RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu  wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu 

ZAMU TASHI 

 soron shi fiye da tunanin su, kasancewar bai taba kai hannu jikinsu ba. . Hajiya Salma ta fito a gujen gaske tana ganin abinda ya faru, ta sa Salati da Karfi tare da dafe Kirji. Tana Karasowa ta dauke shi da mari. Ya rike fuskarsa zuciya tana wani irin cinsa. Ji yake kamar dukan da ya yi masu bai gamsar da shi ba, yana jin zai iya aikata komai akan yaran da ya Kwallafa ransa a kansu. Sultan ya juya kawai zai tafi, Umma ta sake fizgo shi, “Zo nan shugaban marasa imani, ba ka isa ka tafi  ba, sai ka kashe su. Zo ka kashe su, ka fita duniya ka gaya masu ka nakasa Kannenka saboda ‘ya’yan shegu.”  

Sultan dai bai ce komai ba, har ta gama  masifarta ta fice da yaranta. Shi kuma ya fice yana Kwalawa masu kula da yaran kira. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sau tari suna mamakin yaro Karami ya tsaya yana basu manyan dokoki. Su dai sai hakuri suke bashi. Ya karisa ya dauki naufal yan girgizashi ya bashi madara Yasa bakinsa a kunnensa yana masa addu’a har barci ya kwashe shi. Nasreen dai ta ki __ yin shiru sai kuka take tsalawa. Ya karbeta yana

Www.bankinhausanovels.com.ng  kallonta. Yadda ta bude idanunta tana kallon Sultan ya sa ya yi murmushi, “Ke sarkin kuka. Ke ragguwa ce ko? Oya yi min shiru ko in zane dan bakin nan.” Cikin ikon Allah ta yi shirun, haka idanunta Kyar akansa. Hajiya Salma ce zaune da Hajiya Ladidi suna tattaunawa, “Wato ni abinda ke damuna, macen nan da aka Haifa. Tana iya girma ta zame mani matsala, Kila daga Karshe ta biyo halin uwarta na bin maza. Gara namijin bana jin akwai wata matsala da zai bani. Don haka ne nake neman shawararki yadda za a yi inbatar da Nasreen daga duniyar gaba daya.” Hajiya Ladidi ta numfasa, “Maganarki gaskiya ce. Ai ina ganin ki ba su Rainbow aikin nan a kwana daya za su kashe kayan banza su watsar.” Hajiya Salma ta yi na’am da wannan shawarar, don haka ta hadata da Rainbow ta gaya masu yadda take so. Cikin dare, Sultan ya idar da Sallar dare, haka kawai yake jin ba zai iya barci ba, idan har bai je yaga ‘yan biyu ba. A hankali ya fito yana takawa har ya iso dakinsu. A lokacin Rainbow ya shigo jin motsin Sultan yasa ya makale a gefe yana kallon ikon Allah.  Nasreen ce idonta biyu, shi kuwa Nawfal sai shaikan barcinsa yake yi. Sumbatar yaron ya yl ya sake tofe shi da addu’a. Nasreen kuma ya dauketa yana dubanta. “Abba ya ce ke RUBUTACCIYA ce, zai yi wahala mai nemanki da sharri ya same ki.” . : Dauketa ya yi ya nufi dakinsa da ita yana jijjigata. Akan Kirjinsa ya kwantar da ita yana bubbuga bayanta har barci ‘ya sureta. A Kalla Rainbow ya kwatanta zuwa gidan yafi a Kirga, amma samun ko taba jikinta ya gagara, domin kullum yazo sai ya sami Sultan a tare da su. Wannan abu shi ya Karawa Umma jin tsanar Sultan a zuciyarta, kuma ta yi alKawarin indai ita ce sai taga bayan Nasreen. Shi kansa Abba yanzu hidimomin fice-ficensa sun sanya shi a gaba, don hakane baya samun wani cikakken zama Babu abinda zai baka mamaki sai yadda yaran suka yi bulbul suka yi wayo. Kullum kyawun yaran gai sake fitowa yake yi. Suna samun kulawa sosai daga Sultan, haka yaran sun yi wata shaKkuwa da Sultan har suna iya gane shi Www.bankinhausanovels.com.ng  da zarar yazo wurin su. Rashin jituwa tana sake kusanto shi da mahaifiyarsa. ” “Yau gaba daya suna zazzaune a falo suna cin abinci. Abba ya dubi Sultan ya ce, “Yanzu sai makarantar likitoci ko?” Sultan ya girgiza kai, “A’a Abba na sauya ra’ayi Dan sanda nake son inzama.” Umma ta dafe Kirji da Karfi, “Yau na shiga uku! Dan sanda a gidana? Wai me yake damun Kwakwalwarka ne? To ba ka isa ka zama dan sanda a wannan gidan ba. Yadda na tsani dan sanda Wallahi ba ka isa ba.” Abba ya kurbi ruwan shayinsa yace, “Oh me kuma dan sanda ya yi maki? Ke kin huta komai baki so.” Ya Karashe da yi mata gatse, Ta hada rai ta ce, “Ni dai na gama magana.” Sultan da kansa ke Kasa ya dago ya ce, ““Abba dan sandan nake son inzama insha Allahu. Umma ki sa min albarka kawai.” Umma ta sake zabura kamar za ta kai masa duka, “‘Albarkar wa? Ba zan sa ba shegen yaro kafaffe. Kaje indai dan sanda ne nawa ido.” Abu kamar wasa har sai da maganar ta iso gun Hajiya Gwaggo, wanda ta yi mata fada sosai, ta kuma tursasata sai da tasa masa albarka Www.bankinhausanovels.com.ng Mutane da yawa suna kallon Sultan a matsayin wani miskili wanda bai damu da magana ba, amma kuma idan ka same shi a cikin su Nasreen ya cika masu daki da kayan wasa, sai kayi ta mamaki kana cewa anya Sultan ne kuwa? A guje ta fito da ‘yar bebinta, kai tsaye jikin Sultan ta fada tana KyalKyaltan dariya. Sultan bai tabata ba, ya tsaya yana kallon wanda ya sa Nasreen irin wannan dariyar. Nawfal shima ya fito aguje yana bude haKoransa. Gaba daya gaban Sultan suka tsaya suna haki. Kamar ba zai yi masu magana ba, kasancewar bai jima da dawowa aiki ba, kuma ya gaji da yawa, amma dole ya amsa masu yana murmushi, “Me ya same ku kuke dariya haka?” Nasreen ta dube shi da idanunta kamar madara, ta ce, “Dee ni zan fara gaya maka, Bros Nawfal ne ya biyo ni zai dakeni. Shi ne Anti Hafsa ta biyo mu da bulala za tayi mana dukan gaske.” Fitowar hafsat a fusace yasa duk suka bita da kallo. Tana ganin Sultan jikinta ya yi sanyi ta koma da baya har tana tuntube. Nasreen ta shige jikin Sultan tana Boye kanta. Sultan ya dagota ya zuba mata ido Www.bankinhausanovels.com.ng kanta ya sha gyara da Kananun ribom masu kyau. Kurawa Kafafunta idanu ya yi gabansa yana ci gaba da fadiwa da Karfi. 

« BAYAN WASU SHEKARU 

Doguwar yarinya ce, mai yalwataccen gashin kai wanda ya taho tun daga goshinta har zuwa bayanta. Tana da saje irin na mata wanda yake nuni da alamun yarinyar tana da gashi. Ba fara ba ce kai tsaye kana kallonta za ka kira ta mai kalar choculate. Duk da hasken ya rinjayi duhun. Ko alama ba ta da jiki, siririya ce wanda sirrancin ya yi matuKar yi mata kyau kasancewar ba ta da rama. Kugunta a dan bude suke, haka daga samanta Allah ya wadata dukiyar na Fulani. Har yanzu akwai yarinta a tare da_ ita, kasancewar shekarunta ba za su wuce sha shida ba a duniya. Tana da sassanyar kyau, haka da za a shiga gasar kyawawa da ita, babu abinda zai hana ta cinyewa, Muryarta ta cika sanyi da yawa, haka komai take yi a sanyaye take yinsa, kamar wacce ba ta dauke da kayan ciki. Fuskarta kullum dauke yake da murmushi ko da kuwa kuka take yi, sai ka hango murmushin nan. Www.bankinhausanovels.com.ng  Sanye take da kayan Makaranta mai kalar blue hijabinta kuma fari tas! Shigowar Sultan yasa ta Karaso kusa da shi tana mika masa hannayenta, “Dee ka taimaka ka cire min abin hannun nan kada a Kwace min a Makaranta.” Kafe ta ya yi da idanu yana tuna wasu abubuwa, sal kuma ya kama tsintsiyar hannun yana kokarin cire mata. Cikin sa’a ya dago kansa ita kanta shi ta kafe da idanu tana kallon sa. Manyan idanunta suka hade da nasa masu yawan lumshewa. Gaba daya suka sakarwa .. kansu murmushi, ‘sannan ya cire mata. “Lazy baby, ki yi sauri ni zan ajiye ku in wuce office.” Marairaicewa ta yi , “Ayyah Dee, Kila ma kai kayi min baki shi ya sa har yanzu nake Lazy.” Murmushi ya yi ya dauki jakar makarantarta suka fito. Umma ta dube shi ta riqe baki, “Oh wani sabon gulmar ce kuma yau Za ka rike mata jaka? Kullum da sabon salon iskancin da yarinyar nan take dauke da shi.” Wucewa tayi . Sultan suka kalli juna da Nasreen sai duk suka basar. Www.bankinhausanovels.com.ng Sultan zai tafi kwas wanda za a Kara masa girma, sai dai wannan ne karo na kusan hudu yana soke tafiya kwas dinsa sabod su Nasreen. Amma a yanzu tunda sun girma za su iya yin komai da kansu, yana da buKatar tafiya. Yafi tausayawa Nasreen da ta dora shaKuwar duniyar nan akan Sultan. Haka ya dinga shirye-shirye jikinsa babu Kwari. Nasreen ta shigo dakin ta dube shi ta ce, “Dee in kawo maka Assignment dina ka taya ni dubawa ko nayi dai-dai?” = Dubanta yake yi kamar yau ya fara ganin ta, “Nasreen kin ga na gaji da yawa, ki bari sai ~ an jima ko?” Gyada kanta ta yi tana duban yadda yake shirya kaya, “Dee ina za ka je da kayan nan? Na san ba za ka tafi ka bar ni da Umma ba ko? Umma ba ta sonmu ni da Nawfal, ban san me muka yi mata ba. Dee me muka yi mata?” Shafar gefen sajenta ya yi yana KirKiro murmushi, “Babu abinda kuka yi mata, tana son baku tarbiyya mai kyau ne, Tana sonku kun ji? Ko kin taba ganin inda uwa ta tsani ‘ya’ yanta?” Www.bankinhausanovels.com.ng Nasreen ta yi narai-narai da idanun dake firgita “yan maza ta ce, “Ai ta ce ba ita ta haife mu ba, wai mu a Karkashin gada aka same Sultan da ya ji gabansa ya fadi, ya mike jikinsa har yana kyarma. Kai tsaye falon mahaifinsa ya nufa, wanda yake zaune da Umma. Ya dube su ransa a matuKar bace ya ce, “Umma don girman Allah ki daina cewa yaran nan bake kika haife su ba, har kina gaya masu daga inda suka fito. Yaran nan ba su san komai ba, bai kamata ana yi masu hakan ba.” Abba ya dube shi cike da mamaki, haka ya dawo da kallonsa gun Hajiya Salma tare da ware ~ idanu, “Salma! Kina nufin duk irin gargadin da nayi maki baki ji ba kenan? Me ya sa za ki dubi yara Kanana kina gaya masu irin wannan maganar?” Hajiya Salma ta dinga auna wa Sultan harara, ta kuma hada rai ta Ki yin magana. Haka Sultan yasa kai ya fice ransa a bace. Alhaji Lukman ya mike yana dubanta ya fice ya bi bayan Sultan. Www.bankinhausanovels.com.ng Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Sultan dai ya bar garin zuwa Enugu, ba tare da wata matsala ba. Haka ya jaddada amanar Nasreen a gurin Mairo ya fi a Kirga. Da zai tafi yaran suka yi masa layi kowannensu ya yi tagumi. Gabadaya ji yake ya karaya. Ya sa hannu ya yafito su duk suka Karaso gabansa yana dubansu. “Nawfal, Nasreen ba za ku yi min dariya ba?” « , Dukkansu suka fidda murmushi wanda kallo daya za ka yi masu ka fahimci iyakarsa fuska. Shafa kansu ya yi ba tare da ya iya furta komai ba, direba ya ja motar suka fice. Rintse idanunsa ya yi da Karfi yana jin gabansa yana tsananta fadiwa. Ji yake kamar ba zai dawo ya same su da rai ba. Hajiya Salma ta gama leka ko’ina ta tabbatar da babu Abba a gidan, hakan ya sa ta jawo Nasreen da Karfin tsiya ta fesa mata wani abu a cikin idanunta. Yarinyar ta sanya Kara mai Karfi, ta fadi tana shure-shure. Nawfal ya Karaso da gudu ya tallafo ta yana Kwala mata kira. Nasreen tana kuka Nawfal yana kuka, gaba daya an rasa wanda zai lallashi wani Www.bankinhausanovels.com.ng  Nawfal ya dago ya zuba wa Hajiya idanu, yana jin haushinta da tsanarta a cikin ransa. Ko da yake yaron yana da tabbacin Umma bata kaunarsu. Yana kallon yadda su Haidar suke kwasar dariya. Hafsa ta ce, “Shegiya ba kina taKama da idanunki ba ne? To an nakasa su sai mu ga wani abin yangar.” Haka suka wuce suka barsu cikin kuka. Ita kuwa Nasreen saboda azaba a take ta suma. Umma ta sake dawowa, ta damki wuyar rigar Nawfal ta ce, “Wallahi kuka sake kuka fadawa waml Wai ni ce nay mata wani abun, sai na kashe ka Nawfal ya gyada kansa yana ci gaba da hayyacinsa saboda kuka. Cikin ikon Allah sai ga Abba ya dawo, kai tsaye ya nufi yaran don ya duba su. Haka yana son ya cika alKawarin da ya daukarwa Sultan zai hada shi da su. Ganinta a kwance bata motsi ya daga hankalinsa. Bai tsaya bin ba’asi ba, ya dauketa sai asibiti. Yana nan tsaye ya kasa zaune saboda tunanin mai ya sami Nasreen haka? Ya fi Karfafa zarginsa akan Hajiya Salma, idan kuwa ita ce, Www.bankinhausanovels.com.ng  babu shakka zai ya sakinta ta koma gidan su. Kiran wayar Sultan na biyar kenan, yana kasa dauka. Dole yasa wayar a kunne yana cewa, “Sultan ban iso gidan bane. Ka kwantar da hankalinka ina isowa zan hadaka da yaranka.” Sultan ya cika da mamakin mutumin da ya ce masa yana kusa da gida, yanzu kuma zai ce bat iso ba. “Abba fa ka ce min kana kusa da gida, yanzu kuma ka ce baka iso ba. Abba ko dai da matsala ce?” Jikin Abba ya yi sanyi, yau ya yi wa dansa karya har ya kama shi, “Ka yi haKuri Sultan babu matsalar komai, har na kusa gida aka sake ~kirana, wani abokin mu bai da lafiya shi ne yanzu na iso asibitin.” Dole Sultan ya ajiye wayar yana ci gaba da saKe-sake. Lambar mahaifiyarsa ya kira, tana kallo ta Ki dauka gabanta yana fadi kada Nasreen ta farka ta ambaci sunanta. Da kiran Sultan ya yi yawa ta dauka cikin daga murya ta ce, “Wai menene haka kamar kana bi na bashi?””“Umma don Allah ki taimaka ki hada ni . da su Nasreen, Abba ya ce bai iso gida ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng  “Umma taja dogon tsaki, “To ba zan hada ka da su din ba. Ka ga Sultan? Ka kiyaye ni! Idan ba haka ba, ni na san yadda zan yi da kai. Kada ka sake kirana.” Kawai sai ta kashe kiran. Wayarsa yabi da kallo yana jin kashe wayar har tsakiyar kansa. Ya kasa jure rashin jin muryar yaran, don haka ne ya ci gaba da jin damuwa da bacinrai. _  Likitocin suka fito suka bukaci Abba da ya biyo su Office. A nan suka yi masa bayanin wani Chemical aka zuba mata a idanun, a sakamakon hakan da wahala ta sake gani da idanunta, sai kuma-_wani ikon Allah. Abba ya yi suman zaune. A yanzu me zai iya gayawa dansa? Dakin da Nasreen take zaune ya shigo yana dubanta, “Nasreen.” Lalube take yi tana fadin “Na’am Abba. Me ya sa bana ganinka? Abba ina Nawfal? Shi ma ba zan iya ganinsa ba? Abba ka bude min idanuna ina son inganka. Abba idanuna har yanzu Zafi suke yi min.” Hawaye mai dumi ya biyo idanun Abba. Zuciyarsa ta karye, ba shi da wani Karfin guiwa. Zama ya yi kusa da ita ya kamo ta, ya mayar da www.bankinhausanovels.com.ng ita jikinsa, ‘“Nasreen dina. Wannan Kaddararkice, haka komai za a yi maki insha Allahu sai kin kai labari, domin ke RUBUTACCIYA ce, wanda Allah ya rubuta sai kin sha ruwa a duniyar nan. Ciwo kika ji za ki warke har ma ki fara gani da idanunki kin ji? Yanzu gaya min waye ya watsa maki abu a cikin idanu?” Nasreen da ta gigice ta hau girgiza kai “Ni ma bansan waye ba Abba: Ka kai ni wajen Dee in nuna masa idanuna, bana ganin kowa sai duhu.”  Wannan karon kalaman bakin Abba sun Kare, dole ya koma kamar kurma. Satinta guda a asibitin, kullum Abba ke kulawa da ita, haka ya Ki yin magana ne yana jiran a sallamota. Nawfal da Mairo mai aiki suke zaman kulawa da ita. Ranar da aka sallame su, suka tattaro suka dawo gida. A bakin Gate suka sami Nawfal kusa da mai gadi ya zauna ya yl shiru, kasancewar a ranar Abba ya hana shi zuwa ya ce ya bari kawai yau za su dawo da Nasreen din. Yana ganinsu ya taso ya Karaso da saurinsa kamar zai kifa. Ganin Nasreen tana lalube yasa Nawfal kafe ta da idanu. Abba ya jawo Nawfal Www.bankinhausanovels.com.ng yayi masa dabarar duniyar nan amma ya Ki fadin wanda ya yi wa Nasreen wannan aikin. A tunanin Nawfal da gaske Abba yake yl, yau Nasreen za ta fara gani da idanunta, kafe ta ya yi da idanu, zuciyarsa tana gaya masa Nasreen ta tabbata makauniya.Sai kawai ya hau kuka mai tsanani yana tausayawa ‘yar uwarsa. Abba ya dubi wayarsa yana kallon kiran Sultan, ya dubi yaran ya ce, “Ga Daddynku zai yi magana da ku, idan kun dauka ku tabbatar masa kuna lafiya kun ji? Idan ya san abinda ya faru zai fasa aikinsa ya dawo nan, ku bari har ya gama sai ya dawo sai ya gani. Nasreen ke kuma insha Allahu zamu nemo maki magani ‘har ki warke.”Dukka yaran suka amsa masa. Da kansa ya kira Sultan ya mika wa Nawfal. Muryar Nawfal da yaji yasa ya saki ajiyar zuciya, suka gaisa da yaron yana masa ‘yan tambayoyi. Daga bisani ya ce, a baiwa Nasreen. Cikin Shagwababbiyar muryarta ta ce, “Dee…” Sai – kuma_ tayi shiru. Siririyar muryarta ta ci nasarar tsinka masa zuciya, “Nasreen kin ‘yi kuka, Nawfal ma ya yi kuka, gaya min waye ya Www.bankinhausanovels.com.ng  saki kuka? Ko wani ya duke ku ne?” Girgiza kai tayi kamar yana ganinta, “Babu komai, muna son mu ganka ne.” Yarinyar har ta san gyara magana. Girgiza kansa ya yi yana latsa laptop dinsa, “Kada ki damu zan dawo in dauke ku gabadaya daga gidanmu. Zamu je wani wuri mai nisa muyi ta rayuwarmu mu uku ko? Oya ki share hawayen nan bana sonsa… Haka suka yi ta shirmensu kafin ya yi sallama da su yana Kara gode wa Abbansa. ‘ A falon ya tara kowa yana faman kaiwa da komowa ransa a matuKar bace.,“Ya zama dole ku gaya min wanda ya aikata wa Nasreen wannan abin,:ko kuma in hada ku dukka in kulle.” Hajiya Salma da ba ta dauki lamarin zai yi irin wannan zafin ba, ta ware idanu, “Yanzu a kan wannan yarinyar za ka kulle su?” Alhaji Lukman ya Karaso har gabanta kamar zai dake ta, “Me ya sa kike cire kanki a cikin mutanen da zan dauki mataki a kansu? Ke ce mace ta farko da zan fara kiran “yan sanda su tafi da ke, su tuhumeki. Domin na fi zarginki, 

Hmmmm tofa labari nata zafi fa koya zata kaya kudai kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *