SALON SO CHAPTER 4

SALON SO CHAPTER 4

 
 
 
Haba Faruk yaya za a yi na kwantarwa da wannan karamar yarinyar kai. shi kenan na ba da kaina girma kuma ya fadi, ni dai kawai aure zan yi na rabu da ita ta karaci tsiyarta ita kadai. Faruk ya daure fuska alamar ba wasa ya ce, “To kai duk abun da ake gaya maka ba za ka ji ba ko, to shi kenan ka je ka aika ta abun daka ga dama, in kuma abu ya kwabe maka kada ka sake ka nemeni tun da ban isa na ba ka shawara ka dauka ba, “Faruk ya juya ya fice tare da bugo kofar. Haidar ya yi ajiyar zuciya tare da tallefe kansa da hannu biyu, “Gaskiya ba na jin zan iya fasa auren nan, ni kawai zan yi auren nan ne don debewa kaina kewa da sha awa saboda kullum ni na san yanda nake kwana ina cutuwa. To me yayi zafi ni dai ba zan kai kaina ga halaka ba bare na nemi matan banza Allah ya kiyaye mu da aikata zina gwara kawai na yi auren, “Haka dai ranar ya wuni babu wata walwala. Alhaji Sa’adu mashi, babban ma’aikacin gwamnati ne wanda aiki yake yawo da shi ko ina a Nigeria. A haka ne ya zo Kano inda ya yi gida ya tare da iyalansa. Da yake makotaka suke da gidansu Haidar to sai shakuwa da aminci suka shiga tsakaninsu. Kasancewar Alhaji Sa’adu ba shi da wani dan uwa a garin kano to da ya samu Abbansu Haidar sai ya rike shi ya zama dan uwanshi na kut da kut. Faruk da Haidar sa’o’in juna ne tare suka ta so iyayensu suka sa su primary tare, secondary ma tare Faruk da Haidar sun shaku da junansu. Abun ya wuce abotaka ya koma ‘yan uwantaka. Bayan gama secondary dinsu ne aiki ya kuma mayar da Alhaji sa’adu gida wato katsina ya tatara iyalinsa suka koma can gida. Hakan kuwa bai yi wa su Haidar dadi ba sai dai don basu da yanda za su yi ne, to daga nan ne Haidar da yaya Abba suka tafi America karatu. Bayan dawowarsu ne da za a bikin bude masa kamfaninsa da mahaifinsa ya bude masa to sai ya tafi garin mashi ya lalubo Faruk. Bayan bude kamfanin nasa ne dai suka ci gaba da zumuncinsu. To faruk din yayi aure yana zaune kusa da iyayensa Yau Haidar bai samu zuwa office ba don Abuja yake shirin tafiya, don haka tun tara na safe ya kammala duk shirye shiryensa ya nufi hanyar Abuja. A hanya ya lodar musu tsaraba. Bai samu matsala dangane da kwantaccen da ta yi masa, tun da ya san unguwar da suke zaune fitacciyar unguwa ce ta manyan kasa masu fada a ji ne. Kausar kuwa a na can an gama duk wani shirye shirye na taryar gwarzon masoyi. An gyara falo an kayatar dashi, ana jiran masoyi. Kausar ta yi wanka ta sha kwalliya da dandatsetsen less. wanda za mu iya cewa kwalliyarta ce, ta fito mata da kyau. Don kun san ba a mummunar mace sai marar gyara. don duk munin mace kwalliya sai an ga kyata. Don naka gyara da kwalliya shine mace. Kausar baka ce amma a yanzu da yake durfafi yin shafe shafe da mayuka ‘yan kanti za mu iya cewa ta koma fara. Doguwa ce, tana da kiba da fati. ba ta da wani girman nono, kanana ne wanda har sun riga sun zube, amma wayayyiya ce ba ta shiga abin da be shafe ta ba akwai hutu da jin dadi rayuwar duniya. Haidar ya iso lafiya. “Ya kuke murna da rawar jiki a wajen Kausar. Tuni ta sa a ka shigar da Haidar dakin da aka wuni ana gyarashi don zuwasa. Tuni aka gama cika gabasa da kololin abubuwan ci da na sha. Can Kausar ta shigo cikin washe baki tana fara’a don bakin yaki rufuwa ta ta ho ta saurin ta ta zauna kusa da shi a guje ta rirrike hannuwansa, “Oh ni ‘yar nan! Allah na gode maka da ka sake hada ni da abun sona, burin zuciyata wato Haidar, ubangiji yanda ka hada mu a nan yanzu ubangiji Allah ka hada mu a gidansa a dakinsa, a matsayin matar aurensa,. Ta shafa. Haidar ya ce, “Irin wannan doguwar addu’a haka to kada ki yi wacce za ki rike ni a gidanku na kasa komawa gida. Ta kyalkyale da dariya ta rinka zuba masa girke girgen da aka yi masa kamar ta ba shi a baki haka ta rinka yi masa. Suna dade suna hira duk wani dan gidasu sai da ya zo suka gaisa. Haka ya shiga ciki ya gaida Babarta da kishiyar babarta. Ta hau da shi falon sama har wajen babanta sai da ya ce, Baban nata yayi murna da ganin shi don ya yaba da hankain haidar a kan zai turo iyayensa don a yi maganar aurensu da Kausar. Babanta ya yi ta sa masa albarka inda Haidar din yake ta malala masa godiya. Haidar sun sauko daga saman sun dawo wajen hirarsu Kausar sai munrna take kamar ta goya shi. Ya sa yaron gidansu ya kawo musu tsaraba a but din motarsa ya yi wa kausar sallama don yana so ya tafi gida kada dare ya yi masa a hanya. Da kyar ta kyale shi ya tafi don gani take yi kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Haidar daga Abuja duk dumbin gajiyar da ya kwaso bai wuce gidansa don hutawa ba sai ya zarce gidansu, yanda ya shiga a hargitsensa Abba da Aunty suka san ba lafiya ba. Bayan sun gaisa ne ya koma gefe daya ya yi zugum da shi yana tunanin ta ina zai fara ne. Abba ya shi, “Haidar lafiya? Me yake faruwa ne? “Wallahi Abba abun da yake damuna ne na rasa ta inda zan bullo masa bare na gaya muku “Ba komai gaya mana ko meye, kana da wadanda za ka gayawa ne wandada suka fi mu? Ai ka ga babu ko? Gaya mana menene damuwarka?” “Wato Abba tun muna America akwai yarinyar da muka yi alkawarin aure da ita, to bayan mun gama na taho gida Abba kuka tayar min da maganar auren jawahir. Abba don kada na bata muku rai ne shi yasa ban yi muku maganar kausar din ba. Ita dai na gaya mata, na ba ta hakuri, to ta tashi hankalinta sosai, to shi ne na kwantar mata da hankalinta da cewar zan aure ta bayan shekara daya. da kyar Babanta ya amince mata shi ne yanxu kuma uban nata ya takura mata da maganar auren, nake so don Allah Abba ku bar ni na aure ta. Aunty kuwa ta mike tsaye cikin fada take nuna shi da yatsa, “Kai ka kiyaye ni, wallahi ka shiga hankalinka. A aura maka ‘yar uwar tawa auren naku shekara daya ka ce za ka yi mata kishiya, to ba ka isa ba ka yi kadan jawahir ta fi karfin ka wulakanta ta.” Abba ya daga mata hannu ya ce, “Aisha ya isa haka. Haidar tashi ka je gida tukunna sai mun yi shawara za ka ji komai. Ya mike, “To Abba na gode ku tashi lafiya. Aunty sai da safe ya wuce sukuku kamar wanda kwai ya fashewa a ciki Abbansa ya ce, ba a yin haka Aisha ki duba ki gani yaron nan ya yi mana biyayya lokacin da muka tursasa shi auren jawahir yanzu bai kamata ya zo da tasa bukatar mu ki biya masa ita ba, kin san ‘ya ‘ya amana ne a hannunmu duk da cewar mu muka haife su to idan muka zalince su Allah fa ba zai kyale mu ba sai ya tambaye mu, to kin ga dai bai kamata da farko mun bi son rainmu mun yi masa aure ya hakura sun zauna sannan yanzu ya kawo bukatarsa mu bi son zuciya mu hana shi, aikin ga ba mu dai dai ba bare lamarin aure da ba ayi masa katsalandan. Abun duniya duk ya dagulewa haidar duk dai da ya ga alamun nasara a wajen Abbansa, to Aunty fa Ai ita za ta zamo babbar matsala. Yana zaune a falon kasa jawahir ita ma tana waje daya zaune kan kujera tana yi wa Sayyid karatun Alkur’ani yana biyawa. Wayar Haidar ta fara ruri ya daga, “Hello Kausar ina gajiya. Ba gajiya sweety, yaya ka dawo gida? “Lafiya lau kausar ai na sha wahalar tafiya dag kano zuwa Abuja a mota kuma a dawo a ranar, ai akwai wahala. Ko da yake ba komai tun da Hausawa sun ce garin masoyi ba ya nisa, duk ranar da Allah ya mallaka min ke na fanshe wahalata…… Wani katutun bakin ciki ne ya tsayawa jawahir a zuciya, rainin hankali wato a gabana ma yake yi wa mace waya? wallahi bai isa ya yi min wulakanci ba, ina zaman dole a gidansa ‘yar sakin fuska ba yayi min bare mu yi hira amma shi ne yake kyalkyala dariya da budurwarsa, kawai sai ta mike a fusace ya riga ya shagala da yin magana a wayar ta fizge wayar daga hannunsa ta doka ta da kasa. Wayar ta tarwatse sai ta ya daki a guje ta rufe kofa duk da haka sai ta fada gado ta sa kuka. (To in banda abun jawahir kukan me kike) Bari dai mu ci gaba labari mu ji me yake faruwa a zukatan guda biyun. Haidar ya bi wayarsa da take tarwatse kan kafet da kallo, “To me jawahir take nufi da za ta fizge masa waya? Kishi take yi ko kuma dai ta fara raina shi ne? Lallai zai yi wa tufkar hanci kada nan gaba abin ya shafi aurensa. Da safe ya gama shirinsa ya sauko ya nufi tebir don yin break ya ga wayam babu break bare alamarsa. Ya kwallawa sayyid kira ya fito da gudunsa, “Ina Antinka?” “Tana daki.” “To je ka ka kirawo min ita.” Ya kirawo ta ta fito yayin da ta durkusa, “Ga ni.” Ke me ya hana ki yin break? Kina nufin haka zan tafi offi

ce da yunwa.? Kanta yana sunkuye a kasa ta ce, “Ai ca nake za ka biya ta wajen masoyiyar taka ka ci a can. Ke ba na son shirme kin ji ko, tashi ki je ki hada mana break. Bakin ciki ya ishe ta ba abin ta ce ba za ta yi ba ta sabawa ubangijinta. kawai sai ta mike tana kuka ta nufi kicin din. Sai tausayinta ya kama shi yarinyar tana burge shi ko don biyayyarta. Ta gama soya dankali da kwai ta dafa ruwan shayi sai dammaman kunun gyada da ta yi masa kofi daya kamar yanda yake sha lokaci lokaci. Za ta wuce daki ya yi kirata, “Ke zo nan. Ta dawo ta durkusa. Ya ce, “Ta so ki yi break. Ta girgiza kai na koshi. Ya daka mata tsawa. “Ta so mana jinkinta na rawa ta mike ya hada mata ruwan tea me kauri ya mika mata. Ya tura mata dankali da kwai da biredi gaba ya ce, “Ki ci da yawa ko yanzun nan ranki ya baci. Haka ta rinka ci ana hawaye yana kallonta sayyid kuwa ya tafi wajen Dela za ta yi masa wanka. Haidar ya gama break dinsa ya mike ya nufi office jawahir ta kifa kanta a kan tebir din ta ci kukanta ta koshi ta gama ta shafe hawayenta ta koma daki. Sayyid ya shigo an yi masa wanka ta shirya shi ya rinka jijjiga ta dole ta fito ta hada masa break ta koma daki. Zuciyarta tukuku take yi mata sam ta kasa samun sukuni a zuciyarta tun daga wayar nan da ta ji haidar ya yi, “Wato ma ina ruwanta ne da wayarsa.? To me yake neman faruwa da ita ne? ke wallahi na gaji da zaman banza a gidansa ya zo mu yi duk wace za a yi, na cire tsoronsa da shayin komai don ni mutum ce ba dabba ba yanda yake da a gidansu haka nima nake a gidanmu. Yau ma dai haidar daga office da ya tashi gidansu ya kuma waccewa a kan maganarsa ta jiya. Abbansa ya ce, Ka kara hakuri Haidar a bi komai a hankai ba a son gaggawa don gaggawa tana daga shaidan. Aunty ta ce, Alhaji ka rabu da yaron nan, nema yake ya tozarta mu ya bata mana zumunci to wallahi ba ka isa ka shiga tsakanina da dan uwana ba. Abba ya ce, “Haidar tashi ka je gida zan je na nemi Daddyn jawahir din na yi masa bayanin komai, na san shi mutum ne me fahimta ba zai kawo komai ba to daga nan sai mun shirya ranar da za mu je Abujan wajen iyayen yarinyar. Haidar ya rissina, “To Abba na gode Allah ya saka da alheri, ubangiji ya kara girma. Ba komai haidar kai dai ka rike amana kuma ka sawa zuciyarka adalci ya yi musu sallama ya tafi. Yau a falo ya samu jawahir tana kallon wasan Hausa. Be kalli inda take ba ya haye samansa. Ita kuwa daman a cike take ta shi jira take yi ya dawo su yi wace za su yi don ta gaji da zaman gadin gidansa. Sai da ta bari ya kammala dun wani abu dayake yi ya dawo falon kasan ya zauna yana duba jarida sannan ta fara magana ba tare da ta kalle shi ba. “Yaya yau dai magana nake son mu yi da kai. Ba tare da ya dago kai ba ko ya bar karatun jaridar ya ce, Uhm ina sauraronki. Ta ce, “Wai menene matsayina a gidan nan ne? “Bai dago kai ya kalle ta ba ya ce, “Matsayinki kike son sani? Ta ce, “Kwarai kuwa.” “Ya ce, “In dai ba mantawa kika yu ba matsayinki yana na kanwata da kuma wai matata ta aure, don wai zance. Ta ce, “To in haka ne me zai hana ka sake ni ko ma huta daga ni har kai da wannan daurin da bai bayin da aka yi mana. Ya ce, mata, “Ai dama ba ni na gayyato ki ba in wanda ya kawo ki ya gaji da zaman naki za ki ga ya zo ya dauke ki. Zumbur ta mike tsaye ta rike kugu ta nuna shi da dan yatsa, “Kai bari ka ji, ni ba irin ballagazayen matan nan ne da ka saba wulakantawa ba, ni na fi karfin wulakancinka, ina bin ka ne gudun kada na sabawa ubangijina da kuma gudun wargajewar zumuncin iyayenmu da nake yi wa biyayya, to yanzu na gaji da zama da kai don ka san ba na son ka a ka ba ni kai, na yi hakurin zaman shekara a gidanka, to yau hakurina ya kare ba zan sake kwana a gidanka ba dole ne ka sake ni. Tana rike da kugu tana yamutsa fuska tare da girgiza jikinta na jin bala’i. Ya kalle ta daga sama har kasa, dariya ce ta kwace masa ya dai daure ya gintse dariyar ya ce, “Ni nan da kika ganni ba zan taba sakinki ba, in kin ga dama ki zauna in baki ga dama ba ki je duk inda za ki amma maganar rabuwa babu don ni ba wawa ba ne. Idan ba ki sani ba ma ki sani aure zan yi kwana nan. Ta dafe kirji, “Aure! Aure fa ka ce? Da gaske kake yi? Wallahi ba zan zauna a gidanka ba bare matar ta zo ita ma ta raina ni, ban da kaddara ma me zai sa na aure ka? Ni me santalelen saurayi da yanzu ina gidansa. Ya mike kuwa cikin sauri zai kai mata mari ta yi saurin kaucewa ya ce, “Ki yi a hankali duk san da kika sake fadar wani namiji a gabana da sunan yana sonki sai kin raina kanki. “Ya yi hayewarsa sama ya bar ta tana kuka. Haka kawai be yi min abun da na nema ba sannan ya ce aure zai yi, wallahi ba zan zauna ba tafiyata zan yi, duk abin da ma zai faru ya faru. “Da sauri ta fada dakinta ta kama hada kayanta tana zuvawa cikin akwati ta turo akwatin da kyar ta kirawo Dela ta ce ta bawa yaron gida ya sawa Haidar a but din motarsa. Cikin rawar jiki ta karbi aiken uban dakinta duk abin da ta san za ta bukata ta sa an kai but. Ta fito da shirinta za ta fita lokacin Sayyid ya tashi daga bacci ya ce, “Aunty ina zaki? Ni ma zan biki. “Ta shafa kansa, “Ka yi hakuri Kayyid zan siyo maka jirgin sama me tashi. Ya makale kafada alamar bai yarda ba. Ta ce, “To je ka dakin Yaya ka ce ya zo mu tafi. Ya ce, “To Ya hau san a guje. Ita ma saurin ta yi ta fice ta shiga motar Haidar ta tashe ta ta tafi ba ta taba tuka mota da kanta ba sai yau, amma ta iya don duk sanda za su fita da direba sai ya koya mata. Haidar yana jin tashin mota ya turo Sayyid daga jikinsa ya mike zumbur sai sannan ya tuna ya bar mukullin motarsa a falon kasa. Ya gangaro falon kasan da sauri yana salati, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji un. Hankalinsa ya yi mugun tashi. “Na shiga uku. Kadda yarinyar nan ta yi wani wajen yanzu idan wani abu ya samu yarinyar nan yaya zan yi da rayuwata? Ga Sayyid ya ishe shi da ihun kuka yana kiran “Aunty Dole Haidar ya dauki wani mukullin motar ya saba Sayyid a kafada suka fita. Ya shiga mota a hankali yake tuki yana kallon hanya ko zai hango motarsa da jawahir a ciki. Jawahir kuwa cikin nutsuwa da tsoron ta gudanar da tukinta har ta zo kofar gidan Inna tayi hon megadi ya bude mata ta shiga ta yi parking ta sa shi ya jidi kayanta da yake but ya shigar mata da su cikin falon Inna. Inna ta ce, Lafiya na ganki da kaya? Ta ce, “To lafiyar kenan. Inna ta ce, “Me yake faruwa ne na gan ki da kaya kuma kin rame a kan san da kuka zo, ko ba ki da lafiya ne? Ta ce, “To ba dole na rame ba an aurawa wanda ba ya so na ni yana ta gasa ni ga shi nan ai yau ya koro ni gidanmu ko.?” Inna ta dafe kirji ta ce, “Shi da kansa ya ce ki taho gidan? “Shi ne mana Inna kullum sai dai ya kira ni da tatsitsiya ko kwaila, ya mai da ni ‘yar aiki na girka masa ya ci ya koshi wallahi sai kwanan nan ya fara yi min magana amma da ko meye sai dai ya rubuto min a takarda sai ni ma na ba shi amsa a rubuce sai ka ce kurame. Inna ta saka salati, “Au ni ina ta murna na zata ciki ne da ke ashe ba wani bayani. Ta ce, “Uhm inna ke nan, to ko matsayin kyakkyawan kallo ba na samu a wajensa duk na yi hakuri na jure to wai yanzu aure zai yi. Inna ta ce, “Aure, lallai ma yaron nan ban ni da shi boye ki zan yi, zan gyara ki na kula da ke har sai kin zama cikalkiyar mace zai raina kansa ne da ni yake zancen. Duk waigen da Haidar yake yi bai hango jawahir ba har ya iso gidansu. Aunty ya samu a falo tana kallon labarun kasa ya sauke Sayyid ya tafi da gudu ya fada jikin Aunty yana kuka. Aunty ta rungume shi tana cewa, “Haba Auta me aka yi maka kake kuka.? “Bayan Auntyn gidan Yaya ce ta gudu ta bar ni. “To yi hakuri tun da an kawo ka wajena ka ji.” Ya daga kai Ta kalli Haidar, “Ina jawahir din take?” Ya ce, “Wallahi ban san inda ta tafi ba, kawai na ji karar mota, ashe ita ta fice ta yi tafiyarta. Aunty ta dafe kirji, “Ita kadai ta ja motar ta fita? Wato ka yi mata maganar auren naka ko? To wallahi tashi ka fita duk inda take sai ka je ka nemo ta. Abbansa ya shigo, “Lafiya na gan ku haka? Aunty ta ce, “To ba dole ka ganmu haka ba, ya salwantar min da ‘ya. “Wa ce ‘ya?” Jawahir mana, wai be san inda take ba. Abba ya yi saurin zama don jin faduwar gaba da ya yi, ya kalli dan nasa, “Haidar me ya hada ku har ta fita?” Haidar ya ce, “Ni kaina ban san abun da na yi mata ba, ta ji dai ina waya ta kwace wayar ta tarwatsa

ta sai na mike na hau sama, to ban ankara ba na ji tashin motata. Aunty ta ce, “Uhm ka ji ba, in ban da rainin hankali yaushe zai je gabanta yana waya da budurwa suna hirar aure. Ni na san wannan rawar kan da kake yi sai ka jawo mana tashin hankali, ka ga in ka ga ba hali ka sakar min ‘ya mu ba neman kai muke yi da ita ba. Abba ya ce, “Duk haka ba ta taso ba, ku kwantar da hankalinku da safe zan je gidan na su sai na ji dalilin tahowar tata. Yanzu tashi ka tafi gida. Aunty ta ce, “Ba fa tabbas din gidan ta tafi dole ne a yi binkicen ta tun daga yau.” Ta dauko mayafinta ni bari na je gidan na su yanzu. Ta shiga mota direba ya ja ta suka nufi gidansu jawahir. Tana shiga gidan ta tarar da mommy da Nasir da su Auwal da Sani. Aunty ta zauna duka suka gaishe ta cikin fara’a ta amsa tana wasa da dariya ta su. Suka gaisa da momy da tsokana irin wasan nan na kannan miji. Ta ce, “Yaya kuwa yana nan? Momy ta ce, “Eh yana sama. Auwal je ka gaya masa Aunty ta zo, “Ya hau da saurinsa ya sauko ya ce, “Ki hau saman Ta hau. Bayan ‘Yan gaishe gaishe da suka yi sai ta gyara zama ta ce, Yaya ina Jawahir din?” Cikin mamaki ya ce, “Au ta zo ne? “Uhm wai rigima suka yi da mijin nata ta taho. Ya ce, “Ikon Allah ai ni ban ma sani ba bari na tambaye ta Ya dau waya ya kirawo momy ta yi sallama ta shigo ta nemi waje ta zauna. Ya kalle ta ya ce, “Ina jawahir take? Momy ta ce, “Tun da aka yi auren ta ba ta zo gidan nan ba. Wani abu ne? “Wai sun yi rigima da mijin ta taho. Momy ta ce, “Oh ni ‘yasu, yara ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba, yanzu duk fadan nan da aka yi wa jawahir sai da ta sabawa nijinta. Aunty ta ce, “A’a ai ba laifinta ba ne, da ai lafiya suke zaune auren nan da ya rakitowa kansa duk shi ya hargitsa musu zaman.” Momy ta ce kin ji irin shashancin ko, ai komai na Allah ne, namiji da aka halicce shi don mata hudu ka hana shi kara daya. Aunty ta ce, A’a ba ta fa da laifi ko ke da kika girma da Yaya ai ce zai kara aure da sai kin hana mu sakewa bare ita da ga yin aure shekara daya a ce namiji zai maka kishiya, ai dole a ji kanku. Dady ya ce, Ai kun san ma ba za ta zo nan ba tun da ta san ba goyon baya za ta samu ba. Tana gidan Inna, tun da ta je hannun Inna kuwa kwato ta sai wani ikon Allah. Aunty ta ce, “Ai maganinsa kenan wallahi gwanda ta hora shi tukunna. Momy ta ce, “A’a ni dai ba na son son kai don dai kin ga ‘yarki ce kawai kuke son ga sa masa gyada a hannu. Dady ya ce, Ba me wahalar min da da, duk zan tara su na san meye matsalarsu. Hankalin Haidar ya kara mummunan tashi yayin da ta bayyana cewa jawahir ba ta gidansu. Goma na dare Haidar ya isa gidan Inna a gigice yana neman jawahir din. Inna ta fututtuke ta ce ita yaushe rabon da ta ga jawahir ma? Wallahi ya je duk inda jikarta ta take ya nemo mata ita in ba haka ba kuwa ya gamu da fushinta. Haidar kamar zai yi kuka magiya yake yi wa Inna idan ita ta boye jawahir ta fito da ita don ya ga motarsa a gare jin gidanta wadda da ita jawahir din ta fito. Inna ta ce, To sai dai in zuwa ta yi ta ajiye motar ba ta shigo ba ta fice, “Ta ce, “Na gaya maka wannan kame-kamen ba zai yi maka ba, ka je ka nemo min jikata. Sha daya na dare ya bar gidan Inna ya isa gidansa. Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, amma haka ya kwana yana juyi da tunanin inda za a ga jawahir. Ga yunwa ta gallabe shi ga ba abinci, shi kuwa ko ruwan shayi be iya dafawa ba, bare ya dafa ya sha. Haka ya yi ta juyinsa har aka yi, sallar asuba. Daga masallacin gidansu ya taho a motarsa. Abba ya yi mamakin ganinsa inda yake tambayarsa, “Lafiya haka da asuba.? “To Abba ina zan iya samun sukuni ba a fa ganta ba. “Ba ka ce ka ga motar gidan Inna ba.?” “Ai Inna ta ce ita ba ta shigo mata ba ajiye motar ta yi ta san tana waje. Allah ya kyauta, Abba ya lallaba shi ya yi wanka suka yi break tare. Abban ya dauko shi suka yo gidan Inna wai ko za su ga jawahir din. Amma Inna tana jin tsayuwar mota ta tura ta wani dan daki ta yi zamanta a falo. Abba da Haidar suka shigo duk yanda suka yi don su bigi cikin Inna su ji ko jawahir tana gidan Inna ta fututtuke ta ce ba ta zo mata ba. Dole suka hakura suka yi mata sallama suka fita. A mota kawai Haidar sai ya sawa Abbansa kuka, “Don Allah Abba ka tainaka min a ga jawahir, yanzu in ban gan ta ba ai na shiga uku ya zan yi da rayuwata? Ya dafa kansa ya ce, Ka yi hakuri Haidar za a ganta ne insha Allahu. Bayan fitarsu Inna ta yiwa danta Aminu da yake Abuja waya ta gaya masa komai ta ce tana so ta turo masa jawahir nan kada ya sake ya ce tana gunsa. Aminu ya amsa da to! Ya ce da kansa zai zo tararta filin jirgi. Jawahir ta gama shirinta a boye direban Inna ya kai ta filin jirgi ta hau zuwa Abuja sai da ya ga tashinsu sannan ya dawo ya shaidawa Inna. Can kuwa Uncle dinta yana Airport yana zaman jiranta. Yana hango ta ya taro ta da murna suka rankaya zuwa gidansa matarsa Maryam ta yi farin ciki da ganin jawahir, don Maryam mace ce mai faran-faran da son jama’a ga ta wayayyiya. Irin gogaggun matan nan ne wadanda suka san makamar kama da namiji. Ba bata lokaci Uncle ya karbi takardun makarantar jawahir ya samar mata University of Abuja. Ba bata lokaci jawahir ta zamo daliba a jami’ar. Jawahir an shiga cikin wayayyun ‘yan matan jami’a ta goge ta kile, ta kara kyau da girma babu yanda za a yi wanda bai yi mata cikakken sani ba, ya gane ta, don yanda Maryam ta ke gyara ta kamar ‘yar cikinta don wani magunguna da tsumi na mata da take dibga mata tana sha. Sai maganin ciko da nono da tsaitsayar da su don har ya zube, shi take ba ta tana sha. Kasancewar hankalinta a kwance yake ta yi ‘yar kiba ta murje jikinta mulmul kamar na jariri, sabon haihuwa. Kirjinta ya cika fam yana tsaitsaye ba shi da alamar rankwafawa, duk wanda ya kalle ta sai ya juya ya kara kallonta saboda tsabagen haduwa da wani shirtaccen kyau da ya kara bayayyanar mata.16/18

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *