’i kulashi”.

“Hmmmmm Irfan kenan kasan Baze gane Me kake nufiba Ahaka, kamata Ya yi  kaja shi Ajiki ka nuna Masa Abin da yakeyi badai dai bane.

Hakane zaka cetoshi daga Rayuwar dayake so yajefa kansa”,  “To Mommah Bari nawuce Saboda Kar na makara, Addu’ar fatan Alkairi Tai Masa  tare da Samasa Albarka.

Ficewa Ya Yi daga   gidan cikin Nishad’i da kwanciyar Hankali Direct gidansu Mubaraq ya nufa Koda Ya Shiga cikin gidan Shiru yaji ba Alamun Motsi Akata faren falon gidan, Sallama ya kwad’a Nan ma yaji Shiru can dai yaji Kamar Ana Sakkowa da Stears.

Umminsu Mubarak ya hango da Sauri yak’arasa gunta ya tsugunna Agabanta Had’i da gaisheta, cikin Fara’a ta Amsa Masa kana Tace “Har kazo ko Irfan Mutumin naka nacan Yana Sharar bacci Sai kaje kataso shi yau Hauwa Me Aiki ta Makara ya kamata Ace Yan zu tashirya Su Arfa ma”.

“Mik’ewa ya Yi ya yace “Bari naje nataso shi muwuce karmu makara” ko Ajikinta ta Shiga k’walawa Hauwa Me Aikinta Kira da Sauri Hauwa Me Aikin ta iso tana faman murza Ido ta zube gabanta tareda cewa ” gani Hajiya”

“Meyasa Baki Shirya yaran Nan ba gashi sun kusa makara”.Kiyi hak’uri jiya ban kwanta da wuri bane jiya”

“To naji kitashi kije ki shiryasu Sannan ki Kama Aiki Kuma Zan fita yan zu bazan samu dawowa ba saboda Zan wuce gidan k’awata Muna da biki sosai da suna Dan Haka ki kula dasu saina dawo”.

“To Hajiya insha Allahu Zan kula kamar yadda kika buk’ata”, Tafiya ta somayi irinta wayayyun Mata harta fice daga falon.

Shi kuwa Irfan Kai tsaye d’akin mubarak ya nufa Da Sallama ya shiga d’akin Can cikin bargo Ya hango Mubaraq Kan Makeken gadonsa.

Takaici ne ya kamashi zuwa ya Yi ya yaye bargon firgigit Mubaraq ya tashi Tare da kaiwa Irfan duka da Mugun Sauri ya rik’e Hannun Mubaraq.

“Kai kenan Kazama kasa kullum cikin Barcin tsiya Duk Alherin da kake gani na Duniya da Lahira ba’a Samun sa cikin barci Dan Haka Malami Mik’e mutafi School”.

Mubarak ne ya k’wace Hannunsa “Baka da kirki Irfan Ina cikin baccina Me Dad’i Ina Mafarkin zeeza kazo ka katsemin Bacci”.

Nan da nan Irfan ya had’e Rai “Mubarak Rayuwa da kake gani bakasa k’afa Acikin taba Duka-Duka Shkararka 17 fa Yan zu Ina Kai Ina zan can wasu Mata”.

Yarinyar da kowa Yasanta A School Fitsararriya ce ta bugawa A jarida Dan tana tak’ama Ubanta wanine. 

Kuma Kadena biyewa Sadi Reeza Yaron da Sunan sa na Musulunci ya can za shi zuwa na Yara Marasa kirki idan Zan Gaya maka kaji karka Sake Shiga Harkarsa Kadena kulashi Banaso kaima Kazama irinsa kasan Adadin Yara nawa ya koyawa D’abi’unsa cikin School dinnan to daga Yau Babu Kai babushi, In kuma ba Haka ba wallahi Zan Sanar da Abbanka kasan dai in ya Sani to wlh kashinka ya bushe”.

Da Sauri Mubarak yakama Hannun Irfan ya had’e da nasa guri d’aya da nasaYana Mai Rok’ansa da karya gayawa Abbansa “kaje kashirya Malam zanjiraka A Babban falo”.

Cikin Mintuna k’alilan Mubarak ya Shirya Dan yasan Halin Taufeeq Koda ya fito zau ne ya Sameshi Kan kujera Yana ganinsa kuwa ya mik’e “Muje ko” cewar Irfan  “Bari nayi Break fast Dan gaskiya inajin Yunwa”.

Hanyar waje Irfan ya nufa “katsaya kaci Saika taho Kai kad’ai banaso na Rasa Darasin farko Dan lokuta da dama Haka kake sawa Muke makara”.

Dagudu Mubarak ya nufi Stears yaje yaywa Dad d’insa Sallama tare da karb’o kud’in break d’insu Shida Irfan Dan kullum tare take ke Basu da Sauri ya fito Hara bar gidan be ganshi ba cikin Sauri ya k’wala wa Drivernsa Kira Sai gashi da Sauri yafito daga d’akin Da Aka bashi,

“Tada Mota!!-tada Mota!! maza muje Irfan Ak’asa ze taka  Har School d’in cikin Sauri Drivern Ya Shiga ya yiwa Motar key Shima Mubarak d’in Shiga Ya Yi Dan Yasan Halin Mubarak in Yana buk’atar Abu.

Tun fitowar Mubarak me gadi ya lura dashi ya je Wangale k’ofa cikin Wani gudu Drivern ya figi Motar Abakin Titi Suka Samu Irfan “Bro!!!! Kashigo Mutafi” Tahowa ya yi ya shiga Motar Drivern yaja Suka tafi.

Hak’uri Mubaraq ya Shiga bashi Koda Suka Isa School d’in Sun tarar Har Anfara Assembly layi Suka bi Suma, Kamar Yan da kowane Student ya yi Bayan Angama Sukayi Aji gaba d’a yansu Zeeza ce tazo zata Shiga Class Irfan Ma yataho Shida Mubaraq.

Sunkai bakin k’ofa A dai-dai zeeza tazo Kamar zata bige su “keeeeee!!!! Bakida Hankaline Agidan ku ba’a Gaya Miki gogayya da Maza Haramun bane ke wace irin sokuwa ce Dak’i k’iyar Aji wadda batayin Abin da ya kawota School Sai biyewa k’awayen ban za”. 

“Kai Ni kake gayawa irin wad’an Nan bak’a Ken magan ganun Aikuwa Sai NASA Sadi Reeza yay ma duka Agabana Naga Wan da ya tsaya maka Agarinnan”.

“Kiyi hak’uri my love be San ya muke dake bane” cewar Mubarak wani bak’in cikine ya tur nik’e Irfan ya Yi Aji cikin b’acin Rai Mubarak bayaji Mezesa bazai maida Hankali Akan karatunsa ba wannan wace irin Rayuwa yakeso ya jefa kansa da iyayansa Shi kad’ai Shine Babban D’ansu duk wani burinsu Yana kansa kuma Sun kwallafa Rai Akansa why Mubarak!!!!!!! Ya fad’a cikin k’araji tareda dukan Table d’in dake gabansa……….

          ASALIN LABARIN

…………✍️wanene Irfan? Sunan Mahaifin Irfan Alh. Habu Mahaifiyarsa Kuma Sunanta Saratu Mahaifinsa nada Arzuk’i Sosai Amma kud’insa banaci bane hasalima Gidan Zama ma Agidan k’asa Suke zaune.

Saboda shi duk tunaninsa Irfan da Mahaifiyarsa ne ke cinye Masa Abin duk yasamu Abinci ci kullum Sai ya Auna musu kafin yafita Sannan ya kulle d’akinsa.

Ba sabulun wanka bana wanki ba omo ba Suttura ba komai na kayan Amfanin gida ba zai siyaba Asibiti ma ba’a Zan cansa danshi ba Ruwansa da ciwo.

Da farko kafin ta haihu Suna zaman lafiya Amma tunda ta haifi Irfan Shikenan Kuma tun tana zuwa tana Kai k’ararsa gurin iyayansa Hardai tagaji ta Hak’ura ba yanda zatayi domin Mahaifinsa ya Rasu Agurin Mahaifiyarsa ya tashi.

Bata San b’acin Ransa kwata-kwata ko ta Kai Mata k’ara Bata wani d’aukan mataki, ita Kuma Ba yar’ Kano bace iyayanta yan’ jigawa ne Baya barinta zuwa gida da yake ya iya takunsa duk Sanda zata gida zai Siya Musu kayan sawa Sababbi.

Ita da Irfan ya had’awa iyayanta goma ta Arzuk’i yabata ta kaimusu Dan Haka duk Abin da zata fad’a musu basa yarda Haka take zau ne cikin bak’in ciki da takura Metsanani ga Abu kad’an Sai duka.

Haka take faman hak’uri dashi kullum cikin Babu Kuma Yana dashi Amma Sai Kiran Babu tun Irfan Yana d’an Shekara uku(3) ya fahimci Halin Mahaifinsa hakq Allah ubangiji ya Samasa zuciyar nema

Lokacin da Irfan yakai Shekara ta kwas yaga matsin ya yi yawa Sosai da Sosai Haka ya Fara tallan fiyo wata inya je islamiyya ya dawo Sai yaje ya Saida Ruwan ya Samo musu Abin da za suci Abinci.

Sun Had’u da Mubarak wata Ranar juma’a ya tafi tallan Ruwa Shi kuma sun taho Shida Mahaifinsa Amota Nan Suka bige shi Bayan sun kaishi Asibiti ya farfad’o Daddyn Mubarak
ya tambayi Irfan gidansu.

Koda ya fad’a Masa Sai yaga Ashe unguwarsu ma d’aya cewa ya yi ya rakashi gidansu Koda sukaje suka Sami Umman Irfan Hankalinta ya yi Matuk’ar tashi duk da bawani ciwo yaji Sosai ba.

Koda ya tambayeta Ina Mahaifinsa be kamata Subar yaro Kamar Irfan Yana tallan Ruwaba shekarunsa sunyi kad’an kamata Ya Yi ya kasance A Makaranta Yan zu.

Halinda suke ciki ta zayyanewa Daddyn Mubarak Dan Basu da wata Mafita, ya tausaya musu sosai Kuma yabata tabbacin Zaisa Irfan makarantarsu Mubarak Sai Drivernsa ya ringa kaisu tare.

Umman Irfan tayi Murna sosai da sosai Nan yasa Aka kawo musu kayan Abinci Masu yawa yace “zuwa dare zai dawo yagana da Mahaifinsa hakan kuwa Akayi bayan ya Abban Irfan yadawo Daddyn Mubarak yazo yasa Akayi Masa Sallama dashi.

Bayan ya fito Sun gaisa ya Yi Masa bayanin bige Irfan da ya Yi ya kuma d’ora da cewa “Zan d’auki Nauyin karatun D’an ka tun daga primary Har inda yaga ya yi Masa yanaso ya tsaya Amma inaso nai maka nasiha dakaji tsoron Allah, da Mata ya’ya’ da kake gani Amanace Allah yabamu Kuma Sai Ubangiji ya tsayar Damu Ranar Shaida ya tambayemu Akan kiwonsu Daya bamu”.

Dan Haka karike su sune Ahalinka idan girma yazo maka zaka gane cewa Sunada Matuk’ar Amfani”.

Godiya Abban Irfan ya Yi Masa Kamar ba komai Amma zuciyar sa bak’in k’irin Haka ya koma gidan Ranar sunga tashin hankali daga Umman  Har irfan d’in ya had’asu ya Zane Wai Sunje cikin unguwa suna tona Masa Asiri yana zaune cikin Rufin Asiri meye banai muku magan ganu dai iri-iri Haka ya Yi ta Sababi shi kad’ai.

Cikin ikon Allah Irfan ya Fara zuwa Makarantar su Mubarak Kuma Yana ganewq Sosai Saboda yanada hazak’a Haka ya Raba Abubu Wanda yakeyi Ranar Makaranta zeje Makaranta Ranar da Babu Kuma zeje tallan pure water.

Yan zu Irfan  da Mubarak Sun  shiga SS3 (Shekarar k’arshe ta kammala School d’insu A Nan Mubarak ya had’u da Sadi Reeza wan da Transfer Akai Masa daga wata Makarantar Aka kawo shi Nan.

Bayaji Sadi ya buwayi yaran Makaranta har Malaman Bai barsuba domin babansa Me kud’in gaske ne kuma An Shagwab’a shi Agida Shiyasa yake taka Wan da yaga dama.

Ita kuwa zeeza Asalin Sunanta Zainab gaskiya Itama Maman tace ta tab’a rata Sosai Dan ita da Maman Mubarak Aminai nai irin iya Yan Nan ne da kasuwancin ne Agabansu Sai yawon gidan suna gidan biki kullum suna titi Basu Damu da tarbiyyar yaraba komai nasu me Aiki CE ke musu Shiyasa tun suna Yara ita da Mubarak Basu San dai-daiba Basu San ba dai-dai ba kullum iyayansu na hanyar K’asashe suna Saro Kaya.

      CIGABAN LABARI

Bayan sun tashi daga Makaranta Driver ne ya koma ya  D’auko su Mubarak Irfan ne ya Fara Sauka don gidansu ne A farko Koda ya shiga Soron gidan kukan Mamansa ne yacika Masa kunne Ai be san San da ya Yar da School bag d’insa ba Ya Yi cikin gidan da gudu Turus ya yi ganin babansa da belt A hannu Yana dukan Ummansa ……….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *