RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?” Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Www.bankinhausanovels.com.ng Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.” Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.” Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen,

ZAMU TASHI 

Sultan har yanzu babu labarinsu. Wannan ciwon na tabbata da shi zan koma ga Mahaliccina.”  Hawayen da Abba yake Kokarin dannewa sai da suka zubo, ya sa hannu da sauri ya goge kamar mai tsoron wani ya gani. Sultan ya kasa cewa uffan har Abban ya gaji ya juya wurin motarsu da ‘yan, sanda za su jagoranci tafiyar tasu, saboda yanayin hanyar. Hannu kawai ya iya daga masu har suka fice. Cikin sauri-sauri ya shirya cikin

kakinsa ya fito hannunsa dauke da wayoyl. — Zakiyya ta yi narainarai da idanu tana dubansa, “Ka zauna a gida ma.. Hannu ya daga mata ya wuce abinsa. Abinda bai sani ba, yana fita Zakiyya ta gayyato ma’aikatan jaridu tasa aka dauke ta hotuna, tayi bayani dalla-dalla a matsayinta na matarsa. Ta kuma cewa a daina cewa mijinta bai da mata ita ge matarsa, Kwanan Sultan biyu bai leKa gidansa ba, ita kuwa ko a jikinta. Haka tana sane da ya sallami mai girkin gidansa kasancewarsa namijl, amma ko sau daya ba ta taba Sa tsintsiya ta share ko da falo ba. Haka ruwan fridge ya dinga zuba Www.bankinhausanovels.com.ng yana shiga KarKashin kafet din, nan da nan dakin ya dauki wari. Kitchen kuwa wasu abubuwan da ba a sanya a fridge ba, har sun lalace suna wari. Ko a jikinta, ita dai idan ta samu ta ci abinda take son Ci, Za ta nemi wuri a falo ta sa film din batsa tana kallo. Gabadaya Sultan ya mance da Allah ya yi ruwan wata Zakiyya a cikin gidansa. Tunanin halin da mahaifinsa yake ciki ya fi komai daga masa hankali. Kai tsaye ya gane mahaifiyarsa ta yi amfani da bokayen tsubbu domin cimma burinta. Mahaifiyarsa ta yi nisan da ba ta jin kira, ” tayi nisan da take mance girman Aljannah, da kuma abubuwan da ya kamata ta bi domin shigarta Aljannah. Gabansa ne ya fadi da Karfi da ya tuna da Kannansa da ke cikin gidan, yana —tsoron lalacewar tasu tarbiyyar. Ya zama dole ya je idan har abin da matsala ya kwashe su daga gabanta. Yana tsoron bakin da Umma take yi wa ‘ya’yan wasu ya faru akan ‘ya’yanta. Duk yaron da ta gani dan iska ne, nata ne masu kirki. Kowa ta gani mazinaci ne, nata ne masu kare kansu daga sharrin zina, kowa ta gani aron addininta suka yi,
Www.bankinhausanovels.com.ng nata ne wadanda suke da asali a cikin addini. Ta ya ya Allah ba zai aiko da jarabawa cikin gidansu ba? Ta ya ya Zakiyya ba za ta zamo matarsa ba? A bayyane ya yi magana, “Ya Allah! Ban kasance mazinaci ba, kada ka jarabceni da rayuwa da mazinaciya. Allah ban taba jayayya da yinka ba, kada ka jarabceni da_laifin mahaifiyata. Allah mahaifina bai ° kasance azzalumi ba, kada ka jarabce shi da macen da za ta zalunce shi. Allah ka warware mana wannan matsalar da ke tunkaro mu, ka kare min Kannena a duk inda suke. Allah ka bayyana min Nasreen da dan uwanta cikin Koshin lafiya.” Zare rigarsa ya yi ya kama hanyar gidansa jikinsa a sanyaye. Har a lokacin babu dan sandan da ya gaya masa cewa Zakiyya ta gayyato ‘yan jarida. Yana sa Kafafunsa a cikin gidansa hankalinsa ya ninku a tashi. Ransa ya yi mugun baci, ya dubeta rai a Bace ya ce, “Ke ba ki da hankali ne? So kike ki mayar min da gida dafidalin wari? Ko bola kika samu ne? Ki tashi ki gyara gidan nan tun kafin bacin raina ya sauka akanki.” Jikinta yana rawa_ saboda_tsoron Www.bankinhausanovels.com.ng yanayin da taga Sultan, ta wuce kitchen domin dauko tsintsiya. A lokacinne ya bayyana a kitchen din. Ya ma kasa magana saboda azabar warin da ya ziyarci hancinsa. Dole ya sa hannu ya toshe hancinsa. Haka ya koma hankalinsa a tashe. Sultan ya tsani Kazanta fiye da tunanin mutum, dakinsa ya koma ya kwanta yana kallon sama, cikin tunanin da shi kansa bai san ko na menene ba. Nazari yake yi ta yadda za a yi ya iya rayuwa da Zakiyya a matsayin mata. Yana nan kwance bai motsa ba, ta gyara dakunan sama-sama ta je ta sheKa wanka ta antaya maganin da uwarta ta ba ta, sannan ta Kara shiga ruwan zafi, kamar yadda Hajiya Ladidi ta karanta mata, domin aikin da aka yi mata don ta koma budurwa har yanzu tana dan jinsa. Ita kanta yadda aka dinke ta abin yana bata tsoro, haka tana shakkar zai iya ganewa cewar ita ba budurwa ba ce, idan hakan ya faru tana da tabbacin Sultan korar kare zai yi mata. Shi kuwa wanka ya shiga ya fito daure da tawul yana tsane ruwan jikinsa. Ta shigo dakin babu ko sallama, kallo daya ya yi mata ya dauke Www.bankinhausanovels.com.ng kansa gabansa yana fadiwa. Babu laifi yarinyar tana da kalar tata kyan, sai rashin kamun kai da ke dawainiya da ita. Jikinsa ta Karaso tasa hannu ta rungume shi. Kamshin maganin da ta yi amfani da shi, ya yi ta dawainiya da shi, don haka ya fara mayar mata da martani, da taimakon tsaftace jikinta da ta yi. Ba shi ya farka ba, sai da asubahi. Ware idanunsa ya yi yana duba irin barnar da ya yi wa ‘yar mutane. Mamakin samunta a budurwa yafi komai tsaya masa a rai, domin yadda yaga bai taya taba, ita ta fara kawo kanta yasan da matsala. Haka wannan budurcin da ya samu ya sanya ya Kara ganinta da girma da mutunci a idanunsa. Gabadaya zanen gadonsu ya lalace da uban jini. Tana nan kwance kamar kayan wanki tana shakar barcinta. Mamaki ya sa ya kafe ta da ido, yaushe za a yi wa mace hakan ta kwantar da hankalinta? A hankali ya zame kansa ya shiga bandaki ya tsaftace jikinsa, kafin ya sa hannu ya tasheta, tana bude idanu ta fara magana cikin magagi, “Bilal ka rabu da ni barci nake ji.” Sultan ya zaro idanu yana sake dubanta, “Bilal kuma? Waye Bilal?” Www.bankinhausanovels.com.ng Ware idanunta ta yi gabanta ya fadi da Karfi, sai yanzu ta tuna abinda ya faru, don haka ta fara raki, “Wash! Don Allah ka taimaka min ba zan itya tashi ba.” Sultan dai kallon ta kawai yake yi, haka kuma zai iya makara yin Sallar asuba, don haka yace “Ki yi haKuri Zakiyya zan makara.” Ya sa kai ya fice abinsa. Yana fita ta mike ta shige bandaki ta gasa jikinta, sannan ta cire zancn gadon ta shimfida masa wani ta sake hayewa gadon tana shaKar barcinta. Babu Sallah bare Salati. Yana dawowa ya dube ta yana tantaman anya ta yi Sallah? Sai kuma ya kau da wannan tunanin a cikin ransa, ya yi tagumi. Wannan ranar ya tanadarwa Nasrcen dinsa, sai ga shi a lokaci guda Allah ya yi ikonsa, wanda babu wanda ya isa ya yi jayayya da yinsa. Shirin zuwa office ya fara, yana tunanin dole sai an samo ma’aikata sun yi masa gyaran gidansa domin har yanzu wari yakeyi sosai. Tashinta ya yi yace ta koma dakinta zai rufe Kofarsa. Ba ta yi mamakin rashin mutuncinsa ba, domin tuni ta fara haddace su. Tana dingishi ta fice.
Faruwar wannan lamari tsakanin Zakiyya da Sultan ya sanya mata wani irin sonsa, a cikin zuciyarta kamar ta mutu. Tana jin bata taba Www.bankinhausanovels.com.ng mu’amala da wani namijin da ya gigita tunaninta irin Sultan ba. Duk inda ake neman namiji mai mantar da mace damuwarta, Sultan ya hada abubuwan nan. Tana jin ko dukanta zai dinga yi kullum ba za ta rabu da shi ba. Haka ta raina iyawar Bilal duk yadda take yabonsa kuwa. Shi kuwa ya kasa farin ciki da irin sabon lamarin da ya shiga, abin ya kasa burge shi, haka shi bai san yadda budurwa take ba bare ya fahimci abinda Zakiyya ta yi. Yan sandan ya basu umarnin su samo masu aiki a tsaftace masa cikin gidansa, a fitar da dukkan abubuwan da suka lalace.. Jaridar da ya samu a cikin motar ya dauka yana dubawa. Gabansa ya fadi da ya ga hotonsa hade da na Zakiyya. Cikin sauri ya ware ya fara karantawa. Ya gigita iya gigita, don haka ya ce wa direba ya juya gidan. Yana fitowa daga mota ya dubi-~daya daga cikin ‘yan sandansa yana tambayarsa yaushe akayi wannan hirar? Cike da tsoron yadda ya ga yanayin Ubangidansa ya gaya masa komai. Sultan ya daga hannu ya wanke shi da mari, ya sake daga hagunsa ya dauke shi da mari yana huci. “Ashe baka san aikinka ba aka kawo min kai? Ashe idan kashe ni za a yi zaku iya ba barawon hanya? A cikin gidana zaku bar ‘yan jarida su shigo har falona? Wannan wani irin shirme ne‘ Www.bankinhausanovels.com.ng sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.” Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?” Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?” Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.” Sultan mutum ne mai son mutumin da

Hmmmm labari fa nata tafiya shin koya zataci gaba da kayawa kudai kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *