SALON SO CHAPTER 3
Ba ce mata komai ba ita ma ba ta kalli gun da yake ba. Can ya ce mata kinci abinci? “EH na ce. Ya janyo ledojin da ya shigo da su da karamar akwati ta siyen baki ya tura mata gabanta ya tashi ya fita. Jawahir ta yi tagumi a ranta ta ce, “O ni ‘yansu, ga me so na can an kawo ni gidan wanda ba ya kauna ta ko da yake ni ma zan zauna ne darajar iyayenmu. “A nan ta tuno nasihar da mommynta ta yi mata. Jawahir ni dai babu abin da zan ce miki sai fatan Allah yayi miki albarka yanda kike binmu kike mana biyayya ubangiji ke ma ya baki ‘ya ‘yan da za su biki haka. Jawahir ta dauki duk abin daya same ki a rayuwa matsayin kaddara. ki kasance me biyayya ga mijinki ki boye sirrinku kada ki buda shi ga wani don Allah ya tsinewa matar da take bayyanar da sirrin mijinta. Duk abin da ya yi miki yi hakuri kada ki kai kararsa wajen kowa. Ki dage ki yi ta yi muku addu’a don Allah ne zai warware muku matsalarku. Ka bacin rai ya sa ki bin boka ko malam babu abin da za su yi miki face ki barnatar da kudadenki a banza kuma ki jawowa kanki tsinuwar Allah ki rike alkur’ani dan zancen Allah ne shi ne waraka ga komai. Jawahir ta saki ajiyar zuciya ta ce, “In Allah ya yarda zan rike nasihar mommyna. Haka ta kwanta ita kadai ga tsoro da yunwa tana jin amma ba ta bude ledojin da Haidar ya ajiye mata ba. Da asuba ta yi sallah ta dauki kur’ani ta karanta abin daya sauwaka ta yi addu’a ta ta sha fa ta cire hijabinta ta ajiye. Ta yi takumi, “Ni kuwa na je na hada break ko kuma na kyalle shi? Kai gwanda na yi ko ya ci ko ba ya ci Allah ya gani dai na fita falon tsarin falon ya yi mutukar burge ta da ba ta sha awa, lallai daddynta ya kashe mata kudi. Ta bude kicin din shiga haduwarsa ya yi mugun gigita ta, sak irin wanda a ke nuno tallolinsu ne kasashen waje, duk wata na ura ta amfanin dan Adam don hada abu a saukake an tanadar mata a kicin din nan, sannan duk wani kayan girki da za su bukata an tanade shi ta bude disk freezer cike yake da kaji, zabi xuwa naman kasuwa duka danyu, sai daya firizar kayan miya ne irinsu attarihu tattasai, tumatir, albasa, koren, wake, karas, kabeji da sauransu. Firinjin tsaye kuwa lemummuka ne kala kala na kwali da na gwangwani da robobin ruwan sha, kamar su swan water, Highland water, da dai sauransu. Ta ga wata kofa daban a kicin din ta bude ta ta shiga ashe sito ne kalolin abinci iri iri buhunan shinkafa, katon dinsu taliya, makaroni, kuskus, buhun sikari da na fulawa, garwar manja da na jan kuli da kuma man shanu, busasshen kifi, daddawa, kanwa busasshiyar kubewa, magi kama daga Reko, onga, kori, Ajino-moto da dai sauransu, babu abin da za ta nema na amfani komai an dire mata.: Ta debo dankali ta fere ta soya ta jona ruwan zafi ta sa citta da kanun fari, ta zuba ganyen shayi me kamshin Nescafe ta koma daki ta dauko ledar jiya gasassun kaji ne manya guda uku ta zuba su a oben ta dumama su. Ta fasa kwai ta soya ta debo filas-filas masu kyau ‘yan dubai ta zuba komai a ciki ta rufe ta juye ruwan shayin a fulas din shayi wanda yake duk saiti ne da fulas din da ta zuba ragowar kayan a ciki. Ta jere komai a tebir ta debo kofuna da filet da cokula duk ta zube kan tebir din ta sa wani farin kyalle me ban sha awa ta rufe kayan kan tebir din. Ta dauki nata break din ta yi dakinta da shi. Ta rufe kofarta ta shiga toilet ta yi brush sannan ta ci ta koshi ta koma gado ta kwanta. Mintina kadan bacci ya yi awon gaba da ita. Shikuwa Haidar da ya tashi da asuba ya yi sallah ya yi karatu ya shafa addu’a gado ya koma ya kwanta saboda baccin gajiya da yake ta dawainiya da shi. Karfe tara ya tashi na safe ya yi mika tare da salati ya duro daga gadon ya nufi toilet. Ya salla wanka ya zo ya gama goge gogensa da shafe shafensa ya yi tsantsararriyar shiga, shiga ta alfarma ya feshe jikinsa da turaruka. A zuciyarsa yake cewa ya kamata na je na gano yanda yarinyar nan ta tashi ko don nasihar da Abbansa ya yi masa kamar haka……. “To Haidar yau Allah ya nufa an daura auernka da jawahir to duk wani nauyi da hakkinta ya koma kanka, amana ce a gare ka, idan ka zalince ta ko ka cutar da ita kai da Allah, idan ta yi maka abin da be yi maka dadi ba ka zaunar da ita ka nusar da ita cikin nasiha da tattausar murya. Kar ganin yanzu ta zama ikonka tana zaune a karkashinka wallahi idan ka zalince ta ubangiji ba zai taba kyale ka ba, sai ya fitar mata da hakkinta don haka ka kiyaye.” Ajiyar zuciya Haidar yayi, “Haka kawai a daure ka da jijiyar jikinka, bari na je na gani ko ta karya. Ya sauka kasa da yake benen nasa a cikin falonta yake. Ya kula da tebir din da ya sha kwalliya da kayan alatu. Ya karasa wajen ya yaye farin kyallen ya bude komai. Kamshi ya daki hancinsa nan da nan sha awar abincin ta kamashi. Ya zauna ya hada ruwan tea me kauri ya debi soyayyen dankali da kwai da kaza daya. Haidar ya rinka ci yana lodawa cikinsa don jiya da daddare bai ci komai ba ya kwanta, yanzu kuwa ai ya yi lodi, ya yi gyatsa tare da yiwa Allah godiya. Ya mike ya nufi kofar dakin jawahir ya ji ta a rufe. Ya samu takarda da biro ya rubuta mata sako kamar haka: “idan kin tashi ki yi break ni mun fita gaisuwar surukai sai yamma zan dawo.” Haidar Ya ninke ya dora kan tebir din. Ya fice. Ya samu abokanansa suna jiransa suka tafi gaisuwar surukai. jawahir sai sha biyu na rana ta farka, tana mikewa ta fada toilet ta yi wanka ta kammala shirinta sannan ta fito falo, ga mamakinta ta ga Haidar ya ci break din da ta shirya masa. Ta hango takarda ta dauka ta bude ta karanta ta tabe baki, “Kada ma ya dawo ni ko kwana zai yi me ya dame ni?” Ta dauko yogougt ta zauna tana yagar kazar tana korawa da nonon har ta koshi. Wajen sha biyu da rabi direba ya kawo Inna da kannanta Auwal da sani da su Hassana da Usaina kannan Haidar. Jawahir ta cukuikuye inna tana tsallen murna. Inna ta dube ta tana dariya ta ce, “Ke cika ni kada ki karasa ni, ni ina can zuciyata ta kasa sukuni sabo da tunanin yaya kwana ke kuma kina kokarin karasa ni. jawahir ta yi dariya, “Amma dai inna a nan za ku kwana ko?” Inna ta tabe fuska ta ce, “Ke ba na son hauka yanzun nan ma za mu juya. Hassana ta ce, “Allah Aunty ni dai gidanki ya ba ni sha awa zan kwana. Usaina ta ce, “Lallai kina so Yaya haidar ya yi tamaula dake kenan.? Jawahir ta ce, ba wani abu da zai yi mata kin ji Usainar nan wai don kar ta kwana, ba abin zai yi miki Hassana.” Inna ta ce, “Babu wanda zan bari, kafata kafarsu. Auwal ya ce, “Su Aunty jawahir ‘yan gayu. “Gaba daya sukai yi dariya. Sani dauko muku ragowar break din Yaya ku ci. Ta tashi ta shiga kicin ta kwaso musu yogouht da lemummuka da ruwan sanyi ta zube musu. Da ragowar gasassun kajin amarcinta. Inna ta gyara zama da jikokinta suka ci suka koshi. Inna ta kara yi mata fada da nasiha. Karfe hudu suka tafi. Jawahir ta mike ta yi sallah bayan ta idar ta shiga kicin ta dauki kaza daya ta yayyanka ta yanka albasa ta sa gishiri da citta da magi ta dora kan wuta. Ta debi kayanmiya yanda zai wadace ta ta markada ta dora ruwan kuskus. Ta gama hada soyayyiyar miyarta ta dafa kuskus dinta da ya sha karas da koren wake ya yi wara wara da shi gwanin kyau. Ta gasa kifi irin manyan nan ta yi farfesun kayan ciki, ta markade kwa kwa a ciki blinder ta tace ta sa madara, filebo, sukari ta hada lemo me dan karen dadi. Ta samu wasu kayatattun fulas ba irin na safe ba ta kuma jere komai a kai. Ta hau saman dakin nasa, ga mamakinta sai ta gan shi a bude ta gyara masa gadon da ya kwanta ta kade komai ta share masa dakin. Ta wanke bandaki ta goge ta kunna turarukan wuta ta fesa Air freeshner a kowacce kusurwa, ta sakar masa A.C Nan da nan sanyin dadi ya soma tashi. Ta rufo masa dakin ta sauko ta gyara falon kasa da nata dakin ko ina ta feshe shi da Air freshner da turaren wuta dan maiduguri ta saki labulayen ta kunna A.C ta rufe kofar falon ta shige dakinta ta rufe ta fada toilet don yin wanka Sai karfe biyar da rabi Haidar ya dawo gidan a gajiye ga yunwa da take azalzalassa don tun break din da ya yi bai sake cinn wani abun ba. Don shi Allah ya yi shi mutum ne mai kyankyami ba ko ina yake iya cin abinci ba. Megadi ya wangame masa get din ya shigo ya rissina ya yi masa barka da zuwa. Ya murda kofar falon ya shiga tare da yin sallama shiru kamar ba kowa a gidan. Daddadan kamshi ya bugi hancinsa, ko ina tsaf a share a goge ya ji gyara, ya y
i sha awar yanda take da tsafta take kula da komai. Ya haye samansa yana tura kofar dakin, nan ma sanyin da kamshin dadi suka yi masa sallama. Ya sheka ya limshe ido ya yi godiya ga Allah, shi kansa falon saman nasa ta canja masa tsarin gyara wanda kuma hakan ya fi kyau yana shiga cikin dakin nasa sai kansa ya kwance, wani hadadden zanin gado ta shimfida masa , ai yanda ta dame gadon ya burge shi ya cire kayansa ya fada toitel ya fara wanka.Ya gama shirinsa ya sa kananan kaya. Sun karbe shi kuwa sun yi masa kyau. [07069210827: Ya feshe jikinsa da turaruka ya sauko kasa ya hau tebir ya bude komai, kamshin girkin ya buge shi sha awa da jin dadi suka bige shi. Ya zauna ya rinka dibar garar girki, yana ci komai na kan tebir din sai da ya ci da ya wa ya ci ya koshi ya yi hamdala ga ubangiji. Ya rinka tsiyayar lemon kwa kwar nan yana sha, don Allah daman hausawanmu sun iya hadadden lemo haka, amma muke bugewa kullum yawon siyen juice. Ya cika kofin tangaran da shi ya tashi ya koma kan kushin can gefe daya ya dauki jarida yana karantawa yana kurbar lemon kwakwar. Ita kuwa jawahir tana daki ba ta ma san ya dawo ba ta gama shirya kwalliyarta cikin riga da siket na atamfa kwali wax, rigar fitet ce ‘yar firit,siket din ya yi tsantsan a jikinta. Ta dora daurin dan kwali wuyanta da kunnanta wani rantsattse fashion ne mai kyau. Ta feshe ilahirin jikinta da daddadan turaruka masu kamshi. Ta bude kofar dakinta ta fito kamshin da ya ji ne ya sa shi dago kai ya kalle ta, a ransa ya fada, “Yarinyar tana da kyau sai ka ce Aljana, ga shi ta iya gyran jikinta. Yanda siket din ya matse ta dole ta rinka takawa sannu a hankali gudun kada ta harde. Ta shiga kicin ta debo abinci a filet dan kadan sai ka ce wadda za tabawa dan yaye sai robar nono yogougt dake daya hannun nata. Ta zo ta nutse a cikin kujera ta dauki remote ta kunna T V. tashar CNN ta kunno, sannan ta fara cin abincin, yanda take diban abincin kamar ba ta son ci a yangance. Duk abin da take yi idon Haidar yana kanta, ita kuwa ba ta san ma ya dawo ba bare ta san yana falon. A zuciyarsa ya ce, “Yaushe dama za ta girma tana cin wannan dan mitsitsin abincin kamar na ‘yar yaye. Can wayarta ta yi kara ta dauka, tana dubawa da murnarta ta dora a kunnanta, “Hello Dadyna. sai ta kunna (Handsfree) Daddy ya ce, “Jawahir yaya kike? Ya megidan naki? “Wallahi lafiya lau Dady muna zaune kalau. “Kina son masu aiki ne a kawo miki? Cikin shagwaba ta ce, “Lah Dady mai aiki, ni wallahi ba na son kowa su zo su yi batawa mutane waje. don iya girkinmu mu biyu da gyaran dakunanmu Dady ai duk zan iya. “To jawahir wanke-wanke fa, ga sharar harbar gidanku.? Dady ka san ba na son kazanta da gama girki nake wanke kayan na goge su na mayar inda suke. Harabar gidan kuma dakin saukar baki yana da yaro da yake gyara masa me bawa fulawowiyin gidan ruwa. “To jawahir wa zai rinka ba su abinci ko har da su za ki yi rinka yin girkin? Ta kara shagwabewa, “Uhm Dady wallahi ba zan yi musu girki ba, abincina daga ni sai Yaya kawai. “To shi ke nan jawahir za a samu haidar din na yi mishi magana na ji yanda za a rinka yi da su wajen ba su abinci.” Cikin shagwaba ta ce, “Don Allah Dady kada ka yi masa magana ya zo ya ce sai na rinka girkin da su ka ga wahala zan sha. “To jawahir ai a karkashinku suke, dole ku rinka kula da hakkinsu ko to kwace kuma za ku bar su da yunwa. Cikin shagwaba ta ce, “Haba Dad. to Dady na yarda a kawo tsohuwa amma ba za ta rinka shigo min sashena ba, sai dai ta tsaya can bangaren masu aiki ta rinka da fa musu abincin, ai ya yi ko Daddy.?” “Yauwa ko ke fa jawahir gobe za a kawo ta, Ki kara hakuri jawahir ki dinga biyayya ga mijinki. Allah ya yi muku albarka . To Dad na gode, “good day Dad.” Tayi ajiye wayar ta mike ta dau filet din ta shiga kicin. Haidar ya mike ya haura samansa ya yi dai dai a gadonsa yana tunanin hirar jawahir da Daddynta. A ransa yake cewa, “Ko dai don muna ‘yan uwa ne halayyarmu da ra’ayinmu suke neman zama daya? Gaskiya ta burgeni da za ta rinka yi min komai da kanta, don ni na tsani gidan da me aiki take yi wa matar gidan da mijinta girki, amma jawahir tana da dadin murya ga dadin saurare, ban so suka gama hirar ta su ba. To haka da i zaman ya ci gaba tsakanin miskilan guda biyu. kowanne yana ji da girman kai da miskilanci babu wanda zai wa dan uwansa magana idan har sun hadu da safe za ta ce masa ina kwana. Yayin da shi kuma yake daukan lokaci kafin ya amsa da lafiya lau. To sai ta yi shigewarta daki ba ta fitowa har sai ya tafi. sannan ta zo ta gyara musu dakunansu ta turare da turaren wuta ta feshe ko ina da Air freshner ta zauna ta shirya musu hadadden girki me gamsarwa. Ta hada masa lemo da kanta kullum da sabon samfir din girki da lemon da take yi masa. Ba ta taba barin waje da datti ko kura ko ina fes a gyare dai dai da wanke kwanikanta ita take yin abinta. Ta gyara kicin dinta fes kamar ba a yi komai a ciki ba. Tukwane ne kawai da kaskon suya saboda maiko take bawa Dela me aikinta ta wanke mata Tun da akawo Dela take zaune a bangaren masu aiki za ta yi girkinsu su uku da maigadi da ita sai yaron gidan da ta yi gama za ta wanke komai ta share ta goge da yake ita ma me tsafta ce shi ya sa suke shiri da jawahir din. Haidar kuwa yana jin dadin yanda jawahir take da tsafta komai take kulawa da shi yanda ya kamata, don haka duk san da ya taso daga office burinsa ya yi sauri ya dawo gida don ya narki special din girki da jawahir za ta yi masa. Ya zauna a kayataccen falonsu yana shakar daddadan kamshin falon. Idan ya tashi daga office yana biyawa ta gidansu a gurguje yake yin komai don yana sauri ya koma gida. Idan Aunty ta ce masa ga abinci ya kan ce um Aunty sai na je gida zan ci. Duk da ba magana suke yi wa junansu ba, to amma hakan bai hana su kyautatawa junansu ba Ana yawan kawo mata kannanta Auwal da Sani da kannan Haidar Hassana da Usaina idan yamma ta yi direba ya mayar da su gida Yaya Abba ma da yaya Nasir suna yawan zuwar mata. Inna ma ta na kan zo amma ba sosai ba iyayensu ne dai har yau ba su zo ba. HAIDAR ya samu kwanciyar hankali don ba a bin da ya ke damunsa don haka jikinsa ya kara murjewa kyansa ya kara daduwa kowa ya kalli fatarsa ya san ta goge da jin dadin duniya ita kuwa jawahir da yake abincin be da meta ba to yanda take haka take babu wata ‘yar kiba da ta yi. Shekara daya ke nan da yin auren har yau jawahir ba ta taba lekawa kofar gida ba. Yau asabar da jawahir ta kammala da hada break dinta ta diba ta ci ta gama gyara wajen ta sa turaren wuta ta feshe da gidan ta shige toilet ta yi wanka. Yau shigar turawa tayi ‘yar bingilar shimi ta saka iya cibiya me siririn hannu sai dogon wando da ya dame mata cinyoyi da kafar wandon an bude shi ta hade gashinta a tsakiyar kai ta sa tafkeken ribon ta daure shi. Cikinta a dame kamar ba ta zuba masa abinci ba, fuskar nan tata sai fitar da sheki da wa ni asirtaccen kyau ta ke yi, ta gama feshe jikinta da tuararuka ta fito falon inda Haidar ya ke break ta durkusa ta ce, “Ina kwana?” bai juyo ya kalleta ba ya ce, “Lafiya lau. Ta mike ta isa bakinTV ta dauki takarda da biro ta koma ckin kujera zaman mutu daya ta kwanta tana rubutu. Tun da ta mike Haidar yake bin ta da kallo sai hadiyar yawu kawai yake yi ta yi mugun ba shi sha awa, hankalinsa ya tashi sosai. Ta gama rubutu a takardar ta ninke ta taso cikin nutsuwa ta zo gaban Haidar ta ajiye masa a kan tebir dinta ta juya ta koma daki, shi kuma ya bi ta da kallo. Sai da tashige daki sannan ya ware takardar ya fara karantawa . Yaya Don Allah yaya ina so zan je gidanmu da gidan inna da wajen Aunty. Ina so na taho da sayyid Autan Aunty idan ka yarda. Jawahir Yana gama karantawa ya ajiye ya ci gaba da yin break dinsa sai da ya gama sannan ya mike ya dauko takarda da biro shima ya rubuta mata kamar haka. “In kin shirya ki jira ni na kai ki da kaina, Sayyid kuma in kin ga ba zai takura miki ba kya iya daukoshi Haidar Jawahir duk ta matsu da ta ga amsar da zai ba ta. don ita dai tana so yau ta je gidajen nan ko dan dadewar da ta yi rabonta da fita . Ita jin kanta da miskilancinta ya hana ta ta fito bare ta ga amsar da ya rubuta mata , shi kuma girman kansa da isarsa ba za su bar shi ya kai mata ba. Sai da ya gama kallon sa da hutawarsa sannan ya koma sama. Sai da ta ji tafiyarsa ta fito ta dauki t
akardar ta karanta, aikuwa sai ta hau tsalle tana murna kamar yarinya. Nan da nan ta shiga shiri a kakale nan a kakale can ko ina ta yi fes kamar wacce aka karawa kyau. Wani dandasheshen less ta saka me dan banzan kyau da shegiyar tsada. Ta yi kyau kamar ka sace ta ka gudu don haduwar da ta yi. Ta kalminta da mayafinta da jakarta duk ruwan less din ne. Takalmin me tsinin dunduniya. ta hakimce a falon tana jiran futowarsa megidan Ba ta jima ba sosai ya fito cikin shiga ta wani danyen boyal baki sai sheki yake yi, hular kansa baka mai gashi, takalminsa baki sai agogon hannunsa na Daimond. Duk sun yi kyau kamar wadanda za su zaben sarauniyar kyau. Ya yi waje ba tare da ya kalle ta ba, ta mike ta rurrufe ko ina ta fito tana takawa sannu a hankali yana kallon ta ta mudubin motar, duk sha awarta ta motsa shi, amma saboda iya jan ajinsa ba zai taba nuna mata ba, ko ya bari ta gane ba. Ta kama murfin mota ta bude ta shiga baya ta zauna, be kalle ta ba kuma be yi mata magana ba be kuma ja motar ba. Ya yagi takarda ya yi rubutu ya cilla mata baya ta dauka ta duba, “Ba ki kai matsayin da zan zama direbanki ba, “Tana gama karantawa ta bude ta fito ta dawo gaban motar ta rufe. Ya kuwa figi motar a guje kamar me shirin tashi sama. Babu wanda ya yi wa kowa magana haka suke tafe sai da suka zo wani super market ya fita ya yo musu tsaraba suka ci gaba da tafiya. Gidansu ya fara kai ta, yana tsayawa ya mika mata takarda ta duba ta karanta a wa daya na baki ki yi ki fito mu tafi. Ba ta ce komai ba ta bude ta fita ta yi sallama falon ta shiga. Aunty tana ganinta ta mike ta taro ta da murna tana jawahir ‘yata barka da zuwa ‘yata ta kaina.” Ta rungumeta ta a jikinta, “Zo mu hau sama Alhaji ya ganki tukunna, “Suka hau ta durkusa har kasa ta gaida Abba cikin fara’a da murna yake amsawa, “Jawahir ke ce haka? lallai yau zan huta da mitar Auntynki.” Aunty ta ce, “Wa ya kawo ki ne? ko kun dauki direba ne? Cikin jin kunya ta ce, “Ai yaya ne ya kawo ni. Tana rufe baki ya yi sallama ya shigo kai tsaye ya wuce gaban Abbansu ya zauna ya gaishe su. Abba ya dafa kan Haidar ya ce, “Yau na ga jawahir na gode muku da yanda kuka rike kanku ba ku mu kunya ba. Haidar ya ce, Yanzu ma cewa ta yi na kawo ta za ta dauki Sayyid ga shi ban gan shi ba. Aunty ta ce, jawahir ta Sayyid ai yanzu ba irin da ba ce da kike zuwa ki dauke shi ya yi kwana da kwanaki a gidanku yanzu ai sai ya takuraki. Cikin jin kunya ta ce, “Lah Aunty wallahi ba komai ai ba zai takura ni ba. To shikenan gobe za a kawo miki shi ya yi kwana biyu kawai. Ta ce, to Aunty na gode. Aunty da kanta ta kawo musu abubuwan ci da sha suka sauko kasa da Aunty. Duk yanda Aunty ta yi don ta ji ko da wani abu a tsakaninsu amma jawahir ta ce kalau suke. Haidar ya shigo ya yi wa Aunty sallama ya fita jawahir ta kalli agogon hannunta ta ga awa dayan da ya ba ta saura minti uku ta mike ta ce Aunty zamu tafi. “Haba jawahir tun yanzu? Ta ce, Ai za mu bi ta gidanmu da gidan inna. “To jawahir na gode Allah ya yi muku albarka. Manya ledoji biyu Aunty ta ciko mata da kayayyaki. Abba kuma ya ba ta dubu ishirin. Daman Haidar ya sa maigadi ya shigo musu da tsarabarsu. Ta bude motar ta shiga awa dayan ta cika dai-dai shi ma ya shigo suka tafi. Gidan Inna ya kai ta shi ma sai da ya ba ta takarda ta karanta kar ki wuce awa daya. Ta shiga gidan inna murnarta da tsallenta ta cukuikuye inna. Inna ma murna take yi ta zaunar da ita “Daga ina haka? ke me Haidar din yake baki kika sake zama baturiya haka sai dai rashin kiba amma kin kara kyau ko dai ciki ne dake? Daidai shigowar Haidar a zuciyarsa ya ce, “Ciki yaya za ayi ayi ciki yanzu ai ta yi kankanta. Ya yi sallama falon ya shiga inna ta tare shi da murna duk bakinta yaki rufuwa ganin jikokinta shar dasu babu wata alamar damuwa a tare da su. Inna jikinta sai rawa yake yi ta rasa inda za ta sa kanta don murna, ta kawo musu wancan ta kawo musu wannan tana ta hira. “Dan ka’ida bature ya duba agogo saura minti biyu awa daya ta cika Haidar ya yi wa Inna salllam ta rinka yi masa godiyar wannan uwar tsarabar da suka kawo mata. Ya fita ya koma mota yana jiranta. Sai hira kuma ta dawo sabuwa tsakanin inna da jawahir har ta manta da dan ka’ida lokacin da ya ba ta, to tana ta shan labarai da abubuwan ban dariya daga inna. Ba ta yi aune ba ta ga kara minti arba’in da biye a kan awa dayan da ya ba ta zumbur ta yi ta mike inna za mu tafi sai kin zo. Inna ta ce, Au ba sai magariba za ku tafi ba? “Ta ce, “Uhm yana mota yana jira na. “To shi ke nan na gode ku gaida gida. Allah ya yi muku albarka. A cikin mota ta same shi ya kwantar da kujera ya na shan A.C da sautin rediyo ya lumshe ido kamar mai bacci. Ta bude mota ta shiga ta zauna. Ta fi minti goma ba shi da niyyar ta shi bare ya tuka motar su tafi. Ta gaji da jira ta ce, “Yaya na fito. Ya bude ido daya ya ce, Awa nawa na baki.? Ta ce, “Awa daya.” “Sai yanxu awa dayan ta cika.? “A’a Inna ce ta tsayar da ni da hira.” “To kin cinye lokacin da za ki yi a gidanku, yanzu gida za mu tafi sai wani lokacin kuma.” Gabanta ya fadi, duk da dokin da take yi na zuwa gidansu ga shi ta fito din amma ba damar zuwa gidan nasu. Ita girman kanta ba zai bar ta ta ba shi hakuri ba bare ya hakura yakai ta. Kawai sai ta ji hawaye yana zubo mata. Haidar na kula da ita amma sai ya dauke kansa ya ci gaba da tukinsa kamar be san tana yi ba. Tana kukanta har da shassheka amma sai ya karo rediyon ma don kada yaji kukan. Ba wanda ya sake cewa da kowa komai har suka je gida Yana tsayar da motar ta bude ta fito tana goge ido ta bubbude ta shiga dakinta ta fada gado ta yi rub da ciki ta ci kukanta ta koshi. Ta shiga ban daki tayi alwalla ta yi sallar la’asar zuciyarta tana ta zuga ta da kada ta yi masa girki don ya dan dani bacin ran da ta ji, to kuma sai ta yi wani tunani ai ita ta fara bata masa kuma girman kai ya hana ta neman afuwarsa to idan ba ta yi masa girki ba ai ta dada shiga hakkinsa kuma ita ba iya cewa za ta yi ya yi hakuri ba, kuma zai yi bacin ran da ya fi nata, ita kuma ba burinta ke nan ba. Duk da irin zaman da suke yi na rashin yiwa juna magana to amma ba ta so ko kadan ta ga ta bata masa rai. shi yasa kullum take yin abin da ta san zai ji dadi. Ta mike ta fito falo takarda ta gani a ninke, “Na fita unguwa sai magariba zan dawo,” Ta yaga takardar ta fada kicin ta dora girki . Yau tuwon samovita ta yi miyar danyan kubewa da ta burge kaza a ciki. Sai ta gasa masa dan shila ta soya masa kifi ta hada masa lemon abarba ta jere komai a tebir. Yau Dela ta bawa wanke wanken don zuciyarta a bace take. Kafin ya dawo ta gama abin da take yi ta gyara wajen ta shige dakinta ta kulle kofa. Sai da ya yi sallar magariba sannan ya shig, ga mamakinsa sai ya ga tayi abinci a zatonsa yanda ya bata mata ba za ta yi girkin ba, har yana shirin fita Hotel ya siyo musu. Duk kuma sai ya ji tausayinta ya dame shi a ransa sai ya yi da yasanin bai ki kai ta gidan nasu ba. Ya zauna ya ci abincinsa ya koshi yau har da senti ya mike ya je ya sake alwalla ya yi sallar isha’i. Haka ya yi zaman falon har goma na dare amma bai ga fitowar ta ba, abun ya dame shi dan be ji dadin yanda ta takura kanta ba. Haka tai ya hakura ya je ya kwanta zuciyarsa ta na ta tunane tunane. “Washegari da safe da ta gama komai da ya shafe ta ta daddasa kwalliyarta yadda ta saba ta fito yana tebir yana break ta durkusa ta ce, “Ina kwana.?” Ya amsa, “Lafiya lau jawahir kin kwana kalau.?” “Lafiya kalu.” Ta ce ta mike tana koma daki tana mamakin canjin yau da ta samu na sakin fuskar Haidar. Har ya fadi sunanta ba tare da ya ce mata kwaila ko tatsitsiya ba. ******* ******** ****** ******** Haidar bai dade ta fita ba direba ya kawo Sayyid, jawahir ta yi murna da farin cikin ganin sayyid don ta samu abokin debe kewa. Sai magariba Haidar ya dawo sayyid yana jin karar motarsa ya fito a guje ya tarye shi, Haidar ya dauke shi ya rungume shi, “Auta wa ya kawo ka? ina ka baro Auntyn taka? “Tana gida Abba ya ce kada na dade kwana biyu zan yi.” Haidar duk ya gama wani abu da zai yi na game da cin abinci, wanka ya sa kananan kaya na shan iska ya haye saman gado yana shan surutun Sayyid da yake ba shi dariya. Wayarsa ta fara ruri alamar ana kiransa. Haidar ya duba ya ga bai san lambarba ya share ya ki dauka, ta katse dan kanta, can aka sake bugow
a be dauka ba ta kuma katsewa. Sai da aka yi sau biyar a na shi dan Haidar ya gaji ya dauka, “HELLO. Ya amsa a kasan makogaronsa. Cikin doki Kausar ta amsa, “Ranka ya dade saraki har yazu mulkin yana nan ne ba a sauke ba?” Ya ce, “Wake magana ne? ko sai na ajiye kan wayar ne.? Ta ce, “A’A ayi hakuri Saraki kausar ce. Yac, “Wa cece kuma me wannan sunan.? “Ranka ya dade Saraki Kausar dinka da kuka yi karatu America tare ka gudo ka bar ta. “Oh. Kausar kenan kin cika na ci, yanzu sai da kika lalubo ni.” “To ya zan yi Haidar wallahi tun ranar da ka taho ban kuma nutsuwa a zuciyata ba sai yau da na ji muryarka. Haidar ciwon son ka ya zamo gyambo a cikin zuciyata. Haidar ni musulma ce ka tallafi rayuwata Haidar ka zo gare ni ka aure ni. “Haba Haidar ka san darajar ‘ya mace da kimarta amma duk na watsar na tunkare ka na ba da kai na ke rokonka da ka aure ni. Haidar wace irin zuciya ce da kai? Ka tuna fa kana da kanne mata kuma nan gaba in Allah ya ba ka haihuwa kila ka samu ‘ya ‘ya mata, to ya za ka ji yayin da ‘yarka ko kanwarka ta fada irin wannan halin da na fa da akan kan wani? Ka san kaddarar ubangiji babu inda ba ta fadawa mutum.” Haidar ya ce, Ki yi hakuri ba burina na yi miki wulakanci ba, ai duk inda masoyinka yake ya fi makiyinka sau dubu, to amma kin ga yau shekara daya ke nan iyayena sun hada ni aure da wata ‘yar karamar kanwata, wadda har a yanzu da nan gaba rainonta nake yi.” Kausar ta ce, Haidar don Allah don Annabi ka amincewa bukatata wallahi ni ba ruwana da wata matarka don ba a kanta zan zauna ba. Ya ce, “To shi kenan Kausar ki ba ni lokaci zan yi shawara. Ta ce, “Haba Haidar. Ya ce, “Uhm no kada ki damu ba matsala insha Allahu komai zai zo da sauki. Suka yi sallama kowa ya dire wayar. Haidar ya fada tunani ko na amince da bukatar Kausar na aure ta, ko ni ma na ji yanda auren yake? To ya zan yi da Aunty da Abba? ko da yake in sha Allahu ba za su zamo matsala ba. Haba dai ya kwanta yana sake- saken abinyi. Washegari yana office wajen azahar jawahir ta yi baki kawayenta ne suka zo. An sha hira kuwa inda jawahir take cewa, “Bilki ai kun yi min rashin mutunci wai duk yanda muke da ku aure shekara daya amma kuka kasa leko ni.” “To ai kin san abun ne sannan ba kwa shiri da shi mu zo wani abun ya faru sai ya zamo matsala, some kin ga yanzu ai komai normal don yanda kike wannan kyallin goshin na san an samu rabo ma ( Hahaha kunji gulma. Hmmm Ni dai Bomboy ba ruwa na idan Haidar yaji ku). Ta yi dariya, “Uhm kwa ji da shakiyancinku ku zo mu ci abinci.” Wajen karfe hudu suka gama shirinsu suka fito za su tafi ta yo musu rakiya har bakin get, megadi yana dan dakinsa yana lazimi, Hira suke yi suna tafawa tare da shewa da dariya. Sai ga motar Haidar ya. [8:35PM, 12/6/2016] : shigo ya danna hon megadi ya taso da sauri ya bude masa get. Haidar ya hango jawahir ba mayafi a jikinta ta yi kwalliya tana ta faman dariya duk sai ya ji kishi da bakin ciki ya dame shi. Yaya za ayi ma ta fito nan a haka? Ga megadi da ‘yan aikin gida suna nan du su gano ta. Lallai ma yarinyar nan. Ya yi parking ya fito gunsu ya nufa kawayenta suka gaishe shi ya kalli jawahir ke me ya fito dake nan? Wa ya ba ki izinin zuwa kofar gida.? Kanta a kasa ta ce, “Kawayena ne suka zo shi ne na rako su. Rakiya ba ta isa ba iya kofar cikin gida har sai kin fito bakin get.? Ya shige ciki ya bar ta a nan. Kawayenta suka ce, “Lallai Haidar yanzu har wani kishinki yake? “To Allah ya sa dai mu jawo miki wata matsalar ba.?” Ta ce, “Haba dai ba komai ai yana da saukin kai shi ke nan kuma fadan ya wuce. “To mu dai mun tafi sai wata rana.” Suka fita ta juyo ta shigo cikin gidan. Yana zaune a falo ta tafi za ta shige daki ya ce, “Ke zo nan. Ta dawo ta durkusa nesa da shi. “Daman in ba na nan bain da kike yi ke nan ko? Kalle ki yanda kika fita ga megadi da yaran gida duk suna ganin ki ko kin manta cewar ke matar aure ce? To bari ki ji duk da an aura min ke ba tare da ina son ki ba, to hakan ba zai hana ni yin kishinki ba, kuma dole ne na sa miki ido don ganin yanda kike tafiyar da rayuwarki, kada na kara ganin wata kawa ta zo miki kin ba ta fuska bare su zo su bata miki tarbiya ko su rinka zuwa tsegumi su samu damar bugun cikinki kina gaya musu sirrinki ko? Ita dai ba ta ce koami ba ya karaci fadansa ta tashi ta yi shigewarta daki. Tana barin wajen wayar Kausar ta shigo, “Hello Kausar kina lafiya.? “Lafiya lau Haidar shiru banji ka ba. Ya ce, “Kai kausar kin fiya gaggawa, amma ki ba ni adres din gidanku insha Allahu jibi zan zo, ta saki wani ihun murna yayin da take gaya masa adres din gidansu dake Abuja. Suka yi sallama ya ajiye wayar. Washegari yana zaune a office ya kifa kansa da tebir tunanin yanda zai bulluwa da iyayensa maganar Kausar yake yi. Abokinsa ne ya shigo ya sa me shi a haka. Duk sallamar da yayi bai ji shi ba bare ya amsa masa. Faruk ya kwankwasa masa tebir din gabansa. Haidar ya yi firgigit ya dago kansa ya kalli Faruk din ya saki ajiyar zuciya. Ya ce, “Yaushe ka shigo ban ji shigowarka ba.? Faruk ya ce, “Yaushe dama za ka ji ka tafi cikin wannan zurfaffan tunani haka, wai don Allah me yake damunka ne? jiya da yau duk wani sukoko nake ganin ka. Ya ce, “Ga ni nan dai abubuwan ne suka tarar min “Ba dai matsalar jawahir ba, ca nake mun gama wannan maganar da kai. Haidar ya ce, “Ai ni ba zan taba iya abun da ka ce na yi ba. Ciknin zaro ido ya ce, “Ba dai kana nufin har yanzu babu abun da ya hada ku ba?. Aure shekara daya. “To kai me kake tunanin zai faru? kanwata ce fa. yarinya ce, ko hannunta na kama ai raina ni za ta yi.” Faruk ya ce, “Amma wallahi kana daukan alhakinku. Gaskiya ba ka kyauta ba, yaya za ka rinka wahalar da yarinya, kana zaton dutse ce ita ko waliya ce da ba za ta ji sha awa ba? Haidar ya ce, “Ko dai take wahalar da ni tana gasa ni, ka ga dai ni nake gaba da ita ya kamata ta fara neman sulhu da ni, to amma yarinyar nan gaisuwa ce kawai da safe take hada mu. Ga yarinyar ta iya tsara kwalliya komai ta sa sai yayi mata kyau ya yi das a jikinta kamar Aljana. Duk dare yanzu bacci gagarata yake yi, na dinga murkususu ke nan ina juyi sai ka ce dole, ai ba waliyyi ne ni ba, don haka na yanke shawarar aure zan kara a kwanan nan. Faruk ya dafe kirji ya ce, “Aure Haidar! kai kuwa me yayi maka zafi? Ba gwanda ka nemi sulhu da matarka ku dai daita ba. : (Hmmm barshi da kanshi zai sauke wannan jiji-da- kan. Mu dai yan kallo ne kuma yan rahoto. Da fatan dai idan anzo kamen dan leken asiri ba zaku nuna ni ba).