RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.”
Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa
Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wani boyayyen labari mai matukar muni a tsakanin mu da gidan ku, ban sani ba, ko tsinto mu aka yi. Sai dai idan na tuna kalaman Abba da yake cewa tun muna ciki kake dawainiya da mu, haka kai ma kana yawan gaya min tun muna ciki kake son mu, sai indimauce, inrude ina neman wanda zai buda min wannan sarkakKiyar da ke faruwa. Don Allah ku sanar da ni abubuwan nan domin infahimta. Su waye lyayena?
‘““Wacce Kaddara ce haka a jikinmu da har Umma take tsananin Kyamatar mu? Da gaske mu din haihuwar Karkashin mota ce? Ko kuwa wata Hausar ce daban? Ka gaya min wacece ni? Kai kadai za ka iya bude min komai kai tsaye. Ban taba tunanin tambayarka ba ne, saboda ina tsoron jin irin amsar da za ka ba ni, ko kuma irin yadda za ka daukeni a matsayin butulu wacce ta
ZAMU TASHI
kasa godewa Allah da irin baiwar da ya bani, wajen suturtani a cikin gidanku, ya yi min baiwar ilimin addini da na boko.”
Sultan idan hankalinsa ya yi dubu to ya tashi, ya jima yana tsoron zuwar wannan ranar domin ba shi da cikakken amsar da zai iya ba ta, haka har yanzu ba ta yi girman da za ta iya daukar tashin hankali irin wannan ba, ya so ne sai komai ya natsa sannan ya dauke ta zuwa gun dangin mahaifiyarta. Haka yana tsoron ya gaya’ mata ta tada hankalinta wajen neman ubanta, wanda a yanzu bai san wanene wannan uban ba.: Sai da ya tattaro dukkan natsuwarsa sannan ya ja dogon hancinta, wanda kullum ya hadu da ita sai ya taba, “Nasreen na san idan na rantse maki za ki yarda da ni ko? Wallahi ba a KarKashin mota aka haife ku ba, ina kika taba jin an haihu a KarKashin mota? Kuma kina da uwa kina da uba kina da dangi kamar kowa. Ina jiran mutane su gama abubuwan su ni kuma a lokacin ne zan ba kowa kunya, zan dauko mahaifinki ki gan shi har ku zauna kusha hirarku. Don Allah kada ki sake yi min irin maganar nan kin ji?”
Babu musu ta daga kanta, “Na ji, don Allah ka yafe min don Allah. Insha Allahu, ba zan sake yin maganar ba.
Sai da yasa hannunsa ya warware gashinta. da ta tubke sannan ya ce, “Ba ki yi min komai ba, haka yin maganar da kika yi, ba zaisa ince maki butulu ba, har abada kin gama min komai da kika zauna a matsayin matata. Ki Kara haquri watarana sai labari.”
Ba ta yi magana ba, domin sakon da yake tura mata suna cin nasarar isowa inda ake bukatar su iso. Sun yi nisa a wata. duniya suka ji bugun Kofa hakan yasa ta. Kankame shi.
Ya zame kansa ya mike zai je ya bude, ta kame shi ta mayar da shi Kirjinta da yake sake gigita shi, ta yi magana a hankali, “Za ka bude kofa a yanayin da nake ciki?” Sai yanzu ya dawo da dubansa jikinta, ta dan haskem fitilar ya fahimci abinda take sufi, don haka ya mayar mata da kayanta a natse kamar ba shi bane ake buga masa kofa da Karfin tsiya. Ya maidata ya kwantar ya jawo mata bargo, sannan ya kashe wutar dakin gaba daya ya dawo duhu. Yana budewa Zakiyya tana kokarin cusa kanta a cikin dakin. Ya kalleta tare da yamutsa fuska yana
* kallon su Umma da Hafsat da duk suka yi cirkocirko, “Umma lafiya kuwa? Me ke faruwa ne?”
Umma ta tabe baki, “Yau sai Nasreen ta bar gidan nan. Ashe yawon dare yarinyar nan take fita?” Sultan ya bata fuska, “Haba Umma ki dinga kyautata zato a gun dan’adam. Me ya faru kuma?”
Umma ta ce, “Idan Nasreen ba tana tare da kai bane, to babu ita a cikin gidan nan.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya zaro idanu kamar gaske, ya kuma nuna tashin hankalinsa a fili, hakan ya sa dukkansu da suke zargin Nasreen tana tare da shi * suka kauda tunanin, “Nasreen ta fita a gidan nan? Kuma anduba ko ina? Kai babu yadda za a° yi ta iya fita bayan ga “yan sanda. Mu je gurin su din.”
A Kaggauce suka fice, Umma tana jin dadi a ranta ta riga tasan Karshen zaman Nasreen ne yazo a gidan, domin ita zarginta ya koma ko tana tare da daya daga cikin ‘yan sandan ne?”
Suna ficewa Nasreen ta laluba ta nufi Kitchen, ta laluba ta tara ruwan zafi a famfo ta tsaya shiru gabanta yana fadiwa da Karfi. Tunani ne fal a cikin cikinta, haka kalaman Umma da ta ji suna ta yi mata yawo a tsakiyar kai, tana
mamakin yadda Umma za ta dinga cewa tana bin maza, tana dangantata da Zina, wannan abun yana matuKar yi mata ciwo. .
Sultan ya tsaya a gaban daya daga cikin ‘yan sandan wanda idanunsa biyu ya ce, “Kun ga Nasrcen ta fitonan?”
Ya girgiza kai ya ce, “Oga sir, ina nan zaune ban tashi ko‘ina ba, babu wacce ta fito nan.
Kawai Sultan ya juya yana cewa, “Anya Nasrcen ta bar gidan nan a tsohon daren nan? Babu mutumin da zai iya fita a gidan nan ba tare da izinina ba, bare kuma ficewar dare, ai da na sallame su domin sun zama marasa amfani. Mu koma ciki a sake duba bandaki ko wani wurin.”
Hafsat ta yi carab ta ce, “Har bandakin na duba babu ita.”
Banga komai ba, suka dawo falo yana . magana da Karfi, “Yanzu ina Nasrccn taje? Lallai idan ya tabbata ta fitan, zan kuwa bata mata rai. Ko da kuwa nan da Gate ta je. Yarinyar da bata iya dogon tafiya ita kadai shi ne za ta fice?” Nasrcen ta saki ajiyar zuciya, sannan ta dan kwarawa Kafarta ruwan zafin da ta dibo, duk da babu zafin kirki sai ta fasa Kara, hakan yasa
Sultan yayi hanyar kitchen da sauri har ya riga su shiga. Yana zuwa ya riketa sosai a jikinsa, kasancewar akwai Kamshin turarensa a jikin Nasreen Umma tana iya ganewa suna tare shi ya sa ya yanke hakan. Gabadaya aka shigo ana leken Kafafun da take ta wash! Wash!! Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultanya dubi’ Hafsat ya ce, “Ke kawo min gishiri. Haba Nasreen na fara gajiya da : lamarinki, kina’sane da ba gani kike yi ba, amma – sai ki dinga zuwa inda za ki ji ciwo don ki bar ni . da wahala ko? Me ya sa:ba za ki tashi Hafsat ta kawo maki ruwan zafin ba?”
Hafsat ta murguda baki tace “Kuma ” Yaya idonta biyu*lokacin, ashe ta sadada ta fita.”
Sultan ya dago yana dubanta cikin takaici, “Cewa na yi ki:samo.min gishiri.”*
Nasren ta fara fitar da hawayen bakin cikin yadda Umma bata taba kamata da wani ba, amma take dangantata da zina. Bayan ta sani shaidar zina a musulunci abu ne mai matuKar wahala. . .
Umma da Zakiyya suka dub juna cike da farin ciki yau Sultan ya taba ‘yar Gold. Da kansa ya shafamata gishirin kadan don yana sane da ba konewa ta yi ba. Yana dago ta ya ce.
“I love you wife.” A hankali ya yi maganar babu wanda ya ji sa ita da aka fada dominta.
Sakon ya ratsa ta har ta saki murmushi cikin hawayen ta motsa labbanta. A wurin duk suka aika wa juna sako wanda a zahiri babu wanda ya gani haka babu wanda ya fahimta, duk wayewar da Umma take kirawowa kanta.
‘ A falo ya ajiye ta ya dubi Hafsat ya ce, ‘ “Ke, hado mata tea.” Babu musu ta wuce ta hado tea, ya mika mata tana sha. Bayan ta sha fiye da ” rabi ne ta ajiye a nan. Umma ta tabe baki, “In banda iyayi wai * tashin shan tea a daddare, da a can gidan matsafan waye yake kawo maki tea cikin dare? Ke ni bari in gaya maki ba na son tashin dare, ki daina bana so. Wannan iskancin ba zan taba daukarsa ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya kafe mahaifiyarsa da idanu yana jin dacin abubuwan da take fada akanta, sai dai ba shi da daman hanawa, da yan. dama da bai bari har abin ya yi nisa haka ba. Ya dube ta yadda ta yi shiru ya ce, “Gobe zan kai ki asibiti a sake duba idanun nan, kafin tafiyarki London ya tabbata. Sai ki shirya da wuri in kai ki in dawo in mayar da ke gida.”
Umma ta dubi Zakiyya sai kuma ta ce, “A‘a bai kamata ka je kai ta asibits ita kadai ba, kamar babu mutine a gidan. Ke Zakiyya da Hafsat ku shirya goben ku raka su.”
Dukkansu suka amsa, shi kuwa kallon mahaifiyarsa kawai yake ransa a Bace. yanzu ba shi da halin fita da matarsa har sai an hada shi da ‘yan rakiya? Shi kenan tsakaninsa da matarsa an sa Hijabi kenan? Rintse idanunsa ya yi yace. “Hafsat, kama hannunta ku koma ciki” ~
Umma ta ce, “A kama hannun wa? ~ Yarinyar da ta iya zuwa kitchen, ta iya shigowa nan, ita ce yau saboda gulma za a kama ~~ hannunta? Ban yarda ba, ban amince ba_ Ta tashi ta lalubi bango ta koma inda ta fito. Ke hafsat wuce ki bar ta.”
Nasreen ta yi saurin miKewa tana dan rintse idanu, “Deedi ka bari zan iya tafiya da kaina ba sai an kai ni ba. Mu tashi lafiya”™ ta yi gaba abinta.
Da idanu ya rakata yana jin tausafiitta, ana cin zarafinta a wurin da aka fi Karfinsa;Saboda bakin ciki a nan falon ya kwanta, musamman da yaga Zakiyya ta ki tafiya don haka yake zargin idan ta bi‘shi za ta gane Nasreen ta shiga dakin
don haka yaki amince mata ya kwanta a nan falon. Sai da asuba ya koma ciki, a nan ya ga ribom dinta haka gadon gaba daya a yamutse yake. Murmushi ya Kwace masa, ya shinshini ribom din ya tura shi cikin kayansa sannan ya yi alwala ya wuce .
Da safe ya gama shirinsa tsaf! Ya fito zuwa dakin Zakiyya, abin mamaki ba ta nan, don haka ya wuce dakin Nasreen. A nan ya sameta ita da Hafsat sun caba kwalliya kamar wadanda za su je gun biki. Gaishe shi suke yi, ya kasa amsawa saboda mamaki,
“Ina za ku je haka kuka yi wannan kwalliyar?” Gaba daya jikin su ya dan yi sanyi, don haka suka hau kame-kame. “Asibiti da Umma ta ce za mu raka ku.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Mamakin fuskarsa ta Karu. Ya waiwaya yana duban Nasreen, tana zaune daga ita sai doguwar riga, hannunta rike da dan Karamin carbi tana ja. Ya sake waiwayawa yana duban . Umma da ke zaune tana karyawa hankalinta kwance. Ya ce, “Amma dai kuna da Karfin hali, ita wacce za a kai ta asibitin ba ta shirya ba, sai
ku ne iyayen iyayi ko? To babu inda zaku je.Tunda baku da lissafi.”
Umma ta karkace bayan ta danna dankalin turawa a baki ta kurbi ruwan tea sannan ta ce, “Babu abinda zai hana su, zuwa Asibitin nan. Karyar banza kake yi Wallahi. Ai ba sai ka zo gabana kana kushe su ba, na sani sarai ban isa da kai ba, amma ina tabbatar maka duk abinda ka shuka a gidan duniya sai ka girbe shi.”
Sultan ya shafi kansa, “Umma ki yi wa Allah kada ki yi min baki akan yaran nan. Ni abin ne ya bani mamaki, ta yadda daga zuwa Asibiti sai ayi kwalliya, sai ka ce wanda na gaya masu za mu je gidan biki. Ke me ya hanaki . shiryawa?”’
Kafin ta yi magana Umma ta yi carab, “Gulma mana! Wai ita mai addini ta tsaya tana jan carbi kamar sabuwar tuba. Ko da yake menene ma..”
Sultan ya yi saurin taran numfashinta, “Umma ki barta a haka za ta tafi kin san ita bata kwalliya.”
“ Umma ta tabe baki, “To ina makauniya ina kwalliya? Ai ko ta yi sai dai ta bata fuskarta, tunda ba kallon madubi za ta yi ba.”
Sultan yana kallon yadda fuskar Nasreen ta sauya, bai ce komai ba, ya dubeta, “Nasreen tashi ki dauko Hijabinki.” Babu musu ta tashi ta nufi dakinta. Tana shiga ya bi bayanta.
Umma ta saki baki tana kallonsa. Abinda ya yi zato shi ya tarar, tana share hawayenta wasu suna sake zuba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Jawo ta ya yi jikinsa hakan yasa ta fashe da kuka. “Bana son kuka Nasreen, idan kina kukan
nan sai in ga kamar baki dauki Umma a matsayin uwa a gareki ba. Ya kamata a ce kin saba da dukkan irin wannan halayyar na Umma.”
Nasreen ta ce a zuciyarta, shi cin mutunci ba a sabo da shi, domin kullum danye yake sake komawa, a maimakon a barshi ya bushe har ganyen ya kakkabe. A zahiri kuma sai ta shiga goge hawayenta yana taya ta. Ya dauko hijabin ya sanya mata, sannan ya dube ta ya ce, “Baki ga yadda hijabin ya yi maki kyau ba.” Ya sumbaci goshinta sannan ya kamo hannunta suka fito. Suna kawowa falon ya saki hannun ya Karasa gun Umma ya ce, “Za mu tafi sai mun dawo.” Ta amsa da a dawo lafiya.
A hanya babu wanda ya cewa wani zo ka ci kanka, kowannen su da irin tunaninsa. Shi Sultan
tuni ya gama kissima dukkan abubuwan da zai yi.
Suna isa Asibitin ya ajiye su a Receiption Ya jawo hannun Nasreen ya ce su zauna anan, su za su je su ga Dokto. Ya zagaya ta baya, ya shiga mota Nasreen ma ta shiga, duk basu sani ba, dan sanda ya ja mota suka fice. Kai tsaye babban Hotel ya wuce da ita, ya kama daki ya shige abinsa.
Nasreen dai binsa take yi bata san inda suka shiga ba, har sai da ta ji sanyin A.C. bayan ta zauna a bisa shimfidadden gadon, “Dee ina ne nan kuma? Wurin wa muka je? Dee ina tsoro kada su Hafsat su ankare bamu nan. Don Allah mu koma.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu
ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.”
Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya Kura mata ido yana murmushi, bai taba sanin tana da kishi ba sai yau, dama kuma abinda yake son ya gani kenan.
“Kishi kike yi ne?” Ya tambaye ta cikin zolaya.
Sake Bata fuska ta yi ta ce. “Dee ni tsoro nake ji me zai kawo mu Hotel? Bai kamata ba, ga gidanmu na sunna sai mun je wani Hotel? Dee gaski…”
Ba ta samu daman Karashe abinda take son Karasawa ba, ta hadu da zazzafar soyayyar Sultan da take kashe ta a kowani irin lokaci. Dole ta sakar masa jikinta, ba don ta so ba, sai dan salon soyayyarsa daban yake. Sun jima a wata duniyar da bata san wacce ce ba, daga bisani ya Kyale ta dan kansa, domin bai mance
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG