RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Ta kasa magana sai mayar da ajiyar zuciya take yi a Kagauce. Ya rasa wani irin Kamshi ne haka yake ratsa shi a jikin Nasreen, Kamshin, akwai sanyi da kwantar da hankalin duk wanda ya shaka. Ga shi abin burgewa wanda yake nesa bai isa ya ji
‘ Kamshin ba, sai ka matso kusa da ita sosai, “Babyna Kamshin nan wai a ina aka samo shi ne? Yana gigita ni da yawa, a gaya min nawa
ne kudin turaren sai inbada a siya da yawa kada ya Kare.” Ita kanta bata san lokacin da take bashi amsa ba, domin kuwa ta fita hayyacinta, “Dee ba turare bane, humra cé irin ta Maidugurin nan. Ko ya Kare ya riga ya kama jikina ba zai daina Kamshin ba…” Ba ta kai ga ajiye numfashi ba, ya sake biyo mata da hanyar da maganar ma ta gagareta, sai ajiyar zuciyar Www.bankinhausanovels.com.ng
A can dakin kuwa Hajiya Ladidi ta dubi Umma ta ce, “Kin gani ko? Karamar alhaki tana neman ta tsole mana idanu Daman Mansur ya fada mana ya ce tunda suka kubuta daga hannun mu za su dawo, hakan ya sa ya ajiye yaransa a bisa layi, ta yadda suna ganinsu kafin su shigo a sake dauke su, ta ya ya har yaran nan suka sami ganin Sultan, duk yadda ganinsa ke da matuKar wahala? Ya aka yi ma suka san yana Abuja?”
Hajiya Salma ta Harare ta, “Ta ina kike jin magana ne Hajiya Ladidi? Ba ki jin a cikin labarin da yaron yake badawa ya ce motar su Sultan ce ta buge suba? Ni ba wannan ba
ZAMU TASHI
ne a gabana ba, ta ya ya za ayi dana ya zauna da ‘yar zina! ‘Yar da bata da asali? Kai .Wallahi da sake ba zai yuwu ba. Ni Ummu Salam ba.zan lamunta ba, basu san da wa suke zance bane. Dole zan koma Abujan da zama, duk hanyar da zan bi inhana wani abu ya faru a tsakanin su babu shakka zan bi inKkwato dana, kafin insan hanyar da zan.° batar da ‘ya’yan shegun gaba daya kowa ma _ ya huta. Wallahi zan iya kashe yaran nan-: musamman ma Nasreen din da hannayena. ° Kai ina ba zai sabu ba! Kaf zuri’ata babu . shegu, babu mazinata babu arne babu yaddaza a yi ace wai dana ne da kansa zai kawo. min wannan masifar. Yau har gara ‘a Kwankwasa min Kofa ace mahaifiyar Sultan ce ta zo tana fadin Sultan ba dana bane, ba_ jinina bane. musayarsa aka yi min. Yaron da.. ko irin dokin mahaifiyar nan da wasu yaran suke yi baya yi? Kwata-kwata Sultan bai ~. .~ damu da ni ba.” Sai kuma tasa kuka. Jikin :: Hajiya Ladidi ya yi sanyi, ta tabbatar da’ ‘gaske Hajiya Salma take yi ta tsani yaran tsana mai tsanani, hakan ya dan ragewa Www.bankinhausanovels.com.ng
Zakiyya irin tarin matsalar da ke cikin zuciyarta, domin ji take yi kamar ta kashe kanta ta huta. Umma ta ce, “Zo mu je falon, ba zan taba barin su su sami sukuni ba indai ni ce.” Nawfal yana shigowa ya hango su Umma da Hajiya Ladidi da Zakiyya sun nufo falon, haka yana da tabbacin Sultan yana tare
_ da Nasreen, don haka dabara ta fado masa, ya yi sauri ya riga su Karasowa bakin Kofar ya dinga magana da Karfinsa, “Nasreen Abba ya ce mu je mu ci abinci.”
‘ Sai da ya maimaita sau biyu sannan dukkan su suka ji, Sultan ya dinga jujjuya dalilin da zai sa ya tsaya yana magana da ihu, daga bisani ya mike ya barta a nan ya taho bakin Kofar don yaga abinda ke faruwa. Umma ta watsawa Nawfal harara ta ce, “Mene ne haka zan gani? Meye na yi mana ihu a gida bayan kasan gidan nan ba a ihu? Ko bayan makantar da ke gareta har ta koma kurma ce?” —
A take Sultan ya gane abinda Nawfal ke nufi ya saki murmushi yana jinjina wayon _yaron. Umma ta dube shi tana mamakin dama su biyu ne a falon? A Kufule ta ce, “Ina Abban naka?”
Daga baya Abba ya ce, “Ga ni wa ke nemana?” Umma ta sake cika da al’ajabi. Da gaske take yi ta shirya zama ta yi _ gadin Nasreen da Sultan. Falon ta kutsa abin mamaki Nasreen barcinta take yi. Umma ta waiwayo tana duban Sultan, “Ita Nasreen din har tayi barcine?” ~~ –
Sultan ya saki ajiyar zuciya, yana sane da idanunta biyu amma sai ya yi fuska ya ce, “Ni ma yanzu na shigo falon na sameta tana barcin.”
Umma ta gyada kanta ta koma ta zauna tana zazzare idanu. Hajiya Ladidi ta bar Zakiyya a nan ta ce ta zauna taga abinda ke faruwa, sannan ta yi masu sallama da za ta tafi Sultan ya dibi dubu ashirin ya bata. Ta dinga godiya sannan ta wuce tana tunanin mafita. Taso ta turo Mansur, sai dai irin tsaron da suke tafe da su, sun yi matuKar razanata. Dare ya tsala wuri ya yi shiru babu abinda kake ji sai kukan abubuwan daji da ba za a rasa ba. Sultan idanunsa biyu ya kasa Www.bankinhausanovels.com.ng
barci, haka Umma idanunta biyu, Zakiyya ma idonta biyu. Nasreen kuwa ta yi nisa cikin barcinta, a cikin dakinta da take tunanin ba za ta sake zama a cikinsa ba.
Sultan yana tsaye ta windo yana kallon wutan dakin Umma a kunne. Ya riga ‘ya fahimci abinda take nufi. Yana nan tsaye a bakin windo yana kalle-kalle ya ga Umma ta wuce dakin Abba hannunta dauke da ruwan zafi, hakan yasa tana wuce wa ya fada dakin Nasreen. Sai da ya murza dan makulli sannan ya haye gadon, ya jawo ta jikinsa. Cikin magagin barci ta sake shige masa, ya saki ajiyar zuciya. “I love you’ Wife.” Ya furta a fili yana Karewa kyakkyawar fuskarta kallo. Wannan karon ta farka sai dai yadda gabanta yake faduwa ya sa ta kasa nuna masa ta tashi. Wani sako ya aiko mata mai matukar mahimmanci da tasiri ga jikinta, hakan ya sa ta riKe hannunsa ta ce, “Wash! Deedi zan mutu kaina ciwo.” Ya rada mata a kunne, “Sorry za ki ji sauki kin ji?”
‘Yadda take mutsu-mutsu .ya sa ya rungume ta kawai ya ce su yi barci. Nasreen
tasa masa rigima ita ba za ta iya ba, shi kuma ya yi rantsuwa ba zai kwanta a ko ina ba sai a dakin nan. Haka ta hakura ita kanta tafi son ta ji ta a kusa da shi. Daga shi har ita suka yi wani irin barci mai dadi da sanya natsuwa. Ya jima bai yi barci mai dadin na yau ba. Hancinsa yana shakar daddadan Kamshinta mai ratsa Zuciya. ,Www.bankinhausanovels.com.ng
A kunnensa aka kira sallar asubahi, don – haka ya sake jawota sosai cikin jikinta ya ce, “Wife ta shi an kira Sallah.”
Ta rasa yadda za ta gaya masa ba ta yin Sallah, sai kawai ta tura kanta cikin jikinsa, “Dee sai anjima zanyi.” Yadda ta yi maganar yasa shi murmushi, ya kuma kai hannunsa ya laluba ya ji alamun ta sanya pad ya ce “Iyye “yar yarinyar nan ta girma fa. Nasreen har yanzu ina mamakin girmanki. Ashe matata nake reno. Mu maza mun more, mu ci zamanin mu mu ci na ‘ya’yanmu daga Karshe kuma mu ci na jikokin mu.”
Nasreen ta yi matuKar jin kunya hakan yasa ta KanKame jikinta a cikin nasa tana ‘yar dariya. Da Kyar ya Kyale ta ya shiga bandaki
ya yi alwala a gurguje bai yi garajen fitowa ba, har sai da ya leKa ta windo sannan ya fito. A lokacin kuma Umma ta fito daga dakin Abba, sai kallon-kallo tsakaninta da Sultan. Gabanta ya fadi tana tunanin ashe gadin banza ta yi jiya kenan tunda gashi ya shiga dakin Nasreen ba tare da ta sani ba. “Kai dai ka ji kunya. Uban me ka je yi a dakin yarinyar nan? Da wani lokacin ma ka shiga? Yau na ga masifa anya yarinyar nan ba mayya ba ce?”
Sultan ya yi murmushi cikin salonsa ya ce, “Umma da mayya ce ai babu wanda zai sha a cikin gidan nan. Ba ki gan ni da alwala ba? Yanzun nan na leKa ta in ga yadda ta tashi tunda kin san ba idanu gareta ba.”
Umma ta sake Kufula duk da ta sami natsuwa da ya ce yanzu ya leKa ta, ta ce “Ban sani ba! Na ce maka ban san makauniya ba ce, amma yanzu ai da ka gaya min ka ga na fahimta. Iskancin banza kai Yau ta fara shiga bandaki ita kadai? Ko kuwa kai kake yi mata jagora a lokacin da suka tafi yawon gantalin su? Ga Zakiyya can da ta baro gidansu ta zo Www.bankinhausanovels.com.ng
nan ta kwana ka je ka duba ta? Bana son rashin adalci, idan ka fara bambanta matanka ni ina tabbatar maka zan dauki mataki.” Sultan bai ce komai ba yana KoKarin wucewa Masallaci Abba ya fito suka hada hanya. Nawfal ma ya fito daga dakinsa duk suka dugunzuma. Sai bayan sun fito ne Sultan ya gaida mahdifinsa, sannan Nawfal ya gaida su. Suna hanyar dawowa Abba ya dubi Sultan cike da damuwa ya ce, “Sultan ka bi a hankali da mahaifiyarka, ka kiyaye mata tun kafin ta hanaka zaman lafiya a tsakaninka da iyalanka. Bana jin dadin abinda ‘ Salma take yi, amma babu komai akwai lokacin da ko kudi aka bata ba za ta aikata ba: Kai dai ka zama tsayayyen namiji a cikin gidanka, duk yadda kafi son dayaka daure ka – dinga boye soyayyarta a zuciyarka idan ba haka ba, za ka siyo masifa ne da kudinka ka kawo cikin gidanka. Ita mace haka Allah ya Halicce ta komai ta fi son ta ji ance ita ce gaba. Saken da namiji yake yi a cikin gidansa ‘ shi ke kawo matsalar’ zaman lafiya. Sai ka jajirce ajiye mace fiye da daya a cikin gida
sai Jarumi, jarumin kuma yana wahalar samu, shi ya sa Za ka ga namiji har namiji amma ba shi da wani Karfi a cikin gidansa, ina nufin muna da Karancin jarumai. Ina fatan za ka ba ni mamaki wajen ganin ka hana matanka jin zafin juna irin wanda addini baya so?”
‘ Sunkuyar da kansa ya yi ba ya iya boyewa Abbansa komai don haka ya ce, “Abba akwai wahala gaskiya. Bana son Zakiyya na yi iya bakin KoKarina in ga nasa soyayyarta a zuciyata tun kafin in gano Nasreen abin ya faskara. A yanzu kuma bayan bayyanar Nasreen sai na ji na.sake tsanarta. Abba da ina da yadda zan yi da ba zan zauna da Zakiyya ba, domin tarbiyyar
_ yarinyar ba ta yi min ba. Abba ko sallah Zakiyya ba ta yi, bare har a kai ga wataran ta dora abinci a tukunya. Har yanzu siyan abinci nake yi a kasuwa sannan in ci.”
Abba ya dubi Sultan, haka ya jinjina masa a cikin zuciyarsa, bai taba tunanin Sultan zai iya haKuri da mace har irin hakan ba. Abba ya ce, ““Yadda ka yi haKuri da ita a farko haka za ka sake yin haKuri da ita a Www.bankinhausanovels.com.ng
yanzu. Ka dinga nuna mata mahimmancin addini kana sanya idanu a kan yadda take addininta, domin mace babu addini tamkar gidan da akayi shekaru da zama ne ba a shiga ba. Ban taba sanin ba ta da addini ba, saboda daman zabin mahaifiyarka ce, amma idan ka tsaya ta gyara kaima kana da lada Sultan. Sannan ina gargadinka da boye soyayyar Nasreen, idan baka Boye soyayyar Nasreeen ba, idan ba ka nuna kamar Nasreen ba ta gabanka ba, za ka sha wahala a gun mahaifiyarka da gun matarka. Ya zama dole ka Boye dokin da kake yi a kanta. Ka san jiya hango mahaifiyarka na yi ta windo tana ta leKenka?
“Ganin hakan ne ya sa na _ yanke shawarar aikenta ta kawo min kofin shayi. Sultan ka siyawa Nasreen zaman lafiya ka boye soyayyarta, duk da abu ne mai matuKar wahala, amma za ka iya. Dan lokaci ne kawai watarana a gabanta za ka nuna kana son Nasreen hakan zai faranta mata rai, watarana za ka iya bata wa Nasreen mahaifiyarka ta nuna maka bacin ranta.
Sultan ya girgiza kai, “Abba gani nayi kamar wannan ranar ba za ta zo ba. Tu Nasreen tana cikin mahaifiyarta, Umma ta furta tsanarta ga uwarsu, har suka zo duniya bata sauya ba. Abba sai mun tsufa sannan zata sota?”
Abba ya yi dariya a lokacin da suk karya kwanar shiga gidansu, “Ni na gaya maka za ta sauya ina raye ko ina ciki Kabarina za ka tuna da ni watarana. Idan ka dukkan shawarwarina za ka ga abin ya zaizo maka da sauKki.”Www.bankinhausanovels.com.ng
Nawfal duk yana jin abubuwan da suke tattaunawa, har kowa ya koma dakinsa domin samun barci. Kamar a mafarki ya ji mutum kusa da shi, yana ware idanu yaga Zakiyya tana zaune ta hade rai kamar za ta yi “kuke Ji ya yi kamar ya kwasa mata mari sai kuma ya dake yana dubanta, “Lafiya kike tashina_ina barci?”
Ta dan dube shi, “dama..damaaa…” Ya daka mata tsawa ya ce ta fice masa, yana dubanta cike da takaici, “Ke yanzu a gaban Umman kika wuce kowa saboda ke ce sarkin
narasa kunya, kika zo dakina? In yi maki nene? Don Allah tashi ki fita barci nake ji.”
Jiki a sanyaye ta mike har ta kai bakin ‘kofa ya ji a zuciyarsa bai kyauta ba, da ya yi mata hakan, ya tabbata da Nasreen ce ta shigo cikin bargo zai maidata. Ya zama dole ya jinga Kokari wajen ganin ya bi shawarar nahaifinsa.
“Zakiyya.” Ya kira sunanta cikin sanyi.
Ta waiwayo cike da mamaki. Har hawaye sun sami daman zubowa.
Gabansa ya fadi, domin ya san kai tsaye gun Umma za ta wuce. Hannu ya mika mata, hakan ya sa ta dawo da sauri ta kama hannunsa ya zagayo da ita kusa da shi. Hijabin da tasa ya yaye sannan ya hadata da jikinsa. Warin attachment din kanta da Karni suka dake shi, ya dan kawar da hancinsa sannan ya fara magana cikin lallabawa, “Zakiyya ba na son ina bata maki rai amma ke kike sawa. Ki yi hakuri kin ji? Ba na son a yi maki kallon mara kunya ce, ki koma cikin jama’a.”Www.bankinhausanovels.com.ng
Zuciyar Zakiyya fari sol! Ji take yi kamar duk duniya babu ‘ya macen da ta yi dacen da ta yi. Yana kallon ta ta fice tana ‘yar dariyarta. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yana son ganin Nasreen yana son ya yi barci wuri guda da ita, ta haka ne zai iya samun natsuwar da yake da buKata. Sai dai maganar mahaifinsa ita ke danne shi, dole ya mayar da kansa kawai ya kwanta.
*********
A daddafe suka kai kwanaki biyu, yau ne kuma suke sa ran tafiya. Shiru-shiru Sultan yana jiran mahaifinsa ya hada su amma bai yi hakan ba, don haka ya ci gaba da zuba idanu. Yana daki yana shiri aka aiko Nawfal wai ya zo. Babu bata lokaci ya iso falon, abin mamaki dukkan halittun dake cikin gidan suna nan zaune a falon nan. Nasreen tana zaune kusa da Abba kanta a Kasa. Umma kuwa ta cika ta yi fam! Sai girgiza Kafafu take yi.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG