RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

JIYA MUN TSAYA 

Yan sandan sun so su raba shi da gawar, Abban ya dakatar da su, “Ku bar shi ya rage radadin da ke damunsa, tun dazu yake mana magiyar mu je mu dauko ta ashe mutuwa za ta yi .” Kwalla ta ziruro masa daga idanunsa, ya girgiza kai kawai. A dai-dai lokacin kiran Hajiya Salma ta shigo wayarsa. Ya ji duk ya tsaneta. Ya tabbata duk namijin da ya ce zai biye wa shawarar wata macen sai ta kaishi ta baro. Dauka ya yi ya sa a kunne yana magana cikin rawar murya, “Baiwar Allan da take miko hannu take bukatar taimako kika hana, saboda dalilin kin tsani zina, kin tsani mai dauke da cuta, kin tsani wacce ta tuba ta koma addininki. Wadanda suka fi ki tsanar wadannan abubuwan sun kashe ta sun kawar da ita daga duniyar gaba daya.” Sauke 

ZAMU TASHI

 wayar ya yi, tare da kasha ta, yana jin danasanin biye wa matarsa. 

Kallon likitan ya yi yana_ sauraren maganarsa. “Yallabai ina tunanin idan aka yi gaggawa zamu iya ceto abinda ke cikinta, ta hanyar yi mata aikin gaggawa.” Gabadaya aka yi amanna da bayanan likitan. Sultan yana rike da ita yana sharar hawaye, rigarsa duk jini gani yake kamar za ta tashi. Abbansa ya zame hannayensa bisa gawar saudat. Yana kallo aka sata a mota. “Ruwa! Ruwa!!” Sautin muryarta, ya dake shi.

Kufe idanunsa ya yi domin ya baiwa hawayensa daman sauka. “Ku taimakeni ku raba ni da nan, za a kashe ni. Ku taimake ni ina son abinda ke cikina.” Kalamanta suna yi masa kuuwa da Karfi. Shiru ya yi yana duban su Abbansa. Ganin ba ya kallonsa ya shige Karkashin motar nan ya jawo buhun yana bincike a ciki, Ya ci karo da littafi Kato, dauke da hotuna wanda bai tsaya duba komai ba, ya mayar cikin nigarsa. Muryar Abba ya ji yana Kwala masa kira, ya yi sauri ya fito. Ya kama hanyar shiga motar hawaye suka sake Www.bankinhausanovels.com.ng tsinke masa. Yana goge wasu, wasu kuma suna sake kwaranya. 

Sun kama hanya, muryar Saudat ta ci gaba da yi masa kuuwa, “Zan gaya maka wani abu.” Sultan yasa hannu ya toshe kunnuwansa da Karfi. “Abba…” Ya ja sunan mahaifinsa da Karfi tare da fashewa da kuka. Abba ya cika da al’ajabin irin kukan da Sultan yake yi, domin har kiransa ake yi mai taurin zuciya. An sha a yi mutuwa kowa na kuka, amma idanunsa ko gezau baya yi. Abba da ya gama karya hanya yasa hannunsa daya ya jawo shi jikinsa. “Abba tana ta kirana da hannu, amma kuka rabani da ita, tana son ta min maganar da kowa ya kasa sauraronta, amma baku ji tausayinta ba, kuka hanani sauraronta. Ban san me take son gaya min ba. Me yasa Abba?”Shi kansa hawayen danasanin ne kwance a idanunsa. Bai san me yasa mutuwar Saudat ya tsaya masa a rai ba. Bai taba kawowa zai taba shiga irin wannan damuwar ba. “Kayi hakuri Sultan, Allah ya riga ya aiko bamu isa mu kaucewa Kaddarar mutuwarta ba. Kayi shiru ka daina kukan haka. Kukanka yana karyar min da www.bankinhausanovels.com.ng zuciya. Ta fi buKatar addu’arka fiye da wannan kukan” Shi dai Sultan saurarensa yake ba don yana fahimtarsa ba. Kwanciyarsa ya yi a jikin mahaifinsa yana faman sauke ajiyar zuciya. Wannan karon duk sonsa da kallon titi, bai kalla ba, domin zuciyarsa a Kuntace take, ta yadda komai ba ya yi masa dadi. Kai tsaye aka iso da gawar (GIWA HOSPITOL) Asibitin da ake matuKar ji da shi a garin na Kaduna. Cikin gaggawa aka karbe ta tare da shirye-shiryen shiga da ita aiki. Su Abba suna nan tsaye aka wuce da ita, don hakane suka yi ta kaiwa da komowa. Tun suna sa ran fitowarsu har suka gaji suka koma gefe guda. Hajiya Salma kuwa duk da jikinta ya yi dan sanyi da mutuwar Saudat sai da ta tsinci bakinta da cewa, “An rage mugun iri. Da haka ake bin mazinatan nan, ana kashewa da masifu sun yi mana sauki.” Ita damuwarta danta da mijinta su dawo gida, Agogon yana buga sha biyu dai-dai na wannan dare, aka fito da yara biyu a nannade cikin zani. Daga ‘yan sandan har zuwa Sultan an rasa wanda ya riga wani isowa gun yaran.. Www.bankinhausanovels.com.ng  Mikawa Abba yaran ta yi_, tana murmushi, “An ciro mace da namiji a cikin mahaifiyarsu. Sai dai yanzu za mu mayar da su, saboda yunwa ta fara lalata masu jiki. Ya yi wani irin yanayana alamun dai yunwa ce, don haka yanzu za a ci gaba da basu taimakon gaggawa. Sultan dai bai karbe su ba, amma kuma yana tsaye yana kallonsu daga hannun mahaifinsa. Doctor din ya Karaso ya ce yana son ganin Abba a office dinsa. Suna isowa ya dubi Abba ya ce, “Alhaji za a mayar da yaran domin kulawa da lafiyarsu , za kuma a bar mana ‘yan sanda a nan saboda kada mutanen da suka kasheta su sake dawowa kan yaran. Ita kuma idan Allah ya kaimu gobe sai mu bayar da gawarta. Allah ya jikanta ya raya marayun da ta bari.”Sultan da ke zaune ya hada kai da guiwa ya sharce hawayensa yana jin Kaunar da yake yi wa Saudat tana dawowa kan ‘ya’yanta, Yana ji a ransa Zai iya cikawa Saudat alKawarinta, ko da kuwa wannan shi ne aiki na Karshe da zai yi a duniya. Sai dai tarin damuwar rashin matar da a lokaci daya ta shiga ransa, ya kasa yunkurin barinsa ko taba yaran ya yi. “Me ya sa kuka yi www.bankinhausanovels.com.ng gaggawar kashe ta? Me ta yi maku? Anti Saudat! Me za ki gaya min? Me yasa Umma ta hana ni saurarenki? Wasu hawaye suka shiga kwararowa daga idanunsa. Sosai yake shessheKa. Mahaifinsa ya kamo shi suka nufi mota. Sai da ‘yan sandan nan suka raka Alhaji Lukman har gida kafin suka koma. A falo suka ci karo da Hajiya Salma. A cikin Kwayar idanunsu ta karanci saKonni kalakala da kai tsaye yake mata nuni da haushinta suke ji. Kawar da kanta ta yi kamar bata san suna yi ba. Sultan kuwa zama ya yi a Kasa idanunsa sun ki daina zubar da hawaye. Barci ke fizgarsa, dole ya wuce dakinsa ya yi wanka ya cire kayan da jini suka bata masa. Zoben nan da littafi da hotuna kuwa, ko kallonsu bai yi ba, ya cusa a cikin wani akwatinsa ya mayar ya rufe. Jallabryarsa ce a jikinsa har barci ya kwashe shi a nan, ba tare da ya tuna da addu’a ba. Alhaji Lukman ya mike da nufin duba dansa, cikin rashin sa’a idanunsa ya hadu da na – Hajtya Salma. Dukkansu suka dauke kansu. Dakin Sultan ya shiga ya gyara masa kwanctyarsa tare da addu’a ya tofa masa. Ya www.bankinhausanovels.com.ng  fito ya jawo masa Kofa. A falon ya sameta, zai wuce ta sha gabansa. “Me hakan ke nufi?” Harara ya sakar mata, “Abinda zuciyarki ta gaya maki.” Shiru ta danyi tana nazarin inda kalamansa suka nufa. “Kana nufin akan wata za ka juya min baya?” “Eh idan har ta kasance abar halitta ce, kamarki zan yi abinda ya fi haka.” Zamewa ya yi zai wuce sai kuma ya juyo, “Ki shirya zaman yaran da aka ciro daga cikin mazinaciya, ki shirya renon yaran da aka ciro daga jikin mai dauke da ciwon nan da ke karya garkuwar jiki. Haka ki shirya zama inuwa daya da yaran da uwarsu ta aro addininki kike yi mata gori.” Kafin ta dawo daga doguwar sumar da ta yi, har ya shige dakinsa. Bata bishi ba, ta tsaya a falo tana faman kaiwa da komowa, “Wallahi! Babu wanda ya isa ya kawo min dan shege gida in rene shi. Ashe Alhaji ya dibo tashin hankalin da bana jin sauke shi zai yi masa sauki. Lallai a tsawon shekaru goma sha takwas da muka yi a tare, bai taba sanin wace ce, Salma ba, amma daga yau zan fito masa da asalin kalata.” Dakin www.bankinhausanovels.com.ng  ta shiga. A kishingide ta same shi, yana karanta labarai a cikin wayarsa. “Ina son magana da kai.” Hajiya Salma ta yi maganar cikin shan mur da nuna masa da gaske take, kuma tana nan akan bakanta. . “Kunne ke ji.” Ya bata amsa ba tare da ya dago ya dubi inda take ba. Ta gyara tsayuwarta ta sake cika ta yi tam! Ta ce, “Kada ka dauko masifa da hannayenka ka kawo cikin gidanka, kayi tunanin zaman lafiya.” Har yanzu bai dago ba kuma bashi da alamun dagowar. Ya ce, “Namiji ke da iko da gidansa, -shi ya sa aka halatta mana, mu je gidajenku neman aurenku, mu bada sadaki. Daga nan mu dauki nauyin ci da shan ku. Idan kuwa .har za ki iya shimfida doka a gidan mutumin da ke da ikon daga Kafafunsa ki shiga Aljannah, ina ganin da tuni an halatta maku ikon aurenmu, da kuma ikon mika sadaki.” “Duk maganar da ka gadama ka gaya min a kan matar da baka sani ba. Amma sai ka fara gaya min wacce waina kake tunanin za a toya a www.bankinhausanovels.com.ng cikin gidan da ke dauke da shegu marasa addini?” Sai yanzu ya dago kai yana dubanta fuskarsa dauke da murmushin da ke nuni da murmushin takaici yake yi. Ya ce “Wainar Kasa za a toya. Dagowa ta yi a fusace ta ce’ Sanin kanka ne wainar Kasa ba za ta taba ciwuwa ba.” Tashi ya yi da wayarsa a hannu zai bar dakin, dai-dai saitinta ya tsaya yana yi mata duban kin bani mamaki, sannan ya _ ce, “Kin san ba zai ciwu ba kuma kike’ son ci? Kamar yadda kike tunanin wainar Kasa ba za ta ciwu ba, haka kema tsarin da kike son shimfidawa a gidan da ba mallakinki ba, ba abu bane mai yuwuwa ba. Don haka ki gyara wannan kuskuren da kike KoKarin tafkawa idan bahaka ba, zan auro wacce za ta iya tsayawa ta yi min rainon marayun nan, ta inganta min rayuwarsu, Kila a dalilin taimakon nan da zan yi inshiga Aljannah. Kada ki sake biyo ni idan ba haka ba, zanyi mummunar saba maki.” Ya sa kai ya fice abinsa. Hajiya Salma da wani irin kishi ya cika mata zuciya, ta durkushe Kasa tana kuka. Haushin Sultan yafi yawa a zuciyarta, da bai www.bankinhausanovels.com.ng kawo masu masifar nan ba, da babu abinda zai Sanyata sa’insa da mijin da take matuKar so kamar ta kashe kanta. Mutumin da ya ce baya sha’awar aure yau shi yake fadin zai Karo mata kishiya? Ita kuwa da ya Karo wata mace a gidan nan da sunan aure gara mala’ikan daukar rai yazo ya dauki ranta tun kafin zuwar ranar. Ta rasa menene mafita? Allah-Allah take yi gari ya waye, ta kira Yayanta Alhaji Mu’azu, domin shi kadai ya isa ya gayawa mijinta ya Ji. A wannan dare Alhaji Lukman ya kasa barci, sai juyi yake yana tunanin ta hanyar da ya kamata ya biyowa matarsa. Ya tsani abinda zai ° kawo masu rashin jituwa a_ tsakanin su. Washegari da sassafe ya wuce Asibitin, ya bada * kudi aka yi wa yaran siyayya, daga can yasa aka daukota akayi mata Sallah a Masallaci aka kaita gidanta na gaskiya. Alhaji Lukman ya kira Kanwarsa ya nemi taimakonta, Anti lyami, ita ta tsaya akan yaran har aka basu sallama suka kwaso zuwa gida. A lokacin Sultan ya dawo daga Makaranta dama kuma tun da ya tashi gaisuwa ce kawai ta hada shi da mahaifiyarsa, www.bankinhausanovels.com.ng haka yanzu din ma, gaishe ta ya yi ya nufi hanyar ficewa. Hannunsa ta jawo tana dubansa, “Yanzu Sultan akan bare kake fushi da ni? Insha wahala akanka amma yau da ni kake fushi? Kana son ka gama da duniyar nan lafiya kuwa? Abbanka ya yi min kaima kayi min?” Jikin Sultan ya danyi sanyi, don haka ya bata hakuri kansa a Kasa, sannan ya wuce. Duk da haka dai yaki sakewa. Jin Sallamarsu yasa Sultan dawowa da baya ya kafe mahaifinsa da ~ idanu, haka ya kasa murnar ganin jariran kamar yadda kowa ya za ta. Anti Iyami ta zauna tana gaban mahaifinsa yana gaida shi. Abban ya mika masa da namijin ya ce, “Sultan ga amanar da ka dauka. Wadannan ‘ya’yan ka dauka cewa ‘ya’yanka ne. Namijin Nawfal, macen kuma Nasreen. Ina fatan ka san ma’anar Nasreen?” Sultan ya daga masa kai ba tare da ya iya furta komai ba, haka kuma bai da alamun karbar yaron, kamar yadda mahaifinsa ya buKata. Anti Iyami ta mike tana murmushi, ta ajiye masa Nasreen a jikinsa, wacce take ta faman tsotson www.bankinhausanovels.com.ng  hannu. Karbarta ya yi ya tsura mata idanunsa, yana son dole sai ya Kare mata kallo. Yarinyar bata da auki, amma kuma sambaleliyar mace ce. Yatsun Kafafunta ya kafe da ido gabansa yana fadi da Karfin gaske. Amma kuma ya rasa dalilin irin wannan faduwar gaban. A hankali ya yi magana wanda kaf falon babu wanda baiji ba, “Allah ya rayaku. Allah yasa ku yi wa addinin musulunci hidima.” Sau tari Abba yana mamakin irin iya tsara magana da Sultan yake yi, wanda ko babba sai hakan. Hafsat da Haidar suka Karaso suna leKen yaran. Sai kuma suka dago suna duban Sultan, “Yaya Sultan Umma ce ta haife su?” Hajiya Salma da dama jira take yi ta mike tsalam jikinta har kyarma yake yi. “In ji uban wa? Allah ka raba zuri’ata da haihuwar kwararo haihuwar titi, haihuwar KarKashin babbar mota! Wadannan yaran da kuke gani, shegune ake neman liKa mana tsiya.’ Abba ya mike jikinsa yana kyarma ya ajiye Nawfal ya daga hannu da nufin zabga mata mari, sai kuma ya dakata sakamakon muryar Sultan da ya ji ya ce, “A’a Abba!” Www.bankinhausanovels.com.ng  Hajiya Salma ta ware manyan idanunta tace, “What! Alhaji ni za ka mara a kan ‘ya’yan arna? Ni za ka mara akan ‘ya’yan ‘shegu?  TirKashi! Tun yanzu kenan suna cikin tsumma, ina kuma ga sun girma? Don Allah zo ka mare ni kada ka fasa. Kai kuma Sultan! Daga yau ka dauka cewa ni ba mahaifiyarka ba ce, ka je gun ubanka dake daure maka gindi ni na cire ka daga jerin ‘ya’yana.” . Ta sa hannu ta finciko Haidar da Hafsat, ta ce, “Daga yau su Hafsa sune jinina ba kai ba Sultan. Na yafewa duniya kai. Yaran nan kuma sai sun koma inda suka fito indai ni ce Ummu Salma!” Yaron ya zuba mata idanu kawai ba tare da ya iya furta komai ba. Haka bata ga ko alamun razana daga idanunsa ba. Abba ya dube ta jikinsa a sanyaye, domin baya son Salma tana yiwa ‘ya’yanta baki. “Salma… Ki dauka cewa. Nasreen RUBUTACCIYA ce daga Allah. Haka Nawfal RUBUTACCE ne daga Allah. Tunda Allah ya rubuta za su fito daga cikin matacciya kuma a raye, bana jin ke Karamar alhaki zaki iya yi masu www.bankinhausanovels.com.ng  abinda ba Allah ne ya rubuta ba. Sultan tashi mu je ciki.” Iyami ta mike tana yiwa Salma kallon mamaki, amma ko a jikinta. Tare suka shige, Iyami ta yi masu wanka, ta sauya masu kaya, sannan ta dauko madarar su mai dauke da sinadare ta basu suka sha sosai. Sultan dai kafe yaran ya yi da ido, ya rasa mai ke masa dadi. Ji yake kamar bashi bane wani Sultan din aka aro. A zuciyarsa ya maimaita, RUBUTACCIYYA. Hakika mahaifinsa ya yi gaskiya. Anti Iyami ta koma gida ta bar Sultan da yaran. Dole ya naimi taimakon Mairo mai aikinsu, don haka ne take taya shi kula da yaran. Hajiya Salma ce da Alhaji Mu’azzam_ babban wansu. wanda shi yake matsayin kamar mahaifinta, tunda shi ya raineta tun suna Kanana. – Malami ne sosai, haka bai taba sa doka ankarya masa dokarsa ba. Kusan halayyarsa guda da hajiya Salma, gashi dai yana da sani a addini sosail, amma kowa yasan mutum ne mai akida. Kowa tsoronsa yake ji. Www.bankinhausanovels.com.ng Alhaji Mu’azzam ya dubi Alhaji Lukman ya ce, “Wai da gaske ka kawo ‘ya’yan shegu cikin gidanka?” Alhaji Lukman ya hada rai sosai, “Na kawo marayu gidana, ba ‘ya’yan shegu ba ne. Ina kuma roKonka da kayi amfani da sanin da Allah ya yi maka, kayi adalci. Ya zama dole ko kare na kawo gidana Hajiya ta girmama min. Bai kamata ina fada tana fada ba.” Alhaji Mu’azzam ya mike yana dubansa, “Gaskiya na raina wayonka Alhaji Lukman, da girmanka da darajarka a idon duniya za ka je ka kawowa kanka masifa? Matarka tana KoKarin dawo da kai hanya, amma ka zama makaho? To ka sani, babu ruwana da mazinaci ma, ni idan na – ganshi zann iya kashe shi, ba na yiwa mazinaci uzuri. Bare kuma a kai ga cikin shege. An ce fa tsintar uwar ka yi. Ka canza tunani zan sake dawowa.” Ya mike ya fice abinsa. Alhaji Lukman ya bi shi da ido, yasan za a rina, Sai dai yana jin ko mahaifiyarsa ba za ta hana shi taimako ba, bare yayan matarsa. Karin Jin dadinsa ma, da Hajiyarsa ta nuna masa goyon bayanta akan renon yaran. Haka kowa ya bar www.bankinhausanovels.com.ng  gidan zuciyoyi babu dadi. Shi kuwa Sultan Makaranta kadai ke raba shi da yaran. Kullum yakan tasa su a gaba ya yi ta kallonsu kamar mai son gano wani abu. Mahaifiyarsa bata shiga sabgarsa, haka ta hana Kannensa shiga huruminsa, idan ya gaishe ta bata amsawa, shi kuma bai fasa ba. Hajiya Salma ta sauke wayar da ta gama yi da Kawarta Hajiya Ladidi ta kuma yi na’am da shawarar da Kawarta ta bata. Don haka ne ta sami Alhaji da ke zaune yana duba Jarida fuskar nan babu fara’a ta nemi wuri ta zauna, “Alhaji ka ~ yi hakuri ka yafe min, na tuba. Fushinka yana daga min hankali. Na amince ‘yan biyu su zauna ’ a gidana, amma da sharadi.” Alhaji Lukman ya dube ta da fara’a sosai a fuskarsa domin shi kansa ya yi kewar matarsa. “Ina jinki fadi sharadin.” Muskutawa ta yi tana murmushin mugunta, “Sharadina ba zan tsaya kulawa da yaran ba, ka ga kasuwancina ma ba zai barni ba, sai dai a Karo masu kula da yaran, ni zan dinga biyan ma’aikatan domin bada gudumawata. Shi kuma Sultan ina son in nuna masa kuskurensa na www.bankinhausanovels.com.ng  gujewa maganar mahaifiyarsa. Don Allah ka bar ni a hakan mu shirya kanmu.” Alhaji Lukman ya dubi matarsa, yana jinjina ita mace har tsufanta da yarinta a ciki. Don haka babu dogon tunani ya ce ya amince, ya kuma ji dadi da har Hajiya za ta iya bada gudumawarta wajen kawo masu aiki. Miji da mata sai Allah, a nan suka shirya kansu. Babban damuwar Sultan a yanzu bai wuce yadda mahaifiyarsa ta nunawa Kannensa Sultan a matsayin maKiyinta ba. Yanzu Kannansa bayan gaisuwa basa shiga huruminsa. Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu  wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu 

Hmmm koya zata kaya kudai kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *