RAYUWAR ZAMANI (KO SON ZUCIYA) COMPLETE
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
_Na nawa masoyana wannan pejin kyauta, love you wujiga wujiga_…
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
1⃣♾2⃣
Sulaiman baiyi mamakin ganinta ahakan ba domin hakan dabiar tace, taku take cikin isa da gadara irinta ‘ya’yan masu kud’i y’a’yan masu hannu da shuni, Muhievert kenan yarinya fara doguwa kyakyawa, gata da k’ira mai kyau tsaruwarta ya zarce duk inda mutun ke tunani. Akance mutun ba komai yake iya samu ba arayuwa itakam Allah ya mata baiwar kyau kyaun jiki da k’ira mai kyau ba za’asa haskenta acikin abunda ya k’ara k’awata siffarta ba domin asalin kyau take dashi irin na mutanen Yobe, ga ilimi na addini dana zamani sai dai kuma abunda taji aranta shi takeson aikata wa sam-sam bata duba kyaunsa da rashinsa duk abunda take so shi take aikatawa.+
Sanye take cikin riga mai guntun hannu launin fari da kuma gajeren wando baki ta kama gashinta da bakin ribon ta mai dashi ta gaba sannan tayi irin kwalliyar daya dace da shigarta, rike take da d’an k’aramin jaka wanda ta saka jotter da biro aciki sai farin takalmi mai tsini. sam-sam ba zaka kalleta ka sata acikin jerin masu imani ba sai dai ahlul kitab domin batayi kama da wacce za’a cewa musulma ba.
Tafiya takeyi kamar wata hawainiya sai karairaya takeyi tana cin chewgum kamar wata karuwa tana isowa yayi saurin bud’e mata gidan baya kafin ya gaisheta ta amsa ciki-ciki, rufe mata k’ofan yayi da sauri sannan ya shiga ya ja tare da d’aukan hanyar Federal University Bauchi State muryar ta yaji tana cewa “ka tsaya a jifatu saboda akwai abunda zan saya ka kuma k’ara gudu kada nayi latti” ya amsa da “toh hajiya.
Suna isa bata tsaya ya gama parking ba kawai ta bud’e k’ofa ta fita, shi damuwarsa bai wuce da ace taji ciwo ba yanzu sai ta jawa mutun wani bala’in kamin ya gama tunanin har ta fito, abun mamaki ya ganta da sweet a hannu da sauri ya fita yana cewa “Hajiya akwai kaya a cikine?” ta amsa da “aa daman ga abunda naje saya” tana magana ta nuna mishi sweet din hannunta kafin ta shige mota, atakaice yaja d’an karamin tsaki shima ya shiga ya tada motan suka nufi hanyar makaranta aranshi yana cewa daman abunda yarinyan tazoyi kenan!
Yana zuwa yatarar dasu a falo, sallama yayi kafin ya nemi guri ya zauna ya shiga gaishesu, cikin kulawa suka amsa da fara’a kafin kannenshi suka gaida shi shima ya amsa tare da tambayar su yaya karatu? Sannan ya k’ara da tambayar ina Muhievert? Ammi ce ta amsa da cewa “ai kaima kasan bata kaiwa karfe takwas a gida indai ba tare da kwakwaran daliliba”.
Murmushi ya kirkiro kafin yace “hakane amma yau satin mu uku rabon damu ga juna kuma wai gidan mu d’aya tana matsayin kanwata atleast ba zata iya jira in dawo mu gaisa kafin ta rufe k’ofan d’akin nata ba? gaskiya Ammi ni banajin dadin abunnan ki saka baki ta dena shegen gantalinnan tunda shi dai Abbu bame zama bane ni keda alhakin kula dasu amma ni banganta bama balle insan ta ina zan fara gyarawa.
Abbu dake kwance akan sofa yana lallatsa naura me kwakwala yace “ni dai nagaji da magana kullun akan yarinyannan ban san dai ko sai ta
kasheni zataji dadi ba gashi dai Allah ya bamu ku dukanku masu hankali da natsuwa ilimin addini babu mai nuna muku sai dai ku nunawa wasu sai dai duk da haka Allah ne ya jarabce mu da halin Muhievert kuma abunda ya dace shine addua dan duk wani kokari munayi ni da Amminku da yayar taku amma abun nata sai gaba yakeyi” Raihan yace “haba Abbu dan Allah ka daina fadan haka mu dai mu cigaba dayi mata addua harta shiryu ta gane gaskiya, Zarah na school koh?” Ammi ta amsa da “eh yanzu ta fita itama wai tana da lecture din karfe tara ganin cewa zatayi latti yasa bata jira kun gaisa ba wad’annan kuma yau suna midterm break shiyasa basuje ba” Laure ce ta shigo tare da sallama ritsinawa tayi ta gaidasu sannan tace “Hajiya na kammala aikin akwai wani abunda zanyi ne” Ammi ta ce”okay toh bari inzo in duba nagode miki sannu da aiki zaki iya tafiya Sahura zatayi sauran” godiya Laure tayi sannan ta koma kitchen “ina kuma zataje Ammi?” Raihan ya tambaya “yau za’ayi bikin wata kawarta na islamiya kasan Laure da son zuwa biki shine ta nemi izinin zuwa” ajiyar zuciya kawai yayi yana tunanin Muhievert bai sake magana ba ya nufi dinning suma suka mara masa baya yau daga su sai yan samarin yaranta.
STORY CONTINUES BELOW
Suna isa makarantar sai ga tawagarta sun iso da sauri har suna rige rigen bud’e mata k’ofa, bayan ta fito ta tsaya musu kallon tara saura kwata amma bai dame suba tunda dai suna samun rabonsu a jikinta tsaki taja sannan tace “haba Slimzy wai meye haka kukeyi sai kace wasu ‘yayan kaji please behave mana” duk da maganan ya dan b’ata musu rai basu wani damu ba saboda sun riga sun saba da irin haka dan ba sabon abu bane a gurinta juyawa tayi ta kalli Sulaiman sannan tace “zaka iya tafiya idan nayi zan nemeka, ba tare da taji amsar saba tayi wucewar ta ko waiwayar sa bata sake ba.
“Muhievert kinsan cewa idan na shiga aji banason kowa ya kuma shiga ko? dan haka ki fita kafin ran kowa ya 6aci” kallonsa tayi atsanake kafin tace “tsaya tukunna wai ma meye matsalarka da latti na ko an saka gadi nane? In dai ba gadina aka saka ba saika rike damuwarka ka bar shiga nawa yanzu in shiga ne ko na fita dan banson matsala? takaici ne ya kamashi kawai ya tattara kayansa ya bar ajin.
Sulaiman bai tsaya jiranta ba kamar yanda tace zata neme shi idan ta gama mota yaja yayi wucewarsa dama yasan in ya tsaya jira shine dai zai sha zama jira gashi ko karyawa baiyi ba, yana zuwa ya samu har Laure ta ajiye musu da sauri ya wanko hannu ya d’auki nashi ya faraci dan gaskiya yunwa yakeji shi bai san ko tsutsan ciki ke gareshi ba dan yanzu ya fiye saurin jin yunwa.
Suna kammala breakfast yace dasu Abbu “Ni zan wuce office gashi har tara ya wuce kada na makara” Abbu yace “ok sai nazo dan inason in koma Yobe gobe akan wani aiki dana fara ga chan brief case dina ka wuce dashi, Allah kiyaye hanya” ya amsa da amen sannan ya fita.
Yana fita yaci karo da Sulaiman, tsayawa yayi suka gaisa sannan yace “ka kaita makarantan koh, ka cigaba da hakuri da ita dan Allah kamar yanda ka saba dan nasan cewa kana hakuri Allah ne zai shirya Muhievert” ajiyar zuciya yayi tare da d’an murmusawa kafin yace “bakomai wlh ranka ya dad’e ai yanzu an zama d’aya ni ina mata kallon kanwata ne, zaka wuce kenan ko inzo in kaika ne?” shima murmushi yayi sannan yace “ka barshi kawai sai na dawo kar abubuwa su maka yawa tunda zaka kai Abbu kuma ga ‘yar rigimata yanzu sai ta bullo da wani abun ka kula da gidan dan Allah” toh kawai yace mishi yana mamakin inda ita ‘yar rainin wayon ta samu halinta.
Ammi ce ta shiga kitchen dan ta kira su Sahura su zo su kwashe kayan da sukaci abincin tana shiga ta samu suna faman aiki zama tayi a kujeran dake jikin centre table din cikin kitchen din sannan tace “ina fata dai kunci abinci saboda na sanku yanzu zakuce sai kun gama komai da komai kafin kuyi karyawa”.
Jummai tace “Yau kam mun karya Hajiya sai dai hajiya karamace batayi kariba kuma har anyi duk abunda ta buk’ata” tsaki Ammi taja kafin tace “ku bar zancan yarinyarnan ita ta sani idan ma taga dama tayi ta zama da yunwa ni dai kuje ku gyara min dinning mun kammala” Kande tace “Hajiya kiyi hakuri ki rage fushi da ita dan Allah kawai kiyi ta mata addua insha Allahu watarana sai labari” murmushin takaici Ammi tayi kafin tace “Allah ya shirya mana zuri’a domin yanzu Rayuwar Zamani ya dukusar da tarbiyyan da muke kok’arin bawa yaran mu saboda Son Zuciya irin nasu”.
Suna fitowa daga lecture ta fito sai kace ana tura ta, da sauri ta nufi office din Prof Maisamari babu neman izini tayi shigewa abunta sai dai abunda ta gani shi yayi mugun daga mata hankali kuma ya razanata Malamin da ake mishi kallon mutumin kirki ana girmama shi ashe mugu ne azzalumi gashi yau ta kama shi dumu dumu yana aikata zina tare da wata matar aure wacce take ajinsu kuma wannan abu tasan ba zai wuce dan ta samu sakamako mai kyau ba, dadin ta d’aya basu san ma ta shiga ba kuma kila ya manta rufe k’ofan ne hakan yasa ta rufe tayi saurin fita ta samu guri ta zauna a k’ofar nashi sai da ta kusan awa tana zaune sannan matar ta fito tana waige-waige, duk kallon nata bata kula da Muhievert ba ta wuce tana murnar cewa ta haye babu sake zaman wannan jarabawan, ita kuma tana ganin matar ta tafi itama tayi tafiyarta dama danta rufa musu asiri shiyasa ta zauna (ina zaki damu duniya tabbas duniya abun tsoro ne yana rud’an d’an adam wannan shine abu mai girma dake faruwa cikin jami’a babu tsoron Allah matar aure zataje ta yaye mutuncin aurenta dan kawai abun duniya haka yan mata zasu lalata rayuwarsu dan samun abun duniya su bawa malamai kansu dan kawai suci jarabawa daganan kuma shikenan sun samu sana’a suna yaudaran kansu, iyayensu, mazajensu saboda Son Zuciya. ya Allah ka rufa mana asiri duniya da lahira kasa mufi k’arfin zuqatanmu malamai kuji tsoron Allah domin ance kama tudinu tudan duk abunda kayi za’a maka).
Yana shiga kowa ya tashi aka fara gaishe shi d’aga musu hannu kawai yayi sannan ya shiga lifter dan zuwa office dinshi a second floor ya fita yana shiga ya ajiye jakanshi sannan ya fita zuwa first floor inda office din Abbu yake bayan ya ajiye brief case din ya wuce third foor danyin supervision din ayyukan da akeyi a ranar.
Abbu na fitowa awanka ya kira sulaiman yace mishi idan yana gida ne ya jirashi yanzu zasuje office, bayan ya ajiye wayan ya shiga yayi wa Hajiya Rashida sallama sannan ya fice ya shige mota suka kama hanya kamfaninsa dake cikin garin Bauchi.
♾♾♾
Dan jakan uba wato tun safe kanata zuba barci sai kace kaza zaka fito ne ko sai na fito da kai mara mutunci ko ance maka gidan ubanka ne nan din?” tsaki yayi yana cewa “haba dan Allah Goggo ya zaki zo kina damun mutane da safe sai kace wata…”
Da sauri ta amsa da cewa “sai kace wata me dan ubanka, karasa mana fisararre ni bansan cewa haka uwarku Aisha ta koya muku ba tarbiyyan data baku kenan amma uban naka zai zo ya sameni ai mara kunyan banza.
Yatsine fuska yayi “toh in banda ke bama kinsan in ba dan ance nazo na duba ki na danyi kwana biyu ba kema kinsan ba abunda zai kawoni tunda bakya tsinanamin komai sai masifa da zagin iyayena na yau daban na gobe daban ni kam dama ke kika mutu ba kakanmu ba saboda shi kam baya takuramana kamar yanda kika tsanemu”.
Shuran daya matane ya dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga yace “ke kuwa Aisha meyasa kika shiga tunani haka? ba tare data kalleshi ba tace “wlh tunani na yaron nan kasan sam bayajin magana, sannan ba shiri suke da Goggo ba ni kam hankali na bai kwanta da zuwanshi ba, shiyasa tun farko naso ka aika Salma ko Sarah ko Kabir tunda Sulaiman bayanan sbd Hanif bayajin magana yanzu zai jawo mana wata fitinar”.
Malam yace ” hakane kam Hanif bayaji sai dai kuma shine dai-dai da zaman gidan Goggo ki kwantar da hankalinki rashin jin maganar shi zai sa su zauna lafiya”.
♾♾♾
Sharif ne ya doso inda su Slimzy suke yayi musu hy azarihin gaskiya shi dai friend din samra ne yana sonta sannan kuma yana son yaga ta shiryu amma abun yaci tura sabida yanda sauran ke hure mata kunne.
Dogone mai farfadan kirji, da ka ganshi kaga yanayi na hutu atare dashi yana da tsawo kuma yana da kaurin jiki gashi fari tas ya hadu dai-dai misali hasken su d’aya da Ilham kawar Muhievert dan sunfi Muhievert haske kyau kawai zata nuna musu da kuma kud’i. shigar farar riga yayi mai bakin rubutu ajiki inda aka rubuta (crazy boyz) da bakin wando yana karisowa yayi sallama duk ba wanda ya amsa amma hakan bai dame shi ba “little kin gama lectures ne inyi dropping dinki? kallon sama da k’asa tayi mishi sannan ta d’auke kai dan batason wa’azin da yake mata chan kuma tace “eh na gama muje amma ba gida zani ba sannan idan kasan zakamin surutun daka saba ne gwara ka kyaleni inbi wani hanyan” murmushi yayi yace “kiyi hakuri ba zanyi ba ranki ya dade” sannan suka nufi motarsa kirar venz
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Autan Hikima😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
3⃣♾4⃣
Raihan na komawa office ya aiki masinga akan yaje yace ma head din ko wani department yana son ganinsa aconference hall, babu 6ata lokaci duk yabi ya fadamusu kafin ya koma ya sanar da zuwansu.
Yana zaune a office kafin ya fara komai yaga hoton kannen nasa dake cikin karamin frame fuskar Muhievert ya shafa yace “I love you sister but you won’t understand why am always harsh toward you
change for good please (inasonki kanwata amma ba zaki gane mai yasa nake takuraki ba, dan Allah ki chanja hali)” ya fad’a yana murmushi sallaman Baba masinja ne ya katse mishi tunani bayan ya amsa masa sai yace ya duba mishi office din Abbu koya iso bai dade ba ya dawo yace ya iso, tashi yayi ya wuce conference hall bai kai minti goma ba yaji sun shigo, tashi yayi ya kira Abbu kafin ya dawo ya zauna ajerin kujerun da ke jikin babban table din babu dadewa Abbu ya fito atare suka tashi sai da ya zauna sannan suka gaisheshi suma suka zauna babu 6ata lokaci kowa ya gabatar da duk ayyukan da akayi acikin Department dinsa da yake duk sun saba da barin record hakan ya saukaka musu. k’ar6a Abbu yayi ya fara gani, inda za’ayi signing yayi inda yaga da bukatan karin bayani sai ya sake tambaya kafin Raihan yayi stamping sannan ya k’ara musu albashi daga kan k’ananan maaikatan zuwa manya kafinnan ya sallame su sosai sukayi murna tare da mishi fatan alkairi.
Ammi ce a kitchen tana dafa abinci dan duk kudin su bata wasa da damarta wajen yima mai gida girki in dai ba abunda yaran suke sonci ba duk wani girkin Abbu ita takeyi bata sakaci da hurumin mijinta tana aikinta tana ta salatin Manzo (s.a.w). Chan dai tayi shiru tana tunanin yarta kafin tayi ajiyar zuciya sai da ta gama komai ta kwashe na Abbu akularsa wanda yake daban dana yaran gida harma dana bak’i kafin ta kira kande cikin dadin murya ba cikin nuna isa ba tace idan sun gama gyaran cikin gidan su jera abincin a dining na Abbu su kai sama na yaran abari ak’asa sai su saka turaren wuta aduk kusurwan gidan domin ya fitarda kamshin daya shigo daga kitchen sai Ac shima su kunna dan kamshin ya bada abu mai dadi kafin ta wanke hannunta ta nufi sama.
Dakin Abbu ta shiga ta k’ara gyarawa tare da sanya turaren wuta sai d’akinta shima ta gyara ta saka turaren wuta ta kunna Ac kafin ta shiga band’aki ta wanke tas ta fesa airfreshner daganan ta shiga wanka tare dayin alwala fitowa ta shiga shafe shafen su humra don lokacin sallah bai karisa ba, kaya ta saka riga da zani mai manyan pattern wanda akayi design din jikin kayan da pattern din bayan tayi simple makeup ta duba agogo taga har lokacin salla yayi da sauri tasa hijab dinta tayi kabbara bayan ta idar ta dad’e tana yiwa iyayenta da yaranta da mijinta addu’a kafin ta tashi daga kan darduman. Tana idarwa taji horn din mota ajiye hijab din tayi ta fita danyi musu sannu da dawowa.
♾♾♾
Yana karasawa ya bar gurin da gudu saboda ya san halin Goggo sarai yanzun nan sai ta daka mai dundu, kama baki tayi tana cewa “yau ni dannan zai ce dama ni na mutu, lallai ubanka zai zo yatarar dani wato har ya haifi dan da zai iya fadamin haka da sauri ta kwalawa Ibro kira ta mika mishi waya ungo danno min layin balarabe yi abu da jiki maza-maza karka 6atamin lokaci” ringing daya biyu ya dauka yana cewa “hello Goggo” tace “elon ubanka, eh nace elon ubanka ko kanada magana ne” sai kuma ta fashe da kuka “wato d’an nan katuromin hatsabibin yaronnan saboda yazo ya cimin mutunci koh? ya zageni tatas daga ni har zuria ta balarabe kayi kokari da kai da wannan munafukar matar taka”.
Kukan data k’ara sawa ya d’aga hankalin Malam Balarabe arikice yace “haba Goggo dan Allah kiyi haku…” bata bari ya karasa ba tace “nace hakurin ubanka wallahi zan tsine maka tunda baka da mutunci” ta fada tana wurga wayan.
Goggo! Goggo!! Goggo!!! Da sauri ta fito tana cin goro tana kokarin gyara zaninta “nace lafiya daiko kake min kira haka ubana dan ko ubana ne kawai zai kirani irin haka banza gantalalle mara mutunci”
Hararanta yayi kafin yace “ba lafiya ba Goggo taya za’ayi ke kici abinci ki rage sannan wai inci? ai wannan ci bayane kawai cin abincin da kika rage haka kawai nasan ba wai wani wanke hannu kikayi ba kilama kinaci na bakin naki na komawa ciki but you’re expecting me to eat this haba ai wannan abincin dabbobi ne kawai zasu iya ci ni kuma kinga mutunne ba dan kuikuyo ba” salati Goggo tayi ta rike baki tana kallonsa har zata d’auko muciya ta bi bayansa sai kuma ta fasa tace “lalle dannan wuyanka yayi kauri ya isa yanka, wato nikake fadawa haka saboda ka mugun rainani wlh ba laifinka bane laifin uban kane daya aikoka kaci zarafina kuma na gode amma dan uwarka mai zakaci inba wannan din ba sai dai idan zaka dafa danwake inkuma ba haka ba sai dai fa ka kwana da yunwa”.
Hararanta yayi yace “cin abincin gidanki ko virus ni kinga tafiyata zanje naci indomie da kwai awajen mai shayi koba komai yafi wannan dattin tuwon da kika rage”.
Haushine ya kama Goggo kawai ta saka kuka tana cewa “oni yau naga yaro jarababbe aiko iyayenka zan sama duk sai naci mutuncin su”.
♾♾♾
Awani babban mall suka tsaya koda taga haka ba tace komai ba dan tasan suna da bukatan sayan kaya saboda haka itama ba tace kala ba ta fita suka shiga kantin, vibration din wayanta ne yasa ta tsaya ganin mai kiran yasa tayi murmushi.
“Hello darling brother my one and onl….” bai bari ta k’arasa ba azuciye ya amsa da cewa “waye darling din naki kina matsayin kanwata gida daya muke kwana muke tashi but you cant check on me kullun bana ganinki da safe, da dare kuma kinyi barci shin me kike nufi me kike tunani kina koyawa yan uwanki eh?”
Marairaicewa tayi kafin tace “Yaya plx am sowie yaukan zan jira ka dawo cox i really missed you dear kayi hakuri zan kiyaye ba zan sake haka ba kaji” ok kawai yace har zai kashe wayan sai kuma ya sake cewa “kar ki kuskura ki kai 6 awaje baki dawo gida ba” kafin ma ta amsa ya kashe ta6e baki ta ajiye wayan ta shiga ta iske harsun gama jakarta ta fitar ta cire makudan kudi ta mika musu sannan tace “gashi idan ya rage sai ku raba chanjin.
Zaune yake a farfajiyar gidansa yana shan iska Hajiya ta shigo rike da tray babba “barka da hutawa baban Raihana” murmushi yayi kafin yace “yawwa barka dai uwar ‘ya’yana wani beta kika had’omin tun dazu kamshi ke tashi? Alhaji kenan baka rabo da zolaya.
“Ammi me kika dafa mana” Zahra data dawo daga makaranta kenan ta hangosu a gurin shan iska shine ta nufi gurin dan ta gaishesu hannu ta mika zata bude flask din cikin zolaya Hajiya ta buge hannunta tana cewa “ban sani ba yar nema kije dinning naku yana chan “haba Ammi ni gaskya da Abbu zanci koh Abbuna? ya amsa mata da eh yana murmushi.
Ammi tace “haba dan Allah wallahi kai kake shagwaba su da yawa
saboda meye ba zataje gurin yan uwanta ba?.
“Yawwa ai naji dadin haka gwanda data zauna kinga Ammi shikenan sai in had’a da nata da nawa duk saina cinye” Raihan ya fad’a dan neman tsokala.
Ammi tace “gaskiya kam gwanda kayi hakan” aiko tanajin haka ta ta6e baki tayi kitchen aguje shima yabi bayanta yana dariya rufe kofan yayi, haka tayi ta ihun ya budeta amma yaki Ammi kam bata kulasu ba ta mijinta takeyi shi kuma Abbu bai kula ba sai da yazo shiga shine ya bude daya ganta yayi dariya kad’an yana bata hakuri dan yasan Zahra akwai daru.
“Hello kana inane kazo yanzu? a dayan bangaren Sulaiman yace “yanzu na ajiye su daddy agida “ok
na baka nanda mintina talatin karka kuskura ka wuce hakan kasameni a gidan Anty Raihana” tsaki yaji kasa kasa kafin yace “ok toh angama saina zo” tsaki tayi tace “karma kazo nidai na baka minti talatin.
Anty Raihana data tsura mata ido tace “kedai baki rabo da masifa toh Allah kyauta miki” dariya tayi tace “amen Anti ni kinsan bana son bata time” Anty Raihana tace “wai kwata
kwata minti nawa kika min daza kice nanda minti talatin” dariya tayi sannan tace “ahaba Anty wallahi na kai awa biyu kuma kinsan yau inason inga yan gida musanman yaya Raihan saboda 3wk kenan ban ganshi ba har gwara Zahra muna ganin juna a school su Yazid kam na manta when last muka had’u shiyasa zan koma da wuri Anty tace “lalle ma yarinyannan wai wato kinfi karfin kije gaida Raihan ne kafin ki fita school ko kuma what is the reason behind this your stupidity? ta6e baki tayi tace “kai dan Allah Anty ni banda tym ne shiyasa.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to my dear daughter pureheart (Fulani)
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
5⃣♾6⃣
Umma! Umma!! Da sauri Umma ta fito daga d’aki tana cewa “meye haka kuma kike kirana kamar anyi mutuwa ni har kinsa zuciyata tsinkewa?” Sarah dake kokarin rufe kyaure tace “Umma wlhy na samu Allah kuwa na samu Ummana ki tayani murna” ta fad’a tana taka rawa.
Umma dai ta rasa gane kan zancen Sarah kallo kawai take bin ta dashi kafin tace “kinsamu toh mai din kenan kika samu Sarah?”.
Sake daka tsalle tayi tana cewa “ahayye Umma na samu wayyo jama’a ina murna na haye ni Sarah”.
Rankwashinta Umma tayi tana cewa “banason rashin hankali Sarah zaki dawo cikin hankalinki ki fadamin meke faruwane ko kuma na wuce abuna?
+
Kanta ta mulmula tana cewa “kai Umma shine harda rankwashi to kiyi hakuri ni kawai dadi naji da akace na samu jamiar bauchi yanxu nazo wuce wa naji Abba da malam Habu suna maganar”.
Murna Umma itama tayi tana tace “Alhamdulillahi Allah abun godiya lailai naji dadin wannan abun Allah yasa ki fara a sa’a saura shirin tafiya kenan amma ina zaki zauna toh koda yake bari Malam ya shigo sai mu tattauna”.
Assalamu alaikum Aisha! Aisha!! Umma ta amsa da “naam Malam, sannu da dawowa” tabarma ta d’auko ta shimfid’a bayan ya zauna ya sha ruwan data kawo mishi sannan yace “Allah abun godiya wato Aisha yau ga abun alkairi na taimakon da muka samu daga Malam Habu mu dai sai dai mubi shi da addua”.
Gyara zama Umma tayi kafin tace “toh Malam ai ka sani aduhu kayimin bayani yanda zan gane”.
Murmushi Malam yayi sannan yace “wannan yarinyar ya sama wa makaranta achan jamiar bauchi kuma harya biya duk wani abunda ake biya yanzu saura ta fara zuwa karatu tare da cike wasu abubuwa ayanda ya fadamin”.
“Masha Allah mun gode wa Allah mun gode mishi ai haka akeso ka taimaki na kasa dakai gasky nayi murna Allah ya saka da alkairi ita kuma ya bata ikon fito da sakamako mai kyau”.
Sarah! Sarah!! Sarah dake la6e ajikin kofa ta amsa da “Naam Umma ganinan zuwa” bayan ta fito ta tsuguna agabansu ta gaida mahaifinta kafin Umma tayi mata bayanin abunda Malam ya shigo da shi kamar irin basu san komai akai ba.
Wani irin farin ciki ne ya bayyana afuskarya sai kace batasan da zancen ba kafin tace “Allah ya saka mishi da alkairi in nayi zanje inyi mishi godiya Abba” duk suka amsa da ameen kafin suka cigaba da zancen karatun nata da kuma inda zata zauna.
♾♾♾
Toh Anty sai kuma kinzo ko kuma dai sai na sake dawowa” Anty Raihana ta yatsine fuska tana cewa “Ni rufamin asiri ai Ammi ta bani lakacin zuwa gida idan na kuskura naje nan kwana kusa sai raina ya 6aci”.
Dariya Muhievert tayi kafin tace “ai maganinki kenan Anty if not nasan da har kwana zaki rinka zuwa kinayi tunda baban Nuwaira ba shida takura ke dai kinji dadi Anty sai dai kuma kinsan Ammi tana da gaskiya dan dai acikin tsari mai kyau bai dace matar aire tayita fitan ba gaira ba dalili ba in dai ba tare da wani kwakwaran dalili ba”.
STORY CONTINUES BELOW
Hararanta Anty Raihana tayi kafin tace “Naughty girl ki gaida su Abbu sai nazo din dai kawai idan yaso saiki yasani agaba kimin wa’azi, tukunna ji irin shigar da kikayi babu maraba da arna Allah dai ya shirya mana ke”.
Dariya tayi tana kokarin fita waje a haraban gidan taga motar daya zo dashi fa sauri ya fito ya bude mata motar ta shiga kafin ya rufe shima ya shiga mazaunin direba, glass din ta sauke tana cewa “bye Anty ki gaida uncle B da yarana idan sun dawo tell them i miss them” toh zasuji Anty Raihana ta fad’a kafin ta koma cikin gida.
Suna isa gida ya fito ya bud’e mata k’ofa ko kallo ma bai isheta ba ta d’au jakarta tayi wucewarta ko godiya babu shima ko ajikinshi domin inda sabo ya saba da hakan, gyara parking din motar yayi sannan yayi 6angarensu na masu aiki.
Babu kowa a falom sai kamshin turaren wuta mai dadi da kuma sanyin Ac dinning ta nufa ta fara bawa cikinta hakkinsa bayan ta gama ta d’auki jakarta ta nufi d’akinta, wanka ta farayi bayan ta fito tayi drying gashinta sannan ta shafa mai tayi kwalliya ta sanya wani karamin riga purple sai dogon wando fari sannan ta nufi sama dan ta gaida su Ammi.
Kamar kullun da sallama ta shiga bayan ta samu guri a kasa ta zauna ta fara gaida Abbu tare da tambayar yaushe zai tafi Yobe dan tanason ta tuna mishi da dak’on turarenta “gobe zan wuce kuma ban manta sakon naki ba dan nasan dalilin da yasa kika tambaya kenan” dan dariya tayi kafin ta gaida Ammi sannan suka d’an ta6a hira tare dayi mata nasiha as usuall ita dai kawai jinsu takeyi amma yana shiga yana fita ne koda yake in ta tashi ma agurin zata bar musu.
Bayan ta fito daga gurin su Abbu d’akin Zahra ta shiga inda ta ganta tana karatun alkur’ani kofar ta rufe ta wuce last floor din inda d’akinsu Yazeed da Adnan da ya Raihan suke dan dama first floor din shine nasu Ammi second nasu sai third na mazan saida ta fara shiga dakin Yazeed kasancewa shine karami shekaransa goma murmushi yayi mata tare da mamakin ganinta dan rabonsu da had’uwa tun sati biyu da suka wuce shima din yaje tambayan Anty Zahra wani abu ne shine ya ganta zata wuce school toh tun rabar bai sake sata a ido ba iskan data hura mishi a ido shi ya dawo dashi daga tunanin daya tafi “ya dai Autan Ammi ko kamanta kamannina ne kake kallo na haka” dariya yayi kafin ya gaisheta ta amsa cikin kulawa tare da tambayan shi ya school yace lafiya haka ta cigaba da mishi tambayoyi yana amsawa har karfe biyar yayi kafin ta wuce d’akin Adnan dan shekaru goma sha uku kallonta yayi da mamaki cikin zolaya yace “to fah su Anty Muhiee ce yau a gidan namu lailai munyi gamdakatar da babban rabo” dariya duk sukayi tace “toh uban maza da mata sarkin manyance ai dama nasan yanzu zata fara zuba da sharhi” dan murmushi yayi sannan yace “daga fadar gaskiya sai cibi ya zama kari abu kamar mak’ota wai sai an sha wahala ake ganinki ni kam banajin dadi wllhy Anty Muhiee gaskiya ki rinka bari ana haduwa ko sau daya a rana” ya fada yana marairaicewa “toh shikenan zanyi kokari mu rinka haduwa sau daya a sati ai hakan yayi maka ba” shekeke yake ganinta wai sati daya abun ma gwanin ban dariya ahaka suka cigaba da hiransu shima dai sai data mishi mintina talatin, biyar da rabi ta mishi sallama ta wuce d’akin babban yaya.
Knocking tayi sai da ya amsa mata sannan tayi sallama ta shiga bayan sun gaisa ta samu guri kusa dashi ta zauna ta fara bada hakuri da dadin baki yanda ta saba daker dai ya sauko yayi ta mata nasiha tare da nuna mata illar duk abunda takeyi musanman ma shigar da takeyi kamar dai ba diyar musulmai ba dabi’arta sam bai dace ba hakan zubar da martaba da kimar gidansu ne sosai yayita zuba yana shiga yana fita har shima ta mishi minti talatin sannan ta koma 6angarensu.
Dakin Zahra ta koma duk yaran gidan fararene na ban mamaki domin har sunfi Ammi haske dan shi Abbu ba wani haske ne dashi ba sai dai ba zaa sashi a sahin bakake ba kuma ba zaa sashi a sahun wankan tarwada ba yana da haske amma bai kai Ammi ba su kuma yaran sun zarce Ammi a haske sosai, Zahra ma kyakyawace dukansu suna kama da juna bama kamar Anty Raihana da Raihan da suke yan biyu kamanninsu kaman an tsaga kara sai Yazeed da Adnan suma kaman dai yan biyi banbancin girma na jiki da kuma shekaru ne sai Zahra da Muhiee suma sosai suke kama sai dai Muhiee tana da dimple Zahra kuma tana da hushirya dan tsawon nasu ma kusan daya ne.
Zama tayi a kan doguwar kujeran dake cikin dakin ta daura kafarta akan tebir din dake gurin har zuwa lokacin Zahra bata kammala karatun nata ba dan hadda sukeyi su Anty Raihana sun gama hadda sai su Zahra dake izifi arbain da biyar sai su Yazeed dake izifi talatin da biyar dan koda wasa Ammi bata tsaya sanya akan karatun addini ba shiyasa suma suka bada himma sosai.
Mintina goma tsakanin shigowarta Zahra tayi addua ta shafa tare da ajiye quranin sannan ta nade sallaya ta tattare sauran takardu sai da ta cire hijab din ta nade kafin ta gaida Muhievert wacce har ta fara barci akan kujeran amsawa tayi tare da tambayan ta ya karatu ta amsa da lafiya hira sukayi sosai wanda duk sukaji dadin kasancewa da juna a wannan rana sai da aka kira magrib sannan suka rabu ba dan suna so ba.
Washe gari da safe yaran sukayi shirin makaranta abun mamaki yau Muhie ce tayi musu breakfast dan sunji taste din girkin ta, sultan potato cracks tayi tare da shayi da yaji kayan kanshi da ferfesun kayan ciki sosai kowa yaci cikin farin ciki harda Abbu da Ammi yau suka hadu sukaci abinci sai santi sukeyi ita kanta taji dadi dataga suna cikin farin ciki sai dai wannan farin cikin nasu ba zai ta6a zama a haka ba ita kanta tanaso ta chanja amma ta kasa kuma ba zata iya chanjawa ba tafi jindadin ganin kanta cikin nishadi ba wai a yanda akeso aganta ba duk wani abunda tayi mara kyau ko mai kyau tana sane dashi ahaka suka gama cin abincin kafin suka yiwa Abbu rakiya zuwa airport Ya Raihan ke tukawa sai da suka ajiye Yazeed da Adnan a makarantarsu. Yazeed na primary five Adnan kuma na jss2 sai Zahra level1 tana karanta law sannan Muhievert da take level2 tana karanta medicine shekaran Zahra 18 Muhie kuma 20 sai Ya Raihan da Anty Raihana da suke ishirin da biyar Raihana journalist ce tana aikin jarida shi kuma Raihan engineering yayi inda yake aiki acikin kamfaninsu na RAMZRY Company wanda ya hada sunan yaran gidan baki daya, yana ajiye su Zahra a Federal University ya wuce office shima akan idan ya tashi yau shi zai mai dasu gida dan tare sukace zasu fito daga lectures (yau su Muhiee za’ayi abun kai).
Yau dai Sulaiman ya huta kamar yanda sukace haka ne ya kasance inda ya Raihan ya dauko su kafin suka bi suka dauki su Yazeed sannan suka wuce babban plaza na RAMZRY bayan sunyi sayayya suka wuce gida direct. A falo suka hadu da Ammi tana kokarin zama a kan sofa da gudu su Adnan sukaje sukayi hugging dinta su Zahra na musu dariya kafin suka zauna suna gaida Ammi ta amsa musu da kulawa tare da nuna jindadin ganinsu tare sai da suka dan ta6a hira suka sata farin ciki kafin suka wuce dakunansu dan hutawa.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Mrs Noor😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
7⃣♾8⃣
Alhaji Hamza d’ane ga malam mahdi, ‘ya’ya biyu Allah ya ba mahdi wato Hamza da Muhievert (Goggo Hama) tun suna k’anana mahaifyarsu ta rasu wanda asanadiyyan hakanne mahaifinsu ya kamu da ciwon zuciya, ana cikin haka wata rana kawunsu Sagir yazo dan duba jikin Malam Mahdi ganin yanda jikin yayan nasa yake yasa ya dauke shi dan zuwa kauyensu a cikin jihar Yobe wato Fika dan sama masa magani. Daya tashi tafiya sai ya tafi da Hama acewarsa ba zai barta ita kadai tare da kaninta ba dan haka sai ya bar hamza agurin mak’ocin Malam wanda ake kira da Malam Adnan ahanyan zuwa garin Fika sukayi hatsari wanda har hakan yajawo mutuwar mahaifinsu da kawu na kawunsu Sagir wanda ba shida kowa matarsa ta dade da rasuwa kuma Allah bai bashi haihuwa ba ita kuma Hama ba ita ba gawarta bayan anzo musu da wannan labari mara dadi hamza yayi kuka harya gaji shi kuma Malam Adnan ya dauki alkawarin rikeshi kamar d’an daya haifa domin zuwansa Darazo bashida komai mahaifinsu ne ya bashi mafaka a lokacin kasancewa matar malam Adnan din ta rasu tabar y’arta mai suna Rashida wacce tazamewa Hamxa kanwa. Malam Adnan yayi kokarinsa gurin kula da ‘ya’yan nasa duka biyu
ba tare da nuna banbanci tsakanin Hamza da y’ar sa ba.
+
Malam Adnan ma’aikacin gobnatine kuma malamin makaranta yana koyarwa a wani makaranta dake babban titi acikin garin Darazo, yana kuma da d’an karamin shago inda yake sai da abubuwan amfani wanda ba sai anje kasuwa ba kuma achan gurin aikinsa yana kar6an albashi dubu ishrin ahaka yake biya musu kud’in makaranta, alokacin Hamza na aji shida na secondary ita kuma rashida tana shirin kammala aji uku na secondary..
Sun zana jarabawa kuma sun fitoda sakamako mai kyau inda ita Rashida ta wuce aji na gaba wato aji hudu amakarantar kwana
dake cikin garin bauchi shi kuma Hamza ya tafi jos yayi karatu afannin kasuwanci.
Alokacin Goggo Hama ta samu kanta agidan wani mahauci Malam Sada da matarsa Lami agarin mamud’o wadannan mutane sun kasance ba su taba haihuwa ba ko 6ari Lami bata ta6ayi ba kuma Malam Sada yaki ya kara aure hakan yasa danginsa suka tsaneta duk da haka tana kokarin kyautata musu, ana cikin haka ne Malam Sada ya tsinci Hama shine suka yanke shawaran riketa a matsayin nasu haka ita ma Hama ta zauna dasu cikin jindadi ba tare data sake tunawa d’an uwanta ba. su kuma sun d’auka da gaske bata da kowa kamar yanda ta shaida wa Malam Sada asanda ya tsinceta cewan hatsari sukayi da iyayenta kuma duk sun rasu ita ka d’ai ta rage kuma batasan inda danginsu suke ba batare da kokantoba suka yarda ita, ita kuma abunda yasa taki fadi musu cewa tana da d’an uwa saboda kar suce zasu daukoshi azo ana raba musu dadin tare..
A6angaren su Hamza kuma har Rashida ta kammala aji shida inda kuma Hamza yakasance yana ajin karshe ajamia.
Malam Adnan ya nema mata coleji a bauchi inda ta za6i karanta fannin addini wato(islamic studies) shi kuma Hamza yana shirin tafiya bautan k’asa.
Akwana a tashi asaran mai rai yau Hama tacika shekara ishirin da bakwai aduniya Hamza kuma ya cika ishirin da hudu yayin da Rashida take ishirin.
STORY CONTINUES BELOW
Jibir ne ya aiko iyayensa akan anema masa auren
Hama ba tare da 6ata lokaci ba Malam Sada ya amince kuma yayi farin cikin hakan saboda ya dade yanason ganin hama tayi aure amma sai yanzu burinsa zai cika kuma yace dasu bayaso ajinkirta dayawa yafison ayi komai da wuri.
A6angaren su Malam Adnan Hamza ya gama service dinshi ya fara aiki awani company kuma yana samun albashi mai kyau hakan yasa ya daukewa Malam Adnan nauyin komai agidan ita kuma Rashida tana ajin karshe a colejin bauchi.
“An sanya bikin Jibir da Hama sati biyu masu zuwa” Malam Sada ke fadawa matarsa, sosai tayi murna saboda itama burinta taga Hama tayi aure kullun fatanta taga zuwan wannan rana inda itama zata aurar da yar ta duk da ba jininta bace amma tana kaunar Hama.
Ita kuwa uwar gayyan tana chan gidansu Inno kawarta tanata sheke ayarta da Muntari yayan Inno, kwance take akan cinyar Muntari, shi kuwa kullun adduarsa ya samu galaba akanta, ana cikin haka yasa hannunshi a kan kirjinta, wani kallon data mishine yasa yayi saurin janyewa saboda sanin bakaramin aikinta bane ta marishi ko kuma ta jibgeshi.
“Haba Muntari meye kuma haka? kafi kowa sanin cewa banason irin haka kuma koda wasa kar ka kuma gigin yimin irin wannan abun dan ma ka samu ina soyayya da kai shine zaka nemi kaci min mutunci toh wallahi ahir dinka daga yau ya kare ni dakai babu wata alakar soyayya tunda ksi dan akuya ne” tana gama
fadin haka ta mike ta bude kofan tabar dakin ko takan Inno dake ta faman kiranta batabi ba sai da ta biyo bayanta da gudu shine ta samu ta tsaya “Haba Hama meye haka kika fito ranki a6ace kuma inata kiranki kin wani shareni gaskiya ni banji dadin hakan ba ai koma menene ya faru a tsakaninku ni bai kamata kisani a ciki ba” ta fada cikin tsigar rarrashi “ni ki barni dan Allah kinaji dan iskan yayanki dan akuya yana neman ya yagamin rigar mutunci haba dan kawai yaga ina bari yana ta6a hannuna kuma ina kwanciya ajikinshi sai akace mishi ni yar iska ce?” shekeke Inno take kallonta irin na bakida hankali baki da wayo “ai daman nafada miki duk fa wanda baiji bari ba zeji hoho, tun yaushe ina ta rabaki da soyayya dashi saboda nasan halinshi amma kinki yarda dani toh yau dai ya gwada miki sai dai kiyi hakuri kuma ki d’auki matakin
rabuwa dashi, sannan da kike cewa dan kina bari yana ta6a hannunki ai har da laifinki ke baki da kaine da har zaki kwanta ajikinshi ko shi din mijinki ne ai duk macen da bata rike mutuncinta ba babu namijin da zai tayata rike wa dan haka sauki kiyaye gaba” (wannan zamanin da muke ciki wata masifa data tunkaro mu itace wai soyayyar shan minti wanda duk yan mata da samari da basa aikata hakan ma sai adinga musu kallon basuwaye ba. Wannan dabi’a irin ta yahudawa ce wadda ba ta cikin tsarin kowane addini ko kuma yare a fadin Arewa. Gurbacewar tarbiyyar matasa a yanzu takai inda ta kai inda abin baa cewa komai. Ita daj wannan soyayya ita ce mabudin zinace-zinace da karuwar karuwai a cikin al’umma. Wanda hakan na jawo fadawa wani hali na da-na-sani bayan aikata hakan. shi wannan Soyayyar shan minti dai wani irin salon soyayya ne inda zaa ga matasa ba tare da sun yi aure ba suna aikata abun alfasha awurin tadi, cikin mota, ko kuma wasu daj wurare a wani guri inda ba mai ganinsu wanda abin da suke yi ko masu aure ba su aikata hakan. Kwadayi da son zuciya su ke jawo yawancin ‘yan mata fadawa cikin hakan da kuma rashin kulawar iyaye, a haka sai yarinya daga nan ta fara bari ana fita da ita a mota ana kai ta wurare daban-daban na shakatawa, wani abin takaici ma har ta kai ga idan saurayi na gari ya zo nemanta wanda ko hannunta ba zai iya rike wa ba, sai ku ji tana cewa ai dan kauye ne bai iya soyayya ba. Haka zalika mazan ma, in suka hadu da budurwa natsatsiya sai ku ji yana cewa ba ta waye ba. Wa iya zubillah Allah ka nisance zuqatan mu daga tabewa. Ina mai tunasar da masu aikata wannan alfasha su sani Allah yana kallonsu, za su koma gare shi su tarar da makomarsu. Sannan kuma suma za su haifa yara shin zasu so ace sun zamto marasa hali marasa tarbiyya. Idan har ka bata diyar wani to kai ma za a yi ma taka. Gareku ‘yan mata domin ku ne iyayen gobe, kukula da mutuncinku sakama kon lokacinku kalilan ne ku yi kokarin tsare kanku da budurcinku. Allah kara shiryar da mu da dukkan al’ummar musumi baki daya amen).
Tabbas maganar Inno gaskiya ne kuma zancen ya shigeta hakan yasa ta fara istigfari dan neman dacewa. A kwana atashi asaran mai rai yau Allah ya kawo ranar biki, Hama tana kwance a daki tana ta kuka saboda tunanin rabuwa dasu Malam, ita ko lnno sai barcinta take
da yake sunyi party jiya da dare kuma sungaji.
Uwar amarya kuwa farin ciki ba iyaka sak washe
hakora taketayi, taro yayi taro saboda Malam Sada da matarsa mutanen kirkine sunada jama’a sosai amma inda ace dan saboda Hama ne toh ko shi angon zai ji tsoron zuwa saboda fitina da balai irin nata. kowa dai agurin yayi mamakin jin cewa Jibir ne angon dan sanin kan sune Jibir dai mutumin kirkine ba kuma maj rigimaba. anyi taro lafiya an watse an kai amarya gidanta inda su Inno sukaje kwanan gidan amarya shi kuwa ango aka barshi da kwanan shago.
Alhamdulillahi Rashida ta kammala karatunta lafiya yayinda shi kuma
hamza yayi nisa a harkan kasuwancin daya fara ya ajiye aikin kamfanin daya samu kuma ba laifi yana samun riba sosai yana dawowa yatarar da ita a tsakar gida tana saka da gudu taje ta karbi abin hannunsa tanayi mishi sannu da zuwa, cikin jin dadi da zumudin ganinta ya amsa yana washe hakora ya marasa mai zai ce dan rabonshi da ita ya d’an kwana biyu.
Dakinsa ta kai mishi kayan sannan ta dawo ta shimfida tabarma bayan ya zauna ta shiga ta dauko ruwa mai sanyi ta zuba mishi a kofi ta mika mishi sannan ta wuce kitchen ta dauko mishi abinci da abubuwan da tayi domin tarbansa
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Aisha uthman (Madeena)
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
9⃣♾1⃣0⃣
Malam Adnan ne yashigo ganin Hamza yasa shima ya washe hakora yanata dariya cike da farin ciki “d’annan saukan yaushe ai nayi tsammanin baka shigo gari ba har yanzu shiyasa nayi zamana a kofar masallaci”.
Tashi yayi ya rungumi Malam Adnan cike da farin ciki shima yace “ban jima sosai ba Baba kuma motarmu da wuri ya tashi ai shiyasa kuma bamu samu matsalar go slow ko check point ba da fatan na sameku lafiya Baba?”
Zama Malam yayi akan taburman sannan shima Hamza ya zauna kafin yace “Alhamdulillahi mun gode Allah muna cikin koshin lafiya da fatan kai ma kazo lafiya ya ayyuka da hidima damu? Allah ya saka da alkairi ya kara bud’i”.
Dan 6ata rai Hamza yayi kafin yace “yanzu Baba dan d’a yayi wa iyayensa hidima sai arinka gode mishi, ai kulawa da kai wajibi ne agareni domin kai din uba ne nagari”.
Murmushi Malam Adnan yayi sannan yace “tabbas ya dace ace uba yayiwa d’ansa godiya domin kara karfafa mishi gwiwa kuma domin shima yaji dadin abunda yayi ai ance yaba kyauta tukuici kai dai Allah yayi albarka”.
Amin Hamza yace sannan suka cigaba da hira cikin natsuwa da kwanciyar hankali sai daf da magriba sannan suka fita danyin salla suka bar Rashida a gida.
Yau kwana uku kenan da dawowar Hamza, Malam Adnan ya kirashi bayan yazo ya neman guri ya zauna “Baba sannu da
hutawa” yace yana gyara akan tabarman.
“yawwa d’an albarka har ka dawo kenan dafatan ban tsaidaka daga wasu ayyukan ba, ka samu Malam Saminu ne?
“Eh na dawo Baba, haba dai ai ko mai nakeyi inka kirani dole ne in tsayar in dawo domin kiranka yafi komai mahinmanci naje ban sameshi ba amma zan sake duba shi zuwa anjima”.
“Toh madallah nagode da irin wannan girma da kake bani Allah ya muku albarka” Gyara zama yayi sannan ya cigaba da cewa “yanzu tunda Allah yayi ka kammala karatun naka kuma kafara sana’a, shin batun aure fa, akwai wacce kukayi alkawarin aurene ko kuma ba’a dace ba har yanzu?
sosa kyeya yayi sannan ya fara kame-kame”uh toh toh dai gaskiya Baba babu wata wanda nayiwa maganar aure asalima ni banda budurwa amma dai kuma” sai yaui shuru.
Malam yace “yanaji kayi shuru Hamza amma dai meye kayi magana mana in kuma har ba wanda ka tsayar toh mai zai hana a had’a aurenka da yar uwarka RASHIDA?
Murmushi yayi me nuna alamun cewa ya amince kafin yace “wallahi Baba duk yanda kake so hakan za’ayi domin hangenka yafi nami.
“Aa tambayarka nayi tayi maka kana sonta ko aa, idam baka amince ba, ni ba zanyi muku dole ba”.
Sosa kyeya yayi kafin yace “wallahi Baba ni dai na amince kuma daman tun kafin kafada nikam ina sonta domin auren mu shine zai zame mana gata idan bakanan yanda muma hankalin mu zai kwanta muna tare baza muyi nisa da juna ba”.
STORY CONTINUES BELOW
Sosai Malam Adnan yayi farin cikin jin haka kuma yayi hamdala aransa dan dama shima abunda ya hango musu kenan idan bayanan ba zai so ace aure ya rabasu ba hadin auren nasu shine gata a garesu “Baba nace wani hanzari ba gudu ba mai zai hana abarta tukunna ta kammala karatunta a fannin islamiya kaga dai insha Allahu zauwa nan da shekaru biyu zatayi sauka, nima kuma inason inyi masters dina inyaso kaga lokacin mun gana tare sai a hada da daurin aure da saukanta tunda kaga hadda takeyi itama tana bukatan natsuwa”.
Jinjina kai Malam yayi kafin yace “eh kuma fa hakane gaskiya kaima kayi magana shikenan hakan ma za’ayi kawai Allah ya shige mana gaba ya kuma bada sa’a.
Da sauri tabar gurin ta wuce dakinta, murna ne ya cikata, ashe daman ya Hamza yana sonta, ai ta zata ita kadai take dakon sonsa, toh meyasa bai ta6a fada mataba, koma menene dai taji dadin wannan abun musanman ma tunda yana sonta, toh kuma meyasa bai bari an yi bikinsu kwanan nan ba, kash yanzu sai ta jira har nan da shekara biyu koda yake yana da gaskiyarsa Allah dai ya nuna musu lokacin kiran da Baban yayi matane yasa ta dai daita natsuwara sannan tace “naam ganinan zuwa Baba.
Tana fitowa ta nemi guri ta zauna sannan tace “Ya Hamza barka da hutawa Baba gani”.
Bayan Hamza ya amsa Baba yace “yawwa dama dai akan batun aurene, a iya sanina babu wanda kika tsaida kuma babu wanj wanda kike zance dashi, in kuma akwai to saiki fadamin?
Akunyace tace “aa Baba babu kowa ni bana kula kowa kuma banda wani tsayayyan saurayi kuma babu wanda nama ta6a tsayawa dashi”.
Har zuciyar Hamza ya fara buguwa amma da yaji tace babu sai ya danji sanyi acikin ransa, Baba yace “Alhamdulillah dama inason zumuncin mu ya kara karfi hanyar hadaku keda yayan naki, shin hakan ya miki ko kuma kinada ja akan hakan?
Sunkuyar da kai tayi kafin tace “aa banda tacewa duk abunda kace shine dai dai ai hukuncinka akaina kar6ar6e ne duk yanda kakeso haka za’a yishi.
Malam yajidadin abunda tace amma ya sake cewa “ba wai abunda nace ba shin kin amince koh aa domin bani son in shiga hakkin kowanne acikinku kudin amana ne agareni.
“Na amince Baba” tana gama fada ta fita tabar gurin, sosai Hamza yaji dadin hakan da Baba yayi shima kuma Malam yaji dadin amincewarsu dan bai yarda da tursasa yaro akan abuna kar azo aji kunya.
♾♾♾
Sand’a yakeyi kamar dai wani 6arawo daker ya samu ya bude kofan a
hankali, ganin cewa baiji muryan suba sai yayi tunanin cewa kila basu tashi ba babu shiri ya buga ihu yana kankame jikinshi, Hama ce ta zuba mai ruwan sanyi abaya sosai ruwan ya ratsashi hakan yasa ya kasa cewa komai “ah haba dai Malam Jibir ashe kaine ai ni ce nake 6arawone, ya zaka shigo kanayiwa mutane sanda fisabilillah taya zanyi tunanin mai gidanne, toh ba kowa daga ni sai inno don duk an watse ita kuma inno sai tayi wata daya zata wuce domin bazan iya zaman kadaici ba zuwa lokacin na koyi zaman gidan”.
Zaro ido yayi da zaiyi wani maganan amma ya kuma ya fasa kawai yace “toh Allah ya kaimu” tace “yawwa daman ina son akaimin nikan wake dan saboda yau alala nakejin ci kuma ba almajirai, ga kuma kasan dai bazan iya zuwa ko inaba shine nace mai zai hana kakai min nikan ai ba wani abu bane tunda dai markade ne kawai kuma nan gurin Maman Tatai ne kaga ba nisa”.
Shuru yayi kawai yana kallonta bai iya cewa komai ba kawai ya kar6a nikan da muttala biyun
data bashi ya kama hanya zuwa gurin markade.
Tafiya yakeyi ya daura bokiti akai “kai meye haka kuma Jibir? muryan Tanimu yajiwo daga chan bayansa “ya naganka da bokiti akai lafiya dai koh? Tanimu ya tambaya yana kallonshi.
Sosa kai yayi sannan yace “wallahi Hamace ta aikeni in kai markade wai tanajin cin alala kuma ta guraren namu babu yan aike.
“Subhanallahi eh lailai ka haukace, matarka ta aike ka wai ka kai mata nika ko markade nema ba wai bata da lafiya ba, aiko dai bata da lafiya babu yaran makota ko almajirai ne ko kuma baka da kannai da zata iya kira ko nata k’annan?
Tsaki Jibir yayi yana cewa “dan Allah abar wannan maganar kaga karna 6ata mata lokaci kasan halin Hama dai bata son jira kuma kar azo ranta ya 6aci”.
“Toh sannu mijin hajiya lailai zamani ya chanja to dan Allah yi maza ka kai mata niqan ka dawo da wuri kafin ta nikisaka ko tayi jajjage da kai sakarai wanda bai san inda yake mishi ciwo ba ni kaga ma tafiyata, wannan wani irin rayuwace tun ma bata kai sati agidan ba har ta fara saka aiki lailai akwai aiki babba ya fad’a yana kad’a rigarsa.
Shidai jibir bai damuba shi damuwarsa ma bai wuce yayi ya kammala da wuri ya koma gida ba yana isa kofan gidan yayi sallama Maman Tatai ce ta fito cike da mamaki da hat zatayi dariya amma ta tsare, azuciyarta tana cewa (ai maganinka ba karasa wacce zaka aura ba sai Hama aiko yanxu kafara ganin wahala ga chan Tatai dina ta soka amma ka k’ita) maganar da yayi ne ya katseta “na kawo nikan wake alale za’ayi dashi” hararansa tayi afakaice kafin tace “toh kuma gashi ba wuta sannan injin ma ya lalace kuma kasan dai kaf cikin kauyen nan ni kadai ce ma nika inba wuta”.
Cikin damuwa yace “toh amma ba inda kike ganin zan iya samu? hararansa ta karayi sannan tace “eh gaskiya babu inda zaka samu sedai kila kadawo anjima in sun dawo da wuta”.
Kwasan kafarsa yayi ya bar gurin yanata tunanin mai zai ce mata in yaje gida yana isa kofan gidan ya tsaya yayi yan adduo’i yayi ta tofe tofe sannan yayi bismillah da sallama ya shiga kamar munafuki.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Rahma Kabir marubuciyar *So Sartse*😍
Thank you so much Mrs Noor for the dedication Allah ya bar kauna🌹💃🏻
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
1⃣1⃣♾1⃣2⃣
Zaune take akan gujeran k’arfe tanayi tana duba agogon dake mak’ale a jikin bangon falon chan kuma ta d’auki kujeran nata ta fita tsakar gida kaman ance ta juyo ai kuwa ta ganshi yana ta k’orarin gyara kofar gidan hararanshi tayi tana wani kad’a kugu “dan gidanku mai ka tsayayi achan da sai yanzu zaka dawo, tun dazu kafita amma shine ka tsaya shirmen banza da wofi, daman ka auroni ne don ka barni da yunwa ko kuma mai kake nufi da hakan eh?”
+
Marairaice fuska yayi kafin yace “dan Allah ki ki kiyi kiyi hakuri wallahi na zaga ko ina babu wajen nika kuma maman Tatai tace wai injinta ya samu matsala sannan duk cikin garinnan babu mai nika in babu wuta sai ita”.
Tsalle tayi ta dire kafin tace “eh mai naji kace ne tukunna dan ban gane ba kana nufi kacemin wai ba ma ayi nikan ba ko kuma mai kake nufi?
Cikin i’ina yace “eh ranki ya dade wallahi ba’ayi ba dan ban samu ba amma kiyi hakuri bari dan Allah bari in dafa miki ko d’an shinkafa da wake ma”.
“Uwar shinkafa ne bama shinkafa ba, sakarai wato shinkafa zanyi ta durawa cikina koh, toh gwanda dai ka zage wallahi kaje duk inda zakaje kayimin nika ehe ni dai na fada maka idan ba haka ba in tattara kayana duka inbar maka gidanka” ta fada tare da jan tsaki ta wuce daki sai mita takeyi.
Jawo kujera yayi da zai zauna amma kuma sai tsoron Hama yakamashi nan da nan ya mike yafita yana tafiya ne kawai dan shima bai san inda zai dosa ba, maganar dahiru ne ya dawo dashi cikin hankalinsa “toh kuma dai yau kenan ta haka kuka fara, ai dam wanda baiji bari ba zaiji hoho, nasha fada maka kabar wannan yarinyan amma bakaji ba tph yanzu gashi ka auro wa kanka jaraba” ya fada yana dariyan shekiyanci.
6ata rai Jibir yayi sannan yace “ni yanzu dan Allah ba wani dogon magana nake soba kai dai kawai kafadamin inda zansamu wajen nika yanzu saboda kaga dai matata ba taci abinci ba tanachan tana tajin yunwa kuma sannan ita alala take sonci”.
Mamakine ya cika shi ya sake kallonsa daga sama har kasa sannann yace “toh ai abokina duka ma zatayi maka kenan kawai dan naga yana jikinka ke 6ari abun ba sauki?
Jibir yace “haba dai duka kawai dai bana son 6ata mata rai shiyasa kuma kasan ba dadi a 6atawa amarya rai”.
Dariya Dahiru yayi kafin yace “Jibir kenan muje to chan wajen gidan Tsohon direba akwai wata mata tanayin nika agurin idan mukaci sa’a ta kunna sai tayi mana koya kace?
Washe hakora Jibir yayi yace “indai har za’a samu ai koma inane muje ni dai ko nawa ne zan iya biya babu matsala”.
“Za’a samu kila in munyi sa’a muje dai mu duba saboda Iya makwabciyar mu naga chan take tura yaranta idan ba wuta”.
STORY CONTINUES BELOW
Jibir yace “Toh shikenan, yawwa ya maganarku ne da Kubra ko kuma itama yaudaranta kake so kayi daman?
Dahiru yace “dan Allah abokina kabar wannan maganan kaima kasan inba Hindu ba sai rijiya”.
Jibir yace “eh gaskiya da wannan ma dan naga alama kamar kafi bata kulawa sosai”.
Dariya Dahiru yayi kafin yace “ai ban samu lokaci bane shiyasa ban fada makaba muda har ansa rana mako biyu masu zuwa idan da rai”.
“Kai haba dan Allah aboki shine banda labari karka fadamin da gaske kakeyi amma idan hakane baka kyautamin ba”.
“Wallahi da gaske nake aboki duk wad’an chan yaran barsu kawai nina Hindu ne kuma itace dai kawai agabana”.
“Ai dole kace haka tunda ita baka gama da ita ba su kuma sauran tunda ka gama kwasan gara6asa ai shikenan, wai ku kam baku tsoron abunnan da kukeyi za’a iya yiwa naku yaran ko k’anne gaskiya ku tuba ku kuma basu hakuri ku nemi yafiyarsu domin bakin wani guba ne mai kaifi, sannan ina tayaka murna ai gwanda kayi akan kadinga 6ata yaran mutane”.
Cikin rashin jindadin maganar nashi Dahiri yace “kai abokina bakada dama ai yanzu mun dai na wannan harkan kuma mun tuba nima ina dan fargaba akan abunda na aikata, Allah dai ya mana magani”.
Inno ce ta fito daga daki tazo falo ta taras da ita ta zuba uban tagumi sai da ta kare mata kallo kafin tace “toh fa Hama mike damunki haka lafiya dai koh naga kin zuba uban tagumi kamar an aiko da sakon mutuwa?
“inafa lafiya ai gwama sakon mutuwar tun dazu fa na aiki yaronnan duba kiga lokaci kusan mintina arbain da biyar amma har yanxu shuru kikeji sai kace yaje kai ziyara wani kasa daban ko kuma an shuka dusa.
Inno tace “toh naji ki nata cewa yaronnan wai wani yarone kike fada kenan?
“wani yaro zance inba wannan asararren ba to bari inyi miki dalla dalla Jibir nake nufi”.
Dafe kirji tayi ta buga salati “Jibir fa kikace, eh lailai Hama yanzu kuwa na yarda cewa baki da hankali, yanzu mijin naki kika aika shi kuma shine ya kama yaje toh ma wai aiken menene?
♾♾♾
Umma Lami tana zaune tana hura wuta sai tari takeyi amma takasa dai hakuri tafito tadan shaki iska, daker dai ta samu ya kama”Malam Sada ne ya shigo rike da d’an leda ahannunsa, dasauri tabar abunda takeyi ta fito ta kar6a sannan ta mishi sannu da zuwa tajawo
taburma ta shinfida masa.
murmushi yayi sannan ya zauna “sannu da aiki nasan kingaji yau kam sosai”.
“Ai dole ingaji tunda duk an watse an barni da aiki sai yanzu na gama shine nake kokarin iza wuta, bari ina zuwa” tashi tayi ta nufa kitchen ta daura tukunya akan wuta tasa ruwa daidai nayin dan wake, sannan ta fito da
garin don ta kwa6a.
“Nikam koya jibir suke karewa da Hama oho” ta fada tana kallon Malam Sada.
“Ke dai lami bari kawai nima tunanin dana keyi
kenan Allah dai yasa suna lafiya sabida nasan Hama da rigimar tsiya”.
“Gaskiya Hama kam ba kanwar lasa bace yanzu zata iya yi mishi rashin mutunci, bari dai idan na kammala inje in dubasu”.
“Aa ba zaayi haka ba kinga ko sati ba ayi ba kibari rana ita yau sai kije idan Allah ya kaimu”.
“Toh shikenan malam haka za’ayi, Allah dai ya basu zaman lafiya.
na fita ta wuce dakinta tama rasa inda zata saka kanta don murna ganin dai ta kasa zama yasa ta tashi taje ta dauro alwala danyin nafila tana idarwa tayi adduoin ta tare da rokon Allah ya cika mata burinta, sallaman Zulaine yasa ta tashi tafita, tana zuwa ta ganta da Kuluwa 6ata rai tayi ta cewa “dan Allah Zulai meye haka ya zaki kawomin wannan munafukar har gidanmu dan Allah ki fita da ita ban kaunar ganinta” Rashida ta fada tana mata kallon tsana.
“Haba Rashida nifa ban sanki da fadaba nikam in zaki bamu guri mu zauna toh in kuma a’a sai muyi tafiyarmu?
Asanyaye tace dasu “ku shigo ku zauna” ahankali suka shiga suka nemi guri suka zauna, bude labulen window dana kofa tayi sannan ta dibo
musu ruwa ta ajiye musu kafin tace “ina sauraron ku mai ke tafe daku?
“Rashida kenan saurin mai kikeyi, nazo ne in sanar dake cewa ansa rannan bikinta” tayi mata nuni da Kuluwa”.
Mamakine ya kamata “shin daman ba son Ya Hamza kikeyi ba, toh mai yasa kike yawan bibiyar sa?
Gyara zama tayi sannan tace “kamar yanda Zulai
ta shaida miki bikina sati biyu masu zuwa karshen wata kenan sannan bari in baki amsar tambayan naki, wato akwai wata
rana na fito daga gidansu Zulai zan koma gida sai ga Ya Hamza yazo zai wuce yana ganina sai ya min sallama na amsa kasancewar yasan bamu jituwa tsakanina dake shi yasa ya tsayar dani dan in taya shi yin wani aiki..
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Nusaiba gentle lady😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
1⃣3⃣♾1⃣4⃣
Nace mishi “wani irin aiki kenan haka” sai yacemin “kar in damu zai sameni gobe a makaranta inyaso sai muyi maganan”.
Ta cigaba da cewa “toh washe gari idan dai baki mantaba shine ranan da kike bata labarin yanda kike matukar son yayanki kuma alokacin na riga na amsa cewan zamu hadu dashi so idan ban cika alkawari ba kin ga kenan ban kyauta ba nasan zaki min rashin fahimta shine ma abunda yafi damuna alokacin toh bayan mun fito daga second lectures shine yazo lokacin kuma fitowarku kenan kuka gan mu muna magana a zato na zaki tsaya sai kuma kika ja tsaki kika wuce ni dai abin dariya ba bani shi kuma abun ya bashi mamaki saboda rashin kulashi da kikayi bayan wucewarki shine yake cemin daman ba wani abu bane yanason sanin ko kinada saurayi a cikin makarantan nace mishi gaskiya baki dashi yace min shikenan yanason mu kulla abota dashi ta yanda zakiga kaman ko muna soyayya idan yaso
reaction dinki shine zai tabbatar mishi shin kina sonsa ko a’a domin yana zargin kaman kina sonsa amma bayason ya miki maganar cewa shi yana sonki don kar asamu akasi kila ba sonsa kike ba kuma karya takuraki don yasan zaki yarda kodan kifaranta mishi”.
+
Kallon Rashida tayi kafin ta cigaba da cewa “Yayi hakanne don ya gane ko kina sonsa ko kuma kina da wani dan yanaso idan Baba ya tambaya saiya ce keya za6a aura amma fa in kina sonsa dan baya son takuraki sai kuma ya kasance kin nuna kishin karara akansa hakan ne yasa yaji dadi dan haka inaso ki sani tsakanina dashi zumunci ne kawai kuma nazo ne in baki hakuri sannan in cireki daga zargin da kikeyi a kaina sannan kuma ina gayyatanki bikina”.
Ita dai mamaki ne kawai ya cikata saboda batama ta6a tunanin Ya hamza zai so taba kuma ko da ya amince da aurensu a zatonta saboda biyayya ne da kuma dan faranta wa Baba amma ashe abun ba haka bane shi yasa akacs zato zunubi koda ya kasance gaskiya Kuluwa ce ta dan jijjigata afirgice ta dawo daga duniyar tunanin data shiga “hhm dan Allah Kuluwa kiyi hakuri kuma ki yafemin tabbas nasan ni mai laifi ce agareki so ne ya rifemin ido amma bai dace ace na rikeki a zuciyata ba amatsayin mu na musulmai kiyi hakuri dan Allah, batun zuwa bikinki kuma zanyi kokari inje kinsan kowani
juma’a muke bada hadda amma dai zanyi kokarin in bada ranar alhamis saboda na samu damar zuwa Ince dai akwai anko saboda gaskiya biki inba anko baya birgeni”.
“Eh akwai anko kala biyu daya na ran walima daya
kuma na ran daurin aure, walima zai kama laraba sai daurin aure jumaa, kuma na yafe miki Allah ya yafe mana baki d’aya”.
“Amin kuma Allah kaimu” tace kafin suka cigaba da hirarsu cikin jindadi sai kace basu ta6a samun rashin jituwa ba ita kam Zuwai har mamaki suka bata, bayan sunci abinci sukayi sallan azahar sannan sukayi mata sallama suka nufi gida ba don ta soba saboda rabon dasu zauna irin haka ya dade.
Ya hamza ne ya fito tsakar gida ya taddata tanasurfe, sa hannu yayi ya kar6a ta6aryan ya jawo kujera ycigaba da dakan,itakam mamaki ya bata kawai ta tsaya tana kallonshi “ke meye haka kuma kinsani agaba? kunya ne ya kamata dauke idonta tayi sannan
ta juya ta jawo wake ta fara gyarawa saboda ta samu tayi wa baba kosai don yana azumi.
♾♾♾
Nikan wake ya kai min saboda sanin kankine tun jiya nake kwadayin son cin alala amma bansamu ciba, na nemi almajirai ban samu ba shine da yazo nace ya kai min, sannan rashin hankali ya wuce wanda kikayi wato zama agidan amarya har zuwa wannan lokacin wai da sunan kinzo tayani da zama toh shi Jibir din meye amfaninshi ai shi ya kamata ya zauna dani sannan kuma ba inda zaki sai kinyi wata gida ko kinso ko kinki saboda na riga na fada masa cewa zakiyi wata kuma ai
kinga in kin tafi kenan kamar nayi mushi karya ne” ta fada tana dariyan mugunta.
Suna isa gurin markaden kuwa suka samu zata kunna inji da alama ita ma niqa zatayi, sallama suka mata sannan suka gaisheta, ta amsa musu fuskannan ba alamun rahama, daker suka iya ce mata “daman nika ne muka kawo na alala”.
Fizgar bokitin tayi ko wanke injin batayiba ta juye kuma da alamu bata dade da yin nikan hatsiba shine ta maka nasu akai haka sukayi shuru sunaji suna gani babu damar magana gata da kiran manya.
Bayan ta gama musu markade suka biya ta kudinta sannan suka kama hanyar gida Dahiru gidansu ya wuce Jibir kuma yayi hanyar gidansa.
Ita dai Inno tagumi kawai tayi tanajinta, ta inda fa Hama take shiga bata nan take fita ba sai zuba takeyi “ni kam wai meye hakanne har sha daya da kusan rabi mutane basu samu sunyi karyawaba ko a ina yatsaya ma..bata karasa maganar ba taji sallamansa Allah sarki Inno kam harya bata tausayi, ga bokiti akai ga takalmi a hannu, wato da alama ya tsinkene da dan saurinta ta mike ta nufe shi “sannu da zuwa dan uwa ina kwana” sannan takar6a ta wuce kitchen shi kuma ya amsa yana murmushi Hama kuwa sun mugun 6ata mata rai sai wani cika take tana batsewa “daman wai kai achan gidanku shadaya akeyin kari ne toh in dai haka kukeyi ni gidannan ba za’ayi hakan ba dan haka gwanda kazage ka bada himman yin girki da safe idan yaso ni nayi na rana ita kuma ta rinkayin na dare” mamaki kawai ta bashi wato yanda take magana sai kace itace mijin shine matar Inno kuma mai aikinta ko yace kishiyarta, bai tanka mata ba kawai ya fice ya nufi shagonsa Inno dai har tafara hadawa tama kulla aleda ta daura ruwa
akan wuta jira takeyi ya tafasa sai ta saka.
“Toh hajiya uban wayace kije kinayi masa kini bibi sai kace mijinki, ai babu wanda ya saki zuwa ki gaisheshi balle kuma har kiyi wani kalan tausayi Inno dai bata tankamata ba don tasan Hama dai rigima take nema suyi da ita amma bazata biye mata ba zatayi hakuri da ita, wani guntun tsaki taja sannan ta fice ta nufi daki ta kwanta danyin barci ko zata samu ta huce takaici, Inno dai dariya tayi sannan ta duba ruwan ganin ya fara tafasa sai ta d’au alalen tasassaka daya bayan daya sannan ta rufe shi kirif ta rage wutan ta wuce falo ta kunna tv tana kallo
Yana zaune a shagonsa ya fara tunanin yanda Inno ta tarbeshi amma ita matar tasa zamanta tayi in banda masifa ba wani abunda takeyi aiko uwarsa ce ita din iyakaci kenan tunanin dalilin da yasa yake jurewa akan
halayyanta ma kawai yakeyi ahakadai yayi ta tunani har barci yayi awun gaba dashi.
Akwana atashi yau satin Hama biyu acikin gidanta Jmmace ta shirya domin taje taga wani hali ake ciki agidan d’iyar nata.
Suna tashi abarci jibir ya shiga kitchen ya fere doya ya soya sannan ya musu sauce na kifi, Inno tana tashi tajiyo kamshi yana tashi, da sauri ta nufi kitchen ta gaisheshi sannan ta tayashi suka gama hada kayan karin, suna gamawa ya shiga wanka ya fito alokacin Inno kuma har ta gama gyaran kitchen din ta kimtsa gidan sannan ta shiga ta watsa ruwa tana fitowa ta shirya cikin kayanta material mai
kyau tashiga dakin Hama don tada ita.
Da mamakin ta sai gashi ta samu har ta tashi ta gyara dakin tayi wanka ta shirya cikin atamfa me kyau gashi taci kwalliya ta daura dankwali yakalli gabar da gani tana cikin farin ciki, neman guri tayi ta zauna tadafa ta “Hama ince dai yau lafiya na ganki cikin fara’a? dariya Hama tayi tace “ai dole ki ganni haka yau Ummana ne zatazo.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Jidda A Alkali😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
1⃣5⃣♾1⃣6⃣
Kallonta Inno tayi kafin tace “eh gaskiya naga alama ai dole kiyi tajin dadi yar gaban goshi”.
Jibir ne ya shigo tare dayin sallama hullarsa ya d’auka ba tare daya ko kalleta ba yayi ficewarsa Umma tana isowa ta fara buga sallama cikin sauri Hama ta fito sai washe hakora takeyi “sannu da zuwa Ummata” ta fad’a tana kokarin janye labule, kallonta Umma tayi kafin tace “yawwa sannu yar albarka” jerawa sukayi suka shiga falon, bayan Umma ta zauna akan kujera ita kuma akasa kafin tace “Ummata ina wuni, ya gida, ya kwanan Baba dafatan duk kuna lafiya?” Umma ta amsa da “lafiya kalau muke daga ni har Baban naki kuma yace na gaisheki, dafatan kuma kuna lafiya?.
+
Murmushi tayi sannan tace “Lafiya kalau Umma sai dai gaskiya nayi kewarku sosai kaman in koma gida kawai”.
Umma tace “ja’ira wato har so kike ki koma gida saboda kewarmu, toh ai ko wata mace da haka ta saba muma kuma munyi kewarki, ina Jibir din?
“Lafiyanshi kalau Umma shima yanzu ya d’an fita” Inno ce ta shigo falon tana wani washe hakora “Umman mu sannu da zuwa anzo lafiya yasu Baba ya kwana biyu?”
“Lafiya kalai Inno ashe kema kinzo duba kawar taki gaskiya kin kyauta sosai yasu umman naki?
“Lafiyansu kalau wallahi ai ni in…… kafin takarasa Hama ta amshe da cewa “itama kila unguwarnan za’a kawota ai an tsaida maganarsu da Malam Suyudi ai in fada miki Umma sanda na mata gori kamin tazo dubani don tun randa suka kawoni tayi niyan tafiya daker su Ramatu sukasa ta zaune” ta fada tana hararan Inno.
Inno dai baki bude take kallon ikon Allah wannan
irin karya bako kifta ido lailai Hama ta isa ta rika wuyanta yayi kauri, Jibir ne ya shigo rike da leda a hannunshi, da wuri Hama ta isa inda yake ta kar6i ledan tayi mishi sannu da zuwa sannan taje ta kai kitchen ta dawo, Umma taji dadi ganin yanda yar nata take kokarin kula da mijinta.
“Sannu da zuwa nasan ka gaji, ai sanda nace kabari kawai base ka fita sayo wani abuba tunda Hmma ce ai bakomai kai kanka kasan cewar baka jindadi kuma fitan naka zai kara maka zazzabi ne kawai gashi naga har wani rawan sanyi kakeyi” Inno dai da Jibir an barsu cikin rud’ani ganin abun nata da gaske yasa ya nemi guri ya zauna kallo kawai yake ta binta dashi sai zuba takeyi kamar
ruwan famfo, tashi tayi ta nufa kitchen ta hado abubuwan daya kawo ta jerasu a tray sannan ta kaiwa Umma a falo”.
Kazane gashashe sai kuma lemon kwali da
sinasir, Jmma se washe hakora takeyi basabon ba yau ga kaza guda agabanta zataci ta koshi iyason ranta, sai sannan Jibir ya tuna basu gaisa da Umma ba,nan yafara
jero gaisuwa Umma tana amsawa cike da zumudin yayi yafita ta samu ta 6antara.
Hama ce ta sake fita ta hado tray biyu d’aya ta kai dakin Jibir daya kuma ta ajiye musu afalo kafin tace “ya Jibir ga abincin nakana kai dan Allah kayi kokari kaci kasha magani saboda ni lafiyan mijina yafimin komai, yau kam
bazama kaje gun aiki ba gaskya zaka huta agida” daker ya amsa mata da toh sannan ya tashi ya shiga dakinsa cike da tsananin mamakinta yana tambayan kansa toh wai ta chanja haline ko kuma dai ganin umma ne yasa tayi haka bari dai
ya zuba mata ido yaga iya gudun ruwanta, Inno kam dai tamarasa mai zatace mai zatayi, shin
meke damun Hama ne ko dai asiri aka mata, kai ba asiri bane kila ganin Umma ne kawai, dan irin wannan karya haka sai shirgawa takeyi daya bayan daya ba sassauci.
A6angarem Hama kuwa taji dadin yanda taga
Umma ta nuna farin cikin ta karara ” su kuma yan jakan uba wato azatonsu ma ta chanja haline” ta fada aranta.
Tusa abincin kawai yakeyi badon ya samu
kuzarin ciba, yanzu ana zaune kalau ta kama tace bai da lafiya toh gashi ai yafara jin zazza6i gasken sai tasan kuma yanda
zatayi dashi dan gaskiya ba zai iya fita ba kuma
ya bar wayansa a shago jiya da yamma sannan ya san dai bazata je chemist da sunan sayo masa magani ba kuma bazatabar Inno taje ba shi kam ya shiga uku yau, tura abincin yayi gefe guda sannan ya kwanta jikinshi sai wank karkarwa yake daker ya iya jawo bargo ya lullu6e jikinsa.
Sai gaftaran kaza takeyi bata bar ciba sanda taga
taci rabi kuma daker take numfashi sai nishi takeyi tamkar wanda tayi gudun kilomita 50 kwankwwade juice din tayi sannan tayi godiya ga Allah “gaskya naji dadi dana sameki cikin kwanciyar hankali tare da mijinki, Allah ya kara azziki ya kuma bada zuria dayyiba”
“Amen umma, nima zanzo ai wani sati insha Allahu” cikin jindadin tace “toh shikenan ai kuwa Babanki zaiji dadin hakan, yanzu dai bari ni zan tafi sai kin kara gani na”.
“Toh bari inyi mishi magana” tashi tayi ta shifa dakin salati kawai tayi ganin yanda ya wani kwanta ya kudundune a cikin bargo kamar wani jariri tsugunawa tayi tace Jibir menene?
ganin dai yakasa magana yasa ta fita ta kira Umma, Umma na shiga tayi salati tace “ai bamuga ta zama ba bari mu kaishi asibiti, daker suka iya dagashi ita kuma Inno taje ta nemo
mota akasashi a ciki.
Ganin cewan dreban na tafiya a hankali yasa ta
wankeshi da mari “dan jakan uba zaka daga kafane kayi tuki da kyau ko kuma saina shakeka” sanin halin Hama yasa yayi shuru ba shiri yafara gudu dasu, aransa yana cewa “badon sai Jibir ba da ban dauko kuba” suna isa asibitin akayi sauri aka kaishi emergency
room, ansa mishi ruwa sannan akace dasu yana
bukatan jini.
♾♾♾
su Rashida manyan kawayen amarya sai kaiwa suke da komowa tayi kyau sosai kamar ba itaba, fitowa tayi domin neman ya Hamza tana tsaye taji sallama a dan firgice ta juya ta amsa asanyaye sannan ta sake juyawa zata tafi “aa dan Allah dan tsaya mana minti biyu pls ina da yan tambayoyi ne”.
“ok inajinka minti biyu” ta fada tana kalle kalle dan tana tsoron fushin yayan nata “dan Allah ke matar aurece, indan aa toh ko zan iya samun lambarki? yana karasawa yaji an shako wuyarsa mari ya kifa masa wajen guda 4 sannan ya wullar dashi kasa daker aka rikeshi aka bashi hakuri, kasa magana tayi sedai binshi da kallo da takeyi juyowa yayi ya harareta da sauri ta juya tafara tafiya a
hankali “zaki wuce cikine ko sai na biyo bayanki” bata kara minti daya ba ta shige cikin gida ta nufi
daki wajensu Kuluwa ta zauna a gefen gado tana
mamakin ya Hamza” sam ita bataji dadi ba daya dokeshi ai daya jira yaji amsar dazata bashi amma dai ta danji sanyi aranta tunda ya nuna kishinsa akanta.
A6angaren Hamza kuwa huci yakeyi jiyake kamar ya 6a66alla wannan mutumin zuciyarsa sai tafasa yake daker ya
iya controln temper dinsa.
“Kawata ya naga kinyi shuru lafiya dai koh? Kuluwa ta tambaya.
murmushi kawai tayi tace “lafiya kalau kawai dai kaina ke ciwo kinsan munyi aiki mun gaji”
“Gaskiya kam toh ki kwanta ki huta ai kinsha aiki gaskiya Allah ya nuna mana naki, ina ya Hamza ince dai tare kuka zo koh?
“Eh tare muka zo yana chan waje gurin su ya Aliyu”.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Deeya A Alkali😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
1⃣7⃣♾1⃣8⃣
Hama tace “toh muje ad’ebi nawa jinin” Likita yace “aa semun gwada tukunna duk wanda yayi matching sai asa mishi” Ana cikin hakan sai ga Sagir kaninsa ya taho da sauri yana cewa “Likita nawa ya kamata a saka mishi saboda dama tun ba yanzu ba nawan ake bashi” Likita yace “toh ai shikenan muje adiba”.
Inno dai tana ta adduan Allah ya bashi lafiya ita kuwa Hama sai dirzan kuka takeyi wai ita dai su ceci ran mijinta, mamaki Inno tayi akan yanda duk taga Hama ta shiga wani irin yanayi “ashe daman tana son shi shine takeyi mishi abunda ranta yaso lailai kuwa in dai hakane mun samu yanda zamu gyarata bari dai Jibir ya samu lafiya ai anzo gidan sauki” ta raya haka acikin ranta, Sagir na fitowa ta rikeshi tace “ya warke ne ko kuma farfadowa yayi da aka bashi jinin naka kaman na sidabaru sai wani rawan kai kakeyiwa mutane ana maganan gaskiya kana saka baki kabari asa mishi nawa kazo da wani shishiginka kai ala dole kaninsa koh” ta fada tana hararansa.
+
“Haba Yaya Hama kiyi hakuri mana meye dan na bawa dan uwana jini ai ko ba dan uwana bane kina mace ai bai dace in bari adebi naki ba wallahi ni banyi haka dan in 6ata miki rai ba” Sagir ya fada cikin sanyin jiki.
“Zaka rufemin bakin kane ko sai na kwadeka ni za’a ciwa mutunci dan rainin wayo da munafirci lailai ka manta wacece ni” ta fada tana huci.
“Kiyi hakuri nayi shuru Allah ya huci zuciyarki ya kuma ba Ya Jibir lafiya” ya fada dan kawar da zancen.
“Amen sai kuma ka wuce gida kasanar musu cewa bai da lafiya amma dai ya dan samu sauki dan kar hankalinsu ya tashi” toh kawai yace sannan ya kama hanyar gida.
Zama tayi akusa da Inno wacce ta zuba tagumi sai jimami takeyi, tsakin data ja shiya sa Inno kallonta kafin tace “kiyi hakuri yar uwa kinji, Allah dai ya bashi lafiya yasa kaffara ne sannu kinji” hararanta Hama tayi kafin tace “eh wato ga mijinki koh eh ai dole ki wani zuba tagumi kamar kinrasa tsofaffinki mara mutunci ashe kina sane bai da lafiya amma kika ki kifadamin dan dai kawai kin iya munafirci”.
Kallonta Inna tayi cikin takaici tace “Ni bansan sanda zaki farayin zato mai kyau ga yan uwanki ba wallahi Hama ni ban san komai ba akan haka amma kiyi hakuri Allah ya bashi lafiya”.
“Dan Allah yima mutane shuru, kina na hannun damansa kice bakisan bai da lafiya ba ni zakiyi wa bariki algunguma eh lailai kin rika” Inno shuru kawai tayi dan tana ganin kishi karara atattare da kawarta aranta tace “dama ashe tana sonsa kaman yadda nayi tunani shine take mishi abunda taga dama Allah kyauta”.
Sunanan zaune shuru ko wacce da abunda take tunani likitane ya fito ya iso inda Umma take yana cewa “shin ku kuka kawo wannan bawan Allah? da sauri Umma tace “Likita mune muka kawo shi da fatan dai ya samu lafiya babu wani matsala” dai dai lokacin Hama suka iso gurinsu Umma Likita yace “Alhamdulillahi ya farfado amma menene alakarku dashi” da sauri Hama tace “mijinane ita kuma ummata sai kuma kawata”.
Likiya yace “toh wanda ya bada jininsa fa? duk da taji haushi jinin da ake cewa Sagir ya bayar sai dai kawai ta daure tace “kaninsane ya bada dan Allah ya jikin nashi zan iya shiga in ganshi ince dai da sauki dai? ta jero tambayoyin a tare, Likita yace “eh da sauki dan ya farka dazu kuma jikinshi ya rage zafi amma munyi mishi alluran barci yanzu saboda ya samu ya huta sosai dan jikinshi ba karfi” Hama tace “toh Likita mungode Allah saka da alkairi” zama tayi a kujeran dake gurin sannan tace “Umma zaki iya tafiya kije gida ki huta dan Allah kuma ki gaida Baba” Umma tace “toh ai shikenan tunda kince haka Allah ya kara sauki bari zanje inyi abinci idan Sagir ya dawo seyazo ya kar6a” murmushi Hama tayi sannan tace “toh Umma mungode, Inno dan Allah dan rakata ta samu acha6a ga kudi sai ki biya” ta fada tana mika mata naira hamsin.
Hasiya sannun da zuwa ga tabarma zauna Kawu ya fada yana murmushi “ina wuni kawu” Hasiya ta fada bayan ta zauna” shima ya amsa da “lafiya alhamdulillahi ya kuma mutanen gidan naku? Tace “lafiya lau duk suna mika sakon gaisuwa dama Goggo ce ta aikoni wajenka wai dan Allah karanta mata kudu zataje biki” shuru yayi na yan mintina kafin yace “toh nima kuma gaskiya dazu na bada rance amma miyasa bata aiko tun tuni ba, ko dayake bari dai na
duba mata ko za’ayi dace” d’aki ya shiga bai jima ba ya fito “toh ga wannan amma kice mata ta rike duka ba sai ta dawo dasu ba, ke ma gashi ba yawa” ritsinawa tayi tana cewa “toh Kawu mungode Allah ya saka da alkairi, Inna sai anjima” Inna tace “toh hasiya mujima dayawa.
Goggo harta gama wanki taga hasiya dai bata dawo ba harta dauko mayafi zata rufe kofa sai kuma ta jiyo sallamarta
ajiye mayafin tayi sannan taje ta bude mata kofa “ya naga kin dade ko baki samu Kawun naku bane? Hasiya tace “aa na same shi yana gaisheki” washe hakora Goggo tayi kafin tace “yawwa ya baki koh? Hasiya tace “eh ya bani gashinan, wannan kuma ya bani muraba nida su Sagir” murmushi Goggo tayi kana tace “Kawu kenan baya gajiya damu to nagode Allah ya saka mishi da wanda yafi wannan” Hasiya tace “amen, sannan yace ba sai kin biya ba ya baki halaq malak” Gogge ta zaro ido tana cewa “haba da gaske yarnan” Hasiya tace “eh wallahi Goggo yanzu dai bari in kimtsa sai muci abinci mu tafi ko?” kafin ta amsa Sagir ya shigo fuskarsa ba alaman murmushi ba kaman kullun ba hakan yasa goggo tace “babana
lafiya kuwa na ganka haka? Sagir yace “inafa lafiya ya Jibir jikinsa ya tashi yana asibiti yanzu hakama sai da aka kara mishi jini” dafe kirji tayi tana cewa “amma dai da sauki koh innalillahi wa inna ilaihi rajiun, toh wani asibitin kuma kai shi ina Hama? Sagir yace “sauki hospital suke Hama suna chan harda Umma ma tana chan nima naje gun abokina ne shine na gansu a gurin” mayafi ta janyo tana cewa “Hasiya tashi ki sayo mishi abun karin kuzari yaci abinci ya huta bari inje indawo” Hasiya tace “toh Goggo ki gaishesu Allah ya kara wa Yaya lafiya”.
♾♾♾
“Kai alamarin zaman garinnan har yanzu na kasa sabawa dashi tun lokacin dana dawo” ya fada yana kada kai “uhm ai ba acewa komai Jauro irin wannan zama yana da wahala musanman a wannan lokacin da jamaa suka koma kiwon dan adam sukabar dabbobi, sai kaga mutun ya 6ata lokacinsa da dama akan abunda bai shafeshi ba” Hamza ta fada yana shan rake “aini wannan abun shi yafi damuna shiyasa ni kam ban damu da zaman majalisa ba domin da an hadu sai afara maganar ya harkokin wane ke tafiya aishi yasa zakaga da an hadu anyi yawa aguri nake hanzartawa inbar gurin sai kaga anata gardama akan wani abu wanda bai shafi addiniba babu sana’a sai zaman kashe wando, bari inje gida sai mun hadu gobe” Jauro yace yana yiwa Hamza sallama.
Tana dawo gida ta tarar har yadawo “Yaya barka da yamma” ta fada tana cire hihab dinta “yawwa harkin dawo” tace “eh na dawo yanaga kadawo da wuri yau? hade rai yayi yace “bansani ba bari Baba ya dawo na fada masa cewa kin fasa auren kin samu wani agarinnan” murmushi tayi tace “yi hakuri Yayana wallahi bazan
sake kula kowaba”.
“Yaya yau danbu zanyi wa baba kuma nasan kai baka so, yanzu fadamin mai zakaci” murmushi yayi yace “duk abunda zakici shi zanci” itama tace “toh nima ai danbun nikeson inci” 6ata rai yayi yace “ok ni baki sona sai dambu toh nagode ni ba zanci komai ba shima Dambun na fara kishi da shi tunda kina sonsa ni baki sona” kallonshi kawai takeyi kamar zatayi dariya sai kuma
tayi murmushi kawai tace “yi hakuri yaya ni kai nake so bari zanyi mana dan wake da hadin salad” murmushi yayi yace “toh shikenan kokefa amaryar Hamza” 6ata rai tayi tace “ayya yaya kai koh” shima yace “menayi kuma toh kiyi hakuri” “toh shi kenan nayi”.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
*Zahrateey98 on wattpad*
Dedicated to Humaira A Alkali😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
1⃣9⃣♾2⃣0⃣
Satinsu Hama biyu acikin asibiti, sannan aka basu sallama. Sosai Jibir yaji dadin jikinsa sannan ya d’au aniyar fara zaman aure da Hama, amma idan bai samu hakan ba tabbas sai dai ya kara aure.
Cikin satin da suka koma gida, Inno ta tattara ta koma gidansu shi kuma Jibir ya angonce. Abun nema ya samu domin wani sabon salon iskanci Hama ta 6ullo dashi na sanya Jibir aiki ba dare ba rana ahaka dai yakeyi dan saboda zaman lafiya.+
Akwana atashi asaran mai rai watansu tara da aure Hama ta haifo d’an ta namiji wanda yaci sunan mahaifinta Mahdi ana kiransa da Balarabe. shekaran Balarabe goma aduniya ta haifi Sulaiman wanda yaci sunan Malam Sada wato marikinta, alokaci Inno kuma tayi aure ta haifi y’ar ta mai suna Aishatu suna kiranta Shatuwa.
Shekaran Sulaiman Biyar ta haifi Hamza wanda yaci sunan yayanta daya rasu (injita da fad’a) suna kiransa da Mufeed sai yan ukunta da sukaci sunan mahaifiyarta dana Jibir sai namiji wanda yaci sunan mahaifin Jibir mai suna Ibrahim ana kiransa Ibro. Watansu uku da haihuwa matan suka rasu sai a sannan Inno ta haifi yan biyunta Samha da salma daga nan duk basu sake haihuwa ba.
Balarabe nada shekara ishirin da biyu aka aura mishi Aisha d’iyar Inno mai shekara goma sha bakwai Bayan auren da shekara d’aya iyayenta suka rasu ahatsarin mota daganan rikonsu ya dawo hannun Hama (Samha da Salma).
Shekaru biyu da Aure suka haifi Sarah wanda a yanzu ta gama ss3 kuma ta samu gurbi a jamiar Bauchi. Kokarinta yasa tana jss1 tayi waec haka a ss2 tayi waec da neco yanzu haka shekarunta goma sha shida amma girman jikinta yasa ba’a ganewa, sai Hanif mai sunan mahaifin Aisha shi kuma yana ss2 shima a jss2 yayi Junior waec, a yanzu haka yana shirin senior waec, shekarunsa sha biyar daganan sai Kabir wanda yaci sunan mahaifin Inno shi kuma yana Jss3, kuma shine kawai bashida kokari, shekarunsa sha uku.
Malam balarabe da sulaiman NCE sukayi, Mufeed ne kawai ya tafi jamiar Jos yana karanta computer science, sai Auta Ibro da yaki karatu yana chan gurin Hama a kauye.
Samha da Salma sunyi karatu a poly inda suka karanta Islamic studies, yanzu haka ana shirye- shiryen aurensu ne da yaran yayan mahaifinsu wanda suke aiki a garin Adamawa. suma kuma tagwaye ne sannan sune auta agidansu.
Hanif yaje gaida Goggo ne saboda rashin lafiya da tayi kwana biyu, da Mufeed ne zai he sai kuma aka kirasu a makaranta ita kuma Sarah tak’i zuwa dan batason masifar Goggo su Samha kuwa suna ta shirye-shiryen bikinsu Sulaiman na chan gurin aikinsa yayinda Kabir ya kwanta zazza6in k’arya, hakan yasa aka tura Hanif badon Aisha taso ba dan Hanif basu jituwa da Goggo sam-sam.
A6angaren Goggo kuwa gani takeyi kaman Aisha ce take sanya jikokin nata suna mata rashin mutunci, alhali ita take janyowa kanta saboda zafin iyayensu da takeyi wanda ke fusata su har suma su bakanta mata rai.
♾♾♾
Shekaru sun shud’e abubuwa dayawa sun faru masu dadi da kuma marasa dadi amma duk mai imani sai dai yayi godiya ga Allah akan ni’imar da yayi masa na ko wani kaddara domin ko wani mai rai yana tare da jarabawa sai dai yayi fatan Allah ya bashi ikon cinyewa.
A6angarensu Hamza da Rashida suma anyi bikin su, bayan bikin da sati guda Malam Adnan ya rasu. Sosai mutuwar Malam Adnan ya gigitasu bama kamar d’iyarsa Rashida sai da tayi sati biyu a asibiti kafin ta dawo dai-dai. A haka ma sai da aka had’a da rokon Allah domin duk ta fige ta fita a hayyacinta.
Mutuwar rigar kowa, bayan wata biyu da rasuwan Malam Adnan suka koma al’amuransu tare da dangana domin sun san cewa hakuri shi ya kamacesu.
Da dadi da ba dadi haka suka cigaba da rayuwa har Allah ya azurtasu da samun yara shida, Anty Raihana da Raihan sune manya dake yan biyu ne sai Muhievert, Zahra sai Adnan sannan Yazeed wanda shine autansu.
Kasuwanci kala daban daban Hamza yakeyi kuma baya raina sanaa duk kankantarsa ahaka har Allah ya azurtashi da arziki mai dimbin yawa wanda bai san iya ma adadinsu ba.
Yaranshi baki d’aya sun samu tarbiyya dai dai gwargwado sa6anin Muhievert da takeson take sani duk da cewa sunyi karatu mai zirfi kuma suna kanyi domin an kusa saukansu na haddar al qurani mai girma.
Tabbas wannan halin na Muhievert jarabawa ne a garesu domin duk wani tarbiyya sunyi kokarin bawa yaransu tun daga kan rainonsu har zuwa girmansu.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Dedicated to Haima Mmn Abul)😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
2️⃣1️⃣♾2⃣2️⃣
Da sanyin safiya Sarah ta fara shirye shiryen tafiya makaranta, duk wani abunda ya dace ta tafi da su Malam Balarabe ya tanadar mata iya karfinsa. Botiki ta d’auka ta d’ibo ruwan wanka, ko da ta fito bata wani 6ata lokaci gurin shiryawa ba. Cikin Farin doguwar riga ta fito, da y’ar gyalensa da ta yafa a saman kan ta.
Zama ta yi a kusa da Umma ta na jimamin rabuwa da ita, kallon ta Umma tayi tare da yin murmushin k’arfin hali dan itama tabbas zata yi kewar d’iyar ta wacce ta fi kauna sama da komai a duniya. Sarah yarinya ce mai biyayya da girmama na gaba da ita, ga tausayi da jin k’ai.
+
Ganin hawayen dake zuba daga idanunta ya d’aga wa Umma hankali “haba y’ar nan sai ka ce rabuwar har abada wato rabuwar mutuwa, idan ki ka sake hawayenki ya cigaba da zuba tabbas zan cewa Malam ya fasa kai ki makarantar tunda ba ki son ki karo ilimi” Umma ta fad’a tana mai kokarin mai da nata hawayen dake komarin zubo wa, a yau ji take yi kamar zasu yi rabuwa ne na tsawon lokaci kuma tamkar akwai abunda zai iya faruwa da d’iyar ta, tun safe take jin fad’uwar gaba wanda ta rasa dalili, amma addua shine zai zame mata makami.
Jin abunda Umma ta ce yasa tayi saurin share hawayenta tare da kirkiro murmushin dole domin kwantar da hankalin Umman “ki yi hakuri kin ji Umma ta, ba zan sake ba, duk da cewa zan yi nesa da ku amma kuma da yardan Allah ba zan bari tarbiyyar da kuka bani ya tafi a banza ba, zan yi kokarin kare martabar kaina da mutuncin gidan mu da yardar Ubangiji, Umma ki cigaba da yi min addua kamar yanda ki ka saba” ta fad’a tana danne kukan da yake kokarin sake zuwa mata, domin bata son ta tashi hankalin Umma, ita kan ta, ta rasa kukan nata ko na meye ne domin tana ji ajikinta kamar akwai abunda zai same ta.
Nasiha Umma ta yi mata mai ratsa jiki wanda ya sa jikinta ya yi sanyi, kafin Malam Balarabe da yake jin su shima ya fito ya yi na shi, sannan ya aika aka kira mishi mai Napep. Bayan sun saka kayan a cikin Napep din, Malam ya zauna a gaba ita kuma Sarah a baya tare da kayanta, Umma ba ta iya komawa cikin gidan ba sai da taga sun kurewa ganinta. Ita kuma Sarah tana ganin ta dena ganin Umma ta fashe da wani irin kuka wanda ya karya zuciyar Malam din, har ya ji kamar ya ce kawai ta fasa zuwa dan tunda yake bai ta6a ganin su cikin wannan yanayin ba, kuma ya rasa dalilin faruwar hakan duk da cewa shima ya fara jin rashin natsuwa akan tafitar diy’ar sa amma dole ya aro jarumta ya yafa dan karsu sanyaya mata guiwa.
Karfe Takwas dai dai ta yi musu a cikin gareji inda mai napep ya sauke musu kayan, Malam ya ce ta jira shi a gurin, shi kuma ya shiga dan sama mata motar Bauchi. Cikin ikon Allah ya samu mota d’aya wanda mutane biyu kawai ake bukata ya cika, kud’i ya biya sannan ya koma suka taho da Sarah. Gaba ta shiga saboda bayan duk ya cika, basu dad’e ba suka samu cikon na biyun, Sarah bata so zama da gardi ba, amma haka ta matsa mishi ya shiga, sai da Malam ya ga tashin su sannan ya koma gida.
Suna cikin tafiya direba ya faki idonsu ya tura wani abu cikin abun Ac, sannan ya kunna Ac din. Cikin kank’anin lokaci kowa yayi barci a motan banda direba da ya rufe ruskar shi da face mask. Murmushi yayi sannan ya k’ara gyara belt dinsa kafin ya juya kan motar zuwa wani hanya daban.
STORY CONTINUES BELOW
♾♾♾
Wanne za’a fasa mutuwa ko hisabi, cikin sati d’aya da Muhievert tayi cikin yan uwanta kamar abun kirki, sai ga shi angulu ta koma gidanta na tsamiya dan yanzu rashin jinta sai abunda yayi gaba, dama chan ba ta shakkar kowa balle yanzu da ta kara yin gaba a harkar rashin jin magana, bata tsoro bare shakkar kowa kawai duk abunda ta ga shi take son yin toh babu shakka shi zata yi.
A yanzu addua shine abunda mahaifiyarta ta duk’ufa yi a ko wani rana dan neman shiriya gareta da sauran yan uwanta da kuma yara ire iren ta. Yaya Raihan shima ya zuba mata ido domin ya rasa abunda zai yi mata bayan addua, kannen ta kuwa dama sun saba shi ya sa ma basu damu ba.
Kamar kullun yau ma karfe Tara da rabi ta shiga aji, a lokacin saura minti talatin a gama lecture, MRM shine ya kasance malamin su na yau, kuma sabon lecturer a department din su, sati na biyu kenan da fara zuwa ajinsu, kasancewar sa ba mai magana ba shiyasa bai ta6a nuna ya ganta ba balle ya kula ta, a cewarsa ai karatun amfanin sune ba nashi ba. Sosai ta ji haushin rashin kula ta da yaki yi hakan yasa ta fara yin k’ara da takalminta ji kake “kwas kwas kwas” duk da haka bai tanka mata ba ya cigaba da lectures din sa, sosai ya burge mafi yawancin d’aliban sa yayin da masoyanta suka ji haushin sa na kin kula tauraruwarsu.
A yanda ta shaka irin wannan wulakancin ba ta jin zata iya zama a cikin ajin, hakan yasa ta fita ta bar makarantar baki daya sun jima suna ta tafiya a kan kwalta kafin ta ce ya kaita gidan Anty Raihana, babu wanda ya sake magana a cikin su har suka isa gidan, suna zuwa ta ce mishi ya je ya dawo zuwa yamma. Toh kawai ya ce mata sannan ya d’auki hanyar gida, da wani irin gudu yake tuk’i saboda yunwar daya addabe shi, tun safe daya kawo ta, ta ce ya jira ta ba zata dad’e ba, gashi babu abunda yasa a cikinsa, tsaki kawai ya ja yana mai Allah wadai da halin Muhievert.
Da sallama ta shiga falon, jin shuru yasa ta kwanta a kan doguwar kujerar dake cikin falon, bak’in ciki yasa barcin dole ya d’auke ta. Ko da Anty Raihana ta fito tayi matukar mamakin ganin ta, murmushi kawai ta yi sannan ta cire takalmin da ke sanye a kafar ta, wanda tsaban lakaci ya sa bata cire ba da ta shigo. Kitchen ta wuce tana tunanin abunda ya kawo Muhievert din gidan ta da sanyin safiya gashi kuma da alama tana cikin damuwa.
Sai kusan azahar ta farko d’auke da adduar barci a bakin ta, tashi tayi kafin ta shiga d’akin dake ta cikin falo, towel ta d’auka sannan ta shiga wanka. Ko da Anty ta fito jere abinci a dinning bata kula da cewa bata nan ba, sai bayan ta gama ta zo da niyyar tashin ta, dan ta yi sallah shine ta ga bata nan, d’akin bak’in ta lek’a ta ji alamun ruwa a band’aki, hakan yasa ta wuce d’akin ta dan yin sallah.
♾️♾️♾️
Babban gida ne, mai matukar girman gaske, wanda daga gate baka iya hango ainihin tsarin cikin gidan, amma daga wajen da iya yanda za a iya gani za a fasalta shi da gini mai kyau da tsari. Domin tsawon katangar gidan ya wuce tunanin mai karatu, Gidan zagaye yake da folisawa ta fanni daban daban kuma ko wanne fuskar sa babu alamun rahama a tare da shi. Wani motar taxi ne ya tsaya a kofar gidan, jim kad’an wani mutun ya fito a cikin sa tare da mik’a wa na taxi d’in kud’i sannan ya nufi hanyar shiga gidan. Cikin sauri suka bud’e mishi k’ofar gate din tare da sara mishi cikin girmama wa. Folisawa biyu ne suka bi bayan sa bayan sun k’ar6i jakar dake rike a hannun sa, har zuwa wannan lokacin fuskar mutumin a rufe yake da wani kyalle.
Tafiya suka yi mai nisa kafin suka iso k’ofar gate na biyu a cikin gidan, bud’e musu gate din aka yi tare da sake sarawa wannan mutumin, wani had’add’en gida na gani wanda za a iya kira da aljannar duniya, duk iya hassadar mai hassada ba zai iya kushe had’uwa da tsaruwar gidan ba, ko ina glass ne a zagaye kamar ginin gidajen turai, wanda na ciki na iya hango na waje yayin da shi na waje sai dai ya ga kan sa ta jikin glass din. Sosai tsarin gidan ya burgeni, ko mai na fenti an yi amfani da fari ne da kuma ruwan toka wanda ya kara haska gurin sosai sai filawowi dake kewaye da ko wani kusurwa na gidan a cikin manyan tukwane na zamani wanda ake amfani da su gurin k’awata guri.
“IMAM” shine sunan da aka ambata bayan ya shiga cikin gidan. Kallon matar ya yi kamar ba zai tanka ba sai kuma ya k’arasa cikin babban falon daya cika da kayan more rayuwa masu d’aukan hankali, zama ya yi a d’aya daga cikin kujerun dake a cikin falon sannan yace “ina fatan ba maganar da muka saba bane? idan shine ki adana kalaman ki Didi dan ba zai shiga kunne na ba, na sha gaya miki cewa ni bana ra’ayin abunda ki ke kokarin son ganin na aikata, dan Allah Didi mu hakura da wannan abun tunda shine farin cikin Momma, kin sani nima na sani matukar muka koma da zummar aikata abunda ki ke so d’in toh Momma ce zata shiga halin damuwa kuma kinfi kowa sanin ciwon ta baya buk’atan hakan” yana gama fad’a ya tashi yayi wucewar sa.
Hawaye ne ya zubo daga idanun Didi tana mai Allah wadai da halayyar iyalen gidan su da kuma yan uwan su da dangin su baki d’aya domin sune silar rushewar rayuwar ta dana tilon d’an ta IMAM. Shin yaushe ne zai samu gatan kiran mahaifinsa da Uba shin sai yaushe ne mahaifinsa zai yarda da cewa shi din gudan jinin sa ne kuma mai iko da wannan mulkin da ake kokarin bawa wani mai amsa sunan Yarima mai jiran gado wanda da za a yi bincike da an tono abubuwa da yawa a kan sa da kuma uwarsa baki daya.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
2
Dedicated to Mrs Aliyu😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
2️⃣3️⃣♾2⃣4️⃣
A maimakon su yi hanyar Bauchi sai suka yi hanyar Jos, tafiya sukayi mai nisan gaske wanda ya kai su cikin Nasarawa. Kuma ko sau d’aya babu wanda ya farka a cikin motar domin abunda ya fesa musu mai karfi ne.
Wani d’an k’aramin kauye suka nufa a cikin garin Nasarawa. Karamin gari ne wanda babu mutane sosai a cikinta, domin jefi jefi za ka ga giftawar mutun. Cikin wani unguwa mai d’an daji daji suka nufa, a bakin wani k’aramin gida direba yayi horn, koda mai gadi ya lek’o sai yayi saurin bude musu gate din. Bayan sun shiga direba ya fita ya shiga cikin gidan.
+
A k’ofa suka yi kicibus da Ogansa Tom wanda yake sanye cikin kaya marasa nauyi rigar jessi kore da kuma short shima kore sai wani katoton sarkar wuya mai alamun cross a jiki. Murmushin jindadi yayi ganin Reza babban ma’aikacin sa wanda ya amince da shi fiye da kowa “Nayi tunanin ko an kama ku ne ai, dan ance min yau mutanen suna aiki a hanya saboda wani senata da aka sace a tsakanin Jos da Nasarawa”.
Murmushi Reza yayi cikin gur6ataccen Hausar sa yace “haba Oga mutanen mu nefa, kolawa ai suna ganin bugun abuja komai ke tafiya dai dai, na had’u da Samuel a check point din ai shine na d’an sa mishi abu a hannu kawai yayi dariya yace mu ware abun mu” ya fad’a cikin jin dadin abunda ya yi din kafin ya cigaba da cewa “Oga an samu Maza Tara da yan mata uku, ga su chan suna mota ina Joy take da Philip suzo mu shigo dasu”.
Sunan su Oga Tom ya kira, cikin sauri suka fito Joy na gyara riga Philip kuma na gyara belt din wandonsa, kallon minti Biyu Oga Tom ya musu ya fahimci abunda suke yi “ku baku gajiya ne da wannan abun da kuke yi? Kulllun safe rana da dare shine abincin ku, ina fata dai kuma zuwa check up dan tabbatar da lafiyan ku saboda nasan cewa da kowa ma kuna yi babu kariya. yanzu ba wannan ba kuje waje ku shigo da mutanen dake cikin mota ina jiranku” ya fad’a tare da koma wa cikin falon yana mamakin su Joy da abunda suka sa a gaba, shi mata basa gaban shi dan bai yarda dasu ba, yanzu sai su 6ata mishi aiki, shi bayan kud’i babu abunda yake ransa kuma ko zai yi auren ba zai iya auren kirista ba sai dai ya auri musulma dan sunfi rike amana musanman wanda sukayi zirfin ilimi na addinin su, kuma shi ba zai auri wanda tayi zirfin ilimin boko ba dan ba zai d’auki rashin kunya ba.
D’aya bayan d’aya aka shigo dasu kamar wasu matattu, kwantar dasu a kayi a falon, sai da Tom ya gama kare musu kallo sannan yace a kai mazan d’aki d’aya suma matan a had’a su a d’aki guda, har sun fara chinci6an su, ya dakatar dasu ya kalli su Philip “kun san dai bana so kuna shiga harkan da bai shafe ku ba, dan haka ku kiyaye kar inji labari ko in gani, babu ruwan ku da mutanen da nake ajiyewa dan haka duk abunda za kuyi kuje waje kuyi akwai ga yan mata da samari da yawa a cikin gari kuyi duk abunda kuke so kuyi dasu, idan kunne yaji jiki ya tsira, zaku iya tafiya” Ko kad’an ran su bai so hukuncin nan ba dan ita Joy taga wani saurayi da ya yi mata kuma idan har ta samu dama ba zata bari ya wuce ta ba, shima Philip tunda ya d’aura ido akan Sarah ya ji ransa ya biya kuma ya d’au aniyar biyan bukatan sa akanta matukar ya samu dama.
STORY CONTINUES BELOW
Kamar yanda Oga Tom ya ce haka suka yi, maza aka kai su d’aki d’aya su ma mata aka ajiye su a d’aki d’aya, bayan sun fito suka gark’ame kofar tare da bawa Reza keys din dan dama a hannun shi ake bari saboda sanin halin su Joy din.
♾♾♾
Direct d’akin Momma ya wuce, sallama yayi kafin ya shiga bayan ta amsa, zama yayi kusa da ita, ya kwantar da kan sa a kan cinyarta “Momma jikalle ya dawo me zan samu ne y’ar matata” murmushi tayi kafin tace “wai sai ka karyani ko Imamu, maza d’aga ni idan kayi zuciya inji labari mai dadi, tashi tashi nace kafin in buga maka wannan sandar da kanka kamar kwakwa”.
Saurin tashi yayi dan ya san halinta tunda tace idan bai tashi ba zata buga mishi sandar toh kadan da aikinta ne “Ni din zaki kwale wa kai, ni din nakin, haba Momma na wanda babu kamarta a fad’in duniya bayan Didi na” ya fad’a cikin tsokala dan ya san sarai Momma akwai kishi bata son a had’a ta da koma waye ne.
Hararan sa tayi sannan tace “an dai ji kunya kana ma kallon kan ka kuwa? Kai din fa ba yaro kake k’ara zama ba, ka bar ganin cewa kana da jiki k’arami shekarunka dai k’aruwa suke yi gwarama ka dai na yaudaran kan ka Imamu, ban san ko ni din ce baka so inga jinin naka ba ko kuma Kubra ce baka son taga jininka Allah masani, ni dai ina fad’a maka kullun ka bar wa Allah komai duk wani wanda ya cuce ka Allah zai saka maka, ka cire duk wani damuwa a cikin ranka kayi walwala yanda ya dace, ga shi ka wani je ka shiga aikin yan sanda ka k’aro lalaci sai kayi ta had’e rai kamar hadari to dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka! Ai ko ni na gan ka ba zan kalle ka sau biyu ba, kwanciyar hankalin Kubra da nawa shi ne muga kayi aure ka zama cikekken mutun” ta fad’a tana ta6e baki tare da 6antaran goro.
Dariyar sa ya gimtse dan sanin cewa yana yi a fili ya shiga uku, hakan yasa ya ja baki yayi shuru tare da fita daga d’akin sakin alin, harara ta sake banka mishi tare da tsuka tana ta mitan cewa aljanu ne suka aure shi shiyasa yaki aure har zuwa yanzu in ba haka ba yaro ya kai shekaru talatin da biyar har yanzu ba labari shuru kake ji kamar an shuka dusa, tabbas dole ta fara yin ruwan addua tana ba shi yana sha saboda ya kore duk wani ifiritun da ke cikin kan sa, idan ma d’an aike ne ya koma gun wanda ya turo sa.
D’akin shi ya haura yayi wanka sannan ya sako kananun kaya ya sauko downstairs dan cin abinci, ko da ya sauko Didi bata falo tana cikin d’akin ta, kallon agogo yayi ya ga lokacin sallar la’asar ya kusa, zama yayi a kan dining table ya bubbud’e kulolin, tuwon alkama ne da miyar kuka sai kuma goten tsaki na gero wanda ya sha ganye da man shanu sai wani kamshi yake yi mai dadi, rufe goten yayi a cewar sa sai dare ya dace yaci wannan, bude tuwon ya yi, ya zuba malmala daya sannan ya diba miya dai dai misali lafin yayi bismillah ya fara ci cikin natsuwa yana yi yana kora zo6on da Momma tayi.
Bayan ya gama ci, sai ya nufi masallacin su dake cikin gidan inda suke salla tare da ma’aikatan sa musulmai. Bayan ya idar ya d’auki qur’ani ya fara tilawa cikin kira’a mai dadi wanda ya sa dayawan ma’aikatan sa ke son zama a cikin masallacin bayan sallar la’asar da sallar asuba. Feji goma ya karanta a cikin suratul bakara kafin yayi adduo’i ya shafa.
Cikin gida ya koma inda ya samu Momma a falo tana kallon tashar Sunna Tv inda shiekh Kabiru gombe yake wa’azi, zama yayi a gefenta ya natsu tare da kasa kunne da kyau saboda sanin halin Momma yanzu zata ce babu abunda ya ji a ciki kawai ya tsurawa tv ido ne, idan ya musa zata fara jero tambayoyi akan abunda yayi, idan ya amsa a rabu lafiya idan ya kasa haka zata yi ta masifa har washe gari.
Wa’azi malam yake yi akan yara marasa jin maganar iyaye da kuma nagaba dasu, yara masu raina manya da nuna isa dan suna yaran wasu, irin tarbiyyar yaran yanzu da yanda Rayuwar Zamani ya kasance mutane na yin abunda suka ga dama ko da ya sa6a wa addini, kaga musulmi ya yi shiga kamar wani kafiri, sosai malam yayi wa’azi da nasiha ga masu halin banza. Tunda malam ya fara wa’azi Imam ya tuno da dalibar sa wacce ko sunanta bai sani ba mai nuna gadara da iko kamar wacce ba a cikin kasa za’a saka ta ba haka zata dawwama a cikin duniya, murmushi yayi kawai dan duk abunda malam ga fada kamar ma ya santa da ita kawai yake yi.
♾♾♾
Bayan tayi salla ta fito ta zauna a dinning tare da bawa cikinta hakkinsa, ko da Anty Raihana ta fito bata kula ta ba itama ta d’ibi abinci ta fara ci tana danna wayarta, sai bayan da suka gama cin abincin Anty tace ta zo falo suyi magana, d’ebe kwanonin Muhievert tayi ta kai kitchen sanin halin yayarta yasa bata yi gigin barin kwanon a gurin ba.
Falo ta dawo ta zauna kusa da Anty Raihana kafin ta fara bata labarin abunda ya faru wanda ya 6ata mata rai shiyasa ta kasa zama a makarantar ta zo gidanta dan baza ta koma gida ba saboda ba kowa duk yaran sun tafi makaranta Yaya Raihan ya tafi gurin aiki, Ammi kuma yau ana bikin yar aminiyarta shiyasa ba zata same ta a gida ba.
Kallonta Anty Raihana tayi na wasu yan mintina kafin tace “yanzu Muhie rayuwar da kika za6awa kan ki kenan? Ina karatun islamiyar naki yake tafiya ina tarbiyyar da Ammi ta mana? Duk kin zubar da su kin ari rayuwar wasu da d’abiar wasu kin yafa wa kanki, wallahi ki kama kanki kiji tsoron Allah kiji tsoron duniya domin shi wannan duniyar ba gurin zama na har abada bace, duniya budurwar wawa ki bi a sannu kafin ke wasu dayawa sun zo sun tafi, kamar kasuwa ce yana ci a koda yaushe kuma mai sa’a ya tashi da riba, kar ki zo kina ihu bayan hari dan shi dana sani ba wai wani dadi yake da shi ba saboda babu halin mai da hannun agogo baya, idan kuma kin kiji gaki ga duniya ya isheki riga da wando har ma da zanin daurawa, gani ga wane ya isa wane tsoron Allah, ki raba kanki da wahala, ni dai na fada miki wallhy ki raba kanki da wahala, wanda bai ji bari ba zai ji hoho, maza yanzu ki kira Sulaiman yazo ya mai dake makaranta tunda ba ku gama lectures ba”.
Takaici ne ya ishi Muhie tsaban haushi da 6acin rai yasa ko ta kan direba bata bi ba, ta kwashi jiki tayi tafiyarta gida a cikin napep, ita dai Anty Raihana ko a jikinta, gaskiya ne dai ba zata dai na fad’a mata ba domin naka naka ne duk lalacewarsa kuma jini d’aya ya wuce wasa, ita din dai itace zata fad’a mata gaskiya a matsayin ta na yayarta.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Dedicated to Ayeesha Song😍 ina jin dadin comment dinki😘
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
2️⃣5️⃣♾2⃣6️⃣
Fushi ta yi sosai da Anty Raihana, hakan ya sa, ba ta sake zuwa gidan ba. Ko da Ammi ta dawo ba ta bi ta kan ta ba, saboda Anty Raihana ta fad’a mata yadda suka yi da ita. Tun da ga ranar, ba ta sake fita ko ina ba har makaranta, sosai abin ya ba wa su Slimzy mamaki hakan ya sa ana gama lectures suka had’u dan zuwa duba ta.
+
Ko da suka isa gidan, mai gadi suka taras a bakin k’ofar gate ya na sauraron Radio. A tare suka gaishe shi sannan suka tambaye shi ko Muhievert na gida, ya na kok’arin amsa mu su sai ga Sulaiman ya dawo da ga kai Yaya Raihan gurin aiki “yawwa ku tambaye shi dan ban sani ba k’ila ta na ciki ko ta fita” ya fad’a ya na gyara zaman shi a saman kujera.
Gaishe da Sulaiman suka yi tare da tambayarsa ko Muhievert na gida “eh ku shiga ta na gida dan yau babu in da na kai ta” ya fad’a musu tare da shige wa d’akinsa. A k’ofar shiga falo suka had’u da Laure mai aiki, gaishesu ta yi sannan ta ce da su, su zauna bari ta kira ta.
Zaman minti biyar suka yi sannan Laure ta fito ta na cewa “ta ce wai ga ta nan zuwa” godiya suka mata bayan ta cika musu gaba da kayan ciye-ciye.
Zaman mintina talatin suka yi, har sun gama cinye cake, spring roll da lemon kwalin da Laure ta kawo musu amma babu alamun Muhievert, suna shirin tafiya kenan sai ga y’ar mulkin ta fito, zama suka yi ran su ba dadi, a hankali take sauk’o wa da ga matakalar benin har ta iso cikin falon ta samu guri ta zauna. Jin shurun ya yi ya wa ya sa suka mik’e tare da cewa “da ma mun zo mu duba ki ne, mu ji ko lafiya ki ka dai na zuwa makaranta, ga shi an kusa fara test k’ila cikin sati mai zuwa” Slimzy ta fad’a cikin 6acin rai a kan abin da Muhievert ta musu, ai wannan walakanci ne, ko da yake su suka kawo kan su dan haka bai dace su ji haushi ba.
Sai da ta hura chewn gum din bakinta ya yi k’ara sannan ta ce “Ayya ai ni ban san cewa za ku zo ba, dace wa ya yi ku fara kira na a waya kafin ku yi min zuwan ba zata, amma dai ya wuce next time sai ku kiyaye, batun zuwa makaranta kuma sai wani sati zan shigo gaskiya dan wannan satin ina huta wa, zaku iya tafiya na gode” ta fad’a tare da mik’e wa ta haura sama ta na tafiya ta na kad’a jiki.
Baki bud’e suke kallon ikon Allah, duk da cewa su na morarta amma kuma abun na ta ya fara yawa gaskiya, walakanci iya walakanci yau ta yi musu shi, tabbas zasu yi maganinta domin ta fara wuce iyaka. Ta shi suka yi tare da fice wa a tare, ko da suka shiga mota babu mai yi wa wani magana a cikinsu har suka k’arasa cikin makaranta.
A 6angaren Muhievert kuwa ko a kolar rigarta, ita bata san ma ta yi wani abin ba gaskiya, bata yi tunanin abin da ta yi zai 6ata musu rai ba, ita haushi ma suka bata da basu sanarda ita zasu zo ba, sai dai kawai ta ji wai suna falo. D’aki ta shiga ta kwanta abin ta tare da manna earpiece a kunnunta ta na sararon wak’ar Nicki Minaj.
Su Slimzy kuwa sun fi minti goma a zaune cikin mota babu wanda ya ce wa wani cas har sai da Tukur ya ja tsaki sannan Babayo ya ce “kai baba a can gidan ya dace ka yi tsaki a ba a nan ba, dole ne mu nuna wa wannan yarinyar kuskuren ta, ta yadda ba zata sake yi wa wani irin hakan ba” Iliya ne ya ci gaba da cewa “tabbas ka yi magana a nan abokina dole ne mu san abin yi wanda zai sa ta yi dana sanin rashin kunyar da ta sa a gaba, domin ita nata rashin arzikin wasan yara ne, mu zamu nuna mata yadda ake buga wasan dan ta san cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane” dariya Slimzy ta yi sannan ta ce “tabbas kun kawo shawara mai kyau yan uwa, dole ne a yanzu mu fito mata a mutum, dan ta san cewa shuru-shuru ba tsoro bane gudun magana ne” Tukur ne ya ce su matso su ji abin da ya dace su yi mata, ai kuwa a tare suka fashe da dariya suna cewa “ashe kai ma mugu ne gaye, tabbas wannan d’in shi ne maslaha a kan abin da muke shirya wa, ta ki ta k’are yar manya” a haka suka ci gaba da tattauna wa har zuwa lokacin tafiyarsu gida.
♾♾♾
Agogon hannunsa ya kalla bayan ya cire coat din da ke jikinsa, mamaki yake yi a kan abin da ya hana dalibarsa mai abin dariya zuwa makaranta kwana biyu, duk da cewa ya ji sunanta yau a bakin wasu in da suke cewa “ai gwara da ba ta zuwa ko ba komai yanzu lectures suna musu lecture cikin natsuwa da aminci” ya yin da wasu suke cewa ai zuwanta musiba ne dan haka idan ma wani abin ne ya same ta, Allah ya k’ara dan su kam sun ji dadin koyar wa cikin satinnan.
Shi kam a sati biyun da ya yi a cikin makarantar ya na jin dadin abin da take yi din saboda ya na sa shi nishad’i a ko da yaushe “Allah dai ya sa ta na lafiya kuma Allah ya sa ta zo wani sati” shine addu’ar da yayi. Ya na gama cire kayan ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya cikin doguwar riga launin ruwan madara, wayarsa ya d’auka sannan ya nufi d’akin Momma.
Sallama ya yi, bayan ta amsa ya shiga tare da rufe kofar, Didi ya samu ta na yi wa Momma tsifa, zama ya yi kusa da ita sannan ya ce “Momma na yau kwalliya za a yi min ne? naga jiya Didi ta saka miki lalle a k’afa da hannu, yau kuma ana ta tsifa da alamun kitso za a yi” hararansa Didi ta yi alamun ya dai na damun mamanta, ko nuna ya san ta yi ma bai yi ba.
Momma ce ta ce “Allah ya tsare gatari da saran shuka, yo ina abin ya ke da zan yi kishi a kai ja’iri, ni dai ba zan fasa fad’a maka ba, ka nemo mata ka huta da gori idan ba haka ba kullum ba zan fasa maka gori ba, ni ban da damuwa na ajiye yara har shida kuma ko wacce na d’akin mijinta ga yara masha Allah, wai ni dan ubanka shanyayye da ba a aure zai auri uwarka har a same ka? Imamu ka fita a idona in rufe wallahi, ka nemo mata tun muna shaida juna kafin ka zo ka na kukan rashi na, dan nice mai yi maka fad’a da saka a hanya ita Kubra ba abin da ta sani bayan ta titse ka a gaba da zancen mulkin ubanka, ni duk wannan ba damuwa ta ba ne, fa ta na in gan ka da iyali kuma ina so ka cika min buri na kafin rai ya yi halinsa” ta fad’a ta na yarfa hannu.
Hawayen da ya gani a idon Didi ya sa kawai ya ta shi ya fita ba tare da ya ce wani abin ba, hakan kuwa ya tunzura Momma ta yi ta mita kamar zata ari baki, jin shesheken kukan Didi ya sa ta juya ta kalle ta tare da cewa “Kubra ki yi hakuri idan dan na yi wa d’an ki fad’a shi ne ki ke kuka hakan, Allah ya baki hakuri ni ba zan sake shiga lamarin ku ba” da sauri Didi ta sauko k’asa tare da durkusa wa a gaban Momma ta na mai bata hakuri “ki yi hakuri uwa ta gari mai son duk wani mutum da alkairi, ki yi hakuri ni ba dan abin da ki ka ce bane na ke kuka, kawai dai na kasa manta k’azafin da aka min ne a gidan Rufa’i, Momma ina mai bakincikin yadda Rufa’i ya rufe ido ya kasa kar6an Imam a matsayin d’an sa, sannan ina mai kishin cewa ba d’an halak ake kokarin d’aura wa a kan mulkin masarautan hankaka ba, ana kokarin bawa kafiri d’an zina sarautan masarautan mu shin har yanzu kina ganin laifina Momma dan ina son mulkin ya dawo hannun d’an halak? Idan har yanzu kina ganin laifi na ne Momma ki yi hakuri ki yafemin ba zan sake mishi maganar zuwa masarauta ba” ta na gama fad’an haka ta fita a d’akin tare da koma wa d’akinta ta kwanta ta na kuka mai ta6a zuciya.
Duk abin da suka fad’a a kunnensa ne, mamaki ne ya kama shi da jin kalaman Didi, dama ashe saboda haka take son ya kar6i mulkin masarautan, shin mai yasa bata ta6a sanar da shi gaskiyar lamarin ba, sosai abin ya ta6a zuciyarsa, ko ba komai ya fahimci cewa mahaifinsa na rayuwa a cikin mugayen mutane ne kuma ya na rayuwa cikin rashin sanin madafa domin ba a cikin hankalinsa yake ba, ya na tsaye a gurin har Didi ta fito a d’akin ba tare da ta lura da shi ba, kamar zai bi ta kuma ya fasa ya shiga d’akin Momma dan yasan dole hankalinta a tashe yake kuma ciwonta zai iya tashi, ai kuwa ya na shiga ya samu tana kwance bata numfashi, cikin sauri ya d’auke ta ya sauko k’asa cikin damuwa, k’aran tafiyarsa ne ya fito da Didi daga d’akinta itama cikin tashin hankali ta d’auko keys din motarta ta bi bayansu, ba tare da 6ata lokaci ba ya kar6i key din ya tada motar dan fita daga gidan, Didi ta na baya ta rike Momma cikin tashin hankali da dana sanin abubuwan da ta furta.
Su na zuwa asibitin aka yi saurin kar6anta, sanin matsayinta a asibitin ya sa duk hankalin likitocin ya zama a kan ta, addua suke yi Allah yasa abin ya zo musu da sauki dan idan ciwonta ya ta shi sai a hankali ba sa samun natsuwa har sai sun ga ta farfad’o. Emergency unit suka yi da ita, likitoci biyar kwararru suka shiga dan ceton ran ta, ganin yanda zuciyarta ya kumbura suka k’ara tsorata da lamarin dan abin ya yi muni fiye da ko yaushe.
Didi ta kasa zaune ta ka sa tsaye duk hankalinta ya tashi, ka sa kiran yan uwanta ta yi dan bata son ta tayar musu da hankali, karshe kuka ta saka wanda ya karya zuciyar Imam, sam-sam baya son ganin hawayenta, tausayi ta ba shi sosai, dan ya san yanzu a kan ta zata d’aura laifin, zuwa ya yi ya zauna kusa da ita tare da kwantar da kan ta a kafad’arsa ya shiga rarrashinta, daker ya samu ta yi shuru ta koma ajiyar zuciya.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Dedicated to Rerheart😍ina jin dadin comment dinki, Allah ya bar kauna😘
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
2️⃣7️⃣♾2⃣8️⃣
Hankalinsu Malam duk a ta she ya ke, ba ma kamar Umma duk ta fita a hayyacinta, tun a ranar da Sarah ta tafi suka rasa natsuwarsu, an gwada wayarta ba ya zuwa wai “not reachable” hakan ya sa suka kira Sulaiman suka sanar da shi, cikin tashin hankali ya shiga nemanta amma ba ita ba labarinta, ganin yanayin da ya shiga yasa Ammi ta ce ya je gida ya gansu ya dan yi kwana biyu sai ya dawo, sosai ya ji dadin karamcin Ammi hakan ya sa ya shirya ya tafi. A can ya samu Goggo Hama ita ma ta ci kuka ta gode Allah saboda 6atar jikarta mace kwalli d’aya. Duk wani masoyin ahalin Malam Balarabe ya na cikin jimamin wannan lamarin, tun suna sa ran samunta a waya har suka cire rai, Umma kam yanzu ciwo ya fara cin ta sosai har ta kai ba ta iya magana sai dai hawaye, duk irin kawaicinta a wannan ga6ar kasawa ta yi, Malam Balarabe kam ya yi dauriya sosai. Sati gida da faruwar lamarin ya cewa Sulaiman ya tafi gurin aikinsa, shima Hanif daker aka samu ya koma makaranta dan ya na shirin tafiya abun ya faru shi ne kawai ya yi zamansa, Kabir ma cikin satin Malam ya ta sa shi a gaba ya fara zuwa makaranta, Mufeed ma ya na shirin koma wa, ita kuma Goggo Hama ta ce babu inda za ta je har sai an samu jikarta za ta iya koma wa gida.
+
Ko da Sulaiman ya koma bakin aikinsa sai ya sa ke koma wa shuru-shuru dan damuwar rashin y’ar yayansa, sosai ya rame ya shiga damuwa, duk wanda ya san abin da ya ke faruwa ya tausaya mishi amma ban da y’ar mulki dan bata san ma abin da ya ke faruwa ba, ta dai san ance ya yi tafiya amma ba ta damu da sanin inda ya je ba, dama fatanta a ba ta mota kuma yanzu ta samu hakan ita ke ja abin ta. Sulaiman ya yi matukar jin haushinta bi sa abin da ta mishi na kin nuna cewa ta san abin da ya faru balle ta mishi jaje, hakan ya kara hura wutar kiyayyanta a ran sa, dan bai yi tunanin cewa ba ta san abin da ya faru da shi ba. Dadinsa d’aya yanzu ba ya tuk’ata da ga Yaya Raihan sai sauran yaran gidan ya ke tuk’awa da kuma Ammi shima ba ko yaushe ya ke tuk’ata ba.
Shiri sosai su Slimzy suke yi akan yanda zasu rushe rayuwar Muhievert su lalata mata rayuwa ta yanda babu wanda zai yi shaawar aurenta sau dai ta kare a wulakance, ko wannensu ya kawo shawaran da ya dace da yanda za su gudanar da komai cikin sauki, Allah Allah suke yi ta fara zuwa makaranta dan ba sa bukatar 6ata lokaci a cikin abin da su ka sa a gaba.
♾♾♾
Tunda Sarah da sauran abokan tafiyarta su ka farka suke ta kuka, dan sun fahimci komai da ke faruwa, tunda tun kafin a yi nisa su ka fara barci ga shi sai yanzu wai su ka farka, Sarah kukan bakincikin rabuwa da iyayenta take yi,da kuma tausayin halin da zasu shiga. yayin da sauran yan mata biyun su ke jin tausayin kan su saboda rayuwar da za su sake fadawa mai kama da wanda su ka baro a baya wanda suke fatan Allah ya raba su da shi har abada.
A 6angaren mazan shida da ga cikinsu ba su wani damu sosai ba dan dama yan gudun hijira ne daga chibok, kuma ba su da madafa sun kwana da sanin cewa rayuwarsu za ta shiga cikin garari dan haka duk yanda rayuwa ta zo musu za su kar6a hannu bibbiyu, sun yarda cewa bawa ba ya wuce kaddararsa, a yanzu babu abin da zai tsoratar da su, an kashe iyayensu ma a gaban idanunsu to meye ne zai ba su tsoro su kam a yanzu. Yayin da sauran maza ukun suke cikin tashin hankali dan tunanin halin da ahalinsu zasu shiga, da ga zuwa makaranta sai a neme su a rasa tabbas duk inda yan uwansu suke yanzu hankalinsu ya tashi fiye da tsammaninsu, addua suke yi Allah ya karesu dasu sharrin mutane da aljanu kuma Allah ya kubutar dasu da ga hannun azzalumai.
Ko da Reza ya dawo daga kai Tom cikin garin Abuja dare ya ri ga ya yi, hakan ya sa bai bi ta kan su ba, dan kafin su fita sai da suka ajiye musu abinci d’azu da ruwa wanda zai ishe su kafin ya rufe k’ofa ya tafi kai Oga Tom garin Abuja, kuma akwai toilet a ko wani d’aki dan haka babu abin da zai iya musu duk abin da su ke so zasu samu a cikin d’akin ga katifa masu yawa da zai ishesu shakatawa ga filalluka a ajiye ga mai bukatar hakan.
Su Phillip kuwa suna can d’aki mak’ale da juna suna aikin da suka saba, duk da haka hankalinsu na kan sabbin kaya da Tom ya yi order inji su da fad’a, kuma sun d’au aniyar d’and’ana su dukansu musanman wanda zukatansu ke muradin samu.
♾♾♾
Ganin tarin rashin nasara a tare da aikin nasu ya sa suka yanke shawaran da ya fi dacewa, wato dole dai a yi dashen zuciyar duk da yadda Momma ta nuna ba ta so, mutum d’aya ne ya fita dan sanar dasu shawaran da suka yanke, sauran biyun suka zauna da ita yayinda biyu su ma suka fita had’o duk abin da za a bukata tare da taimakon wasu nurses biyu.
A lokacin da likita ya fito Didi ta yi saurin tashi har tana tuntu6e, da ido Imam ya mishi alamun kar ya ce komai, kallon Didi ya yi kafin ya ce “kun bar maganinta masu mahinmanci a gida Hajiya kuma muna b’ukatarsu yanzu idan ba damuwa” da sauri ta ce “to Imam kai ka tsaya ni bari inje in d’auko mata ko” gyed’a kai ya yi tare da addu’ar Allah ya sa kar kuma ta ce ta fasa shi ya je. Har za ta tafi kuma ta fasa ta ce “babu wani abin ko Likita ina fatan kun shawo kan matsalar” har sun tsorata dan a tunaninsu fasa tafiyar ta yi, saurin amsa wa yayi da “eh babu komai da yardan Allah komai zai yi dai-dai” cikin sanyin jiki ta wuce bayan ta kar6a key daga hannun Imam.
Tana tafiya Likita ya mishi bayanin komai, dama ya yi tsammanin hakan shiyasa ma ya mishi alamar kar ya yi magana dan yanzu sai ta birkice musu a kasa yin abin da ya dace, office din likitan suka shiga ya sa hannu akan takardun da likita ya ba shi, sannan suka fito likita ya wuce emergency unit daganan suka wuce da ita gurin surgery, dama sun tanadi komai dan zuwan irim wannan ranar dan haka aiki kawai suka duk’ufa yi akanta.
Hankalin Didi sam ya ki kwanciya, ko da ta je ba ta samu da wuri ba dan dama Momma ba ta son magani shiyasa ta ke 6oyewa a wani guri na daban, bayan ta samu ta d’auki flask na ruwan zafi tare da kayan shayi sai purse din ta da atm da kuma wayoyinsu, ba ta isa da wuri ba dan hold up din da ya yi yawa a hanya, ta na isa ta kira yan uwanta da ta sanar da su cewa su na asibiti amma da sauki, ba ta san cewa Imam ya riga ya fad’a musu abin da ke faruwa ba dama itan ce ba a son fad’a mata dan ta na da ciwon zuciyar itama, addua kawai ko wacce ta yi wa Momma ba tare da ta nuna cewa akwai wani abin bayan hakan ba.
Ita dai Didi jikinta har zuwa lokacin a sanyaye ya ke, ta ka sa yarda da abin da likita ya fad’a, ta na zuwa ta samu Imam a waje ya na ta safa da marwa “Imam” ta kira sunan shi tana kare mishi kallo, cikin sanyin jiki ya amsa tare da kar6an abin hannunta “Imam meke faruwa na fara ji ajikina cewar akwai matsala, ka fad’amin gaskiya Imam ko zan samu matsaya d’aya inyi wa mahaifiyata addua” saurin kallonta ya yi dan ya fahimci inda ita tunaninta ya tafi, hannunta ya ja suka shiga wani rumfa suka zauna, kallonta yayi na yan mintina kafin yace “aiki za a yi wa Momma adduarki kawai ta ke bukata, idan ki ka tashi hankalinki tabbas ba zan shiga masarautar hankaka ba, idan ki ka natsu ki ka kwantar da hankalinki nima zan samu natsuwa, ba na bukatar ganin hawayenki domin ya na karyamin duk wani kuzarina, ki yi hakuri ki daure ina son in ga irin dakewar zuciyarki a wannan ga6ar banason ki kasa juriya Didi na” ba ta san sannan murmushi ya su6uce mata ba jin yanda yau Imam din ta ya ke nuna mata ya girma kuma zai iya yi mata wayo dan ta samu natsuwa, uffan ba ta ce mishi ba kawai ta kwantar da kanta a kafad’arsa, shima murmushi ya yi ganin abin da bai ta6a gani ba a fuskar Didinsa a duk sanda Momma ke cikin wani yanayi.
Awa biyu tsakani suka fito da ita suka kaita ICU cike da annuri a tattare da su halaman an samu nasara kenan a aikin da suka mata. Bayan an mata duk wani abin da ya dace suka bar nurses biyu domin su kula da ita, bayan sun fito Dr Rabil ya kira Imam inda ya sanar da shi cewa suna private room wanda ya kasance nasu ne anan suke zama duk sanda wani abin ya kawo su cikin asibitin.
Mintina kad’an ya kai shi d’akin da suke yana fad’ad’a murmushinsa, hakan ya sa su ajiyar zuciya dan duk yaran Momma sun zo dan ganin mahaifiyarsu, ganin Didi cikin natsuwa ya sanyaya ran su duk da sunyi mamakin sauyawarta. Zuwan likita kuma ya kara dad’ad’a musu zuciya, sosai suka yi farinciki suka saki ran su aka koma hira. Sanim cewa Momma za ta samu kulawa ya sa suka koma gida dan ance sai washe gari ake sa ran farkawarta.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
2
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Dedicated to Habiba Adam😍
*Takabbal minna wa minkum. Dafatan anyi sallah lafiya cikin koshin lafiya? Allah ya kar6i ibadun mu ya kuma daura a mizani, ya kuma kawo mana karshen wannan cuta*
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
2️⃣9️⃣♾3️⃣0️⃣
*Masarautar Hankaka*
Kishingid’e take akan lallausar carpet din dake tsakiyar falon, wanda ya sha ado da koriyar filawa, komai na cikin falon kore da ruwan madara ne, ko ina ya sha ado irin na zamani dana gargajiya.
Yan mata biyu ne suke tsaye gefe da gefenta suna mata fiffita, Tuffa ta d’auka ta gutsura kafin ta mai da hankali a kan TV din dake manne a jikin bango da alamu labarai take sauraro, saboda yadda ta natsu ta tsurawa Talabijin din ido.
+
K’aran wayarta ne yasa ta d’an ja tsaki tare da ajiye Tuffa din a cikin tray din dake gabanta, da sauri Meram ta mik’a mata wayar bayan ta d’auka tare da sanar da ita wadda ta bugo wayar.
“Ranki ya dad’e aiki yana tafiya yadda muka tsara, amma sai dai bango yaki faduwa balle mu samu yadda muke so, babban albishir din shine mun samu abin da muke so ta d’aya 6angaren kuma yana daf da shiga hannu”.
Sai yanzu Gimbiya Fatsu ta murmusa sannan tace “aikin ki ya yi kyau sosai, banyi tsammanin samun nasara anan kusa ba, kin chanchanci yabo kuma ki zuba ido zaki samu sako bada jimawa ba Shukra”.
Annuri ne ya bayyana a fuskar Shukra “ai duk inda jirgi yaje, inda hakuri wata rana kunkuru zashi sai dai ya jima bai isa ba, in dai zan zamu abin da nake so ai kema kin haye babu tantama, da sannu komai zai tafi dai dai da tsarinki, mulki a hannunki yake sai yanda ki kayi dashi”.
Sosai Gimbiya Fatsu taji dadin kalaman Shukra “ki zuba ido sakonki na bisa hanya fiye ma da ko da yaushe domin kin faranta rai na, kuma kiyi kokari ki shigo masarauta cikin sati mai zuwa”.
“Godiya nake ranki ya dade, yar sarki jikar sarki, matar sarki kuma uwar sarki mai jiran gado, Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya da tsawon rai, sai na shigo din” tana ajiye wayar tayi murmushi tare da cewa “bazan ta6a bari ki cika burinki ba, ban auri sarki ba ban haifa masa ba, tabbas ba zan bari shegen danki ya mulki masarautar ba, gwara ma idan d’an Kubra ne da sauki ko ba komai ai a matsayin d’ana yake kuma d’an masoyina, kamar yadda na aminci kike muzguna wa Kubra haka kema zaki shiga tsahu ni kad’ai zan zama mata ga masoyina, mu zuba mu gani mai rabo shi zai taki sa’ar”.
Suna gama wayar Gimbiya Fatsu ta aika mata kud’i ta account din ta dan ta san cewa babu abin da Shukra take so a duniya kamar kudi, duk da cewa gidan kudi ta taso kaddara ya raba ta da gidan kuma ta sake samun damar komawa ba tare da wani ya ankara da hakan ba, duk daular da take ciki hakan bai mata ba ko yaushe burinta tayi ta jin kudi a ko wani lokaci.
Wani munafikin murmushi Shukra tayi a lokacin da kud’in ya shiga account dinta, “tabbas zata jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya, Allah dai ya kai damo ga harawa” shine abin da tayi ta ayyanawa a ranta.
♾♾♾
A 6angaren su Sarah kuwa tunda aka kawo su kullun suna d’aki daga salla sai barci, abinci kam kamar magani suke ji a bakunansu. Sosai suka rame sukayi duhu dan damuwa, sa’arsu d’aya duk yanda Philip suka so cutar dasu abin yaki yuyuwa.
Har yau Oga ake jira ya dawo ko ya bada umarni akan su amma shuru shima tunda ya tafi sau d’aya ya kira dan jin ko akwai wani matsala.
Tun suna kirga kwanaki har suka dawo kirga sati daganan kuma watanni amma shuru Oga bai dawo ba kuma bai kira a waya ba, a k’a’ida kuma ba’a kiranshi sai dai shi ya kira in ba dai ya bada umarnin a kirashi din ba toh babu wanda ke gigin kiran wayarshi.
A yanzu watansu biyar kenan a cikin gidan, komai a wadace yake kama daga abinci, abinsha, gurin kwana sam babu matsi a cikin zaman gidan, illa dai kawai damuwa da yayi musu yawa na rashin sanin madafa. Ba’a hana su ibada babu takura sai dai abinci da har yanzu suke kasa cin abin kirki saboda damuwa, kowa na tunanin rayuwa da yanda komai ya lalace a lokaci d’aya.
♾♾♾
A cikin watanni biyar abubuwa da yawa sun faru, ciki harda warkewar Momma, Cikin hukuncin ubangiji ta warke kamar bata yi wani cuta ba, watanni hudu kenan da dawowarta daga asibiti bayan an bata bed rest na wata d’aya kafin aka sallame ta, sosai Imam da sauran yaranta suka yi farin cikin warkewarta, bayan an sallame ta ko wacce ta koma gidan mijinta, ya rage daga Imam sai Didi.
Sai Gidan su Sarah da babu abin daya chanja dangane da tashin hankalin da suke ciki, har zuwa yanzu Umma babu um ba a’a tana kwance sai dai a d’aga a kwantar, sosai hankalinsu ya tashi akan hakan, dan ma dai Malam akwai tawakkali a haka suke rayuwa cikin kunci. Goggo Hama ita ma har yanzu tana gidan bata koma kauye ba, ta dage akan sai jikarta ta bayyana kafin ta iya samun karfin halin komawa, duk da cewa masifar nata babu abin da ya ragu amma dai wani lokacin tana d’an tausayawa Umman ganin halin haula’in da take ciki ta koma kamar mutum mutumi sai yanda akayi da ita.
Sai kuma koransu Slimzy da akayi daga makaranta saboda kamasu da akayi da laifin tura yan daba domin su illata Muhievert, sosai suka yi bakin cikin abin daya faru dasu kuma suka yi alkawarin ganin bayan Muhievert. A 6angaren Muhievert kuwa sosai ta koma shuru shuru saboda abin da ya faru da ita, tayi dana sani mara adani, karshe ma ta dena zuwa makaranta ta koma yin online classes saboda sam yanzu bata son hayaniya kullun tana d’aki. Kowa a gidan tausayinta yake ji dan ba karamin wahala tasha ba a hannun yan daban dai da tayi jinyar watan guda kafin ta fara dawowa dai-dai.
Kamar kullun tana zaune a d’aki bayan ta gama online lectures dinta, tayi assignment din da aka bayar sannan ta kwanta a saman center carpet din dake shimfid’e a tsakiyan d’akin nata. Pop ceiling din ta tsurawa ido kamar mai tunanin yanda aka tsara kwalliyar dake a jiki, ta dad’e a kwance kafin ta tashi ta shiga toilet.
Bayan tayi alwala tayi sallar Azahar sannan tayi yan adduo’in ta, ta dad’e a zaune a gurin kafin ta shafa adduar ta cire hijabin sannan ta nad’e sallayar. Kan doguwar kujeran ta zauna tana tunanin mutumin daya kwaceta a hannun yan daban nan, duk da cewa bata kai ga ganin fuskarsa ba amma kullun da tunaninsa take kwana take tashi, duk da tasan ba zai so auren mace irin ta ba saboda abin da ya faru da ita, amma zata so ko da fuskarsa ne ta gani ko zata ji sanyi a cikin ranta, badan Saviour dinta ba da kila har yanzu tana jinya, dan yayi matukar kokari gurin fafatawa da yan daban domin ceton rayuwarta, duk da cewa tasha wahala a hannun su, amma dai ba kamar ace bata samu mai taimako a lokacin ba, mutane shida akan mace d’aya ai ba wasa bane, kuma karfin mace da namiji akwai banbanci, tabbas Allah yana sonta daya turo Saviour dinta dan ya ceceta. “Saviour” ta fad’a a fili, sunan data rad’a mishi kenan tun lokacin da abin ya faru.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Dedicated to Sadiya Sidi Sidiya😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
3️⃣1️⃣♾3️⃣2️⃣
Muhammad Rufa’i Muhammad (MRM) Imam d’a ne ga Rufa’i Muhammad Rufa’i sarkin dake mulkin Masarautar Hankaka a jihar bauchi.
Imam ya kasance d’a d’aya tilo da Allah ya azurta mai martaba sarki Rufa’i dashi, amma sai haihuwarsa yazo da sarkakkiya domin har zuwa yanzu mahaifinsa yaki amincewa dashi a matsayin d’a.
Haihuwarsa ya janyo rasa rayuka dayawa ciki harda mahaifiyar sarki Rufa’i da kuma kannen mahaifinsa guda biyu, abu na karshe kuma mutuwar auren mahaifiyarsa. Hakan ya janyo mishi tsana daga gurin dangin mahaifinshi. A da Kubra mahaifiyarsa ta so ta barshi a gurin mahaifinsa duk da cewa bai amince dashi ba, sai dai data zauna tayi zurfin tunani akan yanda zai yi rayuwa cikin kunci sai ta yanke shawaran tafiya dashi.
+
Kubra Muhammad Rasheed d’iya ce ga wani babban attajiri a garin Bauchi, wanda ya tara dukiya mai dumbin yawa kuma har ya koma ga Allah babu abin da ya ragu sai dai ma yake kan karuwa a kullun saboda yanda Allah ya azurtashi da dukiya mai albarka na ban mamaki, gashi da yawan kyauta da son jama’a sam-sam bashi da kyamar talaka yana da tausayi da karamci, haka zalika matarsa Maryam itama akwai son mutane da tausayi ga kuma kyauta ko yaushe hannunta a cikin badawa yake, shiyasa ko bayan ran mijinta bata rabu da samun jama’a ba daga danginsa har zuwa danginta da sauran jama’ar gari, mahaifinsu Shukra ya bar musu gidan haya guda goma, gidan gona guda biyar, gidajen mai guda biyar, babban asibiti guda d’aya dake cikin jihar bauchi sannan manyan kamfanoni guda uku na sarrafa kayan abinci.
Allah ya azurta Alhaji Muhammad Rasheed da yara tara, Hanifa wacce take aure a Kano da yara biyar, Wasila tana aure a ibadan da yara hudu, Ali da Sadiq Allah ya musu rasuwa a ranar da aka haifesu, Habiba tana aure a Katsina da yara uku sai Hafiz shima ya rasu shekaru biyu kafin rasuwan mahaifinsu inda yayi hatsari a hanyarsa ta dawowa daga wani leture daya gabatar a garin Minna, sai Nafisa yaranta biyu tana Lagos tare da mijinta sannan Shukra da Kubra yan biyu na biyu bayan su Sadiq da Ali. Shukra ce babba Kubra kuma auta.
Duk yaran Momma Allah ya musu arzikin kyau da kuma wadatar zuciya, dukansu kuma sun auri mazaje masu rufin asiri dai-dai gwargwado duk da cewa arzikin mazajen nasu ko rabin na iyayen su bai kai ba amma suna cikin wadata dan komai na rayuwa sun samu a gidajensu. A cikin yaran gabadaya Shukra ce ta fita zakka domin bata da son jama’a ga son kudin tsiya duk yanda Allah ya basu bata gani hango na wasu take sakeyi, auren gata kawunsu yaso yayi mata da d’an abokinsa inda ta bijire ba tare da tasan ko waye zai zamo mijin nata ba, hakan yasa aka maida abin kan yar uwarta Kubra, ba tare da wani jayayya ba Kubra ta amince, a lokacin da aka ce saurayin zai zo ganin ta Shukra barin gidan tayi dan batason had’a guri da talaka duk da batasan ko waye ba, sai bayan da suka tafi ta dawo inda taji labarin daya tarwatsa mata zuciya wai wanda ta dade tana dakon kauna shi dama aka so a bata amma ta bijire, sosai tayi musu bori akan a juye abin a kanta tunda babu yanda za’ayi ya gane ba Kubra bace dan tsaban kaman dake tsakaninsu, amma Kawu da Momma suka ce taci karya ta kwana da yunwa tana ji tana gani Kubra ta auri d’an sarki jikan sarki Muhamma Rufa’i wanda taso kamar ranta kuma taki aure taki kula kowa saboda sonsa domin a nata tunanin watarana zai sota.
Shukra sun had’u da Muhammad Rufa’i ne a makarantar da tayi a cikin garin abuja wato Nile University, kuma ya kasance course mate dinta, saukin kansa da rashin d’aukar duniya da zafi yasa yake kula duk wani wanda ya nuna son abota dashi matukar dai ya lura da natsuwar ko kamun kai a tare dashi, a haka suka kulla abota da Shukra saboda kamun kanta amma bai san cewa rashin son talaka ne ya janyo take k’in kula kowa tare da shan kamshi ba.
Tunda suka fara abota suke karatu tare kuma kusan ko yaushe tare zaka gansu, wasu sunyi tunanin soyayya suke yi yayinda wasu suke bakin cikin hakan wasu kuma suke ganin dacewarsu, shi a gurinshi babu sonta a zuciyarsa ita kuma tana matukar kaunarsa, a haka har suka gama karatu. Bayan rabuwarsu basu sake haduwa ba sai dai waya, ranar da yaje ganin matar da zai aura yayi matukar mamaki sai da ta mishi bayanin cewa ai ba ita bace sannan ya kira wayan Shukra suka yi magana kafin ya kara tabbatar da cewa yar uwarta zai aura, sosai ya shiga tashin hankali dan ya dade da sanin cewa Shukra tana son shi, sai dai kaddara ya riga fata amma yana gudun kar hakan ya lalata zumuncin yan uwa biyu. Kamar kuwa ya sani hakan ce ta faru bayan aurensu ma aka nemi Shukra aka rasa kuma har zuwa yanzu babu labarinta, ciwon zuciyar Momma harda rashin sanin inda Shukra take.
Kubra yarinyace mai saukin kai da natsuwa da son jama’a kamar iyayenta ga tausayi da hakuri da juriya akan duk wani abin da zai ra6eta, sosai tayi kuka lokacin 6atan shukra kuma ta d’aurawa kanta laifin faruwan hakan domin da bata amince ba da hakan bai faru ba, taso Kawu ya hakura a bawa Shukra wanda take so amma yaki yarda acewarsa ai tun farko ta bari damarta ya su6uce daga hannunta, Momma ma ta goyi bayansa akan k’in amincewa da abin da Shukra take nema a haka har akayi bikin Kubra inda bayan shagalin biki aka nemi Shukra sama ko kasa babu alamunta.
Bayan dawowar Kubra gida tare da d’anta Imam sai da tayi jinyar zuciyarta akan abin da ya mata na k’in amincewa da gudan jininsa, babban abin da yafi bakanta ranta shine k’in yarda da yayi aje ayi DNA test, duk da cewa wani lokacin tafi tunanin cewa ba’a cikin hayyacinsa yake ba, sai dai 6acin rai da kunan zuciya kansa tayi tunanin kawai tozarci yaso ya mata shiyasa, zata iya tuna cewa tun sanda ya auri Gimbiya Fatsu tay bankwana da farin ciki, duk da cewa zato zuniba amma tafi tunanin kila ita ta shiga ta fita harta rabasu, sai dai ramin karya bata kark’o da sannu komai zai bayyana ko dan hakkin Imam dake rataye a wuyan duk wad’anda suka cutar dashi.
Imam ya taso a matsayin yaro mai saukin kai da son jama’a kuma mai kawar da kai akan al’amuran mutane, duk wani abin da zai jawo iyayensa ko danginsa zagi ya kokarin kaucewa, a ko yaushe burinsa ya faranta ran masoyansa, Imam yayi karatu a fannin kula da lafiya, inda ya had’a degree dinsa da masters a jami’ar ABU Zaria. Bayan ya kammala sai ya shiga police force ya fara aiki a matsayin jami’in sirri, cikin lokaci kankani ya dinga samun cigaba saboda kwazonsa da basirarsa, a yanzu haka wani aiki ne ya kai shi jami’ar bauchi, aikin da zai sa dayawan malamai su rasa aikinsu saboda ayyukan da sukeyi marasa kyau musamman cutar da dalibai da sunan cin jarabawa.
Tunda yake sau biyu ya ta6a soyayya, na farkon y’ar uwarsa ce d’iyar Anty Hanifa yaso ta sosai sai dai tafiya bai yi nisa ba Allah ya kar6i ranta. Sosai ya shiga tashin hankali kafin ya rumgumi kaddara. Na biyun kuma Allah yayi ba matarsa bace sai gashi ta auri abokinsa yaransu biyu ma yanzu harda takwara suka mishi. Sai kuma yanzu da yake jin kamar ya fara son Muhievert sai dai bai tabbatar ba balle ya tunkare ta.
Cikin satinnan ya shirya tunkaran mahaifinsa a cikin masarautan hankaka, duk da cewa wani 6angare na zuciyarsa na hanashi zuwa wani kuma na tunzurashi sai dai halin da Didi take ciki na kunci yasa dole ya fuskanci mahaifinsa yayi fita na fito da duk wani wanda yake adawa dashi kuma dole ya kar6i abin da ya kasance nashi duk da cewa bai ta6a shaawar mulki ba amma a yanzu ya shirya shiga ko wani irin hatsari in dai zuciyar mahaifiyarsa zai samu salama.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Sadaukarwa ga _Mrs Aliyu & Mrs Noor_🥰
Dedicated to Haermeebraerh😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
3️⃣3️⃣♾3️⃣4️⃣
“Assalamu Alaikum” Zahra ta fad’a tana kutsa kai cikin d’akin, kwance ta ganta a k’asa tayi nashe nashe cikin zurfin tunani, ita kam yanzu tana matukar tausayawa yayarta, duk ta koma wani iri ta zama wata na daban, ba haka suke son ganinta ba, duk da suna son su dinga ganinta ko da yaushe amma ba’a irin halin da take ciki yanzu ba, ta zama shuru-shuru bata son hayaniya bata shiga cikinsu ko da ta shiga sai dai murmushi maganar yana mata wahala “ba irin wannan Ya Muhie muke so ki zama ba please come back to your normal self, your normal world, kinji Ya Muhie, ganinki haka sam-sam baya saka mana natsuwa, kinsan yanda mukeji a ran mu kuwa game da wannan sabuwar halayyar taki, dan Allah ki koma yanda kike, kuma kizo inji Ya Raihana tana falon kasa, kinsan tayi nauyi stairs na mata wahalar hawa” Zahra ta fad’a tana goge kwallar daya taru a gefen idonta yake kokarin zuba, sannan ta fita. Jikinta ne yayi sanyi ganin yanayin da yar uwarta ta shiga a kanta, to inaga kuma mahaifiyarta, ai kaddara tana kan kowa babu mai guje mata, ita natan a haka yazo and she need to be strong for her self & most especially for her family, tana son yan uwanta da iyayenta su kasance a cikkn farin ciki ko da sau d’aya ne a ta dalilinta.
+
A hankali take saukowa daga stairs din cikin dinkin doguwar riga na material, wanda akayi mishi zanen filawa manya manya da koren ganye sai d’an digo-digon ruwan kasa a jiki, a gaban rigan kuma zubi akayi mai kananan design, sosai kayan ya kar6eta kuma yayi mata kyau.
Tunda ta fito suka zuba mata ido, duk yan gidan suna zaune a falon sai wani bakuwar fuska da bata kai ga sanin ko waye ba, gaban Ammi ta nufa ta tsuguna ta kaisheta, ba sabon ba sai abin ya yi wani banbara kwai wai namiji da sunan mace, amsawa Ammi tayi cikin jin dadi tana shafa kanta tare da sanya mata albarka, juyawa tayi ta gaisa da yayyin nata sannan ta gaida bak’on dake zaune kusa da Ya Raihan, kannenta kuma suka gaisheta cike da nuna jin dadin ganinta a wannan ranar cikin d’an fara’a daya dad’e da gushewa daga kan kyakyawar fuskarta.
Zama tayi akan kujeran da Ya Raihana take kai, “zan biki gidanki Anty, na gaji da zaman guri d’aya kuma ni ba yanzu zan koma school ba sai idan zamuyi exams” shuru Ya Raihana tayi kafin tace “shikenan ki shirya sai mu wuce tare, amma ga abokin aikin Raihan yazo dan ku gana, ki daure ki kula shi ko Ammi zataji dadi a ranta dan ta nuna jindadi a kan al’amarin, dan Allah karki bata kunya, ki amince ki gwada bashi dama”.
Wani irin bugawan da zuciyarta tayi sai data fara jin zafi a kirjinta, raba ta ake son yi da Savior dinta masoyinta na 6oye wanda ya gama mamaye zuciyarta, dan Allah karsu mata haka su barta tajira shi har zuwa sanda Allah zai sake had’a su. Amma kuma ya zatayi da farin-cikin Amminta, kai gaskiya ba zata so ta bata kunya ba, “Anty, kun fad’a mishi abin da ya faru dani ne kuma ya amince da aure na? Ko kuma bai san da zancen ba? Idan har ya sani ya amince, shikenan zan gwada bashi dama saboda farin cikin Ammi amma ba wai dan har a cikin raina ina son hakan ba” ta fad’a tana kokarin mai da kwallarta.
Tausayinta ne ya kama Ya Raihana, amma they want the best for her, kuma ba zasu so ta ga kamar auren dole za’a mata ba, “kiyi hakuri kinji yar kanwata, ki gwada ba shi chance, sannan ki dage da addua, ki kuma yi istihara, idan har akwai alkairi zakiga kema kin fara son abin a ranki, idan babu kuma shikenan sai muyi fatan Allah ya miki za6i mafi alkairi a gareki” ta fada tana murmushi.
Sosai taji dadin shawaran Ya Raihanan kuma ta amince zata gwada hakan da yardan Allah, idan alkairi ne Allah ya cire mata son Savior, idan kuma babu alkairi Allah ya dawo mata da Savior dinta cikin rayuwarta.
♾♾♾
A kofar gingimemen Gate din masarautan yayi parking, sai da ya dad’e a tsaye kafin yayi horn, dogarai biyu ne masu tsaron k’ofa suka l’eko suna zazzare ido, ganin yaki fitowa daga motar yasa suka k’arasa, sai da ya d’au lokaci kafin ya bud’e musu glass din windon, kallo kallo aka tsaya yi tsakanin dogarai biyu, bakinsu yayi nauyi, ganin photo copy din mai martaba sarki Rufa’i yasa duk suka shiga rud’ani, “tuba mukeyi ranka ya dad’e, ayi mana afuwa” da sauri suka koma bakin gate din tare da bud’ewa.
Ko kallon su bai yi ba yayi wucewarsa, sai da ya isa parking space sannan ya tsaya tare da yin parking, motoci ne na alfarma, kala kala a gurin parking space din, sai da ya karewa motocin kallo sannan ya kad’a kai ya nufi k’ofar fada, inda yaga dogarai da yawa kuma yaga tsarin ginin daban yake, duk wanda ya ganshi sai ya duk’a ya kwashi gaisuwa, duk da cewa ko kallo duk basu isheshi ba, kus-kus aka farayi a tsakanin bayi kowa da abin da yake fad’a game da Imam, kamansa da mai martaba har ya 6aci, kawai dai shi da an ganshi an ga yaro dan bai wuce shekaro talatin ba, mai martaba kuwa shekarunsa sittin a halin yanzu.
Tunda ya shiga cikin fadan duk wani mutum mai motsi ya tsaya chan gurin kare mishi kallo, ko kallon su bai yi ba ya isa gaban Sarki Rufa’i yana cewa “barka da rana mai martaba sarkin Masarautan Hankaka, barka dai Sarki Rufa’i mai adalci ga duk wanda ya ra6e shi, adalcin ka ne ya raba d’a da gidan ubansa, adalcin ka ya raba mata mai mutunci da gidan mijinta, adalcin ka ne yake neman d’aura d’an shege a kujeran mulki tabbas ka cika mai adalci Sarkin yau Sarkin gobe”.
Shuru kake ji babu mai iya cewa kowa, zufa ne yake yankowa duk wani munafuki da yake da hannu akan manakisar da ake kan shiryawa da wanda ma aka shirya da dad’ewa, tabbas tunda har ya iya fuskantar sarki da irin wad’annan kalaman to akwai matsala gagarumi “nazo nan ne ba dan ina son ka yarda dani ko ka gaskata kasancewa na d’an ka ba, sai dan in kar6i abin yake nawa abin da yake gado na kuma yake jirana ba wai jiran dan shege ba, karfa ka tsorata, kuma kuma kar ku birkice, ba wai yau nakeso a bani ba, amma zan dawo nan da wata guda, kuyi tunani akai ko kuna so ko bakwa so ku shirya gagarimin shagali na kar6an sabon sarkin ku a ranar dana sake waiwayo Masarautan Hankaka, dan hakin daka raina shike tsole maka ido” ya fad’a yana kallon jama’ar dake cikin fadan wanda sukayi tsuru tsuru da ido kamar sunyi wa sarki karya, murmushi yayi sannan ya fita yana takawa cikin kasaita.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
Sadaukarwa ga _Mrs Aliyu & Mrs Noor_🥰😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
3️⃣5️⃣♾3️⃣6️⃣
Cikin makaranta ya wuce saboda duba wasu ayyukan, yau ma kamar kullun ya duba bai sameta ba, to wai meye matsalar, haka kawai sai ta daina zuwa makaranta dan kaddara ya fad’i a kanta, gaskiya yarannan basu kyauta mishi ba, ga shi yana son ganinta amma ba hali, rabon daya ganta tun ranar daya taimaketa ya kwace ta daga hannun azzalumai. “wucewa ya zo yi shine ya had’u dasu Slimzy suna tattaunawa da yan daba akan yanda zasu tareta a ranar, duk da cewa akwai wani abu mai mahinmanci da zai yi a dai-dai wannan lokacin, sai ya fasa yabi kwatancen inda yaji sunce za’a kaita, duk da cewa ya makara saboda holdup amma ya samu ya ceceta, kasancewar bai san gidansu ba sai ya kaita asibiti sannan yayi kiran yan gidan a wayarta da akaci sa’a babu password, bayan sun zo sai ya barsu da ita shi kuma ya wuce gidan VC ya fad’a mishi abin da yake aukuwa, kasancewar VC ya san shi kuma yasan aikin sirri yakeyi a makarantar yasa yayi saurin yankewa su Slimzy hukuncin kora daga makarantan, dan ya san idan ba hakan yayi ba shima za’a iya sa shi a cikin masu laifin barin yara irin wad’annan a cikin makarantar” tun daga ranar bai sake ganinta a makaranta ba kuma bai san ina ne gidansu ba, har ga Allah sonta yakeyi da gaske kuma aurenta zai yi idan har ta amince mishi.
+
Office din shi ya wuce ya d’auko wasu files, kafin ya bi computer room inda ya samu ba kowa ya kulle kofar ya fara aiki a ciki, CCTV camera din yana mishi aiki da kuma dauka mai kyau, wasu abubuwan ma abin kunya amma ya zai yi shine kawai irin evidence din da yake bukata yayi amfani dashi, bayan ya tattara wasu information ya had’a a cikin flash drive dinsa sannan ya fita daga computer room din ya wuce inda ya fake motarsa.
Tafiya yakeyi a natse yana sauraron wa’azin sheikh Ibrahim daurawa, a gurin traffic ya tsaya yana jiran a bada hannu, kaman a mafarki yana juyawa ya hangota a cikin wani mota tare da wata mace a baya sai direba da yake jansu, ana bada hannu yayi saurin bin bayansu har zuwa inda yaga sun shiga, sallama yayi da mai gadi ya tambayeshi ko matar gidan tana nan, shine yace mishi ai itace ta shigo yanzu, godiya ya mishi sannan ya kama hanyar gida.
Tafiya mai tsawo yayi dan daga gidan Ya Raihana akwai tazara sosai zuwa nasu gidan, wani irin farin ciki yake ji a cikin ransa, ko ba komai tunda dai ya ganta cikin koshin lafiya ai shikenan, zai san yanda zaiyi su had’u zuwa gobe. Yana zuwa yayi horn aka bud’e, bayan ya shiga yayi parking a gate na farko sannan ya taka abin shi zuwa gate na biyu, yana zuwa yaga motar Didi baya gurin alamun ta fita, ciki ya shiga zuwa 6angarensa, sai da yayi wanka ya chanja kaya sannan ya sauko k’asa, 6angaren Momma ya nuna, abinci ya faraci sannan ya nufi d’akinta, a kan sallaya ya sameta tayi zurfi cikin tunani.
“Uwar gida ya haka, ko dai tunanin kar in k’ara aure kikeyi ne hakan, to sha kuruminki duk wacce tazo a bayanki take” ya fad’a cikin tsigar zolaya, kallonsa Momma tayi cikin tausayawa, shikam bai yi sa’ar rayuwa da iyayensa ba, yanzu dama wacce yake tunanin itace mahaifiyarsa ba itan bace? Sosai zuciyarta ya karaya, kuka ta farayi a hankali wanda ya mugun ta6a zuciyar Imam duk hankalinsa ya tashi ya rasa me ya dace yayi a lokacin.
Me yayi zafi shi ba wuta ba, me zai sa Momma kuka a gabansa irin haka, wani abin ne ya faru, ina Didi? Wani abin ne ya sameta ko kuma wani ne ya mutu a cikin yaran Momma “Momma menene kiyi min magana mana, kin barni a cikin duhu menene yake faruwa ko wani ne ya rasu, ina Didi take ko akwai abinda ya sameta ne?” kukan nata ta d’an tsagaita cike da tausayi da jimami ta kalleshi sannan taja hannunshi zuwa wani k’ofa a cikin d’akinta wanda bai ta6a sanin da zamansa ba, suna shiga ta zaunar dashi a kan kujera me zaman mutane biyu, kafin itama ta zauna “Shukra ta cuce mu kuma ta cuce kanta, taci amanar yan uwantaka, taci amanar uwa da d’anta, taci amanar yar uwarta, taci amanar soyayyar da aka ginashi domin Allah, Shukra ta zalinceka ta zalinceni da sauran yan uwanta duka, ta zalinci mahaifiyarka da bamu san takamanman inda take ba” hawayenta ta share sannan ta cigaba da cewa “Didi ba Kubra bace Shukra ce ta zauna tare damu for all this year, ita ce tayi basaja a matsayin mahaifiyarka, itace take zaune damu a wannan gidan, mahaifiyarka kuma tana can gidan sarki tana cikin masarautan hankaka, tana inda bamu san ko ina bane, domin baza mu iya cewa ga ainihin inda suka 6oyeta ba, abin da nasani shine tana raye, amma masarautar Hankaka babban guri ne mai girman gaske me lungu da sako ta ko wani 6angare me d’auke da gine gine da 6angarori daban daban, me dauke da d’akunan bayi ba adadi me gidajen ma’aikata ba adadi, me cike da dumbin jama’a tamkar gari guda, a irin wannan gurin ta ina zaka fara neman Kubra ta ina zaka nemi mahaifiyarka, dole kayi abu da ilimi da tunani, ba zamu ta6a nuna mata cewa munsan ita bace kamar yanda tayi playing din mu haka itama zamuyi playing dinta” karka damu da yadda akayi naji kuma na gane itan ce, kayi tunani akan wani hali Kubra take ciki kuma tayaya zamuyi nasaran fito da ita daga masarautan” naji tsayuwar motarta yanzu, ni zan fita kai ka huta a nan kayi tunani da kyau idan yamma yayi sai ka fito lokacin tana d’akinta” tana gama fad’a ta fita ta rufe kofar tare da saka password, kewaye ta shiga ta wanko fuskarta sannan ta fito ta kwanta kamar me barci, dan a halin yanzu bata kainar son ganin Shukra a cikin idanunta.
Ko da Momma ta fita sulalewa yayi a gurin ya zauna dabas a k’asa “dama ba Didi bace ba mahaifiyarsa bace, dama yar uwarta ce, dama ba da mahaifiyarsa yayi rayuwa ba, to meyasa zata musu haka kuma garin yaya hakan ta faru, me yasa ta aikata irin wannan d’anyen aikin, kenan ita ta shayar dashi ba Didi ba, wani hali Didinsa take ciki, a ina aka ajiyeta, ta yaya zai iya fara gano komai, tabbas sai ya k’ara zama me wayo da zurfin tunani, Anty Shukra bata kyauta masa ba, ko shiyasa bai ta6a jinta a ransa sosai kamar yanda zaiji mahaifiyarsa ba, ko shiyasa ba komai ne idan tace yayi zai aikata a lokacin ba, ko shiyasa yafi jin dadin zama da Momma wani lokaci a maimakon zama da ita” abubuwa da yawa ne suke ta yawo a cikin kansa, sosai idanunsa sukayi jawur saboda 6acin rai, hankalinsa yayi matukar tashi, babu abin da yake damunsa kamar ina zai ina samun Didinsa, kuka yayi irin wanda bai ta6a yi ba, kuka yayi na maraicin rashin mahaifansa ko d’aya a tare dashi alhalin suna raye, kuka yayi na bakin cikin irin rayuwar da Anty Shukra ta za6a wa kanta, kuka yayi na tausayin kansa dana mahaifiyarsa dana mahaifinsa har ma dana Momma baki d’aya.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😍😘
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
3️⃣7️⃣♾3️⃣8️⃣
A yau aka fito dasu baki d’aya zuwa tsakar gida, suna tsaye suna ta zare ido domin basu san ko yaya za’a yi dasu ba a halin yanzu, suna tsaya sai ga Philip ya fito da kujera ya ajiye a gaban su, sannan ya koma ya d’auko wani katoton table ya ajiye, kafin ya koma ta gefe ya tsaya. Jim kad’an sai ga Reza da Oga Tom sun fito, Oga Tom a gaba Reza a baya, bayan sun iso gurin dasu Sarah suke sai sai Oga Tom ya zauna aka kujeran tare da d’aura k’afa d’aya kan d’aya akan table din
IPad din hannunsa yake dannawa cikin sauri sauri, ya d’au kusan mintuna uku kafin ya d’ago kai ya kallesu, “gabadaya yaran kenan ko?” Suka amsa da “eh” sake d’aukan tablet din yayi ya sake wasu mintina biyu sannan yace su matsa gefe mutum d’aya yake bukata a gurin kuma d’aya bayan d’aya zai gansu, Wani yaro aka bari sauran suka ja gefe, tambayarsa yayi sunansa da kuma inda ya fito da inda zai je kafin aka d’auke shi, bayani yayi dalla-dalla sannan aka d’au hotonsa, haka yayi musu baki d’aya sannan ya sake maida hankali kan IPad d’in.
+
Kusan mintina talatin suna tsaya a gurin, chan suka ji k’aran horn, me gadi ne ya bud’e gate din, sai ga wasu motoci kusan kala hud’u sun shigo, na farkon maza biyu suka d’auka bayan sun ajiye wani karamin mini Ghana must go, sai na biyun maza uku dauka sannan suka ajiye Ghana must go wanda yaci na farkon girma, sai na ukun maza hud’u suka d’au sai suka ajiye Ghana must go din da yafi sauran girma, na karshen kuma yan mata biyu suka d’auka ya rage saura mace d’aya, su kuma brief case suka ajiye katoto, juya harshe sukayi cikin yaren da su kad’ai suke ganewa sannan suka tafi, su Philip kuma suka kwashe abubuwan zuwa cikin gida, bayan tafiyansu ya kalli yarinyar data rage, tsaki yaja saboda ita bauchi za’a sake mayar da ita, sannan dole shi da kanshi zai kaita, “ki koma d’akin da kuke sai gobe za’a kai ki inda suka saye ki” gabanta ne ya fad’i, “inda za’a sayeta sai kace baiwa, ko karuwa?” addu’ar neman tsari daga sharrinsu kawai ta fara kafin ta shiga cikin gidan ta wuce d’akin da suke kwana.
A falo kuma d’aya bayan d’aya aka bud’e mishi Ghana must go da brief case din, kud’ad’e ne a cikinsu cike tam, sai dai farashin matan yafi yawa saboda amfaninsu yafi na mazan, sosai Tom yaji dadin cinikin daya samu, Reza ya bawa umarnin ya kwashe ya kai mishi inda yake adana kud’ad’ansa.
♾♾♾
Ya dad’e a zaune a gurin yana kuka har sai da yaji kanshi ya fara ciwo sannan ta kwanta barci ya kwashe shi, sai da akayi la’asar ya tashi, alwala yayi a kewayen dake cikin d’akin sannan yayi salla, ya dad’e yana addua kafin ya shafa, yana zuwa bakin k’ofar Momma ma tana bud’ewa, fitowa yayi sannan ta saka pin ta rufe “wannan d’akin sirrin kakanka ne a lokacin yana raye, d’aki ne wanda ba kowa ya san dashi ba, komai nashi na sirri a nan yake saboda halin rayuwa, code d’in shine sunan kakanka, a duk sanda kake buk’atan kad’aici zaka iya zuwa ka zauna”.
Na sauko zan shiga kitchen nace bari in duba ta, dan yau bata shigo ta dubani ba tun safe, a nawa tunanin kila ba lafiya ba, jiki da jini, ina zuwa bakin kofar har zan murd’a naji maganarta “ni ai nafi karfin ace za’a ja dani, shekaru nawa nake zaune a cikin gidan mu amma babu wanda ya ta6a gane cewa ba Kubra bace Shukra ce, hatta uwar data haifeni ta kasa banbance wacece ni din, idan zan iya zama mai fuska biyu a cikin ahalina ai banga kuma wanda zan yaudara inji zafin yaudaran dana masa ba, gimbiya fatsu kenan, sai na wulakantaki sai na tozartaki, sai ma mayar dake abin kwatance, cikin ruwan sanyi zan lalata sha’aninki, dama shi yaron naki sarauta bai dame shi ba, kinga abin zai zo da sauki, ke kadai kike kid’inki kuma kike rawarki, zan d’aura yaron masoyina a mulki kuma za’a sake d’aura auren mu a matsayin nice Kubra kuma zan haifi magajin masarautar Hankaka, zuwa lokacin da yaro na zai girma zan san yanda zanyi da d’an yar uwata, ita kuma babu fita a haka zata kare rayuwarta a cikin masarauta ba tare da an farga da zamanta ba, naci amanar yar uwata gudan jinina to waye kuma ba zan iya cin amanarsa ba” tuki takeyi yana tuna kalaman Anty Shukra wanda Momma take bashi labarin yanda ta gane gaskiyar wacece a gidan ta, tabbas mutum mugun icce ne, rayuwa ta lalace, son zuciya yayi yawa a cikin zukatan mutane, su dai su samu biyan bukata kota wani hali, basu damu da wanda za’a cuta ba basu damu da halin da zasu jefa wani ba, burin su kawai su kai matsayin da suke so, su samu abin da suke so kowa ma ya mutu basu da matsala.
Ya dad’e yana zagaye garin ba tare daya san inda yake son zuwa ba, shi dai kawai tafiya yake yi yana nazarin rayuwa ya rasa ma wani irin son zuciya ne wannan, Anty Shukra ta cika azzaluma, jini d’aya ai ya wuce wasa amma saboda abin duniya sai kayi tunanin illata d’an uwanka, to abin duniyar ma meye ne shi da zaka barshi a cikin duniyar, wani abin takaici ma meta nema ta rasa kud’i iya kud’i mahaifinta ya bar musu, sarauta dai sarauta dai shine abin da take bid’a, a gaskiya ta bashi mamaki, ya dad’e yana adduar Allah ya bayyana ta ko Momma zata samu kwanciyar hankali, ashe tashin hankali zata zame musu, ashe ma tana cikin su, su ta maida mahaukata, Allah yaso anyi wa Momma aiki da yanzu bai san wani hali zata iya shiga ba, yanzu dole yayi saurin had’a report din daya samu ya damka wa hukumarsu domin ya fara aikin daya tunkarosa, ya zama wajibi yayi abu da tunani kuma cikin sauri, fatansa dai Allah yasa mahaifiyarsa tana cikin k’oshin lafiya.
Juya kan motan yayi zuwa gidan da yaga su Muhievert sun shiga d’azu, yana zuwa yayi horn, me gadi ne ya fito, ganin motar irin na Ya Raihan yasa ya bud’e ba tare da bincike ba, bayan yayi parking ya fito, sai ga me gidan shima ya fito, kallon juna sukayi na yan sakanni cikin sauri mijin Ya Raihana ya isa gurinsa tare da hugging dinsa, “Imam ashe rai kan ga rai? Kasan tun dawowar mu daga Abu nayi loosing contact dinka, kuma nasha zuwa anguwarku amma bana sa’ar samunku a gida, duk sanda naje sai ace ai bakanan, idan na tambayi Momma itama ace batanan, gaskiya naji dadin ganinka yau dinnan” ya fad’a yana k’ara hugging dinsa, murmushi Imam yayi cike da jin dadi, ashe ba zai sha wahala ba, gidan Bukar abokinsa yazo, his long lost friend, cike da jin dadi yace “mutumina ashe kayi aure?” Yace “mu shiga kai dai kaga yaranka”.
Suna shiga Imam ya zauna, shi kuma Bukar ya shiga kiran Ya Raihana, bayan ta fito yayi introducing dinsu, sosai suka gaisa, haka yaran suma suka fito suka gaisheshi, gasu da wayo ga tarbiyya hakan ya burge Imam duk da cewa ba zasu wuce 4years ba, gasu gwanin ban sha’awa kasancewarsu yan biyu kuma identicle, haka yayi ta jansu a jiki, bayan shigan Ya Raihana ciki Imam ya fadawa Bukar abin da ya kawo shi gidan ba tare daya san cewa gidansa bane, sosai Bukar yaji dadi kuma yace zai yi magana da Ya Raihana yaji ko babu wani a kasa, kiran Muhievert yayi dan su gaisa, tunda ta fito zuciyarta ke bugawa da karfi amma sai ta basar, duk da ta gane cewa malaminta ne amma sai ta basar, sai dai cikin girmamawa ta gaisheshi, bayan tafiyar ta shima yace zai wuce, Ya Raihana ta so ya tsaya yaci abinci amma yace mata zai dawo karta damu, har gate Bukar ya raka shi sannan sukayi sallama.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😘😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
3️⃣9️⃣♾4️⃣0️⃣
Yana zuwa kusa da gida ya fara tuna abubuwan da suka sa ya baro gidan, sosai tashin hankalinsa ya dawo amma ba kamar na dazu ba. 6angarensa ya wuce yayi sallar magriba, yau gabad’aya saboda tashin hankali bai yi salla a masallaci ba, bayan ya idar ya yi wanka sannan ya nufi cikin gida dan kar Anty Shukra ta gane wani abu, idan har ya bari ta gane akwai wani abin sune a ruwa. Yana shiga ya taras dasu a falo duk da abin ya ba shi mamaki dan basu cika zama inuwa guda a falo da Momma ita Anty Shukra tafi son kallon fina-finai ya yin da Momma tafi son kallon tashar fadakarwa. Amma yau sai gasu a falo tare suna kallon fina- finan, tabbas akwai abin da Momma ta shirya.
+
Bayan sun amsa mishi sallamar, ya wuce gun cin abinci, duk da cewa tsakura kawai yakeyi, sai dai a haka ya d’an ci ba laifi, bayan ya gama ya koma cikin falon ya zauna a k’asa dan bai cika zama a kureja ba idan dukan su suna zaune a kai, gaishesu yayi sannan ya kalli Anty Shukra yace “Didi baki gayamin komai game da gidan sarauta ba, kawai dai kince inje in kar6i abin da yake nawa dan kar a bawa wanda ba shibda gado kuma ba shi da dangantaka da gidan, sai dai baki yimin bayanin komai ba, matan sarki a yanzu, amintattun bayi, gidaje da mutanen cikin masarauta, halayyar kowa, abin da wasu suka fi so da wanda basu so, duk dai abin da zai sa ayi nasara har ki koma cikin gidan ki” sosai ta fad’ad’a murmushin ta daya mata maganar komawa gidan a matsayin mata hakan yasa cikin zumud’i ta fara bayyana masa mutanen cikin masarauta, matar sarki, mutanen fada, bayi dogarai, da dai sauransu, duk tambayar sai da ta amsa d’aya bayan d’aya, duk da cewa ya d’ana mata tarko ne domin ya gane komai a saukake dan ya san ta inda zai fara, inda zai shiga da inda ba sai ya shiga ba, tabbas amintattunta ba zasu zama nasa ba, dan ba zai ta6a bari wani ya san ainihin shirinsa ba sai dai Momma.
Sosai Momma tafi dadin yanda yabi Anty Shukran cikin hikima ba tare da ta zargi wani abin ba, dama abin da yasa ta zauna kenan a gurin dan ta ga ko jikan nata zai yi abin da ya dace ko zai tsaya sanya da tsanar yayar mahaifiyarsa, sai kuma ga shi komai ya tafi da kyau ya yi kokari gurin dulmiyar da ita cikin abin da take so ta bashi duk wani gamsasshiyar amsa da yake bukata.
Suna gama tattaunawa ya yi musu sallama ya wuce masallaci, bayan ya yi sallar isha’i da shafa’i da wuturi ya yi yan adduo’insa sannan ya fito suka dan yi hira da ma’aikatansa kafin ya musu sai da safe ya wuce. Yana zuwa ya had’a na’ura me kwakwakwa ya saka duka bayanan Anty Shukra sannan ya musu ma’adana me kyau, sai ya koma cikin aikinsa ya had’a duk abubuwan da yake buk’ata ya tura ta email d’insa yanda zai ji dadin budewa a duk inda yake, bayan ya gama ya yi addua ya kwanta barci.
Acikin sati d’aya ya gama had’a duka bayanai akan lalatattun malaman cikin jimi’ar cikin harda Prof maisamari wanda Muhie ta ta6a kamawa da wata matar aure a office dinsa, kusan lecturer ishirin da biyu, goma sha biyar duk maza, bakwai d’in kuma mata. Da masu neman biyan buk’ata kafin su baka maki me kyau, da masu buk’atan kudi, har gwara ma masu bukatan kudin akan masu lalata samari da yan mata har da matan aure wanda shine mafi muni daga cikin laifuffukan.
Ranar juma’a ya shiga office ya bada report sannan ya d’auki hutun watanni uku, kasancewa bai ta6a neman hutu ba yasa suka ba shi wata biyar yaje ya huta, sosai yaji dadin karin watanni biyun da suka ba shi, ya na sa rai zuwa lokacin ya gama komai sai ya samu damar komawa aiki cikin natsuwarsa. duk masu laifin kuma aka tura wa kotu rahotanninsu da duk wani bayanai na rubuce dana zahiri wanda aka d’auki maganar su da wanda aka d’auki hoto da vedion aika aikan da sukeyi bayan an rufe fuskokinsu da fuskokin wanda suke aikata hakan dashi. Ba a wani wahalar da sharia ba kasancewar komai a bayyane yake yasa aka yanke musu hukuncin shekaru biyar a gidan yari tare da horo me tsanani sannan kuma aka kwace shaidar kasancewarsu malamai domin basu cancanci zama abin koyi ga al’umma, tunda da gyara aka san malamai bada 6atanci ba, hakan kuwa ya zama izina ga yan baya, cike da bakin ciki da nadamar son zuciyar da ya kaisu ga danasani aka tasa k’eyarsu zuwa gidan yari, suka bar iyalansu da kunya a idon duniya.
Gida ya koma cike da farin cikin nasaran da ya samu, barci ya yi sosai dan huta gajiya, domin cikin sati me zuwa yake son ya shirya komai na tunkarar masarautan Hankaka.
♾♾♾
Washe gari da safe suka d’au hanyar zuwa bauchi, duk da cewa batasan ina zai kaita ba amma sai ta fara jin natsuwa, suna cikin tafiya aka kira shi a waya, bayan dogon jawanin da aka yi masa yace “Okay sir” sannan ya ajiye wayar yana me bakin cikin abin da aka sake saka shi a yanzu, juya kan motar yayi zuwa Abuja.
Ita dai tana zaune shuru babu um baba a’a kawai ta sadakar domin yanzu bata san inda zai sake kai ta ba kuma, ta zama waina sai juyata akeyi yanda aka ga dama, tun tana kuka a 6oye har ya fito fili da haka har barci ya d’auketa, ko ci kanki bai ce mata ba.
Sun dad’e a hanya kafin suka isa, bayan sun tsaya a wani restaurant ya tashe ta, abinci suka ci, duk da cewa kawai tusawa takeyi dan kar yunwa ya illatata, a d’an tsorace ta tambaye shi ko zata samu masallaci a kusa, nuna mata wata mata yayi, yace taje ta tambaye ta, cikin sa’a kuwa matar tace mata akwai.
Bayan tayi salla ta same shi a mota suka wuce wani guri, sun dad’e a gurin kafin suka wuce wani gida a maitama, suna zuwa ya nuna mata d’akin da zata zauna, sannan yace da sassafe zasu fita gobe, dan haka ta zama cikin shiri. Take away din dake hannunsa ya mik’a mata tare dayi mata sai da safe.
Washe gari ta tsinci kanta a filin jirgi, duk da dai a tsorace take amma haka ta daure zuciyarta, duk abin da yace tayi shi takeyi, a haka har jirgin su ya d’aga zuwa inda bata sani.
Ita dai bata san tafiyar awanni nawa sukayi ba, domin barcin ta tayi har sai da suka isa, tashin ta ya yi yace mata sun iso, a hankali ta bud’e idonta ta ganta a wani uwa duniya, “New Delhi” ya fad’a a cikin kunnen ta wanda hakan da ya yi sai da tsigar jikin ta ya tashi, ta gefenta ya wuce, da sauri tabi bayansa, “India kenan fa” ta dinga maimaitawa a cikin ranta, ikon Allah ita da take zumudin zuwa gurin karatu sai ta kare a hannun masu satan mutane, yanzu kuma gata a wani k’asar da ba k’asar haihuwarta ba, ko a mafarki bata ta6a tunanin zuwa Niger ba balle India, sosai ta dinga wurga ido tana karewa ko ina kallo a haka har suka shiga wani taxi.
A bakin wani babban gida suka tsaya, yana gaba tana biye dashi a baya, sosai gidan ya burge ta domin komai a cikin tsari yake kuma ba’a cika komai yanda zai yi yawa ba.
Suna shiga ya nuna mata d’akin da zata shiga, da kuma kitchen idan tana buk’atan wani abu zata iya shiga ta dafa dan akwai komai na kayan abinci “Toh” kawai ta iya cewa domin bata san me zai sake faruwa da ita ba kuma, yanzu dai gata a New Delhi kuma tare da mutumin daya sace ta.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😘😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
4️⃣1️⃣♾4️⃣2️⃣
Washe gari Imam ya shirya ya nufi gidan Bukar, Ya Raihana ce ta bud’e mishi k’ofa a lokacin Bukar ya dan fita yana dawowa, Ya Raihan ne ya d’aga dan ganin ko waye, cikin fara’a ya tashi yana cewa “Yallabai kai ne a gidan yau, maraba da zuwa naji dadin ganin ka, dama ina ta neman ka domin mu sakeyi maka godiya” murmushi Imam ya yi yace “ba komai ai yiwa kaine” Ya Raihana ce bayan sun gaisa take cewa “Dama ka san shi ne Raihan?” Ya Raihan yace “ai shine wanda ya ceci Muhievert a ranar da abin ya faru har ya kai ta asibiti shine ya kira gida ya fad’a, a lokacin ni na fara zuwa asibiti, bayan tafiyarsa ku kuma ku ka zo, shiyasa baku gana ba.
+
Sosai maganar ya daki zuciyarta, dama shine Saviour dinta, shine take so take kauna? Yanzu to ya zatayi? Haka tayi ta tunani har Ya Raihana ta shigo dakin, kallonta ta tsaya yi na d’an lokaci, Bukar ya mata maganar abokinsa, kuma tabbas tunda har ya nuna yana sonta lailai har zuciyarsa ne, tunda ya riga ya san abin da ya faru da ita, shi kuma abokin aikin Ya Raihan dama basu riga sun fad’a mishi ba, ita kuma bata samu dama sunyi maganar da shi ba akan sai wani sati zai dawo su fahimci juna “tashi kije ku gaisa da Imam din, abokin mijina da yazo rannan, ashe ma shine ya kwaceki a gurin azzaluman nan, kuma ya kai ki asibiti, tabbas naji dadin hakan kuma ya burgeni, sannan kuma ya yi magana da Bukar akan yana sonki, kije ku gaisa ki tantance idan shi din kike so tunda ya riga ya san komai amma ya nuna yana so, idan kuma abokin aikin Raihan ne shikenan” wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar Muhievert wanda ya gaza 6oyuwa, har sai da Ya Raihana ta gano ta, “ko dai shine dama kike jira yar kanwata?” Rufe idanunta tayi da tafin hannunta cike da jin kunya, hamdala Ya Raihana tayi cike da jin dadi, abin ka yazo da sauki tunda itama tana son shi, dole a bar batun abokin aikin Ya Raihan.
“Tashi ki shirya, zansa Raihan ya bud’e muku falon bak’i sai kibi ta kitchen ki d’auki abin motsa baki ko” kai kawai ta d’aga tana kokarin shiga ban d’aki, da kallo Ya Raihana ta bita, kafin ta fice zuwa kitchen, a lokacin Bukar ya dawo, kiran Ya Raihan tayi, bayan sun ke6e tayi mishi bayanin komai, duk da yaso Muhievert wa abokin aikinsa amma kuma farin cikin ta yafi musu komai, sosai ya nuna farin cikinsa, kuma yace idan yaje gida zai yi wa Ammi bayanin komai, sannan zai bawa abokin aikinsa hakuri.
Wanka tayi taci kwalliya ta sanya atamfa riga da skirt ta d’aura dankwali me kyau sannan ta yafa gyele ta fesa turare guda uku masu kamshi. Kallon kanta ta sakeyi a madubi, sai da ta tabbatar komai yayi dai-dai sannan ta fito ta shiga kitchen, a lokacin Ya Raihan har ya tafi, Ya Raihana kuma tana d’akinta, yaran sunji weekend gurin kakarsu, Bukar kuma suna tare da Imam a falon baki.
Bayan ta had’a snacks din da sukayi jiya da Ya Raihana a wani kwano mai kyau sai ta d’auki zobo da kuma lemon kwali, dan wasu basu fiye son lemon kwali ba sun fi son na gida, bayan ta jera komai a tray ta saka kofi da ruwa me sanyi da mara sanyi sannan ta d’auka ta fita.
A hankali take takawa cike da yanga yanda ta saba, sallama tayi suka amsa sannan Bukar ya fita ya basu guri, table ta ja ta ajiye a gabansa tare da d’aura tray din a kai, sai da ta zuba mishi ruwa a kofi ta mik’a mishi sannan ta koma ta zauna tare da gaisheshi.
Amsawa yayi yana kallon ta, sosai tayi mishi kyau kamar ya sace ta, tunda yake bai ta6a ganinta da kayan arewa ba sai kayan turawa, ga daurin nata ya zauna da kyau kamar kar a kunce “yau dai gani nazo gurinki a matsayin me neman yardarki, soyaryarki da kuma amincewarki” ba tace komai ba sai dai murmushi da tayi wanda ya nuna cewa ya riga ya samu kar6uwa, “yau ina yar kwas-kwas din da ake dagulamin aji da shi?” kallon kafarta tayi ta sake yin murmushi “naga alama ba zaki ce komai ba tunda baki sona, bari kawai in tashi in tafi sai in nemi wata” nan ma shuru tayi sai da taji alamun bud’e kofar falon sannan tayi saurin d’aga kanta ai kuwa sai a cikin nashi, sosai taji kunya ta sake sunkuwar da kanta “Muhievert kiyi min magana mana, kina azabtar dani da shurunki, kin san tun yaushe nake dakon sanki kuwa? Tun a ranar dana fara ganinki naji kin kwanta min a rai, duk da cewa ba zan ce wani halayya ko dabi’a na gani tare dake me kyau ba amma yanayin neman fitinarki yana bani dariya, kullun sai nayi tunaninki da kuma tunanin yanayin rayuwarki, burina bai wuce ace kin shiryu kin kama gaskiya tare da kare martaban kanki dana iyayenki, kuma yanzu na fahimci kin fara komawa irin mace da nake so ki zama, fatana bai wuce ki amsamin da bakin ki cewa kina sona ko baki sona ba, dan Allah kinji ko zan samu sukuni inyi barci me dadi!” Ya fad’a yana lek’ar fuskarta da take kokarin rufewa.
Sake jan gyalen tayi ta rufe fuskarta tana d’an murmushi, wani irin so da kaunarsa ke dawainiya da ita, tabbas tana son shi kuma fatan ta shine ya zama mijinta a duniya da lahira, tun batasan cewa shi din takeso ba har ta fahimci cewa a zahiri ma shine gwaninta sannan a bad’ini ma shine yake zarya a cikin zuciyarta “na amince Allah ya shige mana gaba Ya Imam” ta fad’a tare da barin gurin cikin sauri, murmushi yayi domin ya fahimci cewa ba iya amincewa tayi ba ta riga ta fad’a tarkonsa kamar yadda ya fad’a tarkonta.
♾♾♾
Kamar yadda yace idan ina bukatan wani abu in shiga kitchen hakanne ya faru, yunwa ta faraji tun bayan sallar ishai, hakan yasa ta shiga kitchen din ta dafa indomie guda d’aya da kwai biyu, tana gamawa ta goge ko ina daya 6aci sannan ta d’auki plate din abincin ta wuce d’aki.
Bayan ta gama ci, ta zauna tana tunanin rayuwa da tausayin halin da iyayenta suke ciki da kuma halin da itama zata iya shiga, bayan ta gama karanta wasikar jaki ta tashi ta d’auki plate din ta kai kitchen tare da wankewa sannan ta koma d’aki tayi wanka tare da saka kayan barci, ta kwanta.
Tana kwance taji an bud’e kofar d’akin da take, rufe ido tayi kamar me barci, tana jin alamar mutum a tsaye a kanta, shi kuma Tom kare mata kallo ya shiga yi, yarinyar tana da kyau ba laifi dan haka zai iya aurenta ya zauna da ita harta haifa masa yara kamar yadda ya tsara, shi iyakacinsa ya sayarda mutane ayi harkar karuwanci dasu ko harkar kayan maye ko luwad’i amma bai ta6a sayar da mutun a yan shan jini ba kuma ba zai fara yanzu ba, abin da ogansa ya nema kenan a gurinsa kuma yaga ba zai iya ba shiyasa ya yanke shawarin barin k’asar baki d’aya idan kura ya lafa sai ya koma, shi batun mamansa ma ba case din daya takura mishi bane domin zama guri guda baya tsarinsa, ba zai iya zama sarki kamar yanda take buk’ata ba, ba zai iya zama cikin masarauta Hankaka a matsayin magaji ba, alhali shi din ba d’an sarki na gaskiya bane dan saurayin mahaifiyarsa ce wanda suka haifa bata hanyar aure ba. Cire wannan tunanin yayi a ransa ya tsuguna a gabanta tare da shafa fuskarta, ya dad’e a gurin sannan ya yi mata peck ya kashe mata wuta kafin ya fita zuwa d’akinsa.
Yana fita tayi wani irin ajiyar azuciya, a tunanin ta shikenan ta gama rasa martabarta a yau, domin fad’a da karkarfan namiji irin Oga Tom ba wasa bane ita har tana da karfi ai tuni zai 6a66allata, tayi tunanin zai yi mata wani abu amma ganin babu abin da yayi yasa tayiwa Allah godiya tare da adduar Allah ya kareta daga duk wani sharri.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😘😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
4️⃣3️⃣♾4️⃣4️⃣
Cikin sati biyu kowa a gidansu Muhievert ya san da soyayyarsu da Imam, shi kuma a nashi 6angaren Momma ce kawai ta sani kuma ta sanyawa abin albarka.
Shiri yayi cikin wando da riga na kafta launin toka, sosai kayan ya kar6e shi kuma ya mishi kyau, yar karamar jakan laptop ya d’auka tare da wani jaka babba na trolley, sannan ya fita, bayan yaransa sun saka mishi kayan a cikin mota ya shiga gurin su Momma.
+
A falo ya same su kamar ko yaushe, yanzu ya lura suna yawan zaman falo tare, kuma kila kawai duk shirin Momma ne na son sanin meke tafiya a tare da Anty Shukra, bayan ya gaishesu, yace musu zai wuce amma kila zai rinka shigowa a kai a kai, duk dai abin da yake ciki zai sanar musu, albarka Momma ta sa mishi tare da fatan alkairi Anty Shukra kuwa nata cikar burin shine a ranta, dan tana son kasancewa da masoyinta ko zata samu biyan bukatunta.
♾♾♾
Yana isa bakin gate din masarautan yayi horn, da sauri masu tsaron kofar suka iso suna mika gaisuwa, bayan ya amsa suka koma tare da bud’e mishi gate din, cikin kwarewa yake tuki har ya isa babban parking space din yayi parking na shi motar, kafin ya isa cikin fada har labarin labari ya kai musu, da yawan mutane har sun tsure domin sun san cewa ta faru ta kare musu, daga masu fiffita da hullarsu sai masu yi da malun malun din jikin su.
Labari na kaiwa kunnen Gimbiya Fatsu duk ta rasa natsuwarta, sai safa da marwa takeyi a cikin d’akinta, tun dazu take kiran wayar Shukra sai dai a kashe balle taji ko meye ke faruwa, duk ta jike da zufa ta rasa meye mafita a gareta, ga yaron nata da takeyi dominsa sam abin baya ransa yaki bata had’in kai, a halin da ake ciki ma batasan inda yake ba, tayi ta kiransa a waya amma sai dai ace mata network ba kyau a haka har ta hakura, ga kuma wani rigima ya 6ullo wanda bata san ta yaya zata magance ba tunda babu abin da Shukra take mata game da hakan, ta dai san dama sunyi akan zai zo kuma zai ce baya son mulkin amma labarin da taji rannan ya sa6awa abin da suka kulla da Shukra.
Tafiya yakeyi cikin isa da jin shi din wani ne, duk da cewa shi wanin ne domin ya gaji arziki tako wani 6angare gaba da bayansa duk arzikine na gani na bari bana karewa ba, domin daga y’ay’ansa har jikokinsa har jikokin jikokinsa har tatta6a kunninsa duk zasu mora arzikinsa. Yana shiga ya k’arasa gaban mahaifinsa ya yi gaisuwa sannan ya juya ga mutanen fada yana fuskantar wanda suka fi yin tsuru tsuri da idanu.
“Kamar yanda na fad’a a lokacin zuwana dole ne hakan shi zai kasance, ina fata kun riga da kun shiryawa hakan? Koma dai menene gobe da safe dole za’a nad’ani sarki a masarautan Hankaka, dan haka kuje kuyi shiri kafin wayewar safiyar gobe” yana gama fad’a ya juya ga mahaifinsa “gobe za’a bani abin da yake nawa dan haka sai kazo da shirin murabus domin kana bukatan hutu sosai ni zan cigaba daga inda ka tsaya” ya fad’a yana murmushi sannan ya fita bayan yayi wa dogarai biyu alamun su biyo bayansa.
Gurin motarsa sukaje yace su kwaso kayan dake ciki su kai mishi 6angaren da yake nashi wanda wani daban ya gaje, cike da ladabi suka bi umarninsa, suna tafe yana biye dasu a baya har suka isa 6angaren Tom wannan ake kira Samir, suna zuwa suka gyara mishi komai tare da mishi sallama suka fita kamar yadda ya bukata, suna juyawa ya kira Momma dan ya bata labarin abin da ake ciki, bayan sun gama ya kira masoyiyarsa Muhievert suka sha jiransu sannan ya kwanta dan hutawa.
♾♾♾
Washe gari da safe bayan ta farka tayi wanka sannan ta shirya cikin riga da zani, falo ta fita anan ta same shi yana sha shayi, bayan ta gaishe shi ta wuce kitchen inda itama ta had’a shayi ta sha da bredin data gani a gurin dinning. Tana gamawa yace mata zasu fita, cikin sauri ta dauko gyalenta sannan ta same shi a mota. Tafiya sukeyi shuru babu me cewa wani komai har sai da suka isa gaban wani karamin gida, kallonta ya yi sannan yace “Zaki aureni?”.
Sosai zuciyarta ta tsinke, kamarya kenan me hakan yake nufi, aure wani irin aure, itace zata aureshi, to ta aureshi a matsayin ta auri wa kenan, chabdi jam akwai aiki, gaskiya bata ga abin aure a tare da shi ba, yana Arne tana Musulma gaskiya ba zai yiyu ba ita kam ba zata iya auren wanda ba Musulmi ba, sai dai tana tsoron tace mishi a’a domin bata san me zai iya biyo baya ba, ita dai duk ta rasa mafita, kafin tayi magana taji yace ” bafa shawararki nake nema, yanzu gurin da zamuje aure za’a daura mana na addininku daga nan sai muje ayi na addinin na, ko ki yatda ko kar ki yarda ya rage naki amma dole ne a yau in zama ango kinga kenan za6i ya ragewa me shiga rijiya ko ki amince ko kar ki amince duk ruwanki ni dai yau ango nake gwara ki shirya”.
Gaba daya tama rasa abin yi, ango fa yace zai zama a yau kuma tunda har ya furta to dole ne zai aikata gwarabta rufawa kanta asiri ta amince kafin ya barta da dana sani, “Na amince” kallon ta yayi yana dariyar mugunta, dama ya san hakanne kawai zai sa ta amince dan ya san a addinin musulunci abin Allah wadai ne ace mace tayi ciki ba aure ko kuma taje wani gidan babu martabarta a tare da ita “muje” yace mata, yana gaba tana biye dashi a baya, a falon suka samu wani tsoho tare da wasu samari biyu se yan mata hudu, bayan sun gaisa matan suka shige su kuma aka barsu da dan tsohon, bayan doguwar jawabi tare da amincewar mutane biyun aka yanke cewa za’a yi daurin auren su bayan sallar azahar.
Tana zaune a kan sallaya bayan ta idar da salla taji sun shigo falon, wani irin faduwar gaba taji amma haka tayi ta ambaton Allah tare da rokon alkairin dake cikin tarayyarsu, ta dade a zaune tana adduoin ta kafin ta shafa, matar gidan ce ta shigo tana cewa ta fito mijinta na jiranta, kalmar mijin da matar ta fad’a sai da ya tashi hankalinta, jiki a sanyaye ta fito falon, nasiha wannan tsohon ya musu sannan matarsa ta kara da nata daganan suka musu sallama suka tafi. A bakin wani babban guri suka tsaya, mutane sai shiga da fita sukeyi bayan yayi parking suka shiga anan ta gane cewa inda za’a daura musu aure ne irin na arna, basu wani jima ba sukayi signing wasu papers sannan suka wuce gida kowa na musu fatan alkairi.
Sosai jikinta ya k’ara sanyi data ga har sun iso gida, yanzu fa ita matarsa ce shi kuma mijinta, sai dai tana son sanin dalilin aurenta da ya yi, amma waye ita da har zata tambaya, gum tayi da bakinta har suka fita daga motar. A falo ya zauna ita kuma ta shige d’akinta tare da saka key, dariya yayi bayan yaji karan key din data murza, wato bata san cewa ana ajiye wasu keys bane dan emergency, lailai ma zata yi bayani kuwa. Bai kula da lamarinta ba har sai bayan sallar isha’i bayan ya yi wanka ya kar6o sako daga gurin me gadi sannan ya nufi d’akin nata.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😘😍
*Alhamdulillah mun samu bouncing baby boy, Mrs Noor ta haihu lafiya cikin koshin lafiya, fatan Allah ya raya baby bisa suna*
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
4️⃣5️⃣♾4️⃣6️⃣
Washe gari suka tunkare shi akan maganar aure domin gauro baya mulkin masarautan hankaka sai me iyali, a gurinsa sunyi tunani me kyau duk da cewa ya san suna son su kara samun lokaci ne domin ida nufinsu akan shi, bai musa musu ba ya basu adreshin gidansu Muhievert bayan ya sanar da Bukar cewa ga shi zasuje nema masa aure. Ba tare da 6ata lokaci me tsawo ba aka basu auren tare da saka rana sati biyu masu zuwa a yadda suka bukata.
+
Sosai 6angarori biyun suka shiryawa bikin aure da kuma nad’in sarauta, ko da wasa Muhievert bata ta6a sanin cewa shi din d’an sarkinsu bane, kuma bata ta6a mafarkin aure a gidan sarauta ba saboda yadda takeji ire iren labarai na manakisa da mugayen abubuwa akan masu mulki. Rana dai bata karya sai dai uwar d’iya taji kunya, A yau aka shirya gagarimin taro na musanman na d’aurin auren magaji tare da nadin sarauta, yayin da mahaifinsa ya yi murabus, duk da cewa mahaifin nasa yaji dadi sosai amma sam bai nuna ko a fuska ba, wasu daga cikin mutanen fada sunji dadin nad’a Imam da akayi haka zalika mutanen cikin masarauta sunji dadi sosai yayin da wasun su suke bakin cikin faruwar hakan. Sosai aka gayyato manya da kananun masarautu dan su halarci wannan taro, kuma cikin hukuncin ubangiji komai ya tafi cikin tsari, kamar yadda mutanen Gimbiya Fatsu suka so kashe shi haka mutanen Anty Shukra kuma suke kokarin kare shi, domin shi din a gurin Anty Shukra me rikon mulkin da d’an ta zai hau ne wanda ko haifarsa ba’a yi ba tukunna.
A 6angaren Anty Shukra da Gimbiya Fatsu kuma ce mata tayi, a hakan ya faru ne saboda bata son sarki ya yi tunanin nad’a wani tunda shi yaronta yaki kar6a, zuwa lokacin da d’an Gimbiya Fatsu zai fahimci cewa mulki shine abin da ko wani dan adam yake bukata sai ta sa Imam wai ya sauka ya bashi, maganganu dai da irin su masu karamin kwakwalwa suke fahimta irin shi tayi mata kuma ta yarda dari bisa dari. Sai a lokacin nad’in sarautan Anty Shukra ta san cewa harda d’aurin aurensa, sosai ranta ya 6aci ko da ta tunkaresa da maganar cewa ya yi su suka bukaci da sai ya yi aure shine yace musu su za6a mishi mata, sosai ta sausauta fushin nata dan a ganinta sakin matar ba zai mishi wahala ba tunda ba sonta yakeyi ba dama. Momma kuwa sosai take cikin farin ciki jikanta ya yi aure kuma sannan ya samu gadon kujeran mahaifinsa.
Tarba me kyau amarya da masu rakiyarta suka samu a cikin masarauta domin kwata kwata Gimbiya Fatsu bata nuna alamun wani halayya na daban ba, tarba ta sa aka musu me kyau wanda hakan yasa mutanen da suka kawo Muhievert sukayi ta yabonta. Sai da akayi Walima sannan aka kaita d’akinta wanda iyayenta sukayi matukar kokari gurin k’awata mata komai. Bayan an watse aka bar amarya da angonta cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Cikin sati biyu Memartaba Sarki Imam da amaryarsa wacce yanzu suke kira da Fulani suka gama cin amarcinsu, cikin so da kaunar junansu, bayan nan kuma Imam ya sake appointing wasu sabbin mutanen fada bayan ya gama nazarin cikin masarautan, kad’an ne kawai ya bari akan matsayinsu saboda gaskiyarsu da rikon amanarsu, yayinda da yawansu ya tugesu ya sanya wasu daban, haka ya nad’a sabbin maaikata a 6angaren kula da girki ya tabbatar komai yana tafiya dai-dai, duk wani korafi na cikin masarautan sai daya dai-daita su ya tabbatar ya kawo musu sauyi da maslaha cikin al’amuran su sannan hankalinsa ya koma kan yadda zai nemi mahaifiyarsa.
Wasu mata biyu wanda suka kasance sune amittattun mahaifiyarsa kamar yadda yaji labari su yasa aka nemo mishi dan suyi aiki a 6angaren Muhievert, daganan kuma ya rinka bugun cikin su akan rayuwar masarautan tun daga zamanin kakansa har zuwa na mahaifinsa, sosai ya samu bayanai wanda zasu taimaka mishi daga gurin su, daga nan ya samu wasu manyan fada wadanda dama bai sauke su daga matsayinsu ba saboda yadda yaji ana musu shaidar kasancewa dattijan kwarai kuma amintattun mai martaba, bayanan komai ya kai musu akan abin da yake faruwa, sosai sukayi mamakin hakan saboda basu ta6a sanin cewa har zuwa yanzu matar sarki ta farko tana cikin gidan ba, kuma sunyi alkawarin taimaka mishi ta ko wata hanya.
♾♾♾
A 6angaren Sarah kusan watansu guda kenan da aure, sosai take samun kulawa da soyayya daga gurin Tom, da fara batayi tsammanin samun shi a matsayin mutumin kirki ba duba da ayyukan da yakeyi, sai daga baya ta fahimci harda karancin tarbiyya da kulawa daga gurin mahaifinsa shi ya haifar mishi da wasu halayyar banza da yake yi, duk da cewa shi ba mashayi bane kuma ba me nenan mata ba, amma safaran yaran mutane da yakeyi ba abu ne me kyau ba, babban abin da ta fahimta ma kamar a karkashin mahaifinsa yake wannan aikin, amma zata saka mishi ido domin ta taimaka gurin gyara rayuwarsa kuma da yardan Allah sai ta musuluntar da shi domin ba zata so ace yara su shiga tsakanin su kuma ubansu ya kasance kafiri ba.
Suna zaune a falo bayan sunci abinci ta nemi daya bata tarihin rayuwarsa, duk da cewa cikin tsoro tayi maganar amma bata san cewa zai kulata ba, gyara zama yayi sannan ya fara bata labarinsa.
Mahaifiyarsa ta kasance matar sarkin bauchi ta biyu, kuma Allah bai azurtata da samun zuria da shi ba, zugin kawaye da son zuciya ya kaita ya baro ta inda tayi tarayya da mahaifinsa wanda ya kasance kirista kuma saurayinta, cikin ikon Allah kuma ta samu cikinsa harta haifeshi a cikin masarautan da sunan d’an sarki kuma magajin masarautan hankaka, sannan sukayi wani hade hadensu suka kori matar sarki ta farko tare da d’anta da sunan shine ba d’an sarki na sunna ba.
Bayan daya girma shine mahaifinsa yace dole ne ya kasance kirista idan har mahaifiyarsa na son asirinta ya rufu, a cikin masarauta dai za’a iya daukarsa a matsayin musulmi amma a zahiri shi ba Musulmi bane, ya kuma yi hakanne saboda ba shi da d’a ko daya a duniya matarsa bata ta6a haihuwa ba, sai a kan Tom din ya samu haihuwa, kamar yadda yace hakan ne ya kasance shi musulmi ne a cikin masarauta amma kirista a zuciya da kuma gurin mahaifinsa. Bayan daya mallaki hankalinsa kuma sai mahaifinsa ya d’aurashi akan sana’ar da yakeyi na safaran mutane kuma yace ya zama dole ne ya yi ko yana so ko baya so matukar yana son asirin mahaifiyarsa ya rufu, a haka baban yayi ta threatening dinsa har ya amince amma ba wai a son ransa yakeyi komai ba saboda mahaifiyarsa ne, kuma sannan yana da burin son komawa cikin musulunci amma saboda tsaron dake tare da rayuwarsa yasa ya kasa dan ko wani lokaci akwai masu bibiyarsa.
Sosai ta tausaya mishi tabbas mahaifiyarsa ba mutuniyar kirki bace, taci amanar aurenta kuma taci amanar addininta kuma bata kautawa dan ta ba datayi silar fitowarsa ta hanya mara kyau, bama wai a matsayin saurayi da budurwa ba a matsayin matar wani tayi tarayya da wani, wanin ma kirista ga shi ta janyo wa kanta da danta masifa wanda babu ranar fitarsu daga ciki, duk saboda sarauta da son zuciya ta lalata rayuwarta dana danta, tabbas rayuwar zamani yana cike da ababen son zuciya.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😘😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
4️⃣7️⃣♾4️⃣8️⃣
Wata mace ce zaune a bakin wani bukka tana hura itace, ga shi yaki kamawa, tun safe take abu d’aya amma abin yaci tura, kallon tsohon dake kwance tayi yana numfashi sama-sama, ta san cewa yunwa ne yake damunsa, tashi tayi ta shiga cikin bukkan, ta dauko mayafinta ta yafa sannan ta fita, gidan makociyarsu ta shiga ta samu a dai-dai lokacin tana sauke abinci, bayan sun gaisa ta tsaya kame-kame, fahimtar abin da ya kawo ta yasa matar ta d’auko gawayi da kalanzir kad’an a leda ta mika mata sannan ta diba abincin a leda karami ta bata, godiya tayi mata sannan ta tafi tana tafiya tana share hawaye harta shiga cikin gidan nasu wanda daker suka samu suka kewaye shi da itace da buhu.
+
Abincin ta juye a leda ta ajiye a gaban tsohon sannan ta taimaka mishi ya zauna, abincin ta fara bashi a baki yanaci a hankali yana hawaye, duk shine silar komai saboda son kud’insu yanzu komai ya lalace, son kudi ya kai shi ya baro shi, inda ya bada yarsa a wani abokinsa da sunan zatayi karatu a birni kuma zata dinga aiki wa matarsa. Ko da suka tafi sai abokin ya mayar da yarinya kamar matarsa sai da tayi ciki kusan sau biyar suna zubarwa, ana karshen shine ta mutu bayan ta haihu, shine abokin ya kawo mishi yarinyar ba kunya ba tsoron Allah kuma ya shaida mishi cewa bai aure ta ba wai kaddara ne yasa komai ya faru harta haihu, ga shi yanzu babu me auren yarinyar tasu saboda bata fito daga tsatso me kyau ba, kuma duk gari kowa ya juya mishi baya sai makociyarsu itace take kokarin ciyar dasu wani lokacin, babban abin damuwar ma rashin auren yarinyar, kowa yaki aurenta hakan yasa ya yanke shawaran barin garin zuwa wani gari daban ko zasu samu sausauci, ga shi matarsa ta rasu daga shi sai yarinyar suke rayuwa.
Babban abin damuwar ma shine dama abokin nasa maraya ne har yazo ya yi kudi, kuma yanzu haka bai dade da rasuwa ba a yadda yaji labari daga bakin wani mutumi dake aiki a birni, jikarshi bata da kowa sai shi dan shima maraya ne, iyayen matarsa kuma sun rasu dama ita kadai suka haifa, yanzu burinsa bai wuce ya samu ya aurar da yarinyar ba, domin shekarunta ishirin da biyu kenan a halin yanzu, kullun ya tuna da cewa sanadinsa ne har yanzu ta kasa auruwa sai ya yi kuka domin da bai aika yarsa birni da sunan son samun kudin aikinta ba da hakan be same shi ba, da yanzu ta hanya me kyau aka samu jikarsa kuma da kila itama tana da aure harda yaranta.
A yau suka shirya barin Azare zuwa cikin Bauchi. Kayan nasu ba wani me yawa bane, daga nashi seti uku sai nata seti biyar sai wasu yan abubuwa da suka kullo cikin bako guda sannan kudin gidansu da suka sayar wanda zasuyi amfani dashi a birni, cikin ikon Allah suka shiga bauchi lafiya cikin koshin lafiya, sai dai kaddaran haduwarta da maceccen mahaifinta da akace ya mutu shine ya kaita garin bauchi, suna kokarin tsallake kwalta wani mota yazo ya buge kakanta kuma buguwa sosai, kasancewar jini ya 6ata mishi fuska shine yasa bai gane abokin nasa ba, kafin su isa asibiti harya cika ganin haka yasa yacewa direban ya juya zuwa gidansa, sai a lokacin ya gane cewa abokinsa ne, saurin kallon yarinyar da take kuka yakeyi kenan yarsa ne wannan wanda ya wurgar da ita a lokacin baya cikin hayyacinsa, kasancewar ya san abokin nasa musulmi ne shiyasa ya yi wa wani malamin dake gefen gidanshi magana, inda cikin lokaci kadan aka shirya shi aka mishi salla tare da kai shi gidansa na gaskiya.
A gidan malamin ta zauna har akayi sadakan bakwai, ba laifi mutane sun shishiga yi mata gaisuwa kuma anyi zaman makoki kasancewar mutumin yace musu dan uwansa ne ya rasun, kuma a matsayinsa na malami me jama’a shiyasa aka taru aka mishi kara. A ranar da akayi bakwai mahaifinta yazo ya mishi godiya tare dayi mishi bayanin matsayin yarinyar da kuma mutumin daya rasun a gurinsa, sosai malamin yayi mamaki amma duba da yadda yarinyar ke kama dashi yasa bai musa ba, a ranar ta koma cikin gidan mahaifinta da zama.
Bayan ta koma ya kirata ya sanar da ita matsayin ta a gurinsa, ita dai kawai kallonsa takeyi tana me jin bakin cikin kasancewarsa mahaifinta, tabbas mahaifiyarta bata kyauta mata ba, ta rasa da wanda zatayi tarayya sai Arne wanda da ganinsa ma kasan yasha arnanci ya koshi, tana cikin tunanin ya soma mata bayanin yadda suke da kakanta.
Sun taso tare a gidan marayu amma saboda yadda ake wahalar dasu yasa suka gudu, zaa kawo abinci iri daban daban masu yawa domin su amma sai ma’aikatan su rabe a tsakaninsu sai a barsu da shan garin kwaki ko ruwan shayi a kullun sai an samu wadanda suka mutu a cikinsu saboda yunwa mafi yawancinsu ma suna fana da cutar ulcer. Bayan sun gudu suka fara bara a cikin azare a haka har suka tara abin hannun su shine kakanta yayi aure, inda shi kuma yace ba yanzu ba, a lokacin ya kan shiga cikin bauchi har ya hadu da uban gidansa wanda yake yiwa safaran yara mata da maza, samari da yan mata kuma yana samun kudi sosai, karshe ya koma cikin Bauchi da zama harya auri matarsa wanda suke tare yanzu me suna Favour, bayan wasu lokaci ya shiga harkan yan shan jini inda kuma suka bukaci dole sai yayi tarayya da budurwa kuma musulma, a lokacin an haifi mamanta shine ya yi wa kakanta dadin baki tare da bashi kudi masu yawa yace zai sata a boko kuma zata dinga taya matarsa aiki sannan zai dinga turawa kakanta kudin, haka akayi bayan an kawota batama cikin hankalinta dan akwai maganin da aka bashi yake amfani da shi akanta a haka har ya mata ciki sau biyar suna shanye jinin yaran kamar yadda suka bukata. A cikinta na karshe ne kuma aka haifi Amatullah wanda kakanta ne ya rad’a mata sunan kuma a lokacin mahaifiyarta ta rasu bayan ta haifeta, sonta da tausayinta ne yasa ya yanke shawaran riketa, bayan ya kaiwa matarsa daker ta amince ta riketa daga baya kuma ta mishi magani har sai da ya mayar da ita gurin kakanta, a lokacin ne ya sanar musu da rasuwan yarsu hakan kuma shine silar mutuwar kakarta, kakanta kuma ya samu shanyewan 6ari daya, da taimakon makocinsa kafin ya rasu yarinyar ta samu kulawa harta girma ta fara taimaka masa.
Sannan kafin ya fara tarayya da mahaifiyarta akwai budurwarsa yar gidan wani senata wanda tun kafin yayi aure suke tare ita ma kuma tun kafin tayi aure suke tare, bayan auren ne suka dai na mu’amala, sai bayan wani lokaci da bukatar hakan ya taso shine sukayi tarayya har ta haifi d’a namiji, a lokacin bai ta6a haihuwa ba sai a kan yaron, daga baya kuma bayan tarayyarsa da mahaifiyarta shine aka haifeta, tun daga lokacin kuma ya fita a cikin kungiyar duk da cewa sai da ya biya su makudan kudi sannan suka barshi ya fita, tun daga lokacin kuma ya bar kasar bai cika zama a Nigeria ba sai jefi jefi, a haka har yaron ya girma ya daura shi akan harkokinsa na safaran yaran mata da maza duk da cewa ya lura yaron ba son yin hakan takeyi ba amma kuma ya zama dole ya yi saboda ya rufa asirin mahaifiyarsa.
Bayan ya dawo cikin hayyacinsa sosai sukayi fada da matarsa har sai da ya kora ta gida saboda bacin rai, daga baya iyayenta suka roke shi akan ya yi hakuri shi ne ya hakura saboda ganin girmansu a idon shi, yaso yaje ya samu kakanta domin ya nemi yafiyarsa, sai dai kunyarsa yasa ya kasa zuwa, amma kullun yana ransa haka itama kullun yana tunaninta yana son sanin ya kamanninta suke da mamanta take kama ko da shi take kama, a ranar da abin ya faru ma yana kan hanyar zuwa wani aiki ne a Abuja shine kaddara ya hadasu.
_*D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻
🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng………..✍🏻
🌐 *R̥ͦḀͦY̥ͦU̥ͦW̥ͦḀͦR̥ͦ Z̥ͦḀͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦ*
( _K̥ͦO̥ͦ S̥ͦO̥ͦN̥ͦ Z̥ͦU̥ͦC̥ͦI̥ͦY̥ͦḀͦ_)
W̥ͦr̥ͦi̥ͦt̥ͦt̥ͦe̥ͦn̥ͦ b̥ͦy̥ͦ
_*Z̥ͦḁͦh̥ͦr̥ͦḁͦ Ḁͦ Ḁͦl̥ͦk̥ͦḁͦl̥ͦi̥ͦ (D̥ͦi̥ͦd̥ͦe̥ͦe̥ͦy̥ͦl̥ͦo̥ͦv̥ͦ)*_
_Sadaukarwa ga Mrs Aliyu & Mrs Noor_😘😍
_B̥ͦI̥ͦS̥ͦM̥ͦI̥ͦL̥ͦL̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦM̥ͦḀͦN̥ͦI̥ͦR̥ͦ R̥ͦḀͦH̥ͦI̥ͦM̥ͦ_
4️⃣9️⃣♾5️⃣0️⃣
Yau gidansu Muhievert sun tashi da manyan baki, yan uwan Sulaiman ne suka zo godiyan irin hidimar da aka musu lokacin bikin Sulaiman din, kasancewar ya samu aikin koyarwa a wani makarantar gobnati shine ya bar aiki a gidan ya d’ora d’an uwansa Ibro a kai, bayan nan kuma ya shirya aurensa, inda su Ammi suka mishi kara sosai duk da cewa basu samu zuwa bikin ba saboda wasu dalilai amma sunyi rawar gani sosai a kan abubuwan da aka gabatar gurin bikin.
+
Suna zaune a falo tare da duka yan gidan su Ammi suka fito suna yar hiran su, cikin sauri Goggo Hama ta tashi har zaninta yana kuncewa tana cewa “wa nake gani kamar Hamza da Rashida?” Sai a lokaci su Ammi suka d’ago suka kallesu, da sauri Abbu ya k’arasa gabanta yana cewa “Yaya kece ko dai gizo kike min kamar ko yaushe?” Cikin kuka da kuma dana sani ta isa gareshi itama suka kankame juna kamar wasu kananun yara suka fashe da kuka, kowa a gurin sai da ya yi hawayen tausayin yanayin da suke ciki.
Sun dad’e suna kankame da juna suna kuka kafin suka tsagaita tare da sake junansu “Yaya dama kina raye duk tsawon shekarunnan, kar dai ace Sulaiman d’ana ne yake min aikin direba idan kuwa hakan ne wannan abu bai yi dadi ba gaskiya, ina kika shiga duk tsawon shekarunnan meye ya hanaki bayyana kanki Yaya? Ai ko da ace chan garin mu kika koma kikayi cigiyar mu zaki samu masu kawoki domin bamu wofintar dasu ba muna zuwa a kai a kai”.
Wani kukan ta kara fashewa da shi sannan ta fara bada labarin duk wani abin da ya faru da kuma dalilinta na kin komawa gurinsu wanda sai yanzu take kara tabbatar da cewa tayi wauta ba kadan ba, anan take sanar dasu cewa Sulaiman d’anta ne na biyu, sannan ta nuna musu yaranta da jikokinta, sannan ta basu labarin 6atan Sarah da kuma halin da mahaifiyarta take ciki har yanzu tana kwance. Sosai suka tausaya musu duk da cewa sunji haushin abin da ta aikata sai dai sun barshi a matsayin kaddara wanda bawa baya iya tsallake wa.
Bayan sun gama jimamin Abbu yake cewa ” Yaya ai ga irin ta nan ace d’an yar uwata ne yake aikin tuki a gidana, gaskiya kinci amanar zumuncin mu, ni a ko da yaushe ina tunanin ina zan ganki a wani hali kike, dan ban ta6a ji araina cewa baki raye ba, ga shi har ya kai zuri’ar mu basu san juna ba, idan da ace Allah bai kawoki gidannan yau ba da haka y’ay’ana zasuyi ta yimin aiki a gidana ba tare da nida su mun san cewa muna da dangantaka ba? Shin hakan rayuwar zamani ne ko kuma son zuciya ne Yaya”.
Share hawayenta tayi kafin tace “son zuciya ne Hamza, tabbas son zuciya ne kawai ya kai ni ya baroni, nida nake ganin na samu gurin zama bana son muzo muci arziki tare sai ga shi zuri’ata ma arzikinka suke ci, haka zalika ni kaina arzikinka nake ci ba tare dana sani ba, ba zan iya maida hannun agogo baya ba, amma dan Allah kayi hakuri ka yafemin kanina na tuba nabi Allah, ka duba girman Allah ka yafemin”.
Ajiyar zuciya ya yi kafin yace ” na yafe miki Yaya, Allah ma muna mishi laifi yana yafe mana, waye ni da bazan yafe miki ba, Allah yana son masu yafiya dan haka ni kam na yafe miki duniya da lahira. Ai Yaya ko a iya yanayin rayuwarmu yaci ace na fahimci cewa sakaryar ubangiji ne, kin nufe ni da karewa a talauci sai Allah ya azurtani ke kuma ya barki a yadda kika so ganina, tabbas Allah ba azzalumin sarki bane kuma na gode mishi bisa ni’imar dayamin, Allah ya yafe mana baki d’aya shine kawai zancen”.
STORY CONTINUES BELOW
Amin duk suka amsa dashi sannan aka koma hiran duniya, sun dade suna hiran rayuwa da yadda kowa ya fuskanci nasa rayuwar sannan suka dawo zancen 6atan Sarah inda Abbu yace in sha Allahu zai yi magana da manyan jami’an tsaro akan lamarin kuma komai zai zo da sauki da yardan Allah, kalamansa ne suka sanyaya musu zuciya inda suka ganin tabbas hakan zai faranta ran mahaifiyarta. Bayan sallar la’asar suka shirya tafiya gida, Abbu yaso su kwana amma sukace ba zai yiyu ba saboda sun bar Umma ita kadai a gida. Bayan komawarsu suka sanar da Sulaiman labarin komai, sosai ya jinjina lamarin a ransa yana cewa ashe yar bala’in yar uwarsa ce, amma daya tuna da cewa yanzu ta shiryu ta zama saliha sai ya yi murmushi kawai yana cewa duniya juyi juyi. Aisha ma ko da aka bata labari harda hawayenta na taya Goggo Hama farincikin samun dan uwanta.
Bayan sati guda Abbu ya aika aka d’auko su, inda ya saya musu gida me kyau me d’auke da bangarori guda uku, d’aya a Goggo Hama daya na Malam Balarabe sai d’aya na Sulaiman shi da matarsa, sosai sukayi farin ciki harda kukansu, yaranta da jikokinta kuwa tunaninsu shine Goggo Hama ta cutar dasu tun farko da basu taso cikin bakin talauci ba, gasu da gatansu amma son zuciya yasa ta lalata rayuwarta da tasu, sai dai kuma da suka sake tunani suka fahimci cewa bawa baya wuce kaddaran rayuwarsa, kuma hakan jarabawa ne a garesu, hakan yasa suka cire komai a ransu suka yafe mata.
Zama sukeyi cike da jin dadi da so da kaunar junansu, gidansu na da duk sun bada hayarsa, sannan Abbu ta d’auki Malam Balarabe da Sulaiman aiki a cikin kamfaninsa, Ibro kuma aka maida shi makaranta, sauran yaran Malam Balarabe suma aka sanyasu a makarantarsu Yazeed. Yanzu basu da matsalar komai sai tunanin Sarah da kuma yadda za’ayi ta dawo garesu.
♾♾♾
A 6angaren Sarah suna zaune lafiya da mijinta harda d’an karamin ciki a tare da ita, kullun burinta ta dawo gida ko hankalin iyayenta zai kwanta, sai kuma yadda zata samu damar musuluntar da mijinta tunda ta ga yana ra’ayin musuluncin, abin farin ciki guda d’aya ne a yanzu shine barin harkan safaran yara gaba daya ya fita a cikin gur6ataccen sana’ar da ba shi da fa’ida ya koma business me kyau inda yake saro kayan kasarsa da babu a kasar waje yake saidawa.
♾♾♾
A 6angaren Amatullah kuwa tunda mahaifinta ya gama mata bayanai marasa dadin ji duk ta shiga tashin hankali ta rasa sukuninta babban abin da yake bata mamakin shine wai tana da dan uwa kuma kirista kuma shima ba dan sunna ba kuma a gidan sarki aka haifeshi a matsayin magaji, sosai ta jinjina lamarin tana me tunanin duk hakan son zuciya ne ko rayuwar zamani?…
_________________
Bayan shekaru uku…
Bayan wadannan shekarun abubuwa da yawa sun faru, na farko Imam ya samu mahaifiyarsa wacce ta sha wahalar rayuwa duk ta fita hayyacinta, sai da aka had’a da zaman asibiti da kuma addua sannan ta dawo dai-dai, a nan ne kuma take sanar dasu cewa bayan dawowarta gida watarana aka kirata daga fada akan cewa sarki bashida lafiya kuma yace yana son ganinta, cikin tashin hankali ta isa fada inda ta samu ashe hadin baki ne tsakanin Shukra da Gimbiya Fatsu akan cewa zasu tsareta a inda baza’a sake ganinta ba, Shukra kuma zata koma gida a matsayinta, yayin da d’an Gimbiya Fatsu zai d’ale mulki. Ita Gimbiya Fatsu bata da labarin cewa Shukra tana son sarki kuma hakan duk cikin shirinta ne na son komawa gidan a matsayin Kubra, duk wani makirci da cin amana da suka mata sai da ta bada labari, anan take sanar dasu cewan d’an Gimbiya Fatsu ba d’an me martaba bane d’an wani k’asurgumin arne ne, sosai Gimbiya Fatsu tayi nadamar abin da ta aikata musanman hukuncin kisa ta hanyar jifa da aka yanke mata.
Haka zalika Shukra an yanke mata zaman gidan yari na shekaru biyar tare da horo me tsanani, haka zalika kuma ance su biya kudi na 6ata sunan da sukayiwa Kubra da d’an ta Imam amma tace ta yafe musu duniya da lahira, suna ji suna gani suka rasa abubuwan da sukayi aikin mugunta dan tarawa, babban abin bakin cikin su Kubra ta koma d’akinta sannan Imam ya tabbata me mulkin Masarautan Hankaka, ga kuma magaji da suka sake samu Muhievert ta haihu y’ay’a biyu, na farkon namiji na biyun kuma d’iya mace, Gimbiya Fatsu abin harya mata yawa, ga d’anta da ya yi aure ba tare data sani ba kuma har da zuri’a a tsakaninsu da matar daya aura yara uku na farkon yan biyu mata na biyu kuma namiji. Sosai duk sukayi nadaman ayyukan da suka aikata na son zuciya duk da cewa sunji bakin cikin cigaban dasu Kubra suka samu ita da d’anta amma hakan bai hanasu nadamar rayuwar da suka jefa kansu ba. a 6angaren Shukra daker Momma ta yafe mata haka zalika yan uwanta suma sunyi bakin cikin abubuwan data aikata ga Kubra, kuma albarkacin Kubran ne ta samu sausaucin hukuncin da aka yanke mata zuwa shekaru uku a gidan yari.
Abu na biyu shine 6angarensu Sarah, Tom ya musulunta ya koma Muhammad Al’amin, kuma Allah ya azurtasu da samun yara uku, na farkon mata biyu Fatima me sunan Gimbiya Fatsu da kuma Aisha me sunan mahaifiyar Sarah, sai kuma namijin me sunan kawunta Hamza wanda take fatan Allah yasa watarana su gana da Goggo Hama… Cikin ikon Allah bayan dawowarsu da suka ziyarci me martaba domin ba shi hakuri da nemawa Gimbiya Fatsu yafiya ta had’u da iyayenta, a lokacin Goggo Hama da Abbu sunje yiwa me martaba jaje shine suka hadu, sosai sukayi farin ciki tare da jinjina al’amarin junansu kuma suka sanyawa auren albarka.
Abu na uku shine auren Raihan da Amatullah, bayan Tom (Muhammad Al’amin) ya had’u da yar uwarsa ya gabatar da ita gasu Ammi tare da bada ita wa Ammi domin ta kula da tarbiyyanta anan Raihan ya fad’a kogin soyayya har ta kaisu ga aure, yanzu haka tana da d’an karamin ciki wanda yake matukar bata wahala, mahaifinsu kuma ya rasu bayan ya musulunta, inda suka yi hatsari tare da matarsa a hanyarsu ta dawowa daga gidan marayu.
Duk wanda ya shuka alkairi ya girbi fiye da abin da ya shukan, wanda ya shuka sharri shima ya girbi fiye da hakan… Duk wani mugu yaga rayuwa kuma yaga ishara, duk wani me kyaun zuciya kuma yaga rayuwa me kyau tare da alkairai masu dimbin yawa… A yanzu farin ciki da kwanciyar hankali shi ya cigaba da wanzuwa a cikin rayuwarsu tare da kuma jarabawa wanda baya wucewa a cikin rayuwar d’an adam na dadi ko ak’asinsa…
Alhamdulillah Tammat Billah😍
Laifin dadi karewa Alhamdulillah ala kulli halin duk abunda yayi farko yanada karshe abunda muka fada daidai Allah ya hadamu a ladan kuskuren da mukayi kuma Allah ya yafemana baki d’aya.