RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu
ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.”
Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya Kura mata ido yana murmushi, bai taba sanin tana da kishi ba sai yau, dama kuma abinda yake son ya gani kenan.
“Kishi kike yi ne?” Ya tambaye ta cikin zolaya.
Sake Bata fuska ta yi ta ce. “Dee ni tsoro nake ji me zai kawo mu Hotel? Bai kamata ba, ga gidanmu na sunna sai mun je wani Hotel? Dee gaski…”
Ba ta samu daman Karashe abinda take son Karasawa ba, ta hadu da zazzafar soyayyar Sultan da take kashe ta a kowani irin lokaci. Dole ta sakar masa jikinta, ba don ta so ba, sai dan salon soyayyarsa daban yake. Sun jima a wata duniyar da bata san wacce ce ba, daga bisani ya Kyale ta dan kansa, domin bai mance
ZAMU TASHI
alKawarin da ya yi ba. Nasreen tana gigita shi ta yadda yake jin kansa kamar sabon Sarki. Yana sonta ya shirya fuskantar kowani irin Kalubale ne akanta.
Tana kwance a gefensa barci ya kwasheta, shima a nan ya sami natsuwa har barcin ya kwashe shi, cikin kyakkyawan mafarki mai cike da natsuwa. Zai iya rantsewa bai taba samun irin wannan barci ba kamar yau. A Kalla sun kwashi awa biyar suna barcin sannan Nasreen ta fara farkawa, ta lalubo shi tana bugunsa a hankali. “Dee ka tashi mu tafi bansan Karfe nawa ne . yanzu ba.” Sultan ya sake jawota jiki ya rufe su da bargo ya ce, “Yanzu Karfe goma sha daya na safe, sai Karfe daya zamu koma.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Bata da yadda za ta yi dole ta koma ta kwantar da kai. Irin abubuwan da yake yi mata ne, yasa ta riKe hannunsa tana girgiza masa kai kamar za ta yi kuka. Yana son salon shagwabar yarinyar. Karfe daya ya fada bandaki ya watsa ruwa, ya taimaka mata itama ta yi wankan, duk da bata iya yi a gabansa ba har sai da ya fice saboda kunya. Alwala suka yi, sannan ya ja su Sallah suka gabatar da Sallar azahar, sannan ya rike hannunta suna jerowa. Duk wanda ya zo
wuce Wa Sai ya sake waiwayowa ya dube su, sun yi matuKar kyau, haka sun dace da juna.
Suka fito suka koma Asibitin, ta inda suka bi ta nan suka sake biyo wa suka dawo inda suka bar su Hafsat. Gaba daya kwalliyar nan da suka sha, ta watse, fuska sai maiko take yi saboda wahala. Sun gaji da zama, har sun siya maltina sun sha, amma duk da hakan sai mita suke yi. Suna ganin sun iso, kowacce ta ja bakinta ta yi shiru. Yadda Zakiyya ta kafe su da ido yasa Sultan daure fuska sosai, ya kuma kamo hannun Nasreen ya ce, “Mu je cikin mota.” ’
Babu musu ta biyo shi, sauran ma suka mara masu baya. A mota kowacce tambaya ce cike da cikinta, amma babu fuskar aiwatar da hakan. ‘ , Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sun iso gida ne, Umma ta ce, “Ya na ganku duk kun sha wahala?” Hafsa ta hada rai ba tare da ta ce komai ba, sai Zakiyya ce ta ce, “Umma tunda suka shiga cikin asibitin babu wanda ya sake sanya su a idanunsa. Muna zaune duk mun sha wahala mun lalace.”
Umman ta dubi Sultan, wanda tuni ya kama hanyar barin falon. Umma bata iya cewa komai ba, har ya bacewa ganinta. Juyo wa ta yi gun
Nasreen tana harararta, wai aikin banza a harara a duhu, domin kuwa Nasreen bata san ma tana yi ba. Ta antayo mata tambayar da ya gigita ta, “Ke Nasreen ki gaya min gaskiya tun kafin in yi Kasa-Kasa dake wani lungun kuka shige a asibitin? Ina ya kai ki?”
Nasreen ta dan diririce, hakan yasa Umman ta sake hasko wani abin, ta gyara zama, “Ina takardun da Doctor ya baki? Me ya ce akan idanun?” Nasreen ta rude ta kasa magana, sai muryar Sultan suka ji yana magana, “Doctor ya ce mu dawo gobe za su sake gwada idanun, daga nan kuma sai su bamu result
Umma ta Harare shi, a lokaci guda Nasreen ta saki KaKarfar ajiyar zuciya. Bata kallon Umma, amma jikinta yana bata tana shan uwar harara. Umma ta zame mata kishiya, ta hanata sakat! Ta Ki amincewa ta barta da mijinta, ta amince ta kashe nata auren ta zo ta zauna tana zaman kashe auren danta. Da za ta iya da ta baiwa Umma shawarar auren Sultan Kila ta sami natsuwar irin wannan dakon da take yi
Ita kuma Zakiyya da ta zama bita zai-zai da za ta iya da ta bata shawarar ta koma ta nemi dukkan abubuwan da za ta gyara kanta, domin Www.bankinhausanovels.com.ng
dawo da martabarta agun miji, a maimakon zaman sa ido da take yi masu, da kuma kasa Kyale su su zauna su biyu. Sai dai duk wayonta, duk irin gadin da take yi wa mijinta, duk irin matakan tsaron da take sakawa, hakan bai hana mijinta nuna mata cewar shi namiji ne mai cikakken wayo da dabara ba.
Ya nuna mata har yanzu mata basu yi wayon da za su iya gwada wayon su da na mijin su ba. Ya nuna mata ita Karamar ‘yar sa ido ce, sai dai idan bai yi ninyar aikata abu ba, amma da gudu zai aikata ba tare da wata ta taka masa burki ba. Suna ta gadinta, shi kuma yana daukarta a duk lokacin da ya so ya maidota lokacin da yake so. Da za su gane da sun daina wahalar da kansu wajen sanya masu idanu a cikin rayuwar amarcinta.
Umma ta dube shi rai a Bace, “Wai shin kai na tambaya ne? Kana bani mamaki idan kana da gaskiya menene naka na tsoma min baki? Ka barta mana ta yi magana da bakinta, ai makauniya ce kawai ba kurma ba. Kar ko ka dauki mataki akanta tana son raina ni ina magana ta yi banza da ni? Jiya-jiya na gaya maka matar nan taka yawon banza take fita,
amma ka yi min kunnen uwar shcgu, kai a dole baka son laifinta ko? Wallahi ba baki nake yi maka ba, jiki magayi, lokacin da za ta nuna maka asalin kalarta, nawa idanu.” Nasrcen ta dafe Kirjinta tana cewa a zuciyarta, “Insha Allahu, babu ranar da Dee zai yi danasanin aurena, babu ranar da zai kamani da ha’intarsa. Allah ka raba ni da hada aurena da zina, idan nayi hakan me zan gayawa Mahallicina? Da wasu idanun zan dubi mijina in ce ya yafe min?”
Tuni hawaye suka tsinke mata, idan da abinda ta tsana bai wuce a hada ta da sharrin zina ba, da a ce Zakiyya ta yi wannan maganar, da har tashin dare sai ta yi ta roki Allah ya saka mata wannan Kazafin, ta tabbata Allah ba zai jinkirta amsar addu’arta ba. Sai dai wacce ta yi wannan addu’ar ta fi Karfinta, hasalima a matsayin uwa take kallonta. Sultan ya shafi kansa yana satan kallon Nasreen tana kuka, duk sai ya ji babu dadi, ya tsani a taba masa Nasreen, baya son ganin hawayenta tun tana Karama bare kuma yanzu da ta girma.
“Ki yi hakuri.” Ya fada yana duban Umma, wanda a zahiri da Nasrcen yake yi, yaci gaba da cewa, “Bana son in zama ni ne sanadin zubar da hawayenki, ki dinga yi min addu’a ne watarana sai labari.”
Nasreen da maganganunsa suka shigeta, ta ji wani irin sanyi yana shigarta, tabbas saKon da ya aika mata sun iso har cikin kunnuwanta zuwa zuciyarta, da ke narkewa da wani abu mai sanyi, sabanin dazu da yake tafarfasa saboda bacin rai. Www.bankinhausanovels.com.ng
Umma kuwa sai ta sakankance da ita yake yi, don haka ta ji sanyi a ranta. Sultan ya juya kawai yana cewa, “Allah na gode maka. Nayi amfani da kalamai masu Karanci, na wanzar da farin ciki a zuciyoyi biyu masu matuKar_. mahimmanci a zuciyata. Allah ya saka maki Umma, ke kika kawo ni duniya kika rene ni, har na girma na ga mahaifiyar Nasreen na zama silar taimakonta. Da baki haifeni ba, Umma da ban zama abinda na zama ba. Allah ya saka maki mahaifiyata, Allah ya haskaka maki duk wani abu da kike ganinsa a cikin duhu. Har abada ke nake fara yi wa addu’a kafin kowa ya biyo baya.”
Kai tsaye Office ya nufa, yana jin nishadi idan ya tuna kasancewarsa da Nasreen dinsa. Yana tashi daga office kai tsaye ya nufi gidan ‘
Yumnah ya sameta da mijinta a falo suna shan hirar su. Ya shigo suka zauna yana cin abinci suna dan taba hira.
Yumnah ta mike za ta basu wuri domin taga sun dauko maganar case din su. Sultan ya dube ta ya ce, “Kanwata zo mana, wurinki na zo.”
Yumnah ta dawo da baya ta zauna tana dubansa. Ya tashi zaune ya ce, “Don Allah wannan Kamshin da na ji a wurin Nasreen, da yadda fatarta ta yi kyau gashinta ya sake wani tsawo da sheki, a ina kika samo wadannan abubuwan ne? Da gaske nake yi, da kaina zan je innemo mata kayayyakin nan. Ni kadai nasan irin farin cikin da nake tsintar kaina da zarar na shaki Kamshin nan.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Yumnah ta yi dariya, haka ma Dr Astlaf, kuma gaba daya suka zuba mata idanu domin da gaske suke yi, suna jin dadin Kamshin nan. Yumnah ta dauki wayarta ta ce, sanya lambar nan tukun, 08068906212. Babu musu ya kwafe lambar yana sake dubanta domin neman Karin bayani. Ai kuwa ta dan gyara zama,
“Sunansa Jafar, yana kasuwan sabon gari a birnin Zaria, haka duk inda kake a fadin duniyar nan yana aiko da kaya. Shago ne da ya amsa
sunansa, kaf Zaria suna alfahari da shi. Kana zuwa Sabon Gari wajen kasuwar mata, ma kawai ka ce shagon Jafar kake nema, za a kai ka har can. Duk kalolin sabulai humura dilka da komai da komai da ya Kunshi Kamshi yana saidawa, haka yana siyar da kaya Original baya kawo kaya marasa kyau. Idan kana neman ko misk ne, indai mai kyau ne, to ka garzaya shagonsa.”
Ta dan muskuta ta gyara zamanta sosai, don ta ji dadin yi masa bayani. Ta ce “Kuma babu abinda zai baka mamaki sai idan na gaya maka da dubu dayanka ma idan kaje shagon Jafar za ka sami abubuwa masu inganci.Yadda kasan domin talakawa aka bude shi, Idan a wani shago ana siyar da abu dari uku a wurinsa za ka samu a dari biyu da hamsin. Ban taba ganin wanda ya siya abu a gunsa ya dawo yana danasani ba. Kayan gyaran gashi kuwa, abin ba’a magana, ka dai ga yadda kan Nasreen ya yi kyau da cika da tsawo, wannan duk aikin shagon nan ne dai da nake gaya maka na Jafar. Za ka gane abinda nake gaya maka ne, idan ka je shagon ka gan shi cike da matan Shuwa, sai abin ya baka tsoro. Hausawan mu ma ba a bar su a baya ba, duk sun gane sirrin. Doktona ka matsa min kana son sanin sirrin Kamshina, yau dai ga Yayana ya sanya na fada ban shirya ba, kuma abinda ya sa na gaya masa, don dai Nasreen din mu bata gani ne, haka bata san gari ba.”
. Ta Karasa tana zura idanunta a cikin na mijinta, a lokaci guda ta kashe masa idanu tana jifansa da shu’umin murmushi.
Shi kuwa Sultan ji yake idan ma miliyan ne zai kashe a shagon Jafar. Zai je da kansa ba aike ba, ya sake siyawa Nasreen, duk da ta gaya masa Kamshin ya zauna sosai a jikinta, hakan ba zai hana sake siya mata ba. Babu namijin da a ~ duniya zai ce baya son Kamshi sai dai idan bai samu ba. , Www.bankinhausanovels.com.ng
Aslaf ya dubi matarsa cikin kulawa ya ce, “Na gode maki da wannan bayanin, nima yanzu zan tura wa amaryar da zan Karo lambar Jafar din,ta je ta nemi Kamshin nan, domin kuwa abinda ya hanani Kara aure kenan, tunanin yadda zan iya hada shimfida da wata, bayan bata kasance mai irin Kamshinki ba, ko bata iya girki ba. Babu matsala zan ci da hakuri, amma rashin Kamshin nan matsala ce, saboda tana cire soyayya a Zuciyar miji.”
Yumnah ta kafe shi da idanu har ya dire maganar sannan ta yi murmushi, “Oho sai-ta Zo. Akwai inda har abada bata isa ta kamo ni ba, in dai ni ce babu duka babu zagi, babu habaici, da Kafafunta za ta fice ta bar min gidana, domin sunanta wacce ta zo kallon baKin ciki.”
Sultan ya shafi kansa yana murmushi, “Mata! Kun shiga uku da kishi. Kun ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, anya da gaske ne? Idan gaskiya ce, ai murna za ki yi da zuwanta, sannan ki gaya mata dukkan sirrikan rije miji.”
Yumnah ta dalalo idanu ta dafe Kirji, “Wa? Ni? Allah ya tsareni Yaya Sultan. Ai lokacin da zan gaya mata sirrina na shiga uku na lalace, a lokacin ni kuma za ta yi ta Kokarin ganin ta watso ni waje, da ni da ‘ya’yana. Mutanen yanzu ne sam babu Allah a zuciyarsu, za ka ga kai ka rike mutum da zuciyarsa guda, shi kuma yana can yana haKa maka Katon rami. Wallahi idan na ga mutum a rana ba zan sake ingiza shi ba, amma kuma zan ratsa in wuce shi. Kai dai Allah shi kyauta, Allah kuma ya tsare Nasreen da wannan Zakiyyar don naga babu Allah a ranta.”
Kamar ta fama wa Sultan inda yake masa KaiKayi ya yi murmushi wanda iyakarsa fuska ya shafi sajensa yana sake duban yadda Aslaf ya
~ kafe Yumnah da idanu kamar mai son fahimtar wani abu. “Ni zan koma gida, tunda na sami abinda nake so. Haka kuma Umma tana gida takan so in zo mu zauna muna ‘yar hira.”
Aslaf ya mike yana cewa, “Yumnah babu abinda zai sa in Karo maki kishiya, saboda matan yanzu ba a Kwankwasa su bare ka gane ta gari. Kada in zo in auro wacce za ta raba ni da ke, ta raba ni da ‘ya’yana. Kin ga kuwa mutuwa zan yi, tunda ku ne rayuwata.” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan ya jinjina kai ya ce, “Kai dai kawai ayi addu’a. Da Umma za ta bar ni sai na dauke Nasreen daga gidana, in sauya mata wani gidan. Idan basu ganin juna komai zai zo da sauKi.” Aslaf ya dubi Sultan ya ce, “Ahaf! Ni tausayinka nake ji duk ranar da Umma tasan cewar ka zuga anyi mata kishiya. A wannan ranar sai ka gwammace baka fito duniyar ba.”
Sultan ya yi murmushi, “Kasan Kara auren kamawa take yi, yanzu hankalin mahaifina da na danginsa duk sun kwanta. Abbana ya yi Kiba ya ci gaba da harkokinsa kamar kowa. Duk da har kullum yana yawan yi min maganar Umma, Abba yana son Umma Aslaf, amma Umma ta
kasa gane hakan. Ni insha Allahu ma ranar da za ta san da wannan labarin tuni bana Kasar, ina can _ ina neman lafiyar idanun matata.”
Cikin raha suka rako shi suna ‘yar hira atsakani. Aslaf ya tabbatar masa da zai zo ya gaida Umma. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da isarsa gida ya sami Nasreen ce kadai a falo tana goge-goge. Saura Kiris wata kwalba ta fado mata, ya Karasa cikin sauri ya rike kwalbar tare da sauya mata wuri. Ransa ya kai matuKa abaci don haka ya ce, “Ke! Waye ya sa ki wannan aikin? Iyye Nace wa ya sanya ki aikin nan?” Nasreen ta yi shiru saboda wani irin tsoronsa da take ji, ga shi dama dazu ta gama kukan rashin Nawfal dinta a kusa da ita, da yana nan duk irin ayyukan nan zai iya amsa yayi Ga masu aiki nan birjik a gida, amma Umma ta tsani ta ganta a zaune yanzu za ta hau Kirkirar aiki tana sanyata. Ita ba gani take yi ba..Ta Kone a hannunta, don haka bata son ya guni ta dunKule jikinta, duk da . irin azaban da hannun yake yi mata. Da Karfi ya – daka mata tsawan da yasa ta daya hannunta har ya ci nasarar ganin Konewar da ta yi. Shiru ya yi yana duban hannun, hakan yasa hawayen – fuskarta Samiun daman ci gaba da sauka. Yana da
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG