RUMFAR BAYI COMPLETE
A Shekara ta alif sha tara da sittin da tara 1969 a masarautar 'daura' dake cikin jihar katsina.
'A lokacin ne Sarki 'MUHAMMADU ABDUL-JABBAR UMAR' ya amshi mulki daga wajen mahaifinsa wato SARKI UMAR NA BIYU bayan wata sarka'kiya da fadace fadacen da suka wakana a cikin wannan yan shekarun' bayan rasuwar tsohon sarki Abdul-samadu kenan,a inda jama'a da yawa ne suka rasa rayukansu acikin masarautar da ma garuruwan dake kusa dasu'
A cikin wannan karni ne na sarki Abdul-Jabbar ya saka dokiki masu tsauri da yawan gaske ga alummar sa dan samun cikakken kwanciyar hankali a cikin kasar ta sa.
"Babu wani mahaluki dake zaune a kasar ta daura ko ince a cikin masarautar ta daura" da bai san da zaman RUMFAR BAYI ba ,waje ne da zan iya cewa DUNIYAR BAYI ,wato a nan ne gaba daya bayin dake masarautar daura suke Rayuwarsu a ciki.