Da’u shima ya mike, kaka ta ce “Ashe baku ta re da Tafida.”
Suka dan kalli juna Da°u da Balele, saboda maganar da suke yi kenan sai ga kakan, Da°u ya dan juya da sauri ya kalleta ya ce “Kaka Tafida ya sallameni ya wuce birni.”
Gaban kaka ya dan fadi amma bataso ta nuna,
Da’u ya ci gaba “Ko käka ke bai miki sallamar dake ba ne.” Kaka ta girgiza kai kawai ta san abinda suka yin a jiya, Balele yana rike baki ya ce “Lallai Tafida!”
Da’u ya ce “Ni ya zo ya ce min wai zai wce birni birnin má kuma Kano ni na dauka ya sallami kowa ashe ke ma da kuke makwanta guda baki sani ba.”
Kaka kawai shiru tayin daga bayan tace “Shi kenan.” Ta wuce cikin sanyin jiki sosai.
Da°u da Balele suna dan bata baki da hakuri don rashin kyautawar Tafida tana bada baya suka danyi dariya, Da’u ya ce “Kuma duk rintsin fadan nasu na baka yau zuwa kwanciyar bacci, ba ga shi ba ita kaka har ta sauko ta zo tana nemanshi.” Suka Kara dariya.
Har sallar azahar kaka ta kasa sukuni da walwala Tafida ya tafi birni Kano ya kyaleta har a
sanda ta baro su Da’u a dazu da safiya tana bawa ranta ba inda Tafida ya tafi zai dawo ne, to amma rana tana dada ja zuwa farfe uku komai sai ya karye mata ta dinga jin da gasken Tafida ya yi tafiyarsa, har a sanda Nana ta shigo jan ruwan (sanwa) girki, kaka ke gaya mata yadda sukayin da Tafida, ta ce “Iyi yanzu saboda Allah Nana meye laifina da na matsa Tafida ya yi aure me ya rasa na rike aure duba dakunan ciki gidan nan.” Tana nuna dakuna biyu na cikin gidan, bayan nata da na Tafida, “Bai ishi Tafida ya zauna da mace ba, Tafida na da ‘yar sana’ ar yinsa ga gonar Tafida kin sani duk shekara ana bada abinda akai hayar ta, to me ya ragewa Tafida a rayuwa na karasa zama cikakken mutum amma Tafida ya sa wasa a al’amuransa.”
Nana kuwa tayi shiru tana son fahimto abinda ya farun, Kaka ta ce “Wai don a jiya nayi masa nunin haka shi ne yau tun ban farka ba ya yi ficewarsa, da nake bincikensa ma Nana sai na tadda Tafida ya bar gari kwata-kwata.”
Nana ta kallo kaka a tsorace da maganarta kaka ta girgiza kai cikin takaici tana amsa mata haka ne, ta ce “Amma babu komai shi kenan tunda ya zabi hakan ya je Allah ya bada sa’a, mahaifinsa ma ai duk da bana son tafiya birni a haka yake lallabani ya yi tafiyarsa wai shi ya tafi neman kudi ba gashi ba har a hakan a hanyar birnin Allah ya aiko mishi da karar kwana, yau ina ya ke? Amma Tafida bai lura.”
Nana ta dan katseta a hankali ta ce “Kaka kowa dama akwai dalilin barinsa duniya ki daina bawa ranki a haka dama shi can marigayin baba hakan ne hanyar tafiyarsa.”
Kaka bata kula ba ta ci gaba “Burin rayuwar
Tafida kenan ya tafi birni neman sana’a ya yi kasuwanci, ki duba Nana duk sa’o’in Tafida akwai me dan abin da Tafida ke da shi wanda mahaifinsa ya bar masa, yana da rumfarshi a kasuwa ta sa ce ta mahaifinsa kuma ba laifi duk ran kasuwa ana dan samu ga gonarsa duk da kwara guda ce itama idan anyi hayar ta duka shekara ana dan samu, to me ya rage masa.”
Tana kallon Nana.
Nanar kuwa tayi tsugune ta takure tai shiru tana ji itanma daga kallo abin ya tsumata, kaka ta ce
“Tafida na da zuciyar nema kuma alamunsa na nuna yana da zuciyar rike iyali, sai dai zuciyar mai da hankali na ajiye iyalin ne kawai babu.” Ta fadi hakan a raunane don yadda ta fadadin har kwalla ta ciko a idonta tasa gefen zaninta ta shafe.
Nana ta sake matsowa cikin jimami ta ce “Kaka ba haka za ki yi ba idan ma tafiyar ya yi kawai addu’a za ki Allah ya waiwayo da shi ya dawo da wuri, don shima nasan ko da ya tafin bai jimawa hankalinsa zaiyo ya dawo din.”
Kaka ta ce “Babu irin yadda banyi da Tafida yaje a yi baikon su da Dubu ba ya kiya wai shi sai ya gama taron aure yadda da an sa lokaci kadan za a kai musu a yi biki babu dadewa, to a hakan da yake fada ya lallaba ni don nima naga kyautawar haka, amma har yanzun da nake miki magana Tafida bai taba kawo ko gyauto (fallen zani) ya ce a ajiye da sunan taron auren sa ba, ke Karuma jiya zuwa yayi yacemin wai shi zai hakura da Dubu damma yanzu sun Sata.”
Nana ta sake zaro ido tace “Duk son da Dubu ke yiva Tafida. Kaka ta ce “Gane min hanya… makaho ya so tsegumi, to shine jiyan daga haka yau ya wuceya bar gari ai shi kenan. Nana tashi ki ja ruwanki kada kiyi daren tuwo.”
Nana ta mike a sanyaye tana cewa “Amma kaka kada ki saka abin sosai a ranki nasan duk inda Tafida ya tafi ba zai jima ba zai davo.”
Har Nana ta shiga gidansu tana jimamin wai
Tafida ya bar gari, amma ko Innarsu bata yiwa zancen ba bayan da ta ciccikawa Kaka ko ina, amma duk bayan hakan shigowar ta biyu itama kakan na lura da itan duk ta kasa sukuni, ta dinga jin ko banza ta samu mai tayata jimamin tafiyar Tafida, duk da bata son fitowa sosai ta nuna abin.
Ko da magariba ma sai ga Nana ta sake shigowa don da kanta ta kawowa kaka tuwon gidansu, amma bayan sallar isha’i da kadan sai ga Tafida kamar wucewar hanya ya shigo da ‘yar sallama kadan don fuskarsa dake haden ya bankada kofar dakinsa ya shiga, kaka da ta yi shimfida daga kofar tata dakin ta saki baki galala tana kallonsa har sanda ya shige din zuwa can ta yunkura ta shuri takalmanta sai gidansu Nana, ta saka Kanin nana ya nemo mata Babansu Malam Mado.
Tafida na cikin dakinsa ya vi sallama ya shiga ya ce wai yaje in ji babansu, don har Tafidan yana tambayarsa ya ce yana cikin gidan ya fita ya barshi, amma ko da Tafida ya shiga tsakar gidansu Nana ya riske kaka a ciki ya san kwanan zancen tana zaune bisa tabarma da Innar su Nana ta shimfida mata yayin da Malam. Mado (baban su Nana) yana zaune kan ‘yar tsuguno (kujera) shima a hankali Tafidan ya raba ya zauna.
Malam Mado ya shiga yi masa fada da abinda ya ji daga bakin kaka ya ce “Haba Tafida da hankalinka ace ka bar gida tun da duku-duku sai
Hmmm