RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Nusreen taci gaba da cewa, “Kishiya ba ita bace mafita kayi tunani da kyau.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya karaso gabanta yana_ son Nasreen fiye da tunanin mutum, “Nasreen ki bar wannan maganar na rufe ta. Ya aka yi kika zo nan?”
Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Mai aiki ta saita ni har inda kaKake. Su Umma suna
ciki suna cin abincin da dan sanda ya kawo. Yanzu kana ganin haka zamu zauna ana siya mana abinci? Ni ba idanu gareni ba bare in shiga kitchen.”
Sultan ya ce, “Wallahi ni kaina abinda ke damuna kenan. Yanzu ya zaa yi?”
_ Sai da ta jingina da bango kafin ta ce, “Ina ganin a shawara, ka sanya a nemo mana mai aiki wacce ta Kwarai a iya ayyukan abinci sai mu mayar da ita mai girkinmu. Amma ya ka gani?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai da ya lakaci hancinta sannan ya ce, *‘Abinda kika ce shi za a yi. Wannan ma shawara ce mai kyau. Yanzu kin gane dalilin da yasa Umma ta sauka a dakinki?” Girgiza kai ta yi cike da rashin fahimta, : “Wallahi ban gane komai ba.” : Nan da nan fuskarsa ta nuna bacin rai, “Umma ta zo garin nan ne saboda ba ta son mu _ kadaice ni da ke. Na rasa irin wannan abinda Umma take yi.” Nasreen ta yi murmushi, “In dai haka ne ai ni ta taimaka. Allah ya Karawa Umma lafiya.” Mamaki yasa ya murde hannunta ya ce, “Maimaita abinda kika ce. Ni kuma tunda kika
ZAMU TASHI
fada hakan a gabanta zan dinga daukarki in wuce dakina da ke.”
Tana Kyalkyatar dariya ta ce, “Wallahi na yarda.”
Shi ma murmushin kawai ya yi suka ci gaba da ‘yar hirarsu. Da suka gaji ne ya kama hannunta ya saita ta a kan hanya sannan ya tsaya yana kallon ta har ta shige, shi kuma ya fice Zuwa gidan Ashmaan. Ba shi ya dawo ba sai dare, abin mamaki har yanzu suna nan zaunea a falon wai suna kallo. Sai da ya dan saci kallon Nasreen baiwar Allah barci take yi a zaune.
Ya dubi Umma ya ce, “Umma ku tashi ku ~ je ku kwanta dare ya yi.”” Umma ta tashi tana hamma ta bubbugi Nasreen ta tashi tana magagi, ta kamo hannunta ta juyo tana duban Sultan. “To sai da safe, ina ganin kamar Zakiyya ta yi barci ka tasheta.” Dama tuni Hafsat ta shige abinta. Takaici da bakin ciki suka hana shi sakat ya bi su da kallo kawai har suka shige. Gyara zamansa ya yi a falon, daman shi bai ce zai yi wa Nasreen komai ba, yana jiran har sai ta sami lafiyar idanu, ta yadda yana kallon kyawawan idanunta, tana kallonsa. Amma yana da buKatar kwana kusa da matarsa. Zakiyya ta tashi kamar tana magagi wanda a zahiri idanunta biyu, “Muje mu kwanta.” Ya dubeta cike da bakin ciki, “Kwananki ne? Ina zaton sai Nasreen ta yi kwanaki bakwai dinta kafin ma a raba girki? Ki je dakin ki taho min da ita.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Zakiyya ta dube shi shekeKe da alamun har ta mance irin marin da ya yi mata dazu ta ce, “Wallahi ba zan je ba. Ni lokacin nawa ai ba wata ta kirawo ni ba, ni na kai kaina da kaina. Kuma ina zaton ko za ka yi kwanakinka ai sai ka jira Umma ta tafi ko? Ko kuwa a gabanta za ta dinga tsallake Umman tana zuwa wurin miji?” Shikam Sultan kansa ciwo yake yi, amma duk da hakan sai da ya ba Zakiyya amsarta, “Kin ga bambancin Zakiyya da Nasreen ko? Kin kawo kanki wurin miji ba tare da ya neme ki ba, babu aji ko kadan, dole miji ya dinga yi maki kallon wacce bata kai ba, ita kuma saboda kunya ba za ta iya kawo kanta wajen miji ba. Ina gaya maki ki dinga sanin irin maganar da za ki gaya min, idan ba haka ba jikinki ne zai dinga gaya maki, daga Karshe ki bar min gida, domin ba ayi yarinyar da zan auro ta zo har cikin gidana tana gaya min abinda ranta ke so ba, ya zama dole ki koyi ladabin magana.” Ya shige dakinsa yasa dan makulli. Www.bankinhausanovels.com.ng
Zakiyya ta je ta taso Umma tana gaya mata tana kuka. Nasrcmeen dai tana kwance a gado tana jin su tayi shiru, da farko tana zaton Sultan hasashe yake yi akan abinda Umma take nufi, a yanzu kuma ta fahimci da gaske Umma take yi ta shirya rabata da Sultan. Hawaye kawai ke sauka a idanunta, domin a zahirin gaskiya tana buKatar ko babu abinda zai hadata da Sultan ta kwana a gefensa suna hirarsu da baya gundurarta. Umma ta fito tana kwankwasa Kofar Sultan, kamar ba zai bude ba, jin muryar Umma yasa ya bude fuskarsa babu ko alamun fara’a.
Umma ta dubi Zakiyya ta ce, “Maza shiga gun mijinki. Me yasa ka rufe Kofa ka bar matarka?” Kamar ya ce mata wancan ba matarsa ba ce? Sai kuma ya share kawai. Ya bar Kofar a bude ya shige. Zakiyya ta kutsa kai. Da taga ba zai bata hadin kai ba, sai ta koma ta sanya wannan turaren ta dawo. Babu shiri ya amince ya aikata abinda take so ba tare da natsuwar zuciyarsa ba, Warin nan nata yana nan har yanzu babu canji. Ganin ta kwanta tana shirgar barci
yasa ya bubbugeta yace sai ta tashi ta je ta yi wanka, sannan zai kwanta gado daya da ita. Bayan ya fito wankan tana kallonsa ya zauna gaban madubi ya matso wannan turarcn ya matso wancan. Sai da ya tabbatar da Kamshinsa ya saje ko ina na jikinsa sannan ya saki ajiyar zuciya. Ya koma ya haye gado, tunanin Nasrcen kawai yake yi. Kwanaki biyar a tsakani Sultan ya shirya yaje aka daura auren Abba, wanda shi ya bayar da sadaki akayi komai. Hajiya Gwaggo ta ji dadin wannan auren don haka ta hada su ta yi – masu fada. Mairo mace ce mai alkunya da kawaici, . haka ansha wahala matuka kafin Mairo ta amince da auren da take ganin tsabar cin amana ne ta auri mijin uwar dakinta. Ita kuwa Umma ta kafe ta tsare, ta hana Sultan Karasowa kusa da matarsa. Shi kuwa iya haKurinsa ya kai Karshe don haka yau ya yi rantsuwa sai ya san yadda zai yi ya shaki Kamshin matarsa. Yana shigowa falon ya same su gaba daya suna kallo ya duba ko ina babu Nasreen, don haka ya mike ya kama hanyar dakinsa. Zakiyya ta shigo ta sami har ya fara barci don haka ta koma suka ci gaba da hirar su. Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali ya fito babu wanda ya ankare da shi ya shige sashen Nasreen, Tana _tsaye hannunta dauke da turaren wuta da mai aikinta ta kawo mata tana turara dakin. A hankali ya shigo kawai ya tsaya yana kallonta.
Ga mamakinsa sai yaga tana murmushi, har ya sha jinin jikinsa ko dai idanunta sun bude ne? “Barka da shigowa Deena. Nayi matukar kewarka ta yadda baki ba zai iya fadin iya adadin kewar ba.”
Sultan ya ce, “Oh ya akayi kika san na shigo?” Sai da tasa bakinta ta hura masa hayakin – turaren sannan ta bashi amsa, “Ashe dai ba gaskiya ba ne da ake cewa idan har jini ya hadu wuri guda rabuwarsu abu ne mai matuKar wahala? Ina da tabbacin idan jini ya hadu bin ilahirin jiki yake yi yana kaiwa da komowa alamun ya riga ya hade da dukkan sauran jinin da ke jikinka. Ka ga kuwa mai iya raba wannan jinin sai ya zo da shiri ba na wasa ba. Ko a gida ko a Office ko a kasuwa, ko a cikin hawan idi, ko a filin sukuwa ko kuma a cikin taron jama’a da yawansu ya kai iya adadin buhun gero, inhar jan Gwarzona zai gifta, jinina zai motsa alamun farin cikina yana kusa da ni. Bare kuma a gidana,
a gidan nawa ma a cikin tsakiyar falona, a falon nawa ma a kusa da ni. Sannu da zuwa mijina, ba irina mai sonka za ka boyewa kanka ba. Me ka samo mana ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Yarinyar kullum sake rikide masa take yi, a hankali ya Karaso ya karbe turaren wutan, ya dauketa cak! Sai cikin dakinta yasa key ya rufe. Tana girgiza masa kai, sai dai bai kai cikinta ba, domin cike take da kewarsa sosai. Suna nan kwance sun lula wata duniyar, suka ji Kwankwasa Kofa. Nasreen ta gigice tana son yin magana, ya sake hade bakin su wuri guda, hakan ya hanata furta komai, sai gabanta da ke faman bugawa da Karfi. A hankali ya yi mata magana “Ki natsu ki kwantar da hankalinki da muijinki kike tare ba kwarto ba. Bansan dalilin da yasa Umma ta zo ta sa mana Katon lullubi ba a tsakanin mu, bayan tuni Allah ya yaye mana wannan Katon hijabin, ya bani dama inyi abinda na gadama da ke domin ke matata ce. Yau a dakin nan zamu kwana ni da ke, na bar sake raba makwanci da ke Nasreen, Ni kadai nasan wahalar da na sha da baki kusa da ni a kwanakin nan biyu. Ki daina tsoro kin ji?” Gumi ne ke tsattsafo mata a kowani irin bugun Kofa da
Hafsat take yi. Bata damu ba, ba ta kawo komai a ranta ba, ta juya abinta.
Ta dubi Umma tace, “Rufe Kofar ta yi. Kina ganin makiran yarinyar nan? Tun ranar da kika rabata da Yaya kullum kwanan kuka take yi.”
Umma ta tabe baki, “Karshen rufe Kofa ta zo ta koremu ne daga gidan. Ita da Sultan sai dai ta hango wata da shi amma Wallahi ba dai ita ba. Sai naga ta inda dangantakan musulunci da rashin addini suka hada hanya.”
Zakiyya ta dubi wayar Umma da ke Kara ‘ ta ce, “Umma, Abba ke kiranki.” Umma ta harari wayar cike da bakin ciki. Dallah ja can ki bani – wuri ba zan dauka ba. Ya addabeni da azaban kira kamar tsohon makahon da ya rasa gane hanyar gida.” Zakiyya da Hatsat suka yi dariya suka tafa. Nasreen da ta lume a cikin wata duniya, ta kasa ko da motsa hannunta ne. Shi kansa ya fahimci yadda ya wahalar da ita, tausayinta ya kama shi, da ace bai dau alKawarin ba zai amshi hakkinsa ba, har sai idanunta sun bude yau da ya nunawa su Umma shima namiji ne cikukke mai lafiya. Haka ya tashi kafin ya tafi
ya manna mata sumba, sannan yace“I love you Wife.”
Ta kasa magana sai motsa labbanta da ta yi ta mayar masa da martani. Ya gane abinda take nufi don haka ya jawo bargo ya rufeta, ya fice tare da jawo mata Kofar. Jin kansa yake yi kamar sabon ango, dukkan Kuncin da yake tare da shi, ya kau, sai murmushi yake saki abinsa. Umma da Zakiyya da Hafsat suka bi shi da kallo cike da mamaki.
Hankalin Umma idan ya yi dubu to ya tashi, “Kai da kake barci yaushe ka fito ka shiga dakin Nasreen? Me kaje yi a dakinta?” Tambayar taso ta bashi dariya, sai ya kirne kawai yana murmushi, “Umma don na shiga dakin Nasreen kawai sao a ce min me naje yi? Naje inkai mata waya Nawfal ya addabi Abba sai an bashi Nasreen. Sai na sami dakin a rufe. Da Kyar ta bude Kofar tana magagi wai barci take yi, ni kuma na fito na Kyaleta zuwa anjima sai insake kiransa suyi magana. Ta gabanku na wuce na shiga, abin mamaki babu wanda ya kula da ni. Hira ta yi dadi kenan. Ke Hafsat dauko min fura a frij da Cup.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana maganar tare da gyara zama, haka yaki yarda su hada idanu da mahaifiyarsa domin , ya sani tana kallon Kwayar idanunsa ta gama gano shi. Domin idanun a lumshe suke sunyi jazir, ga wani irin kasala da yake fama da ita. Yana nan zaune yana shan furar, Nasrcen ta shigo tana bin bango. Yana son zuwa ya Karaso da ita, idanun Umma yana kafe akansa. Ta laluba ta zauna tana gaida Umma cikin yanayinta na sanyi. Babu wanda ya amsa mata, don haka_ tayi shiru tana wasa da ‘yan yatsunta. Babu wanda ya yi maganar Kamshin Sultan da ke fita* daga jikin Nasreen, amma kuma zuciyarsu a cike suke. Sultan ya mike, ya Karaso gabanta ya kama hannunta ya manna akan kofin furar sannan ya ce, “Gashi ki shanye ragowata.” Nasreen ta yi murmushi ta kafa kofin a baki, shi kuma ya sha mur kawai ya wuce ciki. Umma_ ta yi shiru tana nazarin irin wannan farin cikin da Sultan yake ciki na menene? Zakiyya ta dubi Umma tana son yin kuka, Umma ta harareta, hakan yasa ta dake kawai. Cikin dare kowa yana barci, Sultan yana kwance tsakiyar gadonsa ya kasa tsaida KwakKwarar tunani. Ya Kosa su sami appointment kamar yadda Al-ameen ya gaya
masa, su bar Kasar nan. Sauko da Kafafunsa ya yi yana jin zai bi shawarar da zuciyarsa take gaya masa. A hankali ya fice zuwa dakin da Nasreen take kwance kusa da Hafsat. Sai da ya wuce Ummansa a falo tana kwance a nan, da alamun yau a wurin take jin kwana. Nasreen ma idanunta biyu, tana jin motsi ta ji Kamshinsa ta rufe idanunta tana Salati a zuciyarta, ta tabbatar yau zai tona mata asiri. Dauke numfashinta ta yi a lokacin da ya dauketa cak! Tsoro sosai ya _ Shigeta, za ta yi magana yasa bakinsa ya hanata maganar. Sai da ya tabbatar da ta yi _ laushi sosal, sannan ya fice da ita. Yana kusa da ‘ mahaifiyarsa ya ji motsinta, hakan yasa ya dakata har sai da ya tabbatar da ba tashin za ta yi ‘ba, sannan ya wuce abinsa. A tsakiyar gadonsa ya shimfideta ya dora kansa a bisa kafadarta, “Nasreen..” Ya kira sunanta cikin wata murya wacce bata san yana Boye da irinta ba. Ta kasa amsawa sai ma sake tattaro natsuwarta da ta yi akansa. Hannunta ya kama ya tura a cikin gashin gansa kafin ya fara magana, “Nasreen, ina shan wahala a sakamakon rashin ki kusa. A baya nasha wuya, a zatona Karshen wahalar ta zo? Ashe yanzu aka fara? Ki Www.bankinhausanovels.com.ng
gaya min ta inda zan iya ci gaba da zuba idanu, ganinki ma yana neman ya gagareni. Sai inje wurin aiki ban saki a idanuna ba, idan na dawo zan ga kowa zaune a falo amma banda ke Nasreen. Don Allah ki dinga daurewa kina yakice dukkan wata kunya kina fitowa nima in ganki kin ? Gobe ki shirya zan gayawa Umma zan kai ki asibiti a duba idanunki za ki ga likita kin ji? Yi min alKawarin za ki biyo ni.” Tana jin sonsa kamar ta faso Kirjinta ta ciro Son ta nuna – masa don ya fi gazgata ta. Ta rasa ta yadda zata
iya yi masa bayanin irin abinda take ji a cikin zuciyarta a sanadiyyarsa. ,
A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.”
Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa
Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wani boyayyen labari mai matukar muni a tsakanin mu da gidan ku, ban sani ba, ko tsinto mu aka yi. Sai dai idan na tuna kalaman Abba da yake cewa tun muna ciki kake dawainiya da mu, haka kai ma kana yawan gaya min tun muna ciki kake son mu, sai indimauce, inrude ina neman wanda zai buda min wannan sarkakKiyar da ke faruwa. Don Allah ku sanar da ni abubuwan nan domin infahimta. Su waye lyayena?
‘““Wacce Kaddara ce haka a jikinmu da har Umma take tsananin Kyamatar mu? Da gaske mu din haihuwar Karkashin mota ce? Ko kuwa wata Hausar ce daban? Ka gaya min wacece ni? Kai kadai za ka iya bude min komai kai tsaye. Ban taba tunanin tambayarka ba ne, saboda ina tsoron jin irin amsar da za ka ba ni, ko kuma irin yadda za ka daukeni a matsayin butulu wacce ta
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG