RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace,
Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a
cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci abinda take nufi, ya ce, “TirKashi! Ni mace ma ba ta gabana bare har in iya yin abinda kike nufi.” ’ Mikewa ya yi ya shige bandaki ya sa key Zakiyya ta mike ta shige dakinta tana cizon yatsa Ya riga ya dandana mata zuma mai wahala mancewa. Shigewa dakinta ta yi ta kira mahaifiyarta, “Momi mutumin nan fa ya iya komai Naji dadi da kika hada ni da shi. Wallahi yanda nake jin sa babu abinda zai raba ni da shi, gashi baya ~ son hayaniya.” A nan ta yi ta ba mahaifiyarta labarin yanayin Sultan, wanda karaf sai a kunnensa.

ZAMU TASHI 

RUBUTACCIYA 2

Sultan ya gama sauraren dukkan maganganun da take yi a waya, ya zuro kansa cikin dakin cike da takaicin jin matarsa tana bude masa sirrinsa.

Yana sanye da jallabiyarsa fara sol sai Kamshi ke fita daga jikinsa. Shigowa ya yi ya zauna yana duban ta. “Ke kuma haka Allah ya halicce ki fadin sirrin mijinki ko? A haka dai kamar mai wayo ashe sakarya ce. To daga yau na bar sake zama kusa da ke, tunda baki da sirri.”

Zakiyya ta gigice ta ce, “Wallahi ba wata bare nake gayawa ba, Momi ce ta kira nake bata labari kayi hakuri ba zan sake ba.”

Sultan ya zaro idanu sosai. Kamar zai yi magana sai kuma kawai ya fice abinsa. Mamaki ya ci gaba da dawainiya da shi, ta yadda yarinya za ta iya kallon idanun mahaifiyarta ta gaya mata sirrin da ke

Www.bankinhausanovels.com.ng tsakaninta da mijinta, abin ya yi masa tsauri sosai.

Duk yadda Mansur yaso ya ga ya sami kan Nasreen abin ya faskara, hakan yasa ya daina basu abincin, ya koma ba su wahala yana gana masu azaba kala-kala.

Da Nawfal ya gaji ne ya ce, ‘Nasreen ki amsa masa ko za mu samu a rangwanta mana. Ba ki jin tausayina ne Nasreen? Ina shan wahala.”

Nasreen ta goge hawayenta, tana laluban Nawfal da kwana biyu ya Ki yarda ta taba shi, sakamakon jikinsa da ya yi zafikamar wuta, “Nawfal don Allah ka zo kusa da ni, ka daina guduna kaji Nawfal?”

Nawfal ya Karaso ta rungume shi, a lokacin ta ji jikinsa zafi rau! Ta goce da kuka sosai, “Nawfal baka da lafiya ne? Me ya sameka? Nawfal so kake ka kashe min kanka? So kake ka sani maraici?” Dukansa take yi da dukkan hannayenta tana kuka. Shi ma kukan y.ake yi azaban ya ishe shi haka.

Www.bankinhausanovels.com.ng “Nawfal… bari Mansur ya zo sai ya nemo maka magani.”

Girgiza kansa ya yi, “Mansur ba ya nan, ya tafi ya barmu a Karkashin kulawan Kattan nan.”

Ajiyar zuciya take yi da Karfi. “Nawfal lallaba ka je waje ka samo ruwan_ sanyi ingoga maka a jikinka ko zai rage zafin.”

Babu musu ya aiwatar da abinda ta ce, ta sa gefen hijabinta a ruwa tana jiKawa tana goga masa a jiki. Sun dauki tsawon lokaci a hakan har jikinsa ya fara sanyi sannan ta sa kansa a Kafafunta tana tofa masa addu’a. Wani ya shigo yana dubansu ya ce, “Yanzu sai ki fara takaba barayi sun kashe Sultan.” –

Wani abu ta ji ya ratsa mata tsakiyar kanta, tunda ta fasa wata Kara ta kifa kanta a jikin Nawfal bata sake sanin inda kanta yake ba.

Nawfal ya tashi yana rintse idanunsa, da Kyar ya iya duban mutumin ya ce, “Ka ji tsoron Allah. Yaushe Deedi ya rasu? Na san

Www.bankinhausanovels.com.ng kun yi’ hakan ne domin ku cimma wata manufarku ,akanmu.” Mutumin ya girgiza kai jikinsa,a sanyaye, “Da gaske Sultan ya rasu. Ni kaina naji rasuwarsa, kasancewar kisan wulakanci akayi masa. Haka kuma anrasa gane su waye ke da alhakin wannan _,aikin. Ka. taimaka ‘wa ‘yar uwarka ta farfado.” ~*~ ~ . Nawfal yasa kuka mai sauti yana jin zuciyarsa tana yi masa ciwo. Cikin kuka ya – dubi mutumin ya ce, “Don girman Allah ka sadamu da’ gidansu Deedi muyi masa addu’a. Mutuwar Deedi tamkar tonan asirin mu ne.. Mun shiga uku don Allah ku taimake:mu ku kaimu gida mu zauna cikin ‘yan uwanmu domin yi wa Deedi addu’a.” Mutumin da ya fara jin tausayin su har cikin zuciyarsa ya girgiza kai, “Yin hakan zai iya jawo nima inrasa rayuwata agurin Oga Mansur, Zan baku shawara ku bi shi a hankali za ku rabu lafiya. Ka duba lafiyar ‘yar uwarka bari in kawo maku abinci ku ci.” Nawfal ya fara watsa wa Nasreen ruwa,

Www.bankinhausanovels.com.ng ta ja dogon numfashi, taso Kwarai yau da idanunta suna gani ta kalli mutumin da ya kawo mata wannan mummunar sakon. A yau ta sake kukan rashin idanunta. Tun Nawfal yana iya rarrashinta har ya koma ya zuba mata ido kawai. Ta kasa ci ta kasa sha, sunan Deedi kawai take fitarwa daga bakinta. Ta tabbata lokacin mutuwarta ce ta yl. Fuskarta suka kumbura suka yi suntum saboda tsabar kuka.

Washegari Mansur ya shigo gidan yana duban Nasreen, “Yanzu za ki iya aurena? Ki fara zaman takaba, ki samu ki gama so nake muyi auren gaske. Shi ya sa ban taba yunkurin cutar da ke ba. Ki zauna kiyi zaman takaba idan kika gama zan kawo malamai gidan nan a daura mana aure da ke. Allah ya jiKan Sultan yasa ya huta.”

Nasreen ta sake sa kuka mai ban

tausayi tana girgiza kai, “Deedi bai mutu ba, ban yarda ba, idan da gaske Deedi ya mutu ka dauke mu ka kaimu gida.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Harararta ya yi ya ce, “Dama ance makahon mutum shegen kafiya gare shi. Da ni aka yi jana’izar mutuwar Sultan. Don  haka ba yardarki nake nema ba. Zan fara Kirga daga yau.”’ Nawfal yana jin su bai ce komai ba, shi kadai yasan abinda yake saKawa a cikin zuciyarsa. Haka bai taba jin zai iya daukar mataki wajen ficewa daga wannan wurin ba, – sai yau dinnan da aka sanar da shi mutuwar Sultan. Kai tsaye ya fara dora laifin akansa, ~* tunda babu yadda Nasreen ba ta roKe shi ba, a kan su koma gida, amma ya Ki amincewa.
Mansur yana fita ya dubi’ Nasreen ya ce, “Nasreen. Gobe ki cewa Mansur kin amince da shi a matsayin miji.”” Nasreen ta rarumi sandarta za ta kwada masa, ya sa hannu ya amshe sandar.

Cikin zafi take magana, “Wallahi ba zan taba yin wani auren ba, tunda Deedi ya rasu me kuma zan nema a duniyar nan? Na rasa shi na rasa farin cikina. Nawfal kana ta juya min rayuwata kamar kai ka kawo ni Www.bankinhausanovels.com.ng duniya? Na gaji da irin abubuwan da kake yi ka fita ka bani wuri tun kafin fushina ya Kare akanka. Kana da yadda za ka yi mu koma gida, amma ka bar mu cikin wahala, har abin ya kwabe mana. Yanzu kana ganin waye zai iya fitar da mu a cikin gidan nan? Nawfal mutuwa zan yi, zan mutu Nawfal komai ya tsaya min, zuciyata tana yi min

ciwo na kasa amincewa na rasa tsayayyen mutum kamar Sultan. Don Allah ya zan yi? * Ya zan yi?

“Nawfal Dee shi ya dauki dukkan dawainiyar mu, shi ne gatan mu a gidan duniya. Ya juri abubuwa masu yawa saboda kawai ya faranta mana rai. Yau ga mu muna da yadda zamu yi mu isa gare shi, amma muka gwammace mu nesanta kanmu daga gare shi, muka gwammace mu katange kanmu a wurin da bai kamata ba. Idan Umma ta yi mana laifi ba za ta ci albarkacin danta mu yafe mata ba? Na tabbata Dee ba zai taba yafe mana ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

Nawfal ka fice min daga dakin nan tun kafin indaga sandar nan in kwada maka.”

Yadda ya ga tana cikin fushi ya sa ya fice kamar yadda ta ba shi umarni. Hada kansa ya yi da guiwa yana shessheKan kuka. Tana jin irin kukan da yake yi wanda bata taba jinsa yana irinsa ba. A take danasani ya shigeta, yau da babu Nawfal a rayuwarta da  tafi haka wulakanta. Ya zama dole ta yi masa uzuri. ; “Nawfal!” Ta Kwala masa kira, babu

shiri ya taso ya Karaso wurinta suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi. “Nawfal ka yi hakuri bacin rai ne yasa na gaya maka magana.. Amma kasan bamu yi wa Dee adalci ba, ba mu kyauta masa ba. Ga shi Dee ya yi kwanan Kabari babu mu a cikin masu yi masa addu’a. Nawfal gaya min kana da mafita? Ko wurin Abba ne mu samu muje na tabbata kafin mutuwarsa ya bar mana abinda za mu dinga tunawa da shi.”

Www.bankinhausanovels.com.ng Nawfal ya goge hawayensa, haka ya sa hannu ya goge mata nata hawayen da suke ta zuba. “Nasreen ya zama dole ki nunawa Mansur kin hakura kin amince da shi, ta hakane zai saki jiki damu har mu samu hanyar da za mu gudu. Ina da lambar Dee, ina da ta Abba, ban yarda Dee ya rasu ba gaskiya. Ki natsu ki bi Mansur har in . sami mafita.” Gyada kanta kawai take yi hawaye na . kwarara, bakinta ya mutu, ta ji dadin kalaman Nawfal a kan Sultan yana nan a raye bai mutu ba. Idan kuwa ya tabbata yana da rai, sai ta yi azumi uku domin nuna godiya ga Allah da ya bar mata Sultan a raye na wani lokaci.

“Yanzu Nawfal ya za mu yi? Ni na tsani Mansur dinnan duk wani mummunar labari daga bakinsa muke fara ji. Don Allah kada ka dauki lokaci wajen nema mana mafita, kuma Nawfal tuntuni kana da lambobin su Abba ka kasa kiran su?” Www.bankinhausanovels.com.ng

Nawfal ya dan yi shiru kafin ya ce, “Kuskure ne anriga anyi Nasreen sai mu tari gaba.” Bata ce komai ba, ta kwantar da kanta a jikin bango kawai tana jin sanyin simintin yana shigarta.

Sultan ya yi bala’in daukewa Zakiyya wuta, ta yadda ya rage zaman gidansa, kullum yana cikin aiki. Yau Lahadi, sanye yake da wando iya guiwarsa sai t shirt mai ° dauke da sunansa a baya. Shigar ta yi matuKar dacewa da shi, fatan jikinsa ta sake laushi sai walKiya take yi, kallo daya za ka yi masa ka fahimci yana cikin natsuwa, sai dai a zuciyarsa ba haka abin yake ba. Yana zaune a cikin garden dinsa ya_ harde Kafafunsa a kan wani yana karatun jarida. Wayarsa ce ta dan yi Kara hakan yasa ya fahimci kira ne, don haka ya dauka ya manna wayar a kunne.

Ashmaan ya ce, “Ka jira mu sati mai zuwa zamu zo gidanka. Na samo wasu bayanai akan Saudat bayanan suna da mahimmanci, don haka ne nake son mu
Www.bankinhausanovels.com.ng hadu mu dukka domin ganin yadda zamu bullowa abin.”

Sultan ya rasa bakin magana, ya rasa yadda zai fara godewa abokansa, da suka hana kansu barci saboda shi? Kafin ya yi magana har Ashmaan ya datse wayar.

Murmushi ya yi ya ce, “Girman kai a wurinka Ashmaan abin ba a cewa koma. Ibtihal ce kadai ta isa ta yi min
* maganinka.” Zakiyya da ta dade tsaye akansa tana – Kare masa kallo, ta lumshe idanunta tana jin waye ya kaita sa’an miji? Dogo ne tsayayye mai faffadar Kirji. Yana da haske irin hasken nan mai kyau da daukar hankalli. Hancinsa ya dace da bakinsa.

A hankali ta Karaso tana washe hakora. “Ina son magana da kai.” Ta fada masa tana tsaye a kansa tana yi masa wani shu’umin kallo wanda yasa ya tamke fuska. “Ina jinki. Kuma ke baki iya gaisuwa bane? Menene na tsaya min akai haka?” Www.bankinhausanovels.com.ng Zagayowa ta yi sannan ta gaida shi, bai amsa ba, haka bai daina kallon ta ba. Shi tunda yake anya ma ya taba ganinta babu kwalliya? Har yanzu ba zai ce ya taba ganin asalin fuskarta ba. “Dama ina son ingaya maka ne, ni ba zan iya jure rashin kusanto ni da kake yi ba, sai ka dinga ja baya da ni sai kace ba matarka ba. Ina da buKatar mijina.” Sultan dai yana ganin abin al’ajabia_ – duniyarsa, “To na ji ki shiga ciki zan zo.” Babu musu ta mike tana tafiya tana » yanga, abinda bata sani ba, ko daga kansa bai yi ba, bare har ya dubi 1rin takun da take yi. Tunani ya yi tunda yarinyar nan ga kalarta gara ya yi iya yinsa ya sauke hakkokinta tun kafin watarana ta kawo masa Kato cikin gida. Rintse idanunsa ya yi kasancewarsa namiji mai tsananin kishi musamman a kan abinda ya shafi iyalansa. “Ta kawo min wani gidana? Ashe da na kashe ta kowa ma ya huta.” Yana jin dadin yanayin wurin don haka ya kasa tashi yana nan zaune har sai da Www.bankinhausanovels.com.ng ta sake dawowa. Babu shiri ya mike sam ba ya jin sha’awar komai, haka ya same ta. Maganin da ta shafa a jikinta shi ya rinjaye shi har ya aikata abinda take so.

Wani abu da Sultan ya gama fahimta da Zakiyya shi ne ba ta Sallah kwata-kwata hakan ya tashi hankalinsa har ta kai yau ya yi mata magana, “Wai ke me yake hanaki Sallah ne? Kina nufin in zauna da kafira a

” cikin gidana? A’a ba za a yi hakan da ni ba, idan baki iya bane zan tattaraki da direba ya * kai ki gidanku ki koyo yadda ake ibada, kafin mu iya zaman aure. Domin bana jin ko wankan tsarki kin iya yi.” .

Idanun Zakiyya ya raina fata sai – girgiza kai take yi alamun babu inda za ta je. Tsaki ya ja ya fice daga dakin kawai. Washegari ya gama shiryawa zai wuce aiki, yana fitowa Zakiyya ta fito da gudu kamar mahaukaciya ta kama _ Kafar wandonsa. Kunya ya kama shi, ya kafeta da ido kawai. Yau babu kwalliyar a fuskarta, hakan yasa ya fahimci dalilin da yasa take Www.bankinhausanovels.com.ng kwana da kwalliya. Kallon ‘yan sandan shi kawai ya yi gaba daya suka watse. Dubanta ya yi cike da takaici ya ce, “Me yake damunki ne Zakiyya? Baki ganin ina gaban yarana ne? Me kike tunanin abinda kika yi zai jawo min? Kada ki sake yi min haka.” Kin sakinsa ta yi tana magana cikin kuka, “Wallahi zan dinga yin Sallah kada ka ce inkoma gidanmu.” Sai yanzu ya fahimci dalilin haukan da take yi, “To koma ciki.” Sakinsa ta yi ta kama hanyar cikin gida, ya bi bayanta da ido. Ya tsani ya ga mace tana sanye da riga daban zani daban, amma Zakiyya kamar hakan ya zame mata jiki, za ta yi kwalliya yadda ya kamata ta dauko riga daban zane daban ta sanya, ita kuma ba ‘yar kauye ba. Tunda tazo gidan bai taba cin wani abu da ya shafi girkinta ba, ita kanta baa bin arziki take dafawa ba, wataran kuma ta ba masu gadi kudi su yo mata order. Shi ya sa yake ta tunanin yadda zai yi da su Ashmaan da suke shirin zuwa

Www.bankinhausanovels.com.ng gidansa, kuma ya tabbata za su zo ne daga nan su ci abincin amarya. Ya zama dole yasan yadda zai yi kafin ranar tazo idonsa ya raina fata. Yana kan hanya ya kira mahaifinsa a waya suka fara tattaunawa akan matsalar su Nasreen. Abba ya nisa ya ce, “Sultan mutanen da suka bace menene amfanin bin diddigi akan Saudat?” Sultan ya shaki iska ya fesar, “Abba
“na yi wa Anti Saudat alKawarin zan Kwato mata ‘yancinta. Ko su Nasreen suna nan, ko  basa nan, sai na nemo wanda ya kashe Anti Saudat na hada shi da hukuma ta hukunta shi dai-dai da irin laifinsa.” Abba ya gyada kai ya ce, “Idan kuma mutumin ya mutu fa?” Sultan ya ce, “Irin wadannan azzaluman Allah yana jinkirta mutuwarsu domin suga ishara tun a gidan duniya. Abba ka bari duk yadda al’amuran suka kasance zan sanar da kai insha Allahu.” Suka yi Sallama ya ajiye wayarsa. Duban yaransa ya yi ya ce, “Ranar Lahadi Www.bankinhausanovels.com.ng insha Allahu za ku nemo min ma’aikata masu aikin abinci za su kawo mana lunch, ina da baki.”
Da girmamawa suka amsa masa.

. Sultan ya Kurawa gefen titi idanu, har yanzu yana nan da halayyarsa na son kallon gefen titi. Haka abubuwan da suka faru shekarun baya suna nan manne a ransa sun Ki gogewa. Yana jin yanzu ne zai dauki fansa akan koma waye ya ingiza rayuwar Saudata ° cikin Kunci.

Nasreen tana zaune a gaban Mansur ° ya ajiye mata nama zuciyarsa cike da farin cikin yadda Nasreen ta kwantar da hankalinta. Doguwar riga ya kawo mata ya ce ta sauya wanda za ta yi zaman takaba da ita. Yana fita ta rungume doguwar rigar ta shaki kukanta yadda ranta ke so. Sannan ta sauya kayan kamar yadda ya buKata. Bata san ya shigo ba, sai muryarsa ta ji, “Kin yi kyau sosai. Bari ki gama takabanki za ki ga yadda zan mayar da ke Nasreen. Idan har za ki dinga bani hadin kai ni kuma zan mayar

HMMM MUN SHIGO BOOK2 FA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *