RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Sultan yana nan zaune yana kallonta. Farin ciki ya tsirga masa. Yumnah ta gaya masa babu wata matsala mai girma, amma abin mamaki sai yanzu Nasreen ta farka. Hannunta da taji a hannun mutum yasa ta yl shiru. Ta dora tunaninta akan abinda ya faru kamar cikin Mafarki. Ko mutuwa ta yi ta dawo, inhar Sultan zai zauna a wun kawai ya tashi sai ta gane, bare kuma ace wai yana kusa da inda take. Ta gigice da 


yawa, sai kama hannunsa da tayi, “De… Don Allah Dee kayi min magana. Kana kusa da ni kai ne, hannunka ne. Dama dama zan sake jinka a kusa da ni? Deee..” Www.bankinhausanovels.com.ng 


Cike da nishadi, ya sa dayan hannunsa ya lakaci hancinta, “Deee… Ga Dee a kusa da Nasreen dinsa. Bana son kuka, baki da lafiya ki koma ki kwanta kin ji?” 


. Babu abu daya da ta iya aikatawa a cikin abinda ya ambata mata. Sai sake jawo Www.bankinhausanovels.com.ng 


shi ta yi ta kwantar da kanta a bisa kafadunsa. “Dee kada ka sake barin a rabamu da kai. Mun sha wahala. Nawfal ya yi Kokari, Dee ina Nawfal? A dawo min da dan uwana kusa da ni.” 


Zuba mata ido ya sake yi yana kallon yadda Kasusuwa suka fito mata kwance a wuyanta. Ko bata gaya masa ba, ya san sun sha wahala. Hannu ya sa a cikin gashinta da duk suka dunkule saboda wahala, “Allah ya yi maku albarka. Allah ya sakawa Nawfal ya baki ikon kyautata masa. Nawfal yana nan kwance kusa da gadonki bai da lafiya, 


ZAMU TASHI 

ki kwantar da hankalinki dukkanku ina kulawa da ku, insha Allahu ba zan sake barin ko da kuda ne ya cutar min da ku ba. Koma ki kwanta ki daina kukan nan kin ji? Idanunki idan kina kukan nan za su sake rufewa ne idan aka zo yi maki aiki asha wahala.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Nasreen ta koma ta kwanta tana ajiyar zuciya, a natse kuma ta fara magana, “Idan wannan ne Karshen ganina a iduniya, inhar ‘ ina tare da kai ba zan damu ba. Ina cikin wahala da tashin hankali ma, ban damu ba, ~ bare yanzu da Allah ya kawo min Karshen wahalata. Dee har matsafa sun sa min kayan da za su yanka ni, idan kayan jikina jajayene har yanzu to sune kayan da aka sa za a yanka ni.” Sultan ya shiga rudu da tashin hankali, don haka ya dubi kayan jikinta a gigice. Sai dai ba su ba ne a jikinta Yumnah tasa an sauya mata kayan jikinta da doguwar riga wanda ta aika aka kawo mata. Ya dan rintse idanunsa yana mayar da ajiyar

zuciya. “Allah ka Kara bamu kariya da ikonka da isarka.”

Nasreen ta dinga surutai har barci ya sake yin awon gaba da ita. A lokacin ne kuma Nawfal ya motsa tare da ware idanunsa. Daman tun suna Kanana Nasreen ke fara tashi, idan ta koma Nawfal zai bude nasa idanun. Sultan bai san ya farka ba, kawai yaji a jikinsa ne ana_ kallonsa. Juyowan da ya yi suka yi ido hudu. Nawfal ya cika da al’ajabin wannan lamari. KoKarin

» dole sai ya tashi yake yi yaje ya rungume shi, sai akasin hakan domin Kafafunsa sun . rike kuma suna yi masa zogi. Da ka kalle shi za ka tabbatar da cike yake da wani irin matsanancin farin ciki. Sultan ya Karaso har gaban gadon yana murmushi. Www.bankinhausanovels.com.ng

Suka rungume juna Sultan ya dinga shafa kansa yana jin Kaunar yaron yana sake ratsa shi. “Allah ya yi maka albarka Nawfal.” Abinda bakinsa yake ta maimaitawa kenan babu tangarda.

Nawfal ya fara zubar da hawaye, domin ya rasa a cikin masu sa’a su din wasu iri ne? Bai taba tunanin zai sake yin ido hudu da Sultan ba. “Deedi we really miss you. Please Deedi forgive us for our mistakes!”

Sultan ya shafi kansa yana bubbuga bayansa, “Be a Man. Stop saying that! Ka gode wa Allah Nawfal babu abinda kuka yi min.Ka daina bari hawaye suna zuba a, idanunka, kada ka zama ragon maza. Mata aka sani da kuka ba namiji ba. OK?”

Nawfal ya shanye wani irin kuka da ya taho masa aguje. “Ok Decdi. Ina Abbana?”’

Bubbuga bayansa ya ci gaba da yi kamar mai lallashin yaro Karami, “Abba is fine! Go back to your bed please.” Babu musu ya koma ya kwantar da kansa ba tare da ya saki hannun Sultan ba. Haka idanunsa tunda suka kalli Nasreen ya kauda idanunsa yana ci gaba da kallon Sultan, ya tabbata Nasreen tana cikin kyakkyawar kulawa

tunda har Sultan yana kusa da ita. Rufe idanunsa ya yl yana son yin magana, amma yadda Sultan ya kafe shi da idanu yasa ya kasa Kwakkwarar motsi har sai da barcin ya sake kwasarsa. Sultan ya yi ajiyar zuciya ya mike ya shige bandaki ya dauro alwala domin sake mika godiyarsa ga Allah. Www.bankinhausanovels.com.ng

Haka Sultan ya yi ta zarya a kan su

” Nasreen ya kuma Ki gayawa kowa abinda ke faruwa. Har yau dinnan da aka sallame

* su yana wurin aiki don haka ya ce Yumna ta wuce da su kawai zai biyo baya.

Abinda Yumnah ba ta sani ba, tuni Sultan yasa “yan sanda su bi bayansu har su raka su gida, haka ya sa wasu gadin gidan Aslaf. Mamaki ya kama Aslaf da masu gadin gidansa suka koma ‘yan sanda. Nawfal aka sauke shi a bangaren baki, ita kuma Nasreen suka wuce da ita ciki. Yumnah ta zage ta fara gyara Nasreen babu ji babu gani, haka tana yi tana koya mata wasu abubuwa ta hanyar yi mata bayanin su. Hatta rayuwar aure da yadda ya kamata

ta riKe mijinta sai da Yumnah ta karanta mata. Haka ba ta yi. bayanin banza ba, domin duk abubuwan da take gaya mata suna nan a cikin KwaKwalwar kan Nasreen. Sai yamma likis Sultan ya taso daga Office a gajiye kai tsaye gidan Aslaf ya wuce. Yana fitowa daga Motar ya hango Nawfal ya zauna ya yi tagumi shiru, da alamun ma bai san ya shigo ba. Cikin takunsa na isa, ya * Karaso har gabansa ya durKusa yana sake nazarin yaron. “Nawfal me ya yi maka zafi ” haka?”

Dago kansa ya yi cike da hawaye, “Deedi ina son ganin Abbana ina son inyi masa wata tambaya.”

Gaban Sultan ya fadi da Karfi, ya daure ya sake zuba masa ido, “Me za ka gayawa Abba bayan ga ni? Nawfal ka taimakeni ka kwantar da hankalinka a cikin gidan nan, zuwa wani dan lokaci zan kwashe ku muje gaban Abba. Idan na kaiwa Abba ku a irin wannan yanayin ciwon hawan jininsa yana iya tashi saboda bakin

ciki. Ka saki jikinka nan gidanku ne, duk abinda za ka yi a gidana a nan gidan ma za ka yi mafiyinsa.”Www.bankinhausanovels.com.ng

Nawfal ya gyada kai, kafin ya kamo hannunsa suka tashi suna jerawa. Duk wanda ya gansu zai rantse da Allah yaya da Kaninsa ne, haka kamannin su da juna ya sake fitowa fes! Sai dai wasu abubuwa da Sultan din zai nunawa Nawfal, musamman ta fuskar shekaru. A bakin babban falon suka yi Sallama, Nasreen ce kadai zaune da sandarta a gefenta. Fuskar nan dauke da matsanancin farin ciki. Tokarewa ya yi a bakin Kofa yana kallon yadda ta yi kyau, , duk da haskenta bai fito ba. Yadda ya kashe ta da idanu yasa Nawfal zame kansa ya fice ya koma gun ‘yan sandan. Bata dauki sandar ba, ta miKe tana bin Kamshin turarensa. Har ta kusa taba shi ya lallaba ya sauya wuri. Ta sake bin inda ya tsaya ya sake kaucewa. Yana tsaye sai murmushi yake aika mata, zai so idanunta suna bude ne. Tuni ya ji damuwa ta lullube shi, baya

son ya yi mugun baki a kan wanda ya aikata mata hakan, domin jikinsa yana ba shi Ummansa ce ba wata ba. Cikin muryarta mai sanyi take magana, “Ka gani ko? Wallahi Deedi sauya wurin tsayuwar kake yi don ka ga bani da ido bana gani.”

A natse ya Karaso gabanta ya jawo hannunta ya hade ta da jikinsa ya rungume. Dukkansu suka saki ajiyar zuciya KakKarfa. Nasreen da bata taba tunanin wannan ranar za ta zo ba, ta sake shige masa sosai tana jin saukar hawaye a idanunta. Bai iya hanata kukan ba, domin shima da yana da iko da ya Sanya su sun zubo ko zai huta da radadin da yake ji a zuciyarsa. Sannu a_hankali tsayuwar tana neman gagararsa don haka ya jawota zuwa kujera suka zauna. “Ina Yumnah take?” Ya tambaye ta yana dubanta.

Ta ba shi amsa da tana ciki, don haka ya dan yi shiru kamar mai nazari. “Share hawayenki ki daina kuka inbaki wani laban mai dadi.” Babu musu ta share hawayen ta

kwantar da kanta a kafadarsa. “Ki daina kuka kin ji? A duk lokacin da kika tuna wani abu kiyi fara’a ki godewa Allah. Dukkan abubuwan nan da_ suka faru. jarabawa ce, ke malama ce kin sani dole sai‘ mun shiga aji mun dauki darasi, daga nan kuma jarabawa ta biyo baya. Kuka ba ita bace mafita, haka idan kina tayar da  hankalinki ba za ki murmure ki yi Kiba ba, bare har indauke ki zuwa wajen Abba.
Kinga muna da tafiya zuwa Lagos, amma saboda ke na kasa tafiya, idan kina kukan nan sai intafi abuna, amma idan kika kwantar da hankalinki sai mu zauna muyi ta shan hira, kina yi min labari’ da wannan muryar taki mai dadin sauraro.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Murmushi ta sakar masa. Mamakin yadda take maKale masa ya_ ci gaba da kama shi, yarinyar da a idanunta idan ka kalla za ka tabbatar da tsoron Sultan ne kwance a cikin su. Shi bai san cewar tasan ita matarsa ba ce, haka ya rasa ta hanyar da zal gaya mata. Danna wayarsa ya yi ya kira

daya daga cikin ‘yan sandarisa ya ce a kira masa Nawfal. A lokacinne kuma Aslaf da Yumnah suka shigo falon. Ya daure fuska sosai ya ce, “Mene ne haka? Ai sai ku tsaya kuyi Sallama inbaku izinin shiga, ba wai ku fado mana daki haka kawai ba.”

Nasreen tana KoKarin janye jikintadaga na Sultan, amma sai ya: hana hakan. Aslaf suka dubi juna da Yumna sannan ya – ce, “Duk irin sallamar da muka yi bai gamsar da kai ba?” | ,

Dukkansu suka nemi wuri suka zauna, suna kula da yadda Nasreen taki sakin jikinta hakan yasa ya Kyaleta ta raba kanta da jikinsa. Sultan ya dubi Aslaf ya ce, “Dokto wai kuwa kunsan ranar da aka buge su Nasreen a mota daga gidan matsafa suke?”

Daga Aslaf har Yumnah suka zaro idanu. Sultan ya ci gaba da magana yana

duban Nawfal, “Nawfal fada mana yadda akayi kuka baro gida daga _hanyar dawowarku Makaranta.” Nawfal ya dan yi

shiru, gaba daya yanayinsa ya sauya. Sannu a hankali ya basu labarin komai. Nasreen ta yi magana cikin sanyi, “Nawfal baka gaya masu Mansur ya ce mana Deedinmu ya rasu ba. Wai kuma an daura mana aure..”

Sai da ta fada kunya da danasani suka kamata, ta sunkuyar da kanta_ Kasa. Gabadaya suka yi mata murmushi. Haka

, labarin su ya taba zuciyar duk wani.halitta da ke cikin dakin. Aslaf ya dube shi ya ce, “Yanzu za ka iya gane gidan da aka kaiku na matsafa? Za ka gane gidan da Mansur din yake?”

Nawfal ya dago yana duban Aslaf ya ce, “Uncle ko kun je ba za ku ga kowa ba. Gidan tsafin kuma bamu san ta inda aka shiga damu ba, ba zamu iya gane komai akan gidan ba. Amma ai shi Deedi yasan Mansur din ya taba zuwa gida.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Sultan ya dube shi, “Nawfal ka gaya ‘min gaskiya, waye kaji sun ce ya turo su su sace Nasreen? Yanzu kuna da ‘yan Kananun Shekarunku kuka dibi irin’ wannan

gwagwarmayar? Nawfal ka yi namijin KoKari, haka ake son dan uwa. Gaya min waye kuka ji sun ambaci sunan su?”

A yadda Nawfal yaga fushi a idanun Sultan yasan akwai matsala idan ya gaya masa gaskiyar lamari, don haka ya girgiza kai suka hada baki da Nasreen kamar wadanda suka gayawa juna abinda za su ce, “Ba su gaya mana wanda ya turo su ba.” ‘

Sultan ya rintse idanunsa, zai so ace yasan waye mai wannan halin. Haka suka ci * gaba da tattaunawa har Ashmaan ya shigo ya same su.

Sosai yake kallon Nasreen sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Har na tuna da Www.bankinhausanovels.com.ng

_ Ibtihal dina da aka ba ni ita a matsayin kurma.” Sultan ya ce, “Kwarai kuwa, basu san wannan dan jaridar na gaske bane.” Sannu a hankali aka sake ba shi labarin su Nasreen ya jinjinawa Nawfal haka yaran sun burge shi da yadda suka riki addini a lokacin da suke cikin tsanani. Daga nan suka ce Yumna ta kama Nasreen su koma

ciki, su kuma suka zauna suna ci gaba da tattauna hanyar da ya kamata su bi wajen ganin komai ya zo masu a cikin sauki ba tare da wata matsala ba, musamman wajen yin takatsantsar da su Nasreen, domin suna son su buga cewa ‘ya’yan da Saudat ta Haifa suna nan da rai, kuma sun girma a yanzu. Www.bankinhausanovels.com.ng

Haka suka zauna su Kullawa wannan su kwance wancan, har aka kira Sallah suka mike suka nufi Masallaci. Da Karfe goman dare yana nan zaune a falonsa Zakiyya tana latsa remot, ita a dole fushi take yi da shi, kasancewar kwana biyun nan duk ya sauya mata, haka yaki tsayawa ma ya ji matsalarta bare har ya bata hadin kai akan rayuwarsu ta aure. Lokaci zuwa lokaci tana satan kallonsa amma shi ko waiwaye. Shi ji yake kamar bai da lafiya a jikinsa, musamman ta bangaren kiyaye hakkin aure. Ji yake idan har wannan abin shi ne auren, to baya daya daga cikin irin mazan da suke da lafiyar aikata hakan. Haka zamansu da Zakiyya zai yi wahala, domin ita bata san komai a aure ba, sai

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *