RAYUWAR WANI CHAPTER B KARSHE

 RAYUWAR WANI CHAPTER B KARSHE

💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*©® 2018.*

   
      *8/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

_FAN’S INA MAI BAKU  HAK’URI NA JINA DA BAKU YI BA TSAWON WANNAN LOKACI,SAI DAI UZURIN DA YA HANA NI KASANCEWA TARE DA KU MAI GIRMA NE,NA SO KAMMALA WANNAN NOVEL NA *-RAYUWAR WANI-*,A LOKACIN BAYA,ALLAH BAI NUFA BA,DUK DA WASU SUN SAN NA JIMA BA NI DA LAFIYA,BAYAN NA SAMU SAUK’I KUMA LOKACIN YAYI DAI² DA LOKACIN DA ZAN FARA EXAM,GA MAHAIFINMU KUMA DA SUKE KWANCE BASU DA LAFIYA,WANNAN SU NE UZURIN DA SUKA HANA NI K’ARASA WANNAN RUBUTU,AMMA YANZUN *-ALHAMDULILLAH-* KOMAI YA DAI²TA IN SHA ALLAH YANZUN ZA KUNA JINA AKAI²……._+

*_HAK’IK’A NAJI DA’DIN ADDU’O’INKU GARENI,WANDA HAKAN BA K’ARAMIN NASARA YA BANIBA A RAYUWA……_”*

*_’YAN UWANA,MASOYANA,HAR KULLUM INA ALFAHARI DA KASANCEWATA TARE DA KU,ADDU’ARKU GARENI,DA IRIN KULAWAR DA KUKE BANI,BANI DA BAKIN MAGANA,FATANA A GAREKU BAZAI WUCE NEMA MUKU,AMINCIN ALLAH,RAHAMARSA DA KUMA ALBARKARSA SUCI GABA DA KASANCEWA TARE DA KU A DUK INDA KUKE………_*

*_HAK’IK’A BAKA TA’BA SANIN INDA MASOYINKA YAKE,SAI WANI ABU YA SAMEKA,KUN NUNAMIN K’AUNA TARE DA HALACCI ARAYUWA,BAYAGA ‘DAWAINIYA DA KUKA DUNGAYI BISA SANIN HALIN DA NAKE CIKI,MUSAMMAN JAJURTATTUN ‘YAN UWANAH,KUMA ABOKAN AIKI……._*

*~>>>>>>>>KAMAR SU<<<<<<<<~*

_AMINA SALIS MUSA (LITTLE)_
_HABIBA IDREES (HUBBEY)_
_SAFIYA BALA (MOM HANAN)_
_MURJA SALIS (NA’IKKE)_
_HAFSAT MAI SHERRIF_
_FATIMA IBRAHIM (MUNEERAH)_
_AYUSHA ILYAS_
_REAL MAE DAMBU._
_AUNTY MAIMOUNATH_
_RUQAYYA HASSAN UTHMAN_
_FATIMA A¹ (PHERTEENJEEY)_
_FATIMA A² (FATEEY AFIRST)_
_QUEEN HAFSY_
_HAUWA (QUEEN HAUSEY)_
_BILKISU M.ADAM (Y’AR ABBA)_
_QUEEN ACID_
_AISHA WHITE (DOUGHTEEY)_
_MAMAN BOY_
_KHADIJA DEE_
_PRINCESS ESHAT AYSM_

*_ARADU WANNAN SHAFI NAKU NE,NA BAR MUKU SHI,SAI YADDA KUKA SO ZA KUYI DA SHI,ALLAH YA BAR ZUMUNCI,MU KASANCE HAR A ALJANNAH…_*
*~_________________________~*
                                     
*_GAISUWA TA MUSAMMAN GAREKU Y’AN UWA,ABOKAN AIKI._* 🏵🏵🏵

_AISHA SADA MACIKA_
_HAWWER A SARKI (NAMECY)_
_REAL NASBASH_
_BILLY S FARI_
_FA’IXA (ANFA)_
_FAUZIYYA._
_MUHIBBAT INDIA_
_AYUSHA_
_FATEEY TAMBARIY_
_FULANI_
_KHADIJA SALEEHU._
_KHADIJA S.DOGARAI (LIPTON)_
_RAHEEMA 💘_
_REAL RAHAMA NA LELE_
_AISHA (MUMMYS FRIEND)_
_SAWWAMA A_
_HEARMEEBRAERH._
_SARAH ADIYA (SARARA)_
_SUMMY NICE_
_AYUSHER MUHAMMAD_

_SAURAN WA’DANDA BAN AMBATABA KUMIN UZURI,INA NAN TAFE ZUWA KANKU,ALLAH YA BAR ZUMUNCI…._

*•••••••••••••••••••••••••••••••••••••*

_INA MATUK’AR GODIYA DA ADDU’O’INKU GARENI FAN’S,INA GANIN SAK’ONKU A KO DA YAUSHE,INA GODIYA SOSAI,ALLAH YABAR K’AUNA…….._
*_#IYA WUYA MUNA MUGUN TARE….❣🕊🌹_*

*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*
*℘ąɠɛ 51↔52*

Har ta fito daga toilet en, little na zaune kan bed,can kuma ta kwanta,idonta rufe…..

STORY CONTINUES BELOW

Kallonta ta  sake yi,ta nufi kan stool en dake gaban mirror, ta shiga murzawa jikinta lotions, simple make-up tayi,ta nemi dogon riga ta d’ora kan nighty en dake jikinta….

Fita tayi ta nufi kitchen, dan ita kam yunwa take ji,ko a skul snacks kad’ai ta iya ci da lemo…..

Indomie ta iya dafawa a daddafe ta juye a plate ta dawo d’akin, har lokacin bataji little ta yi mata maganar phones enba…..

A ranta take cewa “thank God bata gansuba still now”…..

Zama tayi ta fara cin abincin cikin kwanciyar hankali,har ta kammala…..

Dagowa tayi ta kalli inda little take,amma ga mamakinta har ta yi bacci…

Tattara komai tayi,ta nufi k’ofar fit a,babu kowa a parlor,hakan ya tabbatar da kowa yayi shirin kwanciya kenan,bata tsaya b’ata lokaciba itama,ta wanke hannunta…..

Fitowa tayi,tana faman hamma,alaman bacci a idonta,ta kama hanyan bedroom ensu…..

Da k’yar take iya d’aga k’afafunta,dan jinsu take yau kam tamkar ba nataba,saboda gajiyan dake jikinta…

A haka ta fara haura staircase en,idonta na lumshewa,k’ok’arin ci gaba da tafiya take,har Allah ya bata ikon tsallakewa….

A hankali ta murd’a handle en k’ofan d’akin…..
Koda ta shiga kashe light en d’akin tayi,ta kwanta kusa da little,da tun tuni tayi bacci dan har ta wuce (Darazau)……

   *~SABAHUL KHAIR…..Y’AN MATAM MAMMY…~*
Ko da asuba Jiddah kad’ai ta tashi,bayan ta idar da sallah,ta kammala duk wani aiki daya zame mata d’abi’a….
Kwashe phones en tayi ta adanasu gurin da little bazata ganiba,ta fice daga bed room en,kitchen ta nufa dan taya su mammy aiki…..

  A parlor ta hango boss zaune yana watching T.V,as usual face en kamar baya dariya….

Haka ta sakko,kamar zata wuce ta d’an tsaya dai² saitinsa ta sunkuya kad’an tare da fad’in
“yah barka da safiya”….

Cike da Isa kamar jinin sarauta ya d’ago,kafin ya d’aga mata hannu,cikin wani salo ya kalleta had’e da jifanta da murmushin da ta kasa fassara ko na mene ne……

Jikinta a salub’e haka ta lallab’a tabar gurin….

Kitchen enma da tayi niyyan zuwa fasawa tayi ta koma da baya,kamar wacce tayi mantuwa……

Juya bayan da tayi shi ya bashi damar k’are mata kallo,har ta b’acewa ganinsa…..

Da gudu² ta k’arasa shigewa,k’irjinta na dukan 3²…..
Da k’arfi ta mayar da k’ofan,wanda hakan yayi sanadiyyar farkawar little…….

Dafe k’irji tayi,banda addu’ah babu abunda take….

Tsakin da little tayi ya jawo hankalinta,mugun kallo jiddan ta watsa mata, kafin ta bar gurin….

Cike da takaicin an katse mata bacci,little ta mik’e tana ta jero tsaki…….
Ko kallo bata ishi Jiddah ba…..

Barin gurin tayi,ita kuma Jiddah cikin hanzari ta d’auka phones en….
Direct d’akin mammy tayi,don nuna Mata,sosai mammy taji dad’i,ta kuma yi musu fatan alkhairi………..

Zama tayi d’akin mammy ta hau k’ok’arin kunnawa,amma ta kasa….
Kan dole ta hak’ura ta kwashe komai ta nufi parlor……

Zaune ta tarar da shi kamar yanda ta barshi……

Ganin ta nufoshi da abu a hannunta,yasa shi d’aga kai ya kalleta…..

Take ya had’e giran sama dana k’ada,ganinta d’auke da ledan daya bata jiya…….
“Me Kenan?”…
Ya tambayi kansa, ba dal dawowa da shi tayiba…..

STORY CONTINUES BELOW

Ga mamakinsa,saiji yayi tana fad’in “yah na kasa ganema kan phone en”………..

*KUMIN UZURI FAN’S COZ NA KASA DOGON TYPING, ABUNKU DA WACCE TA JIMA BATAYI TYPING BA,AMMA IN SHA ALLAH ZAMU HA’DU A NEXT PAGE…*
  
*_~KEEP MOVING FAN’S….😍😍😍~_*
        

*_REAL SMASHER 🤞🏻😘_*
[2:39PM, 3/24/2018] Hassan ATK.: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*©® 2018.*

   
      *9/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*_HAPPY GRADUATION TO BOTH OF US…..AKCILS 001 CHAPTER,CLASS OF 2017/2018.._*

_THESE PAGE GOES TO….._

_RABI’ATU ADAM MUHAMMAD_
_HABIBA YAHYA HAROUN (HABIBATY)._
_ZUBAIDA ABDULLAHI MUH’D (ZUBEEY)._
_BARA’ATU LAWAN._
_NA’IMA KABEER SHU’AIB._
_AISHA ABDULLAHI ABUBAKAR_
_AMINA IBRAHIM SALISU._
_HUSSAINA HUSSAIN TIJJANI._
_AISHA SHEHU JIBRIL_
_RAMLATU NURA AMINU._
_FADILA HUSSAIN._
_AISHA IBRAHIM_
_FATIMA AHMAD ABUBAKAR._

  *DA SAURAN WA’DANDA BAN AMBATABA,KUYI HAK’URI DUKKANNINKU KUNA RAINA,ALLAH YABAR K’AUNA.……*

*_________________________*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 53↔54*

Yanayin da tayi maganar ya tabbatar masa da gaske take…..

Hannu kad’ai ya mik’a,ledan ta mik’a masa,ta nemi guri ta zauna,tana kallonsa ya kunna phone en.………

Mik’a mata yayi,tare da d’auke kansa daga inda take,karb’a tayi ta koma ta zauna tana ta danne²,sai dai ta rasa ina ya kamata ta shiga….

Haka taci gaba da dannawa,har tsayin wani lokaci…..
                *************

Ta gefe yake kallonta,wanda ita kam batama san yana yiba, abunda ke gabanta take fama…..

Cikin wasu y’an dak’ik’u ta fara fuskantar phone en,murmushi tayi ganin abun babu wahala…..

Mik’ewa tayi,ta chanza seat,tana ta danne²…….

                *°°°°°°°°°°°°°°°*

Takun tafiyan da tajiyone,yasata d’agowa da sauri ta maida phone en bayanta ta b’oye,alaman rashin gaskiya duk ya bayyana a face nata……

Kusa da ita little ta samu ta zauna,tana fad’in
     ”me kike b’oyewane?”

”Dillah babu komai” tana gama fad’a ta mik’e tayi hanyan stairs….

Mik’ewa little tayi tabi bayanta a guje suka kasa tsere zuwa d’akin…..

Duk wannan abun da suke a kan idon Yah BOSS dake zaune kamar wanda aka shuka…..
Barinsu gurin suna dariya,shi kuma ya tab’e baki kamar wanda yaga abun k’i…….

   Shigansu d’akin suka fara zagaye,ita little burinta taga abunda ke hannun jiddah,ita kuma tak’i yarda ta nuna mata….

Kan dole little ta hak’ura,ba don ta so hakanba…..

STORY CONTINUES BELOW

Zama tayi alamar tayi fushi,sai a lokacin jiddah ta dawo gabanta,tana fad’in ”albishir y’ar uwa”……..

‘Dagowa little en tayi ta sake kallonta,da hannunta dake bayanta b’oye still…….
”Allah idan ba zaki amsaba zan fasa fad’a” Jiddan ta sake fad’a……

Da sauri little ta amsata,tana washe baki…..
”Sai kin bada goron albishir tukun”, jiddan ta sake fad’a teethingly….

Ke wallahi matsalarki kenan,komai mutum sai yabaki cin hanci….

”Wannan ne cin hanci,to kin yiwa kanki aradu,samuwarki ce ae ba nawaba”,tana gama fad’a ta juya zata fice…..

Da sauri little ta dakatar da ita, ”eh naji to fad’amin zan bada”…….

”Ko kefa”,fad’in jiddah data juyo tana wani mugun smiling……
Amma wallahi da sharad’i dan karma kice zaki wani sayamin ice cream,ehee albishir ena ya wuce haka…….

”Naji to fad’a min”,
little ta fad’a da alamun son jin abunda za a fad’a…..

”To uwar son story yanzun duk abunda nace kiyi kawai kiyi banda musu”, jiddah ta fad’a….
Hararar jiddah little tayi amma sai dai bata bari ta ganiba,saboda son ganin k’wak’waf,kan dole tayi yadda aka ce…….

Da sauri jiddan ta d’auko phone en ta dawo kusa da ita,a kan laps enta ta d’ora mata,tana fad’in ”bud’e idon”……..

Cikin hanzari ta bud’e,take tayi arba da kwalin wayan dake kan cinyanta k’irar *phantom 6*………
Ihu ta fasa cikin k’araji take fad’in
    ”sisi na waye wannan?”….
Naki ne,nima kinga nawa,ta fito da hannunta dake mak’ale a bayanta…..

OMGH!!! ”Sisi yaushe hakan ya faru,ban saniba?”……

Yesterday,ba nazo ina miki maganaba kika wulak’antani……
Eyyahh!kiyi hak’uri sisinah,banyi tunanin kiran da kikeminba kenan……

”Waima sis kaddai kicemin YAH BOSS ya bamu”,ta tambaya……

Fari jiddah tayi,ga murmushi a face nata,da yake nuna tsantsar farin ciki,kafin ta amsawa little da cewa
   ”Yeahh!idan ba shiba da wa kike tunani?”
Dariya itama little en tayi,kafin ta mik’e taja hannun jiddah suka nufi parlor…..

Tun kafin su k’arasa take rad’awa jiddah cewa ”yau kam sai munje gidansu hubbey duk da jiya mun had’u a skul”…..
Murmushi kad’ai tayi ba tare da rayi maganaba…..

Shigowansu parlor suka nufi inda yake…..
Kallonsu kad’ai yayi ya sake juya kansa gefe……
Kan sofan dake opposite da nashi suka zauna,suka masa godiya…..

Yana jinsu yak’i tankawa,har sukayi suka gama,bai yi koda tariba…..

Su kam nan suka zauna suka fara sana’a…….

Hankalinsa ne ya bar kan abunda yake,gaba d’aya ya koma kan jiddah,duk wani motsi da zatayi akan idonsa…….

                 *°°°°°°°°°°°°*

Da yamma, bayan sun gama shiryawa,suka d’auka hanya,sai gidan su hubbey……

   Zaune suka tarar da ita a parlor da phone a hannunta tana ta faman chat,sai dariya take saboda yadda take cike da nishad’i…….

Sallamansu ne ya katseta,da gudu ta tashi ta taresu,sunata dariya,kamar ba jiya suka had’uba……

‘Dakin Mama suka nufa,sai da suka gaisa tukun,sannan suka nufi d’akinta……
Nan suka sake baje kolin firansu….

“Sisi baki san wani abuba,mun faso garifa mumafa”,fad’in little….
Da mamaki shimfid’e a fuskanta,take kallonsu,kafin ta samu k’arfin guiwar tambaya……
     ”Kunfa sani a duhu”
Ta fad’a,da son jin inda labarin ya dosa…….

STORY CONTINUES BELOW

Phones en little ta d’ebo ta d’ora mata a cinya…….
k’ara ta fasa,had’e da rungumesu,tana fad’in ”kai mutanena,yaushe mukayi abun arziki?”……..

Ke dai bari jiya,yah Boss ya bamu,kai amma naji dad’i,wollah Allah yasanya alkhairi……..
”Gaskiya yanzun abunda za ayi mu fara hawa neteork”……
Ta fad’a tana d’aukan phones en,ba tare da shawara da kowaba ta shiga tura apps,ba a d’auki lokaci mai tsayiba ta tura,nan ta shiga setting bayan ta duba taga akwai enough money,tayi subs ta shiga setting whatsapp…….

Abunka da wacce ta k’ware within  few minutes ta gama……

Nan ta shiga nuna musu yadda za suyi,da yake akwai kwakwalwa,take suka gane…..

Nan kuma aka fara d’ora numbers a line en,na class mate……

Haka suka gama firansu da murna,suka kamo hanyan dawowa gida………

                *°°°°°°°°°°°°°°*

Bayan sallan isha lokacin ne suka k’ule a d’aki nan aka fara sana’a…..

Jiddah dake kwance da phone a hannunta,ta gama game kenan,ta kunna data…….
Whatsapp ta hau,tana bud’ewa taga har an sasu groups,text sai shigowa yake,murmushi tayi…..
Kafin ta fara bud’ewa tana dubawa,nan aka shiga fira da su a group,kamar dama can dasu a group en,sun nutsa anata fira,sai tsokanar juna ake,suna ta dariya…….

K’aran shigowan text yasata fita a group,ido ta fito waje ganin bak’uwan number,nan ta shiga tunanin waye……..
Murmushi ta sake yi,tunaninta ko a y’an class ensu ne wata ta mata magana P.C……..

Sallaman ta amsa,kafin ta tambaya waye yake magana……

Murmushi kad’ai aka mata,kafin aka bata amsa da
     ”BAWAN ALLAH”……

Ido ta zare waje,ganin amsan da aka bata……….

*~_Nima ido na zarooo waje,da tunanin wane mai d’anyen aikin ne……._~* 😨😨😨

*_~KEEP MOVING….. 😍😍😍~_*

*_REAL SMASHER 🤞🏻😘_*
[2:39PM, 3/24/2018] Hassan ATK.: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                    🌹
*©® 2018.*

   
      *21/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_
*~_________________________~*

*ADDU’AH KAN ABOKIN GABA…*

_ALLAHUMMA ANTA ADHUDHIY,WA-ANTA NASIYRIY,BIKA AHULU,WA-BIKA ASUULU,WA-BIKA UK’ATILU……_

  _ALLAHUMMA INNA NAJ’ALUKA FIY NUHURIHIM,WANA-UZHUBIKA MIN SHURIRIHEEM……_

                *_~#HISNUL MUSLIM….~_*

*~__________________________~*

*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA’IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA’ADAHU…….._*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI’I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA’U MINHUM WAL-AMWAT…._

*~__________________________~*

STORY CONTINUES BELOW

_Yau ranar farinciki ne,gare mu baki d’aya,sisinah *HALIMATUS-SADIYA MUHAMMAD (LEEMA)* ina tayaki murnar kammala littafinki na 🌸 *QURUCIYAR JUMMAI* 🌸,Allah yasa mutane su amfana da darussan dake cikin wannan labari.Allah kuma ya baki ikon fara wani lafiya……._

         *_#Stay blessed sisinah…._*
*~__________________________~*

_Ban manta dake ba y’ar uwata *KHADIJA (DEEE)* ina tayaki murnan kammala novel enki na 💔 *KALMAR RABUWA* 💔,Allah yasa kin gama a sa’a,k’aunar da kika nuna mana muna godiya,Allah ya bar zumunci da k’aunar juna…….._

   *_#So much love dear,irin ana togeda ennan,baza a rabuba na har abada…._* ❤💘

*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 57↔58*

Tana yin block en ta sake sauka,tun daga lokacin kuma ta koma cikin group aka hau fira da ita nan aka shiga yi mata tsiyan ina ta tsaya bata shigo da wuriba yau…….
Wasu har tsokanarta suke ko dai yalla’bai ya hanata motsi yau…..
Ita kam sai dai tayi dariya,haka sukaita fira,zucinyata fayau babu fargaba…….

                   ***************

Dai² lokacin yana shirin bata amsan tambayanta,kira ya shigo phone ensa,daga wani friend nasa,sun jima suna fira,kafin sukayi sallama…….

Komawa yayi ya gama rubutun abunda zai fad’a mata……
  Sai dai kashhh!yana tura sak’on ya fahimci tayi blocking nasa…..
Murmushi ya saki,a fili kuwa ya furta
     ”great deal”…….
Shawaran da zucinyansa ya yanke yake k’ok’arin bi,tabbas dama yasan za a rina (WAI AN SACI ZANIN MAHAUKACIYA)……
Kiranta ya yanke shawaran yayi,duk da baya tunanin zatai picking,haka ya dage don jarrabawa……

                     *************

Dai² tana k’ok’arin sauka online saboda bacci data fara ji…..
Sallama tayi da kowa,ta rufe hotspot nata,tana shirin ajiye phone en,kiransa ya kunno kai cikin phone nata…..

Bata tsaya duba wanda ke kiranba,ta ajiye phone en,har kiran ya katse bata ko kalli inda ta ajiyeba…….
Sake shigowan wani kiran,shi yasata bisa dole janyo phone en,badan tasoba,sai dan son sanin waye yake shirin takurata,da tsohon daren……

Har wayan ya kusa katsewa,sannan ta d’aga,cikin alamu na mai jin bacci tayi sallama……

Cikin wani kasalallen voice YAH BOSS dake d’ayan gefen ya amsata,had’e da sauke siririn ajiyan zuciya……..

Shiru sukayima juna na wani lokaci…..

Ganin shirun yayi yawa,JIDDAH tayi k’ok’arin dakatar da shirun,ta hanyar fad’in
    ”Wake magana pleaseeee”
Ta jaa kalmanta na k’arshe…..

Shirun ya sake yi,yana tunanin mae zai fad’a mata…..
Bai tsaya b’ata lokaciba,tuna k’udirin dake zuciyansa……

*”GIMBIYATA* barka da wannan lokaci”
Maganar ta zo a bazata….

Ba shi kad’ai ba hatta ita kanta JIDDAH taji shigar maganar tasa,har cikin vain nata…..
Take baccin da take ji ya kufce maya,ta neme shi ta rasa……

Dad’a bud’e idonta tayi tana son tabbatar da gaskiyar abunda kunnuwanta suka jiyo mata…..

Bata samu damar amsawa ba,sai wasu siraran ajiyan azuciya da ta shiga yi,wanda bata shirya musuba……

”Nasan ni en mai lefine tunda kuwa saboda girman laifina har ya janyo an yankemin hukunci”……
Ta tsinkayi muryansa yana fad’a…..

Wani kunya ne ya kama JIDDAH lokaci guda,da ya hanata magana….
Fuskantar ta kasa sakewa suyi magana yasa shi fad’in…..
  ”Idan babu damuwa,ina rok’on a yafemin laifina,idan kuma ban takurakiba”……
Yanda yake maganar cikin k’asaita….

STORY CONTINUES BELOW

Ita kanta JIDDAH mamakin yanda akayi ta tsaya saurarensa take,tana kwance bakinta bud’e da tsantsar mamakin wannan bawan Allah…….

Janta yaci gaba da yi da fira,tun bata iya magana idan ya tambayeta,har ta fara bashi amsa da UHMMM,A’A ko EH…..
Sosai firan da yake mata ya fara mata dad’i, lokaci d’aya damuwanta duk ya tafi…..
Sai dai har zuwa wannan lokaci bata samu amsan tambayanta ba,abunda kawai yace mata
”Ki jira zuwan lokaci,akwai lokacin da *ZAKI SAN KONI WAYE”*……..

Murmushi kad’ai tayi bata sake tambayaba,har sukayi sallama…..
Da tunanin firansu tayi bacci wanda bata san lokacin da ya d’auketa ba…….

Gefen YAH BOSS kuwa shima haka ne ta kasance da shi,dan kuwa yana da yak’inin zai yi wining game en……..

Zuciyoyin mutanen biyu cike da farin ciki haka suka kwanta bacci……

                        ************

*_SOME DAY’S LEFT……._*

Rayuwa ta cigaba da tafiya,inda su LITTLE ke dad’a maida hankali kan karatunsu……

A gefe d’aya kuma soyayya,shaquwa na dad’a k’arfi tsakanin YAH BOSS da JIDDAH…..
In da yanzun har ta kai basa iya rabuwa da juna,ko yaushe suna mak’ale akan phone,da ma chat……

Abu d’aya JIDDAH ta manta maganar aurensu da YAH BOSS tafi maida hankali kan *NEW LOVE* da tayi…….
Sha’anin soyayyarsu suke sha,ba tare da fargaba ba……

                       ***********

Yau ya kama FRIDAY saboda haka,da wuri suka taso daga skul…..
Tafe suke cikin motor da aka samu promotion,dan yanzun su suke kai kansu skul su kuma dawo……

Tafe suke suna firansu cikin kwanciyar hankali,har suka k’araso bakin gate en gidan…..
HORN sukai,baba dake cikin d’aki yana sauraren radio ya fito da sauri…….
Suka kunna kan motor en zuwa parking lot,ko gama tsayawa basuyi ba,baba ya k’araso kusa da su yana fad’in
”Ranku shi dad’e kunyi bak’o,dan tun d’azun yake zaman jira”…..

Nan aka shiga kallon² tsakanin JIDDAH da LITTLE……….

*_~KEEP FOLLOWING FAN’S….~_* 😍😍😍
*_REAL SMASHER 🤞🏻😘_*
[2:39PM, 3/24/2018] Hassan ATK.: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*©® 2018.*

   
      *20/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*~_________________________~*

*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA’IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA’ADAHU…….._*

  _ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI’I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA’U MINHUM WAL-AMWAT….._ 🤲🏻🤲🏻🤲🏻

*~__________________________~*

_Tabbas ina godiya,nayi murna da ganin addu’arki,a kullum zamu ci gaba da kasancewa tare,har illah masha Allah…. *MY HUBBEYY*, a koda yaushe ina tare da ku……_
  *_REALLY HEART U DEAR…._* 💔💘

STORY CONTINUES BELOW

*~__________________________~*

_Na juyo gareki y’ar uwata,ban manta dakeba,abun alfahari ne gareni,irin soyayyar da kika nunamin,ina miki fatan alkhairi a rayuwa,na gode da k’aunarki gareni… *SALMAT SA’EED ADAM*  Allah ya bar zumunci……._
    *_~AHABBAKILLAHUL-LAZIY AHBABTANIY LAHU…..~_* 💔❤

*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 55↔56*

Sake tambaya tayi,dai² lokacin da sak’onta ya shiga wayansa,tana jiran reply,taga yayi offline…..
Tsaki taja,saboda haushin rashin amsansa…..
Can kuma ta tuna cewa ai zai gani kuma zai mata reply…..
Group ta koma akaci gaba da fira kamar kamar sun jima aciki….

Tanayi tana dubawa ko ya mata reply,amma shiru,zuciyantane ya shiga damuwa,haka kawai taji bazata iya ci gaba da chart enba,lokacin da k’irjinta ya tsananta bugu,kan rashin sanin abunyi……
Offline tayi itama,ganin cewa chart en ya dena mata dad’i duk da d’okin hawa net da suke…..

Ita kad’ai ta kwanta kan pillow,ta shiga thinking akan wannan mutumin…..
Duk tunaninta ya tsaya chak kan son tuna waye wannan mai k’arfin hali haka…..
Rashin samun amsa yasa ta bawa kanta hak’uri ta juya don yin bacci,amma abun ya gagara…….

                     ***********

‘Bangaren YAH BOSS kuwa,lokacin da ya mata sending amsa da BAWAN ALLAH,ya kashe phone ensa yana murmushi……
Shi kad’ai ya shiga raya yadda zaiyi playing game en tsakaninsu……
Da yadda zaiyi winning akanta,bashi da burin da ya wuce ta fahimci irin yadda yake dakon soyayyanta…..
Murmushi ya sake yi,lokacin da tunaninsa ya tsaya kan yadda ya barta a yanzun,da haka bacci yayi gaba da shi,murmushi shimfid’e a face ensa……

         *NEXT MORNING….*

Yanda ta kwanta ranta a dagule haka ta tashi,fiskanta turb’une…..
Ko little ma data ganta haka bata shiga sabgartaba,rabuwa tayi da ita har ta gama abunda za tayi ta sauka zuwa parlor…..

Kamar ko wane lokaci tana sakkowa ta tarar da gogan a parlor yana kallon labarai,sanye da jallabiyya fara sol,kansa sai shek’i yake…..
Kallon side en da yake tayi,lokacin da idonta ya kai kansa,tsayawa tayi tana kallonsa yau kam sai taga ya mata kyau sosai fiye da ko yaushe……
Heartbeat enta ne ya sauya salo,into paster speed….
Da sauri ta dafe saitin gurin tare da juyawa da baya,da d’an gudunta ta koma sama,tunawa da ko phone enta bata d’aukoba……

‘Dagowa yayi yabita da kallo lokacin da ta juya,murmushi yayi dan tun daga tahowarta har zuwa juyawanta akan idonsa komai ya faru……
  Yana ayyana irin rayuwar da zasu shimfid’a bayan aurensu…..
Babban abun da yafi mai dad’i bai wuce tuna ranar da zata gane shiba,a matsayin wanda yafi kowa k’aunarta……

                    *************

Shiganta d’akin babu kowa ciki,kan bed ta koma ta kwanta,tare da janyo phone enta ta shiga chart ko zataji sauk’in abunda take ji a yanzun…..
Amma ta gagara fargaba duk ya cika mata zuciya,wanda ta rasa fuskantan na mene ne…….
Baccin wahala ne ya kwasheta,ko break bata samu tayiba,haka take baccin a wahale……

Fitowan little daga toilet ta tarar da ita tana bacci,ganin yanayinta,ya dad’a tabbatar mata da sisin nata ba lau take ba,addu’an samun sauk’i tayi gareta,duk da bata san ainihin abunda ke damuntaba…….

Sai after 11:00am ta tashi tana mik’a kasancewar yanda take jin jikinta duk a d’aure kamar wacce akayiwa duka…….
Toilet ta nufa ta jima cikin ruwan da ya mata dad’i kamar kar ta fita haka take ji,dan har lumshe I do take,da k’yar ta watsa ruwa ta fito daga toilet en,after ta fito ta tarar da little ta shigo….
”Yawwa sisi Mammy na kiranki,tun d’azun take tambayana kinyi break? nace mata a’a,shi ne tasa na zo na duba,idan baki tashiba na taso ki”….

STORY CONTINUES BELOW

‘Dan murmushin yak’e tayi kafin ta kammala shiryawa,riga da skirt ta sa na material black da jaa,ta feshe jikinta da turaruka…..
K’ala batacema little ba tayi waje,da phone enta a hannu…..

Dining ta nufa,babu kowa cikin parlorn har ta kammala abunda za tayi,duk da bawai taji dad’in bakinta bane,ta dai kawai turawa cikinta abincin ne…..
Har ta kammala ta tashi,ta shiga kwashe kayan zuwa kitchen…..

Parlor ta dawo,ta kwanta kan sofa,nan aka fara sana’ar ta game…..
Rashin dad’insa yasa data gaji ta bud’e data…..
Texts suka shiga tururuwan shigowa phone enta,ganin yawan firan na groups ne dan wasuma na NOVELS ne da aka sata wanda bata san dasuba,yasa tayi d’an murmushin k’arfin hali,tare da fara bud’ewa……

Duk iya lek’enta na son sanin amsar tambayanta shi yafi damunta,har ta gama kewayenta a yanar gizon bata ci karo da kwatankwacintaba,kan dole ta hak’ura ta sake sauka……

                *****************

Yinin ranar haka ta k’areshi babu dad’i,har zuwa lokacin kwanciya bacci…..
Sai da ta kammala duk wani abu da yazame mata al’ada kafin ta kwanta,kusa da little da take ta faman doka smile,saboda yanda take jin dad’in chat a dare……

Kallonta kad’ai tayi tare da fatan inama ta kasance haka cikin wannan dare….
Bijirowar wannan tunanin shi yasata bud’e data,wanda batai niyyaba…..

Cikin sa’a tayi katarin samun sakonsa,da ya turoshi a dai² lokacin……
Ajiyan zuciya ta sauke mai nauyi,kafin ta bud’e…..

_”Aminci ya tabbata gare ki ya mafi kyan halitta a idanun masu kallo….”_
Abunda sak’onsa ya k’unsa kenan

Duk da ba haka tasoba,ta amsa masa…..
Tare da sake maimaita masa tambayanta da ta k’agu tasan amsan sa……

_”Haba mana gimbiyata ai kya bari mu gaisa kafin ki tambayeni”……_

‘Dan murmushi ta tura masa da,after sukai exchanging na greetings…..

”Nasan kin damu da sanin amsan tambayanki ko?”
  Yayi tambayan……..

Smile en ta sake aikawa da shi,tana jiran ganin amsan sa……
Duk firan da ake yau a group ensu tak’i saka baki,kasancewar tafi maida hankalinta kan bak’uwan numberta…….

Offline en data ga yayi shi ya d’an sosa mata rai,take zuciyanta ta raya mata kawai tayi blocking ko waye,itama ta huta……
Bata jira shawara daga d’ayan zuciyanba,ta sank’ama masa block…….
*IDO WAJE NA KALLI JIDDAH DA TA TAFKA D’ANYEN AIKI….* 😨😨😨

*_~KEEP FOLLOWING FAN’S….~_* 😍😍😍

*_REAL SMASHER 🤞🏻😘_*
[2:39PM, 3/24/2018] Hassan ATK.: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*©® 2018.*

   
      *22/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_
*~_________________________~*
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

      *_Happy, Happy Birthday!_*

🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

  _I hope the day has been blessed with the presence of those you love most, and many magical moments!._

STORY CONTINUES BELOW

      _Appy bufday to u admin of admins HAYAT BABA ZUBAIR…._

*Real Smasher Novellah Group*
*Smasher nd Hubbey Novels Group*
   _Wish u a happy bithday,appy fruitful years……._ 🎂🎂🎂

*The whole todays page is ur’s……* 💃🏻

*~_________________________~*

*ADDU’AH YAYIN TASHI DAGA BACCI*

_ALHAMDULILLAHIL-LAZIY AHYANA BA’ADA MAA AMATANA WA-ILAIHIN-NUSHUUR…_

_ALHAMDULILLAHIL-LAZIY AFANIY FII JASADIY WARADDA ALAIYYA RUHIY WA-AZINALIY BIZIKHRIY….._

         *_~#HISNUL MUSLIM…~_*

*~_________________________~*

*_ALLAHUMMAGFIR LII HAYYINA,WA-MAYYITINI,WASHAHIDNA,WA GHA’IBINA,WA-SAGHIRANA,WA-KABIRANA,WA-ZAKHARINA,WA-UNSANA,ALLAHUMMA MAN AHYAYTAHU MINNA FA AHYIHI ALAL ISLAM,WAMAN TAWAFFAITAHU MINNA FATAWAFFAHU ALAL IYMAN,ALLAHUMMA LAA TAHRIMNA AJRAHU,WALA-TUDILLANA BA’ADAHU…….._*

_ALLAHUMMAGFIR LI ABIIY WA KULLI JAMI’I MAUTAL MUSLIMIYN,AL-AHYA’U MINHUM WAL-AMWAT…._

*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 59↔60*
Kallon baba suka sake yi fuskokinsu d’auke da alaman tambaya…….
Murmushi LITTLE tayi tana kallon JIDDAH kafin ta samu daman furta
”Sisi sai daifa idan gurinki aka zo”…..
Wata uwar harara JIDDAH ta jefeta da shi
”Saboda dama kin san ai ina fitowa ko,kike fad’in haka,idan ma zaki wuce ne kije toh,dan ni kam ba gurina aka zoba”….
Tana gama fad’a taja k’afafuwanta za ta bar wajen…..

”Dan Allah sis ki tsaya kin san dai nima ba fita nakeba”……

A hankali ta juya tana kallonta,zuwa can kuma ta d’aga mata kai alaman suje su duba ko waye……
Cikin sanyin jiki suka nufi parlorn bak’in…..

Da sallama suka sa k’afafunsu ciki……

Yana zaune kan sofa dake opposite en k’ofan shiga parlor,k’afansa d’aya kan d’aya….
Kansa na kallon phone en dake hannunsa,wannan shi ya hana su ganin face nasa,tun shigowansu….
Yana daga haka ya amsa su,ba tare da ya d’agoba….

Matsawa LITTLE tayi jikin JIDDAH dake k’ok’arin zama kan sofa……
Cikin rad’a
”Sisinah waye ne wannan en?”……
Kallonta kawai tayi,bata kai ga bata amsa ba,ya d’ago,wanda gaba d’ayan hankalinsu na kansa,da son su san waye…….

Murmushi kwance a face nasa,yake kallonsu……

Suprisingly JIDDAH ke kallonsa…
Kafin cikin murmushi ta iya furta
  ”Shekara sabuwar kamawa”……

Murmushin ya mayar mata shima….
”To ya za ayi,rayuwan ne sai addu’ah”….

”Irin wannan b’oyewa da kayi haka,babu labari”…..
Ta sake fad’a…..

”Gaskiya dai na b’oye da yawa,amma amin uzuri,da ina cikin k’asan ne babu abunda zai hana ba a gaji da ganina ba”…..

Allah sarki,babu komai ai,nan suka gaisa da JIDDAH sai tsokanan juna suke…..
Su LITTLE kam anyi shiru,kamar wacce bata gurin,kanta a k’asa,tana wasa da phone enta dake hannunta…..

Mik’ewa JIDDAH tayi ta nufi hanyan fita
”Toh ni dai nayi ciki sai anjima,mun gode da ziyaranka”….
   Ta fad’a tana kallon LITTLE da duk take a takure,kamar wacce ke jin sanyi……

Sai da ta mata dariya tayi waje…..

Fitowanta daga ciki,ta zaro phone enta dake jaka,text ta rubuta cikin sauri,ta turama little……

Parlorn yayi shiru,tamkar babu mutane cikinsa….
K’aran shigowan text wayanta,ya katse shirun na wasu dak’ik’u……
Bud’ewa tayi don ganin daga CWEET SIS text en yake

     _”Dan Allah malama ki saki jiki,kin wani kama kinma mutane shiru kamar kurma,Allah yasa kar ki masa gidadanci,dan na fuskanci abunda kike k’ok’arin yi kenan”….._

‘Dan murmushi tayi kad’an,ta shiga typing mata reply

   _”Ya muke da juna wajen shiru”…._

Tana turawa tayi back light na wayan….
Cikin siririn murya ta shiga gaida shi….

Duk wani motsinta yana kan idonsa,tun daga shigowansu,har zuwa yanzun…..
Amsawa yayi cikin jin dad’i kafin shiru ya sake biyo baya…..

_”Ina fatan dai gimbiyar tawa bata manta dani ba”…._

Bata ce komai ba,saima wasa da ta shiga yi da yatsun hannunta….

_”Nine dai UMAR FAROUK na sake dawowa a karo na biyu da k’ok’ona,da fatan dai wani bai min shigar sauri ba”…._

Ci gaba yayi da magana ba tare da ya sauraraba,cikin hikima yake janta da surutu,har ta saki jikinta,ta soma bashi amsa….

Sosai suke firan,duk abunda ya tambaya,tana k’ok’arin bashi amsa…..

                        ************

Kamar wacce tayi mugun gajiya,haka take tafiya,har ta k’arasa shiga parlor,gidan shiru kamar babu kowa….
‘Dakin MAMMY ta fara dubawa,cikin sa’a kuwa ta sameta tana shiryawa….

”Wow! MAMMYNMU gaskiya kinyi kyau wollah”…..
Da sauri MAMMY ta juyo ta kalli JIDDAH tana murmushi…..
”Yawwa tunda Allah ya dawo daku,maza kuje ku shirya,yanzun yayanku zai kaiku airpot DADDYNKU yana hanyan dawowa”….

Tsalle tayi kamar wata IKHRAM kafin cikin fara’a ta furta
”Gaskiya DADDY bai tab’a tafiyan da ya jima bai dawo ba irin wannan”……

”Barin sauri kafin YAH BOSS yazo ban shirya ba”…….

Sai bayan da ta fad’i sunan sannan ta tuna abunda bakinta ya furta…..
Dafe bakinta tayi,cikin sauri had’e da fad’in wayyoo Allah!!!……

Dariya MAMMY tayi
   ”Wato wani sunan kuka sawa yayan naku koh?
Maza yaji ku,lokacin nunawa zan ban san kuna fad’aba”…..

Rau² idon JIDDAH yayi kamar za tayi kuka
”Dan Allah MAMMY kiyi hak’uri karma yaji”……..

  Basu ji shigowansa ba,sai maganarsa da suka tsinto yana fad’in
  ”Mene kar a fad’a naji?”
Yayi maganan yana kallon JIDDAH da ta diririce,alamun rashin gaskiya ya bayyana kan fuskanta…….

”Babu komaifa YAH”…….
Tana fad’a ta nufi hanyan fita daga d’akin cikin sauri……

Hannunta ya kama ya janyota da k’arfi…
MAMMY kam tsayawa tayi kallon ikon Allah,wannan rashin kunyan har ina,kuma a gabanta,cikin sauri kuma ta d’auke kanta a kansu,yi tayi kamar bataga komaiba……
Tunaninta ya tafi kan da zaran DADDY ya dawo zata tuntub’eshi kan maganar auren yaran…..
Ba zata zuba ido a fara wannan rashin kunya a gabantaba……

Janye hannunta ta shiga k’ok’arin yi daga nasa,amma ta kasa…..

”Dan Allah YAH kayi hak’uri,zanje na shirya nefa”……

Da kyar ya kyaleta ta tafi,shima sai da ta kusa yin kuka……..
Kallon zamu had’u kuma za kiyi bayani ya mata……

Da d’an gudunta ta bar gurin ta nufi d’aki……
*_~KEEP FOLLOWING FAN’S…~_* 😍😍😍
*_REAL SMASHER 🤞🏻😘_*

💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *25/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*~_________________________~*
  *ADDU’AR SANYA TUFAFI.*

_ALHAMDULILLAHIL-LAZIY KHASANIY HAZAS-SAUBA WARAZAK’ANIHI MIN-GHAIRI HAULIN MINNIY WALA QUWWATA…_

          *_~#HISNUL MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

+
*℘ąɠɛ 61↔62*

Cikin sauri ta shiga wanka,ta shirya….
Har zuwa lokacin LITTLE bata shigo ba……
Tana fitowa daga wanka ta d’auki waya coz bata son tafiya ita d’aya,tun tasowarsu har kawo yau d’aya bai tab’a fita ba tare da d’aya ba…..
Kira ta dannama LITTLE,tana mamakin ya akai ta jima haka a gurin FAROUK,ita da ba a son ranta ta zauna ba…..
Murmushi tayi,kafin cikin sautin da ba kowa zai iya fuskantar me tace ba ta furta
   ”Ana so ana kaiwa market,su LITTLE an iya gulma,bari tazo zamu had’une”…..

**************

”Daga d’ayan ‘barin kuwa LITTLE ana tsaka da zuba love kiran JIDDAH ya shigo wayanta dake hannun FAROUK,mik’a mata yayi,tasa hannu biyu ta amsa…..

Cikin sauri ta d’aga tana fad’in
    ”CWEETY ya ne?”…..

”Kefa muke jira MAMMY tasa mu shirya zamuje taron DADDY airpot,tun d’azun nake zuba idon ganinki”…..
Ta k’arasa tana sauraron abunda LITTLE zata fad’a……
”Eyyahh ganinan zuwa ki kammala shiryawa kafin na k’ariso”…..

”OK” Kad’ai ta fad’a tayi hanging up na kira….

Cikin sauri take komai har ta kusa gama shiryawa amma shiru LITTLE en bata shigoba…..

Sake kiranta tayi,tana d’auka kuwa JIDDAH tahau fad’in
    ”Amma dai baza kiba ko ?
To ba driver zai kaimuba,YAH BOSS ne,kuma kina sane da yanda ya tsani jira”….
Tana gama fad’an nata uzurin ta sake katse kiran,ko bari taji me LITTLE en zata fad’a bata yiba……

Cikin wani rantsatstsen tsadadden lace sea green mai yarfen storns pink ta kammala shirinta,plat en shoe taja tasa pink colour shima,had’e da yalwataccen vail,tayi rolling nasa bisa kanta…..
Ko tsayawa d’aura head tie en batayi ba tayi waje…..

Dai² zata sauka daga stairs en ta hangosa ya hard’e kan sofa,tun d’azun sai faman duba agogon dake d’aure bisa tsintsiyar hannunsa yake na rolex……
‘Dagowa yayi ya dubi hanya,jin sanyayyen k’amshinta dake nufosa….
Ko k’arasa sakkowa bai bari yia mik’e cikin takunsa na isa ya nufi hanyan fita….

Da ido ta rakasa,maimakon ta bisa saima hanyan bedroom en MAMMY da ta nufa….
Knock!Knock!!
  Kafin ta murd’a handle en k’ofan ta shiga,da sallama….

MAMMY na tsaka da duba magazine ta amsata,cikin sakin fuska ta kalli JIDDAH dake ta faman doka smile,uwa wacce akama bushara…..

”Sai tafiya kenan?”
Tayi tambaya tana mai kallonta…
”Ehh MAMMY buh LITTLE fa bata shigoba har yanzun kenan babu ita zamu tafi?”…..
Idonta uwa zai zubda ruwa ta k’arasa maganan….

STORY CONTINUES BELOW

  ”Haba mana y’an matana karki b’ata kwalliyan,ko so kike DADDY yaganki idonnan naki a kod’e,yi shiru kinji,maza wuce ku tafi,ita tunda tana tare da bak’o ba sai kunje tare da itaba”…..
Haka MAMMY tayi ta faman rarrashinta da k’yar ta samu ta tafi badon ta so hakan ba…..

Cikin sanyin jiki ta juya ta fice,MAMMY dake binta da ido har ta fita bata d’auke kanta daga gareta ba,sai da ta turo k’ofan…..

YAH BOSS da tun fitarsa yake tunanin tana bayansa,shiru ya ga bata fito ba….
Jingina yayi a jikin motan,yana jiran ganin fitowanta….
Shirun da yaga yayi yawa,shi ya dad’a bashi haushi,kamar ya tashi sama dan sauri haka yake ji,tun d’azun da shi d’aya zashi ai da yanzun ya tsufa a airpot en….
Yanzun gashi sun tsaya masa b’ata lokaci…..
Tun tsayawansa a gurin yake jan siraran tsaki,yana kuma dad’a duba agogonsa…..
Tunaninsa bai wuce ganin saura y’an mintinu ya rage flight en yayi taking arrive ba…..
‘Dagowa yayi da niyyan barin gurin ya hangota tana tafe kamar wahainiya……

Wani siririn sabon tsakin ya sake jaaa,yana kallonta…
Aransa yake fad’in dama nasan za a rina,wancan yarinyar bata gama shiryawaba kenan,tunda naga d’aya,ita kenan ko skul zasu itace k’arshen shiryawa…..

Kansa ya kad’a a fili kuwa yana fad’in
  ”Yau kam sai dai idan baza kiba”….

Dai² lokacin JIDDAN ta k’ariso….

Kallonta kad’ai yayi ya d’auke kai,ko tambayanta LITTLE baiba ya bud’e mata car door en,sai da ya tabbatar ta shige motan,sannan ya zagaya ta d’ayan side en,shima ya daidaita zamansa,kafin yayima motan key……

Tana zaune side ensa fuskanta kamar zai fashe dan haushi da LITTLE ta bata…..
Shi kuma wannan motan kamar na kurame babu komai cikinsa sai sanyin AC dake busawa…..

A hankali ta d’ago cikin sa’a kuwa idonsa na kanta…
Nan kuwa idanunsu suka sauka kan juna….
Kallonta yake bama kamar yanda ta cuno d’an mitsitsin bakinta gaba…..

Lips en nata yake kallo yanda yake ta kyalli uwa wanda aka tsinto cikin tandun mai……

Da sauri ta kauda kanta daga nasa,tana fad’in
”YAH karfa ka watsar damu a kwalta”…..
Har ta k’are maganar bata saki ranta ba……

Kansa ya d’auke daga gareta…..
Gefe taga yana sauka,cikin alamun tambaya ta juyo tana shirin magana….

parking yayi ya juyo da hankalinsa duka kanta,so yake ya tambayeta,amma ya tsaya tunanin ta ina zai fara magana…..
kafin ta kai ga yin maganan ya rigata ta hanyar fad’in
”Me aka miki zaki zo kina wani had’emin rai,uwa wacce nama wani abu,salon DADDY ya ganki a haka,yayi tunanin ko na miki wani abune”….

”Kin gyara face enki ko kuwa?”….

Dad’a cunoo bakin tayi gaba tana mirgina kanta gefe…..

Haushin kansa yaji na maganar da yayi mata,cikiin fushi ya janyota yana d’ago fuskanta….
Yanayinsa da taga ya chanja shi ya bata tsoro cikin wani irin yanayi jikinta ya shiga rawa…..

”Who dare u da ina miki magana kina d’aukemin kai,na fara wasa dake ne?”
Kai ta jijjiga masa,idonta taf kwalla

”Ki maida hankalinki jikinki idan ba hakaba kuma
  Tammm”…..

Cillata yayi kan seat nata,ya dafe kansa da hannu,shi kansa mamakin yanda ya mata masifa yake,to wai menema ya jawo masa wannan fushin da bai san dalilinsa ba….

Kuka ta shiga rerawa,kanta ta cusa tsakanin laps nata,sai sheshek’an kukanta dake ratsa kunnensa….

Kallonta yayi da eyes nasa da suka fara canza colour zuwa jaa² jaa²….
Duk kuma sai yake jin abunda yayi bai kyauta ba,ita da ba laifi tayi masa ba…..
STORY CONTINUES BELOW

Tausayinta had’e da soyayyanta mai zafi ne suka bijiro masa lokaci guda..
Kukanta ya cika masa kunne,a duniyarsa idan akwai abunda ya tsana baya wuce hawayen mutumin da yake da wata k’ima a idonsa…..

So yake yace mata tayi ”hak’uri” amma ya kasa,ji yakema shi bakinsa yayi masa nauyi….
Cikin zuciyansa kuwa gani yake idan batayi shiruba,a kowane irin lokaci zuciyarsa zata iya sashi ya aikata abunda take k’ok’arin kissima masa…..

Daurewa yayi cikin sweet husky voice nasa ya furta
  _”Am so sorry baby,i just lose my temper…._

Banza da shi tayi kamar bata jiba,ta ci gaba da rera kukanta,tamkar wacce akace taci gaba…..

Hannu ya mik’a ya d’agota..

Babu zato ta tsinto hannunsa ajikinta…..

Bata san lokacin da nemi kukan ta rasa ba,sai raba ido da ta shiga yi,uwa mara gaskiya….
Kallon yanda tayi shiru lokaci guda yayi ba tare da ya furta ko da  ”A” ne ba,yace
“Thank God”…..

Ajiyan heart yayi,cikin sanyin murya ya shiga furta
   ”Bakya tsoron kanki ya miki ciwo hala,
komai agurinki na kuka ne kam?”….

”Lallaima YAH BOSS  en nan,yanzun ya gama min fad’a kan rashin dalili,amma kuma yanzun yana tambayana”……

Karaf yace ”waye ne YAH BOSS?”…….

Ido ta zare,sam batayi tunanin a fili tayi maganar tata ba….
Nan wani sabon kukan ya zo,yau kam ta san mai k’watanta hannunsa sai Allah……
Ta kasa cewa komai sai kukan da taci gaba dayi….

Tsayawa yayi kallon ikon Allah,daga tambaya sai kuka,shi kam a nasa ganin,wannan idan aka biyeta nan gabama magana akayi kuka zata sawa mutane….

Jingina yayi jikin seat en ya zuba mata ido…..

Zuwa can ya tuna dalilin fitowansu
Agogonsa ya kai duba,take kuwa zuciyansa ta tsinke….
Tab’b’b’! ai kuwa suna daf da yin late…..

Bai sake bi ta kanta ya tsaya jin abunda takema kukanba,ya fisgi kan motan,da mugun gudu ya bar gurin………

                  #Allah ya kaiku lapia…….

*~#TEAM J².~*

*_REAL SMASHER_* 🤞🏻😘
[5:17AM, 3/27/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *26/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*~_________________________~*
  *ADDU’AR SANYA SABON TUFAFI.*

_ALLAHUMMA LAKAL HAMD ANTA KASAUTA NIHI AS’ALUKA KHAIRAHU WA-KHAIRA MAA SUNI’A LAHU,WA’A’UZU BIKA MIN SHARRIHI WA-SHARRI MAA SUNI’A LAHU…_

          *_~#HISNUL MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 63↔64*

Ikon Allah ne kad’ai ya kai su cikin airpot en,suna shiga kuwa suka fara jiyo sanarwar jirgin da ya taso daga k’asar SINGHERPORE ya sauka…..
Ciki saurin da bai saba da yinsa ba,ya shiga tafiya,gudun kada DADDY ya zo yana nemansu…..

STORY CONTINUES BELOW

Abaya ta shiga binsa,sai dai duk da haka ya wuceta sosai…..
Tafiya take,ga rana da ke kwad’arta,ita kuma sai k’ok’arin karewa take…..
Cikin takunta nan kamar bata son taka k’asan…..

Wani motane dake  cike da passengers zai reverse lokacin da yake shirin barin cikin airpot en…..
Side ensa babu mirror,bare ya kula da abunda yake bayansa…..

Kanta a k’asa tana ta faman tafiya,bata kula da abunda ke gabantaba….
Sai tsintan kanta tayi a k’asa,lokacin da motan ya bada wani sauti,da gaba d’aya hankalin mutane ya dawo kansu…..
Sai salati suke,kafin wasu dak’ik’u har gurin ya soma d’inkewa da jamaa’a……

Tana nan durk’ushe a gurin sai k’afanta data rik’e k’am,hawaye na zarya kan face enta….
Kowa ya kalleta yasan tana jin jiki…..

Shi kuwa gogan naku yana cikin motan yak’i fitowa,saima k’ok’arin barin gurin da yake…..
Mutane sai magana suke masa amma yayi biris dasu tamkar kurma…..

YAH BOSS da har yaje bakin k’ofan da zata kai shi cikin airpot en,yajiyo karan,take jikinsa ya bashi ba lao ba….
A hanzarce ya juya,sai dai me…..

Duk iya hangensa na ya ganta hakan ya faskara….
Saima taron mutane da ya hango sunyi cycling a kan hanyan da ya baro…..

Cikin sauri ya dawo da baya,ta tsakanin mutane ya shiga ratsawa,yana shiga…..
Ga maganar mutane da take ta dad’a birkitashi……

Zaune ya hangeta rik’e da k’afanta,sai hawaye dake fuskanta uwa a kwance tap…..

Da matsanancin tashin hankali ya nufeta,kneeling yayi a gabanta,yana kallon yanda take faman rik’e k’afan ….
K’ok’ari ya shiga yi ya d’agata,nan maganar da ake ta dakatar da ahi daga nufinsa…..

*************

‘Dan zafin kan kuwa da k’yar aka fito da shi daga motan,sai rashin mutunci yake zubawa jama’a….
Sai cika yake yana fad’in duk maganar da tazo bakinsa….

Kyaleshi mutanen sukayi,sai wani dattijo da ya zo wucewa ya bud’e baki yana fad’in
”Kai yaro ai ba a haka,ta ina zaka kad’e mutum kuma kak’i fitowa ko da ban hak’uri?”…..

Katse baba yayi da fad’in
  ”Kaga baba itace fa tana tafiya bata kallon gabanta,dan na d’an tureta sai a wani hau maganganu akai,ai da bata tsaya a hanya ba da haka bata faruba”…..

Mamakin furuncinsa mutane suka shiga yi nanfa abun ya d’aurewa kowa kai….

Baba dake gefe ya bud’e baki yana fad’in
  “Amma duk da haka kai ne mai babban laifi,ta Ina za kayi tuk’i babu side mirror?”….
Ya sake bud’e baki  da niyyar sake yin magana,sai dai kash kafin ya ida nufinsa d’an zafin kan har ya tare shi….

”Kaga baba nifa ban son shishshigi,kawai ka kama hanyarka ka bar nan”…..
Gaba d’aya mutanen gurin suka shiga salallami,masu fad’in albarkacin bakinsu nayi,masu kama hanya suna barin gurin suma haka…..

Ci gaba yayi da fad’an abunda ke zuwa bakinsa,mutane sai Allah ya kyauta sukefad’i…..

  YAH BOSS dake durk’ushe gaban JIDDAH yana k’ok’arin d’agata,bai san lokacin da ya mik’e cikin fushiba….
Wuyan d’an taxi en ya shak’o,ya tsinka masa wani gawurtaccen mari….
Da ya sashi shiga number 6 ensa….

Tuni jama’a suka fara maganganu kan yayi dai² tun da bai san hak’k’in d’an adam ba ai gara a kyaleshi jikinsa yayi laushi gobe bazai sakeba….

Security en gurin ne suka kawo d’auki,nan aka samu wani ya rik’e d’an taxi en….
Da kyar suka iya raba shi da hannun YAH BOSS……
Suka danna shi cikin mota sai station,inda aka samu wanda zasu rakasu YAH BOSS hospital……

Tambayanshi suka shiga yi kan alak’arsa da ita yarinyar…..
Wani kallon banza ya watsawa mai tsmbayar….
  Cikin b’acin rai yace ”bansaniba…..
Idan za kayi abunda aka sakane to bismillah”…….

STORY CONTINUES BELOW

Daga haka ya juya,bai sake tanka masa ba……

                           **********

Sakkowan DADDY daga flight yaga bai yi arba da kowa da yake tsammanin zai zo taronsa ba,jiran ganin ta ina zasu billo ya shiga yi,sai dai baiga kowa ba har zuwa shud’ewar wasu minutes….
Seat ya samu ya zauna,zuwa wani lokaci…..

Shirun da yaga yayi yawa shi yasa shi,yanke shawaran d’aukan taxi ta kaishi gida….
Yana gama wannan tunanin kuwa,ya ja luggage ensa yayi waje…..

Da fitowansa ya hangi wani babu kowa,tsayar da shi yayi ya masa bayani…..

Dai² sunzo giftawa,DADDY ya hangi taron jama’a a gurin,kallon gurin yayi ganin har da mobile police…
Suna k’ok’arin tura wani a motansu…

”Allah ya kyauta DADDY ya furta”….

Ai nan mai taxi en da yake ciki ya hau bashi labari,duk da bai tambaya ba…..

Har sun gota gurin kamar ance ma DADDY ya juya,ya hango JABEER ya d’auka JIDDAH  tamkar wata jinjira,haka yake tallafe da ita…..

Cikin sauri kuwa DADDY ya dakatar da mai taxi en,ko bari ya gama parking baiba ya fice da sassarfa,ya k’arasa kusa da motan da YAH BOSS ke shirin sanya JIDDAH……
Yana tambayar ”mai ya sameta?”….

Jin voice en dake magana daga bayansa,ya sashi juyawa don gasgata zatonsa….
A kan DADDY idanunsa suka sauka wad’anda suka rine da b’acin rai…..

Kasa furta komai yayi,sai mutanen gurin ne aka samu wani ya shiga koro jawabi kamar shi aka tambaya….
Shikam DADDY baima san me yake fad’aba,dan gaba d’aya hankalinsa yana kan yaran nasa…..

Basu tsaya b’ata lokaciba suka wuce hospital,JIDDAH na baya sai hawaye take,tana yarfi da hannu….
Sai sannu take ta faman sha,daga gurin DADDY….
Shi kuwa gogan sai dai ya d’ago ta mirror ya kalleta,hankalinsa na kanta…..

Kiran MAMMY ne ya shigo…..

DADDY yayi k’arfin halin d’auka,jin yanayin yanda yake amsata ta fara magana da fad’in
   ”DADDYN yara lafiya najiku shiru har yanzun?”…..

Sai da yayi dogon ajiyan zuciya kafin ya amsa
”Mun samu matsalane amma yanzun zamu k’araso”….
Daga haka ya katse wayan….

                      *************

Jin wayan yayi shiru ta duba ta gani,sai dai an riga anyi hanging kiran nata…..

Hankalinta duk ya kasa kwanciya,haka ta shiga SAFA & MARWA,ta san ko kira ta sake yi babu tabbas su d’auka…..

Hak’uri tayi amma bata sake kiranba…..
Sai dai addu’ah da ta shiga yi a ranta na nema musu kariya…..

                       ***********

Da shigansu cikin hosputal na MUHAMMAD ABDULLAHI WASE basu zame ko ina ba sai A & E…
Kasancewar akwai police da suka biyosu,basu sha wahalaba aka karb’eta…..

Kuka kam ta sha shi,har ta godema Allah,da hawaye na k’arewa da yau na JIDDAH ya jima da k’afewa…..

Zuwa shud’ewar wasu sa’o’i DR ya fito,yana murmushi,kusa da DADDY ya tsaya yana fad’in
   ”Alhamdulillah!! Zaku iya shiga ku ganta,idan kun so ma zaku iya tafiya da ita tun da ba wani ciwone da zaisa ta zauna a hospital ba,sparing ne ta samu a k’afan”……

Godiya suka masa,kafin suka shiga d’akin da take….
Tana kwance kan bed idonta a rufe kamar mai bacci….
Sai dai jin alaman tab’a k’ofa ya sata juyowa…..
Ganin DADDY da tayi shi yasa ta murmushin dole,wanda da gani kasan ba komai a cikinsa face azaba…..

STORY CONTINUES BELOW

Banda sannu babu abunda DADDY ke jerowa,yana kallonta da tausayawa…

Bayan sun barta ta huta zuwa wasu awanni,DADDY yama JABEER maganan ya amso musu sallama,gara su wuce gida,tunda abun ya xo da sauk’i……

  After an basu sallama…….

‘Dakin ya dawo da receipt’s a hannunsa na charging ensu da akayi….
Yana shigowa idonsa ya sauka akanta,nan ya fara tunanin yanzun ya zasuyi da ita…..
Ko k’arasa tunanin baiba,yana tsaye inda yake jikin k’ofan DADDY ya katsesa….

”To malam k’araso mana ka d’auketa mu tafi ko”….
Ya tsinkayo muryan DADDY yana fad’a…..

Jiki ba k’wari ya k’araso,ya shiga gyara mata vail enta dake kanta….
Duk abunda yake DADDY na kallonsa,ganin ya tsaya kame²,hakan yasa DADDY ficewa…….

  A bakin motor en suka tarar da shi tsaye da police en da suka rakosu….
  COMPLEMENT CARD ensa ya basu,yana fad’in zasu iya samunsa a office,coz yanzun daga tapia yake,suka ma juna godiya suka tafi…..

Mota ya sanya ta,suka shiga,nan suka nufi hanyan fitowa daga hospital en…..

                       *************

A dai² bakin gate en sun fito zasu d’auki hanya…..

Suka ga ana d’aga musu hannu,dakatar da shi DADDY yayi,tare da sauke glass en…..
Yana kallon mutumin dake tsaye…..

”ALHAJI nine mai taxi en da ka hau,ka manta jakar kane,lokacin da ka fita”…
murmushi yayi da yake sai yanzun ya gane,yana mai bashi hak’uri….

Jakan ya mik’a masa,DADDY ya masa godiya,had’e da mik’a masa CARD ensa sukayi masa sallama……
                        **********

MAMMY dake tsaka da SAFA & MARWA,tana ta faman addu’ah….
Sai dai haryanzun hankalinta ya gaza kwanciya……

Tana tsaka da zagayen d’akin taji yo horn,bata jira komaiba tayi waje…..

Hangosu da tayi,shi ya d’an bata nutsuwa,sai dai bayan sunyi parking a gabanta,ta bud’e door en baya idonta ya sauka kan k’afan JIDDAH da ta sha bandage…….
*~#TEAM J²~*

*_REAL SMASHER_*  🤞🏻😘
[3:57AM, 3/28/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *27/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*~_________________________~*

*ADDU’AH IDAN KAGA WANI DA SABON KAYA.*

  _TUBLIY WAYUKHLIFULLAHU TA’ALA…._
_ILBIS JADIDAN,WA’ISH HAMIDAN,WA-MUT SHAHIDAN._

          *_~#HISNUL MUSLIM.~_*

*~__________________________~*

  _Hak’ik’a soyayya da k’auna a cikin zuciya suke,babu wanda yasan adadin masoyansa a rayuwa,sai dai idan sun bayyana maka kawunansu *KHADIJA S DOGARAI (LIPTON)* ina godiya da soyayyarki gareni Allah ya bar k’auna, *REAL SMASHER* na k’aunarki…_

*_AHABBAKIL-LAHUL LAZIY AHBABBTANIY LAHU.._* 💔💔💔

  _Wannan shafin gaba d’aya sadaukarwa ne gare ki…_
*Really heart u dear 💔*
*~_________________________~*

STORY CONTINUES BELOW

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 65↔66*

Ido ta sake bud’ewa tana son gasgata zatonta da abunda idanunta suka gani…
Anya kuwa ta ga dai²?….

Kai wannan ba gaskiya bane,ido ta shiga murzawa,amma me zata gani tana bud’ewa ta sake yin arba da k’afar JIDDAH nad’e a cikin bandage…..

*INNALILLAHI WA-INNA ILAIHI RAJI’UN!!!*
A bunda ta shiga maimaitawa kenan,har zuwa lokacin da ta ji zuciyanta ta fara sauk’i…..

Har su DADDY suka fito tana rik’e da k’ofan motor en,ta kasa cikawa bare su samu su fito da JIDDAN zuwa cikin gidan…..

Ta jero mata sannu yafi a k’irga,amma duk da haka bata matsa daga gurin ba….

DADDY ne yayi k’arfin halin yjn magana
  ”Hajia da kin matsa ai ya shiga da ita cikin gida ko,sai ki ci gaba da kallonta”…..

Da k’yar aka samu MAMMY ta matsa YAH BOSS ya fito da ita daga cikin motor en ya nufi cikin gida,su kuma suna binsu a baya….
Bama kamar MAMMY da tafi saurin binsu duk inda YAH BOSS ya d’auke k’afarsa nan take mai da nata….

A parlor ya direta akan rug en gurin,pillow MAMMY ta kawo aka jingina mata a bayanta…..
Sai lokacin MAMMY ta shiga sake jero mata sannu,fuskanta duk tausayi ya cika ta….

DADDY kam da YAH BOSS y’an kallo suka koma,yanda MAMMY ta shiga ji da JIDDAH tamkar kwai….

                         **********

  Ko da LITTLE ta shigo gida lokacin bayan sunyi sallama da FAROUK akan zai dawo zuwa dare don yayima DADDY barka da zuwa….

Ta shigo da murnanta ta haura sama,rashin ganin SISIN nata shi yasata jin babu dad’i,ta tabbata sun tafi….
Haka tayi wanka,ta kwanta kan bed take bacci yayi gaba da ita….

Har suka dawo daga hospital tana sama bata san wainar da ake toyawa ba….

Gajiya da kwanciyan tayi,tunawa da batayi sallan Asar ta juya tana duba wall clock ensu….
Da sauri ta mik’e ta nufi toilet….

Sai da tayi wanka tukun ta d’auro alwala,bata tsaya shafa ba ta zura dogon riga,ta kabbara sallah….
Yunwa ne taji yana neman lahanta mata kayan ciki ba shiri ta ajiye hijab en tayo waje….
  Har ta gama sakkowa idanunta basu kai kan mutanen da ke parlor en ba……..
Burinta kawai ta samu abunda zata sawa cikinta…..

                         **********

  ”Wai ni kam garin yaya wannan abun ya faru ne?”
Tayi tambayan tana kallonsu DADDY….
YAH BOSS ya nuna mata da hannu.

Saboda haka ta mai da hankalinta kansa..
Bai san da shi take magana ba sai da ta furta
   ”Da kaifa nake JABEER”….

‘Dagowa yayi yana kallonta kafin cikin sanyin jiki ya furta
   ”TSAUTSAYI ne MAMMY kuma Allah ya K’ADDARA faruwan haka”…

Hannu ta d’aga masa tana fad’in ”nasan da haka,cewa nayi garin yaya hakan ya faru?”…

”MAMMY nimafa bansan ya akayi hakan ta faruba coz na rigata yin gaba”……

Ko kafin ya k’arasa MAMMY ta katseshi da fad’in
  ”Zancen banza kenan,kai kana babba amma kai ne a gaba”….

   Nan ta shiga fad’a ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,tamkar zata ari baki haka tayi ta masa fad’a…..

Kansa yana k’asa ko tari baiyiba sai da ya tabbatar ta gama,sannan ya shiga bata hak’uri…..
Banza tayi da shi,bata tankasa ba….

STORY CONTINUES BELOW

Duk abunda suke DADDY na zaune ko ‘A’ bai furta ba har tayi ta gama,murmushi kad’ai yayi….

                         **********

Maganar MAMMY kad’ai ta tsinkayo acikin kanta wanda ya sata juyawa ta kalli gurin…..

DADDY ta hango zaune yana murmushi,da gudu ta nufi gurin sai da ta je daf da gurinsa ta ankara da YAH BOSS tsaiwa tayi chak tana washe baki…
Cikin sanyi ta k’arasa tana fad’in ”barka da dawowa DADDY”….

‘Dagowa sukayi gaba d’aya suna kallonta…
‘Daya bayan d’aya ta shiga kallonsu,kamar yanda suma sume kallonta….

Kan k’afar JIDDAH dake mik’e ta sha rawani da bandage idonta ya sauka….

Zare ido tayi,cikin kid’imewa ta nufeta….
Ko kafin ta k’arasa hawaye har ya soma ambaliya a face enta….

IKHRAM da ta shigo da sallamarta,duk jinta take a gajiye….

Kan sofa ta samu ta cilla skul bag enta,tana zare socks en k’afanta….
Sheshshek’an kukan LILLTE ya ratsa kunnenta…

Kallon gurin tayi nan idonta sukayi arba da abunda ba tayi tsammaniba…

Mik’ew tayi ta nufesu babu tambaya itama ta bi bayan LITTLE…..

Kuka suke kamar sune suka ji ciwon ba ita ba…..

Ita kam ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah,ta kasa ce musu komai,sai da sukayi mai isar su,dan kansu sukayi shiru…..

DADDY ne ya kalleta bayan sun gama shan kukan nasu da fad’in ”y’ar gidan MAMMY bakya gane kowa ne?”…

Suprisingly ta kalli inda tajiyo maganar…
DADDYN dai ta gani yana mata murmushi….
  Ihu ta fasa,tana tafe hannu take fad’in
  ”Allah DADDY ban san ka dawoba,an dawo lapia?”…

”Lapia k’alau,ya makarata?”….

”Babu dad’i” ta fad’a tana b’ata rai….

Dariya yayi,ba tare da ya sake magana ba…
Haka suka ci gaba da zama jugum,motsi kad’an JIDDAH za tayi suna faman jera mata sannu…..

MAMMY ce ta tashi da taimakon LITTLE da IKHRAM suka shirya dinner…

Su JIDDAH ana zaune,sai dai tayi ta binsu da kallo…
Koda lokacin sallan maghreb yayi,a inda take zaune MAMMY ta taimaka mata tayi alwala,tana daga zaune tayi sallanta….

Ranan kam a nan cikin parlor sukayi dinner,after sun kammala aka dasa fira,har zuwa time en bacci…

Koda DADDY yace ma YAH BOSS ya kai JIDDAH d’aki ba a son ran MAMMY hakan ke faruwa ba,kawai dai tayi shiru ne….

Haka ya d’auketa zuwa bed room en su,after ya kwantar da ita,ficewa kad’ai yayi ba tare da yayi magana ba….

Da ido JIDDAH ta rakashi har ya k’arasa ficewa daga d’akin….

Murmushi tayi gano irin yanda yake had’e rai idan an sashi d’aukanta….
Kanta ta d’ora kan pillow ta lumshe idanunta,tana shak’an perfumes ensa da sukayi saura a jikinta,kamar wacce aka shafawa…

                        ************

  Ganin kowa ya watse parlorn hakan ya sa MAMMY tabi bayan mijinta….

Abun duniya duk ya isheta,akan mene za ana sa JABEER yana d’aukan JIDDAH,ai yin hakan sab’awa addini ne,ta yaya baligi kamarsa zai kinkineta,ita da ba muharramarsa ba,duk da larura ne yasa,ita kam bazata zuba ido tana kallon haka yana faruwa ba….

Sai da ta bari sun gama shirin kwanciya,sannan ta shiga yiwa DADDY k’orafin abun,sannan ta fad’a masa dalilinta na ganin rashin dacewar hakan….

Murmushi yayi,bai tanka
ta ba,sai da ta gama sannan ya fara magana…

STORY CONTINUES BELOW

”Duk abunda kika fad’a haka ne,na san ba dai² bane,buh idan kika duba,cikinku akwai wanda zai iya d’agata bare ya canza mata gurin zama?”….
Kai ta kad’a masa,alaman
   A’a….

”To kinga kuwa sai kinyi hak’uri,dan a yanzun shi kad’ai zai iya d’awainiyar d’agata daga nan zuwa can,amma kiyi hak’uri komai lokaci ne,bana son ki dinga kawo wasu tunanin na daban a ranki”….
Murmushi kad’ai tayi,tana neman gurin kwanciya…..

”Haba my LADY bacci tun yanzun,ni ko tarbar kirki ban samu ba,ana jinyar y’a,tun d’azun kamar nayi laifi…
Ai yau tun da na dawo sai an lallab’ani nima zanyi bacci,kuma kowama zaiyi”….

  Ita kam kalamansa kunya ma suka sa taji,ba shiri ta rufe idonta tana juya baya…..

                        ************

  Har ta fara bacci ring en wayanta ya farkar da ita..
Bata tsaya son sai ta gane mai kiran ba ta d’auka…
Cikin murya da ke nuni da mutum ya fara bacci,tayi sallama…

Amsa mata yayi,cikin sanyin murya yake fad’in
  _”Am so sorry,MY QUEEN na katse miki bacci”…_

Bata ce komaiba,tayi shiru tana sauraresa…

_”Ya k’arfin jikin naki?”…._

Babu shiri ta nemi baccin dake idonta ta rasa,tana ma kanta question
”A ina yasan bata da lapia?”….

_”Kinsan ikon Allah ba ta yadda baya kasancewa,a jinin jikina nasan kina cikin prob”_
Maganarsa ta daki kunnenta…

Dafe kai tayi kenan a fili tayi maganar tata ko me?…

_YEAH_ ya bata amsa…

Wayan ta katse,babu shiri ta kasheta gaba d’aya,chest enta na bugawa into paster…
  Ita kam wannan ko dai ALJANI ne bata sani ba,komai nata ya sani,hatta maganar da za tayi a zuciyanta yana jinta…

Nan ta shiga tunanin mafita ita d’aya…….

*_~#TEAM J2~_*
*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
[7:03PM, 3/28/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *28/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*~_________________________~*
  
*ADDU’A YAYIN CIRE TUFAFI.*

       _BISMILLAH!!_

*ADDU’A IDAN ZA A FARA ALWALA.*

       _BISMILLAH!!!_

         *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

  _Sisinah ina miki fatan alkhairi arayuwa,ubangiji ya tashi kafad’unki,ina missing enki sosai na rashin kasancewa tare da ke.._
  _Wish u quick and speed recovery *MY HUBBEEY* ,I so much heart u dear.._ 💔💔💔
*~_________________________~*

_*MY MEINERH (LITTLE)* kina nan acikin birnin zuciyata,soyayyarki ta dabance,ban had’aki da kowa,sha sha’aninki wannan page en gaba d’ayansa na kine,ke d’aya…_ 👌🏻
_I so much miss u dear,feeling lyk crying till tomorrow…._ 😭😭😭

*Heart u nd miss u cweety 💔*

*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

STORY CONTINUES BELOW

*℘ąɠɛ 67↔68*

Tunanin mafita ta shiga,tana kwance ta ja jiki ta jingina bisa pillow….

To waima wane irin mataki ya kamata ta d’auka?
Tayima kanta tambayan…

Zuciyanta ne ya kasu biyu ko wanne da irin tunanin da yake kawo mata…
‘Daya na fad’a mata ta sashi a blacklist…

Kai ta kad’a yayin da zuciyanta ke fad’in
    _”noooo dont even try”….._

”To wai ya zanyi ne kam” ta sake tambayan kanta…
‘Dayan zuciyan ne yace
   _Kibi a sannu har ki gane wanda ke bibiyanki.._

Finger enta tasa a baki tana ciza,tana ci gaba da tunani,da haka har bacci ya d’auketa garin tunani…

Ko da Asubah ma MAMMY tazo har d’aki tasata tayi alwala ta gyarata yanda zata fuskanci alk’ibla,haka tayi sallanta har ta idar…
Azkar tayi na safiya da maraice,tana zaune har gari ya gama wayewa sosai rana ta hudoo…
Sallah tayi raka’a biyu ta ci gaba da addu’o’inta zuwa rana ta gama game garin baki d’aya….
_(YIN SALLAH RAKA’A BIYU BAYAN RANA TA HUDO, MUTUM YA IDAR DA SALLAR ASUBAH,YA ZAUNA YANA AMBATON UBANGIJI A INDA YAYI SALLAH,BAYAN RANA TA HUDO YA TASHI YA SALLACI SALLAH RAKA’A BIYU,ANNABI (S.A.W) YACE:”KAMAR MUTUM YAYI AIKIN HAJJI DA UMRAH NE TARE DA SHI…)_
  _Allahya bamu ikon aikatawa…._

Kamar ko wane lokaci yauma haka YAH BOSS ya d’aukota daga d’aki zuwa parlor…
Sai b’ata rai yake shi a dole bai so hakan ba…
Cikin zuciyansa ko fal farin ciki haka yake ji,ga wani tausayinta dake ratsashi…
Amma uban girman kai da miskilancin nan nasa ya hana masa ya nuna..
A nasa ganin yin hakan zai sa ta raina sa…

Sai da ya direta sannan ya koma yayi shirin ficewa daga gidan….

Haka LITTLE ta kammala shirinta itama ta sakko kusa da sisin nata ta samu guri ta zauna,suka hau jinyan su biyu…

IKHRAM da ta fito daga d’akin MAMMY Kusa da su ta zo ta zauna tana gaida su…
  Suka ci gaba da fira,don d’ebe mata kewa….

*IN D EVENING…*

   Sallam HUBBEEY ce ta katse musu firan da suke…
Da murnansu suke welcoming nata…

Sai da suka gama tsokanar juna kafin ta mik’e zuwa inda MAMMY take ta gaidata….

Firan suka ci gaba da yi,nan ta kalli JIDDAH da salon tsokana take fad’in
     _”Allah sarki matar babban yaya an zama gurguwa”…._

    Dariya suka fashe mata da shi,nan ta murgud’a musu baki tare da fad’in
   _”Eh naji babu komai,ai dai bazai daina sona ba ko me zai sameni”….._

Dariya suka sake sawa…
  ”Waye ya fad’a miki bazai daina sonki ba?”…
”Lallaima yarinya kin yaudari kanki,idan bai daina sonki ba to kuwa zai miki amarya”….
    Suka ci gaba da tsokanarta….

Banza tayi da su bata sake kula suba…
Su kuma kamar wad’anda ta sa suci gaba….

  Sai sunyi shiru sai su ci gaba….

”Allah sarki gurguwar amarya shi kenan haka zaki dinga fama da cangala k’afa…
  Haka za a bamu rabin sadaki”…..

Ko K’arasawa basuyiba tasa kuka nan su kuma suka samu abunyi dariya suka sata gaba suna yi…..

YAH BOSS da ya shigo yanzun ya tarar da su suna ta faman dariya,ita kuma hakimar sai kuka take……
Sallama yayi ciki²,ya shiga takowa cikin takunsa na k’asaita….

Babu wanda ya ga shigowarsa cikinsu…

Juyowa LITTLE tayi tana tsaka da dariya ta hango shi yana takowa inda suke….

STORY CONTINUES BELOW

Bakinta ta rik’e tana dungurin HUBBEEY da IKHRAM da suke ta faman dariya….

Shiru kowacce tayi tana rik’e baki…..

Kallon su yayi d’aya bayan d’aya,rashin gaskiyan da ya gani a kan fuskokinsu ne yasa shi cilla musu harara ya juya yana haura stairs en d’aya da d’aya….

                       ***********

*MONDAY EVENING..*

  Da yammacin ranar Litinin,da yawa daga cikin course mate en su suka zo duba JIDDAH…

Haka aka dinga zuwa dubata daga k’awayensu,k’awayen MAMMY da ma abokan DADDY na kasuwanci…

   Haka JIDDAH ta ci gaba da jinyan jikinta har zuwa tsawon sati uku…

                    *************

Sosai jikinta yayi kyau,zuwa wannan lokacin JIDDAH ta saba da ganin sak’onnin mutumin da bata san ko wayewa ba a fuska,sai dai sunansa da tayi saving MUHAMMAD…
Tana farin ciki haka zata d’auka kiransa,su jima suna shan fira..
Ko ina suna tare da juna akan waya…

Shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakaninsu….
Har ta kai idan basu kasance tare da junaba na yini d’aya ko wannensu zai kasance cikin ALHINI….

  ‘Ban garen LITTLE da FAROUK ma ba a barsu a baya ba,dan kuwa soyayya suke nunama juna mai cike da tsafta ga girmama juna….

Ko da wasa babu wanda yayi tunanin cewa JIDDAH tana soyayya da ‘BOYAYYEN MASOYIN nata…..
        Wannan kenan….

                    ***************

Tsawon wannan lokaci an samu chanje² ta fuskoki da dama….
 
   Kamar ko wane lokaci yauma zaune DADDY yake akan cuition yana duba DAILY NEWS PAPER….
  Da farin medicated glass sanye a idanunsa….

MAMMY tayi sallama hannunta d’auke da tray,samansa lemone na sob’o cikin babban jug na glass….

Da fara’arta ta k’araso ta nemi guri kusa da shi ta zauna,tana fad’in
   ”Barka da hutawa”…..
‘Dagowa yayi yana ninke newspaper en..
Saman table en dake gabansa ya d’ora yana fad’in ”kamar kuwa kinsan ke nake ta zuba ido naga ta inda zaki fito”….

Murmushi tayi dake nuna tsantsar farin ciki
  ”To ai gani yanzun,Allah yasa dai lapia”..
  Tayi maganar tana saurarensa taji abunda zai fad’a….

Sai da yayi murmushi irin nasu na manya,kafin ya fara magana…
  ”Eh to shawara ce dai nake so muyi kan maganar yaran nan,mu ga abunda ya kama ta ayi,idan yaso,sai mu tsaida matsaya guda d’aya”…

   Ajiyan zuciya tayi,tana mai dad’a nutsuwa kan abunda yake son su tattauna…

”Gaskiya dai Alhaji na dad’e da wannan tunanin,kawai dai nayi shirune naji me zaka ce akai”….
  Ta fad’a cikin sigar tabbatar da abunda ta fad’a…

”To dakikayi shiru ina amfaninsa?
Kinsan da cewa lokaci ba jira yake ba,yanzun da banyi maganar ba haka zaki zuba ido kenan?”…

Shiru tayi babu amsa
Shi kuma yaci gaba, ”dalilin da yasa nayi wannan maganar kuwa shi ne
  Yanzun tun da Allah yasa AMINATU ta samu wanda yake sonta da gaskiya,me zai hana ba zamu d’auko wannan tsohuwar maganar ta had’a JABEER da JIDDAH aure,lokaci yayi da ya kamata ace muma mun sauke nauyin da Allah ya d’ora mana..

Baya ga haka,su y’ay’an zamani ne,ba kamar muba,kana iya b’ata lokaci kana bawa d’anka tarbiyyah da zarar ya fita waje ya had’u da sha³n abokai ko k’awaye sai su canja masa tunani..
Shi yasa naga dacewar tak’aita lokacin nan da zuwa watanni biyu masu zuwa”….
Ko kuwa me kike ganin ya dace ayi…

STORY CONTINUES BELOW

Fuskanta cike da farin cikin maganar tasa,ta amsa masa da
   ”Duk hukuncin da ka yanke ai an riga an gama kuma,mu namu aikatawa,abun da zance dai ba zai wuce Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa ba”…
Ta fad’a tana murmusawa…

To shi kenan Allah ya nuna mana lokacin muna masu rai da lapia….

           
”Yanzu abunda yayi saura magana da yaran ki ji ra’ayinsu,kafin nan ni kuma zanyi magana da yaron da yake zuwa wajen AMINA…
Zan kuma tuntub’i JABEER kan maganar auren nasu”…..
  DADDYN ya fad’a…

  ”To shi kenan in sha Allah zan musu maganar,Allah yasa muji alkhairi….
                  *#AMEEEEN….*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *31/mąrcɧ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM…_

*~_________________________~*
   *ADDU’AR SHIGA BAN’DAKI.*

     _BISMILLAHI!!! ALLAHUMMA INNIY A’UZHUBIKA MINAL-KHUBSI WAL-KABA’ISI.._

*ADDU’AR FITOWA DAGA BAN’DAKI.*

   _GHUFRANAKA…._

         *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

    _Masoya *Y’AR GARUWA* ina mai baku hak’uri sakamakon bazan samu damar posting ba yau,coz bana cikin yanayin da zan iya dogon typing yau.._

  *_#Luv u oll…_* ❤

*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 69↔70*

   Tsaf suka kammala shirinsu na tapiya skul,dan kuwa zuwa wannan lokacin sosai ta samu sauk’i,MAMMY suka ma sallama suka wuce,inda LITTLE ke driven…
JIDDAH na gefenta gurin mai zaman banza,tana d’an duba lecture note nata,coz tsawon 2 weeks kenan bata lek’a skul enba,tana jinya….
Sai dai yanzun kam Alhmdllh jikin yayi kyau sosai,saboda tana da jiki mai kyau….

  Tafe suke,in da ba komai ke tashi cikin motanba sai wak’an P.SQUARE nd DAVE SCOTT mai taken ”BRING IT ON”….

  Kowa da tunanin da yake har suka shiga cikin skul en…

Parking tayi suka fito,cikin salonsu mai burgewa suka fara ratsa hanyan har suka kai lecture venue en nasu….
  Tun daga shigarsu sai zuwa ake ana duba JIDDAH ga wad’anda basu samu damar zuwa gidaba….

  Ranan haka suka wuni cikin skul sai after 4:00pm sannan suka samu daman samun sarari….
A gajiye suka koma gida,bama kamar JIDDAH da ta kwana biyu bata lek’a skul enba….

Zuwansu gida basu tsaya k’asaba suka haura sama,sai bayan maghreb suka sauko shima,firane ya zaunar dash,sai jiran dinner da suke…

Sai kuma MAMMY da ta sanar da su tana son ganinsu…

Kowa jiki a salub’e haka suka tarar da ita a parlor tana zaune daga ita sai IKHRAM da tayi pillow da cinyanta…
Neman gurin zama sukayi kowa da abunda yake sak’awa a ransa…

Bata ce musu komaiba,har zuwa shud’ewar wasu mintuna….
Su kuma kowa yana sauraren jin ta inda zata fara magana…

Shigowan YAH BOSS,hannunsa sak’ale da lab coat ensa yana tafe cikin k’asaita…
  Ya k’araso cikin parlor,MAMMY ya gaisar kafin ya mik’e yana shirin haurawa sama..
Dakatar da shi MAMMY tayi ta hanyar fad’in
   ”Idan ka gama abunda kake ina son ganinka”…

STORY CONTINUES BELOW

Dawowa yayi yana zama,fuskansa na nuna alamar damuwa coz baisan me zata fad’a ba,shi kuma gashi baya cikin type en da idan kace zaka fad’a masa magana ka jaa lokaci…
Bai cika son zama cikin damuwa ba shi yasa,ek’ok’arin guje mata…

”Kaje ka huta tukun,ai ba inda zaka yanzun da dare kam ko?”….
Kai ya kad’a mata,yana fad’in
”No MAMMY gara dai kiyi maganan,idan na haura yanzun babu tabbas na dawo nan maybe sai da safe,coz akwai aikin da zan k’arisa”….

   Kai ta kad’a alaman ta gamsu da maganarsa,kafin ta fara magana….

“Dalilin da yasa nace ina son magana da ku,sa’one da DADDYNKU ya wakiltani na sanar daku dukanku..
Ku ba yara bane da za ana fama da ku,kun riga kun mallaki hankulanku….

”Kai kaine babba cikinku,saboda haka kai zaka nunawa k’annenka hanyar da za subi wajen yi mana biyayya,idan bakayi hakanba to suma suna iya yin fatali da hakan..
  Babban abunda yasa na kasance tare da ku a yanzun,baya wuce taso wani tsohon magana da na tabbata acikinku babu wanda ya manta da ita,sai dai ina son tunatar daku..
   Kun riga kunsan maganar da DADDYNKU ya yanke kan maganar aurenku,ya bar maganar ne saboda son had’aku da yake duka ya aurar lokaci guda,sai dai ya bar maganar zuwa lokacin da AMINATU zata samu tsayayye,kuma wanda babu k’arya a lamarinsa”….

‘Dan dakatawa tayi,tana kallon yanda kawunansu ke a k’asa,kamar basuba,kafin taci gaba….

”To Alhamdulillah Allah ya kawo lokacin,wanda a yanzun haka nake farin cikin sanar daku DADDYNKU ya tsaida lokaci nan da watanni biyu masu zuwa”..
  Ta fad’a fuskarta tana mai bayyana farin cikin da take ciki….

”Kai JABEER kai ne babba kariga kasan da wannan maganar,kuma da amincewarku akai hakan tun tuni,shin ka tuna wannan maganar?”…

‘Dagowa yayi ya kalleta,yana fad’in
  ”Eh MAMMY”…

”To Masha Allah,tunda baka manata ba,kuma ina fatan baku mantaba ko?”..
  Amsawa sukayi suma,nan dai MAMMY ta d’anyi musu nasiha,kafin ta sallamesu,ta nufi d’akinta…

  Da k’yar suka bar parlor jikin kowa yayi sanyi saboda nasihan nata ya shigesu,sai kace mai bada WASIYYA haka ta musu,shi yasa jikinsu duk ya mutu….
  Haka suka nufi d’aki kowa shiru babu maganar kirki….

Har suka kwanta babu wata fira,kowa da tunanin dake ransa….

B’angaren LITTLE kam murna take kan CIKAR BURINTA,wato FAROUK sai dai nasihan MAMMY ya hana mata murnan nata ya bayyana…

  Ga JIDDAH itama ta rasa fahimtar al’amarin zuciyanta,coz ta kasa tantance wanda tafi so tsakanin
  MUHAMMAD da kuma YAH BOSS en nasu…

Tunaninta ya tsaya cak,burinta ta bambancewa zuciyarta matsayin kowanne,amma abun ya gagara…
  Har yanzun a position d’aya take jinsu…

  ”Shin ina mafita?”
Tayiwa kanta wannan tambayar yafi a k’irga,amma ta kasa…
   Kuka tasa  k’asa²,wanda yasa LITTLE mik’ewa zaune tana tab’ata…

”SISINAH whats going wrong?”….

Rashin amsa yasa ta fara lallashinta,amma kamar dad’a zugata tayi,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru…

”Kin san dai sis bana son ganinki cikin irin wannan halin,ko mene ne yake damunki bazanso ki kasance cikin damuwa ke d’ayaba,amma tunda baki so na sani,zan tayaki da addu’an neman sauk’i,kiyi hak’uri ki daina kukan nan please kada kanki yazo yana miki ciwo”…..

  ”NOOO!Sisinah ba wai banson ki sani bane,ni kaina nasan yaudaran kaina nake,amma bari kiji YAYA ABUN YAKE”….

  Nan ta kwashe labarin abunda yake faruwa kaf ta sanar da ita….

Dogon ajiyan zuciya tayi,kafin ta dafa ta,tana fad’in
  ”NOOOO!sisi bakiyi ba dai² ba,sai dai kin kusa yin ba dai² ba,amma anawa shawaran,yanzun abu d’aya ya dace kiyi…
   Duk da kasancewar YAH JB matsayin d’an uwa gareni,bazan so idan har bakya sonsa kiyi shiruba,coz ke zaki cutu….
  Mafita d’aya ne,shi ne kiyi musu jarabawa tunda kin kasa bambance wanda zuciyanki ke so,me zai hana ki cema da MUHAMMAD en kina buk’atar ganinsa,tunda baki tab’a yin hakanba
  Ina tabbatar miki da cewa idan yak’i amsa tayinki to ki tabbatar ba soyayyarki a tare da shi,maybe kuma yana da wata manufa akankine”….
  Kinga daga nan saikima kanki da kuma iyayenmu adalci…..

  Sai yanzun taji zuciyanta yayi mata fayau babu damuwa kamar d’azun…
  Tunani ne ya sake bijiro mata,itakam ta yaya zata iya bijirewa umarnin wad’anda suka rufa musu asiri,gaskiya dai itakam ba zata iya aikata hakan gare suba,ko dama ace babu soyayyan YAH BOSS en a ranta,gara ta sadaukar da farin cikinta wajen faranta musu suma…
  Wannan shawar da zuciyanta ta bata,shi ta yanke zatayi amfani da shi,da niyyar neman MUHAMMAD en ko dan ta fad’a masa gaskiya kan lamarinta,sai dai tsoro daya baibaye mata zuciya,ko zata iya?”……

Sosai taji dad’in shawaran zuciyan nata,in da tayi fatali da shawaran sisin nata,da murnanta ta janyo phone enta tana bud’e hospot nata….

Kamar wanda ake jira,sak’onsa ya fad’o cikin phone en nata….
   Kamar yadda sukayi da LITTLE haka cikin dabara ta sanar da shi maganar son ganinsa da take….

Dariya ya mata,kafin ya bata amsa da
   _”Kimin alk’awari koda kin ganni bazaki gujeniba,bayan kin san ko ni en waye…_
    _”Ni kuma nayi miki alk’awarin bayyana miki kaina,soon”_

Sai da ta tabbatar masa da hakan,kafin suka tsunduma tafkin soyayya….

  Haka suka b’ata lokaci mai tsayi suna musayar kalamai masu sawa zuciya nutsuwa,kafin sukayi sallama da junansu,suna jin kamar su kasance a haka kada su rabu….
  Da k’yar suka rabu yana mai mata albishir na zuwansa nan da k’arshen satin,sukayi sallama,zuciyoyinsu fal farin ciki……
*#Kuyi hak’uri da wannan fan’s coz banjin dad’i 2dayz,luv u oll…* ❤💋

*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘

💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *12/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*
  *ADDU’AH IDAN ZA A FARA ALWALA*

  _BISMILLAH!!!_

*ADDU’AH IDAN AN GAMA ALWALA*

  _ASH-HADU AN-LAA ILAH ILLAH,WAHDAHU LAA SHARIKALAHU,WA-ASHHADU ANNA MUHAMMADIN ABDUHU WARASULUH…_

  _ALLAHUMMA JA’ALNIY MINAT-TAWWABIYNA,WAJA’ALNIY MINAL MUTA’DAHHIRIYNA…_

_SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA ASHHADU ANLAA ILAHA ILLA ANTA ASTAGHFIRUKA WA-ATUBU ILAIK…_

    
       *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*

  _Y’an uwa muna godiya bisa addu’o’in da kuke mana,na rashin lafiyan sisinah,cikin ikon Allah ta samu sauk’i,masu kira,text da masu zuwa gida duk muna mik’a godiyarmu gareku,Allah ya bar zumunci.._
  *_#REALLY HEART U…_* 💔💔💔
*~_________________________~*
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
     *HAPPY!*
                *HAPPY!!*
    *BIRTHDAY!!!*
               *TO U DOUGHTER.*

🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻
_May God shower his choicest blessings on you. wishing you happiness, good health and a great year ahead._
🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫

  K        A        S
    H        B        
      A        U       A’
        D        B
          I         A       A
            J         K
              A         A      D
                 T         R
                                
   🌹 *_(KHAIRAT)._* 🌹
🍭🍭🍭🍭🍭🍭
  _Appy bufday dougheeey,wish u many more years ahead,happy fruitful years…_

🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 71↔72*

Washe gari haka ta tashi fal da murna,sai dai gefe d’aya kuma fargaba ne a cikin ranta,na yanda zata fuskanci abunda ke shirin faruwa…
Haka ta labartawa LITTLE yanda sukayi da MUHAMMAD en Nata…..
Itama ta taya ta murna sosai,ganin yanda sisin nata ke tsaka da murna,duk da ta b’oye mata damuwar da take ciki…+

  Duk wani k’ok’ari JIDDAH yinsa take na ganin ba a gane tana cikin damuwa ba…
   A maganar da sukayi da LITTLE akan MUHAMMAD en ta b’oye mata da yawa,kan yanda ta tsara zata tafi da al’amarin…
Fatanta baya wuce tayi komai cikin ruwan sanyi kuma ba tare da an rafkota ba…

Kullum haka take juyayin lamarin da yanda komai zai kasance,tun ranar da ya sanar mata zaizo..
Dan kam zuwa wannan lokacin al’amuran har tsoro suka fara bata,bare kuma yau en da ta san komai zai faru,duk k’ok’arinta kada tayi abunda za tayi DA NA SANI…
Sai dai duk da haka ta dagewa zuciyarta kan practising da kuma hanyan da zata bi tayi solving Case en,idan ta ga yana k’ok’arin rikice mata…..

Haka duk tsayin kwanakin da ya d’iba mata wanda ita JIDDAH ta gansu ne kamar wad’anda ake jaa da K’UGIYA….

Yau en ta kama ranar SATURDAY gaba d’aya suna gida…

STORY CONTINUES BELOW

Maimakon su kasance a parlor kamar yadda suka saba,saima dad’a k’ulewa da sukayi a d’aki su biyun sun bar MAMMY da AUTARTA IKHRAM a parlor tun breakfast,suka tsere,basu ko k’ara waiwayon parlon ba….

Kowa da abunda yake,sai fira da suke jefi²,kowa da waya a hannunta,tana nata hark’allar…

  Game enta take bugawa na ”CANDY CRUSH” cikin kwanciyar hankali…
K’aran text message ya dameta..
Banza dashi tayi kamar bata jiba,zuwa can kuma kamar wacce aka tsikara tayi MINIMIZE na game en ta tafi dubawa…
Aranta dai mita take coz cikin kwanakin COMPANY sun takurata da turo sak’o…
Shi yasama yanzun sai da tayi tsaki kafin ta tafi dubawa tana mita…

Sunan da taga yayi appear ne yasa ta jin wani matsanancin fad’uwar gaba da bataji irinsaba,wanda sai da ya haddasa mata rintse idanunta….
  Sai da ta d’auki tsawon lokaci kafin ta iya k’arfin halin bud’ewa,ta soma bin alphabet en da k’yar…
Kamar mai shirin koyon had’a bak’ak’e haka ta fara binsu d’aya bayan d’aya,yahun bakinta har d’aukewa yake,saboda tsabar tsoro…..
   (ko meye dalilin ohooo)…

Da k’yar ta iya karantawa,cikin hargitsewar da bata tab’a tsammanin zata sameta ba,ba shiri ta hantsilo k’asa,lokacin da tayi arba da abunda ya fad’a,idanunta sun gama bayyana a fili tamkar zasu fad’o…

LITTLE dake kusa da ita tayi saurin kallonta tana fad’in
  ”Sisi lapia kuwa kike?ko dai da matsalane?”…
Haka ta jero mata tambayoyin da bata samu amsar suba sai nuni da tayi mata da phone en dake yashe akan bed….
Hannu ta mik’a ta d’auko ta fara dubawa…

  _Assalamu alaikum warahmatullah…_
_Gimbiyata fatan kina cikin k’oshin lafiya,idan babu wata matsala ina mai alfaharin sanar da ke k’arasowata nan da zuwa 4 Hours…._
             _BISSALAM…_

Dogon ajiyan zuciya LITTLE tayi
”Haba cweety yanzun wannan en har abunda zai tayar miki da hankali ne,bayan ranace da zata kasance miki d’aya daga cikin ranakun farin cikinmu,dan Allah ki bar damuwa akan wannan abun,bana son wani abu ya sameki,pleasee kinji durling sis”..
   Ta marairaice mata kamar zatayi kuka,hakan datayi shi ya sa JIDDAH sakin jikinta,amma da ka kalleta zaka gano irin rud’in d take ciki….

‘Daga kai tayi ta kalli wall clock en dake d’akin taga d’aya saura kwata,wata sanssanyar ajiyar zuciya tayi,ta mik’e ta shige toilet….
Alwala tayi ta dawo ta shimfid’a pray mat..
Sai da tayi nafila tukun ta mik’a kukanta ga sarkin da babu tamkarsa,kan ya kawo mata agaji bisa wannan lamari da tayiwa karan tsaye ba tare da sanin kowaba sai LITTLE….
Ta jima tana addu’ah kafin ta idar,ta ci gaba da lazimi tana k’ara neman sauk’i cikin al’amuran….

Yinin ranar tayi shi ne ba cikin nutsuwarta ba,dan ko magana bata cika yi ba gudun kar a harbo jirginta…..

*3:55pm.*
  Ya k’araso cikin gidan,horn yayi baba ya bud’e masa get en,a parlon bak’i ya yada zango,tun kafin ya k’arasa ciki ya fara kiran line nata…

Zaune take ta gama shiryawa,sai dai gaba d’aya zuwa wannan lokacin tayi losing hope,tana zaune kan stool kiransa ya shigo..
Sai da ta tattara nutsuwarta kafin ta iya d’auka,bakinta na furta kalmomin sallama…
Yayinda chest enta banda dukan Tara² babu abunda yake,jin voice ensa ya k’ara rud’ata…

Cikin wani irin yanayi ya furta
_”Ranki shi dad’e idan har anmin izini,ina son sanar dake k’arasowana…”_
Yana d’an murmushi….

Da k’yar ta had’a kalmomin
    _”U r highly wlcm”…_

Ajiye wayan sukayi,ta tsaya dube²,amma ta rasa ma me take nema,k’afanta ta d’aga da tayi mata wani mugun nauyi ta nufi closet ensu,wani rantsatstsen lace ta d’auka botter milk had’e da red colour na vail,fation jewelry’s ta d’auka wanda suma duka red ne…
Abundai ba a magana bare da ya samu farar fata sai ya hau sosai,yayi mata matuk’ar kyau…
Kamar kazan da k’wai ya fashewa a ciki haka ta jaa jiki ta zura plat shoe enta red colour tayi hanyan fita….

STORY CONTINUES BELOW

Da ido LITTLE dake waya ta rakata,kafin ta iya cewa
   ”Cweety ba ko sallama zaki tafi,tunda sahibi yazo,ni tsoro nakema kada ya k’wacemin fada dan naga take²nsa”,nan ta sa dariya…

Ita dai bata kulata ba tayi saurin ficewa daga d’akin har ta kusa riskar stair case rana jin dariyan LITTLE….

Lokacin da tazo wucewa ta parlor babu kowa shi yasa har ta fice ba ta had’u da kowaba…

Tun da ta doshi hanyan parlorn ta ji wani matsanancin fad’uwar gaba wanda ya ninka nada da take ji,dakewa take son yi amma hakan ya gagara…
Sai da tayi yak’i da zuciyanta kafin ta iya samun k’arfin gwuiwar dosar k’ofan da zai sada ta da cikin parlon..
Baya ga addu’ah da take ta faman jaa,duk wanda yazo mata shi take karantawa…

Idonta ta runtse had’e da sanya k’afanta na dama a cikin parlon tana karanta sallama….

Yana tsaye ya juyama k’ofan baya,wannan dalilin shi zai hana kayi saurin gane wanda ke tsaye…

Bayansa ta kallah tana mai k’arasowa cijin parlon,har lokacin idanunta na kansa….

  Zama tayi tana sak’a abubuwa da yawa a ranta,yayinda tunaninra ya gaza fassaruwa ga tarin tsoro da ya dad’a shigarta,kanta a k’asa tana wasa da yatsun hannunta,idanunta kuwa tamkar zasu fidda ruwa haka take jinta…

Bai juyoba,kamar yadda yak’i yin magana har lokacin tun bayan sallaman da ya amsa mata…

Sai da taga abun ba na k’are bane ta d’ago cikin murya mai cike da son yin kuka ta furta
  ”Bismillah ga gurin zama…”

  Murmushi yayi mai cike da k’warin gwuiwa,a hankali kuma ya shiga juyowa….

Ganin fuskarsa shi ya haddasa mata k’idasa rud’ewa,cikin abunda baifi k’iftawar idoba ta mik’e tsaye tana nuna shi da yatsa,cikin inda² take fad’in

   ”Ka….ka……..kaine?”……

*#Nima dai nan na shiga d’agowa dan ganin wanda JIDDAH ta gani….*

_FAN’S KUMIN AFUWA NA JINA SHIRU 2 DAYZ,BUH AN ‘DAN SAMI PROB NE,DA YASA KO ONLINE BANYI TSAYIN WA’DANNAN KWANAKI…_
_INA NAN TARE DAKU HAR KULLUM…_

*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘

[3:55PM, 4/14/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *14/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’AH YAYIN FITA DAGA GIDA.*

  _BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAH WALA-HAULA WALA-QUWWATA ILLAHBILLAH._

_ALLAHUMMA INNIY A’UZHUBIKA AN-ADILLAH,AU’UDALLAH,AU’AZILLAH,AU’UZALLAH,AU’AZLIMA,AU’UZLIMA,AU’AJHALA,AU’YUJHALA ALAYYA.._

  *ADDU’AH YAYIN SHIGA GIDA.*
  _BISMILLAHI WALAJNA,WA-BISMILLAHI KHARAJNA, WA-ALALLAHI RABBANA TAWAKKALNA._

    
       *_~#HISNUL-MUSLIM~_*
*~__________________________~*
   🎂🎂🎂 *HAPPY!*🎂🎂🎂 *HAPPY!!* 🎂🎂🎂 *BIRTHDAY TO YOU!!!* 🎂🎂🎂🎂

  *Count your nights by stars, not shadows. Count your days by smiles, not tears. On your birthday, count your age by friends, not years…*
🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻

STORY CONTINUES BELOW

  _Once again happy bufday to u_ *SAWWAMA & MARYAM IPTEEN.*
_wish u many years ahead,happy fruitful years…_
🎂🎂🎂🎂🎂🎁🎁🎁🎁🎁🎁🎁
*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 73↔74*
Wani kallo take masa mai cike da tsantsar mamaki,hannunta a sama har zuwa lokacin ta kasa sauke shi k’asa….

Wani killer smile yake jifanta da shi,hannunsa zube cikin pocket ensa…
Kad’a kansa yayi yana fad’in
    ”Yeahhh!is me”

Lokacin da ya k’araso inda take tsaye,jikinta banda rawa babu abunda yake…
Bayaga tsantsar tsoron dake tare da ita,ganin yana daf da k’arasa cike gap dake tsakaninsu yasa ta juya cikin sauri zata bar gurin….

Hannu yasa ya fizgota,a jikinsa tayi masauki,wanda hakan ba k’aramin jefasu yayi cikin wani irin yanayi da basu tab’a kasancewa ba….

Kukan da take k’ok’arin b’oyewa tun d’azun shi ne ya fito fili…
  Warm hug en da ya dad’a bata shi ya tsaida ita…
Tuni ta nemi kukan ta rasa,a haka suka ci gaba da tsaiwa har na wani lokaci…

”YAH ka cikani zan zauna ne”

Bai cikata ba har ta gama fad’an abunda zata fad’a ko ”A” bai ceba,saima tafiya da ya soma tana jikinsa…

Kan sofa ya musu masauki,ita kuma sai mutsu² take na son k’wacewa dan har lokacin tana cikin shock….

”Please YAH kada wani ya ganmu”

Murmushi yayi da ya k’ara masa kyau,ya lakace mata hanci..
”Ke kuma ga d’an karen tsoro koh”

Kai ta kad’a masa..

”Idan wani ya gani sai me? k’arshe dai maganar ta je kunnensu DADDY koh?
to nima haka nake so,ko zasu taimaka gobema su ce a d’aura aure”
Ya k’arasa teasingly…

K’afanta ta shiga bugawa a k’asa,ta cuno d’an bakinta gaba…

Hakan da tayi ba k’aramin dariya ya bashi ba,cikin magana k’asa² yake fad’in
  ”Ko dan gaba ki guji cunomin wannan bakin dan zanyi maganinki ne”

”Me za kayi?”

”Nima ban sani ba,sai dai ko da kin sake bani da damar hukuntaki yanzun,amma…….sooner”
Ya k’arasa yana murmushin mugunta….

Hak’oranta ta washe,tana fad’in
    ”Hakanma yayi dai²..”

”Me kike nufi?” ya tambaya

_”DUBAWA ZA KAYI”_
Maganan yayi escaping,dafe bakinta tayi tana kad’a kai…

Ido ya bud’e yana kallonta,hannu ya shiga tafawa,cikin salon tsokana
     ”OK bari to na duba”
Ya shiga k’ok’arin d’agota yana dariya…

”Wayyoo! YAH dan Allah kayi hak’uri baran k’ara ba”….

Ganin suna kokawa da shi,yana niyyan cire vail en dake kanta,yasa ta kwace jikinta daga nasa da gudunta ta bar kusa da shi,tana haki…

Dariya sosai ya shiga yi,wanda tunda suke tare gida d’aya bata tab’a ganinsa cikin irin wannan yayinba,abun har mamaki yake bata wai dama haka YAH BOSS en yake,amma su kullum yana wani had’e masu fuska…
Dalilin da yasa suka sa mishi YAH BOSS kenan…

Tayi nisa cikin tunaninta,har bata san lokacin da ya tashiba…
Hannunsa da ya d’ora kan cinyanta,shi ya farkar da ita daga mafarkin da take…

”Tunanin me kike haka?”

      ”Babu komai”…
Ba don ya yarda ba,ya k’yaleta,sai don bai son takurata….

Hannunsa ya kalla,nan yaga yanda lokaci yayi matuk’ar gudu..

STORY CONTINUES BELOW

”Kinga kinsa lokaci ya k’ure mana,bamu yi abunda ya kawomuba”…

”Nifa ba ruwana”…
Kafin ta k’arasa ya shiga fad’in
”To laifin waye?
  Ba ke kika mak’aleminba”…

Kamar za tayi kuka haka take kallonsa…
Murgud’a bakinta tayi,tana hararansa…

Huh!”lallai yarinya kin samu sake,ni kikema haka?
Lip ensa na k’asa ya d’an cije,Buh ba komai zanyi maganinki”…

Ko kafin ya sake yin magana,kiran sallah ya katsesa…
Shiru sukayi na wani lokaci,suna maimaita kiran sallan da sukaji…

”Muje lokacin sallah yayi,mayi maganar letter,yanzun tunda kin ganni hankalinki ya kwanta,ki daina mafarkina”…
Ya fad’a yana winking eye en sa
d’aya…

Kukan shagwab’a tasa,shi kuma ya shiga dariya,cikin sauri ta fice daga parlorn tayi cikin gida…
Bin bayanta yayi,yana murmushi…

Tana shiga parlor bata tsaya ba tayi hanyan stairs,dai² lokacin ya k’araso cikin parlon…

Sautin dariyansa da ta jiyo a bayanta,yasa ta juyo tana cuno baki
”Allah bashi kaci sai na rama”…

”Mene naji ana za a rama?”
Maganan MAMMY ta katse su…

Juyowa sukayi duka suna kallon inda maganar ta fito…

Tana zaune kan sofa tana murmushin jin dad’in ganinsu a haka…

Dawowa JIDDAH tayi,ko kafin tace wani abu,YAH BOSS ya bawa MAMMY amsa
”Kawai fa MAMMY rigimarta ce ta motsa”

”A’a fa kaga ban son haka,da gani laifin kane,tunda kace babu komai”…

Kansa ya shiga shafawa,yana murmushi…

”Dama na sani ai,kai kam ka zama BABBAN KWABO”…

Aifa dajin haka me JIDDAH za tayi inba dariyaba…

”MAMMY kinganta ko,kice ta denamin dariya”
Uwa zaiyi kuka yake kallonta,ganin har hawaye take saboda dariya…

Hakan da yayi yasa MAMMY dariya
”Maza kuzo kuga YAYANKU yana shagwab’a”
Tayi maganar dai² lokacin da IKHRAM da LITTLE suka k’araso cikin parlorn…

Ita kam LITTLE kallonsa kad’ai tayi tana tab’e baki..

IKHRAM kuwa kusa da shi taje ta zauna,tana b’ata rai,ita a dole tana tayashi….

Katse firan sukayi suka nufi yin Sallah,bayan nan suka d’ora a inda suka tsaya…

  *9:20pm*
Kowa ya k’ule a d’aki,text ne suka shiga tururuwar shigowa cikin phone en dake ajiye gefen pillow…

Dai² ta idar da sallah ta mik’e,wanka tayi,ta gama shirinta cikin nighteey enta…

Wayanta ta janyo ta shiga chat enta,cikin farin ciki da annashuwa da bata tab’a tsintar kanta a cikiba haka take chat a wannan dare…
Tarin tambayoyi da suke cikin kanta sun mata yawa,wanda take son yinsu,amma ta kasa,haka ta barma kanta abun a ranta zuwa lokacin da zata ji daga bakinsa….

LITTLE ce ta fito daga toilet,sai da ta bari ta kammala shirinta na kwanciya,sannan ta kalli JIDDAH dake ta faman murmusawa…
Har ta kwanta ta juyo tana kallonta
”Wai kam CWEETY bafa kicemin komaiba akan bak’on naki”..

A d’an kaikaice JIDDAH ta kalleta tana dariyan da ita kad’ai tasan ma’anarsa…

Uhmmm! ”kin san kuwa wani abu?”

Shiru bata ce mata komaiba,hakan da tayi yasa JIDDAN sake kallonta…

”YAH BOSS ne bak’on ba wani daban ba”….
Ai kafin ta k’arasa sai ganin LITTLE tayi a tsaye a kan bed en ta dafe chest enta da hannu,tana dad’a zare idonta…

STORY CONTINUES BELOW

Dariya sosai JIDDAH take ganin yanda LITTLE en ta firgice lokaci d’aya…
”Uhmmm! dama kin zauna dan wallahi baki ga komaiba,da kece ni kuma kiyi yaya lokacin da kika gansa a tsaye in front of u?”…

  Kamar wata marainiya haka ta zauna jagwaff a kan bed en tana tallafe kumatunta duka ta side biyu…

Ta kasa magana,ita kuma JIDDAN tana niyyan yin magana kiransa ya katseta,screen en ta nunawa LITTLE dake binta da kallo……….
*_~TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
[4:00PM, 4/16/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *16/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’AR TAFIYA MASALLACI.*

  _ALLAHUMMAJ’AL FIY K’ALBIY NURAN,WAFIY LISANIY NURAN,WAFIY SAM’IY NURAN,WAFIY BASARIY NURAN,WAMIN FAUQIY NURAN,WAMIN TAHTIY NURAN,WA-ANYAMINIY NURAN,WA-ANSHIMALIY NURAN,WAMIN AMAMIY NURAN,WAMIN KHALFIY NURAN,WAJA’AL FIY NAFSIY NURAN,WA-A’AZIMLIY NURAN,WA-AZZIMLIY NURAN,WAJA’ALLIY NURAN,WAJA’ALNIY NURAN,ALLAHUMMA A’A’DINIY NURAN,WAJA’AL FIY ASABIY NURAN,WAFIY LAHAMIY NURAN,WAFIY DAMIY NURAN,WAFIY SHA’ARIY NURAN,WAFIY BASHARIY NURAN,ALLAHUMMAJ’ALLIY NURAN FIY K’ABARIY,WA-NURAN FIY IZAMIY,WAZIDNIY NURAN,WAZIDNIY NURAN,WAZIDNIY NURAN,WAHABLIY NURAN._

           *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*

_Masoya novel en *Y’AR GARUWA* ina mai baku hak’urin jina da kukayi shiru kwana biyu,in sha Allah zan ci gaba nan da wani d’an lokaci._
*#Really luv u irin wujiga-wujiga ennan…* ❤
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 75↔76*

Da sallama ta d’auka kiran,tana murmushi…
Silalewa tayi ta kwanta,idonta a lumshe saboda wani feeling dad’i da take ji,wanda jinta take tamkar bata tab’a kasancewa a cikinsa ba iya rayuwarta…
A zuciyanta kuwa godiya take ga ubangiji da ya k’addara wannnan al’amari,fuskanta d’auke da tsantsan farin ciki….

Duk abunda take akan idon LITTLE,tun da ta tallafe kumatunta,tak’i bari su huta,haka take zaune tana jiran lokacin da zata gama…

Waya suke kamar da,yana dad’a bayyana mata asirin zuciyarsa,ita kam jinta take kamar ba a duniyar take ba…
  Wani sanyi na dad’a ratsa mata zuciya,haka suka kwashe tsawon lokaci,suna abu d’aya..
Ba dan sun soba suka hak’ura,coz dare yayi sosai,nan sukama juna sallama,uwa baza su rabuba…

Idanunta ta shiga bud’ewa da take jin sun mata nauyi…
  LITTLE dake zaune har lokacin idanunta suka sauka akai,hakan ba k’aramin tsoro ya bata ba…
Mitsikasu ta shiga yi,coz ita tayi tsammaninma tayi bacci tun da taji shiru,batayi tunanin tana zauneba still,coz tun da suka fara wayan idanun suke a rufe…

Ajiyan zuciya tayi lokacin da ta gane SISIN nata ce zaune tana waiting enta kan son jin labarin yanda aka haihu a ragaya…..

”kin san kuwa irin tsoron da kika bani,har ga Allah nayi tunanin kinyi bacci zuwa yanzun”

”Ta ina zanyi bacci banji labarin inda aka kwana ba”
Ta fad’a tana mai dad’a baza kunnuwanta ga JIDDAN…

”Ke wallahi son labarinki ne yake had’ani da ke”
tana mai hararan LITTLE take maganar..

STORY CONTINUES BELOW

Ita dai bata ce,komai ba sai dai ta zare hannayenta daga tagumin da tayi…

Haka dai JIDDAN ta bata labarin abunda ya faru daga zuwanta zuwa lokacin da taga face nasa…

Dogon ajiyar zuciya LITTLE tayi tana mai dad’a jinjina al’amarin…

”Kinga ikon Allah koh sis,ke da kina tsammanin mutum biyu,sai gashi kin tarar da duka mutum d’aya ne,gaskiya na jinjinawa YAH BOSS a wannan fagen…
Sai dai har yanzun ban daina mamakin yanda akayi ya aikata haka ba,Allah da wani ya fad’amin zaiyi haka bazan yarda ba,amma sanin ikon Allah ya wuce haka dole ne ka amince
Allah ya sa mu dace”…
Gaba d’aya suka amsa da ameen,suna masu kwanciya,kowa da tunanin da ke zuciyansa…

               *A WEEK LATER.*

Yau tsawon sati guda kenan da faruwar wannan al’amari,wata shak’uwa da soyayya wacce basu tab’a tsammanin nunawa juna ba ko da a labari,ita suke nunawa junansu..
Sai dai duk da hakan tun daga ranar suke wasan b’uya tsakaninsu..

A b’angaren JIDDAH da ta jiyo alamun zai k’araso guri take yin hanzarin barinsa..
Kasancewar a kwanakin bai cika dawowa gida da wuriba,wani lokacin har sai sun kammala dinner yake dawowa…
Wata ranar ma haka zai dawo ya tarar kowa ya shige d’akinsa..

Da safema ya sake ficewa da wuri,kasancewar yanzun suna yawan samun patients…
Sai dai duk lokacin da ya dawo afrer ya kammala abunda zaiyi suyi waya duk da a gida d’aya suke rayuwa,had’uwa ta musu k’aranci…

Yau ya kama k’arshen sati,gidan kuma tunda suka tashi sallan asuba basu zauna ba suna ta fama da aiki…

Ba su suka gama ba sai around 10:00am shima dan sun kasance su 5 suke aiki,coz MAMMY ba irin matan da suke sangarta yaransu da rashin aiki bane…

JIDDAH suka bari a k’arshen fitowa daga kitchen kowa ya tafi wanka…
Sai da ta kammala gyara kitchen en,sannan ta fito tana sauri zata d’akinsu…
  A kan hanya sukayi karo,lokacin yana sakkowa daga stairs,yana d’aura watch a tsintsiyar hannunsa…
Ita kuma tana k’ok’arin hawa,tana tafe tana duba hannunta data buge da k’ofa garin sauri…

Karo sukayi da juna,hakan yasa JIDDAH dake k’asa tayi baya zata fad’i,saurin sa hannu yayi ya tarota..
Idanunta a rufe sabida ta gama tsorata sai ta kai k’asa..

Sosai ya rik’eta uwa wacce za a k’wace masa ita,jikinta sai rawa yake saboda ta gama tsorata…
Kallonta ya shiga yi,duk da babu makeup a face enta tayi matuk’ar yi masa kyau..
Ko kuma dan ya kwana biyu bai ganta ba yasa yake ganin haka…

Jikinta ta shiga k’ok’arin k’wacewa daga garesa,amma ta kasa,saboda irin rik’on da yayi mata…

”Please YAH ka sake ni na wuce”
Kanta a k’asa take maganar

    ”Idan na k’ifa?”

Shiru tayi babu amsa,shi kuma ya ci gaba da kallonta…

Muryansa k’asa² yake magana
  ”Laifin me nayi kike b’oyemin kanki?”..

Bakinta ta cuno gaba,kome ta tuna kuma tayi murmushi…

Hakan da tayi yasa shi yin k’wafa had’e da cije lower lip nasa,yana mai gyad’a kansa…

”To ae ba laifina bane”…

  ”Hakama zaki ce ko?”
Yayi tambayan fuskansa babu alamar wasa…
Ganin bata bashi amsa ba yasake ta,take ta sake tafiya zata fad’i,coz dama a jikinsa take…

Da hannayensa duka biyu ya sake tallafota,sai da ya tabbatar ya tsaida ita sannan ya sake ta,yana shirin sauka,har ya gota inda take…
Ta furta
     ”Thanks!”…

Kamar bai jitaba ya ci gaba da tafiya…

Jingina tayi jikin bango idanunta a rufe ta lula duniyar tunani..
  K’amshin perfumes en sa masu matuk’ar dad’i da kwantarwa da mutum hankali suka cika mata hanci….

Da k’yar ta iya jaan k’afafunta ta bar gurin saboda kasalan da k’amshinsa ya saukar mata…
Haka ta shiga bedroom en,komai yinsa take cikin rashin k’warin jiki…

STORY CONTINUES BELOW

Ko a toilet da ta shiga kwanciya tayi a cikin kwamin wanka,badan komai ba sai dan dad’in da ruwan yayi mata….
Da k’yar tayi wankan ta fito,shima sai da LITTLE ta dameta da kira sannan ta fito ba don ta gaji da ruwanba…
A yaune ake sa ran zuwan iyayen FAROUK gidan dan neman auren LITTLE,bisa rakiyar shi kansa FAROUK en..
Tunda suka zo,FAROUK da LITTLE suke tare a guarding suna fira..
Har su DADDY suka gama abunda za suyi…
Kiran uncle ensa shi ya katse musu firan da suke..

”To mu zamu wuce,kai kam nasan dai ba yanzuba,ko?”
Ya tambaya yana murmushi..

Kame² FAROUK en ya shiga yi kamar mara gaskiya..
Dariya kawai UNCLE en nasa yayi,yana fad’in
   ”Ka same mu a gida”…

”To UNCLE”….

Haka suka ci gaba da firansu cikin nishad’i,da nunawa juna kulawa ta musamman…

Kwance take kan bed en abun duniya duk ya dameta,ta san ko ba a fad’a mata ba,tabbas YAH BOSS fushi yayi da ita..
Damuwa duk tayi mata tawa,ta kasa tunanin mafita…
Mik’ewa tayi ta nufi hanyan fita saga d’akin,a parlor tayi masauki..
  Haka wunin ranar ta yishi sukuku,magana ma bata samun damar yinta sosai..
  Koda MAMMY ta ga yanayinta da ta tambayeta,cewa tayi bata jin dad’i ne…

Sannu ta mata,ta kuma shaida nata ta nemi magani ta sha….

Ko da darema da za ayi Dinner bata wani ci abinci sosaiba,haka har aka gama fira kamar yadda aka saba,kowa ya fashe,sai ita da LITTLE…

Gajiya LITTLE en tayi ta bar gurin,amma itan still tana zaune,tun da YAH BOSS ya fita ko flash be had’a su ba a wunin ranar,ta san kam ba k’aramin fushi yayi da ita…
Tana wannan tunanin bacci ya d’auketa a parlon…

*********

Shigowansa kenan gidan a gajiye saboda tun bayan da suka sallami bak’in DADDY ya fita d’aurin aure daga can kuma suka wuce Dinner party,sai yanzun ya samu kansa…

Har yayi parking ya shigo cikin gidan,shiru babu motsin kowa..
Har ya wuce zai haura stairs en ya juyo ya nufi dinning,sai bayan da ya zauna kamar an ce ya d’aga kansa ya ganta kwance tana bacci…

Mik’ewa yayi ya nufi inda take,har ya zo kusa da ita yana tunanin abunda yasa take bacci ita d’aya a parlor…
Wani murmushi yayi tunowa da yanda sukayi da safe kafin ya fita…

”Allah sarki beautyna,na walar dake yau,ba komai yasa nayi miki haka ba,sai saurin da nake ban son makara”…
Yana binta da kallo yake maganar yanda babu mai ji sai wanda yake closer to him…

Kneeling yayi a gabanta,ya shiga shafa face enta…

Cikin baccinta taji ana tab’a mata fuska,cikin mayen bacci ta shiga bud’e idanunta,ganinsa a durk’ushe a gabanta yasa taji mamaki,tayi saurin mik’ewa ta zauna….

”YAH kayi hak’uri please,nasan kana fushi da ni ne”
Tana maganar kamar za tayi kuka..

Shiiiii!ya fad’a yana girgiza mata kai..

Shiru tayi tana binsa da kallo

”Ba kiyimin laifi ba”

”To amma me yasa ka manta da ni?”
Uwa wacce za tayi kuka take maganar idanunta na son zubar da hawaye…

  Kusa da ita ya zauna yana mai had’a jikinsa da nata..
     ”Don’t cry baby,
Bakiyi laifi ba,hasalima ni namiki laifin,tun da na fita ban kirakiba,
Buh!it will never been happen,ok?”…
Kai ta kad’a masa tana dad’a kwanciya a jikinsa,banda ajiyan xuciya babu abunda take…

”OK! maza tashi muje na baki abinci,nasan da wuya idan kinci”
Ya fad’a yana k’ok’arin sa hannunsa akan plat tommy enta…

Dad’a k’ank’amesa tayi ta hana shi aiwatar da abunda yake son yi…

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi yayi ya mik’ar da ita tsaye,hannunta ya jaa sukayi dinning,da kansa ya bata abincin,a cewarsa ae shi ne da alhakin kula da ita tunda shi ya jaa hakan ya faru……

Sun jima a gurin kafin suka mik’e da nufin barin gurin..
Har sunje bakin stairs ya koma,wutan ya kashe..
Duhun da ya gauraye wajen yasa ta k’ank’ame rillern stairs en…

A cikin duhun ya taho har dai² inda ya barta…
Jinsa kusa da ita tayi masa wani mugun rik’o wanda shi da kansa sai da hakan ya bashi tsoro…
  Light en Phone nasa yayi powering yana haskata duk tabi ta k’ank’amesa…

Murmushi kad’ai yayi ya d’auketa,yana tsallake steps en..

Room ensa da taga yana nufa shi yasata zaro ido waje…

”YAH me zanyi kuma a d’akinka?”

Wani killer smile yayi,cikin rad’a ya furta
”Yau ai tare zamu kwana,dama ai ni kija jira”

Ba shiri ta dire daga jikinsa,da gudu ta bar gurin ta shige d’akinsu…

Shi kuwa nan ta barshi yana kwasar dariya………..

*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[6:26PM, 4/17/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *17/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’AR SHIGA MASALLACI.*

  _A’UZHUBILLAHIL AZIYM,WABI-WAJHIHIL KHARIM,WASUL’DANIHIL-K’ADIYM,MINASH-SHAI’DANIR RAJIYM,BISMILLAHI WASSALATU WASSALAMU ALAA RASULILLAH ALLAHUMMAFTALIY ABWABA RAHMATIK…_

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 77↔78*

  Da k’yar ya tsaida dariyan da yake ya shige bedroom en…

A jikin k’ofan ta jingina bayanta tana tuna yanda sukayi da YAH BOSS yanzun,sai yanzun abun ya soma bata dariya..
  Tana ta faman zuba smiling ta nufi closet ensu..
Nighteey enta ta d’auka ta nufi toilet..

Tun kafin ta kammala abunda take ta soma jiyo kiran da ake mata a waya..
Cikin sauri tayi ta fito,ko kafin ta k’araso har ya katse..
Tsaki tayi ta d’auka phone en coz ta san mai kiran..
Tun kafin tayi wani yunk’uri, wani kiran ya sake shigowa..

‘Dauka tayi tana murmushi,tun kafin ta kai ga yin magana,maganarsa ta dakatar da ita..

”Ina kika shiga ne,ina kiranki?”…

”Ina shirin kwanciyane”…

”Ok bari na k’yaleki tunda dama nina tasheki”
  Ya fad’a yana jiran jin me zata ce..

”Uhmmm!”
Kad’ai ta iya fad’a tana bin lafiyar gadon…

Hira suke cikin nunawa juna kulawa ta musamman,suna cikin hiran ne daf da zasuyi sallama yace mata
  ”Wai d’azu me yasa kika gudu?”

Shiru tayi tana murmushi..

”Matsoraciya kawai,ni na zata jaruma zan aura,ta dinga bani jaruman y’ay’a,sai gashi na b’ige da auren matsoraciya”….

STORY CONTINUES BELOW

Dariya sosai tasa masa kafin ta bashi amsa da
”Tsoro ae halak ne”…

”Heyy!madam inji wa yace haka?bani aya ko hadith da yace haka”…

_”INNAL KHAUFI HALALUN”_

Ai tana fad’an haka suka sa dariya gaba d’ayansu,JIDDAH ko har da hawaye tsabar mugunta,kuma ta fuske kamar ba ita ta fad’a ba….
    ”Wannan dai larabcin kine”

”Ai dai nayi k’ok’ari duk da haka”….

Cike da tsokanar juna sukayi sallama…

                   _#Sabahul khair j².._
                          *********

  MAMMYN yara zauna muyi magana,DADDY ya fad’a yana kallon MAMMY da ta shigo d’akin….
  Jin hakan yasa ta nemi guri ta zauna a kusa da shi..

Ina so muyi shawara kafin wayewar gari game da yanda auren yaran nan zai kasance…
  Kwashe yanda sukayi da iyayen FAROUK yayi ya sanar da ita,sannan ya d’ora da fad’in
  “Yanzun haka mun yanke ranar auren nanda wata d’aya,saboda haka sai a fara shirye²,dan na san ku mata a kwai ku da son bidi’a,duk wani abun buk’ata sai a sanar da ni”….
  Ya fad’a yana dariya….

Addu’ah tayi na fatan alkhairi,daga haka suka ci gaba da firansu,cikin nishad’i…
     Ganin haka yasa nayo waje….

                         *********

  Kwanaki sun dad’a jaa,tun daga ranar da DADDY yama MAMMY maganar auren batayi sakaciba,dan kuwa cikin satin ta nemi mai gyaran jiki ta gaske..
Duk da suna zuna zuwa skul hakan bai hana kyan da sukayi ya bayyanaba..
Kullum sai an musu gyaran babu fashi….

Hidimar biki ya tashi ganga² kowane gefe babu zama…

DADDY da kansa ya tambayi kowa abunda yake so,haka suka zayyana masa babu b’ata lokaci…
Da kansa ya bada oder akan komai da ake buk’ata,dan cewa yayi bai yarda MAMMY ta kwashesu du bar k’asar ba..
Saboda idan ta tafi dawa zasu zauna,lokacin da ya mata maganar dariya lamarin yabata…

Tasan gaskiya ya fad’a,shi yasama bata wani damu ba da ya shaida mata ya riga ya bada order komai…
Godiya had’e da addu’ah su ta masa,na samun bud’i…

                          *********

Ranar ta yau ta kasance Jumu’ah tun bayan da aka sakko a masallaci ya dawo gida…
Wanka yayi ya gama shirinsa cikin k’ananan kaya,black nd red colour…
Sosai kayan suka amsheshi,banda k’amshi babu abunda yake zabgawa…

Dai² saitin bedroom ensu suka had’u da shi yana shirin sauka k’asa…
  Kallon juna sukayi,sukayi exchanging smile..
Har ya wuce ta,ta ce
   ”YAH anguwa za kane?”

Wani killer smile ya saki kafin ya juyo…

  ”Yeah!zance zani,kin san ku biyu za a kawomin,da wani abu ne?”

Wani takaici ne ya k’ulleta,a fusace ta juya ta shige d’akin ba tare da tace komaiba..
K’ofan ta buga da k’arfi,wanda shi da kansa sai da yaji bugun…

Kan bed ta kwanta a kan cikinta,kamar za tayi kuka,duk kuma sai taji haushin kanta kan tambayar da tayi masa…

K’aran shigowan text ya sata d’agowa tabi wayan da harara,kamar bazata duba ba,zuwa can kuma ta jaa wani tsaki,ta bud’e…

  _Ki sameni a guarding ina jiranki,amma kar a tahomin ana kumbura fuska…_

   Abunda ya rubuta kenan….

Wani sanyin dad’i ne ya ziyarceta,har bata san lokacin da tayi tsalleba…

Cikin sauri ta shirya ta had’e cikin fitted gown na wani robber yard bak’i,jan vail tayi rolling da shi,face ennan ta sha make up…
Cikin takunta mai burgewa ta fito ta nufi guarding en…

STORY CONTINUES BELOW

Tun daga tahowarta yake binta da kallo,a zuciyarsa kuwa fad’i yake
  ”Wato munyi anko kenan”…

Da sallama ta k’araso…
  Maimakon ta zauna kan seats en dake gurin sai tayi zamanta kan grasses en tana wasa da su….

Sai da ya jima yana kallonta ba tare da yace komaiba,zuwa can kuma ya sauka k’asa kusa da ita….

  Phone ensa ya fiddo daga pocket,ya shiga d’aukanta a photo…
Duk abunda yake bata saniba,shi kuma sai murmushi yake…

”D’an d’ago kiga wani abu”

Kanta ta d’aga tana kallonsa,hasken flash en da ta gani shi yasa ta gane me yake nufi…
  Murmushi ta sakeyi ta sunkuya….

Cikin salon tsokana ya kalleta yana fad’in
    ”HAYATEEY!”

Tun daga cikin brain enta har cikin fingers enta sai da kowane gab’a ya amsa….
Ido ta lumshe saboda dad’in sunan da taji ya ambata…

  ”Tashi ki rakani zancen,dama ke nake jira”

  Ko second ba a k’ara ba ta ware idanunta a kansa tana masa wani birkitaccen kallo”

Shi kuma fuskansa babu wasa yaci gaba da magana
    ”Oyaaa!tashi mana karki b’atamin lokaci”
  Ya mik’e yana gyara tsaiwansa…

Kallonsa taci gaba dayi,shi kuma ya had’e fuska kamar gaske….

Hawayen da suka fara sauka kan fuskanta,su suka sashi saurin rage tsawonsa yana fad’in
         ”Ya salaam!!!”

Rarrashinta yake amma kamar wacce ya dad’a zugawa,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru…

Shi kuwa gogan banda aikin goge mata hawayen ba abunda yake….

”Mene abun tada hankali anan HAYATEEY?idan kikace bakya sofa an gama magana,bazan k’ara ba ko da kuwa a wasane”…

Aifa jin ya fad’i haka yasa ta kuma b’are baki tana wani sabon kukan….

Kansa ya dafe yana kallonta..

Sai da ya had’ata da Allah sannan tayi shiru…
Kallonta yayi yace
”Mene kuma ya sake faruwa?”

”Ba kaineba wai kace ko da wasa ba zaka sake fad’a ba,kenanma da gaske ne maganar da ka fad’a”….
  Ta fad’a tana share k’wallan dake gefen fuskanta…

”OHHH! HAYATEEY da wasa nake ba gaske bane,bakina ne ya fad’i hakan,babu wata y’a mace da take burgeni ko zata burgeni idan ba keba”….
Ya d’an saurara yana kallonta…

Bakinta ta cuno ita nan tana fushi…
Kallonta yayi yana rik’e kunne
”Pardon please HAYATEEY,kar nayi miki kuka”…

”Kayi mana nima ae ka sani nayi”
  Tana murgud’a  baki

”Ohh!hakama za kiceba?”
Ta kad’a masa kai…

Murmushi yayi ya jingina jikinsa a nata
”Tunda so kike nayi baran yiba”…
Kamar k’aramin yaro haka yayi maganar,yanda yayi shi yasa ta dariya….

Ganin ta ware shima yaji dad’i sosai,nan kuma yaci gaba da janta da wasa da dariya har ya samu ta ware gaba d’aya….

Fira irinta masoyan da suka juk’u da begen juna ita suke,suna exchanging kalamai masu ratsa zuciyan mai sauraro,haka suka kasance tare har na wani tsayin lokaci…

                      ***********

Yau kimanin sati biyu kenan da saka ranan auren…
Wanda hakan ya rage saura sati biyu dai² kenan…

Cike parlorn na MAMMY yake da y’an kawo lefe daga tawagar gidansu FAROUK…
Kaya sunyi sosai ta inda sai d’agawa ake ana sam barka…

Bakajin komai sai maganar mata suna shewa…
  MAMMY na zaune gefe ita da MAMMAN HUBBEEY suna firansu…

STORY CONTINUES BELOW

  Haka taro ya watse,inda MAMMY ta cika su da garan kayayyaki,kowa ya tafi yana murna…………

*~#Ni da nake gefe kuwa cewa nayi wannan ai bakuga komaiba,ku jira bikin ya k’araso……..~*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER_*🤞🏻😘
[6:34PM, 4/18/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *18/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’AR SHIGA MASALLACI.*

  _A’UZHUBILLAHIL AZIYM,WABI-WAJHIHIL KHARIM,WASUL’DANIHIL-K’ADIYM,MINASH-SHAI’DANIR RAJIYM,BISMILLAHI WASSALATU WASSALAMU ALAA RASULILLAH ALLAHUMMAFTALIY ABWABA RAHMATIK…_

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 79↔80*

   Kwana biyu tsakani kayan JIDDAH suka iso wanda DADDY shi ya d’auki nauyin komai tun daga kan kayan d’aki har zuwa Lefen YAH BOSS…
Dan kuwa cewa yayi tukuicin da zai basu kenan na sashi farin cikin amincewa da hukuncinsa,ba tare da sun yi masa gardama ba…

Akwatinane masu d’an karen kyau,kowanne dank’are da kaya,dan ko rufuwa basayi…
  Kowa sai murna yake,yanda DADDY ya narka dukiya akan auren y’an lelen nasa…
Kaya sunyi kyau sai fatan zaman lafiya ga amaren da angwaye,da ma su kansu iyayen amaren da angwayen….

Lokaci na dad’a tafiya bisa shud’ewar sekonni,zuwa mintuna,hakama awanni suke biyo baya,yayinda dare ya shiga za ka tarar har sapiya tayi Daren ya tafi kenan kamar yanda yini ya wuce…

Haka ce ta kasance ga ragowar kwanakin da sukayi saura,zuwa yau ya rage sati 1,acikin satin ne kuma MAMMY ta hana su JIDDAH fita,kullum suna cikin gida,shima babu mai ganinsu sai ita sai kuma mai gyaran jikin su…

Damuwa kam YAH BOSS ya shigeta na rashin ganin HAYATEEYN nasa,sai dai kullum su kasance tare a waya kamar ba gida d’aya suke rayuwaba…..

Tun yanama MAMMY magiya ta bar shi ya ganta har ya zo ya hak’ura….

Fushi ya shiga yi da y’an gidan gaba d’aya,idan ya fita tun safe baya dawowa sai dare,shima sai ya tabbatar kowa yayi bacci,sannan zai shigo gidan…

  Kwance take har ta fara bacci k’ishi ya dameta,tun tana daurewa har dai ta ga ba abunda zata takura kanta akai bane…
Tashi tayi ta sauka,cikin kitchen ta shiga ta d’auka goran ruwa da cup,sai bayan ta sha tukun ta fito….
Wutan ta kashe ta juya zata koma,ta hango shi yana rufe k’ofan parlor…

Still tayi a wajen kamar an shukata ta kasa motsi…
Rabonta da shi tsawon kwanaki 10 kenan…

A matuk’ar gajiye yake,hakan yasa baiyi k’asa a guiwaba ya juyo da k’arfinsa…
Karaf idanunsa suka sauka akanta tana tsaye cikin kayan bacci…

Sam JIDDAH ta manta wane irin kaya ne a jikinta,shi yasa har ta ci gaba da tsaiwa…

A hankali ya ci gaba da takowa har zuwa gabanta…
Kamar a mafarki haka suka tsaya kallon juna,tamkar sababbin halitta….

STORY CONTINUES BELOW

   Sihirtaccen K’amshin da jikinta ke fitarwa,da azababben kyaun da tayi shi ya dinga fisgarsa,amma yana daurewa coz yasan shaid’an ke son shiga tsakaninsu…
Kallonta ya tsaya yi yanda tayi kyau cikin shigar baccin,kome ya tuna yayi saurin kawar da kansa yana fad’in
  ”A’uzhubillahi minash-shaid’anir rajiim”

Hakan da yayi shi ya ankarar da ita,da sauri ta kalli jikinta,idonta ta fiddo waje,kafin wani lokaci ta b’ace a gurin….

‘Dagowa yayi da niyyar mata magana sai dai ya nemeta ya rasa…

Dak’yar ya iya barin gurin saboda halin da ya tsinci kansa aciki….

  Tunda ta samu ta bar gurin bata k’ara gigin fitowaba tun daga ranan,suka koma wasan b’uya….
                        ***********

  Shirye² sun fara nisa komi ake su HUBBEEY ana kan gaba,dan ko *I.V* da yawa cikin course mate ensu ita ta basu a skul,tunda abun ya zama na zamani,wanima a phone za a turo maka kuma kaje…
  Shi yasa ma da yawa basu wani damu ba,yayin da kad’an daga cikinsu suke k’orafi,sai dai babu wanda yabiya ta kansu…..

A haka har aka soma shiga cikin satin biki…

                       ************

  Tunda kwanakin suka dad’a kusantowa,shirye²n nasu ya dad’a k’arfi,sune gurin saloon ga zaman henna da aka d’auko matar har gida…..

   Yau ya kama ALHAMIS kuma tun daga ranar aka tsara za a fara gudanar da events en bikin,in da za a fara da KAMUN AMARE…..

  *4:30pm*
    Harabar gidan dank’are take da jama’ah wad’anda aka gayyata,dama y’an ganin k’wak’waf…
  Dan kuwa akwai y’an gaiyyar sod’i wad’anda babu wanda suka sani,k’aunar zuwa ganin me akeyi ya kawo su…

   Sai a round 5:00pm amaren suka fito sanye cikin wani rantsatstsen shadda,sun sha ado…
  Gefensu kuma MAMMY ce da MAMMAN HUBBEEY sun kamosu,har mazaunin da aka tanadar musu…
  Kowa ya nemi guri ya zauna,masu gulma nayi masu sa albarka nayi…

    Can kusa² da amare na hango tawagar masoya RAYUWAR WANI,abun har mamaki ya bani,sun sha ado tun daga matan aure har zuwa kan wad’anda suke hanya,ko wacce ta basar gudun kar a raina su,kun san mutanen ba sauk’i……
Hasken flasher ke tashi ana bada selfie…

  Gaba d’aya wunin ranar haka akayi shi babu namiji,har aka k’are taron kamun,kowa kuma yayi nasa guri….

                          ********

  A washe gari kuma ranar JUMU’AH za a gudanar da dinner…

Tunda misalin k’arfe 7:00pm motocin suka fara jidar y’an mata zuwa gurin da za ayi dinner…
   Wato *JAMEYS PLAZA*  daga sama aka rubuta boldly,gurin a matuk’ar tsare yake babu zancen wani ya karewa wani,haka mutane suka zauna kowa a seat ensa…
In da *MR DJ* ya soma sakin sauti,wanda idan ba mutum ya kama kunneka ba ba yadda za ayi kaji me yake cewa….

 
     A can gida kuwa,amaren ne zaune make-up artist’s en sun dage sai fente musu fuska suke,kowacce burinta tayi abunda za ace ita tafi y’ar uwarta….
  Gefensu HUBBEEY ce cikin kwalliyarta wanda idan ba mutum yayi da gaskeba ba lallai ne ya iya ganeta ba,saboda kyaun da ta k’ara……

  Cikin weeding gown blue colour da silver en head nd shoe,,haka ma duk wani abun ado dake jikinsu ya kasance siver, sosai suka fito acikin shigar tasu kamar a sace su a gudu,shigarsu iri d’aya komai da suka saka a ranar…
  Haka aka rako su wasu daga ciki suna d’auke da k’asan rigunansu saboda yanda suke jan k’asa,har bakin motor….

  Nan ko wacce aka nuna mata inda za ta shiga…
Tsaiwa sukayi suna kallon juna,kafin sukayima juna murmushi had’e da rungume juna,sakin juna suka yi kuma suka juya a tare…

STORY CONTINUES BELOW

  Gaba d’aya wad’anda ke gurin suka sa sowa na abunda suka yi,ba k’aramin burge mutanen sukayi ba….

Har bakin motor en aka kai kowacce,tare da bud’e musu suka shiga….

  Tun daga fitowarsu har shigowarta cikin motan akan idonsa komai ya faru,sai dai kasancewar motan mai duhun glasses ba lallaine ka gane da mutum a cikiba…

Ta shigo da sallama a bakinta,kanta a k’asa ta gaida shi…

A ciki ya amsa yana wani d’auke kai…

  ”Uhmmm!miskilancin ya motsa kenan”
JIDDAH ta fad’a a zuciyarta…

‘Dauke kai tayi itama tana kallon gefenta,haka sukama juna shiru kamar basa cikin motar…

‘Barinsu LITTLE kuwa firansu suke babu damuwan komai a tare dasu,haka suke tafiya cikin nishad’i….
 
  Motor en na tsaiwa y’an matan suka fito don tarbar amare…
Haka suka jeru amare da angwaye na tsakiya sai wasu abokan FAROUK da kuma abokan aikin JABEER da suke gurin,wanda suma ba a barsu a bayaba gurin rakiyan angwaye….
  Har mazauninsu suka rakasu,sannan kowa ya nemi gurin zamansa….

Komai da akeyinsa a wannan ranar anyi shi ne bisa wayewa da kuma tsari,coz mafi yawan kaso na gurin y’an boko ne….

Lokacin ne *MC* yakema amare da angwaye barka da zuwa..
In da aka bud’e taron addu’ah,kafin kuma aka buk’aci tak’aitaccen tarihin amaren daga b’angaren babbar y’ar uwarsu kuma aminiyarsu wato *HABIBA IDREES SA’EED (HUBBEEY)*….

Cikin takun k’asaita tamkar wahainiya haka ta bayyana gaban dubban jama’ar gurin,a tak’aice ta bada tarihinsu da yanda sukayi gwagwarmayarsu taree….
   Banda tafi da maganganun mutane bakajin komai,kan yanda ta burge kowa,tana gamawa aka sa mata tafi…

  Bayan ta koma ne aka koma kan angwaye,b’angaren FAROUK kam ba shi da matsala,don kuwa yana da abokai sosai…

A bangaren YAH BOSS ne aka so a kuskure,sai dai Allah ya taimaka akwai wani friend ensa da suke aiki yanzun,wanda shi ne ya zame masa kamar amini saboda tasu tazo d’aya….

Haka akaci gaba da gudanar da taron,amare na high table,sai washe baki suke kowa na farin ciki…

  Duk da kafin zuwansu ya nuna miskilanci yanzun kam ya sake kamar ba shiba ko dan ganin yanda FAROUK suke ta fira ne yasa shima ya d’an fara sakewa….

Kamar daga sama JIDDAH ta fara jin maranta na harbawa,shiru tayi ta dafe kai,baya ga
  ”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”
Ba abunda bakinta ke furtawa…

LITTLE ta tab’o cikin rad’a take cewa
”Sis ina cikin matsala,gashi ba magani kusa,nasan tawa ta kare yau kam sai abunda hali yayiwu”…
  Kamar za tayi kuka take bata labarin…

”Me kike nufi ne?”

”Uhmmm!ke dai bari,i think menses ena ke tafe”

”Dama baki lissafa kwanakin ba ne?”

”Banda abinki muna cikin wannan season en ta ina zan iya tunawa?”
Ta bata amsa uwa za tayi kuka

”Eyyahhh!don’t mind dear anything will be fine”
  Hannunta akan kafad’anta take mata maganar…

  Uwa za tayi kuka haka ta juya,tana kallon taron jama’ar….

Haka take zaune duk jinta take cikin damuwa….

Da kad’an² ciwon ke k’aruwa wanda take dauriya tana dannewa gudun kada a gane halin da take ciki…
  Wani mahaukacin murd’a mata da yayi yasa tayi k’asan table en tana damk’e gurin idanunta a rufe gam,d’ayan hannun kuwa yana kan seat en da take ta dunk’ule shi…

Da sauri YAH BOSS ya kalleta ganin abunda takeyi…
A birkice ya shiga tambayanta

  ”HAYATEEY! are u ok?”

Tambayan da yayi mata shi ya dawo da hankalin LITTLE kansu,k’asa tabi sis en nata tana jijjigata…

  Ganin ta kwanta tana juyi a gurin, YAH BOSS a gigice ya kinkimeta ya nufi hanyar fita da ita daga gurin…
  Bayansa LITTLE tabi aka bar jama’a da tambayan meke faruwa….

A bakin motar YAH BOSS ya tsaya ya kalli LITTLE dake kuka
  ”Ki koma ciki kada kuma gurin ya zama babu kowa,shi dawa kika barshi,maza koma muma xamu dawo kinji”…
Badan ta so ba haka ta koma,shi kuma ya kwantar da ita a back seat,shima ya shiga…

  A 360 motar tasu ta bar harabar gurin,drivern na tambayansa asibitin da zasu…

”Kaimu wanda yake kusa”

Amsar da ya iya bashi kenan,hankalinsa na kan JIDDAH da gaba d’aya sai dad’a cukuikuyeshi take saboda azabar da take ji…

  Zip en rigan ya zuge,ya bud’e rigan sosai,dai² saitin maranta ya sa hannunsa yana mata massaging gurin…
  Ciwon taji yana d’an lafawa kad’an…
  Kafin su k’arasa hospital en ciwon ya dad’a k’arfi har ya so yafi na farko…

Wani irin juyi tayi a jikinsa,take kuma jikinta ya saki,ta sank’ame,tuni ta daina motsi……….😭😭😭
*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘

💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *19/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’AR FITOWA DAGA MASALLACI.*

  _BISMILLAHI WASSALATU,WASSALAMU ALAA RASULILLAH,ALLAHUMMA INNIY AS’ALUKA MIN FADHLIKA,ALLAHUMMA A’ASIMNIY MINASH-SHAI’DANIR-RAJIYM…_

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*

🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀?‍
      *MARAYUMA Y’AY’A NE.*
🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀🤹🏻‍♀

_Duk da ban kasance mutum ta farko wajen tayaku murna ba,hakan ba zaisa nayi k’asa a guiwaba gurin gabatar muku da nawa farin cikin,Allah yasa yadda kuka fara lafiya ku kammala cikin aminci da kwanciyar hankali._+

_Fatan alkhairi gareku *HALISSA ADAMOU (MY LISSA)* nd ur bestie *KHADIJA S.DOGARAI (LIPTON).*_

*~_________________________~*

  _Ina kuke manyan writer’s *RAHEEMA* nd *MOMMYN ARFAT* ina yi muku fatan alkhairi cikin abinda kuka rubuta,Allah yasa abunda kuka rubuta ya amfani al’umma,jama’ar da suka bibiyeshi kuma ina yi muku jinjina na hak’uri da juriyar ganin kun cimma k’arshen labarin,ina tayaku murnan kammala novels enku na  💘.  *UWAR MIJI* 💘  nd 😭  *RAYUWATA CE* 😭 lafiya,Allah ya baku ikon dawowa da sabo wanda yafi na baya,,,,,ameen…_

*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 81↔82*

   Addu’ah kawai yake,jin yanda jikinta ya gama saki,wani irin tashin hankali ya ziyarce shi lokaci guda..
  Kallonta yake ba tare da ya saniba wasu hawaye masu d’umi suka shiga tsere akan kyakykyawar fuskansa…
  Bayyana irin tashin hankalin da YAH BOSS ya tsinci kansa a ciki shi yasa ya manta matsayinsa na likita wanda ake da buk’atar juriyarsu…

Kamar mace haka ya zage yana ruwan hawaye…

  Ganin tafiyan na masa nisa,yasa ya d’ago a fusace ya hau fad’a wa drivern
  ”Dan Allah MALAM idan ba zaka k’ara sauriba ka fice ka ban guri”

Cikin fad’a² yake maganar wanda shi kansa drivern yayi mamaki ganin yanda ya masa masifar,tsawon shekaru yana aiki tare da su amma hakan bai tab’a faruwaba….
  Kai ya kad’a yana jinjina al’amarin,lallai kai da gani kasan ba k’aramin matsayi ke gareta ba a gurinsa…

Speed en ya k’ara kamar yanda aka umarce shi,dan gwammacewa yayi gara ya k’ara gudun da ya barshi yayi driven a cikin irin wannan halin….

Kafin cikar wasu mintinoni sai gasu tsaye bakin wani *SPECIALIST* da aka rubuta *BAREWA CLINIC* dake kan *ZARIA ROAD* a *KANON DABO*…
Basu wani b’ata lokaci ba sukayi parking…

  Kamar y’ar baby haka ya d’aukota tana kwance cikin hannunsa,ya nufi cikin hospital en da ita….
   Duk k’ok’arin NURSES akan su karb’eta hanawa yayi,sai tambayansu yayi ina ne A nd E…
  Tsayawa sukayi za su masa iskaci,a fusace idanunsa cike da masifa ya hau musu fad’a…
 
  Suna nan tsaye wani DR ya k’araso gurin har ya gota kuma ya dawo,Kallon JABEER yayi da mamaki ya furta
   DR.JABEER me ya kawoka nan yana bin hannunsa da kallo..

  NURSES en ya kalla cikin rud’ewa da yake yana aiki da hospital en,ya musu maganar ai maza a kaisu A nd E na gurin…
  Da yake sunsan waye DR. SAIF babban likita ne,yasa cikin sauri suka rakashi…
  Da harara ya rakasu,har zuwa room en…..

STORY CONTINUES BELOW

  Wasu NURSES mata daban DR SAIF ya turo su kula da lamarin JIDDAH,ko kafin su zo tuni JABEER har ya bata taimakon gaggawa,inda ya mata allurai,had’e da d’aura mata drip….

  Sai a lokacin hankalinsa ya d’an kwanta,bayan an canja mata d’aki…
  Zama yayi kan wani kujera yana kallonta,yanda take sauke numfashi peacefuly ba kamar d’azun ba….

                       *************

Can a gurin dinner kuwa hankulansu MAMMY yak’i kwanciya,tun bayan barowarsu,take k’ok’arin kiransa sai dai kiran ya k’i shiga…
  Kowa sai faman trying yake amma sam wayan yak’i tafiya…
  LITTLE kam tun dawowarta ta birkice banda kuka babu abunda take…

  MAMMY ce tayi k’arfin halin kiran DADDY ta shaida masa halin da ake ciki,hankalinsa shi kansa sai da yayi rabin tashi,take kuwa ya shiga neman line en YAH BOSS….
  Cikin sa’a kuwa wayan ya shiga sai dai har ya k’araci kiran ba a d’auka ba…

Ci gaba yayi da kira,sai da ya jima yana kira,idan ta shiga haka za ta k’araci ringing enta ta katse…

  Haka aka watse daga Dinner en,ga dangin Amarya JIDDAH da YAH BOSS kam abun bai musu dad’i ba,haka dai suka koma gidan,suna sauraron dawowarsu,duk da yanzun in sun kira wayan na shiga sai dai ba a d’auka…
  Haka suka fawwala lamarin ga ubangiji….

                       ***********

Sai da ta shafe tsawon awanni 3 tana bacci kafin ta farka…
  Bud’e idonta tayi,tana k’arewa d’akin kallo,ko ba a fad’a mataba ta san dai a asibiti suke..

Ganinsa kusa da ita kansa a kife wanda hakan da yayi bazai bawa mutum damar ganin fuskansa ba,da gani kasan ko dai mutum na cikin tsananin tashin hankali,wanda ya sa yayi hakan ko kuma bacci ya d’an d’aukeshi bai sani ba…

Batayi tunanin idon sa biyu ba,shi yasa ma tayi k’ok’arin d’ora hannunta tana shafa suman dake kansa…

  Har lokacin yana zaune closer da gadon,kansa na kusa da gefen cikinta…

  Bai san ta farka ba,sai da yaji lallausan hannunta yana zagaye akansa..
Cikin sauri ya d’ago,ganin idanunta a bud’e kuma a kansa yasa ya damk’e hannunta gam,kamar zai had’esu da nasa..

Murmushi ta masa,tana k’oka’rin mik’ewa,Dakatar da ita yayi ya shiga k’ok’arin rabata da gadon…

Da sauri ta dire k’afafunta a k’asa ta mik’e da kanta…
  Ji tayi abu na bin k’afafunta da sauri kamar ana tsiyaya mata ruwa..
  Ko bata tambaya ba tasan mene ne,take ta durk’eshe a gurin ta fara aikin ruwan hawaye…
  ‘Dagota yayi,yana shirin tambayanta yaga jini ya d’an taru a inda ta tsuguna..
Kansa ya dafe a hankali ya furta
     ”Ohh!ya Allah”

  Sakinta yayi ya shiga toilet en,ya had’a mata ruwa,dawowa yayi bai tsaya b’ata lokaciba ya nad’e hannun rigansa,ya rabata da gurin,sai da ya shiga da ita toilet en sannan ya direta,yana fad’in
   ”Kiyi wankan bari na dawo yanzun”

  Har da zai bama Drivern sak’o sai kuma ya fasa..
Nurse yasa a tura mata da zasu zauna kafin ya dawo,duk da ba wai nisa zaiyiba…

  Key en ya karb’a ya fice,baiyi wata tafiya mai nisa ba ya riski *SAMMANIN FATIHU MALL* da yake duk a kan titi d’aya suke..

Tunani ya shiga yi na abunda zai siyama,kallon kansa yayi,sai a lokacin ya kula da yanda jini ya b’ata masa kayan jikinsa…
Take kuma ya gano dalilin da ya sa mutane ke binsa da kallo tun da ya shiga MALL en…
Girar sama da ta k’asa ya tamke ya sha mazu a bunsa…

  Wucewa yayi ya d’auka abunda zai d’auka,cikin basket…
Can daga b’angaren *BOTIQUE*  ya nufa ya zab’a mata wani dogon riga pink colour,shima ya d’auka one set..
Ya nufi kan counter,lissafi suka masa ya biyasu,ya d’ebi kayan ya sauka k’asa harabar da yayi parking..
A seat en gefensa ya ajiye,hasken da  yaga phone nasa yayi dake zube a baya, ya mik’a hannu ya d’auka…
  Dai² lokacin da kiran ya katse coz dama wayan a silent yake…

STORY CONTINUES BELOW

  ‘Daukan phone en yayi domin duba wanda ya kiran,missed calls ne rututu daga DADDY da sauran y’an gidan…
  Saurin bin kiran yayi,tana shiga DADDY yayi saurin amsawa
  ”Hello!JABEER kuna ina ne yanzun?tun d’azun muke ta k’ok’arin kiranku amma ba a d’auka”…

”Ehhh!DAD muna *BAREWA CLINIC* ,buh yanzun muma zamu taho dan yanzun haka jikin da sauk’i”….

”Ka ga idan jikin bai dai²ta ba kada ka b’oyemin,ka bari zuwa da safe sai a sallameta,gudun tashin ciwon”…

”No DAD da sauk’i sosai”

”To shi kenan sai kun dawo Allah ya k’ara afuwa”

”Ina ita JIDDAN?”

”Na d’an fita ne,bama tare amma yanzun zan koma”

”Ok toh Allah yasa kaffara ne”..
DADDYN ya fad’a yana hanging kiran…

  Sai da ya sauke dogon ajiyan zuciya kafin ya jaa motan yayi gaba,tafiya kad’an ta kawo shi hospital en…
  Parking yayi ya kwashi kayan zuwa ciki…

”Room en an gyara shi,sai k’amshi yake..
  ‘Dakin ya k’arewa kallo kafin ya kira sunanta…
       ”HAYATEEY!”

  Tana daga cikin toilet en tayi masa magana
  ”YAH ganifa a toilet”

”Ok dama kayan na kawo miki”

Kasa magana tayi,tana tsaye sai juya hannaye take tunaninta yanda za ta karb’i kayan…

Jin shiru yasa ya sake fad’in
  ”HAYATEEY kina jina kuwa?”

”Eh!in….in..a….ina jinka…..”

Tana magana sai hard’ewa kalmomin suke..

”Ok toh maza bud’e ki karb’a,kinga zamu wuce gida yanzun BABA na jiranmu a waje”….

  ”Toh bani amma ka rufe idonka,pleassseeee”…
Tayi maganan tana cizon d’an yatsanta…
  Shi kam dariyama maganarta ta bashi…

  Kad’an ta d’an bud’e k’ofan,sai da ta lek’a taga ya d’an juya baya,tace
    ”Bani toh”
Tana mik’a masa hannunta…

  Mik’a mata yayi idanunsa a kulle amar yadda ta buk’ata,da sauri ta maida k’ofan ta rufe,bata wani jima ba ta fito tayi kanta a k’asa,ta nemi guri ta zauna…

Sai da yayi dariya mai sauti sannan ya d’auka nasa kayan ya shiga toilet en,ruwa ya watsa,then kuma ya shirya ya fito…
Ta had’a kayan guri d’aya,yana fitowa ya kalleta..

”Oya taso na d’aukeki mu tafi”

Wani kallo ta masa tana mak’e kafad’a,wani murmushi yayi ya ci gaba da matsowa inda take…

”Yarinya daga baya kenan,da dakika mak’alemun baki san da haka ba sai yanzu?
  Maza taso ni mu wuce,dare na dad’a yi,yana mik’a mata hannu”…

Bata k’i amsan hannun nasa ba,tayi saurin d’ora nata akan nasa,coz tana jin k’afanta sun rik’e,ya ko rik’eta gam,suka fice…
  After anyi discharging nasu,suka dauki hanyan gida…..

*_#UHMMM!naji dad’in yanda kuke nuna kulawa akan wannan novel Allah ya bar k’auna…_*

*_~#D WAY U DROP UR COMMENTS, IS D WAY THAT I ADD MORE TYPING…~_*
*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[5:26AM, 4/21/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

STORY CONTINUES BELOW

*©® 2018.*
      *19/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’O’IN KIRAN SALLAH.*

  _IDAN MUSULMI YAJI ANA KIRAN SALLAH,ZAI DINGA MAIMAITA ABUNDA YAJI ANA FA’DA,SAI DAI BANDA *HAYYA ALAS-SALAH* DA *HAYYA ALAL FALAAH*,ZAI CE *LAA-HAULA WALA K’UWWATA ILLA BILLAH*._

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*

  _My sisi *KHADIJA SALIHU* ina tayaki murnar fara sabon novel enki,Allah yasa yanda kika fara lafiya ki gama lafiya,Allah yasa jama’a su amfana da sak’on da ke cikinsa._

*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 83↔84*

Cikin wani irin yanayi da ita kad’ai tasan dauriyar da take wajen tafiya,haka ta hak’ura take take k’afafuntan,har suka k’arasa shiga parlor…

Cike parlorn yake da jama’a y’an biki,kowa na jiran ganin dawowarsu..
Suna shigowa kuwa akayi caaa a kansu sai sannu akema amarya..

Wata abokiyar wasan su YAH BOSS ce ta matsa kusa da shi tana fad’in
”Ango tunda amarya ba lafiya mai zai hana a d’aga sai ta samu lafiya”..
Ai ko kafin ta k’arasa tuni YAH BOSS ya d’ago yana jifanta da wata uwar harara,take kuwa mutanen gurin suka fashe da dariya”…

Tashi yayi ya nufi sama ba shiri,dan shi irin wad’annan wasannin ba wani burgeshi suke ba,shi yasa ma baya wani sakin fuska ayisu da shi..

Da k’yar MAMMY ta kori kowa daga parlorn coz dama dare yayi,haka suka fashe,kowa ya nemi makwancinsa…

  Hannun JIDDAH ta kama suka nufi d’aki,ta zaunar da ita,da kanta ta had’o mata abinci,ta sata a gaba sai da ta ci sosai duk da yadda take yatsina fuska kamar mai had’iyan magani haka MAMMYN ke kallonta fuskanta babu alamar wasa har sai da tace ya isheta,sannan ta d’auka kayan tayi waje tana mata sannu had’e da sai da safe…

                        **********
Da misalin k’arfe 11:00am Dank’am bakin MASALLACIN na *USMAN BIN AFFAN* dake k’ofar gadon k’aya yake saboda dubban jama’ar da suka halacci d’aurin auren..
Ko ina ka duba dan adam ne,sai hasken tufafi dake haske idanun al’ummah saboda yawanci fareren kaya ne da kuma kaloli masu haske a jikinsu…

Wasu motor da suka zo gurin a lokacin,su jama’ah suka fara bi da kallo..
Haka aka bud’e motor en,fitowa yayi sanye cikin wani d’anyen boyel wanda da gani babu tambaya kasan naira tayi kuka,kalarsa light green,yayin da aka masa aiki da army green,yayi masifar kyau acikin kayan,nan wasu ke fad’in
  ”Ango FAROUK kenan,d’ayan bai k’araso ba?”…
Ko kafin su k’arasa,sai ganin wata motor en sukayi da ta wuce ta farko a kyau da tsaruwa,tayi parking a gabansu,nan suka bi moter da kallo,basu gama tsinkew da lamarinba sai da suka ga ya fito,cikin shiga irinta FAROUK

   ”Kamar had’in baki”

Inji wasu dake gefe..
Nima kuwa na basu amsa da cewa ”ai wannan yafi had’in baki,dan kuwa sai kunga amaren tukun”…

Taro yayi taro inda ba a wani d’auki dogon lokaci ba,bayan k’arasowar angwaye aka soma d’aurin auren…
  Auren YAH BOSS da JIDDAH aka fara in da aka d’aura akan mafi k’arancin sadaki,dan DADDY dagewa yayi akan ba k’arya yake soba shi albarka yake nema,after kuma aka d’aura na LITTLE da FAROUK,d’aurin auren da ya samu halartar manyan mutane,daga b’angaren DADDY dama ABBAN FAROUK coz shima babban mutum ne da aka san shi…

STORY CONTINUES BELOW

                           ********

  A gida kuwa tun wayewar garin ake fama da JIDDAH,dan tun safe take aikin kuka,rarrashin duniya tak’i yin shiru,har kowa ya hak’ura ya zuba mata ido…

Y’an d’aurin aure na fara dawowa,aka soma neman YAH BOSS dan sun san shi ne remote control nata..

Sam an neme shi an sarasa cikin jama’ar da suke dawowa,wasu y’an kai tsegumi aka samu suka kirashi,cikin abinda bai fi minti 5 ba ya bayyana a gidan,mutane sai tsiya suke masa,shi kuwa gogan ya toshe kunnuwansa…
  Haka yaita ratsawa ta cikin jama’ah har bedroom ensu,a can kan gado ya hangota ta k’udundune,kanta a cikin cinyoyinta tana ta faman kuka…………
*#KUYI HAK’URI DA WANNAN,UZURI YASA BANYI TYPING DA WURIBA,IN SHA ALLAH ZAMU HA’DU A NEXT PAGE…*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[3:40AM, 4/22/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                    🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *21/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’O’IN KIRAN SALLAH.*

  _IDAN MUSULMI YAJI ANA KIRAN SALLAH,ZAI DINGA MAIMAITA ABUNDA YAJI ANA FA’DA,SAI DAI BANDA *HAYYA ALAS-SALAH* DA *HAYYA ALAL FALAAH*,ZAI CE *LAA-HAULA WALA K’UWWATA ILLA BILLAH*._

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 85↔86*

  Babban rigansa a hannu,sai kayan ciki kad’ai,dafa kanta yayi wanda k’amshinsa ya sanar da ita ko waye a kusa da ita,ta kasa d’agowa ta kalleshi kamar yadda kukanta ya k’i tsayawa…
  Kan neck nata ya tab’a wanda ya matuk’ar d’aukan zafi,uwa ana kara mata wuta saboda har wani huci jikintan yake yi…
Ciki² ya furta
    ”Ya salaam!”
Fuskarsa na nuna damuwa,d’ago kanta yayi yana bin kumburarrun idanunta da kallo,hatta da ita kanta fuskan ta canja yanayi…

Hawaye ya shiga goge mata da handkeey yanda take kallonsa yasa ya kad’a mata kai,alaman baya son kukan…
Shiru tayi sai ajiyan zuciya da take saki akai²…

  Waya ya d’auka,kiran farko ta d’aga..
  ”Had’omin abinci ki kuma tahomin da magani,ina d’akinku”
Yana gama bada umarnin ya kashe,ba tare da ya jira jin me zata ceba…
Bata jimaba tayi nocking,har lokacin bai zauna ba,sakinta yayi ya nufi k’ofan,kad’an ya bud’e ya amshi sak’on ya mai da k’ofan ya kulle…

Ajiyewa yayi kan bedside drawer,ya shiga nad’e hannun rigansa..
Ita kam baiwar Allah JIDDAH yana sakinta ta sake kwanciya,tana juya masa baya,wasu hawayen suka ci gaba da sakkowa akan pillow en da tayi matashi da shi…

Toilet ya shiga,a wani k’aramin container ya zuba ruwa,fitowa yayi ya duba cikin closet ensu,wani k’aramin towel ya d’auka,a kusa da ita ya ajiye kayan inda ya sauke tray en abincin,ya kuma maye gurbin da container da ta kawo na ruwa…

‘Dagata yayi ta zauna,sai k’ok’arin dad’a zamewa da taci gaba da yi,bai bari ta kai ga kwanciyan ba ya jinginata jikinsa,yana zare zip en riganta,sai da ya rabata da shi,ya rage mata daga ita sai inners,towel en yasa a ruwan ya shiga matsewa yana goge mata jikinta..
Har sai da ya tabbata jikintan ya d’an saki kafin ya k’yaleta,ya janyo trayn,yana k’ok’arin bata abinci tana kauda kai,wani kallo da ya watsa mata shi yasa tayi saurin bud’e bakin,a hankali yake bata tana ci,kad’an taci lokacin da taji tana yunk’urin zata dawo da shi,haka nan ya barta ya bata maganin had’e da ruwa…

STORY CONTINUES BELOW

Tattara kayan ya shiga yi ya jinginata jikin pillow,yana jaa mata duvet en,rigansa da hula ya d’auka ya fita yana rufe mata k’ofa,komai da yayi k’ok’ari kad’ai yake coz ya Riga ya fad’a wani hali,har ya shigo ya fita baya ga wayan da yayi bai ambaci ko da ”A” ba ne haka ya fita ya barta..
Tana ganin ya fita ta silale ta sake kwanciya,kanta kuwa banda sara mata babu abunda yake kamar zai fashe haka ta dafe shi, hawayen na dad’a tsiyayowa ta gefen idanta,daga haka wani wahalallen bacci ya d’auketa…

                           ********

Gurin reception da yawa suka wuce,shima dalilin wayan da aka masa ne yasa ya dawo gidan..
  A can *NI’IMA GUEST PALACE* ya tarar dasu,mutane sai hidima suke,sun ci sun sha,daga nan kuma bak’i suka shiga yi musu sallama masu haramar barin garin nayi,haka suka fara sallama da angwaye cike da fatan alkhairi aka soma watsewa,DADDY kuwa tuni ya bar gurin…
Haka aka bar angwaye da manyan abokansu,suna fira cike da nishad’i da zolayar juna..

Shiru yayi ya zubawa guri d’aya ido,ko tunanin me yake??

FAROUK da ya ankara da yanayinsa shi ya dawo kusa da shi yana tab’a shi…
”Ya dai BIG BROSS kayi shiru?”

”Bar d’an air,tunanin anjima yake”…
  Fad’in wani abokin aikinsa kenan,gaba d’aya kuwa suka sa dariya,banda shi YAH BOSS da ya dad’a d’aure fuska,shi a dole baison raini…

A cikin zuciyarsa yake ayyana
”Yanzun ko wane hali take ciki?ta tashi daga baccin ko kuwa,ta ci abinci ko bata ciba?”

Tambayoyin da suka dameshi kenan,ganin bazai iya jurewa ba,yasa ya kira LITTLE dake tsakiyar jama’a anata hoto da ita..
Da sauri ta bar cikin hayaniyan,wasu na tsokanarta suke fad’in
  ”Dan gulma shi ne har da barin gurin”

Ita dai bata tanka musu ba tayi hanyan da babu jama’a sosai,tana d’aukan kiran yayi wani siririn ajiyan zuciya,kafin ya fara tambayanta jikin JIDDAH…

”Da sauk’i sai dai bata tashi ba har yanzun”

  ”OK!”
Kad’ai yace,can kuma ya ce
  ”Idan ta tashi ki kirani”

Daga haka ya datse kiran…..

                         **********

Zaune suke gaban DADDY su uku YAH BOSS,JIDDAH da kuma LITTLE kowacce kanta a k’asa banda kuka babu abunda sukeyi,nasiha yake musu mai ratsa zuciya wanda shi kansa YAH BOSS en kana kallon yadda idanunsa suka canja zaka san nasihan ta ratsa shi,yana gamawa MAMMY ta d’ora da nata,sai da ta musu nasiha sosai ta kuma tsoratar dasu kan sab’awa miji,kafin ta musu fatan alkhairi da zaman lafiya…

  Tana matse k’wallan da ya tarun mata a gefen fuskanta,sallamansu DADDY yayi,nan suka tashi jiki babu k’wari suna rusar kuka,kusa da k’afan DADDY suka durk’ushe kowacce ta d’ora kanta akan k’afarsa sai kuka suke da k’yar DADDY ya sa a zo a tafi da su,nan suka koma gurin MAMMY sun k’ank’ameta suna kuka,haka itama ta rik’esu,nan kuwa kukanta ya bayyana su sunayi itama tana yi…
Da k’yar aka rabasu,hska aka sauko da su,ko wacce aka nufi moter da ita a moter d’aya aka sasu,har lokacin suna faman abu d’aya,sai da aka fara kai JIDDAH,aiko sun kama juna k’am suka rik’e,IKHRAM dake rawar kan rakiya,ta shiga tsakaninsu haka suka rungumeta suna kuka tana yi,HUBBEEY na gefe itama tana matsar hawaye,nanma sai da k’yar aka b’anb’are su a jikin juna,jama’a da dama sai da sukayi musu kuka ganin yanda suka zama abin tausayi,haka aka barota ita d’aya,da wayo da komai, suka nufi gidan LITTLE da yake cikin unguwa d’aya ne duk RIJIYAR ZAKI ne,sai dai banbancin line…

  An baro amare a gidajensu sai kuma addu’an fatan alkhairi,da zaman lafiya,bak’i kuma Allah ya huta gajiya…

                         ***********

  Gidan shiru sai ita kad’ai,tana ta faman kukanta,tana jin tsaiwan motoci,sai dai bata ji shigowansa ba,saman gadon ya hauro,hannayensa a saman sholders enta ya juyota suna fuskantar juna…
Da farko ta so ta tsorata sai dai ganin shi ne yasa ta fad’a kan wider chest ensa ta kwantar da kanta hawaye na ci gaba da biyo fuskanta…
‘Dagota yayi yana girgiza mata kai
”Kin san nafi kowa jin b’acin rai a duk lokacin da zanga hawaye a kan fuskarki,ko kuwa kina so raina ya b’aci ne?”

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri ta shiga kad’a masa kai,tana goge fuskan da hannayenta.
Murmushi yayi mata yana sumbatan porehed enta…
Hannunta ya kama ya jaa zuwa parlor yana fad’in
  ”Muje ku gaisa da bak’i,kukan kuma ya isa haka,kada rashin lafiya ya kamamin ke”

Da sauri ta kalleshi,shi kuma ya kad’a mata kai,kanta a k’asa har suka isa parlor bata yarda ta d’agoba…

Haka suka gaisa,sai tsokanarta suke,ita dai bata iya cewa komaiba,saima dad’a duk’ar da kanta da tayi,har suka k’ara ci zancensu suka musu fatan alkhairi da addu’an zaman lafiya,daga haka suka mik’e da niyyar tafiya..
Har lokacin kanta na k’asa tana zaune kusa da YAH BOSS…

”To amarya mu zamu wuce duk da dai rowar fuskan ake mana,sai wata rana idan mun sake kawo ziyara”..
Fad’in wani mai surutun tsiya kenan…

YAH BOSS dake zaune ko tari baiba,saima tab’e baki da yayi,mik’ewa yayi ya rakasu,sukayi masa sallama suka d’auki hanya,sai da ya rufe ko ina sannan ya dawo,a inda ya barta a nan ya taddata,hannunta ya jaa ya kaita har d’akinta sannan ya fice..

Bayansa tabi da kallo tana sauke ajiyan zuciya a hankali…
Kayan jikinta ta shiga ragewa,wanka tayi ta saka kayan baccin da ta gani cikin closet en dake d’akin,ta feshe jikinta da sihirtattun turarukan da MAMMY ta had’a musu,light en d’akin ta rage,tana kwanciya ta ja duvet en ta rufe jikinta,bata jima da kwanciya ba ta shigo tana kallon shigowansa tayi saurin rufe idanunta…
Hasken ya kunna,kwance ya ganta,ta k’udundune cikin duvet,murmushi yayi ya kashe..
Tana jinsa ya hauro kan bed en,nanfa k’irjinta ya soma dukan d’ari..
Janyota yayi ya had’e su guri d’aya,yanda yaji jikinta na rawa ya tabbata ba bacci takeba,aikuwa tsoronta ya dad’a bayyana…
A kunne ya shiga fad’a mata wasu maganganu masu dad’i,wanda yasa tuni jikinta ya saki,alaman dake nuna tayi bacci kenan..
Fuskanta ya lek’a ganin tana sakin numfashi a hankali yasa ya tabbatar da tayi bacci…

                         **********

*GIDAN FAROUK*

  Kukan da LITTLE keyi shi ya tabbatarmin da mai afkuwa ta faru…
Su FAROUK an zage sai rarrashi yake,amma kamar zugatama yake..
Kwance take a jikinsa,tana ta fanan zuba shagwab’a…

Lallab’ata yayi da k’yar,ya kwantar da ita ya nufi toilet,ruwa ya tara bayan yayi wanka,ya dawo ya d’auketa,a cikin ruwan ya sata,matar da ta fara bacci bata san lokacin da ta mik’eba tana shirin fita jin yadda ruwan zafi ya ratsata,haka ya maida ta,kukan da ya tafi ne ya dawo,da k’yar ya samu yayi mata wanka sai raki take masa..

Dawo da ita yayi ya kwantar da ita kan jikinsa yana sa mata albarka,ita kuwa tana jinsa,haka bacci ya d’auketa,cike da farin ciki mara misaltuwa yayi bacci cikin nutsuwa da bai tab’a samun kansa a ciki ba…

                          *********

*GIDAN MAMMY*

  Tun da aka fita dasu MAMMY ke zubda hawaye,DADDY ke ta bata hak’uri amma tak’i dainawa,ganin abun nata ba na k’are bane yasa ya kalleta yana fad’in
”Tashi ki d’auko mayafi saiki kaisu da kanki”…

Jin furucinsa shi yasa tayi saurin tsaida kukan nata,tana mai mik’ewa ta bar gurin babu shiri…

Murmushi ta saki irin nasu na manya yana girgiza kai….

                         *********

Ko da asubah shi kad’ai ya tashi,ya jima yana musu addu’ar samun zaman lafiya da fuskantar juna,kafin ya wuce masallaci…

Da ya dawo ma,jallabiyan jikinsa ya rage,ya sake kwanciya yana rungume da ita a cikin jikinsa…

Da safe ta rigashi tashi,hakan yasa ta zare jikinta daga nasa,d’an nesa da shi ta zauna ta buga tagumi,nan ta shiga aikin kallonsa kamar an dasa mata T.V,ganin yana motsi yasa tayi saurin zura k’afanta a k’asa za ta tashi,da sauri ya fizgota ta fad’o kan jikinsa…
Ita abunma tsoro ya bata,idanunsa har lokacin a kulle,ya ratsa hannayensa ta saman cikinta…
  Batayi tunanin idanunsa biyuba,sai jin maganarsa tayi cikin kunnenta a hankali…

STORY CONTINUES BELOW

”Kallon me kikemin,kamar wacce take cinema?”

Kunya kalamansa suka bata,ta dad’a kulle idanunta,tana d’ora hannayenta a kansu…

”Ko kinyi tunanin ban ga tashinki ba,duk abunda kike ina kallonkifa”

Dad’a k’ank’ameshi tayi,tana jin kamar k’asa ta bud’e ta shige…

”Oya! tashi muje muyi wanka,kada bak’i su zo,suganmu haka”…

K’in tashi tayi shi kuma ya d’agata ya nufi toilet da ita,ganin da gaske yake,ta hau bashi hak’uri

”Dan Allah YAH kayi hak’uri ka fita,zanyi da kaina”…

”Uhmm!lallaima yarinya zaki ga na fita,ba indafa zani,idanma zaki daina wannan kunyar ki daina”

Tsaiwa tayi tana kallon ikon Allah,fir YAH BOSS yak’i fita,idanunta ta kulle…………

  *A YAU NE ABBANA YA CIKA KWANAKI 40 DA RASUWA,INA BUK’ATAR DAN ALLAH DUK WANDA YA KARANTA POSTING ENA NA YAU YA SANYA SHI  CIKIN ADDU’AH DAN ALLAH..ALLAH YA MASA RAHAMA TARE DA ‘DAUKACIN AL’UMMAR MUSULMI DA SUKA RIGAMU CIKAWA,ALLAH YA KYAUTATA K’ARSHENMU…AMEEN…*

*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[11:05PM, 4/22/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_

                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *22/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

*ADDU’AH BAYAN GAMA KIRAN SALLAH.*

  _A LOKACIN DA LADANIN YAYI KALMAR SHAHADA SAI MAI SAURARO YACE:-_

  _WA-ANA ASH-HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH,WAHDAHU LAA SHARIKALAH,WA-ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA-RASULUH,RADHIYTU BILLAHI RABBAN WABI MUHAMMADIN RASULAN WA-BIL ISLAMA DIYNAN.._

*BAYAN YA GAMA SAI YAYI SALATI GA ANNABI (S.A.W),SANNAN YA ‘DORA DA FA’DIN…*

_ALLAHUMMA RABBA HAZIHID-DA’AWATITTAAMMAH,WAS-SALATUL K’A’IMA ATIY MUHAMMADANUL WASILATA WAL-FADHIYLAH,WAB’ASHU MAK’AMAN MAHMUDANIL-LAZIY WA’ADTTAH,INNAKA LA TUKHLIFUL MIY’AD.._

*DAGA NAN KUMA SAI MUTUM YAYIWA KANSA ADDU’AH,DOMIN YIN ADDU’AH TSAKANIN KIRAN SALLAH DA IK’AMA KARB’AB’B’IYA CE..*

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 87↔88*

Tsaiwa tayi idanunta a kulle tana tunanin mafita…
Jin shiru yasa tayi k’ok’arin bud’e idanunta cikin dabara
Ganinsa tayi ya juya mata baya, cikin sand’a ta nufi k’ofa,ta taki sa’a kuwa k’ofan a bud’e take,itama kuwa bata yi k’asa a guiwa ba ta bud’e ta fice,tana fita ta kulle ta waje gudun kadama ya fito…

Zama tayi a saman bed tana dariya sama²….

Duk abunda tayi baiga lokacin da tayi yunk’urin guduwa ba,sai k’aran kulle k’ofa da ya katseshi, cikin sauri ya juya,sai dai gurin da ya direta wayam babu kowa….
Kai ya girgiza yana murmushi,haka yayi wankan har ya gama,towel ya d’aura da kuma k’arami a hannunsa yana goge jikinsa,ya nufi k’ofan..
Handle en ya shiga murd’awa,jin tak’i bud’ewa yasa shi fad’in
  ”HAYATEEY!oya bud’emin na fito”

STORY CONTINUES BELOW

Wani tsoro ne ya ziyarceta tana zaune,kamar mara gaskiya ta shiga raba idanu,sam ta kasa tashi,shi kuma sai magana yake mata…
Can kuma ko me ta tuna,ta mik’e cikin sauri ta bud’e,tana gama murza key en ta juya zata bar gurin..
K’afa ya sa mata wanda sanadiyyar hakan ta tafi zata fad’i,cikin wata razananniyar murya ta saki wani d’an marayan ihu….

Hannu yasa ya fizgota,wanda hakan da yayi shi ya dad’a rud’ata,cikin wani irin yanayi ta damk’esa gam,kamar wacce take tunanin za a kwace mata shi…

Kuka tasa masa,tana bugun k’irjinsa,shi kuwa da farko dariya ya soma mata,kukan da ta soma yi masa ne yasa shi fara rarrashinta,cikin hikima ya kaita har tsakiyan toilet,bai jira ta sake yunk’urin guduba,ya sata cikin kwamin wankan da ya cika shi da ruwa…
Runtse idanunta tayi,a tunaninta ya fita,saijin hannunsa tayi a jikinta yana k’ok’arin rabata da kayan jikinta…

Wani ihuu ta sa masa,shi kam ko ta kanta bai biba,ya cigaba da abunda yake ba tare da ya saurara mataba,haka ta ci gaba da kukanta,ko ladan rarrashi bata samuba sai da ya kammala zaresu tsaf…

Bayyanar jikinta waje,shi ya haddasa masa had’iyan miyau,yana bin gaba d’ayan jikinta da kallo,jin shirun da tayi shiya haddasa masa bud’e ido a tunanin tama ya fita ne,sai dai me tana bud’ewa taga ya kafawa na……ido ko k’iftawa baiyi..

Da sauri tasa hannu tana rufewa,had’e da dad’a kulle idanunta tana masa ihuu..
Gajeran murmushi yayi ya kama hannayenta yana k’ok’arin bud’ewa,ita kuma tana dad’a kare abunta,kokawa sosai suke acikin toilet…
Hakane yasa ya zare towel en jikinsa,ya koma cikin kwamin wankan..
Tana jin ya shiga ta mik’e zata bar gurin,da sauri ya dawo da ita,a jikinsa ya kwantar da ita…
Cikin kunnenta yake mata magana k’asa²…

  ”Please HAYATEEY me kike son aikatawa,kina son b’atamin rai ne?”

Da sauri ta girgiza masa kai

”Ok!idan bakya so raina ya b’aci ki tsaya haka kinji”

Gaba d’aya jikinta rawa yake,amma haka ta shiga girgiza masa kai

  Wani murmushin ya sake yi,wanda ban san me hakan ke nufiba…

Jikinta ya soma bi yana shanshanawa,tun daga wuyanta ya soma sakin mata wasu zafafan kisses,har ya gangaro kan fuskanta…….

Kamar an dasata haka ta zama,shi kad’ai yake kid’ansa kuma shi yake rawar,sai dai ya juyata,ta zame masa kamar mutum-mutimi…

Ko me ta tuna kuma tayi saurin zare bakinta a nasa,kallonta ya shiga yi da idanunsa da suka soma canza launi..

  ”Pardon please YAH” tana had’e hannayenta,idanunta har lokacin a kulle…

Jikinsa ya wanke ya fita daga toilet en gaba d’aya…

Kuka tasa a toilet en,ko ba a fad’a mata ba yayi fushi ne,haka ta k’ara ci kukanta tayi wankan ta fito jiki babu k’wari…

Ko da ta fito bata tarar da shi a d’akin ba,haka ta zauna a kan tsool ta buga tagumi,da k’yar ta shirya ta fito parlor..
Nan ta tarar da shi kwance kan sofa,idanunsa a kulle,kusa da k’afarsa ta zauna kafin ta soma magana

”YAH kayi hak’uri please”….

Bai tanka mata ba,har ta k’araci ban hak’urinta ta tashi,d’akinta ta koma ta kwanta hawaye nabin fuskanta…

Wannan wane irin al’amari ne,daga kawota jiya harta wayi gari da kuka,ita bata tsinci komai a ranar ta ta farko a gidan miji ba,sai b’ata masa rai bayan d’inbin nasihar da iyayensu suka musu,ta rasa yadda za tayi,hakan yasa ta mik’e tana share fuskanta,wayanta ta janyo tana neman line en SIS enta,sai dai taji an ce mata switch-up..
Tunani duk ya mata yawa hakan yasa ta shiga neman line en HUBBEEY…

STORY CONTINUES BELOW

Tana d’auka da tsokana ta soma fad’in
”Amarya a gidan YAH BOSS”

Kukan da taji tanayi shi ya dakatar da ita daga tsokanar da take mata,cikin kid’imewa take tambayarta…

Sai da k’yar ta samu tayi shiru,kafin kuma ta soma magana
  ”Sis ina cikin wani hali,ki bani shawara please”

”Shawaran mene?kin sani a damuwafa”

”Fushi yake da ni”
Ta k’arasa tana sake sakin wani kukan..

”No Sis karkiyi haka,kin masa lefi ne shi yasa kikaga yayi fushi,ki yi shiru tukun,ki saurari abunda zan fad’a mi,yanzun kije ki bashi hak’uri da alk’awarin bazaki sake ba”

”Allah kuwan na bashi,ko kallona ma baiyiba bare ya kulani”

Dafe kai HUBBEEY tayi tana runtse ido

”Ya nemi wani abune kin hanashi ba?”
Tayi tambayar ba tare da yak’inin hakan bane…

”Haka ne sis,sai dai kin san bani da tsarki yanzun,kuma Allah ina jin tsoro sosai”….

”Kinga yanzu abunda nake so dake kiyi maza ki jashi a jiki,coz idan kikayi sakaci wollahi kina kallo zai dinga bin wasu a waje,saboda k’adangarun bariki ba saurara miki za suyi ba,idan zaki mik’e tsaye ki tarairayeshi toh,duk abunda ya nuna miki yana so koda baki so ki hak’ura ki nuna masa kin fishi so”….

Haka suka jima tana ta bata shawarwari kan zamansu da hanyoyin sa zata bi ta kyautata masa…

”To sis na gode sosai,in sha Allah zan gwada”

”Yawwa!maza kije ki sake bashi hak’uri,anjima zan zo da yamma”

”To shi kenan sai kin zo en,Allah kawoki lafiya”

  Suka amsa da ameen dukansu….

Tashi tayi ta koma parlor don ta sake bashi hak’uri,sai dai bata tarar da shiba,haka ta zauna ranta na masifar suya,duk haushin kanta da b’ata masan da tayi ya dameta…
Nocking en da akayi yasa ta tashi ta bud’e,ai kuwa sai ganin IKHRAM tayi ta toge k’afa ta sha kwalliya,tana zuba uban smile…
  Hanya ta bata tana maida mata murmushin itama…

A parlor suka zauna,IKHRAM en tana gaisheta,ta dai yi k’ok’arin sakin jikinta gudun kar IKHRAM en ta ganota,haka suka shirya komai kan dinning da taimakon IKHRAM en…

”Wai ni kuwa ADDANAH ina BB ne?”

Sai da tayi yak’e tukun tace
  ”Ina ga yana d’akinsa”

Wani irin kallo IKHRAM en tayi mata na rashin fuskanta,kai kad’ai ta kad’a ba tare da tayi magana ba,suka koma parlor,tsaf suka gyara ko ina na gidan,suka turareshi,ko ina sai k’amshi ke tashi…

A parlor ta bar IMHRAM tana fad’in
”Ina zuwa CWEETY”

  Binta tayi da kallo har ta b’ace mata

Sama ta haura,d’akin dake opposite da nata ta nufa,a hankali ta murd’a handle en k’ofan,ta  shiga da sallama…
Kwance ta tarar da shi fuskan nan uwa bai tab’a dariya ba,haka ya kalleta yana jiran jin me zata fad’a

”YAYANAH!Abinci na jiranka”
Duk maganar tana yine kanta a k’asa sam tak’i yadda su had’a ido,kuma cikin sanyi tayi maganan..

”Ina zuwa”

Haka ta juya jiki babu k’wari,shi kuma ya bita da kallo yana murmushi…

”Yarinya kad’anma kika gani,zan gyara miki zama,ta yanda ko kallonki nayi zaki san me nake nufi”

Da haka shima ya biyo bayanta,a parlor ya tarar da IKHRAM,har k’asa ta gaida shi,ya amsa fuskansa a sake kamar ba shiba,har suka kammala,sai fira suke da IKHRAM…

STORY CONTINUES BELOW

Ita kuwa baiwar Allah duk jinta take a damuwa,haka taita binsu da kallo,ba tare da tace ko uppan ba…

Yini sukayi suna fira tsakaninsu,sai dai su tashi suyi sallah,su sake dawowa,ko da ranama MAMMY ta bawa driver ya kawo musu abinci…

Suna ta hira Sallaman HUBBEEY ya katsesu,cikin murna JIDDAH take kallonta,suna gaisawa da YAH BOSS ta janyeta sukayi d’akinta,nan kuwa suka dasa sabon shafi na karatu,ranar bata bar gidanba sai bayan Maghreb inda YAH BOSS da kansa ya maida IKHRAM,tare da HUBBEEY…

Tun tafiyar HUBBEEY,JIDDAH keta tunanin anya zata iya abunda tace kuwa?

Da k’yar ta samu mafita tunanin maganar HUBBEEY da take cewa
  _”Idan bazaki iyaba ai shi kenan,kina kallo wallahi k’adangarun bariki zasu janye shi,ki tsaya kallon ruwa kwad’o ya miki k’afa,itafa rayuwar nan malama an daina duhun kai,amma idan baki yadda ba,kiyi sakaci ki gani”_

Wannan maganar da ta tuna yasa ta sauke ajiyan zuciya mai nauyi..
”Zan gwada komai wahala,ba zan tab’a sakacin da zan b’ata masa raiba,sai dai ko cikin rashin sani,duk da shima bana fata”….
Tashi tayi ta shige toilet ta jima a cikin ruwan wankan da ya turaruka iri daban²…
Ta gama kwalliyanta tsaf nan kuma ta soma tunanin kayan da zata sa…

Tsayawa tayi tana k’arewa kayan da HUBBEEY ta fito mata da shi,d’aya bayan d’aya take d’agawa tana kallo gaba d’aya ita kam bata ga na sawa ba anan…
Again tasake duban kayan tayi tagumi…

”Idan kikaji ance k’i gudu,to sa gudu ne bai zo ba”
Daga wani b’ari na zuciyanta ta samu hope na sawa…

Wani black three qurter ta d’auka da sea-green en riga,a ganinta sunfi dama² acikin kayan,ta saka ta kama gashinta a tsakiya da ribbon…
  Kowa ya ganta zai so ya sake kallonta,sai dai abun haushin har ta gama yayinta a parlor bata ji motsinsa ba…

Guiwanta sunyi sanyi,haka ta nufi d’aki ta kwanta,damuwa duk ya rufeta,a nan bacci ya d’auketa…
Sai after 11:00pm ta farka,wanka ta sake yi ta saka nighteey enta wasu masu arnen kyau,dai² lokacin idanunta suka sauka kan Wall-clock,ido ta fiddo waje,cikin sauri ta cire na jikinta da tayi niyyar sawa…

Wata k’aramar riga slick ta sa,iya kacin tsayinta saman guiwanta sai da ta k’arewa kanta kallo sannan ta juya da niyyar barin d’akin tana k’ara turaruka a jikinta,da k’yar ta fita ta nufi d’akin data gansa d’azun….

Kwance yake da phone a hannunsa,jin an turo k’ofan yasa ya d’aga kai yana kallonta…

Numfashinsa sai da yayi season na wucin gadi,amma taurin kansan yana motsawa ya juya mata baya…

Hakan da yayi da irin kallon da ya mata kafin ya juya,su suka tabbatar mata hak’anta zai cimma ruwa..
Murmushi tayi ta nufeshi,ta bayansa ta kwata hannayenta na jikinsa ta rungumesa…
  Hak’uri taci gaba da bashi,shi kuma yak’i kulata,ta kansa ta mirgina ta koma suna fuskantar juna…
Sake juyawa zai yi ita kuma tayi saurin hawa samansa,ta hana shi abunda yake niyya…

”Pardon please QURATU-AYNIY ban sake yi maka laifi ko da a mafarki,please ka yafemin”…
Ta k’arasa tana hawaye..

K’arshen rud’ewa sai da yayita,abubuwan sun masa yawa,ba shiri ya hau shafa bayanta,yana rarrashinta,da k’yar tayi shiru kafin tace
”YAYANAH bafa kace ka yafeminba”
Uwa wacce za tayi wani sabon kukan take maganar cike da shagwab’a

  Lips enta ya d’an ciza ganin yadda ta turo masa su

Ai kuwa ta sake sa masa sabon kukan tab’ara ita dai sai ta rama,dariya yasa mata daga haka wasan ya sauya salo,zuwa wani bigire na daban………

                        ***********

  Yau tsahon kwanaki hud’u kenan da kaisu,soyayya gami da shak’uwa ya dad’a shiga tsakaninsu,zuwa yanzun sun riga da sun saba da juna fiye da tunanin mai tunani…

STORY CONTINUES BELOW

Tana tsaye a kitchen dai² lokacin tana son had’a stew saboda yamma yayi,ya shigo cikin kitchen en,rungumeta yayi ta baya kansa na dai² kan neck ta,hannayensa kuwa ya zagaye su a k’ugunta…

”Wai kam HAYATEEY sai yaushe zaki soma sallah ne?”

K’irjinta sosai ya shiga bugawa da k’arfi,duk ta rikice,ta kasa magana…

A ranta kuwa fad’i take
”Wayyo Allah tawa ta k’are duk ranan da YAH yasan na samu tsarki,nasan zan fad’iwa y’an garinmu”

Take ta tuno yanda LITTLE ta bata labarin taci wahala,ai kuwa sai ga gumi na sakko mata,ta shiga sharewa,kuma har lokacin bata bashi answer ba…………

*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[10:31PM, 4/23/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ.   Ɩlıʄɛ…}_
                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *23/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU’AR BU’DE SALLAH.*
_BAYAN AN YI IK’AMA_

  _ALLAHUMMA BA’ID BAINIY WA-BAINA KHA’DAYAYA,KAMA BA’ADTA BAINAL MASHRIK’I WAL-MAGRIBI,ALLAHUMMA NAK’K’INIY MIN KHA’DAYAYA,KAMA YUNAK’K’AS-SAUBUL ABYADU MINAD-DANAS, ALLAHUMMAGHSILNIY MIN KHA’DAYAYA  BIS-SALJ,WAL-MAA’I,WAL-BARAD.._
          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*

  _Ina matuk’ar godiya da addu’o’inku gareni,Allah ya k’ara mana lafiya da nisan kwana mai amfani…Shukhran oll dearies._ ❤
*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 89↔90*

Juya kanta kad’ai take ta kasa amsa masa,hannunta a baki tana d’an cizonsa,duk iya hangentan ta kasa samo amsan da zata bashi…

A hankali ya d’an d’aga kansa jin shirun nata yayi yawa,yana k’ok’arin maidawa ne ya sake maimaitawa cikin wani irin yanayi..
  ”HAYATEEY baki jini bane?”

Da sauri ta fara magana cikin sark’ewar baki
  ”N…O……NO…Najika YAYANAH!”

Yanayin yanda ta amsa masane bai yi ba,shi ya haddasa masa dad’a d’aga kansa yana juyo da ita suna fuskantar juna,dad’a rungumeta yayi,cikin magana k’asa² ya soma fad’in
  ”Me ya faru dake ne?
  Yanzun na taddaki lao amma naga kin wani birkice yanzun”

”Nifa lao nake,babu abunda ya sameni”
Tana yi tana murmushin da da kad’an yafi kuka…

Binta kad’ai yayi da kallo,haka ya kyaleta ba dan ya yarda ba,bai sake ce mata komaiba,yayi shiru…

Da k’yar ta kammala aikin da takeyi,tsaf ta gyara gurin,har lokacin yak’i barinta,yana manne da ita haka take aikin..
”YAYANAH bari na kai sauran kayan na dawo”,kanta a k’asa take maganar…

  K’in sakinta yayi,sai da yaga duk ta nuna damuwa,sannan ya amsa da kansa ya nufi dinning,shi ya k’arasa setting dinning en,ita kuma ta kammala wanke abunda tayi amfani dashi,fitowa tayi tana goge hannunta,tayi hanyan d’aki..
A baya ya biyota har bedroom en,ya tarar data tana cire kayanta zata wanka,zuwa yayi ta bayanta ya sake tsaiwa yana tayata k’arasawa…

STORY CONTINUES BELOW

”HAYATEEY na miki magana d’azun kin tsaya kina bani wahalaba?”

Juyowa tayi,dan kam zuwa yanzun har tayi tunanin abunda za ta fad’a
”No YAYANAH sam abunda kake tunani ba haka yakeba,kawai dai har yanzun ban riga da na samu tsarki bane shi yasa kaji bance maka komaiba”
Tana maganan idanunta a k’asa

Kallon yanda take magana,tak’i yadda su had’a ido yayi,yasan shirya masa zancen tayi,tun da tak’i yadda su had’a ido da ita,wanda ya tabbata da gaskiya takeyi ba abunda zaisa bata kalleshi ba…
K’yaleta yayi bai kuma mata magana ba…

Sai can kuma ya ce
”Ok!muje toh na miki wanka,maghreb ya kusanto”

Kafad’anta ta mak’ale tana cuno baki,kafin tayi wani yunk’urin tuni ta tsinci lips enta cikin nashi,anci sa’a kam zuwa wannan lokacin tana k’ok’arin maida masa,duk wani salo da yasan zai rikitata shi yake mata,ta hakane kad’ai yake samu idan ta kasa d’aukan lesson en zata maida masa da kwatankwacin abunda ya mata…

  Sun jima a haka sunata faman tsotse juna,da k’yar suka tsaya,sunama juna kallon da su kad’ai suka san ma’anarsa,murmushi sukayi dukansu,d’agata yayi ya nufi hanyan toilet en..

”Pleasse YAYANAH ni ka saukeni,kaga inafa da nauyi,zanyi wankan da kaina,ka fara yi tukun”

Bai saurari abunda take fad’a ba,sai da ya direta a toilet en,haka ba dan taso ba sukayi wankan suka fito,suna fitowa ya nufi masallaci,ita kuwa ganin ya fita,tayi saurin komawa toilet en,wankan tsarki tayi sannan ta d’auro alwala,a gaggauce ta zura dogon riga da hijab ta kabbara sallah,har ta idar bai dawo ba,ai kuwa sai murna take…

  Har akayi ishaa bai dawoba coz dama d’abiansa ne hakan

  JIDDAH ta gama had’a muguntanta,kan bara ta bari ya gane ta dawo sallah ba,tana yi tana dariya ita d’aya,haka suka koma rayuwa,da dare zata sa kayan da dasu da babu duk d’aya kuma da sunan kayan bacci,da rana kuma ta matse cikin english wears kamar baturiya haka zaku ganta,idan bashi da inda zashi haka zasu yini cikin so da nunawa juna kulawa ta musamman…

  Yau ranan ya kama  one week dai² da aurensu,wanda yayi dai² da kwanaki 3 da samun tsarkinta,ko sallah za tayi bari take sai ya tafi masallaci takeyi…

  Da yake yau ya d’an fita gidan MAMMY tun yana hanyan Kabuga yake kiranta,amma shiru bata amsa ba..
Dai² lokacin kuwa tana toilet ta idar da alwala,har ta fito ta kabbara sallanta..

  Wani traffic da aka had’a shi ya hana shi k’arasowa da wuri,sai tsaki yake saki…

Tana idarwa kuwa lokacin tana tsaka da nad’e pray mat en ta jiyo horn ensa,da sauri ta k’arasa ninkewa ta kwashe ta d’ora kan bedside drower,cikin sauri ta fita dan taronsa…

  A bakin stairs en suka had’u tana murmushi take fad’in
  ”YAYANAH sannu da dawowa,ya MAMMYNMU?”

Hannu ya bud’e mata,aiko ta shige jikinsa,yana rufewa yake fad’in
”Duk lafiya alau,MAMMY da IKEEY na gaidaki”

”Allah sarki MAMMYNAH,ina amsawa,wai YAYANAH yaushe zaka kaini na ganta Allah duk ina jin kewanta?”

A kunnenta ya rad’a mata
  ”Sai ranar da na maidaki cikakkiyar mace”

K’irjinta sai da yayi wani mugun bugu,da yasata tai tari babu shiri

  Sannu yaita jero mata yana patting bayanta

”Kawai dai bara ka kainiba,shi ne zaka ce wai saika mai dani wani cikakkiyar mace,da an fad’a maka ba cikakkiya bane?”

Ido ya bud’e yana kallon yanda take zuba masa fitsara,sai abun ya masifar birgeshi yanda takeyi kamar wata *BABY DOLL*.
  Amma sai ya b’ige da fad’in coz bai son ta daina

STORY CONTINUES BELOW

  ”Ooooo!HAYATEEY ni kikema fitsara ba?”

  ”Nifa ba da kai nake ba,da wanda yayi magana nake”
Ta k’arasa tana hararan gefe

”To da wa yayi maganan idan baniba,cewa za kiyi da kai nake”

”Allah kuwa YAH BOSS ba da kai nake ba”
Tuna kalman da tayi amfani da shi yasa tayi saurin dafe bakinta,tana kallonsa

Murmushi yayi yana zare hannunta daga kan bakintan
”Haaaaa!yarinya zakiyi bayani duk ranan da na rik’eki,wato ninema BOSS koh? a inama kika samo wannan sunan?”

K’if k’if ta shiga yi da idanunta na rashin gaskiya,tana kad’a masa kai
”Am sorry YAYANAH baran sakeba kaji? pleaseee”…
  Duk tana yine kamar za tayi kuka

”Ok!is fast,muje ki tayani nayi wanka”
Babu musu kuwa suka haura sama bed room ensa suka shiga,wanda k’arshe dai tare suka wanke juna,suna yi suna wasa sai da suka b’ata lokaci sannan suka fito…
  Juyawa tayi zata fita yayi saurin rik’ota
”Ina zakije ne baki gama aikinki ba ai”

”Pleaseee YAH yanzun zan dawo,kayana zan d’auko”

Janyota yayi ya zaunar da ita kan stool

  ”Zauna ina zuwa,barinje na d’auko miki GIMBIYATA”
Ya fad’a yana mata winking,duka suka sa dariya,da sauri ya fita,ya nufi bed room enta,shigansa d’akin ya nufi Waldrop enta,har ya gama d’aukan abunda zai d’auka ya juya,dai² kan bed side drowernta ya hangi pray mat enta da hijab..
  Wani dariya yayi kafin ya juya ya fita..

Yanda ya barta haka ya tarar da ita,har inda take ya k’arasa yana murmushi,itama murmushin tayi masa,kayan ya ajiye ya nufeta,mai ya shiga shafa mata,itama haka sunayi suna tsokanar juna..

”HAYATEEY!wai wannan wane irin abune yak’i tafiya,nifa na gaji Allah hak’urina yana neman gazawa”
  Cike da shagwab’a yake maganan

Idanta uwa zasu fad’o kan kallon da take masa,har sai da ya hura mata iska,sannan ta dawo duniyarta

  ”Kaima dai YAYANAH idan na samu tsarki zan b’oye maka ne?amma idan baka yarda kana iya dubawa”
  Ba tare da tayi tunanin komai ba tayi maganar,shi kuwa kallonta yayi,a ranshi kuwa fad’i yake
”Zaki san ni kika cewa na duba”
Amma a fili sai cewa yayi
        ”Sure?”

Yana d’age gira d’aya,da wani kallo na kin yima kanki wauwauta yarinya

  Kai ta kad’a masa,shi kuwa dama mai jiran k’iris,aiko ya kinkimeta sai saman bed,yana fad’in
   ”Ok!let see,i have to check by my self”

Gaba d’aya ta kasa nutsuwa,ganin da gaske yake,tuni ta hau bashi hak’uri

”Pardon pleassse!YAYANAH bafa da gaske nake ba”

  Ci gaba yayi da tafiya,a tsakiyan bed en ya direta,daga ita sai towel data d’aura iya kacin tsayinsa cinyanta…

  Magiya take masa,shi kuwa fad’i yake
”No HAYATEEY dubawafa zanyi,bayan ke kika bani permission en yin hakan,mene na damuwa,so gara mikima kiyi shiru,dan ba fasa dubawa zanba”…
  Towel en jikinta ya kama zai ja,da sauri ta kai hannu zata rik’e,ya rigata fisgewa,komawa tayi kalar tausayi tana k’ara bashi hak’uri,sam ya garara saurara mata…

  Wasu zafafan kisses ya shiga aika mata,jinsu take kamar saukan ruwan sama,ba tare da ta shirya amsaba ta shiga maida masa,duk da yanda take jin k’irjinta na shivering kamar zai tsage…

Sai da ya gama rud’ata da salon da bai tab’a mata irinsa ba,ya gama birkitata ya tabbata taje linter signing kad’ai take jira ya mata, sannan ya shiga karanto addu’ar da (ANNABI (S.A.W) ya koyar damu,domin neman kariya daga shaid’an,,,,,la’ananne) wato (addu’ar saduwa da iyali)

_(ALLAHUMMA JANNIBNASH-SHAI’DANA,WAJANNIBASH-SHAI’DANA MAA RAZAK’ATANA).._
  _(Wannan addu’ah ba iya maza kad’ai aka keb’anceba,har mata,saboda halin mantuwa..)_

  Take kuwa ya kunna kai zuwa fadar tata,yana ci gaba da addu’o’i a zuciyansa…

  Wani uban zogi,rad’ad’i had’i da azaba ne suka ziyarceta lokaci guda,tako fasa wata irin k’ara,tana bashi hak’uri…

  ”Dan Allah YAH kayi hak’uri,wallahi baran k’ara fad’aba,,,,,wayyyoooo Allah zai kasheni, MAMMYNA ki zo ki ceceni,zai k’arasa ni……
   Ruwan hawaye kuwa ba a maganarsu,sai ya da kai take gefe,abun gwanin tausayi,ta rasa maceci,sunan y’an gidan kuwa babu wanda bata kira ba,kan neman ceto,shi kuwa bai saurara mata ba,sai da ya samu abunda yake buk’ata…

  Jinsa yake kamar wanda akayiwa bushara,lokacin da nutsuwa tazo masa,ya kula da irin ta’asar da yayi,tsam ya k’ank’ame abarsa a jikinsa kamar uwa da take tsoron za a rabata da jaririnta….

  Albarka kuwa babu irin wacce bai samata ba,kan farin cikin da yake ciki a ranan…

Kukanta take risga uwa ranta zai fita,tun sautinsa na fita har ya dawo sai hawayen kawai ke fita,sautinma ya gama b’oyewa….
  Duk rarrashin da yake mata tak’i yin shiru..

  ”Ok! tunda bara kiyi hak’urinba barin k’ara second round,tunda haka kike so,bana son ki sawa kanki wani ciwon”
  Fuskan nan babu wasa yake magana,hakan yasa ta k’ank’amesa tana yin shiru,sai ajiya zuciya da take saukewa akai²……

  Murmushi yayi yana sumbatan forehead enta,ya kwantar da ita,ya nufi toilet,fuskansa a sake da alaman jin dad’i a tare da shi…

  Ruwa ya tara ya dawo ya d’auketa,aciki ya sanyata,aiko ta saki wani d’an marayan kuka,ci gaba yayi da rarrashinta,da k’yar ya lallab’ata tayi shiru…
Tsaf ya wankesu su duka,yako nad’ota a towel ya dawo da ita ya kwantar tana jikinsa,a haka ya lallab’ata take kuwa bacci ya d’auketa tana fama da ajiyan heart har lokacin…

  Kallonta yake cike da so da kulawa,yana tuna shirmen da tayi masa,shi kad’ai yayi dariya yana fad’in
”Allah sarki HAYATEEYNA na baki wahala kam,to ya na iya,hakan ya zama dole ne shi yasa”
  Shi kad’ai yake maganarsa,yana murmushi………..
    _#Haaaaaaaa! Gaskiya kun bani dariya sosai kan comments enku na jiya,ina mik’o gaisuwa masoya gaskiya na jinjina.Y’an *SMASHER/HUBBEY NOVEL GROUP* wollah muna k’aunarku kuma muna tare da ku irin wujiga-wujiga ennan.Allah barmu tare.._

*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘

💠💠   *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_
                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *24/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU’AR BU’DE SALLAH.*
_BAYAN AN YI IK’AMA_

  _SUBHANAKALLAHUMMA WABI-HAMDIKA,WA-TABARAKSMURABBIKA,WATA’ALAA JADDUKA,WALAA-ILAHA GHAIRUKA_

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~_________________________~*
  🎂🎂🎂
        🎊🎉🎊

  🍻🍻🍻
  *HAPPY BIRTHDAY DEEZOH*

💃💃💃
    _May it be the best day of your life thus far, & may your happiness grow with each passing day through the many many birthdays that surely are ahead of you._
🎁🎁🎁🎁🎁🎁

   _Once again happy bufday sis *KHADIJA SALEEHU.*_
🌹🌹🌹
       🎂🎂🎂

💃💃💃💃

*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 91↔92*

    Rayuwarsu mai cike da tsafta haka suka ci gaba da gudanarwa, babu wani abu da yake hanasu nunawa juna soyayya da kulawa ko da kuwa a gaban waye..

  Yau tunda suka tashi take ta faman zuba masa SANGARTA shi kuma sai biye mata yake,duk abunda take yana biye mata..
  Tana kwance saman jikinsa,ta d’ago fuskanta uwa za tayi kuka,ta kalle shi,shima itan yake kallo yana jiran jin abunda zata fad’a

”YAYANAH!”+

”UHMM!Ina saurarenki HAYATEEYNA”

”Allah na gaji da zama guri d’aya,nifa tunda nazo ko bakin get ban tab’a zuwa ba,bare nasa ran zuwa naga MAMMYNA,kuma kai kullumfa sai ka je”

Dariya yasa mata,ita ko ganin yana son waske zancen tasa masa kuka

”Allah ni ka kaini naga MAMMYNA,in ba haka ba kuma”…

  ”In ba haka ba me?”
Ya tambaya yana sake mata dariya

Kuka sosai take tana bugun k’irjinsa,shi ko ya dad’a matseta a jikinsa,fuskanta ya rik’e,idanunta sai fidda hawaye suke
  Harshensa yasa yana d’auke duk wani layin hawaye dake fuskanta,k’arshe ya dire cikin bakinta,jin haka yasa kukan nata tafiya babu shiri,idanunta a kansa..

  Biye masa tayi sai da suka gama jagwalgwala juna,sannan yayi sama da ita yana tsokanarta,ita ko ko kulashi tak’i yi,haka yaita janta da fira iri² amma tak’i sakin jikinta..
  Wanka ya mata,abunda kullum tare suke amma yau saboda tana fishi tak’i kula shi,tsaf ya shiryata shima ya shirya,kayan da ya d’auko musu su suka sa ta kalle shi,bakinta da alamar tambaya,amma saboda tana fushi da shi ta k’i yin magana sai kumbura fuska take..
Duk wani motsi da take yana kallonta,sai da ya gama sannan ya d’aukota har packing lot ya direta,yana k’ok’arin bud’e motern ta bud’e baki da k’yar tace

”Wai ni YAYA ina zamu ne,naga ba kace min zan rakaka ko ina ba”

Murmushi kad’ai yayi ya bud’e motar ya sata,shima ya zagaya ta d’ayan b’arin ya zauna,har ya fice daga gidan bai ce mata komai ba,sai da suka d’auki hanya sannan ya juyo ya kalleta,sai faman cika take..
Kansa ya d’auke yana fad’in
  ”Yau kuma YAYAN ba naki bane?”

STORY CONTINUES BELOW

Baki ta murgud’a masa tana magana k’asa²

”Yarinya yi maganarki a fili,dan in na kama ki zaki san ni kikewa k’unk’uni,ba saurara miki zan yi ba”
  Yana wani mugun murmushi…

  Hanyan gidan MAMMY da taga sun nufa shi yasa ta saurin kallonsa da mamaki,fuskanta da tsantsan murna,ta fad’o jikinsa wanda hakan da tayi yasa shi saurin samun guri yayi packing yana d’agota..

“Kina so mu fad’i ne ko?”

  ”Na gode YAYANAH kamin komai,ban san wane irin godiya zan maka ba”

  Yatsansa yasa kan bakinta,yana murmushi
”Ba buk’atar ki godemin,hak’k’ina ne kula da duk wani abu da zai saki farin ciki”

  Wani warm hug ta dad’a bashi,ta manna masa kiss a kumatu,sai murmushi take saki tana masa kallon da shi kad’ai yasan ma’anarsa

  ”Gaskiya baby ba haka ba”
Yayi maganar yana shagwab’e fuska

Dariya ta saki tana kallonsa
”Me kuma ya faru?”
Ta tambaya duk da tasan me yake nufi

”Ai kin san ko me nake nufi,ko so kike na miki explaining?”

  Kai ta d’aga tana k’unshe d’ariyarta

”Ai kin riga kinsan bana son kiss a kumatu”
 
”Sorry dearnah a ina kake so to?”

”Ban sani ba,kina neman ki rainamin hankali,bar abinki ba na buk’ata”
Yana gama fad’a ya fisgi motar sai gidan MAMMY

Duk maganar da take bai ko saurareta ba,har suka k’arasa sai d’age mata kai yake,rabuwa tayi da shi
Ko da suka je,bai kulata ba ya fice abunsa,itama da d’an gudunta ta shiga parlor tana k’walawa MAMMY kira..

Jin muryan kamar a mafarki,yasa MAMMY saurin fitowa daga kitchen,tana fad’in
”Muryan wa nake ji kamar doughterna?’

”Nice MAMMYNA”
Suka rungume juna,MAMMY na jin dad’i kamar ta shekara bata ganta ba
  Zamewa tayi k’asa tana gaidata,cike da farin ciki mara misaltuwa MAMMYN ta amsa,ko YAH BOSS bata bi takansa ba,sai da suka gama murnan ganin juna sannan ta iya amsa gaisuwarsa
  Ganin ranan MAMMY ba tashi suke ba yasa ya mata sallama zai je ya dawo,aiko haka suka rashe a nan JIDDAH na zubawa MAMMY sangarta

Sai dare ya dawo,yana shigowa,JIDDAH ta farab’ata rai ita a dole bata son tafiya,badan taso ba haka suka baro gidan bayan sunyi dinner,MAMMY na dad’a yi musu nasihar su zauna da juna bisa hak’uri,haka suka d’auki hanyar nasu gidan…

  Motar ta yi shiru kamar babu masu rai a ciki,can ta tuna dalilin shirun nasa,ta gefe ta saci kallonsa duk ya wani b’ata rai

Juyowa tayi tana dariya,ya ko bita da kallo
”Allah ko YAYANAH sam b’ata fuskar nan da kayi bai maka kyau ba”

Baki ya tab’e bai ce komai ba,ya ci gaba da driven d’insa,sai lokacin taji duk ta damu
  Cikin sanyi ta shiga bashi hak’uri,k’in kulata yayi ,ita ko hakan da ya mata shi ya dad’a sata jikinta ya k’ara sanyi,ta san idan batayi wani abuba akan wannan fushin nasa haka har suje gida a haka zasu zauna,ko gama yanke hukunci batayi ba ta kamo fuskansa,cikin salonta da tasan idan ta aika masa sak’o baya musa mata,da sauri ya tsaida motan a gefen hanya
  Ya biye mata,kusan minti biyar suna abu d’aya,ganin yana k’ok’arin wuce gona da iri tayi saurin dakatar dashi,murya a shak’e
”Am sorry YAYANAH muna kan hanyafa ”
Da k’yar ya jaa motan da mahaukacin gudu

Ita ko JIDDAH riganta ta shiga gyarawa,dan kad’an ya rage ya gama cire kayan dake jikinta

  Gudun da yake ne yasa ta kalle shi
”YAYANAH please gudun fa yayi yawa,kar mu watse kan kwalta”

Kallonta kad’ai yayi yana murmushi,tare da rage malejin gudun motar..
  Basu wani d’auki lokaciba suka isa gidan nasu…
  Wanka sukayi kafin suka kwanta cike da nutsuwa da kwanciyar hankali…..

STORY CONTINUES BELOW

                           ********

Kimanin watanni uku da sati guda da auren su kenan..

  ”YAYANAH pleasee dan Allah ina jin son abu mai sanyi”

  A kaikaice ya kalleta kamar wanda ba zaiyi magana ba

”Abu mai sanyi HAYATEEY kamar me?”

”Emmmmm! yawwa! kamar ice cream haka,irin wanda yayi k’ank’ara ennanfa,ba na son mai ruwa ko kad’an”

  Yanda ta dage tana bayani shi yasa shi yi mata wani kallo cike da zargi iri daban²,da haka ya fita nemo mata abun da take so…

  Tun daga ranan ya zamo ice cream kusan shi ne abincin cinta,duk wani abu da zata ci sai ya dawo..

  Sosai abun ya bawa YAH BOSS mamaki,amma babu yanda ya iya,cikin dabara ya mata test,nan ko ya hango ciki kwance a jikinta d’an wata d’aya da sati biyu,murna kam ba a magana gurin YAH BOSS,take ya sanar da MAMMY babu ko kunya,itama tayi murna sosai da jin labarin,bata yi k’asa a guiwa ba ko ta sanarma DADDY…

Ranarma kuwa gidan MAMMY suka nufa a can suka tarar da LITTLE tana fama da cikinta da ya soma bayyana,can suka yini dukansu,sai d’awainiya MAMMY take da su,komai aka dafa JIDDAH bata so,k’arshe dai da k’yar tace ‘DAN WAKE da manja take sha’awa,babu b’ata lokaci kuwa MAMMY da kanta ta mata..
   Shi kad’ai ta iya ci,in da tasa masa uban yaji,tana ci tana jann baki alaman yajin yayi yawa,ko da YAH BOSS ya k’wace kuka ta dasa har da birgima a k’asa…
  Sai da MAMMY tayi da gaske sannan ya bata…
  Tun daga ranar ya zama YAH BOSS ya koma bata kulawa ta musamman,ko kad’an bai so yaganta a damuwa duk abunda ta nuna tana so shima ko Yana sonsa…..

《《》》

   Rayuwar MEINERH (LITTLE) da FAROUK rayuwa ce mai cike da jin dad’i,tare suke gudanar da duk wani abu da ya shafi rayuwarsu,gidan nasu gwanin sha’awa yanda suke rayuwa…

                        ***********

*6 MONTH LEAPS.*

  Kwance take saman sofa tana waya,jikinta sanye da singlet,da gani kasan tana buk’atar shan iska ne,duk kuwa da yanda parlorn yake a sanyaye…

”Pleasse YAYANAH za ka kawomin ko?”

  ”A’a babyna ban son kina shan sanyi sosai”

”Nifa Allah idan ban sha ba,zan iya mutuwa ne”

”Sorry baby amma kam ni baran siyo ba”

Kuka tasa masa had’e da kashe wayan tana jifa da shi kan sofa…

  Jin ta kashe yasa ya hau dariya,yana fad’in
  ”HAYATEEYNAH ba dai rigima ba”

Haka ya gama aikin da yake,cikin sauri ya d’auko hanyan gidan,ko kafin ya k’ara so sai da ya tsaya ya siyo mata ice cream,masu k’ank’ara…

Yana shigowa cikin parlorn,sanyin gurin sai da ya bashi tsoro,kansa ya d’aga,nan yayi arba da k’arfin A.C en gurin,remote ya d’auka ya rage,a kan sofa ya hangota tayi rub da ciki,cikin sauri ya nufeta ya d’agota yana mata birkitaccen kallo

”Haba HAYATEEY kina so ne ki illatamin BABYNAH”

”Ni ka k’yaleni bacci nake yifa,ka wani tasheni”

”Tambayanki nake,kin san irin matsalan da wannan kwanciyan ke haifarwa kuwa?”

Bata kulashi ba ta shiga zamewa zata kwanta

  ”Pleassee dear ka k’yaleni ni”

”Ok zan k’yaleki amma banda irin wannan kwanciyan,promise me Bara ki sake ba”

STORY CONTINUES BELOW

kanta ta juyar bata ce komaiba,shi kuma ya janyo ledan da ya shigo da shi,dan ya san shi kad’ai ne abunda zai sa ta sakko daga fushin da take…

  ”Oyahhh!mik’e ki amsa sak’onki”

Da k’arfinta ko ta mik’e ta zauna tana murna,jin ya ambaci sak’o tana bin hannunsa da kallo,tun kafin ya bata har ta soma tand’e baki………..

*_~#TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[5:54AM, 4/26/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_
                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *25/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU’O’IN RUKU’U.*
    _SUBHANA RABBIYAL-AZIYM3_

   _SUBHANAKALLAHUMMA RABBANA WABI-HAMDIKA ALLAHUMMAGHFIRLIY._

   _SUBBUHUN,QUDDUSUN,RABBUL-MALA’IKATI WARRUUH.._

          *_~#HISNUL-MUSLIM.~_*

*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 93↔94*

  Cikin wani irin yanayi ya kalleta,yana binta da wani irin birkitaccen kallo,kafin ya ajiye cotainer en ice cream..
  Kan cinyanta ya d’ora hannunsa yana binta da ido,ko kafin ya kai ga yi mata magana har ta riga shi..

”YAYANAH please ka bani,Allah na gaji da jira”

”Pleasse HAYATEEY karki sake irin wannan mik’ewan na rok’eki”
  Ya fad’a har da had’e hannayensa guri d’aya…

”Ni Allah ka bani,nafa k’agu na sha”

”Zan baki amma sai kin min alk’awarin bara ki sake ba”

  Hannayensa ta janye daga kan cinyoyinta ta sauka k’asa,take ko ta soma dira k’afafu tana masa tab’ara,ganin za ta soma birgima a gurin yayi saurin rik’eta…

”Me yake damunki kam HAYATEEY?”

”Ni tunda baraka bani ba ka kyale ni,naga dai ai bani nasawa kaina son abunba”
Da sauri ya rufe mata baki,yana janta,kan sofan ya zauna yana zaunar da ita kan cinyansa..
  Containern ya d’auko,yana bud’ewa kuwa ta hau lek’a robbern uwa ba ita zata sha ba..

”Pleasse YAYANAH kayi sauri,kaga miyauna har tsinkewa yake”

”Allah koh?”

”Sosai ma,nifa sai jamin rai kake,idan bara ka bani ba na hak’ura”
  Ta fad’a tana narke masa fuska uwa za tayi masa kuka..

”Bana son kina shan k’ank’ara ne,ki jira kad’an nayi melting nasa”

”Ni Allah baran yarda ba”

Ganin da gaske take,har tana shirin tashi,shi yasa yayi saurin rik’eta,ya hanata tashi..
Bashi da zab’in da ya wuce ya bata,haka ya shiga bata kuwa,yanda yaga tanayi shi ya sa ya soma kallonta,har wani lumshe idanunta take,tana kad’a kai uwa wacce ta samu wani abincin da bata tab’a samun irinsa ba……

  Tsaf ta shanye robber biyu manya,wanda ya mak’ale a gefen bakinta da bata tand’e ba,ya kamo fuskanta ya juyo da ita..
Kallonsa tayi tana murmushi,dai² nata ya matso da fuskansa harshensa yasa ya shiga mata cleaning wajen,dariya tayi masakafin tace
  ”Shukhran QURATTU-AINIY”….
Bata samu damar k’arasawa ba,ta tsinci bakinta cikin nata..
Idanunta ta shiga k’iftawa saboda batayi tsammanin faruwar hakanba…
  Gudun kar tayi laifi yasa ta biye mishi,suka shiga farantawa juna….

STORY CONTINUES BELOW

  Bayan y’an kwanaki,tana zaune ita d’aya a parlor,ta janyo phone enta dake kusa da ita…
  Line en HUBBEY ta shiga kira,tana d’auka ko tahau fad’in
  ”Sannu uwar zumunci,wato tunda an kawo ni dake,bari ki manta dani”

”Laaaa! Sistonah wollah ba haka bane,kinga yanzunma gidanki zanzo,nace ba sai na fad’a mikiba,kawai sai dai ki ganni,amma Allah ba haka bane”

”To shi kenan Allah ya kawoki lapia”
”Yawwa toh sai na zo”

  Tayi hanging kiran,tana kwanciya…

  Har bacci ya fara d’aukanta,taji alaman door bell na k’ara,cikin alamu na mai bacci ta nufi k’ofan parlor,tana bud’ewa,sukayi arba da LITTLE ta wani kama k’ugu,wani kallo ta jefi JIDDAH da shi kafin cikin fad’a ta soma magana

”Wato dan rainin hankali irin naki,shi ne ko kizo gidana kiga yadda yake”

”Ke ni dillah rabu da ni,ke en zuwa kikai da zaki wani hau yimin fad’a kamar wata y’arki”

   ”Hakama za kice?”

  ”Yo gashima kin fad’a”
 
Tayi k’wafa zata juya,kome ta tuna kuma ta dawo

”Amma dai kin san gara ni dake,tunda ranar da aka kawoki har dani aka zo ko?”

”Sai me kuma,wannan ma ai ba zuwan kanki bane”

”Shi kenan ai,ni dillah bani guri na wuce”

  ”Au ai nayi tunanin kin fasa zama ma,da naga kamar tafiya za kiyi ko?”

”Ban sani ba”
Tana doka mata harara,ta wuce tana neman gurin zama..

  ”Mutum daga zuwansa sai neman masifa”
Tana hararanta ta bi bayanta…

  Ba a fi minti goma ba HUBBEEY ta k’araso,da murna ranan suka yini,wanda sun jima rabonsu da had’uwa kamar haka..
  Suna tsaka da hira HUBBEEY ta kalle su tace
  ”Y’an uwa kunsan wani abu kuwa?”

Da mamaki suka kalleta,sai da tayi dariya tukun sannan tace
”Anfa sa ranar aurena”

Gaba d’aya suka had’a baki wajen fad’i
  ”Meeeyyyyyy?”

Aiko take ta sake sakin wata dariyan
”Lallai kin zama y’ar rainin wayo,shi ne har asa rana bamu sani ba?”

  ”Kudai yi hak’uri,kun san ba daga ni bane,wallahi ABBAH ya riga ya tsaida lokacin,muma daga baya ya fad’a mana”

”Kan uba,wallahi k’arya kike,taya zaki raina mana hankali kice wai baki sani ba”

Dariya tasa sosai,sukam sun sata gaba suna kallo,sai da tayi son ranta sannan ta kalle su..
  ”Uhmmm! yanzun dai mubar wannnan maganar coz babu lokaci sosai,kun sanfa yanzun saura 3 weeks fa”

”Meeeeyyyyyy!”

Suka sake had’a baki,suna kallon juna,su kad’ai kuma suka sa dariya..

”Shegen son gulma irin naku,har wani had’a baki kuke”

  ”Wai waye wannan mai nasaran da har ya saye zuciyanki,MR’S BOKO?”

”Amma wollahi JIDDAH baki da dama,sunan da kika rad’amin kenan?”

  ”Yo ba dole ba,tunda na ga samarin University basa gabanki”

”Ke dai bar y’an rainin wayo,bason Allah ke kawo suba”

”Wollahi kuwa,Allah dai yamana mai kyau”

   ”To ai shikenan,yanzun ya ake ciki,tunda lokaci ya k’ure mana gara muyi abunda ya kamata koh kuwa ya kukace ?”
Fad’in LITTLE tana kallonsu…..

  Haka ne kam,shawaran abunda yayi saura za muyi kawai….

   Nan suka shiga shawaran yanda zasuyi komai sun zauna suna ta fama,k’arshe dai suka yanke shawaran zasu sake had’uwa kafin sati guda ko da a gidan MAMA ne,daga nan suka shiga firan duniya,da yanda zasu koma skul nan da one week..

STORY CONTINUES BELOW

  Sai yamma sannan HUBBEEY ta tafi,in da ta bar LITTLE a can,a cewarta idan SWEETHEART ya dawo zasu wuce gidan tare….

  *2 WEEK LETER.*

Sati biyu kenan da had’uwarsu,kamar yadda suka yanke shawaran zasu dunga had’uwa duk sati,haka kuwa akayi,a ranan suka d’auka hanya sai gidan MAMA,duk da kuwa suna had’uwa a skul,coz satinsu guda kenan da komawansu skul,kullum kuma suna tare…

  A ranan suka gama tsaida duk wani abun da zasuyi,na game da sha’anin biki,a ranan ma kuwa sai da suka kira telansu da zai musu d’inkunan fitan biki…..
Kowacce ta nufi gidanta……

*A WEEK LETER.*

    Rana bata k’arya sai dai uwar d’iya taji kunya,kwanakin da sukayi saura har sunzo sun shud’e,har ancinye wasu kwanakin daga cikin satin bikin….

  Kamar ba amaren da akayi bikinsu ba da jimawa idan ba mutum ya cika da tsananin sa ido ba,ba lallai ne ya gano cikin dake JIDDAH ba,sai dai ko na LITTLE da yake bata da wani timbi da zai b’oye cikin nata,haka suka fito fuskokin nan sun sha make up…

Da sauri ta fito daga cikin gidan,dai² haraban gidan ta tsaya tana waige²,motersa daya kunno kai cikin haraban gidan yanzun ta saki murmushi ganinsa kusa da ita,yana yin parking ta zagaya ta d’ayan b’arin tana sakin k’ayataccen murmushi da ba kowa takewa irinsa ba…
  Sai da ta dai²ta zamanta sannan ta kalle shi cikin k’auna tana fad’in

”YAYANAH ba kace nayi kyau ba”
Tanayi tana fari da idanunta

”Bako sannu da zuwa,za kimin zancen wani kwalliyanki?”

”’Eyyaaaehhh !mana YAYANAH am sorry,ka zo lafiya?”

”Lafiya lao HAYATEEYNAH”
  Cike da kulawa yayi maganar yana dubanta..

”Kwalliyan ya miki kyau sosai,sai dai gyara kad’an da zan miki,su make-up artists en sunyi mistake”

  ”Gyaran me kuma YAYANAH?”

  ”Matso kiga zan gyara miki da kaina”

  Cikin nuna rashin damuwa ta tura masa fuskanta
”Gyaramin YAYANAH kaga suna so na k’i yin kyau”…

  Bata k’asa ba,taji ya soma tsotsan lips enta,sai da ya shanye lips-stik en tsaff sannan ya kalleta,yana mata dariyan mugunta

  Uwa za tayi kuka haka ta bishi da kallo..

”Haba dan Allah ya zaka shanyemin jan bakinah?”

  ”Saboda bana so ne”

  Kallonsa tayi tace
  ”To idan kuma ina sofa?”

”Na san bara ki so abunda bana so ba”

  Murmushi kad’ai tayi

”Har yanzun baku gama shirin bane?”

  ”A’a mun gama dan har an soma tafiya,mu kad’ai mukayi saura”

  Suna cikin firan ne aka fito da Amarya HUBBEEY aka sanyata a mota…

Take kuwa kowa ya soma yin gaba,a baya suka bisu har gurin dinner wanda ya masifan tsaruwa,MR DJ ya saki dumaa,ranan an gyagije uwa ba gobe…
  Duk k’ok’ari irin na JIDDAH kan ta tashi YAH BOSS ya kafa ya tsare duk inda zata yana biye da ita…
  Sam ya hanata motsi,sai sai ta kalleshi tayi murmushi,duk wanda ya kallesu yaga tsantsan masoya,mutane sai maganarsu suke,duk inda kuwa suka gifta sai anyi maganarsu,haka taro ya watse,inda a washe gari akayi MOTHER’S EVE…

Ranan sunday da safe aka d’aura auren HABIBA IDREES da angonta ABDULLAH,tun da yamma aka d’auki amarya sai gidan ta dake unguwan TUDUN YOLA,gida ya tsaru dai² gwargwado,abunsu babu k’arya a ciki,haka mutane suka soma watsewa….

STORY CONTINUES BELOW

  JIDDAH da LITTLE sun zo mata sallama,ta rik’e su atafau barasu tafi ba,da k’yar suka samu suka tsere…
  A bakin k’ofa suka tsaya,suna dariya
”To AMARYA Allah ya bamu alkhairi,Allah kawo k’azantar d’aki”…

Wani kuka tasaa,su ko suka fice suna mata dariyan mugunta……

  #To nima dai nace Allah bamu alkhairi amarya,a sha amarci lafiya……..
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[9:15PM, 4/26/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_
                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *26/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU’O’IN ‘DAGOWA DAGA RUKU’U.*

    _SAMI’ALLAHU LIMAN HAMIDAH.._

    _RABBANA WALAKAL HAMD,HAMDAN KHASIYRAN,’DAYYIBAN MUBARAKAN FIYH.._

             HISNUL-MUSLIM.
*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 95↔96.*

     Tun suna hanya take jin jikinta duk yana mata ciwo,jinta take uwa wacce akawa duka,duk gab’ob’in jikinta a d’aure,ita kad’ai sai juyi take a kan seat en…
  A hankali ya kwatar mata da seat en yanda za tafi jin dad’in kwanciya,juyowa tayi ta kalleshi fuskanta d’auke da murmushi,idanun kuwa da gani kasan bacci ne cike a cikinsu…

  ”Shukhran HABEEBEEY!”

Baiyi magana ba ya mayar mata da murmushin shima,yana maida hankalinsa akan driven en da yake…
  Ko kafin suje gida,har ta fara bacci,da kansa ya d’auketa har bedroom sannan ya shimfid’eta saman bed..

  Ruwa ya had’a mai d’an karen d’umi,ya dawo cikin dabara ya zare kayan dake jinta,yayi hanyan toilet da ita..
  Jinta cikin ruwa shi ya bata damar bud’e ido,ta narke fuska uwa zatayi kuka..

  ”Haba dan Allah HABEEBEEY nafa fara bacci zaka wani tashe ni”

”Sorry HAYATEEY idan namiki wankan zaki fi jin dad’in baccin”

Bata kuma cewa komai ba,har ya gama mata wanka ya dawo da ita ya kwantar,har ya juya zai koma ta dakatar da shi..

”HABEEBEY ina ice cream ena?”

Kallonta yayi shi yama manta da sak’on nata,tsaiwa yayi uwa mai nazari,can kuma dabara ta fad’o masa

”Bari nayi wanka na fito,sai na d’auko miki koh?”

Kai ta kad’a masa tana y’ar dariya,har wani gyara zama take,saboda za ta sha kayan kwad’ayi..
  Wayanta dake ring a saman bedside drower ta janyo,da sallama ta amsa…

  Sai da ta soma dariya kafin tayi magana
  ”Amarya bakya laifi,ko da kuwa kin kashe d’an masu gida”

”Muguwa kyace haka mana,tunda kun tsere kun barni wato ba ruwanku da abunda zai sameni ko,ae shi kenan”
  Da sauri tayi magana
  ”Sai munyi waya gobe,ga sunan shigowa”…
  K’it ta kashe wayan,ita ko JIDDAH nan taita dariyanta..

  Line en LITTLE ta kira,a wahale ta d’auka,nan JIDDAH ta labarta mata yanda sukayi da HUBBEEY..

”Bar y’ar air yanzun ta kirani nima,za tamin iskanci,nima na tsigeta,ko an fad’a mata dama zamu zauna mata zaman d’aki ne?”

STORY CONTINUES BELOW

Sun jima suna shak’iyanci,hango YAH BOSS na tahowa yasa tayi mata sallama tana fad’in
  ”Sis sai da safe ga YAH BOSS nan,mu kwana lapia”

Kalamanta na k’arshe su yaji,kallonta yayi yana murmushi yace
  ”Ke dawa kike waya kuma,ba bacci kike jiba?”

Dariya tayi kafin tace
  ”Ai kai ka hanani baccin”

  ”A’a fa HAYATEEY ni ban hanaki ba”

”Allah kuwan kaine ba ruwa kasaminba kaga kuwa dole na tashi”

”Ok toh!zo na miki tausa sai kiyi baccin koh?”

  ”Toh ai ban sa kaya ba,kagafa towel kad’ai ne a jikina”

”No!ba sai kin saba,hakama is ok”

  ”Kasanfa ban saba kwanciya a hakaba”

  ”Yeahh!yau kuma ni nake son ganinki a haka,ko ban isa ba?”

”A’aa YAYANAH harma kayi yawa”

”Oyaahh!kwanta toh na miki tausa sai kiyi baccin,nasan akwai gajiya a tare dake”

  ”Laaa!HABEEBEY banfa sha ice cream en ba”

  Kansa ya dafe,coz shi har ya manta da maganan ice cream en..

  ”Ok ina zuwa”

Ficewa yayi ya d’auko ice cream en a cikin freezer,duk ya zama k’ank’ara,ya dawo ya tarar da ita a zaune tana jiran dawowansa,da murnanta ta kalleshi tana ta faman zuba smiling….

  Tana gama sha kuwa,ta nufi toilet ta wanke bakinta,daga ita sai towel iya cinyanta,fararen cinyoyita duk suna bayyane,tun daga yatsunta yake kallonta,dogayen k’afafuntan da suka bayyana su suka dad’a jan hankalinsa,bai sauke eyes ensa ko ina ba,sai kan k’irjinta da ya dad’a cika,hannunta ya kamo ya kwantar da ita ya shiga matsa mata jiki a hankali,sosai take jin dad’in tausan da yake mata,har wani lumshe idanu take…

  Ji tai ya zare towel en jikinta,a ranta ta furta
  ”Nasan za a rina,wai an saci zanin mahaukaciya”

”Tafiyan tsutsa yake mata a jiki,wanda yasa ta soma dariya,kafin itama ta biye masa suka lula wata duniyar……

          *NEXT MORNING.*

  Tun da safe HUBBEEY ta kirata,ai ko tana d’auka ta hau k’orafi
  ”Muguwa kyayi dariya mana,dama kunsan da haka ba kuyimin bayani ba,wallahi zamu had’u ne saina muku rashin mutunci”

  Banda dariya ba abunda take,haushin dariyan ya k’ular da ita ta kashe tana k’wafa….
   Wata uku da auren HUBBEEY,ranar wata laraba,tun rana LITTLE take fama da nak’uda uwa bazata rayuba haka aka d’unguma da ita asibitin AKTH nan ta sumb’ulo jaririyarta k’atuwa da ita y’ar gwanin sha’awa,kyakykyawa gwanin burgewa,nan dangi sukaita faman murna sun samu k’aruwa…

  Gida FAROUK ya dawo da ita,nan MAMMY taita d’awainiya da ita,ranan suna yarinya ta ci sunan MAMAR FAROUK wato FATIMA ZAHRA,kowa sai son barka yake inda ake kiranta da ZAHRA…

  A ranar da tayi arba’in MAMMY ta tarkata da kayanta ta sallamesu,bayan gyara da ta sha,tamkar wata amarya haka ta koma…
  Watan BABY ZAHRA uku a duniya,amma kamar y’ar watanni 5 ta dad’a girma,gwanin sha’awa,yarinya kamar jinin larabawaa….

  JIDDAH koh duk ta shiga damuwa,yanda cikinta ya bayyana yanzun duk jinta take a takure,har lissafi take na ranar da zata sauke,duk da ya k’ara mata kyau,hakan ba zai hana a gano yanda gab’ob’inta suka dad’a bud’ewa ba,ta dad’a zama uwar mata…

  MAMMY da kanta ta tasa YAH BOSS akan ya dawo da JIDDAN gida,shi ko babu kunya yace
”MAMMY dan Allah ki bar wannan zancen,zuwa wankan nanfa ba addini bane,so ni gaskiya bani da sha’awar barinta zuwa wani wankan gida”

STORY CONTINUES BELOW

  ”K’aniyarka JABEER”
Ta masa dak’uwa,tana harararsa

Kansa a k’asa,yak’i yarda su had’a ido,ambatar sunansa da tayi,wanda tun tasowarsa bai tab’a jin hakan daga bakinta ba,shi yasa ya kalleta..

Cike da jin kunyar abunda tayi itama ta mik’e,sai da taje dai² k’ofar d’akinta sannan ta d’an waigo tana fad’in
  ”Ka tabbata ka kawomin ita cikin wannan satin,inba haka ba,ranka zai mummunan b’aci”…

  Tana gama fad’a ta shige,har ya bar gidan bata kuma fitowa ba….

  Kwanaki uku tsakani kuwa ya dawo da ita,fuskar nan uwa zaiyi kuka,haka ya fice daga gidan ko sallama ba wanda yayiwa…

  Da darema da ya dawo daga gurin aiki,lokacin da ta kawo masa abinci sai b’ata rai yake,uwa ita ta masa laifin…

  Haka ya zauna sai da ya raba dare a gidan,ita ko MAMMY d’aki ta shige tace idan ya fita ya jaa musu k’ofan,ganin ta fara lumshe ido alamar tana son yin bacci yasa ya d’aketa sai d’akinsa da yayi zaman gwaurantaka….😜

  ”HABEEBEY!Me kuma zanyi nan d’akin?”

     ”Ni zaki taya kwana,kinga baran iya bacci ba ni kad’ai”

  ”Uhmmmm! kaima dai HABEEBEY da wani magana kake,to me zai hanaka baccin?”

  ”Tunaninki ne zai hana ni,kinga zanta mafarkinki cikin dare,amma idan kina kusa da ni,bazan yiba”

  ”Da gaske HABEEBEYNAH?”

  ”Ehhh!mana,ko kina so nayi?”

  ”A’aa bana so”
Ta fad’a  tana k’unshe dariyan da ya taho mata

  ”Dariyama kikemin koh?”

”Ni na isa namaka dariya,ai da anmin bulala”

  ”Waye zai dakarmin HAYATEEYNAH?”

Ya fad’a yana fiddo ido waje…

  Sai da tayi dariya mai isarta ganin yanda yayi da idanunsa,sannan ta kalle shi tace

     ”Kai mana”

”Ni kuma da kaina zan dakeki?”

”Ehhh mana,dan bakasa bulalaba ae ka ban wahala a kan bed”

Tana fad’a tayi maza ta kulle idanunta,dariya sosai yayi lokacin da ya ajiyeta kan bed..

  ”Ai ko tunda haka ne,yanzunma ki shirya amsan wani bulalan,yau kwana zakiyi ba bacci”
Yana dariya yake maganar…

”Allah Yaya ba ruwa na,kagafa BABYNMU dama duk ya takurani”

  ”Da gaske kike ya takuraki?”

”Sosaima kuwan Allah,duk mutum bai da kwanciyar hankali”…
  Tana yatsina fuska tayi maganar…

  ”Ke dai fad’i gaskiya,ko dai ni kike buk’ata shi yasa kika ce haka?”

Yana kashe mata ido d’aya….

  ”Kai HABEEBEY Allah ka koyi fassara mutum,ni ba haka nake nufiba to”

”Ok!let me find d truth”

  Ya soma haurawa kan bed en yana mata dariya k’asa²…

  ”Nifa Allah babu ruwana,ka bari HABEEBEY”

  ”Nifa ba abunda zan bari,sai na gaisa da BABYNAH,so nake na miki bulalar da ko gobe nema ki haihu,tunda BABYN nawa ya takuraki,kinga ya k’yale MAA nd PHAA ensa su huta”….

  Daga haka ko bai sake bata damar yin maganaba ya had’e bakinsu guri d’aya yana mai aika mata sak’onni iri daban²,suka shiga faranta ran junansu………
STORY CONTINUES BELOW

*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER_*🤞🏻😘
[4:58AM, 4/29/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_
                  💠💠
                     🌹
                
                   
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *28/ąpril,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU’O’IN ‘DAGOWA DAGA RUKU’U.*

    _SAMI’ALLAHU LIMAN HAMIDAH.._

    _RABBANA WALAKAL HAMD,HAMDAN KHASIYRAN,’DAYYIBAN MUBARAKAN FIYH.._

             *_~HISNUL-MUSLIM.~_*
*~__________________________~*

_Kumin afuwa Fan’s nayi mantuwa a last page da na  na *RAYUWAR WANI* nasa “2nd to the last page, to kuyi hak’uri wannan shi ne maimakon wancan,na gode sosai muna nan manne da juna.._ *#1 Luv my fan’s.💃*
*~__________________________~*

*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

*℘ąɠɛ 97↔98.*

 
  Cikin dare ko wani azababben ciwo ya farkar da ita,ciwo sai kace ba zai lafa ba haka taita fama da shi,ya dank’a ya saki….
  Da ciwon ya ciyota ta sauka k’asa kanta na gefen gadon ta kifa shi……

    Juyawa tayi ta kallo side en da yake,hankalinshi kwance yake bacci,haka taita fama da ciwo,zuwa wani lokaci ciwo ya dad’a kunno ta,ai bata san lokacin da ta kai masa wani mahaukacin naushi ba..

A firgice ya mik’e dan ko yaji dukan,coz a bazata ya zo masa,kallon gefensa yayi,yaga ta dunk’ule guri guda,sai juya kai take,ita kad’ai ta rik’e baya,ana jimawa zata koma ta dafe maranta….

  Da sauri ya sakko yana rik’eta,kallo d’aya da ya mata har ya shiga damuwa…

”HAYATEEY meke damunki?”

  Su HAYATEEY ba baki sai ido,mararta da bayanta ta shiga nuna masa,take ko ya hau aikin murza mata dan ya fahinci abunda take nufi,can ciwon ya d’an lafa mata ta kwantar da kanta a kafad’arsa tana sauke numfashi d’ai²….
Haka ya zuba mata ido yana kallonta shi kad’ai yasan me yake ji game da ciwon nata,kuma lokacin dare yayi sosai…

  Har bacci ya kuma d’aukanta,wajejan Asubah ta sake farkawa da wani gigitaccen ciwon da yafi na farko,nan ko babu shiri YAH BOSS ya sunkuceta yayi waje,ko MAMMY baibi ta kan ya fad’a mata abunda ke faruwa ba,yayi hospital da ita….

  Har gari ya soma wayewa amma labari bai canza ba kuma shima baiyi tunanin sanar da MAMMYN ba,duk ya shiga damuwa,baya ga addu’ah babu abunda yakeyi,yana kanta ya hana kowa zuwa gurin….

  Wajen k’arfe 7:30am BABYN ya kunno kai,bayan d’imbin wahala da JIDDAH ta sha,ba ita kad’ai ta sha wahalar ba,dan ko tare sukayi nak’udar da YAH BOSS,da taimakonsa ya zaro BABYN cikin ikon Allah,tsananin murna yasa ko wanke babyn ba ayiba ya rungume abunsa yana jin tsananin k’aunarsa na ratsa masa zuciya….
  Kallon HAYATEEYN nasa yayi yaga tayi laga² kan bed en tana mai da numfashin wahala,nan ya shiga mata sannu,ai ko tana d’agowa tace dawa Allah ya had’amu ba kaiba…

Sak’on harara ta fara aika masa,cikin wahalalliyar murya ta furta
”Kai da jin dad’i ni kuma da wahala”
  Ta k’arasa tana murgud’a masa baki..
  Dariya sosai yayi,ya jaa hancinta

STORY CONTINUES BELOW

”Bari inyi miki gyara”

”Ba wani gyara ni Allah na yafe gyarankan nan”

Dariya sosai maganarta ta bashi
”To shi kenan tunda bakya so,ai da kanki zaki zo har in da nake”

  ”Tabbbb Allah ba amin ba,haka kawai ka sake d’irkamin wani cikin,in zo ina haifewa da k’yar”

  ”Haba HAYATEEY kifa dena fad’a dan kam Allah zaki kawo kanki,kuma ai naga tare mukayi nak’udan har haihuwanma”

  ”Ba wani nan”

  ”To shi kenan na ji,barin gyaraki da BABYNMU koh?”

  Sai lokacin ta d’an saki fuska tana fad’in

  ”YAYANAH wai me muka samu ne?”

”Oohhh!yanzun kuma kin sakko?”

”Uhmmm dama ba fushi nayi ba ai,d’an nunamin BABYN”

  Ta wani marairaice fuska…

Haka sukaita shirmensu,kafin ya goge babyn da zaitun,tsaf ya gyara su duka,ita ko sai mamaki take…….
  Suka d’auko hanyan gida yana rungume da babynsun….

                        。。。。。。

   A gida ko tun safe MAMMY da ta tashi,ta nemi JIDDAH ta rasa,ranta idan yayi dubu ya kai mak’ura wajen b’aci…

  A ranta ko fad’i take,”lallaima yaron nan wato ni zai mayar sakara da zai d’auke matarsa daga gidan,zasu zo duka su sameni….

  Tana tsaka da wannan tunanin suka shigo parlorn da sallama….

  Da k’yar ta iya amsawa,tana binsu da kallon mamaki,fuskokinsu d’auke da fara’a suka nufe ta…

  ”Meye nake gani haka?”

Tayi tambayar tana bin hannun YAH BOSS da kallo ganinsa d’auke da abu cikin towel na jarirai fari sol…

  Murmushi yayi yana mik’a mata,ita ko cikin JIDDAH tabi da kallo,ganin alamun ba gizo idanunta ke yi mata ba ta amshi yaron fuskanta da tsananin farin ciki,tana fad’in
  ”Sannu doughter,masha Allah,Allah ya baki lafiya”

Shi ko gogan sai amshewa yake da ameen,fuskarnan sai doka murmushi yake uwa an masa bushara,bakinsa yak’i rufuwa…..

  Wani kallo MAMMY ta masa a kaikaice tace ”To sarkin fitsara,ya akayi ka san bata da lafiya?”

  Sosa kai ya shiga yi ba tare da ya iya bata amsa ba,yayi shiru..

  ”Allah ya kyauta,Allah kuma ya shiryamin ku”
  Tana gama fad’an haka ta mik’e ta nufi kitchen,ta shiga had’a mata abinci da masu jego suka fi buk’ata,dai² lokacin da ta fito ta nufi d’aki,ruwa ta tara sai turiri yake,duk abunda take suna zaune parlor sun tusa babyn a gaba suna kallo..
  Fita tayi tasa BABA mai gadi yasamo mata almajiri,aikensa tayi ya samo mata ganyen darbejiya,bai d’auki lokaciba ya dawo da shi da uban yawa,ta amsa ta sallame shi,shigowa tayi har ta wuce su ta dawo tana fad’in ”Doughter,taso ayi wanka ko?”

Mik’ewa tayi tana bin bayan MAMMY har toilet suka shiga,aiko nan ta zauna,MAMMY tana yarfa mata ruwan farko ta fasa ihuu ”Wayyoo YAYANAH zan mutu”

  Kamar an tsikare shi ya mik’e yana bin hanyar d’akin MAMMY,a bakin k’ofa ya tsaya yana jin yanda suke fama da MAMMY ita ko sai kuka take tana kiranshi..
Kasa jurewa yayi ya hau bugun k’ofar yana fad’in ”MAMMY dan Allah ki bar wankan nan,kar ki k’onata”
  Sai rok’onta yake,tayi masa banza,sai da ta k’are wankan,sannan ta fito ta barta ta k’arasa..

  A bakin k’ofa ta tarar da shi yana d’auke da babyn,harara ta watsa masa ta fice ta barshi nan..

   Da k’yar ta iya zama cikin ruwan zafin ta gasa jikinta,towel ta d’auro ta fito,sai narke fuska take uwa za tayi kuka,har lokacin yana bakin k’ofan,tana bud’ewa ko ya rik’ota har bakin bed yana shirin zaunar da ita tayi saurin mik’ewa
  ”Mene ne kuma HAYATEEY?”

STORY CONTINUES BELOW

”Barin k’arasa gyara jikina tukun”

”Ok toh baby”

”Ni ka dena cemin baby,nafa girma”
  Sai wani fari take yi,kuwa ba ita ta gama raki yanzun ba..

”Oohh!haka nefa,sorry toh baran sake fad’aba”
Ya fad’a yana murmushi..

  MAMMY ce ta shigo tana kallon ikon Allah tana shirin magana babyn ya fara kuka ”to rasai bani yaron na gyara shi,ga shima har ya fara kuka da gani yunwa yake ji”
Amsarsa tayi ta wanke shi tsaf,ta shirya shi cikin kayan sanyi masu kyau na jarirai,sai canyara kuka yake,JIDDAH ta kalla tana d’ora mata shi a cinya ”maza a bawa baby abinci kafin na dawo” ta fice daga d’akin..

  ‘Dago babyn tayi tana kallonsa tana murmushi,ita kam ma sai yanzun ta kalleshi sosai,ta shagala da kallon babyn tajiyo hannun YAH BOSS a cikin riganta,da sauri ta kalleshi…
  ”Haba HAYATEEY kina kallon yana kuka kin tsaya kallonsa,oyaa feed him”

Murmushi tayi lokacin da ya k’arasa fito da…… ya shiga sawa babyn a baki,lokacin da ya kama kuwa wata sabuwar azaba taji har tsakiyan kanta,ido ta rufe tana cije lip enta,wani ihuu tasa tana kallon YAH BOSS
”Tabbbb wallahi YAYA da zafi,in ba sai dai a hak’ura da bashi abincin,dan ni dai baran iya ba gaskiya”
Tana fad’a koh ta fito da abunta daga bakin babyn,shi ko kuka yasa jin an yanke masa jin dad’insa sosai yake kuka ko takansa bata biba ta maida cikin riga..

”A’a HAYATEEY hak’uri fa za kiyi,kinga shi ne abin da zai ci ya rayu,kin ga yana kuka,ki tausaya masa mana”

”Nifa gaskiya YAYA ka denamin dad’in baki,dan bazan iyaba gaskiya,sai dai a bashi madara”

  Idanunsa ya zaro yana fad’in
”Madara fa kikace baby”

”Eeehh!mana ai abinci ne shima”

Suna tsaka da jayayya MAMMY ta dawo ta tarar da su a haka,shi yana lallab’ata ita ko tana k’i,kallon tuhuma tayi musu ganin sunyi tsuru-tsuru
”Kin bashi abincin ne?na ga har yanzun yana kuka”

   ”Yawwa MAMMY gara kisa bakima wallahi,wai ba zata ba shiba ita zafi,wai sai dai a bashi madara”

”Zancen banza kenan,kin bashi ko kuwa sai na sab’a miki?haka aka miki ke?”
Ba shiri ta shiga kiciniyar fito da shi tana matsar k’wallah,ta sanya mishi a baki take ya sake yin shiru ya hau tsotsa,haka ya ci gaba da sha,ita ko azaban da take ji ya hanata magana,yana saki ta samu sa’ida…

  A bincin dake hannun MAMMY ta ajiye tana fad’in ”ga shi nan ki tabbata kin cinye kafin na dawo”

”HAYATEEY taho na baki kinji”
  Harara ta watsa masa ta zame ta kwanta,tana rufe ido sauran hawayen dake ciki suka k’arasa zubowa..
Tasowa yayi ya d’agata yana fad’in  ”yi hak’uri ki taso ki ci abinci kin ji,kinga in ba haka ba,babyn baze samu abin da zai ciba nan gaba”
  ”Ni ka kyale ni,bacci zanyi,bayan fad’an da kuka jawomin,za ka wani dame ni da maganar abinci,baran ci ba en,ai dai ciki nane ko?to ban ci”,haka yayi ta fama da ita ta k’i..
  ”Ok toh barin kirawo MAMMY”

Da sauri ta rik’e shi ”A’a karka kirata zan ci to naji”,murmushi yayi ya d’auko ya shiga bata da haka har ta ci da yawa,sai da yaga alamun ta k’oshi sannan ya kyaleta…

  Wayanta ta d’auko dake ring tana karawa a kunne da sallama
”To mara mmm shi ne babu labari kin haihunma?”
”Ke ni rabu da ni,wane labari zan baki banda azaba da nake ta sha tun da na haihun”
Dariya taita mata ita ko tayi k’wafa tana fad’in
”Bashi a gidan b’arawo rance ne”
‘Dif ta kashe,tana kwanciya…

  Kafin wani lokaci gidan har ya fara cika da jama’a wad’anda MAMMY ta sanar da su haihuwar JIDDAN…
Sai baccinta take hankali kwance,shi ko ANGON K’ARNI yana zaune zaman gadinsu,shigowar da MAMMY tayi haka ta tarar ya buga tagumi yana kallonsu yana murmushi..

STORY CONTINUES BELOW

BABYN ta d’auka za ta fita, ”MAMMY ina kuma zaki kai shi?”

”Gidanku” ta masa dak’uwa tana yin gaba da fad’in
”Siyar da shi zanyi”
Ta fice ta barshi yana sosa k’eya..

  ”Wai kam MAMMY ina mai jegon ne?”
Fad’in LITTLE da tazo tun d’azun..

”Tana bacci”

”Haaa!zama ta tashi ne wollahi” ta nufi hanyan d’akin

”Allah baki ikon tashinta”

Da shi ta soma arba tana bud’e k’ofan d’akin,aiko bata k’arasaba ta rufe ta dawo,MAMMY ce ta kalleta tana d’an murmushi ba tace komaiba.MAMMY ai sai ki cemin yana ciki…
”Waye a acikin?” ta tambaya uwa bata sani ba, ”YAH BOSS mana”.
”Au wai da gaske wannan sunan har yanzun kuna fad’ar sa?”

”Uhmm!” kad’ai ta iya cewa,taja baki tayi shiru..

Suna tsaka da fira gidan a cike,DADDY ya shigo kana kallonsa kasan yana cikin tsananin farin ciki,aiko MAMMY ta bi bayanshi hannunta d’auke da BABYN,a parlornsa ta tarar da shi,hannu kad’ai ya mik’a mata,ta bashi tana murmushi,kallon yaron yayi yana murmushi,sai yake ganin uwa JABEER ensa ne yana jinjiri,saboda tsananin kama da suke da yaron..
”An masa khud’ba?”
Abunda ya iya tambaya kenan

”Barin tambaya inji,dan yaron nan akwai shi da shiririta wollahi”

K’asa ta sauka,har lokacin yana zaune,
”Ka yiwa yaron khud’ba kuwa?”,ta tambayeshi,juyowa yayi yana kad’a mata kai ”A’a, daman DADDY nake jira ya dawo”,fita tayi ta koma don sanar da DADDY halin da ake ciki,haka ya masa kiran sallah had’e da khud’ba,ya kuma ambace shi da MUHAMMAD AL’AMEEN…

  Tashi tayi tana mik’a,juyowan da za tayi suka had’a ido,murmushi ya sakar mata yana matsowa inda take,k’ok’arin sauka tayi daga gadon,ya rik’ota
”haba mana HAYATEEY fushin ne baki gama ba har yanzun?”,
A kan k’afarsa ya zaunar da ita yana rungumeta tsam a jikinsa,ko kad’an ya hana mata ta tashi,magana yake shirin yi,MAMMY ta shigo d’akin
”Me zan gani ni y’asu?maza tashi ka fice kafin na b’ata maka rai fitsararren banza”,nan ta kore shi,yana fita ta juyo kan JIDDAH da take ta faman sadda kai k’asa, ”ke kuma idan baki daina shige masa ba ke zai baro,kina fama da d’anyan jego kya dad’a kwaso wani cikin”,ai kuwa jin haka jikinta ya dad’a lak’was..
Haka MAMMY ta barta duk tunani ya dabaibayeta…

Tun daga ranar kuwa ta shiga taka tsantsan,ko kusa da shi bata yarda taje,duk iya yinsa har ya hak’ura ya zuba mata ido,kullum kuma a cikin gidan yake kwana,amma har yau MAMMY bata ankara ba…

  Ranar suna kuwa anyi shagali dan uwa za a sake aurensu haka aka gudanar da taron suna,jama’a da dama sun halarci gurin, taron suna yayi albarka sosai,mai jego da d’ansu AL’AMIN sun samu kyaututtuka na ban mamaki…
  Nan HUBBEEY ta zo sai fama take da laulayi,suko sai dariya suke mata,suna tsokanarta da ta harbu….

   Kowa ya shiga ya fita,situru sunyi kuka,dan kamar biki ake haka taron ya kasance,da yamma ko aka wuce gurin walimar sunan inda aka gudanar da ita a *THE APICENT* taron da ya samu halarta manyan mutane,a nan DADDY ya gabatar musu da kyaututtukansa inda ya mallakawa JIDDAH da LITTLE manyan motoci k’irar MATRIX kowacce colour en tata daban,sai godiya ake ta tayasu,nan DADDY ya kuma sanar da jama’a cewa wannan taron ba iya taron walimar haihuwan takwaransa bane,har da taron walimar taya iyaye ga jaririn murnar bud’e sabon asibitin da aka jima ana aikinsa,nan aka kira JABEER a matsayin shugaba na asibitin tare kuma da gabatar dashi ga sauran mutanen gurin…
  Haka taro ya watse anata sam barka,kowa ya nufi gidansa cike da gajiya…

Haka rayuwarsu ta ci gaba da gangarawa cike da nasarori ta ko wane b’angare,ko wane gida idan zaka shiga sai rayuwarsu ta baka sha’awa saboda yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da so da kuma girmama juna,abun gwanin burgewa….

STORY CONTINUES BELOW

Tsawon sati hud’u kenan da haihuwarta,jaririnsu ya dad’a girma iya wad’annan kwanakin,sam ya dena zuwa kusa da ita,idan yazo k’ark’ari ya ga baby,haka zai raba dare yana masa wasa,idan yayi bacci kuma ya kaishi d’akin ya kwantar,mafi yawan lokaci idan ya shiga haka zai ganta tayi bacci,sai dai ya k’are mata kallo ya gama had’iyan yahu yayi gaba..

  Yauma shigowa yayi da niyyan kwantar da baby AL’AMEEN,ji yayi bazai iya hak’uri ba ganin wani azababben kyau da ta dad’a,ai ko ya kwantar da shi ya hauro kan gadon,cikin bacci taji ana shafa mata jiki,da sauri ta bud’e ido a hankali,ganina kusa da  ita a tsorace ta kalleshi tana fiddo idanu waje,sai jaa baya take,biyota ya shiga yi
”Please HAYATEEY hak’urina ya gaza,duk iya yina akan nayi nesa dake na kasa,pleasee ki taimakeni,ina cikin wani hali komai zai iya faruwa da ni”

”Ni gaskiya YAYA kayi hak’uri,wallahi ina jin tsoron abunda zai faru”
Ci gaba yayi da bata hak’uri,duk hanyar da ya biyo za ta doje,ganin ta k’i yarda yasa ya mik’e a fusace,zuciyarsa na sak’a masa plan en da yasan muddin yayi amfani da shi yasan baza ta k’iba,nunata ya shiga yi da yatsa
”Ni kikaiwa haka ko?to ki rik’e abunki,zanje waje na nema da kud’ina”,juyawa yayi zai fita yana wani murmushin mugunta…….
  Da gudu ta taso ta rungumeshi ta baya,hawaye har sun fara zuba daga idanunta,”Pleasse YAYANAH karkamin haka,ko da can baka nemi matan waje bare yanzun,wollahi na yarda koma mene kayi amma kamin alk’awarin bazaka tab’a neman wata a waje ba”

Yana jin yadda kukanta ke ratsa masa zuciya,amma sai ya dake yana k’ok’arin k’wace jikinsa,sai wani pretending yake mata,shi a dole ta k’yale shi,baya so…

  Sosai take kuka,ganin da gaske yake ta zagayo ta gabansa suna fuskantar juna,bata jira komaiba ta had’e bakinsu guri d’aya,nata salon ta shiga aika masa da ya sa shi shiga shock sai da ta gama birkita masa lissafi sannan da k’yar suka zube saman bed,sun nunawa juna yanda suka yi missing kansu,sun raya daren cike da so da k’aunar juna,kafin bacci yayi gaba da su…

*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[8:49PM, 5/1/2018] rєαl ѕmαѕhєr💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI……*      
             _{ơŋɛ’ʂ Ɩlıʄɛ…}_
                  💠💠
                     🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*

*©® 2018.*
      *1/mąყ,2018.*

*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ…*
         *ცყ.*

_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._

*~__________________________~*

     *ADDU’O’IN ‘DAGOWA DAGA RUKU’U.*

    _SAMI’ALLAHU LIMAN HAMIDAH.._

    _RABBANA WALAKAL HAMD,HAMDAN KHASIYRAN,’DAYYIBAN MUBARAKAN FIYH.._

             HISNUL-MUSLIM.
*~__________________________~*
  *GAISUWA TA MUSAMMAN Y’AN UWA RABIN RUHI,WOLLAH INA MATUK’AR K’AUNARKU..* 💔💔💔💔

_AUNTY KHADIJA MMN K²_
_AUNTY HASSY (GOLDEN VOICE)_
_AMINA HARUNA HALLIRU (MEINERH)_
_AMINA SALIS MUSA (LITTLE)_
_HABIBA IDREES (HUBBEY)_
_SAFIYA BALA (MOM HANAN)_
_MURJA SALIS (NA’IKKE)_
_HAFSAT MAI SHERRIF_
_FATIMA IBRAHIM (MUNEERAH)_
_AYUSHA ILYAS_

_HALISSA ADAMOU (MY LISSA)_
_KHADIJA S DOGARAI (LIPTON)_
_HALIMATU SADIYA MUH’D (LEEMA)_
_RABI’ATU ADAM MUHAMMAD_
_AUSHA ABDULLAHI ABUBAKAR_
_HUSSAINA HUSSAIN TIJJANI_
_AISHA SHEHU JIBRIL (MOM IRFAN)_
_RAMLATU NURA (MMN KHAIRAT)_
_REAL MAE DAMBU._
_AUNTY MAIMOUNATH_
_RUQAYYA HASSAN UTHMAN_
_FATIMA A¹ (PHERTEENJEEY)_
_FATIMA A² (FATEEY AFIRST)_
_QUEEN HAFSY_
_HAUWA (QUEEN HAUSEY)_
_BILKISU M.ADAM (Y’AR ABBA)_
_QUEEN ACID_
_MARDIYYA M²_
_AISHA WHITE (DOUGHTEEY)_
_MAMAN BOY_
_KHADIJA DEE_
_PRINCESS ESHAT AYSM_
_AISHA SADA MACIKA_
_HAWWER A SARKI (NAMECY)_
_REAL NASBASH_
_BILLY S FARI_
_FA’IXA (ANFA)_
_FAUZIYYA._
_MUHIBBAT INDIA_
_AYUSHA_
_FATEEY TAMBARIY_
_AISHA A.YABO (FULANI)_
_KHADIJA SALEEHU (MY DEEZOH)._
_RAHEEMA_
_REAL RAHAMA NA LELE_
_AISHA ISAH (MUMMYS FRIEND)_
_SAWWAMA A_
_HEARMEEBRAERH._
_SARAH ADIYA (SARARA)_
_SUMMY NICE_
_AYUSHER MUHAMMAD_
_DIDILURV_
_NUSAIBA GENTLE LADY_

STORY CONTINUES BELOW

*_ARADU WANNAN SHAFI YAYI MUKU KA’DAN SABODA YAWANKU,ALLAH YABAR ZUMUNCI,MU KASANCE HAR A ALJANNAH…_* *ONE LUV MY PEPS* 👌💓
*~_________________________~*
                                     
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)……..*

          🔚
🔚              🔚

         🔚

*℘ąɠɛ 99↔END.*
  Haka suka shafe ragowar kwanakinsu,duk ranar da yaji bazai iya hak’uriba zai lallab’a ya kwashi gara abunsa,coz satinta biyu da haihuwa ta samu tsarki,kwana suke farantawa juna rai,asuba nayi zai lallab’a ya fice,ba shi zai dawo ba sai gari ya gama wayewa…

Ana gobe zasu cika kwana arba’in suna tsaka da faranta ran junansu,wanda sunyi nisa cikin wata duniya ta daban,
MAMMY ta shigo lokacinma ko AL’AMEEN ta shigo kawo mata shima ranan akasi aka samu yayi bacci ya tashi dan ko gurinta ya koma kwana,salati tasa wanda ya jawo hankalinsu,cike da tsananin kunya JIDDAH ta k’udundune cikin bargo,shiko ficewa yayi yana sauke kai yak’i yadda su had’a ido..

  Ajiye mata shi tayi ta fice bata ce komaiba,sai da ta tabbatar ta fita sannan ta tashi ta d’auke shi,yaro yayi k’ato da shi,gwanin sha’awa,ta gama bashi abincin tasa shi a kafad’anta har yayi gyatsa,ci gaba tayi da jijjigashi har bacci ya d’aukeshi,aiko ta kwantar da shi tana kallonsa,sam ranar tak’i mai dashi gurin MAMMY k’arshe a gurinta ya kwana,ranan kam YAH BOSS tun da ya fice bai dawo ba,direct gidansu da tun ranar da jiddah ta baro shi,shima bai k’ara kwana cikinsa ba,sai dai yaje ya duba ya fito,gyara yasa akayi sosai an kwashe komai an sauya gidan ya koma uwa sabo saboda gyaran da ya sha…
  Shi kad’ai idan ya kalli gyaran da akayi sai yayi mirmushi,yana ayyanawa a ransa,gobe zai kasance da HAYATEEYNSA babu abunda zai k’ara rabasu.Haka ya wuni shi kad’ai sai tunani yake,k’arshe sai nan ya kwana saboda kunya yake ya koma gida su had’u da MAMMY,duk kewarta ta cika masa ko ina na jikinsa..

  Aiko babu shiri MAMMY ta tattara kayansu washe gari,tun da safe ta rattabawa JABEER en kira, ”Maza rasai kazo ka kwashe matarka da d’anka kubarmin gida,ina nan ina jiranka”….
  Ta kashe wayan…
  Ko minti ashirin bata yiba,sai gashi cikin wata dakakkiyar shaddarsa sai k’amshi yake bazawa,yana ta uban murmushi.Sam yak’i yarda su had’a ido da MAMMY..

  Haka MAMMY ta sallamesu ta kuma had’asu da mai rainon AL’AMIN en suka k’ara gaba,cike da d’oki suke tafiya,ko kulawa da mai rainon ba suyiba suke ta harkokin gabansu har suka k’arasa gida,haka suka ci gaba da kula da AL’AMIN cikin so da k’auna.

          *ONE YEAR LEAP.*

Haihuwan AL’AMIN da shekara d’aya,bakin CONVOCCATION ARENA dake cikin BAYERO UNIVERSITY KANO cike gurin yake da dandazon mutane tamkar ranar idi,hakan ya ganar dani taron yaye d’alibai ake…

  Cikin GRADUATION GOWN blue da ratsin purple a wuyansu suka fito,fuskokinsu na nuna tsantsan farin ciki,nufo gurin da y’an uwa da abokan arziki suka yi kowacce fuskarta kar da annashuwa…
    Anyi taro lafiya an watse lapia kowa ya d’auka hanyan gida cike da murnan wannan rana mai cike da tarihi mara misaltuwa…

  Shekaran AL’AMIN d’aya da watanni uku,wanda yayi dai² watanni uku da kammala karatunsu har sunje CAMP sun fito,inda DADDY ya shiga ya fita aka barsu a nan cikin kano,nan JIDDAH ta soma sabon laulayi,bata wani tashi hankalintaba,coz tasan yadda yake da k’aunar yara,hakan yasa tayi tunanin babu wata hanya da zata kyautata masa sama da cika masa gidan da yara….
  Shiko YAH BOSS ko da ya gane tana d’auke da juna biyu murna yaita yi abunsa,data sanar da shi kuwa nan taga tsantsar murna ganin yanda yake farin ciki,itama ta shiga tayashi,ta kuma ci gaba da rainon cikin jikinta,take ko YAH BOSS yasa ta yaye AL’AMIN ya maida shi gurin MAMMY duk da dama ya saba da ita sosai,kuma ba wani yini a gidan ba…

STORY CONTINUES BELOW

  Zuwa wannan lokacin ko HUBBEEY ta haihu da d’anta namiji mai kama ABBANSA,k’ato da shi uwa d’an turawa mai sunan ABBAN HUBBEEY suna ce masa AYMAN….

  Rayuwarsu mai cike da tsabta haka lokaci yaci gaba wucewa cike da nasarori ta ko wane b’angare,ko wane gida idan zaka shiga sai rayuwarsu ta baka sha’awa saboda yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da so da kuma girmama juna,abun gwanin  da tsabta…….

        *SOME MONTHS LEAP.*

  Zaune take da cikinta da ya soma tsufa,wayanta tayi k’ara,sunan LITTLE ta gani yana lilo akai wacce a yanzu ta zama BIG MAMA..
  ”Hellooo MAMAN UKU”
”Ke rufan asiri d’ayan ma na iya saukewa bare har kikemin fatan uku,ya baby ZAHRA?”

”Kinganta tana ta faman jan wayanma wai sai na bata ta miki magana”

  ”Allah sarki babyna,ina kewanki”

”Uhmm!nace anjima zamu zofa kinsan zamu je gida kan kayan IKRAM da za a kawo ko?”

”Eehhh! haka ne amma sai YAH BOSS ya dawo”

  Karaf a kunnensa lokacin yana shigowa ya dawo daga aiki a gajiye,wani murmushi yayi yana k’arasowa kusa da ita…

  Maganarsa kad’ai taji,dan bata ji shigowarsa ba,dai² tana ajiye wayan taji muryarsa yana fad’in  ”Ke da wa kike waya?”

”Har d’an tsoro ya bata,ta juya tana kallonsa,harfa ka bani tsoro”
  ”Eyyeerrrhh!sorry HAYATEEY”

”Ammm! YAYANAH anjimafa zamu gidan MAMMY ina fatan baka mantaba?”

  Ummm!
Har ya juya ya dawo
  ”HAYATEEY yau kam sai kin fad’amin waye YAH BOSS ennan,na jima inajin kuna fad’a,idan  na tambaya amin wayo,to yau kam babu wani wayo da zakimin sai naji”

”Pardon HABEEBEY,Allah bansan me zan ce maka ba”

”Akan wannan en ne baki sani ba?tambaya nefa kawai ehh ne ko a’a fa kawai”

”Ni dai Allah ban san me zan ce maka ba”

”It’s ok” ya furta yana d’aukan wayanta,kiran da ta amsa last ya bi yasa a handsfree..

  ”Hello madam ta YAH BOSS sha alwashi”..
Bata k’arasaba ya katse kiran,dan ko ya gama fahimtar ko waye mamallakin sunan,juyowa ya kalleta yana murmushi
  ”No more hidden again”

  A d’an tsorace ta d’ago ta kalle shi,ganin irin kallon da yake mata,da kuma murmushin dake kan fuskarsa yasa ta yi wata sanyayyar ajiyar zuciya…
Gefen bed en ya zauna yana kallonta,har lokacin ta kasa magana,kansa ya d’ora akan k’afafunta da suke mik’e,cikinta ya dad’a girma,uwa wacce za ta haifi yan uku….
  ”HAYATEEY wato ni nema BOSS koh?”

”Allah YAYANAH”……
Shiiiiiiiii
Ya d’ora hannunsa kan lips enta,”ban son jin komai”

”Da gaske?”
Da murnarta tayi maganar tana kallonsa,kai ya kad’a mata yana lumshe ido uwa mai jin bacci..

  Cikin kansa ta nutsa yatsunta ta shiga sosa masa suman kansa,shiko ya dad’a gyara kwanciyansa a jikinta…
  ”HABEEBEY bacci kuma za kayi?”

”Eehhh HAYATEEY,amma ba jimawa zanba”
”Ok tamm!”
Har tayi shiru kuma ta furta
”Ammmm!HABEEBEY kasan mesa muke ce maka YAH BOSS?”
Tana y’ar dariya tayi maganar…

‘Dagowa yayi yana juyowa
”Sai kin fad’amin yanzun,duk da farko banso tambayar dalilinba,coz naga kin tsorata,amma tunda kinyi niyya oyaah tell me”

”Allah HABEEBEY koh yanda kake had’e fuska da har tsoron mu had’u nake,barinma ace ni kad’ai,uhmmmmm nafa jima ina tsoronka”

”Me yasa HAYATEEY?”
  ”Yanda kake tsare gida ina mutum ya isa yayi wani k’wak’wk’waran motsima,shi yasa fa muke ce maka YAH BOSS,coz baka son raini”….

  Dariya yayi mai isarsa,sannan ya kalleta
”To ae HAYATEEY kinma bawa kanki amsa kinga ni raini ne bana so,amma yanzun ae kin san waye ni ko?”
Ya tambaya yana mata winking…

Dariya tasa kafin ta ce ”Sosai ma kuwa,ai sai dai na bada labari”

”Uhmmmm! HAYATEEY kenan wai tsorona kike,kamar wani dodo”

”Yo HABEEBEY ae kai en ne lokacin fa ko dariya ba kayi a gabanmu,ko saboda mene ohooo!”

  Dai² kunnenta ya kai bakinsa,”kin fa riga kin san dalilin raini ne bana so”
Tab’e baki tayi,”ni fa har yanzun ban daina jin tsoronka ba”
  ”Da gaske?”

”Ehhh!mana”
”Me ya janyo hakan to ?”

Kamar mai tunani ta d’an karkace kai gefe,kafin ta kalleshi idanunta har sun fara canza colour
  ”HABEEBEY za ka iya tuna wata rana da wata yarinya ta zuba maka ruwa,a bakin wani eatry?”

Kallonta kad’ai ya shiga yi,yayin da k’wak’walwarsa ta tafi aikin tunanin wannan al’amarin,ko kafin ya kai ga yin magana ta katse shi da fad’in
  ”Ni ce dai wannan yarinyar da nake cikin daud’a da rashin gata,ni ce wannan yarinyar da ta watsa maka ruwa a rashin sani,ni ce kuma wannan yarinyar da ka fidda hannu ka tsinkawa mari,a dai² lokacin da nake neman d’auki”……
Kuka ne ya ci k’arfinta,maganar na rabewa,ita kuma tana ci gaba da k’ok’arin magana..
  Da sauri ya janyota jikinsa,yana mai rufe mata baki da hannu…
  Hannunsa ta zare daga bakinta tana goge fuskarta,”Tun a wannan ranar tsoronka ya shigeni sai ina ganin kamar ko wane lokaci zaka kumamin abunda yafi na had’uwarmu ta farko,duk da k’arancin shekaruna,sai dai kuma daga baya ka sauya min tunani na,ta hanyar nunamin k’auna wacce ban tab’a tsammaniba”
  Ta d’an dakata tana murmushi,murmushin shima yayi duk da kuwa magaganunta sun sa yaji jikinsa yayi sanyi,lallai dole ne sai ya dad’a jajircewa ta inda zai mantar da ita wannan tunanin,dad’a k’ank’ameta yayi,a kunnenta ya shiga fad’a mata kalamai masu sanyaya zuciya duk dan ya mantar da ita maganar da ta d’auko masa….

”Na gode HABEEBEY da nunamin tsantsar k’aunar da ban tab’a tunanin samunta daga kowa ba,Allah ya biyaku da mafificin sakamako”

”Ameen HAYATEEYNA”

  ”Amma ban son wannan maganar kinji?ko dan halin da kike ciki,ba’a son mace mai ciki da damuwa,kin fahimta?”

  Kai ta kad’a masa

Kallon juna suka tsaya yi na wani lokaci,kafin ya dad’a matsowa,cikin kunnenta ya rad’a mata
  ”HAYATEEY barin miki gyara yanzun”

   Tana dariya ta furta
”Allah ko HABEEBEY na yafe gyarankan nan,coz duk lokacin da za kamin gyara nasan k’arshe result en baya wuce”………

Saurin toshe nata baki yayi,yana mata dariya
  ”Aifa kam HAYATEEY sai nayi gyaran nan”

”Ni dai kam na yafe gyaran nan naka”
Sai narke fuska take
Cike da shagwab’a shima ya furta
  ”Uhmmm uhmmm nifa sai nayi”

K’ok’arin ture kansa gefe tayi,shi ko sai dad’a matsowa yake,suna ta dariya abunsu,da haka har ya samu yayi winning akanta,inda labari ya canja salo suka lula cikin duniyar MARS……………….

   _Sai kuma fatan Allah ya sauketa lafiya…………_

  *ALHAMDULILLAH!*
     *ALHAMDULILLAH!!*
         *ALHAMDULILLAH!!!*

_Anan na kawo k’arshen wannan novel na *RAYUWAR WANI* inda nayi kuskure ubangiji ya yafemin,inda kuma nayi dai² ubangiji ya had’amu a ladan…._
  _Sai kuma mun had’u a cigaban novel ena da na riga na fara wato *Y’AR GARUWA* da yardar Allah,ina muku fatan alkhairi masoya a duk inda kuke cikin duniyar nan,Allah ya sadamu da alkhairinsa….Ameeen._
   *FOR CORRECTION OR COMMENTS JUST CONTACT ME*
         *@08165726609*

   _Taku har kullum nake muku fatan alkhairi._

*_~TEAM J²~_*

*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *