RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Hajiya Ladidi da Hajiya Salma sun shirya zuwa don haka ta ce ta kwantar da hankalinta tana nan zuwa. Kwanaki biyu a tsakani Umma suka iso cikin shigar alfarma. Kallo daya za ka yi masu kasan naira ta yi kuka a wurin su. A

Www.bankinhausanovels.com.ng Kalla idan ka tsaya duba nairorin da ke jikinsu za ka iya Kiyasta dubu dari biyar zuwa sama. Zakiyya ta fito da gudu daga ita sai rigar barci, a lokacin Sultan yana amsa waya, ya dubi su Umma ya Karaso gabansu.

Ganin Zakiyya yasa ya bi shigarta da kallo cikin tsananin bacin rai. Yana kallon yadda ‘yan sandansa suke kawar da kai. Irin kallon da yake mata yasa Umma da Hajiya Ladidi suka dubeta, ita kanta Umman ta ji babu dadi, domin ita ta tsani rashin tarbiyya irin wannan. Babu wanda ya yi magana har suka shiga ciki a tsakiyar falo Umma ta fara magana, “Ke Zakiyya wani irin rashin hankali ne wannan? Me zan gani? Haka kike fitowa a gaban wadancan mutanen masu kama da dogare? Ni bana son rashin tarbiyya sam!” Hajiya Ladidi da ranta ya baci ta danne tana dan murmushi, “Amma dai ke baki da hankali. Me zai sa ki fito kai ko dankwali babu?”

Sai a lokacin Umma ta kai duba akanta, idanunta suka dinga nuna mata ta yi

ZAMU TASHI 

Kari, don haka tasa hannu ta yamutsa gashin kanta, sai ga dinkin atachimen a tsakiyar gashin kanta.

Da Karfi Umma take Salati tare da zazzaro idanu, “Yanzu Karin gashi kike yia gidan nan? Gashin doki? Zakiyya da wannan abun kike zuwa gaban Allah kina gaida shi?” Hannunta ta fizgo tana duba Kumbunanta. Umma fa ta gigice sosai, “Kumban nan da su kike Sallah? Hajiya Ladidi ina tsoro gaskiya! Kin san halina kin san abinda na tsana da wanda nake Kauna. Ya kamata Zakiyya ta gane bambancin Musulmi mai Sallah, da kuma wanda yake zaune zaman kafirci, wato mara addini. “Zakiyya ta yi tsuru-tsuru ta kira Umma domin ta Kwatar mata ‘yancinta, amma sai ta buge da wulaKanta ta a gaban Sultan. Dole dabara ta zo mata, ta ce, “Lahh ji yadda Umma ta rude. Jiya ne da naga bana Sallah shi ne na ce bari indanyi ado. Ai nima bana sawa Wallahi, kawai nace ne bari inkwatata tunda bana Sallah.”

Www.bankinhausanovels.com.ng ta dan saki ajiyar zuciya, “Yanzu na ji magana. Amma duk da haka kada ki sake sawa kin ji Zakiyyata? Kada ki yarda su rinjaye mu gara mu su dinga ganin abubuwan mu suna yin koyi da mu. Kai kuma ka tsaya kana kallon mu ko magana babu. Ai da naga kana amsa waya ka bani mamaki. A zatona ciwon kunne kake yi shi ya sa baka amsa waya, ashe wanda ka raina

‘ ne baka amsa masa.” Murmushi ya yi sannan ya gaida su ya ‘ dora da cewa, “Ina amsawa. Abubuwa ne idan suka yi mana waya bamu sanin ma inda muka ajiye wayar.”

Umma ta yi Kwafa ta ce, “Rufe min baki. Ina jin ka kusan kullum sai kayi waya da mahaifinka. Wato shi ne naka ni kuma ko oho ko? Allah ya yi Haidar magana duk da yana wajen training dinnan duk san da ya samu dama sai ya kirani yana jaddada min irin kewata da ya yi. Yanzu gidan babu dadi daga ni sai Auta, daman ita daga Makaranta sai daki ne baiwar Allah samarin ma taki

Www.bankinhausanovels.com.ng kula su duk wanda ya zo sai ta ce sai ta gama Makaranta.” Sultan ya nufi fridge ya kwaso masu abubuwan sha, tunda ya kula Zakiyya bata iya taran baki ba. Sai da ya dawo gaban umman yana ajiye lemuka, sannan ya ce, “Umma kenan. Ita ba za ta yi aure ba, sai Karatu kawai? Ai kamata ya yi a yanzu a ce Hafsat tana dakin mijinta.

A Kalla tana cikin shekaru ashirin da hudu kenan a duniya.” – Umma ta zaro idanu, “Duka-duka Hafsat din nawa take? In aurar da ita bakin cikin ~  ya kasheta ko? Ai gasu nan muna gani auren yanzu duk babu dadi, kai kanka cutar da ‘yar wasu kake bare har indauki ‘yar tatsitsiya kamar Hafsat inbada ita a kashe min ‘yata. Bari dai idan ta isa yi sai in aurar da ita amma ba yanzu ba. Ada ne nake wannan tunanin amma a yanzu na tsorata.” Sultan ya kama hanya zai fita, Umma ta kirawo shi ya dawo yana dubanta, “Yanzu fita za ka yi Sultan? Ai ka bari mu dan yi hira tukun ko?”

Makullin mota yasa a kunne yana sosawa, sannan ya ce, “Zan aika ayo maku Order din abinci ne, Zakiyya bata jin dadi shi ya sa ba za ta iya girki ba, tana fama da yawan jiri da ciwon kai.”

_ Zakiyya da’Hajiya Ladidi ji suka yi kamar su sa Sultan a Aljannah domin suna zuwa Zakiyya ta fara yanka idanu tana tsoron kada Umma tasan bata iya girki ba.

– Haka sun dauki wani matsayi mai girma sun dorawa kansu akan Sultan yana sonta ne shi – ya sa ya ‘kareta.” Shi kuwa_ mitar mabaifiyarsa né baya so yasan idan ta sani _yau babu mai barci a cikin gidan. Ita kuwa _umma gabanta ne ke fadiwa kada yazo Zakiyya ciki gareta, domin tazo da magani ‘don ta, sake sanya mata a cikin tsumin mata ta bata tasha a matsayin za ta gyara ta. Tunawa da. abinda Zakiyyar ta fada na cewar tana al’ada yasata dan saki ajiyar zuciya. Yana fita’ ta ‘yafito Zakiyya tana. wani shu’umin murmusHi ta ce, “’Yata ko + dai ciki gareki ne? Ko,da yake da kina da
ciki ai da ban ji kin ce kina al’ada ba, duk da wasu suna yi ko da cikin.”
Zakiyya ta yi dariya ta ce, “Babu komai Umma.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
A nan hira ya barke masu kamar Kawayen juna, har Umma ta ci nasarar bankawa Zakiyya magungunan hana daukar ciki. Ita kuwa Hajiya Ladidi dadi ya Kara kamata ana son ‘yarta. Hajiya Salma ta dan dube ta ta ce, “Kin ga ki kwantar da . hankalinki Sultan ba zai sake ganin Nasreen ba, ta tafi kenan. Mansur ya tabbatar min – yana bata dukkan tsaron da ya dace da ita. Babu inda ta isa ta fito ko nan da Kofar gida. Abinda nake so da ke a yanzu ki dage da tsafta. Gidan nan sam ba a tsaftace shi. Ke kanki baki gyara kanki shi namiji ai dan gyara ne. Da zarar yasa hancinsa a wani wuri ya ji da wari shi kenan kin zube masa.”

Zakiyya ta dinga amsawa da to. Shi kuwa Sultan mamaki ne ya kashe shi ganin gashin Zakiyya ba gashinta bane. Shi kwata-kwata bai taba kula ba, gani yake yi

yarinyar Allah ya bata gashi, har yana yaba wa gashinta. Wannan shi ne acuci mazan kenan.

ee KKK KK

A bangaren su Nasreen kuwa sun gama tsara komai yau suke son su gudu. Sai da suka tabbatar da masu tsaron nasu suna daga bakin Kofar tsakar gida, Mansur kuma baya nan. Nawfal ya kamo hannun Nasreen suka kama hanyar shiga bandaki. Suna ‘ shigewa Nawfal ya fara taimaka mata ta dira ta baya, hakan yasa ta taka Kusa ta ” – toshe bakinta saboda irin azaban da take ji har tsakar kanta. Nawfal ya bi bayanta ya dubi Kafafun da suka fara zubar da jini. Ga Magriba tayi, don haka ya fizge mata ta sake toshe baki tana hawaye. Shi kuwa sai fadin sannu yake babu KakKautawa. Tausayinta yake ji da gaske. A haka suka taka har suka isa wani lungu ya fita ya samo ruwa suka yi alwala. Bayan sun idar da SaHar ne suka yi addu’a suka shafa.

Nawfal da Nasreen ba sa wasa da sallah idan lokacinsa ya yi. Haka idan ta fara al’ada shi yake zuwa ya samo mata tsumma, sai dai bata yarda daga wannan ya sake taimaka mata ba, tun tana jin kunyarsa har ta saki, domin babu mai taimaka mata sama da shi, shi kadai ne dolenta. Wani Kyalle ya samu ya daure mata Kafarta sosai ta yadda jinin ya matse baya iya fita. Tafiya suke babu ko waiwaye, domin garin Kauye ne babu abin hawa wadatacce, haka za su iya kiran garin da Dajin Allah, mutane . Kalilan ne.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nawfal ya tari mashin, yana son ya kai su cikin gari, sai dai bashi da ko naira da zai basu. Tunani kawai ya yi idan mutumin ya kaisu inda ya kamata suna sauka su ce basu da kudi. “Ina sake jan hankalin ku, ku guji abinda ba naku bane, ku guji cutar da musulmi koda da kalaman bakin ku ne. Daga Karshe kada ku ci hakkin wani, domin bashi ne watarana za ku biya a inda baku da shi.”

Nasreen da take riKe da hannunsa daya ta dan girgiza shi, “Nawfal! Tunanin me kake yi? Bamu da sauran lokaci fa. Mu yi sauri mu gudu kada su biyo mu.” Mai mashin din ya ce, “Ka tare ni kuma ka tsaya dogon tunani. Idan ba za ka je ba ka gaya min intafi.”

Nawfal ya girgiza kai hawaye kwance a Kwayar idanunsa, “Ka yi haKkuri ka tafi. Na tuna bamu da kudin mashin.” Mai mashin din ya dube shi, “To ku hau muje insauke ku a bakin titi domin nima can na nufa.” Cike da farin ciki, ya saita Nasrcen ta hau, sannan ya hau bayanta. Sun yi tafiya mai tsawon gaske, hakan yasa Nawfal ya dinga godewa mai mashin din yana jinjina Irin nisan wurin da titi. A bakin titi ya sauke su, Suna ta yi masa godiya har ya bace wa ganin su. Wajen wani mai gyaran robobi ya nufa ya roKe shi yana son ya ara masa wuKa zai gasawa ‘yar uwarsa Kafafu ne. Babu musu ya bashi, Nasreen ta zauna daga wani wuri da ta hango ankunna fitila.

A nan ya dinga gasa mata Kafa yana mamakin yanzu har isha’ ta yi amma mai likin roba yaki tashi ya haKura hakannan. Sai da ya gama gasa mata Kafar sannan ya maida masa wuKar yana godiya.

Nasreen ta yi magana cikin galabaita, ““Nawfal ka matso inkwanta a kafadarka ina jin numfashina yana kasa min.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nawfal ya goge hawayensa ya dan kwantar da ita a jikin bishiyar ya nufi wani_ wuri ya roKi ruwa sannan ya dawo ya bata. Tasha sosai sannan ya ce, duk su yi alwala su yi Sallah isha’1. Bayan sun idar ne suka mike suka ci gaba da tafiya cikin duhun nan. Nasreen tana makale da Nawfal kamar tana tsoron wani abu ya same shi. Wata mota ce ta tsaya a kusa da su, ba tare da sun tsaya tantance irin motar ba, aka fizgo su ciki. Jin Nasreen tana ihu yasa suka fesa masu wani irin fauda, tun daga nan basu sake sanin inda kawunansu yake ba.
Tunda Sultan ya fita siyo abinci bai sake waiwayo gidan ba, domin sako ya
baiwa Dan sanda yaje ya yi order ya kawo cikin gidan. Tun Umma tana sa ran ganinsa har ta cika ta yi tam! Bayan Isha’i ya shigo gidan ya tunkaro Umman da suke zaune a falon suna kallon film.

Umma ta ce, “Ni? Abdullahi ni za ka wulaKanta? Da ni kake zance.”

Sultan ya dubeta yana murmushi, “Umma yau kuma Abdullahi kai tsaye?

– Babu ruwana idan Baba Mu’azzam ya jiyo ki.” Harara ta sakar masa ta kawar da kanta.

– “Ki yi hakuri Umma a office aka kiramu muka yi ganawa da Shugaban Kasa, kan tabarbarewar hanyar nan _ shawarar yadda ya kamata mu biyo wa lamarin.” ya Dubi Hajiya Ladidi ya ce, “Mama baki da buKatar komai ko?”
Hajiya Ladidi aka saki fara’a mai nuni da ta ji dadin kulawar da Sultan ya bata, “Ba ni da tunanin komai Sultan an gode.” Hajiya Ladidi ta jawo ‘yarta saboda su baiwa Umma da Sultan wuri, domin sun ji ta ce, jiransa take yi sai ta yi masa ta tas

akan Zakiyya. Suna tashi suka ci gaba da hirarsu tsakanin da da mahaifi sai Allah. A cikin hirar ne take ja masa kunne akan rike amanar Zakiyya. Ta kuma tambaye shi ya ya halayyar Zakiyyar take?”

Ya dubeta ido cikin ido ya ce, “Umma ni yaushe na zauna da ita ‘bare insan halayyarta? Saboda ita ne ma nake Kwace kaina da Karfin tsiya nake dawowa, amma bani da lokaci.”
Umma ta zaro idanu, “Wani irin aiki ne haka Sultan da ba zai baka dama akan – iyalanka ba? Shi ya sa na gaya maka na tsani aikin dan sandan nan.”

Shafa kansa ya ci gaba da yi yana lumshe idanu, “Umma da yake nayi aiki sosai ina da buKatar inhuta. Barci zan je inyi.”

Umma ta sawa idanunta toka ta ce, ita babu inda zai je ta dade bata ga danta ba, ya zama dole yau su yi hirar abubuwan da ke faruwa. Bai musa mata ba, shima yana bukatar mahaifiyarsa da ya rasa kulawarta
Www.bankinhausanovels.com.ng
tun yana dan shekaru goma sha biyar a duniya. Ya rasa gane dadin uwa sai a ‘yan tsakanin nan. “Yaya maganar Nasreen? Yarinyar nan bata san da akwai aurenta a kanka ba, zai fi kyau ka saketa saki uku, ka ga ko ta yi wani auren babu laifi, amma yanzu kana barinta da kaya ne a kanta. Ga hukuncin aikata zina, ga hukuncin laifi mafi – girma, wato igiyar aure. Idan da gaske kana son Nasreen zai fi kyau ka tsinka igiyoyin – auren da ke tsakaninka da ita.”

_ Sultan yana ji a duniya mahaifiyarsa ce kadai za ta iya fadin hakan a kan Nasreen bai dauki mummunar mataki a kanta ba. “Umma waye ya gaya maki Nasreen tana aikata zina? Umma shaidar zina akwai wahala. Shi ya sa ake son ka kyautatawa mutum zato. Kamar misali Zakiyyar nan kowa ya ga girmanta da yadda idanunta suke a bude sai ace ‘yar iska ce, bayan ba haka bane.” Umma ta ji dadin wannan yabon da Sultan ya yi wa Zakiyya, haka ta rage fargaba, tasan halin Sultan idan

dai akan gaskiya ce sai ya fada sai dai a mutu. Amma dai duk da hakan hankalinta bai kwanta ta hada zuri’a da Zakiyya ba. Mikewa ya yi ya ce, “bobe fitan asuba zan yi. Mu kwana lafiya.” Ya shige dakinsa ta bishi da idanu kawai. Yana shiga ya sami Zakiyya har ta yi Sallama da iyayenta tazo wajensa. Babu musu ya biye mata har ta sami natsuwa. Ya rasa dalilin yadda shi kwata-kwata baya samun irin gamsuwar da ya kamata da ita. Yana jinta tana shirgar barci, amma kuma shi barcin ya ‘ gagare shi. Tashi ya yi ya shige bandaki ya yi wanka ya natsa, sannan ya dauko Alqur’ani yana karantawa. Yana _ kallon agogo har biyu ta gota, ya tashi ya sake alwala sannan ya tada Sallah. A gaban Allah yake cikin rauni da KasKantar da kai, yana yiwa Allah kirari, daga bisani ya kwararo buKatansu wanda dukka a kan Nasreen ne da Nawfal. Yana ji a jikinsa suna nan a raye, amma kuma ba a cikin natsuwa ba. Ya jima yana kwararo addu’o’i cikin salon

_ Qira’ar Sudais. Bayan ya yi addu’ar Istahara ne akansa da Nasreen ya yi kwanciyarsa a nan yana Salatin Manzo har barci ya dauke shi.

A wata sassanyar lambu me, ma’abota ‘ya’yan bishiya masu kyau da_ sanya sha’awa. Yanayin wurin yana kadawa a hankali alamun ruwa yana iya kecewa a ko wanl irin yanayi. Yanayin ya sanya masa mugun kasala da dogon tunanin da kullum a cikinsa yake.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nasreen ta Karaso cikin shigarta na vest da wando wanda suka yi matuKar dacewa da jikinta. Kanta babu dankwali don hakane gashin yake a tubke a tsakiyar kai. Tun dazu take nemansa amma ta rasa inda ya Buya. Ganinsa a kwance yasa ta Karasa a hankali, ta kwanta kusa da shi, ba tare da ya ankare akwai mutum a kusa da shi ba. “Amincin Allah su tabbata a gareka, ya kyakkawan mijina, mai rikita ‘yan mata.”

Ware idanunsa ya yi ya juyo yana dubanta tana kwance, kuma sama take kallo.

“Kina ganin na cancanta ki nema min aminci? Na barku a lokacin da kuke da buKatata, na Ki yin abinda ya kamata domin nemanku.”

Ita ma waiwayowa ta yi suna shaKar numfashin juna, domin bata san sun zo daf da juna haka ba. “Ka yi iya yinka Deedina, sai ka zuba ido ka barwa Allah sauran. Mu ne muka yi maka laifi, a lokacin da muke da_hanyar da zamu iya nemanka bamu yi hakan ba. Abinda nake so da kai, addu’ar nan da_ – kake yi mana kada ka daga Kafa da rana daya ka ci gaba da yinsa watarana sai labari.”

Hancinta ya dan ja, ya ce “Wai wa ya koya maki magana ne? Nasan ki magana ma wahala take yi maki.” Juyar da fuskar ta yi tana kallon wani abu can ta ce, “Malamina ne ya koyar da ni tun ina jaririya.”

Hannunsa yasa ya juyo da ita yana
Www.bankinhausanovels.com.ng
murmushi, “Yanzu kin fi malaminki iya komai, kin fi shi iya tsara zance.”

Ta kasa jurewa irin sakon da yake aika mata cikin salonsa na dauke hankalin duk wata mace da ke kusa da shi. Da rabin hakan ya dauke hankalin Zakiyya da take jin za ta iya daukar wuKa domin yaki da ko wace ce a kansa.

A hankali ta yi magana cikin sanyinta, “Idan kana gefena, kana katange

-ni daga dukkan damuwa, damuwa tana samun muhallin zama ne a zuciyata da zarar * kayi min nisa. A lokacin ne nake jin kaina yana KoKarin raba kansa da jikina. Da ace zan 1ya yin ihu inyi shela inkirawo mutane su amsa kirana, da na ambaci mijina a gaban dubban jama’a a matsayin gwarzon da babu irinsa. Da zan sami dama, da na shiga daji, na kirawo za ki da kura, da dukkan wani nau’in ababe masu rayuwa a cikin dokar daji, in tambaye su akwai za ki kamar mijina? In tambaye su da kai da su waye jarumi kuma waye gwarzo?” Sosai ta hada fuskarsu wuri guda, numfashinta yana sauka a bisa hancinsa, “Na tabbata amsar

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *