RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.” Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.” Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa kuka. Iya gigicewa Alhaji Lukman ya gigice, tambayarta kawai yake waye ya mutu? Cikin kuka take cewa, “Abban Sultan yau ni za ka yi wa haka? Duk yadda na baka kulawa na hana kaina kwanciyar hankali don in kyautata maka, yau kuma dan bana nan shi ne za ka kasa jure wa har sai ka aikata Barna?
ZAMU TASHI
To ya yi kyau sosai, ina tabbatar maka ba zan koma gidanka ba, sai ka bani takardata.” : Alhaji Lukman ya _ yi kasake’~ yana Saurarenta, “Me nayi maki kuma Salma? Me yasa za ki jefe ni da irin wannan kalaman?” . Ajiyar zuciya ta yi tana Kokarin share hawayenta, “Hajiya Ladidi bata kama ka da mairo ba? Bata kama ka ba? Me yasa za ka wulakanta ni a idon mai aikina? Ban ga laifin Mairo ba, laifin wanda ya bata fuska ne, amma na gama zama da mazinaci. Tsawa ya daka mata jikinsa yana rawa, “Ya isa Salma! Haba!. Me ke damunki ne? Za ki iya jifana da ko wacce kalma amma banda Kalma mafi muni da Kazanta. Har kullum ku mata Karamin tunani ke Www.bankinhausanovels.com.ng gareku, namiji zai iya kare martabarki a ko ina, ko da kuwa kin sauya, amma ku babban burinku a gaya maku zunubin mazajen ku, ku fita duniya kuna ihu kuna fadin ba a kyauta maku ba, kuna fadin a sake ku. Na ji ciwo da Salmar da nake yi wa irin wannan son ne take gaya min maganganu masu dacin nan, nayi tur da wannan halin da kika ara kika dora wa kanki. Idan aka bani AlKur’ani zan iya dafa wa matata ita ce za ta bayar da shaidan Kwarai
akaina, sai dai abin takaicin yau da raina nake jin Kazaman kalamai daga bakin wacce na mallakawa zuciyata. Gara ki ce min ba zaki dawo ba, sau dubu da ki ce min mazinaci. Ki dinga bincike kafin yanke hukunci, idan ba haka ba za ki yi ta samun matsala da jama’a da dama daga Karshe ki rabu da mutanen kirki ki kama na banza.” . Abba ya kashe wayar yana jin zuciyarsa babu dadi. Ita dai Mairo tagumi ta yi ta zuba masa idanu, tana kallon son uwargidansa a Www.bankinhausanovels.com.ng idanunsa, ita dama tasan ya dai aureta ne kawai, ba dan tana burge shi ba. Sai yanzu ta sake gazgata abinda bahaushe yake cewa, tsohuwar zuma da ita ake magani, haka duk kyan amarya da yadda take ganin mijinta yana sonta, har abada uwargidansa daban take a cikin zuciyarsa, domin kuwa ita ce Mafarinsa. Don hakane take taya duk macen da ta zama Uwargida murnar samun sarauta mai girma a zuciyar mijinta. Zuciyar Mairo ta nemi ta fara zafi, saboda wannan halittacen kishin da ke maKale a zuciyar kowacce mace, sai ta yi saurin karanta A uzubillahi. Ta kori shaidan, domin idan har ta yi kishi da matar da ta zauna a KarKashinta bata yi adalci ba. ” Ba za ta iya yi masa magana a irin yanayin nan da yake ciki na halin bakin ciki ba, dole ya na buKatar zama shi daya don haka ta mike za ta fice, ya kirawo sunanta_ cikin natsuwa, “Maryama zo ki zauna.” Babu musu ta dawo ta zauna, ya dubeta cikin kulawa, “Na ga fuskarki ta sauya ina fatan ba ni bane na bata maki?” Girgiza kai ta yi, tana murmushi hakan yasa ya gyada kai, suka kuma yin shiru, domin ya rasa me zai ce mata. Ita kuwa Umma ji ta yi danasani yana shigarta, ta san halin Hajiya Ladidi ta hada fada, amma kuma ta kasa gano irin ribar da za ta ci idan har ta hada ta fada da mijinta. Zuciyarta ta kasu gida biyu, sai dai yarda da mijinta ya fi yawa a cikin zuciyarta, tana jin ta amince da shi, ba za ta taba yarda a ce wai Alhaji Lukman zai iya zama kujera daya da Mairo ba, “Lallai da sai na kasheta idan ya so nima a kasha ni.” Ta fada a sarari tana huci. Sultan da Hafsat suka dubi juna, kafin suka dawo da kallon su gun Umma. Sultan ya ce. “Wa za ki kashe Umma?” Tana ganin su ta mike sai kuma ta fara kuka, ta dubi Sultan ta ce, “Ka ji Hajiya Ladidi wai Abbanku yana neman Mairo mai aikin mu.” Gaban Sultan ya fadi, lallai yasan akwai yaki a nan gaba. Ya kasa magana sai dubanta kawai yake yi. Hafsat ta dora hannu a kai kamar wacce aka yi wa mutuwa, “Umma mun shiga uku! Kai Karya ne Abba ba zai taba duban wacce ta fi Mairo ba, bare kuma Mairo. Gidanmu cike yake da ma’aikata maza da mata, babu yadda za ayi Abba ya wulakanta kansa a cikin su. Mun bani Yaya Sultan ka kira Abba baya boye maka komai za ka ji gaskiya a bakinsa.” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Umma ta kamo hannun Sultan suka zauna, ta ce, “Gaskiyar Hafsat ce, na kira shi yana ta min wasu maganganu wai anyi masa sharri, amma yanzu kira shi ka Kara murya sai mu ji abinda zai ce ta hakanne kadai ragowar zuciyar da bata amince da shi ba, za ta Karasa yarda da shi. Sultan na gigice da yawa, nasan halin Abbanka ba zai aikata hakan ba.” Sultan da gabansa ke fadi ya dubi Umma ya ce, “A’a Umma ba sai na kira shi ba, ni na yarda da mahaifina babu abinda zai aikata da ake zarginsa. Kawai sharri ne.”
Umma ta share hawayenta, “Eh na sani Sultan kai dai ka kira shi.” Nasreen ce ta shigo tana lalube, ran Umma ya sake baci ta daka mata tsawa, “Ke! Fice ki bamu wuri muna tattauna abinda ya shafe mu ne, ban ga dalilin shigowan bare ba.” Nasreen ta gigice sosai ta yadda har ta taba hannun da aka yi gyara, ta sake komawa da baya ta kusa faduwa, Sultan ya mije da sauri zai iso wurinta, Umma ta sake riKe hannunsa tana harararsa dole ya koma ya zauna yana dubanta. Zakiyya da har ta sawo kai ta ji irin tijarar da aka yi wa Nasreen sai ta koma gefe, ta labe tana sauraran su. Nasreen kuwa ta yi matukKar daurewa bata yi kuka ba, har sai da ta samu isa Www.bankinhausanovels.com.ng dakinta sannan ta fasa kuka mai Karfi. Gabadaya Sultan ya daina fahimtar mahaifiyarsa hankalinsa ya koma kan Nasreen, ya san cewar tana can tana kuka, don haka ne yake jin damuwa a ransa. Babu shiri ya fitar da wayarsa ya danna lambar wayar Abba gabansa yana ci gaba da fadiwa, ya tabbata idan Abba ya dauka asirinsa da na Abbansa ya gama tonuwa, yana da tabbacin tsine masa kawai za ta yi. Cikin ikon Allah aka sanar da lambar Abba 2 kahe take, hakan yasa Umma ta sake gigicewa. Sultan ya tattaro natsuwarsa sannan ya yi magana, “Ki kwantar da hankalinki Umma gobe insha Allahu zan je Kadunan za ki ji komai.” Umma ta yi hamdala ta kuma ba shi Karfin guiwar ya tafi ba tare da ya sanar masa da zuwansa ba. Da Kyar ta sallame shi yana fitowa kai tsaye dakin Nasreen ya shige ya same ta tana kuka, ya jawota jikinsa yana share mata hawaye, sannan ya rungume ta yana bubbuga bayanta, “Na taba gaya maki na tsani in ga kina kukan nan? Haba Nasreen yaushe za ki saba da halin Umma? Tana cikin bacin rai ne, maganar nan ne na Mairo aka gaya mata sai dai cewa aka yi Abba yana nemanta, kin dai san Umma da kishi shi ne yanzu duk ta tashi hankulan mu. Don Allah ki daina kukan nan.”
Nasreen ta yi luf a jikinsa, tana jin ba za ta iya magana ba, domin da gaske kalaman Umma sun yi mata ciwo, tana son sanin su waye danginta? Duk lalacin su za ta iya zama da su. Sultan ya ji duk zuciyarsa ta jagule. Ya rasa me zai ce mata, kawai sai ya kafe ta da idanunsa. A lokacin ya sami kiran gaggawa, za su fita wani aiki. Cikin gaggawa ya mike zai fita, sai kuma Www.bankinhausanovels.com.ng
ya dawo, ba zai iya barinta a cikin wannan halin ba. “Babyna ta shi ki raka ni wajen aiki. Zan siya maki babyn roba ki dinga wasa da ita.” Murmushi cikin kuka ya subuce mata. Hakan yake son gani don haka ya ji sanyi a zuciyarsa, haka yana da tabbacin zai sami natsuwa wajen fitar. Hannunta ya dauka yasa a kansa, “Yi wa mijinki addu’a zai fita gun aiki. Addu’arki za ta taimaka in je lafiya in dawo lafiya. Ki kauda damuwa a fuskarki idan kika yi haka mijinki zai kwantar da hankalinsa a cikin jama’arsa.”
Nasreen ta shanye kukanta ta yi magana cikin sanyi, “Ya Allah ga mijina, yana da . kamanta gaskiya, ya hana kansa cin haram, ya tsarkake zuciyarsa ta hanyar neman halak! Ya goya marayu, ya inganta karatunsu, ya hana su kukan maraici, ya Allah ka taimake ni ka kare min shi, ka bashi sa’a a dukkan lamuransa, ka makantar da idanunsa a lokacin da aka kusance shi da haram, ka Kara masa hasken idanu a lokacin da Halak take tunkaro shi. .Allah ya tsareka Dee, ya baka nasara akan dukkan abinda ka sanya a gaba.” Sultan ya tsinci kansa da jin dadin addu’ar Nadsreen, duk da ta Karashé muryarta tana rawa, hakan bai hana shi sumbatarta ba, ya dubeta “Kin yi min alqawarin in tafi in kwanta da hankalina ba za ki yi kuka ba? Idan kin san za ki yi kuka in fasa fita in zauna ina renon hawayenki don ganin na hana su zubo wa.” Murmushi ne shimfide a fuskarta, za ta so ta iya kallonsa a lokacin da yake wannan maganar, don haka ta daga kanta, “Nayi maka alKawari.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin sauri ya shafi Kanta ya fice. Bai ga ‘Umma ba, bare Hafsat, hakan ke nuna masa lallai yau Umma tana cikin damuwa. Zakiyya tana ganinsa ta biyo bayansa, bai ce mata komai ba, ya fitar da uniform dinsa ya sanya, ya dauké takalmansa da safa ya zura, ya dauki ‘hula ya sanya. Zakiyya ta bude baki tana kallonsa, zata iya rantsewa bata taba ganin mutumin da Unifoam yake yi masa kyau ba, kamar Sultan gaba daya kayan sun Kara haskaka shi. Shi Kansa. ya gamsu kayan sun karbe shi. Duban ta yayi lokacin da yake gyara zaman hularsa yace, zanje Office.”Zakiyyatace,“To.”Ya dube ta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya kama hanyar fita. Ba zai iya wucewa. bai sake zuwa ya duba Nasreen ba, yana komawa dakin ya same ta zaune ta yi Shiru.Tun kafin ya yi magana ta fara murmusho “Ka yi kyau tamkar dawisu Mayar da kanta tayi ta kwanta a gadon tare da rigingine, “Dee kullum idan na yi Sallah ina sake gode wa Alla da ya bani kai a matsayin mijin aure, tabbas ita din ta daban ce a cikin ‘mata. Ban taba ganin mutumin da yake kyau-da kaki ba, sai akanka.” – Sultan ya zaro ido sosai yana dubanta. Yadda ta kwanta tana kallon sama, yasa ya Karaso ya hada kansa da nata suna shakar Samshin juna, “Anya baki ganin komai Nasreen? Abubuwan da kikeyi suna yi min kama da macen da take gani, ba makauniyar dana sani ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nasreen ta yi murmushinta dake Kara kawata fuskarta ta ce, “Babu makauniya a duniyar nan, musamman akan wanda takeso. Makantar zuciya ita ce Makanta, ba ta idanu ba, zuciyata tana ganinka, tana jinka tana iya siffantaka, tana iya idan kana wuri Zuciyata za ta makance ne Kawai a duk ranar da ta daina son ka, hakan kuma ba zai faru ba, ko da kuwa an dauke numfashina daga jikina.”
Sultan ya nemi ya mance abinda ke gabansa, sai da ya fara KoKarin cikuikuye unifoam din da ya sha guga, sannan ta ankarar da shi. Jiki a mace ya mike ta yi masa sai ya dawo ya fice. Ajiyar zuciya ya Kwace mata, tana son jin Naufal a kusa da ita, Kila hakan zai kwantar mata da hankali, da gaske ta yi kewarsa tana son jin dan uwanta a kusa da ita. Zakiyya da bakin ciki ya isheta ta rasa me za ta yi? Sai kawai ta fice ta dawo ta ajiye ruwan zafi a dai-dai hanyar da Nasreen za ta wuce ta koma dakinta.
Nasreen cikin ikon Allah da ta tashi fitowar sai ta zagaye ta wuce ruwan zafin. Sai kuma ga Umma ta fito tana tafe kamar bata gani ta buge ruwan zafin, ya zubar mata a Kafafu. Ta fasa Kara wanda ya jawo hankalin dukkan mutanen da ke cikin gidan. Zakiyya ta rude iya rude wa musamman da ta ga Kafar Umma ana taba wa tana sabulewa. Hafsat ta gigice ta rike Umma tana kuka. “Wa ya ajiye ruwan zafi a kan hanya?” Zakiyya ta fara kame-kame.
Hafsat ta mike a fusace ta shaKo ta, “Gaya min waye ya ajiye wa Umma ruwan zafi? Ba ki isa ki ce Nasreen ba, domin kina sane da makauniya ce.” Zakiyya da ta ji shaka ta ce, “Dama… Dama… Na ajiye ne saboda Nasreen.” Ji kake tas! Hafsat ta dauke ta da mari tana huci, “Ashe ke mahaukaciya ce? Ba ki san Kofar dakinta bane za ki ajiye a nan? Kawai ki ce kin shirya kasheta. Daman Hajiya ta je gidanmu tana neman ta hargitsa mana iyaye shi ne ke kuma_ _ bari ki kasheta ko? Yau sai kema na Kona ki.’Www.bankinhausanovels.com.ng
Hafsat ta fizgota tana KoKarin jefa Kafafunta cikin ragowar ruwan zafin. Umma ta girgiza kai, “Hafsat rabu da ita ba da gangar ta yi ba.”
Nasreen tana sauraren su ta yi shiru tana nazarin wani irin Kiyayyace haka da har za a ajiye mata ruwan zafi akan hanyarta, don kawai an ga bata gani?” Sultan ne zaune a Katon dakin taron gabansa kudadene masu yawa, a cikin wata ‘yar akwati. Ya kafe kudin da kallo yana sauraren jawabin manya-manyan mutanen da suke son a kashe wani Case wanda shi yake jagoranta, haka yaga da damar da zai iya kashe Case din, Ogansa da kansa da suka shaKa masa kudi, ya amince za su wargaza Case din musamman yadda yake shirin taba mutuncin su. Yanzu Sultan ne ya rage, duk da suna tunanin Ogansa ya isa ya gaya masa ya ji, amma da Ogan ya yi masu bayanin wanene Sultan sai suka tsorata ainun, don haka suka yi shiri sosai, sannan suka tunkare shi. Kalaman Nasreen sun taimaka masa Kwarai wajen sake cusa masa tsanar damin kudaden da suke gabansa, “Allah ya makantar da kai daga haramun.” A bayyane ya ce, “Ameen Nasreen.” Ya dube su sosai yana nazarin su, “Gaskiya ba zan karbi kudinku ba, wai don kawai ina son in faranta maku in Kuntatawa wasu. Allah ya riga ya amsa addu’ar matata ya nesanta ni ga Haram, ya makantar da ni ta yadda bana iya ganin kudaden da ke zube a gabana. Ku yi haKuri gaskiyata ta kawo ni kujerar nan, bana jin abinda ban aikata, tun ina Karamin dan sanda ba, zan iya aikata shi a yanzu da nake jin kaina na kai. Ku yi hakuri mu bi wannan case din a hankali har mai gaskiya ya yi nasara, amma ba ta wannan hanyar ba. Ina da abubuwan yi a gabana, ban yi tunanin wannan dalilin ne zai sanya a
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG