RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER  BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

 Sultan ya sake jifan bangon dakinsa da murmushi, ba tare da ya lalubo abinda zai gaya mata ba. Tsintar muryarta ya yi tana cewa, “Na so in riga Nawfal fara ganin fuskarka, naso inga irin kyan da na ji ana kururutawa ka Kara, sai dai hakan bai yuwu ba sakamakon makanta da ta toshe min 

idanun yin hakan. Sai dai kafin Allah ya karbi idanun da ya bani aro, ni shaida ce Dee mai kyau ne, Dee yana da kwarjini a idanun kowa.” 

Kalaman yarinyar suna yi masa kama da mai son cusa masa rauni a Zuciya. ““Nasreen kada ki damu za ki gan ni da zarar muka ci karo da Dokto din da zai yi maki aiki.” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin rauni ta ce, “Don Allah zan roKe ka wani abu. Amma sai a ranar da Za a yi min aikin.” 

“Allah ya kaimu ranar.” Ya mayar mata 

da amsa yana jin barci yana son kwasarsa. 

Zakiyya ta shigo dakin tana Kare masa kallo, “Da waye kake waya?” 

Firgigit ya bude idanunsa, “Kin ajiye ni ne kike min tambaya irin wannan? Ban sani ba.” 

Zakiyya ta shaKa iya shaKa ta fara antayo masa maganar da duk tazo bakinta, 

“Wallahi na dade ina zargin ka koma bin matan banza, ga ni a gida sai ka je waje kana

neman na wasu, saboda haram tana da dadin aikatawa,” 

Sosai ya ware idanunsa, “Ashe kina iya bambance Haram da halas? Idan kika sake danganta ni da aikata zina sai kin yi danasani. Idan na fita waje na nema ina ruwanki? Ki gyara kanki mana ki ga yadda namiji ke zama a like da matarsa. A Kazantar naki ne zan zauna da ke? Ke fice min a daki tun kafin fushina ya sauka a kanki.” 

Zakiyya ta fasa kuka ta fice. 

Nasreen kuma tana gama saurara ta sauke wayar jikinta a sanyaye. Ta fara hango tarin Kalubale a cikin zamanta da Zakiyya. Kalmar warin da Sultan ya yi amfani da ita, ta tsaya mata a rai. Wannan ke yi mata nuni sai ta sake tashi tsaye wajen ganin ta zage dantse domin Kwato mijinta, don ganin ta faranta masa.

ZAMU TASHI 

A zahiri kowa ya san ita ce uwargida ba amarya ba, amma yanzu dole ta amsa suna har kala biyu, gata amarya gata uwargida. Yumnah tana shigowa ta kwashe abinda ta ji a tsakanin Sultan da matarsa ta gaya mata. Yumnah ta yi shiru daga bisani ta ce, — “Mijinki ma dan Kyale-Kyale ne, ko da yake wani. namijin ne a duniya baya son gayu? . Waye zai ce baya son tsafta? Ko Kazami yana _, son tsafta. Zan sake gaya maki wasu * abubuwa, abinci kuma ko da baki gani ai kinga ina yi maki bayanin yadda na hada abubuwa ko? Na tabbata idan kuka dawo daga Asibitin Dr Al-ameen za a ajiye ki a ci-:gaba da ba ki kulawa, kuma nasan gidansa za ki zauna kafin ki gama ganin likita. Ga Jidda can gwana ce na tabbata za ta tsaya maki ki iya komai. Kunya halak ce amma ba koda — yaushe za ki dinga jin kunyar ba, kada ki tauye hakkin mijinki.” Haka suka ci gaba da tattaunawar su, Nasreen tana fatan taga fuskar Yumnah domin ita kanta tana da labarin Six lovers,
bata mance su ba, haka labarin rashin jinta ita da Yumnah suna kama da juna, duk da Jidda ta dameta ta shanye.

Shi kuwa Sultan tana fita ya dubi wayarsa ya kashe, bai ji dadi ba, da Nasreen ta ji matsalarsa da matarsa, kasancewarsa namiji ne da ya tsani wani yana jin matsalar gidansa. Kamar zai sake kiranta yaso Kwarai ta yi masa karatun nan nata mai dadi Kila ya taimaka masa wajen samun barci mai cike da natsuwa. Duk da hakan ya sami natsuwa a ‘yar hirar da suka yi. Yanzu abu daya ya rage masa ya fara shirin baiwa Abbansa mamaki, – yana da tabbacin mahaifiyarsa za ta ba shi mamaki fiye da wanda ya baiwa Abban. Cikin ‘yan kwanaki ya gama tsara komai. Kafin ya tafi ya ba wani dan sanda umarnin ya kai Zakiyya Kaduna gidan mahaifiyarta ta gaidata. Hakan ya faranta ran Zakiyya domin tana kewar gidansu. Tana tafiya, yasa ma’aikata su kwashe komai dake gidan a shimfida sabo. Hatta fentin gidan yasa a sauya. Sai da ya tabbatar ya bar masu kula da – komai sannan ya kama hanya a nufi gidan Www.bankinhausanovels.com.ng 

Aslaf cike da saKe-sake. A farfajiyar gidan ya ganta tana zaune tana cillawa yaran Yumna ball suna kwasar dariya, Nawfal kuma yana wurin filawowi yana tsinkowa yaran. Ganinsa yasa Nawfal Karasawa yana aikin dariya, “Dee na yi fushi.”

Sultan ya matse kunnensa ya ce, “Gaya min kalan fushin da kayi.” Ya riKe hannunsa yana fadin ya tuba bai yi fushi ba. ‘=

* *Yan sandan.suna ta murmushi saboda yadda suka burge su. Nasreen tana cilla Ball din Sultan ya cafe yaran suka zo da gudu

’ guna fadin “Deedi Oyoyo.” .

Farin ciki ya kama Nasreen, kawai ta sa

dukka tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana dariya. . .

Yana Karasowa ya sa hannu ya bude

‘ fuskar yana cewa, “’Yar baby babu kyau fa

abinda kike yi babu kyau rowar fuska.” Sosai

take aikin dariya irin wanda bai taba gani a

fuskarta ba. Ya kama hannunta suka shige falon. Yana shiga a tsaye suka gaisa da ’ Yumnah ya ce ta fito mata da kayanta sauri yake yi za su wuce.

‘ Jikin Yumnah asanyaye ta fito mata da kayanta, daman tuni sun shirya. Nasreen ta rungume yaran tana gaya masu za ta dawo, gabadaya kuka suke yi. Sultan ya kirawo su. yana son lallashin su, suka Ki zuwa suka fice suna kuka. Yumnah idanunta sun kawo ruwa * ya ware idanu, “Kiyi kukan ki ga abinda zanyi maki.”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Aslaf ya shigo yana hararar Sultan, ‘““Me za ka yi mata idan ta yi kukan? Kai haka ake lallashi? Ko kuwa matarka kadai ka iya lallashi ba ka iya na Kannenka ba? Kin ji yi kukanki amma kadan mu ga abinda zai yi maki.”

Yumnah ta kwantar’ da kanta tana dariya a jikin mijinta. Nasreen dai sai wasa take da hannayenta, kanta a Kasa domin ba Karamin kunyar Aslaf take ji ba. Sultan ya yi banza da shi, yana jin haushin yadda yaki raka shi. Haka aka kwashe kayayyakin su aka zuba a mota. Nasreen tana kusa da shi, Nawfal ma yana gefensa, gaba daya sun sanya shi a tsakiya. Nawfal yake bashi

labarin yadda Aslaf ke daukarsu shi da yara ya kai su wuraren shaKatawa.

Sultan ya ce, “Iyye ‘yan gata ita kuma Nasreen fa?”

Nasreen abin nema ya samu, sai kawai ta kwanta a kafadarsa ta ce, “Ni basa fita da ni, wai cewa suke yi ni matar aure cé. Watarana in yi kuka.”

Sultan ya yi murmushi, “Lallai Uncle Aslaf bai kyauta ba sam! Ki kwantar da hankalinki idan muka je Kaduna zamu je wuraren shaKatawa kala-kala nasan za ki ji dadi a zuciyarki ko?” gyada kanta ta yi. Nawfal ya fara yin barci ya kwantar da kansa a jikin Sultan, ita ma ta kwanta a daya barin. Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Haka yana ci gaba da godewa Allah da ya sake dawo masa da farin cikinsa a karo na biyu. Yanzu tunanin masifar da ke gabansa kadai ke fadar masa da gaba. Cikin hukuncin Allah suka dinga keta dazuzzuka da garuruwa, har suka iso garin na Gwamna. Suna isowa cikin gidan -su, Hafsat tana fitowa, ganin Yayanta yasa ta koma da sauri ta sanar da Abba da Umma.

Dama kuma Zakiyya da mahaifiyarta sun zo gidan don haka suka cika da mamaki domin babu wanda yasan zai zo. Gaba daya aka fito kamar sun zo ganin gwamna. Sultan ya fara fitowa, kai tsaye gaban mahaifinsa ya nufa, ya dan rankwafa yana gaida shi, Abban ya kamo shi suka rungume juna yana bubbuga bayansa. .

– Sultan ya yi magana cikin sanyi da mutuwar jiki, “Abba na dawo maka da farin cikinka, bansan irin tarbar da za su samu ba,a karo na biyu.” Abba bai fahimci abinda yake nufi ba, don haka ya dago shi daga  rungume juna da suka yi, ya kafe shi da ido, hakan yasa ya dubi ‘yan sandansa ya yi masu alamu da su bude motar. Nasreen da Nawfal suka fito, fuskokin su cike da farin ciki. Nawfal yake riKe da sandar Nasreen. Ba Umma ba, hatta shi kansa Abban sai da ya fazana da ganin ‘yan tagwayen sun Kara girma, Abba ya kasa magana sai sakin Sultan da ya yi ya nufe su gadan-gadan. Nawfal ya saki sandar Nasreen ya rungume Abba sai hawaye. Nasreen ma ta samu ta lallaba har ta Www.bankinhausanovels.com.ng 

taba jikin Abba ta ce, cikin kuka, “Abbana ne? Allah na gode maka.”

Abba ya hada su ya rungume a Kirjinsa, sai hawaye, “Allah kaine abin godiya. Yau ga ‘yan biyuna sun sake dawowa. Allah kada ka sake jarabtana da rasa su don isarka Allah.” Abba ya yi ta surutai yana maganganu. Umma ta dubi Hajiya Ladidi, haka ta dawo da dubanta ga Zakiyya da ciwon hauka yake shirin kamata. Umma ta yi iya dauriya bata furta komai ba, bare ita Hajiya Ladidi da bata da ikon cewa komai. Zakiyya ta zabura za ta yi magana Hajiya Ladidi ta datse mata Kafa, haka Umma ta Kyafta mata idanu. Shi dama Sultan idanunsa yana kan su Abba da ‘yan biyu don haka ya harde yana kallonsu yana murmushi. Daga bisani ya ce wa su Abba su zo su shiga ciki. A babban falon gaba daya suka zauna idanun Sultan Kyam akan Nasreen har baya son ya kauda idanunsa. Dukka dakin

. suna kula da hakan amma sai suka share. Sultan ya sake gaida iyayensa duk suka amsa babu yabo babu fallasa.

Ya dubi Nasreen ya ce, “Ku tashi ku gaida Umma.” Nasreen ta fara ta shi tana lalube. Kamar za ta fadi Sultan ya yi saurin kamata, ya iso da ita gaban Umma yana murmushi, “Umma ga diyarki ta dawo.” Umma ta saki yake ta ce, “Oh ka barta mana kake ta shisshige mata. Ka barta ai zamu gaisa.”

Sultan ya barta ba tare da ya kawo komai a ransa ba. Abba ya sake duban yaran cike da farin ciki ya ce, “Yanzu ni wani irin tukuici zan baka? Na rasa shin mafarkin da na saba yi ne nake yin sa ko kuwa da gaske ne idona biyu?” Umma ta ce, “Ba mafarki ba ne da gaske ne, Hajiya gwaggo ce ta dawo.”

Dukka dakin babu wanda ya ji mai ta ce, sai Nasreen da ke sunkuye a kusa da ita, hakan yasa ta dan sha jinin jikinta. Abba ya dubi Zakiyya da fara’a ya ce, “Zakiyya kin ga ‘yar uwar zamanki Allah ya yi dawowarta ko?”

Nan ma shiru babu wanda ya yi magana, shi kuwa Abba bakinsa ya gaza rufuwa. “Sultan tun yaushe ka gansu ne?”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sultan ya dan saci kallon Umma ya ce, “Ai sun kwana biyu a hannuna, na ajiye su ne kawai ina son basu kulawa kafin in kawo maka su.”

Umma ta zabura saboda mamaki da kuma gigicewa, da halin Sultan, da ace lokacin da ta haife shi akwai wata a dakin haihuwar da sai ta rantse ba jininta bane, ansauya mata ne. Kowa ya juyo ana kallonta,

, Sai kuma ta wayance kamar tana muskutawa. Zakiyya ce ta daddage ta fashe da kuka,

hakan ya jawo hankalin kowa kanta. Abba ya ce, “Assha! Me kuma ya kawo_ kuka Zakiyya? Me aka yi maki?” ‘

Zakiyya ta fara magana cikin kuka, “Abba ina gidan nan tare da Yaya Sultan amma bai taba gaya min an ga Nasreen ba, ai da. na taya shi da kula da ita. A zatona Nasreen ai ‘yar’uwata ce, me zai sa ya Boye min idan ba ya dauke ni muguwa ba?”

Abba ya ji dadin kalaman Zakiyya don haka ya girgiza kai, “Ba ka kyauta ba Sultan, ko ba za ka gaya mana ba don kana son ka bamu mamaki ita ai matarka ce, sai ka gaya

mata komai, ana boyewa kowa abu amma banda mata.”

Sultan ya dube ta bai yi mamaki ba, idan har da gaske goyon Hajiya Ladidin da ya sani ne, babu abinda ba za taiba. “Zan kiyaye Abba.” Ya baiwa mahaifinsa amsa saboda ba ya son damuwa.

Umma dai sai ta zama:kamar wacce ta zauce, sai ta dubi Nawfal sai kuma ta dubi Nasreen, a lokaci guda kuma ta watsa idanunta akan Abba da Sultan. Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Abbana kullum sai na ganka a mafarkina.”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Abba ya sake cika da farin ciki. A nan Nawfal yake basu labarin dukkan wahalar da suka sha, daga ciki har da sunan Mansur da ya kusa aure Nasreen a cewarsa Sultan ya rasu. Sai dai ya boye sunan Umma. Hakan yasa ta saki ajiyar zuciya mai Karfi. Hakan kuma bai sa ta ji ko alamun tana son yaran ba, haka bata ji tausayin su ba, kamar yadda Abba yake jin tausayin nasu yana ratsa shi. Nasreen ta Kara da cewa, “Abba na gode Allah da na sake jin muryoyinku a duniyata.”

Umma da taji kamar ta shaKeta ta mike, domin gani take yi kamar da gangar suke yin hakan domin su sanya mata ciwon kai. Tana mikewa Zakiyya ta bi bayanta, sannan Hajiya Ladidi. Falon ya rage daga Abba sai Sultan da ‘yan biyun. Babu wanda ya yi mamakin yadda Umma taki jajanta masu.

Sultan dai ya Kosa ya sami dama daga shi sai Nasreen dinsa. Ji yake kamar za a sake raba shi da ita. Abba ya dubi Nawfal ya ce muje a fitarwa ‘yan sanda da abincin su. Abba ya yi hakan ne domin yana karantar yanayin dan nasa. Suna ficewa Sultan ya

_ dawo kusa da ita, ya ja dogon hancinta ya ce, “Nasan da matsafan nan sun yi yunKurin kasheki, da hancin nan za su fara, sai kuma lips dinnan masu kyau da daukar idanu.”

Hannunsa ta rike tana murmushi sannan ta ce, “Deedina wai da gaske ne tun ina Karama suke nemana? Abin ‘ya ba ni tsoro, wai sun sha zuwa za su sace ni Sai su ganka tsaye akanmu kana yi mana addu’a.” Sultan da ya shigar da ita cikin jikinsa sosai ya kai bakinsa cikin kunnenta yana magana,Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Zai yuwu da gaske ne zai yuwu kuma Karya ‘ce kawai irin nasu. Kila akwai wanda ya sanni ne ko yasan ku a cikin gidan -nan. Mutanen nan idan ba ka yi hankali da su ba, sai su dulmiyar da musulmai. Ko sun yi ninyar shan jininki kin fi Karfin su Nasreen, ,_, Kina dauke da abinda ba su da shi. Ke jikinki a tsaftace yake, su kuma babu Allah a ransu. Kullum cikin Kazantar tsafi suke.”

Nasreen ta sa hannu tana KoKarin ture – shi, sai dai yadda jikinta yake a mace ba ta iya daga hannunta yadda ya kamata. “Dee, – babu kyau fa.”

Murmushi ya yi, “Mene ne babu kyau a ciki? Fada min sunan abin sai in daina.”

Ta kasa magana sai mayar da ajiyar zuciya take yi a Kagauce. Ya rasa wani irin Kamshi ne haka yake ratsa shi a jikin Nasreen, Kamshin, akwai sanyi da kwantar da hankalin duk wanda ya shaka. Ga shi abin burgewa wanda yake nesa bai isa ya ji

‘ Kamshin ba, sai ka matso kusa da ita sosai, “Babyna Kamshin nan wai a ina aka samo shi ne? Yana gigita ni da yawa, a gaya min nawa

ne kudin turaren sai inbada a siya da yawa kada ya Kare.” Ita kanta bata san lokacin da take bashi amsa ba, domin kuwa ta fita hayyacinta, “Dee ba turare bane, humra cé irin ta Maidugurin nan. Ko ya Kare ya riga ya kama jikina ba zai daina Kamshin ba…” Ba ta kai ga ajiye numfashi ba, ya sake biyo mata da hanyar da maganar ma ta gagareta, sai ajiyar zuciyar Www.bankinhausanovels.com.ng 

A can dakin kuwa Hajiya Ladidi ta dubi Umma ta ce, “Kin gani ko? Karamar alhaki tana neman ta tsole mana idanu Daman Mansur ya fada mana ya ce tunda suka kubuta daga hannun mu za su dawo, hakan ya sa ya ajiye yaransa a bisa layi, ta yadda suna ganinsu kafin su shigo a sake dauke su, ta ya ya har yaran nan suka sami ganin Sultan, duk yadda ganinsa ke da matuKar wahala? Ya aka yi ma suka san yana Abuja?”

Hajiya Salma ta Harare ta, “Ta ina kike jin magana ne Hajiya Ladidi? Ba ki jin a cikin labarin da yaron yake badawa ya ce motar su Sultan ce ta buge suba? Ni ba wannan ba

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *