RUWAN ZUMA CHAPTER 2

Aliyu ne zaune a cikin gidansu da yamma sakaliya yana cin abincin rana dalilin bai dawo gida da wuri ba sai lokacin. Hayaniya yaji a waje kamar ana kiran sunansa.
Ummansa dake masa fifita ta dakata daga abunda take yi ta rafka salati,
“Na shiga uku ni Nafisatu, me nake ji kamar mutanen Mai Tatsine ne suka dawo garin Kano. Aliyu tashi ka rufe mana k’ofa kar su shigo su yankamu.” A gigice ta yi maganar tana cilli da mafificin hannunta.
Aliyu ya tashi ya nufi bakin k’ofa, a tunanin Ummanshi rufewa zai yi, amma ganin ya fita waje yasa ta yi kuwwa ta bishi babu ko mayafi a jikinta.
Dandazon samari ne suka gani kowannensu d’auke da gora suna ihu suna cewa zasu illata Aliyu, yayinda Haruna kuma ya tsaya a gabansu yana hanasu shiga gidan, kuma shi yake kiran Aliyu ya fito.
Abdul kuma da yanzu ya gane waye Aliyun da ya hurewa Laila kunne sai ya shiga tsananin mamaki da kid’ima kawai ya samu guri ya zauna yana dafe da kanshi.
“Alhamdulillah, ga Aliyun ma ya fito. Zo ka fad’a musu ba kai kake zuwa gurin budurwar Abdul ba.” Cewar Haruna yana sauk’e numfashi dalilin wahalar dashi da samarin suka yi.
Aliyu ya gyara tsayuwarsa ya rik’e k’ugunsa abunda ya zame masa d’abi’a ya ce,
“Idan kuma nace nine fa?”
Umman Aliyu dake bayan d’anta tana zare idanu cikin kad’uwa ta ce,
“Aliyu me yake faruwa ne? Su waye wad’annan?” Me ka musu Aliyu?”
“Umma ki koma cikin gida kin ga ko mayafi baki dashi. Abokaina ne ‘yan majalisarmu.” Ya juya yana lalla6ata tamkar k’aramar yarinya.
“Kai Aliyu! Wannan ziyara tasu bata lafiya ba, dubi wancan yanda yake rik’e da mashi kamar mai shirin soke rak’umi. Me kuka zo yiwa d’ana?” Umma ta fito daga bayan Aliyu tana mai tambayarsu, a wannan karon babu tsoro a tare da ita sai tsantsar dakewa irin ta uwa mai son kare ‘yayanta. “Umma don Allah ki koma gida. Kin ga wancan sunanshi Abdul shine shugabansu, wannan Zailani, wancan kuma Sanusi….” Da haka ya kira sunan samarin kaf Umma na jinshi amma ko kad’an hakan bai kwantar mata da hankali ba. To waye bai san suna da kuma fuskar mak’iyinsa ba? Ita Aliyu zai yiwa wayo?
“Kar ka raina mini hankali mana Aliyu. Ka wuce mu koma gida ko kuma mu wuce Caji Ofis domin ban yarda da wad’annan yaran ba.”
“Malama d’anki…..” Wani mai suna Garzali ya fara magana, amma bai kai ga k’arisa magananshi ba Aliyu ya dakatar dashi ta hanyar daka masa tsawa, yace,
“Karka kuskura ka yiwa uwata rashin kunya. A kul d’inka.” Kana ya juyo ya dubi Yayansa Nazifi wanda shima yanzu ya fito tare da sabuwar Amaryarsa cikin tashin hankali suna tambayar ba’asi.
“Nazifi don Allah ka shigar da Umma gida, babu abunda zai faru. Magana kawai zamu yi.”
Da haka Nazifi ya shigar da Umma gida bayan ya lalla6ata akan cewa zai dawo ya tsaya tare da Aliyu yaji me yake tafe dasu.
A bakin k’ofar gidan Umma ta dawo ta tsaya domin tace bata isa ta shiga gida ta bar Aliyu cikin azzalumai ba.
Sai a lokacin Aliyu ya samu nitsuwarshi ya dubi Abdul da ya samu guri ya zauna a kan wani dakali yana kallon diraman Aliyu da mahaifiyarsa.
“Abdul ya aka yi?” Kawai shine tambayar da Aliyu yayi masa, wacce tasa Abdul harzuk’owa dalilin jin laifin da Aliyu yayi masa ya dawo d’anye a zuciyarsa, ya taso yana nuna Aliyu da yatsa.
“Uban me kake zuwa yi gurin budurwar da zan aura Aliyu? Ashe dama kai munafuki ne mai fuska biyu? Abunda zaka saka mini dashi kenan? Wani shege ne a Samarin Libati bai san cewa Laila tawa bace ni kad’ai? Aliyu son Lailata kake yi?”
Umma da ke bakin k’ofa taji wani tuk’uk’in bak’in ciki ya mamayeta wato duk wannan gororin da mashin da aka zo kashe Aliyu dasu akan mace ce? Wai Laila? A take taji tsanar yarinyar a ranta tamkar taje gidansu ta tsinka mata maruka lafiyayyu.
“Wace kenan? Wai Laila kake nufi?”
“Ka fini sani Aliyu. Tukunna ma so nake inji ta bakinka cewa kai d’inne da gaske mai zuwa gurinta tace ta fasa aurena sai kai, ko dai wani ne?”
“Kafin in ce wani abu zan so ka tuna abunda ya faru a daren Mauludi sati uku da suka wuce.” Cewar Aliyu yana mai fuskantarshi babu alamun tsoro a tattare dashi.
“Me ya faru?” Abdul ya tambaya cikin rashin gane in da maganarshi ta dosa.
Haruna dake gefe guda wanda tunda aka shigo unguwar shi da Hamisu abokin Abdul suka so gane abunda ke faruwa ya tuntsire da dariya har yana fad’uwa k’asa.
Abdul da har lokacin yana cikin duhu ya dubi Haruna cikin 6acin rai ya ce,
“Haruna wai me yake faruwa ne? Uwar me kake yiwa dariya? Menene ya faru sati ukun da suka wuce?”
“Kai da kanka kace babu shegen da ya isa ya je gurin Laila ya hure mata kunne, to ashe Aliyu ya je. Gashi kuma ya doke fadarka da alama kuwa sai ka sake gina wani.” Ya k’ara tuntsirewa da dariya.
Abdul kama kanshi yayi da hannu biyu yana jin 6acin rai da bak’in cikinshi na fita daga zuciyarsa. Fuskarsa Idan ka kalla mamaki ne had’e da murna. Sauk’e hannayensa yayi shima yayi dariya yana nuna Aliyu da yatsa,
“Amma Aliyu ka shammaceni, yanzu kai da gaske zuwa gurin Laila ka yi don ka nuna mini iyakata? Baka kyauta mini ba, amma dai yanzu kam na gane kuskurena. Na ji, ka iya sace zuciyar ‘yan mata.”
Aliyu murmusawa kawai yayi yana kallon Abdul kallo mai wuyar fassara.
“Kai ku zo mu tafi, Ina da gurin zuwa.” Cewar Abdul yana mai juyawa ba tare da ya k’ara sauraran komai daga bakin Aliyu ba.
Da haka samarin suka bar k’ofar gidansu Aliyu, su kuma suka koma cikin gida Ana kiraye-kirayen sallan magriba. Umma da Nazifi dai basu zauna ba, suna tsaye kan Aliyu suna tambayarshi ainihin labarin abunda ya faru, duk da cewa sun gane duk fad’an wai akan mace ce.
“Aliyu wai bada kai ake magana ba kayi shiru ka kyalemu? Wai me ya faru ne? Wace ‘yar iskar yarinyar ce take k’ok’arin sawa a kasheka a gaban idona?”
“Umma ki kwantar da hankalinki ba wani abu bane babba. Wasa ce kawai tsakaninmu.” Da haka ya mik’e ya fita zuwa zauren gidan ya shiga d’akinsa ya kulle.
“Ni Nafisatu na ga ta kaina! Yau dubi yanda yarinya ta so a kashe mini d’a haka siddan bai kashe uban kowa ba. Nazifi kana ganin yaron nan ya k’i labarta mini komai ya tafi ko? Wai ya zan yi da Aliyu?”
“Umma, yanzu da zarar na yi magana anjima kad’an zan ji ba haka ba. Ke da Aliyu ai sai Allah.”
A nan ya bar Umma a tsakar gidan tana bambami ita d’aya ya shige d’akin Amaryarsa.
Daga k’ofar gidansu Aliyu, Abdul bai zarce ko’ina ba sai gidansu, yana sallah ya wuce gidansu Laila wajen k’arfe bakwai har da mintuna, wanda ya tabbatar Babanta ya dawo gida.
Sai da aka masa iso sannan ya shiga falon Baban Laila yana sunkuyar da kai cike da fargaban yanda zai fahimtar dashi halin da ake ciki.
Bayan sun gaisa ne Baba ya dubi Abdul cikin nitsuwa ya ce, “Abdul akwai magana a bakinka ko?”
“Umm.. Dama Baba maganan Laila ce, d’azu na zo zance gurinta take fad’a mini kar in sake zuwa domin ta yi mijin aure. Kuma Baba wanda tace tana so d’in abokina ne, kuma yaudaranta ya zo yi.” Abdul ya fad’a gaba gad’i kamar mai bada rahoto.
Baba ya tattare naman goshinsa alamun rashin gane me ke faruwa yace,
“Abdul ban gane me kake fad’a ba, kana nufin Laila tana kula wani saurayin bayan kai har take fad’a maka shi zata aura ba kai ba? Sannan ta yaya kasan cewa yaudaranta ya zo yi? Ban gane ba.”
A nan Abdul ya bawa Baba labarin duk abunda ya faru tun daga musun da suka yi a majalisarsu wanda yasa Aliyu zuwa gurin Laila, da kuma abunda ya faru yau a k’ofar gidansu Aliyu.
Cikin tsantsan mamaki da kuma wani abu na daban Baba ke kallon Abdul yana girgiza kai. Abdul ya k’arishe magananshi da,
“Kenan zuwan da yayi gurinta wai duk don ya nuna mini cewa za’a iya kwace Laila daga gurina ne. Don Allah Baba a fad’awa Laila yaron nan zuwa kawai yayi ya yaudareta ba don yana sonta ba. Ta yi hak’uri ta janye maganar raba tsakaninmu.”
Baba yayi kusan minti d’aya kafin yayi magana.
“Shikenan ka je gida. Zan yi magana da Babanka Idan na tuhumi ita yarinyar.”
Abdul ya yiwa Baba sallama ya fita daga falon.
Ummii da ke bakin k’ofar shiga falon ta cikin gida ta shigo da sallamarta Baba ya amsa, dama ita ke da girki.
“Sannu da dawowa Alhaji, ka dawo lafiya?”
Ya amsa ta samu guri ta zauna don yanayinsa babu walwala, wanda tasan labarin da Abdul ya gama bashi ne ya sakashi shiga wanna n halin.
“Alhaji lafiya dai ko?”
“Hm, kin ji labarin da Abdul ya kawo mini ko?”
“Na ji Alhaji. Sai dai duk laifin Laila na gani, meyasa ta kasa sanar damu cewa ta samu wani wanda take so? Kuma ita zata yankewa kanta hukunci ne bayan muna raye?
“Kira mini ita.”
Ummii ta tashi ta fita kiran Laila. Minti d’aya da haka sai gasu sun shigo tare, Laila ta samu guri d’aya a k’asa ta zauna zuciyarta na lugude domin jikinta ya bata watak’ila a kan Aliyu ake mata wannan kiran ko kuma sun ji labarin Abdul ya rik’e mata mayafi yau.
Ta gaishe da Baban nata ta mishi sannu da dawowa.
“Laila waye Aliyu?” Shine tambayar da Baba ya fara mata. “Wani ne da yake zuwa gurina a nan unguwar Fagge yake, iya abunda na sani a kansa kenan.” Muryanta ya fara karkarwa alamun kuka na son ku6uce mata domin ta tsorita.
“Laila. Aliyu ba sonki yake yi ba, hasalima zuwa yayi ya yaudareki saboda wani musun banza da suka yi da Abdul kan cewa shi Abdul yace babu mai rabaki dashi.”
A gurguje Baba ya bata labarin abunda Abdul ya zo ya fad’a mishi.
“Kin yi wauta tun farko da kika fara kula saurayi ba tare da ya nemi izini a gurinmu ba, Ina yabon hankalinki Laila, ban san ya aka yi wannan karon na ga akasin haka ba. Ban ji dad’i ba, kuma kar in sake jin haka.”
Fad’in irin tashin hankalin da Laila ta shiga ma 6ata lokaci ne, wani gefe na zuciyarta bai yarda da abunda Abdul ya fad’a ba, meyasa zai k’irk’iri wannan labarin don kawai ya rabata da Aliyu?
Tana son musa labarin amma wani gefe na zuciyarta ta kwa6eta da aikata haka. Babanta yana sonta, yana kuma k’ok’arinshi na nuna musu hakan, sannan Baba ba zai ta6a mata k’arya ba akan wani abu da yake son jawo hankalinta kai ba, sai dai ya bata umarni saboda ya isa har ma ya fi haka.
Hawaye ne suka gangaro kan fuskarta ta d’ago ido ta dubi Baba ta ce,
“Baba kayi hak’uri ba zan sake ba. Amma Baba Abdul ba k’arya ya maka ba?”
“Laila ke yarinya ce wacce soyayya ta rufewa ido. Ba k’arya ya mini ba, sannan duk hukuncin da na yanke zaki ji daga gurin mahaifiyarki. Lene.”
Hanjin cikin Laila ne suka kad’a cikin firgici, kallon Babanta take yi tare da Ummii cikin rud’ewa, amma ganin yanda fuskarsu babu alamun wasa yasa Laila fita daga falon, hawaye wani na bin wani.
“Na shiga uku na lalace. Yau ina zan sa kaina?” Ta fad’a bayan ta zauna a kan katifarta.
A take a lokacin zazza6i ya rufeta ta fara jin sanyi, da zanin gadonta ta rufu hakwaranta na had’uwa kaf kaf kaf, yayin da wasu sabbin hawayen suka fara silalowa ta gefen idonta. Zuciyarta k’una take mata, yayin da take jin kwakwalwarta kuma a cunkushe bata iya tunani d’aya mai kyau, hakan ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani domin ya had’u mata da cewa yau Aliyu ya bar gurinta da rana yana mai mata alk’awarin gobe zai zo mata da labari mai dad’i. Kenan wannan shine labarin?
A cikin wannan yanayi Laila ta kwana wanda kafin asuba zazza6in ya sauk’a, amma kuma ciwon kai sai abunda ya k’aru.
Tana kwance har gari ya fara haske ta tashi su Safa da Marwa suka yi wanka sannan suka tafi d’akin Ummii don karyawa.
Tana zaune Mas’ud ya shigo yana rik’e da jakarsa ya gaisheta.
Yanda ta amsa ga idanunta sun kumbura sun yi jaa yasa Mas’ud ya gane babu lafiya.
“Kalti meya sameki? Baki da lafiya ne?” Ya tambayeta cikin damuwa yana ajiye Jakarsa a k’asa.
Shiru ta yi, sannan wasu hawayen suka k’ara gangarowa kan kumburerren fuskarta.
Ganin hakan yasa Mas’ud ya tabbatar babu lafiya. Zama yayi kusa da ita yana tambayarta ba’asi amma bata kulashi ba.
Har ya gama magiyarsa da nacewarsa bata ce masa u!an ba ya fita ranshi a 6ace domin irin haka bai ta6a shiga tsakaninsu ba.
Minti goma da haka ya dawo d’akin ya dubeta cikin 6acin rai yace,
“Ki bani kud’ina da yake gurinki.”
Laila ta d’ago idanu ta dubeshi itama cikin zafin kai, ganin fuskarsa yasa ta ji jikinta yayi sanyi don bata kyauta masa ba. Amma bata wannan take yi ba.
Hannu ta saka k’ark’ashin katifarta ta jawo wata leda ta kirga iya kud’insa dake gurinta ta bashi kana ta mayar da sauran.
Bai mata magana ba yasa kai ya fice suka tafi makaranta shi da su Safa, Marwa da Shema ‘yar Tabawa.
Haka Laila ta yini sukuku ta ma rasa me zata yi da rayuwarta, har yanzu wani gefe na zuciyarta na k’aryata mata labarin da Abdul ya fad’awa Baba a kan Aliyu. Idan kuma har maganar gaskiya ce Aliyu bai mata adalci ba bata cancanci haka daga gareshi ba.
Ko da Mas’ud ya dawo tana jin muryarsa a tsakar gida amma bai shigo in da take ba. Ummii kuma babu ruwanta, Idan tana da aika ko wani aiki da Laila zata mata, haka zata kirata ta yi. Kuma bata tambayeta me yake damunta ba ko sau d’aya.
Laila ta ji duniyar ma gabad’ayanta ya fita a ranta, tashin hankalin da take ciki yasa ko abinci ta kasa ci a yinin ranar. Tana zaune tana aikin tunani bayan la’asar ta jiyo yaro na sallama a waje wai ana kiran Laila.
Zuciyarta ce ta buga da k’arfi ta nemi nitsuwarta ta rasa. Meyasa Baba ya dawo da Abdul cikin rayuwarta bayan bata sonshi ko na misk’ala zarratin? Meyasa Aliyu ya mata haka? Meyasa rayuwarta ta sauya daga jin dad’i zuwa bak’in ciki lokaci d’aya?
“Tana zuwa.” Shine amsar da Ummii ta bawa yaron ya fita daga gidan.
Tsawon minti uku Laila ta d’auka bata fita ba kuma bata da niyyar fita. Me zata cewa Abdul? Idan ta fita ta san zata iya masa rashin mutunci wanda in maganar ta dawo gida baza ta share ba, kenan rashin fitarta shine mafi alkhairi.
Kuma ta rantse a zuciyarta da kuma a fatar baki cewa da ta auri Abdul gwara ta zauna babu aure a kanta har duniya ta tashi. Ta gwammace ta auri wani bare can amma ba Abdul ba, domin kuwa ganinshi zai sa ta dinga tuno da Aliyu da abunda ya faru a rayuwarsu. To Ina za’a yi zaman lafiya a wannan auren? Ai ba zai yiwu ba!
“Idan na shigo d’akin nan sai na 6ata miki rai Laila. Don Allah ki k’ara minti d’aya ki ga abunda zai faru.” Ummii ta fad’a cikin kufula.
Ummii na sane da halin da Laila take ciki, amma hakan bashi zai bata lasisin k’in kula wasu samarin ba.
Laila na jin haka ta burma hijabinta ta fita zuwa tsakar gida in da Ummii ke harararta ranta a 6ace.
Sum sum ta fice kanta a k’asa, amma kuma zuciyarta tafasa take yi tana kwatanta irin rashin mutuncin da zata yiwa Abdul.
A bakin zauren ta tsaya idanunta a zare bakinta a bud’e tana kallon wanda yayi aikan a yi kiranta.
Aliyu ne tsaye a gaban babur d’insa hannunsa bisa k’ugunshi hankalinshi a kwance kamar bashi da wata damuwa a duniya.
Juyowa yayi suka had’a ido. A hankali fuskarsa mai d’auke da nitsuwa ta fara komawa ta damuwa dalilin halin da ya ga Laila a ciki na rashin kwalliya da kimtsi, ga fuskarta a kumbure har ba’a ganin zara-zaran idanunta wanda ko sau d’aya ba’a rabasu da kwalli.
Meya samu Laila? Kenan abunda ya aikata ya ta6ata har haka?
“Aliyu.” Ta kira sunansa kamar so take ta tabbatarwa kanta cewa shine a tsaye ko dai waninsa.
“Laila.” Shima ya kira sunanta. A hankali ta fara takowa ta zo ta tsaya gabanshi idanunta na tara wasu sabbin kwalla ta ce,
“Shin abunda na ji da gaske ne Aliyu? Wai dama ba sona kake yi ba yaudarata ka zo yi? Da gaske ne ko dai duk k’aryar Abdul ce? Don Allah ka ce mini k’arya ce don nasan baka yi kala da abokan Abdul ba.”
Shiru yayi ya sadda kanshi k’asa domin bai san me zai fad’a mata ba. A yanda ya ga halin da take ciki duk abunda zai fito daga bakinshi tarwatsata zai yi ba wai ya kwantar mata da hankali ba.
Ina tunaninshi da iliminshi yake da ya aikata haka a gareta ba tare da ta masa laifin komai ba?
Tsura masa ido ta yi tana jiran amsarta domin bata son yarda da wancan maganar, yau gashi Allah ya kawo mata Aliyu zata kaishi gaban Baba ya wanke kanshi daga k’aryar da Abdul yayi masa.
Ganin shirun yayi yawa ga Aliyu ya sadda kanshi k’asa yasa jikin Laila ya fara kyarma, ta k’ara zaro ido waje a karo na biyu tana mai cigaba da kallonshi hawaye na tsiyaya a idanunta. Hannunta tasa ta toshe bakinta dalilin kuka mai sauti da ya kwace mata ta fara ja da baya.
Hakan yasa Aliyu d’ago da kanshi idanunshi sun yi jaa yana girgiza mata kai fuskarsa d’auke da tarin nadama.
Ganin hakan a tattare dashi yasa Laila ta gane amsarta ba tare da ya furta ba.
“Ka yaudareni, ka cuceni, me na maka da ka za6i kayi was a da zuciyata? Na aminta da kai Aliyu na baka zuciyata da duk wani so da ban ta6a yiwa wani ba. Me na maka?”
Zai bude baki yayi magana ta dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu hawaye na tsiyaya a idanunta har bata iya kallon gabanta.
“Babu wata kalmar da zaka k’ara fad’a mini, kayi shiru, kayi shiru kawai Aliyu.”
A hankali ta juya ta fara tafiya zuwa cikin gidansu kanta na sarawa tana jinta tamkar akan kwai take tafiya.
Bata juyowa ba, haka kuma bata saurari Aliyu da yake kwala mata kira ba har ta shiga had’e da turo k’ofar gidan ta rufe.
Rayuwa ta mata zafi, komai ya fita a ranta, ji take yi kamar ta kwanta kar ta sake tashi har abada.
Tana kwance da dare Mas’ud ya shigo d’akinta, ganinta a halin da ya barta yasa ya zauna kusa da ita.
“Aliyu bai zo bane?” Shine abunda ya fara tambayarta da mamaki a fuskarsa.
A hankali ta d’ago ido wanda suka rine tsabar kuka ta ce, “Ban gane ba.”
“D’azu da safe bayan kin k’i fad’a mini me yake damunki na koma d’akin Ummii, a nan take bani labarin abunda ya faru. To shine na zo nace ki bani kud’i, daga nan unguwar su Aliyu naje nemanshi. Sanin cewa an yi hargowa a unguwar sai ban sha wahalar gane gidansu ba. Naje har cikin gidansu na fad’a masa cewa kina nemansa, ya kuma mini alk’awarin zai zo da zarar ya gama abunda yake yi. Kenan bai zo ba?”
Wasu sabbin hawayen ne suka gangaro gefen fuskarta ta sharesu tana kallon Mas’ud cikin tsantsar so. Ashe shi ya kira Aliyu? Ashe ziyaran Aliyu ba yin kansa bane dalilin Mas’ud ne? Me ta yiwa Aliyu da ya mayar da ita tamkar mutum-mutumin da zai yi wasa dashi? Me ta masa da har ta cancanci haka?
“Ya zo Mas’ud. Sai dai duk abunda Abdul ya fad’a ba k’arya bane, Aliyu yaudarata yake yi tun daga farko.”
Washe gari haka Laila ta k’ara yini kamar mara lafiya, jikinta duk ciwo yake yi ga kanta dake sarawa har yanzu bai sauk’a ba. Tana sana’ar tata ta kwanciya bayan Magriba yaro ya shigo wai ana kiran Laila.
Tabawa da take tsakar gida ta fara magana cikin 6acin rai. “Haba! Kun ishemu fa, ba garin Allah da ba zai waye ba shikenan zaku fara mana zarya wai ana kiran Laila, ana kiran Laila a waje tamkar itace kad’ai mace a unguwar nan. Dalla ka fita ka bawa mutane guri ka tsura mini ido kamar maye.” Ta k’arishe maganan tana masa dak’uwa cikin kufula.
K’unk’uni yaron ya fara yi da alamar ‘yan rashin kunyar na kusa, ganin ta taso da silifas a hannunta zata dakeshi yasa shima yaron ya danna mata dak’uwar ya fice da gudu yana kecewa da dariya.
Tabawa ta bishi da gudu har cikin zaure amma ko da wasa bata samu daman kamashi ba. A bakin k’ofar ta fara zage- zage ba tare da ta amsa gaisuwar wanda ya aika ayi kiran Laila ba. Ganin tana jawowa kanta abun kunya yasa ta koma cikin gida tana kumfar baki.
Ummii da ke d’akinta ta fito tsakar gida tana jin habaice- habaicen Tabawa amma ko kulata bata yi ba ta doshi d’akin Laila ta d’aga labule.
“Baki ji ana kiranki a waje bane Laila?”
“Na ji Ummii.” Ta bata amsa tana mai tashi zaune gudun kar ta jawowa kanta lik’i.
“Tun da Allah ya miki farin jini kuma kin isa aure ai dole a yi ta zarya a k’ofar gidanku. Maza tashi ki je, mai sonka ai baza ka ta6a korarsa ba.” Cewar Ummii tana mai d’aga murya yanda Tabawa zata ji.
Abun ya so ya bawa Laila dariya duk da halin da take ciki, wato itama Ummii ta iya habaici? Ganin fuskar Ummiin a washe kamar ta ji dad’in abunda ta aikata yasa Laila sawa a ranta zata fita ko don kar ta kunyatata.
“To Ummii.” Ta d’auko mayafinta ta saka ba don tana son fitan ba.
“Me ya dawo da kai k’ofar gidanmu Aliyu?” Cewar Laila kenan daga can bakin k’ofa ba tare da ta iso in da Aliyu yake ba.
Da kaga idanunta zaka san zuciyarta a karye take tana cikin wani hali na tausayawa, amma kuma fuskarta a gimtse take tamkar wacce ta ji mummunan sak’o babu ko d’igon annuri.
“Laila, nasan ni mai laifi ne a gareki, amma don Allah ki bani minti biyu zan fad’a miki wani abu, daga nan zai rage gareki ki cigaba da saurarata ko kuma ki koma cikin gida.” Bata so tsayawa ba, Aliyu ya mata laifi, wasa da zuciyarta da yayi har k’arshen duniya baza ta manta da hakan ba, amma kuma har abada son da take mishi ba zai ta6a gushewa a zuciyarta ba. Son shi kaya ne da ta d’auka wanda dashi zata koma ga mahaliccinta saboda baza ta iya sauk’ewa ba.
“Ina jin ka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *