RIKICIN KAUNA CHAPTER 10 BY MARYAM SALISU MAI DALA

Ya ce «Yawwa ki tafi da wannan ki ce shi zata dafa min kafin na zo.”
‘ Yana miko mata leda.

  • Sannan ya sake miko mata wata ya ce

“Wannan kuma na Inna ne amma kafin haka..

Dubu ta katse sun sa’adda ta iso gurin ita da kawayenta, biyu, Tafida ya karbi duka aiken na hannun Nana ya ce “Kuje ku gama duk abinda kuke saiku biyo ta nan.”Nana ta dan kalle shi kadan sannan a hankali ta juya tace to, yana kallon Dubu har da dan daka

• mata duka a baya ta ce “Kai su ‘yar boko babu ma ko magama.”

Nana ta juyo da dan yake ta ce “Ah Dubu sannunki.” Suka wuce suka barsu a nan.

.. Sai da suka gama siyo abinda zasu siyo suka dawo ta wajen Tafida suka tarar suma su dubun sun tafi Tafida ya bar wani gurin kayan hatsin da yake siyarwa ya jire masa ya ce dasu Nana su biyo shi don har sai da suka dan kalli juna ita da Laure, sannan suka bishi, suka lura shi din ma kamar yana. dan waigen ko wani yana kallonsu, nan’ kuwa tunaninsa ko Dubu bata bar gurin ba tana kallonsu shi yasa yake dubawa, sai gani su • Nana suka yi yaje da su babbar rumfar Alhaji Dalha wadda yaransa suke ciki inda ake siyar da kaya kawai na mata Tafida ya dan matsa yace wa Nana shigowa zakuyi ku zabar mata atamfa guda biyar don nasan ita ba wani sanin kyau sosai tayi ba

Nana ta kalli Laure sukayi murmushi duka suka gane kayan taron aure yake mufi nan suka shiga suna zabo masa suna dagowa suna nuna masa tayi? Ya dan matsa ya yafito Nana ya ce “Ba lallai sai kin nuna min ba in dai tayi miki.

Ya juya ya fita wajen rumfar yana hangen kada

Dubu ta zo don yasan muddin kuwa yau taga yasai wannan to tabbas duka Kauyen sai anji, su Nana suka zabar masa sun kuwa zabi masu kyau guda biyar din kamar yadda ya ce, Laure ta leko tana fado masa ya shigo shima ya gani ya ce a zuba a leda mai girma aka zuba akai mishi lissafi ya duba ya biya yana duba ragowar kudin nasa ya ce musu zai isa har a dan kuma siyan wani abu Laure ta ce a sayi takalmi, Nana ta ce a’a wa ya san irin kafar Dubu sai dai idan da ta sa za a gwada suka yi dariya ya katse sun ya ce “Ku yi sauri yamma na yi.”

Nana ta ce “A siyi mayafi tunda akwai kalar atamfar a nan.”

Tafida ya kalleta ya dan tabe baki ya ce “Oh su

Nana har an san a hada kala da kala.”Ta dan harare shi kadan kada kuma ya zarce da halin shima ya gano yayi sauri ya yi gyaran murya yace To a dauko.”

‘Suka zabi guda uku kalolin

kayan shima ya biya suka fito ya ce “*Yawwa Nana kada ku buda ko a hanya don nan duk kawayenta ne a kasuwar ki kaiwa kaka ta ajiye kafin na iso.” Suka amsa, ya wuto suka biyo shi zuwa tasa rumfar ya basu sakon dazu har zasu wuce ya dakatar da su ya kirawo wata me kayan kwalam ya sai musu da yawa a leda yace to sai ku raba wannan, har ya fadi hakan ya kuma cewa sai ku da irin yadda Nana ke fadar dinta ya fada don itama hakan take cewa, idan zata ce a rarraba, yana ‘yar dariya ya kuma maimaitawa, Nana ta fahimta da itan yake, ta ce “Mu rgrraba har dubun kenan.”

Da sauri Tafida ya ce “A’a ni ba da ita na ce ba kar ma ku doshe ta.

Nana ta ce “Ai kai kacemu rarraba.”

•Ya ce “To ku raba ku biyu ke da Laure.”

Suka yi dariya suka wuce shima ya bisu da kallo yana dariyar Nana wato ita ko a magana sai

‘ta rama, ya koma cikin tasa rumfa.

Da sauri Nana suka shiga gurin kaka Nana da dokin ta tana zazzage kaya tana nunawa kaka, kaka na tambaya ta ce “Na Tafida ne, taronsa ya fara.” Tana daga mata atamfa ruwan hoda tace

“Duba kaka, dubi wani nan don Allah dubi kyanta.”

Don har tana tashi tsayen tana karata a jikinta.

Tace “Tamkar ta zama tawa.”

Kaka ta ce “Ai ko dai tayi kyau wa ya zabo shi din Tafida da kansa.”

Laure ta ce “nanace ta zabo shi yasa kikaji tana ta yaba ta.”Kaka ta ce “Oh! Ashe Allah zai nuna mana

Tafida da shirin aure.” Tana rike baki.

Ta kalli Nana ta ce “Dama na fada muddin anyi baikon zai maida hankali ba gashi ba.” Tana nuna kayan da hannu. Yayin da Nana ke maida su cikin mazubinsu, Laure tace “Ai Tafidan ne sai ki ga ma kamar ma ba son dubun yake sosai ba. “

Kaka ta karba ta ce “Ai irin kalar nashi son kenan Tafida yayi kamar bai damun ba nace miki ba gashi ba, da ko zancen auren bai dame shi ba sai da akayi baikon yanzu kuma kalli ya fara maida hankali Tafida ne taron aure shi da tirame biyar ya fara da gyalulluka, ai kin san muddin yayi auren ma son zai karu ne.”

Nana kuwa ta mike tana dan kallon dakunan biyun tace “Kaka amma har dakunan nan sai an gyara sun.”

Kaka ta ce “Ke dai ya gama mé wuyar idan ya gama wannan shi gyara ko ana gobe za a° saka

Dubu za a iya yinsa.”

Nana ta sake janyo leda tana fadawa kaka yadda Tafida ya ce sa’annan suka raba abinda Tafida ya sai musu har suka dan dibarwa kaka sannan ta dauko ledar gidansu da yace a kawowa

Innarsu suka fito da ita da Laure ta shige gida itama Laure ta yi gaba zuwa gidansu.

Da yammacin ranar Asabar Tafida (Abubakar)

ya biyo hanya shi daya zai Karasa mahadarsu kafin ya Karasa din ya jiyo kamar ana kiransa ya Karasa dan wani loko sai ga Lamimi da farantinta na goro aka ta dan kallace shi a kunyace tana gaisheshi, ya gano ta don yaji rannan Balele ya ce tana sonshi

‘yar gidan baba Wanzan to shi din ma har a lokacin bai sani ba amma a yanzun ya kara fahimta, to hakanma yayi a yanzun tamkar bai san komai ba, yace “Yammata ina gajiya.”Tana boye fuskar ta ta amsa, sannan ta ce “Da ma wannan ne za a kaiwa kaka.” Tana miko goro farare da ja a leda guda biyar.

Tafida ya ce “To! Kaka? Kuma duk har haka?” Ta sake jin nauyi tana boye fuska, ya karba yana dubawa ya dan kalleta sosai sai kuma ya

Hmmmm