SALON SO CHAPTER 5
HAIDAR ya kasa samun nutsuwa dole ya nufi gidan abokinsa Faruk don yanke shawarar da za ta fisheshisu. Yana zaune a falo Faruk ya hada kai da guiwa yana ta tunani tare da karanta wasikar jaki. Faruk ya shigo falon tare da yin sallama. Bai jira an amsa sallamar ba don ya san ba zai samu ba ya karaso ya dafa kafadar Haidar ya ce, Me yake faruwa ne da kai aminina? Wace matsala ce kuma take kokarin danno maka kai ne? Kai da za ka yi auren ke ce raini. Ya ce, “Kyale ni Faruk abin duniya duk ya dame ni, ko ka san jawahir ta gudu ban san inda ta nufa ba. Faruk ya dafe kirji ta gudu fa ka ce? Me ya hada ku, ko na ce me ka yi mata? “Uhm kai dai a yi sha’ani, wai daga na yi maganar aure zan yi sai yarinya ta gudu. Faruk ya ce, “Ai madallah ka ga irin abin da nake jiye maka ko, to ai ga irin ta nan yanxu sai ka je ka bunciko ta a duk inda take. Haidar ya ce, “Wallahi ni dai ina zaton tana gidan Inna don mota ta da ta dauko ta taho da ita, na ganta a gidan Innan. Sai dai amma Innan ta kafe ta ce jawahir din ba ta gidanta. Faruk ya ce, Ka ga taso mu kaje kawai mu shammace ta ba tare da munyi sallama ba mu shiga kawai in tana ciki za mu gan ta. Suka mike suka yi gidan Inna Haka suka danna kai falon Inna babu sallam abun mamaki ba jawahir sai Inna da ta yi zumbur za ta tashi ta ce ni har kun tsorata ni lafiya kuka shigo min haka babu sallama? Faruk ya durkusa yana gaishe ta Haidar kuwa zubewa ya yi a kasa yana yi wa Inna magiya inna don Allah don Annabi Inna ki taimaka ki fito min da jawahir. Inna ta ce, Haidar me kake fada ne? Ni na san inda jawahir take ne? Faruk ya ce, “To ai ni abin da ya fi ba ni mamaki ya a ka yi motar ta zo nan gidan, “Inna ta ce, “Ni dai ina zaune aka aiko min da mukullin motar na ajiye na zata ma ko tare suke da Haidar din motar ta lalace musu suka ajiye ta, su je su dawo. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta ce ga mukullin motarka nan kada ku sake zuwar min idan ba jikata kuka gano min ba. Haidar cikin marairaita kamar zai yi kuka ya ce, “To yanzu Inna ya za a yi da neman jawahir din.? Cikin fada ta ce, To ya za a yi kuwa? Da ka rike ta hannu bibbiyu ai da haka ba ta faru ba ko? Yanxu da ka yi sakaci da ita ta bata ai ko wa sai ya huta. A dauki yarinyar nan cikin girma da mutunci ‘yar uwarka ta jini a baka amma ka rinka wulakanta ta. Ya yi saurin cewa, “Wallahi Inna ba wulakantata nake ba wai don kawai na ce, zan kara aure shi ne ta yi tafiyarta. Inna ta ce, “Uhm ai ka ga yanzu ta bar maka filin gidanka ka fi sakewa kai da Amaryar taka sai ka je kai ta yo auren. Faruk ya ce, “Inna hakuri za a yi in dai an san inda take din a fada mana. Ta ce, “To ban sani ba ku tashi ku ba ni waje. **** ****** ****** Maganar jawahir kuwa tana gidan Ankul dinta ta dage da karatu don makaranta biyu zan ce take yi. Tana zuwa jami’a yayin da kuma Ankul dinta ya daukar mata lakcara guda yake dada tunasar da ita da nusar da ita halayyar dan Adam, yanda ake iya zama da su sannan yana koya mata dabaru na iya kasuwanci da yanda za ka sarrafa kudi duk kankantarsu don juya su. Ta bangaren jawahir kam ma iya cewa Alhamdullihi, don komai a ka gaya mata ya zauna a kwalkwalwarta kenan da yake yarinya ce me kaifin basira da kokari. Jawahir ta gama nazarin abun da aka yi musu lakca a yau ta mike a gajiye ta shiga toilet ta yi wanka ta gama shirinta ta fito falo ta samu Auntynta a zaune. Maryam ta kalle ta tayi murmushi, “Tubar kallah ‘yar gidan Ankul ba dai kyau ba, zo ki zauna na dora miki inda muka tsaya don so nake yi ki mallake Haidar tsab yanda ya raina ki yake kiranki da tatsitsiya ko kwaila to yanzu ki zame masa dan hakin da ka raina. Yanzu abin da zan fara miki da shi shine zan koya miki kissoshi kala-kala don haka dauko littafi da biro ki rubuta komai don gudun mantawa. (Saboda haka idan kuna so nima na fada muku to kowa ya/ ta dauko biron shi/ta domin nima saida na rubuta sannan na iya kawo muku badon haka ba……..hmmm. Gani nan ina zagayawa fa. Hhhhh su o’o akwai akwai tsoro ji harda rawar jiki kar na ganta ba paper). Jawahir ta mike ta dawo da littafi da biro, “To yanzu za mu fara da kissar tsafta don ita ce kan gaba a kan komai. Ki kasance mai tsaftar gidanki ko da yaushe cikinsa da wajensa. Kicin dinki ya zamo a gyare a share, a goge ki turara masa turarukan wuta me dadin kamshi. Toilet dinki ya zamo kullum cikin gyara idan kika wanke kika goge komau kika cire yana ki masa nasa turaren wutar na musamman ya kasance cikin kamshi wanda mutum ya yi bahaya wannan kamshin zai kashe masa jin warin bahayan nasa, idan ba ki da lokacin yin wanki da kanki to a ajiye almajiri idan sun kai kala biyu zuwa uku ki ba shi ya wanke ya goge miki, idan kin tashi sai ki turare kayan naki da turaren kaya sannan ki jera a kwaba. Sai kuma kwabar ki sa mata turaren kaya don gudun warin ruma da dai sauransu. Ki kasance mai kwasar shimin mijinki, gajeren wandonsa, hankijinsa da dai wani karamin abu da yake amfani da shi ki wanke, ki goge su ki turare su da turaren kaya ki adana masa su. Idan kin shiga wanka ki rinka amfani da daddadan sabulu me kyau da dadin kamshi. Ki rinka cuda hammatarki, kasan nonuwanki, matse-matsin cinyarki, ki rinka wanke gabanki sosai da sabulu me kamshi, duk wani lungu da sako na jikinki ki wanke shi ki gyare shi fes in da ko ina mai gida ya sa kansa zai ji kamshi. Ki kasance ko yaushe cikin gamsasshiyar kwalliya, ki daure da asuba idan kun yi sallah me gidanki zai ja ki ku koma gado ku kwanta, to ki yi kokarin hana kanki bacci. Har sai shi ya yi sai ki janye jikinki a hankali ki tashi ki nufi kicin don hada muku karin kumallo. Kada ki yi masa break kala daya saboda saurin ginsa ki yi masa kalolin break kowanne ki zuba a fulas gudun kada ya huce. Daga nan ki jere su a tebir ki gyara wajan ki da turare ko ina da daddadan kamshi me sanyaya zuciya, sai ki je ki yi wanka ki bata lokaci wajen yin kwalliya wannan fa kwalliyar safe ce ta barka da tashi me gida. Za ki saka les ko atamfa ko shadda ko boyal duk dai wanda ya samu, za ki feshe jikinki da kalolin turaruka masu kyau da dadin kamshi wanda har za a kasa tantance wane irin kamshi kike yi, to sai ki nufi dakin maigida. Ba a tashin miji da hayaniya ko surutu ko ki yi ta jijjiga shi kina kiran wane! ka tashi lokaci ya yi, in kika yi irin haka za ki bata ran maigidanki. Abin da kawai za ki yi shine da kin shiga dakin mijinki kin ga yana bacci ga lokacin tafiya Office ko kasuwa ya kusa, to sai ki zauna a gefen gadon ki sa hannuwanki kina shafar fuskarsa kisa bakinki kina hura kunnunsa a hankali kina shafa fuskarsa tare da dan jan karan hancinsa. Ko ki fara shafar kasan mararsa kadan-kadan. To za ki ga ya tashi a nitse ba tare da magagi ko tsaki ba, da ya mike ya shiga toilet ko kafin ya fito sai ki yi saurin gyara gadon ki debo masa kayan da zai sa hade da best da gajeran wando da dan hankici duk kuma ki feshe su da turaruka masu dadin kamshi ki debomasa takalmansa ki goge su fes, da ya fito daga toilet ki yi gaggawar daukan tawul ki rinka tsane masa ruwan jikinsa sannan ki debo mayukan da yake amfani dasu ki rinka shafa masa a hankali kina yi kina ba shi labari na ban dariya a hirar nishadi. Ki taimaka masa wajen sa kayan nasa, ki sa karamin kum ki taje masa sumar kansa, ki dada dauko turaruka ki kuma feshe shi da su, ki sa masa gilas idan yana da ra’ayi. Ki riko hannunsa ku taho zuwa kan tebir kuna tafe a hankali kina yi masa rausaya tare da yawan shigewa jikinsa har ku iso tebir din. Ki rinka zuba masa komai kina turo masa gabansa kada ki damu da sai kin ci a lokacin, ki rinka hada masa abinci me yawa a gabansa ki rinka tura masa kina yi masa shagwabar bai ci da yawa ba, ko ki ce ke ba ki yarda ba sai ya cinye da sauran abubuwan da za su ja hankalinsa ya saki jikinsa sosai ya ci abinci ya koshi. Idan ya mike don ya tafi office ki roko masa jakarsa kina yi masa ‘yar shagwabar Honey da ka tashi daga office ka yo gida kada ka tsaya wani wajen ka ji. Honey idan ka isa office ka tsaida hankalinka ka yi aikinka a nitse kada ka yi tunanin komai bare ya sa min kai a damuwa. Za ki ga ya rungumoki tare da shi miki albarka duk kuma inda yake hankalinsa yana kanki Allah Allah zai yi ya dawo gida don ya tara
r da ke. To da ya tafi office ke kuma a wannan lokacin za ki samu ki yi baccinki kafin lokacin girkin rana ki kula me mijinki ya fi so, me ya fi sha awar ci don ki kiyaye wajen girka masa su, shinkafa da miya, ko tuwon shinkafa da miyar taushe, ko danyar kubewa, ko miyar agushi, ko miyar wake da ganye, ko tuwon dawa, ko na masara, tuwon semovita ko ki daka masa sakwara, ko ki dafa kuskus ko taliya, zaki hada masa da soyayyen naman kaji ko gasasshen naman kasuwa ko farfesun kayan ciki, ko farfesun kan rago ko na jelar sa ko farfesun naman karamar dabba, ( A nan ana magana ne idan mijinki mai hali ne, idan kuwa ba mai hali ba ne sai ki yi masa abin da kika tabbatar yana jin dadinsa dai-dai rufin asiri) To idan kika duba abin da ya fi so a cikin yi masa kika gama komai kafin ya dawo, ki dada gyara gidanki ki turare shi da nau’in kamshi kala kala, ki shiga aiki sake fesa wanka sai ki yi kwalliya ki hade da siket ko riga da wando ko doguwar riga ko dinkakken shadda, ko atamfa, boyal, yadi, material, da dai sauransu, to ya kasance karamin dinki ne dai-dai jikinki ki saka wanda da zarar maigida ya dawo za ki tafi cikin salon murna ki ringume shi kina me yi masa barka da zuwa. Ki fara raka shi dakinsa ki cire masa kayan jikinsa ki hada masa ruwan wanka da turaren wanka a ciki da ya shige tolet sai ki kwashe kayan da ya cire ki rataye masa a anga. Ki fito masa da kanana na shan iska. Da ya gama shirnsa ya fito sai ki zo a nitse cikin dabara ki rinka loda masa abinci yana ci kina fara loda masa wani yanda zai ci ba tare da ya gane ya ci da yawa ba. Kina zuba masa sanyayyen abin sha yana ci yana sha, har sai ya koshi ya yi kat sai ki jawo shi ku baje kan kafet ko kujera kuna wasanni da hirarraki masu dadi ko kallo ku, ki rinka karanta masa labarai masu dadi, amma ki kasance ko yaushe kina manne a jikinsa ki rinka yi masa shagwaba kina mai da kanki karamar yarinya a gabansa kina zama doluwa marar wayo ki rinka sa yin dan sokoncin zai rinka sa mijinki dariya, to yawaita masa irin wannan abubuwan shi zai kara muku shakuwa da fahimtar junanku, za ku kasance cikin bege da son junaku ko da yaushe. Idan kin tabbatar kin wa mijinki lodi da abincin rana to yunwa ba za ta gallabe shi da dare ba, don ba a so da daddare a ci abu me nauyi an fi so a ci irinsu hadin salak, sharfar taliya me romo gasasshen nama, ko hanta ko zaka, farfesun kayan ciki ko na naman romon kai, ko na jelar sa ko naman karamar dabva, kai da dai duk abin da Allah ya hore muku marar nauyi. To kinga wadannan duk inya ci va za su yi masa bauyi a ciki ba bare su hana shi su kuni su takura shi wajen aiwatar sa sunnah Jan hankalinsa ta suffofin kwanciya kala-kala. Duk abin da kika kula ya fi so to ki lakanci abun duk sanda kuke tare ki rinka kirkiro wasu abubuwan ma da bai san da su ba. Ki saki jikinki da shi ki cire kunya ki rinka sarrafa shi kina dan kukan kissa tare da kiran sunansa a hankali kina hadawa da kalaman soyayya don tafiyar da imaninsa. Ki kasance cikin yawan shan kunun aya, shan zuma, shan rake, lemon zaki, kankana, gwanda, abarba, nono, dabino, cukwi, tufa, inibi, kin ga wadannan ki kasance cikin yawaita cin su ko da yaushe don suna karawa mace ni’ima da amfani sosai a jikinta. Ki nemi garin bagaruwa gwangwani daya, garin kurna gwangwani uku, garin habbatus sauda rabin gwangwani, garin dakakken dabino ki rinka samun busasshiyar aya ki daka sai ki hada su waje guda ki samu lafiyayyen nonon shanu marar tsaki kina diban wadannan kayayyakin da kika hada kina damawa da nonon kina sha, to wannan shi ne sirrin yanda kika ga nonuwanka sun cuccuko sun yi manya suna tsaye ba su da alamar rankwafawa. Jawahir ta ce, “Au Aunty kina nufin garin nan da kike ba ni damamme da madarar shanu yana da nasaba da cikuwar nonuwana?” Aunty ta ce, “Kwarai kuwa shi ya sa kika ga ina yawan gasa mana naman karamar dabba ruwa ruwa da kuma romon kai da farfesun wannan sirrika ne na mata. Duk abubuwan da na lissafo a baya su suke bamu ni’ima a jikinmu mu mata suna sa ihu kyan fata, yawan, amfani da man zaitun da habbatus sauda suna sa fata ta yi mul-mul da santsi kamar ta jariri.” Jawahir ta ce, “To Aunty ni da ba a gidan miji nake ba amma kike ta dirka min magunguna da tsumi ina sha. Kuma kullum sai kin sa ni na yi turare na tsugunno da na jiki, meye fa’idar hakan.? Ta dafa kafadarta daya ta ce, “Diyata ke nan, ai duk wannan shiri nake yi miki nake tsumaki don duk sanda Haidar ya kusance ki to haihaita haihaita sunyi sallama da kowacce irin mace don ba me iya gamsar da shi sai ke, na gaya miki Haidar sai ya dawo tafin hannunki, sai yanda kika juya shi. Jawahir ta fada cinyarta tana kyalkyala dariya, “Na gode Aunty sai ya san wadda yake cewa kwaila ko tatsitsiya.”19/20