RIKICIN WANI GIDA CHAPTER 11

  • RIKICIN WANI GIDA






  • CHAPTER 11



  • Ture Suraj yayi tare da zuwa ya dauko rigarsa ya nufi sassan su, duk suka bishi da kallo, Tsoho ya kalli Samirtare da miqa mai wayarsa yace kiramin Dr Munnir, hannu na rawa Samir yayi dialling no din, ringing daya ya dauka ya miqa ma tsoho, Allah ya qara ma tsoho tsawon rai, Dr muna lpy? Ya amsa, yauwa dan Allah kazo ka duba min yaran nan, yace toh gani nan zuwa, Tsoho yace kowa ya tafi sashensa. Zayyad ya kama suraj ya kaishi dakin Ama, aka watse. Ba ajima ba Dr yazo, ya duba Suraj, ya bashi pain reliver Tsoho yace aje a duba Jawad, ko da Dr yaje sashen hajia Babba korarsa tayi tace basa buqatar likita munufukan banza.. Har kwana 2 shiru kakeji, kowa yayi zaton Tsoho zaiyi magana akan fadan shekaranjiya qala bece ma kowa ba, kamar baayi ba, Be qullaci kowa ba, ko da Zaid yazo gaisheshi be nuna mai komai ba faramfaram, yana mai wasan kaka da jika, har suna sa ran Tsoho zai masu magana amma be ce komai ba.
  • Hajia Babba ji take da Zaid, duk cikin jlkoki tafi yi dashi, amma gurza mata yakeyi, mamanshi Abida ma tafl sonsa.
  • Lamarin Gidan ya qara tuburewa sabon Gaba ya qara qulluwa, Samarin Gidan kuwa zumuncin su ya baci, dama suke zumunci a gidan amma tin bayan fadan nan ba me cewa dan uwansa qala, Gaba me qarfi suka dauka da junansu. Duk wa’annan abubuwan da suke Tsoho na sane da su. Ya samu su ldo, yana tunanin shikuma haka Qaddararsa take? Gaban da Iyalansa keyi na matuqar damunsa. Amma Insha Allah komi yazo qarshe, yasan abinyi..
  • Haka ne bigbrosamir abubuwan gidan nan ya rinchabe, kowa gaba yakeyi, ni ba abunda ya damen da gaba kowa nawa ne, yace shiya sa kike burgeni ba ruwan ki da ‘yan ubanci,tace kaima ai haka bigbrosamir shisa nake sonka, yayi daria, yanzu ka fada min wannan shigar zai burge Yazayd? Samir yace sis na flso ki bar mgnr Zaid, tayi rau rau da fuska zatayi kuka, ba zan mishi ba ko yasamir? Ba zaiso ni ba? Duk ta bashi tausayi don yasan ta na son zaid, yace kar ki damu zai soki, bana so kikai kanki ne, na fiso yazo gunki tace toh shkn bigbrosamir, zan kama kaina.
  • Ta shigo Gidan da motarta, Taci gayu sosai, ta flto ta na taku daidai, fitowar Amira daga sassan Umma hajja kenan taga baquwar fuska, Amirah ta nufeta da murmushi sannu da zuwa, Badiyya tace yauwa, Amirah tace gun Hajja Ama kika zo k0 umma Hajja? Badiyya tayi far da ido, ko daya, gun Zaid nazo da fatan yana nan, Nan da nan fuskarAmira tayi dif, tace bashi kike binshi ko tara? Diyya tayi dan murmushi yan dunia tace k0 daya naxo ansar zuciyata ne da ya sace min, da fatan kinsan inda ya ajiye shi, in ran amira yayi dubu ya baci, tace ke shegia yeriska me bin maza har gidansu, ki bar gurin nan ko wlh na miki tunbur kuma na lakada miki dan banzan duka Badiyya tayi daria, ke yarinya, kinsan dai ni ba tsarar ki bace ko?A banza zan baki shekaru 5 ko 6, zan miki uzuri daya dan naga kina kama da myzayd, nd kamar kina hauka da sai kinyi nadamar furucin nan, Amirah tace na rantse da Allah ina iyawa, idan kin san mutuncin kanki ki bar gidan nan ynz, in ko ba haka ba, zaki ga Haukana don mugun bugu zan miki, na kareraya ki, na kaiki asibiti na kuma yi jinyarki, Daria sosai badiyya keyi, Amira ta kwnace dankwali au daria ma na baki k0? Tayi dammara, daidai nan Maysah ya qaraso gun da gudu ta sha gaban Amira, Haba Amira me ya hadaki da baquwa? Wannan er iskarzata shigo mana gida tai mana karuwanci, wai her Zaid, k0 uban wa yabata yazaid din, haba Amira kiyi hqr mana, ke dalla matsa matsoraciya, tsayuwar iriin wannan cikin gidan nan balaee ne, Ji gashin doki,ji man kanti ji matsatsun kaya, wlh kamarjikar bokan tudun qarfe, ai wlh sai ta bar gidan nan ynz ba anjima ba, kafln Allah ya jarrabe mu da Kwarantsa cikin Gida, Maysah tace haba Amira, ita ko diyya daria kawai take,
  • Maysah ta juya ta kalli diyyah haka kurum taji gabanta ya fadi, ko me ya sata faduwal Gaba oho? Ta dai daure tace baiwar Allah kiyi haquri dan Allah, yazayd kike nema? Bari a dubo maki shi, ta ja hannun Amira, daga nesa suka hango Yazayd din na jogging. ita k0 badiyya ta qarasa gun shi, shikuma ya daga ta sama suka rungumejuna, Haka kurum Maysah taji gabanta ya tsananta bugawa, Amira kuwa baki ta bude galala, kaiii Rumguma? Tsanar Yazayd da karuwa(sunan da ta samata)ya shigeta, meye haka, agabansu suke iskanci? Bata ga komai ba sai da taji badiyya nacewa haba Zayd kai da kace zaka nemeni har kwana 5 shiru? Nayi missing dinka, ina tunanin ko ka mance ni? Cikin sigar lallashi yace so sorry my diyyah, wlh i was busy ne, har yau ban siya sim ba shisa ban nemeki ba, but its a good thing u came over, i’m glad to see u, ya akayi kika gane gidan? Ta mai far da ido, kasan familyn Zailani ba boyayye bane,yace haka ne, Sai sannan Zaid ya lura da Meerah da ke tsaye wata a gefenta ba tare da ya kalli Maysah ba, ya kalli Amira yace ke ya ma sunanki?? Amirah ta watsa mai wani mugun harara, Badiyya tace kai honeybunch ur sis is hilarious, ya danyi gyatsine yace haka take bata da hankali, ya qara kallon Amira yace Zo ki kai Badiyya gurin Hajia Babba kice mata baquwa tace, Badiyya tace Oh no dear, ba yau ba, i jus came to check on u, but next time musamman zanzo gaida Inlaw’s na, yayi dariarjin dadi yace yauwa sweety, ya ja hannunta ya rakata har mota, Amirah da Maysa suka bisu da ido, Maysah na tir da wannan hali nasu, Ameerah kuwa takaici da baqin ciki kamartayi kuka, Maysah ta ja hannunta ta fizge tayi dakin Yasamir Na ganinta ya miqe tsaye yace lllsismeerah menene waya tabaki? Ta na huci, bigbrosamir daman Yazayd dan iska ne? Ynz wata tazo gidan nan nemanshi kaga yanda ya rungumeta? Ta kwashe komai ta gaya mai, Samir yace toufa, shima Zaid da rigima yake, yasandai ba wanda zai aura mishi bare, kar ki damu kece matarshi, na auri wannan? Allah shi kyauta na aureshi, kai kaga abunda sukeyi? Ai wlh bazan aureshi ba, shi gashi wayayye. Yayi karatu turai ya zama chris tucker, toh wayewa ma ya ci ubanshi, Samir daria ya fara, is it funny bigbrosamir? Ni ynz wa zai aureni? Kowannen ku is in lov? Kuma ni ba zan auri daniska ba wlh, kar kuma Tsoho yace zai zaban mun daga cikin yayyinmu wanda sukayi aure. Shidai Samir har yagaji da surutan Amira,ya daiyi shiru yana jinta, wani Lokaci tabashi daria wani Lokaci ta bashi takaici, shidai yace Allah ya shirya Amira.Hajia Babba, Hajia Ama da Umma Hajja zaune a parlor, Tsoho ya kalli Ama yace Aishalle me ya faru sati 2 da suka wuce? Aishalle tayi murmushi don ta san ko ba dade ko ba jima sai yayi maganar, nan ta kwashe komai ta fadi mai tun daga shigowan su Hanifa har fadan, Tsoho ya jinjina kai, Charaf hajia babba ta chafe, baka da Iabarin rashin ta idon da Fadlla ta ma Jawad, rashin kunya da zage zage, amma be ko kalleta ba balle ya duketa, toh shi suraj ya hade bilkin da hanifan ya zane. shi ko zaid yazo ya lakada mai najaki ai dan’uwa befi danuwa ba. Tsoho yace shikenan, Allah shi kyauta, ku tashi ku tafl, ya kalli Umma hajja, yace ki turo mun Hassan Hussaini da Gambo tace to Mallam hajia babba ta buga tsoki, M.Zailani ya gyada kai Allah ka shirya. Baba Hassan, B.Hussaini da B.Gambo zaune a kasa kan carpet, Tsoho yace toh kunji hukuncin da na yanke ya kuka gani? Baba hussaini ya nisa yace anya Baba wannan abu xai yiwu, kasan gaban nan me qarfl ne tun kafin a haife mu akeyinshi, sai nake ganin kamar wuta za a qara ma lamarin, tunda duk basu jituwa bare, maganin kar a fara kar ayi, Baba Hassan ya girgiza kai yace aa ina ga hakan ne maslaha a cikin wannan gaban, dole muke kawo qarshen wannan Gaban kuma inaga wannan ce hanyar da zai sa a samu sulhu, So ina ga Baba hakan daidai ne, Baba Gambo yace Hakan daidai ne kuwa baba, sai dai a roqa Allah ya daidaita tsakanin mu duka, M.Zailani yace Hussaini ka fahimci abun da Yayanka yace? Baba Hussaini ya gyada kai, yace wannan gaskia ne, daman bawai naqi bane ina gani kamar ba za a daidaita bane, baba hassan yace always pray for d best broda. Yace toh Allah ya sa mu ga da kyau. M.Zailani yace toh shkn tunda har kun amince da Raayina. Hakan zaayi (ni nace me zaayi tsoho? Harara ya wurgo ni da ita) Maysah da Tsoho suna zagaya gida, ya na bata Iabarin Soyayyar shi da Aishalle, tana ta daria yace muje mu kaima yayanki ziyara, Tace wanne daga ciki? Yace muje dai, rabon da Tsoho yazo bangaren samari Har mantuwa ta manta, kai tsaye dakin farko ya qwanqwasa ya shiga, Zayd ne kwance da fara singileti ba bacci yakeyi ba amma daga ganinshi buge yake, ga kwalbar giya ta Gulder da Star ya shanye, Gefenshi Diyya ce kwance tana bacci, Tsoho flrgici Maysah flrgici, tsaf tagane wanda tayi fada da amira ce shekaran jiya, lallai Abun yazayd ya girmama, har gadon baccinshi yake kawota, Allah ya shirya! A hankali Tsoho yace Giyah? Ga mace Kwance a cikin Gidana? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Zayd ya miqe duk da ya dan tsorata amma da yake dan dunia ne yace me ran qarfe lafia ka shigo Sassan mu? K0 nema na kakeyi? Tsoho ya share yace ziyara kawai na kawo ma, Amma bari muje yace komai Maysah ta riga tsoho,jikinta rawa yakeyi, har suka koma Sassan tsoho basu tanka wa Juna ba, Duk Zuri’ata Zaidu kaine Daban Allah ya shiryaka Dole na muku Aure. dole nake aurar daku Ya Allah kai mana da kyau.
  • Fadlla da Suraj a dakin hajia Ama suna Soyewa, tana zuba mai shagwaba Wai gaskia ba zai tafi kano week din nan ba, yace baby kiyi hqr so kike a koreni a wajen aiki? Tace ba sai a maka transfer ba? Yace ina kike so mu zauna idan munyi aure? Ta daga kai sama tana tunani tace Kaduna, yace daman tunanin mu daya, kar ki damu da hannuna na zana gida a kaduna her an fara gini fadila tayi ihun murna tace thank u mysuraj, Sarkin Gida neya shigo da Sallama yace Tsoho na kiran ku, suraj yace mu suwa? Yace dukkan ku na cikin dakin nan, har da Hajia Ama, taro ne na gaggawa, suraj yace toufa Allah ya sa lapya, fadila gaya ma su hajia a ciki da su lslah, aka sanar dasu duka. Kowa ya Hallara abun mamaki harda yayyinsu da matansu da sukayi aure na nesa ne kawai babu to lapya inji Islah?duk suka zazzauna, One by One tsoho ke kallonsu, daga matayensa zuwa yaransa zuwa jikoki harda masu musu Abincin GANDU, Tsoho ya gyara Murya Ina Zaidu?? Jawad yayi qarfln halin cewa yana Dakih, be ji aikena bane? Jawad ya miqe bari na kirashi, yace kai Jawad Zauna, Ya kalli inda mata suke yace RUMAH jeki kira yayanki Zaid, gabanta ya fadi haka ta
  • miqe tayi Sassan Samari, ta kusa minti 5 tana tunannin yanda zata shiga dakin, sai tayi jihadin Sallama da qarflh, futowanshi wanka kenan, daga shi sai towel, yace waye? Shigo, ta shiga saurin rintse ido tayi, ya daure fuska ke Lapya? Uban me ya kawo ki dakinah? Tace kayi haquri, Tsoho ke kiranka, kowa na chan kai kadai akejirah, tana kai wa nan tayi saurin flta yayi dan jimm tabbas ya san meeting din nan nashi ne, ya dan flrgita amma dayake namijin dunia ne ya dake ya zira jallabiyansa yayi cikin gida da takunsa. Ya shiga wakeken parlom da Sallama, Gabanshi ya fadi ganin idanuwa akansa, duk ya tsargu ya sha jinin jikinsa, kusa da Jawad ya zauna.
  • Tsoho yayi Bismillah tare da guntun
  •  muqqadima da sallama duk aka amsa mai, ya fara cikin maganarsa ta manya :Ahh, batare da bata lokaci ba, kamaryadda kuka sani a wannan Zuriah tawa, idan Namiji ya fara aiki, Mace ta gama sakandire ana masu aure, kuma ni ke zaban musu mataye da mazaje, kuma DOLE abi umarni nah, kasancewar ina da Zuriah da yawa nake
  •  hada aure uku uku, ko hudu hudu wata sain har biyar biyar, wannan abu ne da kuka sani ba sai na dinga nanata shi ba a duk lokacin da zanyi hadi, Bana aurar da Mutane 12, maza 6 mata 6, gaban Masoyan nan 12 yabada RINGIM, fargaba ya shiga zuciyoyinsu, kunsan dai duk maganar da na yanke ta zauna, k0 da yake ban yi tsammanin musu daga daya daga cikinku ba don na san kunsan Qaidojin Gidan nan, ba a soyayyah ko auren bare, wacce ko wanda M.Zailani ya zaba shine magana. Gabansu ya sake yankewa ya fadi Tsoho ya cigaba da jawabi, Toh na riga nayi tsarina kamar haka ;ZAYYAD na baka HANIFA, SAMIR na baka AMIRAH SURAJ na baka BILKISU MU’AMMAR na baka ISLAHULKHAIR, JAWAD na baka FADILA. ZAYD na baka RUMAISAH. Tashin hankali, Firgici, Rudani, Kurumta, Makanta, Bebanci ya dirar ma Masoyan nan 12lokaci Guda basa gane komai ba sajin komai basa fahimtar komai ba kuma sa ganin komai…
  • Shin wannan Hadin Zaiyiwu? 
  • Shin Wannan Gaba zata tsaya kuwa? 
  • Shin Akwai Sulhu tsakanin yan Dakin Hajia babba, da Dakin Ama da na kuma Umma Hajja? This is just the Beginning

  • ACigaba?‘.’ 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *