sai sashin tsakar gidan dake bangaren dakin nasu.
Da’u ya ce “Ai fa kaga ta barka tana jiyoka ta katanga.” Yana dariya.
Tafida ya dan kalle shi yana girgiza kai, “Jiya ma fa wankana biyu saboda zafi yau ma amma.’ Yana cije lebe.
Da’u ya sake dariya ya mike “Ni bani kayana na wuce wannan fadan naku ba karewa yake yi ba.”
Da yamma Tafida na mahadarsu ta matasa ya tsaida yaro ya saya musu fashe suna ci ya cewa yaron ya biya yakaiwa kaka Kulli biyu agida, suna ci din ana ta zuba surutu kowa da abin da yake fadowa na ban dariya.
Da’u ya tabo Tafida ya ce “Kai Tafida mutuniyar ce fa a wancen bayan shigen ta kuwa zubo maka ido.’
Tafida ya ce “Ina kallon ta.”
Balele ya shiga waige yana cewa “Wai wace?”
Da’u ya ce
“Dubu mana ga ta can ga ta can.”
Yana dan dauke ido kada ta gano suna kallonta.
Dayan abokin shima ya saci kallon gurin a hankali ya ce “Allah sarki kai kuwa Tafida ka tashi kaje mana ai kun saba haka ko dan yau bata wuceta gabanmu ba.”
Tafida ya ce “Kai Kyaleta fada mukayi ba zani ba.”
Balele ya balalo ido ya ce “Fada!kace lallai yau *yanmatan za su sami da Tafida.’
Da’ú ya ce “Anya kuwa? Ko sun yi rikici
Dubu zata dagawa ‘yammata Tafida kafa ne duk tsoronta suke yi shi yasa.”
Balele ya dubi Tafida ya ce “Kai me ‘yam
Kai sai zuba fashenka kake yi ma kana jinmu
Tafida ya ce “To me zan ce muku.
Dayan abokin Kasimu ya ce “Rannan baka nan tafida
*yammata biyar mukayi
wadanda ke son ka a karkarar nan ga Dubu ta shida, itan kuma duk ta dokesu ta hana mu kallonka su dinga yi.”Tafida ya kalleshi “Kai Kasimu ka ji
Allah ni da wa? ‘Yammata shida sai kace sarkin mata, ni dai ban san su haka har shida Balele ya ce “Dakata-dakata.” Don har gyara hularsa da zama ya ce “Kaga akwai Ta Baito, ga Lamimi.”
Tafida ya zubo masa ido ya ce “Wacece
Balele ya ce “Lamimin baba wanzan.’
Tafida ya ce “Tow! Ni ban ma sani ba.” Balele ya ci gaba “Ga Atine da Habi, don ita
Atine ma rannan rannan saida suka sha dambe da duba a zaurensu Atinen wai don Atinen ta yiwa kawayen zancen tana, sonka kana bata sha’awa.”
Tafida kuwa yayi tsumu kawai yana ji, Kasimu ya ce “Su fa duk wannan dan kallon soyayyar da idon Tafida ke yi shi suke so, don Dubu ma rannan cewa ta yi wai ta gane kallon Tafida ma kadai yana rudar “yamamta ba wai tsarinsa.”
Tafida ya ja tsaki “Allah ya kyauta.” Ya ci gaba da cin fashensa.
Da’u ya ce “To kai yanzu wannan dan rikicin na kauna da kukeyi da Dubu ka huce don nasan daga gareka ne, gudun ma kada a kuma wani
Balele ya ce “Kai ni Tafida gara ma kai don kana kiyayewa ba wai kullum cikin jansu kake yi ba, ko ka dinga aura kana saki, kun san Magaji dan maizari ya sako Furera duka kwana uku kenan.
Gaba daya suka zubo masa ido, ya amsa cikin
takaici (Furera itace wadda suka so juna ita da
Balele amna akai musu fin Karfi aka rabasu dan maigari magaji ya aura da kansa ya sa aka yi haka). Tafida ya furzar da fashen dake bakinsa ya ce
“Wace irin rayuwa ake yi ne a karkarar nan saboda
Allah duka yaushe Magaji ya auri Furera amma har ya sakota.”
Da’u shima da mamakin ya ce “Yo ko shekara anyi.”
Balele ya ce “Wata tara kenan da auren ya sako ta da ciki.”
Tafida ya sake daga kai yana jimanta abin yayin da kowa ya ci gaba da fado ta bakinsa,
.T’afida ya ce “Babu dabara a irin haka babu wani
• girma da irin haka sai cin zarafi da tauye hakki.”
Kasimu ya mirgina kai, ya ce “A to kowa yana gani a kauyen nan ana yin ba daidai ba amma an kasa magana saboda maasu abin ne da kansu, don yanzu duka da Furera Magaji ya saki yammata tara kenan wadanda ya aure su akan ganin ganiyarsu, kuma kuwacce da ciki take fitowa daga gidanshi saboda Allah!” Yana kallon ragowar.
Balele ya ce “Sai ma da kun duba duka
• Magajin nawa yake kusan sa’ anmu ne ko zai dara mu dan kadan ne amma ya yi aure ya kai sha biyu.
Tafida ya dan zaro ido, Da’u ya ce “Iyi mana?
Ai yanzu tunda Furera ta fito to saura uku a cikin gidan kafin a kwana biyu ya kuma kyallo wata yarinyar ya maidata gurbin Furera.”
Kawai Tafida mikewa ya yi ya shuri takalmansa don ba ma ya son jin kayan takaici yana “To Allah ya kyauta.”
Kasimu ya ce “Wallahi sai dai idan bai gano wata kyakkyawar ba.”
Da dare Tafida na tsakar gidansu kusa da kaka yana cin tuwonsa suna sake jimantawa da ga abinda itama kakan taji wanda Magaji dan Maigari ya yi ga Furerar Balele har tana cewa “Au kai baka sani ba ai har an kwaso kayanta jiya.”
Daga inda suke suna jiyo muryar Malam Mado Babansu Nana shima a nasa tsakar gidan, yana kiran Nana ta zo ta karbi maganin sauro yana miko mata, Kanin Nana ne ya yi sallama ya karaso da kwanan abincin Kaka na gidansu ya aje a gabanta, Tafida ya ce “Sannunka dan Allah dan mikomin ruwa a randar Kaka.”
ya miko mishi, yayin da itama Kaka ta lalubi ragowa fashen dazu a leda ta bawa Ila ya karba ya wuce gida.
Kaka ta ce “Don Allah Tafida ku kada ku yiwa aure irin wannan a dinga sakaku a baka.”
Tafida ya ce “Ina! Inal kaka Allah ya kiyaye ai haushin abin naji sosai da naji bare kuma ni da
Hmmm