SAMAREEN BANA CHAPTER A
*Sabon salo. Hak’ik’a nasan bayanin daxanyi da yawan mutanan da suka sanni xasu fad’i hakan. Ban damu ba dan nad’auki abinda ya dace ne.*
*Ban lamunta ba. Ban yarda ba. Ban Amince ba. Kuma nasaka goka akan ban yarjema kowacce budurwa data karanta novel d’ina ba. Littafina ayanxu xanciga da rubuta shine ga matan Aure. Su kad’al nayarjema suci gaba da karanta littattafaina. Ba ‘yan mata da samari ba. Idan kuka karanta har kukaji wani filing ku kuka sani da. Na garga’deku akan karku karanta*
*idan kinsan ke budurwace. Toh karki karanta novel nawa. Dan ba danke nayi ba*
*Nayi naxari kuma na yarda da gaske dole muyi gyara mu MARUBUTA. Idan kinsan xakiyi gyara arayuwar littafinki na salo dan qarawa mata wayewa wajan fannin auratayya. Toh kifa’da kikuma bari suji su gani dan matan aure kikayi hakan. Baki amince budurwa ko saurayi wanda bayyi aure ba su karanta littafin naki ba.*
*Toh🤔*
*Ni dai na gyara kuma inaso kema Ki gyara.*
*Wallahi ban Amince Budurwa ki karanta littafina ba. Haka kuma ban Amince Saurayi Wanda bayyi aure ba ya karanta littafina bah*
*haka kuma ko kai baxawarine ban yarje maka ba.*
*Haka kazalika koke baxawarace ban amince Ki karanta min ba*
*Allah kanaji kuma kana gani na gargad’esu kuma na fad’a musu dan matan Aure xanci gaba da rubuta littattafaina. Allah karka hukunta ni akan abinda bani da sani akan hakan. Allah kabani damar rubuta abinda ya dace. Allah idan taurin kansu da gaddamarsu tasasu karantawa. Allah karka hukuntani dan Sanda na gargad’esu akan kada su karanta*
*kuskuran dana aikata abaya Allah Kayafemin Amiin. Haka kuma wa’yanda kukejin wani filing wani abu a littattafaina pls kuyafemin nagode*
*Dan matan Aure nace ayanxu xan dinga rubuta littafina*😳
*wallahi ban yanda budurwa ko baxawara ko saurayin da baiyi aure Ba. Ko baxawarin da yarasa matarsa suci gaba da karanta littattafaina ba*.
*Alhamdulillah Masha-Allah.😂😂😂 sai akiyaye*😀
Samareen banah
Yarage daga shi sai ita agun. dan haka yaje gareta ahankali yana cewa Aunty kiyi hakuri da lefina
Afusace tajuyo rannan amugun 6ace tagalla masa wata muguwar hararar data qara mata kyau tanunashi da yatsa Tana cewa karka nemi ka rainamin hankali….
Kasan bala’in dana shiga.
Kasan asarar hawayan da nayi
Kasan ciwan daka sakamin
Na tabbatar da kaga fita daga hayyacin da nayi asanadinka dabaka fara bani hakuri ba
Gayamin……
me kasha Wanda yaja maka wannan baccin daya kusa sani na rasa numfashina….
Xuba mata ido RAMADAN yayi ganin irin ramar da tayi wai akwana hu’du kacal bala’i😳
Ganin yayi mata shuru ya xuba mata ido shiyasa haushi ya kamata ta’daga hannu ta tsinkeshi da wani lafiyayyan mari wanda yayi dai dai da sakin kukanta
Tace ka… Ka… Ka… Gayamin me kasha Wanda yasa ya hana xuciyata kwanciyar hankali. Yaso sata bugawa.
Kafi kowa sani. Na shaqu dakai fiye da komai arayuwata
Kafi kowa sanin ka6ata xuciyata dasan ganinka.kusa dani cikin k’oshin lapia….
Ka gayamin abinda kasha dan in nisantaka dashi
Bana San nayi rashinka kusa dani
RAMADAN dake dafe kuncinsa Cikin matuqar damuwa murya asanyaye. yace bansha komai ba Auntyna….
Dafe kanta tayi tana tunanin yaushe RAMADAN yafara mata qarya
Ko wane d’an iskan ne ya bashi abinda yasha yayi wannan mahaukacin baccin oho…. Amma wallahi saiya gaya mata
Dan haka afusace ta kallesa Tace kasan baxan yarda dakai bah
Baka ta6a yimin qaryaba
Karka fara daga yau
Pls ka gayamin me kasha wlhi nisantaka xanyi dashi dan illane ga rayuwata
Cikin wani hali yace wlhi Auntyna bansha komai bah…..
Yanda yayi maganar cikin sanyin rai da sarewa ga alamar so yake yayi mata shagwa6ar tasa
Hakanne yasata shiga tunanin anya kuwa yasha wani abu. Qila fa Gaskiya yake fa’da mata
Dan haka tayi shuru tana kallansa daga sama har qasa ganin yanda har yanxu hannunsa dafe yake da kuncin nasa shiyasata kawar da fuskarta
Yafi kowa sanin abarsa dan haka ya matso kusa da ita ka’dan yace 1 luv u my Aunty
Qara kawar da fuskarta tayi
Yaqara matsawa cikin shagwa6a yace Aunty xanyi kuka inhar baki saki ranki ba…..
Kallansa tayi cikin so da qauna “Tace kaji dani RAMADAN karka qara bari wannan mahaukacin baccin ya qara cin galaba akanka
Murmushi yayi kad’an ” Yace insha Allah Auntyna hakan baxata qara faruwa ba.
Murmushi tayi dakai hannunta ga kumatun nasa “Tace kayi hakuri kaji
Kawar da fuskarsa yayi Yace gaskiya saina rama aunty
Murmushi taqarayi tajuyo da fuskarsa gareta Tace na yarda qanina karama fiye da yanda nayi maka
Murmushi yayi kad’an da cewa hmm “xanfi kowa jin ciwo araina idan hannun wani yayi gangancun ta6amin lafiyarki.
Gayamin Aunty. “mai zaisa nikuma nayi da kaina…..
Wannan karan dariya tayi tawucceshi dan barin harabar gidan tana cewa ka iya tsarani. Shiyasa kake 6ata tunanin yara ‘yan matanka
Pls kakulamin da kanka sosai
Zanso kaci abin kafin karama sallolinka dan xakafi jin da’din yinsu….
Girgixa kai yayi dayin hanyar falon Dadynsa yana bata amsa da cewa “banxan iyaba Auntyna dan hankalina atashe yake idan natuna nauyin dake kaina. Zanso in gabatar da sallar kafin inci abincin nasan xakifi samuna yanda kikeso cikin nutsowata…..
Qarashen zancan nasa yayi dai dai da sanda tabud’e get d’in fitan. Jin abinda Yace yasata juyowa suka ha’da ido “Tace toh nasan xaka ibi awanni dan haka xanyi amfani da wannan damar wajan yimaka sakwara da miyar ganye had’i da lemun gwaiba.
Murmushi yayi Yace yayi sosai auntyna
Allah yabarni dake….
Tace kamar yanda nake fata
Gyad’a mata kai yayi. cike da tabbatarwa.
Maurmushi sukayi atare kana taficce shima yashige
Wanka yayi sosai dan kunsan RAMADAN ba baya ba wajan tsaftace kai
Haka ya d’auro alwalarsa yaxo ya fara bada farillarsa…..
Ya ‘dauki awanni yana rama sallolin kafin ya idar
Yana me hamdala ga Allah daya bashi damar ramawa
Sosai yake San yaga sakwarar agabansa dan yasan tunda Auntyn tasa tafurta xatamai bako makawa xata shiryamai yanda xai gamsar dashi
Dady da momy sun sashi agaba kan ya gayamai me yasha haka
Ya tabbatar musu da cewa baisha komai dan harda rantse musu sanda yayi….
SAILUBAH Abbanta sai tsokanarta yake shi da kaka. “Fad’i suke RAMADAN yatashi yanxu hankalinta ya kwanta
Murmushi taketayi musu tana aikinta
Can data gama takaima Abban nata nasa Tace wlhi Abba ina San RAMADAN. Ni kaina bansan da hakan ba. Bansan shaquwarmu takai haka ba. Sanda ya kwanta baccinnan. Gani nakeyi kamar baxai tashi ba. Murmushi yayi Yace toh gashi Allah yayi ikwansa akansa ya tasheshi…..
Kakah ta gyad’a kai “Tace aikuwa ni tashi kibani tawa sakwarar yawona na tsinkewa
Turo baki SAILUBAH tayi Tace imma xaki had’iye yawonki Ki ha’diye dan banyi dake ba. Ga Umma can tana muku naku abincin.
Kallan hanyar kitchen d’in kakah tayi Tace kin isa. Kiyi komai akan idona sannan kice baxaki sammin ba. Dan kinga kinba ubanki ko
Dariya SAILUBAH tayi mata yayinda Abbanta Yace “yaleta innah ga nawa kici kinsan baxan iya ciba ke kina so bah.
Tashi SAILUBAH tayi tana turo baki Tace Allah tsohowarnan kinfiya kwad’ayi. Dama hirar da kikemin danake aikin dan in sammiki ne.
Idan kuma na hanaki Abbana ya ‘dauki nasa yabaki
Harararta kakah tayi tajawo fulas d’in da Abban nata ya turo mata Tace eh. Kingani ai da idanki. shi da kika ba yaban….
Ai da sauri taje ta kar6e tana cewa toh bara nakawo miki naki kiyi hakuri. Abba ga kayanka
Kwafah kakah tayi batare datace komai ba.
SAILUBAH ta ficce daga falan tana dariya.
Bayan takawo mata bayan. wanka tashiga bayan tafitoh tagyara kanta da wasu shegun kaya Wanda sukayi anko ita XEE
Riga da siket ne ‘yan kanti jajaye sun amshi jikinta dakyau sosai. Saita yane kanta da gyalan kayan
Nanta fitoh abalarabiya sak
Gaskiya SAILUBAH nada kyau sosai
Feshe jikinta tayi da turare element galaxy BlackBerry sai qamshin suka had’u suka bada wani narkaken qamshi me tafiya da xuciyar masoya.
Khairat takira a waya taxo takwashe girkin datama qanin nata takaimai gida
Sanda tagama jeramai mai komai “tace Yah RAMADAN tace kafara ci kafin taxo. “Toh Yace mata. Sannan taficce
Kallan komai yayi gwanin ban sha’awa yayi murmushi. Gaskiya yana San Auntynsa SAILUBAH xaiji da’din mu’amalat da ita
Toh tayaya kuma yanxu xai 6ullo mata har yasamu yanda yakeso
Yaga dai qoqarinsa sosai amafarkin shi da Junior. Dan komai xuwamai yayi asauqaqe. Yanxu gashi a duniyarsa ta ainihi……….
Tsaki yajah dan gaskiya Junior yayi wasa da tunaninsa ya 6ata masa tunanin… Xaiyi qoqari yaga ya gyara tunanin nasa……..
“Toh gyara na baka…. Momy ta katse mishi tunani da fad’in hakan.
Murmushi yayi tare da shafa fuskarta Yace Ki huta momyna. Auntyna nake jira
Gyad’a kai tayi dan tasan dama xaman jiran da yake…. SAILUBAH ce tashigo da sallama tana me ciga da cewa “hmmm ya xauna xaman jirana ko momy. Ai dama nasani. Tafad’a da xama kusa dashi sannan babu 6ata lokaci tafara xuba masa.
Murmushi momy tayi tace toh nikam wannan shaquwa taku idan ranar rabuwa taxo ya xakuyi……
Da sauri suka kalleta. Lokaci d’aya kuma suka kalli junansu.
Momy taciga da cewa kinga ke SAILUBAH Aure xakiyi kobajima kobadad’e. Kaga ko Dole RAMADAN kasa wannan aranka xuwan ranar da SAILUBAH xata barka…..
Da sauri Yace bana fatan xuwan wannan ranar momy.. pls kimin kyakkyawan fata nagari akanta
Murmushi irin nasu na manya momy tayi “kullun acikin yimaka kyakkyawan fata nake. Saidai ina so Kadena takura mata kan samarinta
Kabarta tayi aure dan kasan darajarta shine d’akin mijinta
Jan numfashi RAMADAN yayi Yace yanxu kuma me nayi momy. Kina fah kallo bacci na sharara na tsawun kwana hud’u. Kinga ko banda sanin meya hana yuhuwar auranta da Alhj Aminu ba.
“Hmm aiba maganar wannan auran nata nake maka yanxu ba. Ina maka magane akan abubuwan da kake mata daxaran samari sunxo gareta…….
Murmushi SAILUBAH tayi “tace Sam baya kyautatamin akan hakan momy na sani sarai. Saidai bansan manufarsa ta’ainihi akan hakan ba
Yana fakewa da cewa har yanxu bana samun wanda ya dace dani. Hak’ik’a momy. RAMADAN yarigada ya xama wani 6angare najikina. Shiyasa duk abinda yake min bani kallansa. kuma koda na kallesa lokaci kad’an ne nake sakewa.
Pls karki takura masa kinga daga rashin lafiya ya tashi. Inaso yaci abinci cikin warwala😒…..
Murmushi momy taqara yi cike dajin tausayinta xuciyarta na qara santa “Tace na fuskanci RAMADAN ya gama dake. Yaro qarami yasameki yanda yake so. Ya cakud’a miki tarbiya da tunaninsa irin na yara irinshi na SAMAREEN BANAH. Idan bacci kike SAILUBAH Ki farka. RAMADAN shegen wayo ne yayi mishi yawa da shegen kishi ne yake damunsa…..
Da sauriSAILUBAH ta kalleta ka’dan da cewa kishi kuma momy
Ta6e baki momyn tayi. “tace eh haka nace….
Murmushi SAILUBAH tayi tana me kallan RAMADAN “tace wai haka. Me momy take nufi ne da wannan kalmar….
Cikin d’an nuna alamun rikicewa dan ya lura yau momy San sakamai gaba da tonamai asiri take shirin yi… Dan haka cikin sauri yanemo abin cewa da…
“Ki lura mana Aunty…
Momy amake take yau.
Kinga ban fahimci me take nufi ba. pls bani inci karyayi sanyi
Murmushi tayi tace toh momy kinga shima bai gane me kike nufi da kalmar kishi ba. Dan haka kibarmu yanda kika ganmu😌..
Tashi momy tayi “tace aishikenan. Xaki sani Idan ya gama tsofar dake agida haka. Kuma Ina tabbatar miki lokacin da xaki Nemi madafa baxakisan lokacin da zaki ture dukkanin wani abu daya shafeshi gefe d’aya ba. Dan kinemama kanki mafuta.
Da’ace asiri yaran nan yake. dacewa xanyi yagama mallakeki
Murmushi taqara yi “Tace o ni yau naga ikwan Allah wai momy ina ruwanki ne…..
Tafiyarta momy tayi tana qara jin tausayin SAILUBAH
Sam taqi ta fahimci inda RAMADAN yasa gaba
Taqi ta fahimci cewa yana MASEEFAR SONTA
Taqi ta fahimci cewa yagama samunta
Toh. wai har yaushene xata fahimta hakan🤔.
Ita kadai taketa sambatunta a Cikin xuciyarta. Ahaka har ta’isa falanta…
SAILUBAH ko sallan RAMADAN tayi ta galla mishi harara “tace kana tunanin bansan gaskiya momy tafa’damin bah.
Nasan so kake ka tsufar dani agida
Wlhi baka i’sa ba. Danna shirya yin maganinka nan gaba…..
Marairaice mata yayi da cewa nafi kuwa sanin hakan Auntyna. Dan Allah Ki yafemin baxan qara ba.
Tace hmm ai maganar qarawa RAMADAN xaka qara.
Kasani barinka kawai nakeyi. Kifara tunanin ranta natashi futar maka a giya. katabbatar ranar saika raina kanka….
Matsowa yayi kusa da ita cikin shagwa6a “yace toh kiyi shuru mana……
d’an gayamin Auntyna. meya hana auranki da Alhj Aminu…
Jimm tayi kad’an kana “tace hmmm wallahi (wlhi) nima bansani ba.
Nasan dai naje na roqi Abbana akan yayi hakuri karya Aura min shi. Saiyace dani inje xaiyi tunani…
Kawai saiji nayi lokacin ‘daurin auran yayi wani me xaqin murya ya fara shelar cewa wai Allah yayima Alhj Aminun rasuwa a lallashi amarya dan har ankaishi gidansa na gaskiya
Duk da gabana ya fa’da Amma nayi murna sosai da mutuwar tasa
Dan kasan dama kagama 6atamin tunanina a washe garin ranar.
Murmushi RAMADAN yayi Yace daga kuma nan sai me. “Tace sai kuma FAWAS da KHAMIS sukaxo da batun wai anyi anyi katashi kaqi tashi
Dama ni naita kiran num naka naga kaqi ka’dauka. Ashe kana nan kana baccin da har yanxu ban gamsu da hujjar da kabani akansa ba.
Kama hannunta yayi Yace wlhi Auntyna Ki yarda dani. Ba abinda nasha😒 wlhi
Kallansa tayi da kyau kana tace “toh naji sakarmin hannu inyi abinda ya dace. Murmushi yayi dayi mata yanda tace sannan tafara xuba mishi sanyayyar lemun gwaiban nan shi kuma yana cin sakwarar cikin nutsuwa yana me godema Allah daya barshi da ita.
Sanda ya gama. Sannan tace toh yanxu hankalina ya kwanta xanje gun XEE dan akwai wani banxan kamu da Surayya tayi. Da alama mutumin yana da kud’i sosai. Ina maka girki ne d’axo XEE take gayamin. Wannan karan alhajin nata ne. Kasan tare muke komai. Kayi hakuri karkace na tsallakeka kaji d’an qanina😀 taqashe da dariya tana shafa kansa dan ganin yanda ya kalleta da tashin hankali….
Jan numfashi yayi ya lumshe idansa xuciyarsa na bugawa. Ya shiga tunanin yaushe Surayya tadawo. Dahar tafara cigaba da d’ora masa Auntis nashi akan Ntwk.
Gaskiya matsala tadawo rayuwarsu. Wlhi daxaiyi ido biyu da Surayya yanxu dasai ya shaqeta har lahira…….
“Kayi shuru dan nata60 maqiyiyarku ko. Toh wlhi xakayi ka gama kaga tafiyata….. SAILUBAH ta fad’i hakan dasan ficcewa daga falan……
Da sauri Yace “pls aunty dan allah karkije.
Juyowa tayi tana harararsa. “Kaima kasan kayi ka’dan. Daban shirya bane. toda najika.
Da kallo ya bita…
Tahad’u iyakar had’uwa. Yana San Auntynsa Allah yasa ya mallaketa.
Wacece Surayya. Surayya wata yarinya ce shed’aniya wacce take janyo hankalin masu ku’din garin nan na kano harda wasu garin ruwan
Qawar SAILUBAH da XEE ce
Tana ha’dasu da alhaxawan dan tasan duk wani d’a. wanda ya amsa sunanshi d’a namiji. bai isa yayima XEE da SAILUBAH kallo d’aya ba.
Hakan ne yasata take ha’dasu dasu
SAILUBAH da XEE dai atakaice Surayya takoya musu damfara😳
Me karatu xakaga yanda suke damfararsu. Kaidai bini ahankali ni Rahamat Nalele
RAMADAN da FAWAS KHAMIS sun tsani Surayya muguwar tsana. Dan sunsan wacce ita. kuma da yanda tajefa su SAILUBAH akan hanya
Ta rabu dasu SAILUBAH ne shekara biyu da suka gabata.
Saboda cigaba da tasamu dan bin wani alhaji da tayi qasar jaman………..
Kammala wannan tunanin na RAMADAN yayi daidai da shigowar FAWAS da KHAMIS…….
Suka tafa FAWAS Yace tunanin me kakeyi ne haka malam me baccin mutuwa😀
“Hmmm kudai kubari. Aha. maseeface ta dawo.
KHAMIS “Yace ban gane ba
“Ina nufin Surayya qawar antyna ce tadawo……
Ihu KHAMIS yasake cikin wani hali Yace yanxu fitan AUNTY LUUVAH da muka gani kana nufin ga Aunty XEE tayi dansu narkar da wani.
FAWAS “Yace kaima kasan hakan take……….
Muje zuwa ma’aurata🤳🏻
[8/30, 8:32 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page* 2
Tsaki yajah Yace “wlhi natsaneta tsana me tsanani
FAWAS yaja numfashi da cewa “Allah da xan ganta dasaina shaqeta shegiya…..
Tsaki KHAMIS ya qara jah da maida hankalinsa ga RAMADAN Yace “ya jiki dama Aunty Rahamat ce nakawo tana San dubaka momy mah na gaisheka. wai sai dare xataxo
Murmushi yayi Yace “ina amsawa ina Aunty Rahaman. “Tana falo cewar FAWAS
Tashi RAMADAN yayi “wlhi yanxu garau nake jina.
momyna mah wai sai gobe zatazo. cewar fawas
“Sannu Aunty Rahamat. “Yauwa sannu RAMADAN ya jikin naka. “Da Sauqi Aunty dan garau nake jina yanxu. “Toh madallah Amma mekasha ne. Murmushi yayi da cewa “wlhi ba abinda nasha bacci dai daga Allah.
“Allahn ya shige mana gaba. Dama yau xan tafi hankali baxai kwanta bane idan na tafi bantabbatar da cewar katashi bah shiyasa nasashi ya kawoni Amma dan ka kula da kanka sosai dan bakaga yanda Auntynka SAILUBAH taficce daga hankalinta ba har XEE. Bana San hakan taqara faruwa. Murmushi ya qarayi Yace “xan kiyaye Aunty insha Allah
Tace “toh madallah. Momy nixan tafi. “Toh Rahama Allah ya saukeku lapia. “Amiien amiin.
“Aunty basai na maidake ba xaki koma ko. Cewar KHAMIS ga. “Ai idan kuka had’u bakusan rabuwa da juna. Sha xamanka xan koma dakaina.
Dariya sukayi gabaki ‘dayansu
Bayan tafiyarta momy tabar gun RAMADAN ya kalli KHAMIS Yace “bana tare da rashin lafiya yanxu dan haka anjima da misalin qarfe gomah mud’an wataya mana
FAWAS Yace “hmmm tunda haka ne gobe saiku rakani QAUYE. Da sauri RAMADAN ya kallesa Yace “gun HAMEEDAH ko. “Eh mana ai kasani tatafi da imani na.
Dariya KHAMIS yayi da dafa kafaɗar Sa Yace ko shakka kam
Babu dan gashi xahiri ya bayyana gareka kamar karufe idanka kakeji kaganka a gabanta
Yace “wlhi kuwa….
RAMADAN Yace da KHAMIS “ina kabaro Aunty XEE.
Lumshe ido yayi Yace wlhi har kasa naji kwad’ayin ganinta yanxu
Shege duk kabi ka furgitamin ita.
Dariya FAWAS yayi da cewa. ” “aika furgita xugatanmu gabaki d’aya pls gayama mah me kashane.
Harararsa yayi Yace me xansha wai. Haka su dady suka sakani agaba wai intemakesu in gaya musu abinda nashi.
KHAMIS Yace “I mana ai maganar gaskiyace dole atambayeka. Kasan tashin hankalin daka jefamu kuwa. Barin Aunty LUUVAH kullun cikin kuka take memah tace ma ne da kuka had’u
Ta6e baki yayi Yace “mari ta sakar min wanda rabona da amin inaga tun ban fara wayo ba.
Yace “aitayima da Sauqi naso yafi haka.
Tsaki yajah Yace “wannan mah ai ba’asan ranta tayimin ba. Kasan baxata iyamin wanda yafi wannan ba.
“Saboda ka6ata mata tunani. Cewar FAWAS
“Eh mana. Dan kunfi kowa sani. RAMADAN ya Bashi amsa
——————
SAILUBAH ko tana zuwa ga XEE. Tasameta akintsanta tagama shirinta tsaf. Mama tace “Wato takoya miki ko SAILUBAH tun baki biyema Zainab da shegen San yawanta wato yanxu tashafah miki kin fara biye mata.
hmm Kaiki xatayi tabaro ki. Na rasa a inda tagado wannan shegen San gantalin. roqo nake Allah ya bata miji me kulle inga tayi.
Haba daga kawai kunga RAMADAN ɗin ya tashi shine har xaku kama gabanku.
Cikin SAILUBAH da XEE bawanda ya biyema faɗan Maman…
haka XEE tafeshe jikinta da turare suka ficce suka barmata gidan. Nan tasake baki😧 tabisu da kallo
Surayya takalli su Sailuba tace “himmm luuvah kenan auntyn Ramadan. Xee budurwar Khamis…..
tsaki SAILUBA taja tace “waike wata irin ‘yar iska ce. idan baki shirya abin faɗa mana ba saimu qara gaba.
murmushi tayi “hmm aina daɗe da shirya abin faɗa. fatana karku yashe su da yawa……..
” Surayya kenan ai tunda sukace iskanci ne agabansu babu tausayi atsakaninmu dasu. kinsan tausayi da imani su suke sawa idan ɓarawo yayma me kaya sata yadawo mishi dashi harma ya bashi hakuri. toh kinga babu wannan a zuciyarmu. dan tunda suka fitoh da maitarsu kuma har muka fahimci manufarsu ba makawa saimun yashe duk wanda yaxo hannummu. pls lokaci na qurewa idan kinga xaki iya gaya mana shirin… gaya mana idanko iskanci kikeji toh xamu baki waje yanxunnan dan muna da abinyi. XEE ce me wannan maganar…….
Tashi SAILUBA tayi ta maida gilashin dake fuskarta takalli XEE. “tashi muje kawai. da alama basu cika mata ajjihu bane shiyasa take rowar faɗin abinda ya dace
tashi XEE ɗin tayi tace “ba mamaki kam
Surayya na kallansu suka ficce daga gidan nata tayi dariya da cewa aranta shegu nasan xaku iya ɓullewa kodako ba’a nuna muku hanya ba.
Shahararran hotel ne wanda kallo ‘daya xaka masa kasan sai wane da wane ne suke zuwa wajan
nan SAILUBA DA XEE suka shiga anan SAILUBA tafaka motar da alhaji AMINU ya siya mata lokacin bikinta.
babu ɓata lokaci XEE takira wata number tana me cewa “mun iso ciki fah. ok. saita kashe wayan
Basu ‘dauki wani lokaci ba wani Alhaji yafito daga cikin hotel ɗin ya nufusu bakinsa yaqi rufuwa dan farin cikin ganinsu yace “sannunku kufitoh mana…..
tare suka jera kafaɗu har yakaisu masaukinsa suka shiga
bashi kaɗai bane su biyu shi da abokinsa. dukkaninsu kallo ɗaya xaka musu kasan manyan mutane ne.
Wanda ya kawosune yace “sunana alhaji iliasu abokina kuma Hameesu. da fatan Surayya tabaku labarina. dan tare muka fitta da ita har gashi ALLAH yayi mana dawowa.
SAILUBA tayi murmushi tace ba shakka munji komai daga gareta saidai bansan ko kaji namu labarin daga gareta bah……..
Da’alama kece SAILUBA ko. abokin nasa ya katse SAILUBA da faɗin hakan.
eh…..
“wow amma kun haɗu sosai. munsan da hakan. xee takatse shi da fa’din hakan
“Gaskiya bata bani labarin komai akanku ba. saidai tace inyi hankali daku. murmushi XEE tayi tace “hmm tagaya maka gaskiya amma kai kalura da wani abu atare damu
“kokaɗan. yabata amsa. “hmm yayi dai. ta mayar mai…..
Hameesu shike san wuɗa dake SAILUBAH. ni kuma ni kuma xan taɓa XEE
” Yayi. SAILUBAH Tabashi amsa
nan XEE suka shige wani ɗaki ita da alhaji iliyasu suka bar SAILUBAH da Hameesu nan
“Gaskiya kin haɗu…
“Nagode da yabawa
“fatan da kika fito ba wanda ya kallemin ke
“kamar na sani na takura kaina wajan Ɗɗauke kai ga kowa har sanda naxo gareka.
“hmm kin taɓa yin soyayyah
“bayan mahaifina babu san wani ɗa namiji acikin xuciya bayan qanina RAMADAN.
“Nasamu labarin idan aka taɓa miki shi kina iya saɓawa da kowa
“eh kamar yanda shima bayasan ɓacin raina. bayasan damuwata. makar banyi lefiba idan na saɓa dakowa akansa
“kina da wayo amma kamar yafiki.
” koxan iya sanin dalilin da yasa kaɗauko min hirarsa
“eh mexai hana
“ai ina sauraranka
“hmmm sonake in rabaki dashi. cikin sauri ta kallesa
“eh inasan rabiki dashi wani abune kikayi saurin kallona
“aa kawai dai nafara jin tsanarka ne. ya shiga raina. nagaya maka kaf duniya bayan mahaifina babu wanda nake raina sai RAMADAN. xaka tabka baban kuskure idan kayi gangancin rabani dashi.
murmushi yace ” xakiyi aure.
“idan da raina ai kasan ba makawa.
“toh kinga aure ya rabaku kenan
“hmmm aiko auran xanyi shixai xaɓamin mijin daya dace dani wanda baxaiyi gangamcin shiga tsakanina dashi ba.
“bashakka ko idan hakanne xaki aureshi.
“idan kashirya faɗar abinda ke ranka ina da lokacin sauraranka yanxu
“auranki nake san nayi amma bayan nasameki yanda nakeso
“kanasan aikata xina dani ne yanxu bayan hakan saika aureni
“eh hakan nake nufi
murmushi SAILUBAH tayi tace “wato har yanxu konanan yanda kuke
“wani abune. naga yau kika fara sani na. amma kina magana kamar damacan kimsanni.
“aa ban sanka ba. kawaidai nayi tunanine har yanxu ashe akwai masu wayo irinka.
“dariya yayi wannan karan yace “bani da wayo idan har na shigo hannun mace irinki
“karka fawa wani alaye kawai kafa’damin waya baka labarin qanina RAMADAN
“Surayya ce take ban labarinki shine tace kina da wani qani kina maseefar sanshi sanna yana da abokanaye biyu fawas da khamis saidai sun tsaneta over
“haka ne.
“toh yanxu tunda na gaya miki saiki tashi muje ciki
“zansha drink.
sannan ina so kaje kayi futsari dan karka ɓatani
“dariya yayi yatashi ya ɗauko mata drink ɗin sannan ya shige toilet. daidai nan XEE tafito tana murmushi tace “yadai ina mutumin naki.
murmushi SAILUBA tayi bayan taxuge jakarta ta ɗauko wani garin magani taxuba kaɗan a cikin kofi sannan tamaidashi jakarta tatsiyayi drink ɗin a kofin tasa agefe sannan takalli XEE Tace “kin gama dashi ne tace eh bara injiraki kaɗan. tafaɗa tana me shegewa ɗakin data fito…… dai dai hameesun ya fitto daga toilet ɗin yana washe baki. yace “toh mushiga ko.
Murmushi SAILUBAH tayi tace “kasha wannan sannan kabani dubu ɗari Biyar kuɗin biyana kafin komai ya wakana.
“haba SAILUBAH saikace xan gudo bayan yanxu nagama cemiki xan aureki.
ɗaure fuska tayi tare da kawar da fuskarta daga kallansa tace “haka tsarina yake Alhaji Hameesu. baxan fara canjashi ba daga kanka. kafin komai ya wakana ake biyana
murmushi yayi kana yajawo wata jaka yabuɗe…… kuɗine maqil acikinta. yaciro bandir ɗin dubu dubu guda biyu ya miqa mata yana cewa “na ninka miki.
murmushi tayi tace “ka kyauta mah kanka. takarɓa tasa ajaka. shikuma ya rufe jakar yana cewa “bangane wanna maganar taki ba
“xaka gane karka damu.
mayar da jakar yayi wajan xamanta sannan ya ɗauki drink ɗinnan ya shanye tsaf sannan SAILUBA tatashi tashige gaba yana binta a baya har sanda suka isa bed ɗin ya xube agadan idansa na juyawa bai ɗau lokaci ba bacci me nauyi yayi awan gaba dashi
murmushi tayi tace “dana so. kasheka xanyi. dan kun fitini al’uma kun damesu da yawan aikata xina. kuna ɓatama mutane tarbiya. na tabbatar anan gaba xakuyi gamo da wacce xata dinga kashe ire iranku har lahira…..
bata manta numbobin daya danna acikin jakar kuɗin da ya buɗe ya bata ba.
dan haka tashiga ɗakin da XEE take…… nan taganta tana chating a wayarta. gefe guda kuma ga Alhaji Iliyasu yana kwance yanata sharara bacci.
SAILUBAH tayi murmushi tace “hmmm lalle aiki yayi kyau. da fatan ya biyaki kafin kika narkar dashi.
“Eh mana. saidai yana da wayo bai bari nasan numbobin nasa ba
murmushi SAILUBAH tadaɗa yi tace “Nikam yayi sake……..
basu ɗauki lokaci bah. suka daɗa gyara kansu sannan SAILUBAH tadaddanna numbobin nan da taga ya danna ɗaxo suka ibi kuɗi san ransu. sannan suka rufe da jamu qofa….😆
kai tsaye gidan marayu suka nufah. me karatu idan baka manta ba kunsan SAILUBA da tausayi da san tayi temako aduk inda take. tana san badawa… dan haka bada kuɗi sukayi sosai ga gidan marayun.
sannan kuma sukaje ga almajirai nan ma suka basu
sannan sukaje spmkt sukayi siyayya san ransu da dubu hamsin kawai suka dawo gida
nan suka raba dubu ashirin da biyar biyar lokacin qarfe takwas ne na dare
Saɗaf saɗaf XEE tashige ɗakinta bata bari tayi ido biyu da mamanta ba.
sanda tayi wanka ne taji maman nata nacewa babanta haryanxu zainab bata dawo ba. shine tayi saurin fitowa tace aitafi awa uku da dawowa.
da mamaki mama takalleta can tace “kice kuna fita kenan kika dawo bansani ba.
eh XEE tace mata da saurin komawa ɗakinta
SAILUBAH KO da RAMADAN taci karo abakin get ɗinsu bayan taje ta ajiye motarta agidansu RAMADAN ɗin.
yayi kyau sosai cikin qananun kaya dai dai mallakar mace ‘yar shekara goma sha takwas…….
“Daga ina kike Aunty….
“Daga inda ka aikeni
harara ya sakar mata. cikin ɓacin rai yace “wallahi saina gayama Abbah gun maxa kukaje ke da Aunty XEE…..
Saurin sakar jakar hannunta SAILUBAH tayi aɗan furgice tace “Abbah ya dawo ne.
“ban sani ba. RAMADAN yabata amsa da faɗin hakan.
marai rai ce mishi tayi da cewa “Haba ɗan QANINA dan Allah karka gaya masa.
harara yadaɗa auna mata yace “wlhi saina gaya masa ince iskanci kuke xuwa keda Aunty XEE😔
saurin waro ido😳 SAILUBAH tayi haɗe da rufe mishi BAKI tasani tunda ya rantse saiya faɗa. mafuta ɗayace da ita shine tasamai kuka idan yaga kukanta xai fasa faɗama Abban dan haka sam bayyi tsammani ba. saiji kawai yayi tarushe mai da kuka…😳
Sake baki😧 yayi yana kallanta har na tsawan wani lokaci sannan yace “toh kiyi shuru baxan faɗa ba amma da sharaɗi baxaki qara xuwa gun wani ba……
Da sauri tace “wlhi na yarda daga skull sai wani abu me mahimmanci
dariya yayi yasan faɗarta ne kawai na wannan lokacin yana da tabbacin gobe mah qarawa xatayi…..
jin hannunta awiyansa yasashi kallanta.
“yajikin naka.
” naji sauqi Auntyna saidai ina san shan wani abu me ɗan sanyi haka ya faɗa ashagwaɓe.
mrmushi tayi tace “bara in haɗama wani drink ko
yace “ok amma yanxu dan idan yaɗau lokaci xaki nemeni ki rasa.
kallansa tayi da damuwa tace “haba RAMADAN daga tashinka har xakuje club.
“Bafa can xamuje ba.
“akwai wanda yasan halinku kamar nice
“kiyi hakuri toh
“hakuri ɗaya xanyi shine kufasa xuwa… da sauri ya kalleta tako gyaɗa mai kai alamar tabbatarwa
“turo baki yayi yace “Gaskiya ina san xuwa Auntyna…
shuru SAILUBAH tayi tana qaremai kallo. sai qamshi yake kamar wani ango sanda tagama kallansa sannan taɗauki kayanta da niyar barin gun dan shigewa falansu.
da sauri ya riqe hannunta tako wurga mishi wata shegiyar harara ba shiri ya saki hannunta. saidai bai daddara ba sanda yasha gabanta ya shagwaɓe mata fuska tamkar xaiyi kuka yace “Dan Allah Aunty kiyi hakuri bana san ɓacin ranki…
kallansa tayi da cewa toh na haquran idan kafasa xuwa…. soso qeya yayi yace “toh nafasa.
murmushi tayi dacewa toh katuro khairat yanxu takarɓarma dan nagaji bacci nakesan yi wlhi…..
wani kallo ya sakar mata na xirgi yana qare mata kallo daga sama har qasa yace “me suka miki Aunty wanda yasa kika gaji 😳
waro ido 😳 SAILUBAH tayi saboda gano manufar tambayar tasa da yayi yanxu. dan haka cikin jin kunya ta hararesa tace “Qaniyarka sukamin. Daga gidan marayu xuwa wajan almajirai. daga nan suka dare dani a suparmarket…… tana faɗin hakan tayi shigewarta ciki.
murmushi😀 RAMADAN yayi da ficcewa daga gidan….
Kakah ce xaune a falan da Abbanta tayi sallamah
Abbah yace daga ina kike
cikin sauri tace Abbah kamanta nace maka xani gidan rasuwar qawar nan tawa wlhi bamu samu dawowaba sai yanxu kuma mun biya jifatu ne shiya dare yayi haka
“ok kikiyaye sosai bana san dawowar dare haka
“insha Allah zan kiyaye Abbah amin afuwa. tana faɗin hakan tayi shigewarta ɗakinta
SAMAREEN BANAN KO sun haɗu su uku reras cikin wannan dare me suke shirin qullawa ne me karatu
” Dabadan dare ba danaje ga HAMEEAH. cewar FAWAS.
“da kamar wiya kabarma gobe kawai. faɗin KHAMIS
RAMADAN yace “muje gun Aymana mana daga nan sai muje ga Meenat. kuma nima xanso inga Haleema………..
furicin nasa ya katsene sakamakwan wasu ‘yan mata da sukaxo wuccewa ta gabansu.
KHAMIS ya kalli agogan hannunsa yace ” bala’i.😳 awannan daran…
RAMADAM yace “amfah sunxo…… musamman waccan ta farkwan. da nuna wata daga cikinsu da ido…….
da qarfi FAWAS yace iya wiya iya wiya…..😀😀😀
jin hakan yasa RAMADAN bin ‘yan matan da murmushin furucin FAWAS
Dafa kafaɗar FAWAS KHAMIS yayi yace da RAMADAN wanda yayi nisa abin ‘yan matan…… ” karka bari kanka ya kulle😀
juyowa RAMADAN yayi ya ɗaga ma KHAMIS hannu alamar sam baxai bari kansa ya kulle akan wa’yan nan qananun ‘yan matan ba.
” ku ɗan jini mana ‘yan mata.
Hmm karkuyi kuskuran jamin aji dan wlhi ni me tsada ne😀…..
gabaki ɗayansu ‘yan matan juyowa sukaji suka kalli RAMADAN dan bayanin da yayi ya isa akallesa tsaf dan a tabbatar da abinda ya faɗa…..
Haɗadɗan yaro ne. san kowa in wanda ya rasa. ya iya wanka ga wani futunannan qamshi da yake fita daga jikinsa. gefe guda ga wasu irinsa su biyu wato FAWAS DA KHAMIS. _wannan bayanin xuciyoyin wa’yannan ‘yan matanne_
da alama kamar na gama ɓata muku xuciyoyinku yanxu ko……
RAMADAN ya katse musu tunani da wannan kalmar
by RAHEEMAT NALELE😂
[8/30, 8:32 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*3
Wata figigiya daga cikin su “tace sabo dame fah
Yace taya za’ayi nasani bayan kince haka
Tace “kana da abin cewa
Yace “da bana dashi aida baxan tsayar daku ba.
Wa’yancan ‘yan uwan nawa ne sukesan magana daku. Ya qarashe furucin da nunasu FAWAS………
KHAMIS naganin ya nunosu Yace da FAWAS “shegen ya jonamu dasu fah😳
FAWAS yayi murmushi. qasa qasa yanda bazasu gane wani abu ba. Yace “hmm aini HAMEEDAH tagama 6ata tunanina dan haka kaji dasu pls.. Ya faɗi hakan dasan barin gun
Ganin hakan yasa KHAMIS saurin riqeshi yana aunawa RAMADAN da ‘yan matan murmushin yaqe tare dajan FAWAS zuwa garesu
RAMADAN naganin hakan yanemi barin gun yana cema su KHAMIS din “ku’ankare da wuri fah dan kyan daga nesa ne idan kuka matso kusa qamshi suke.
Dake sunsan kan yaransu nan take suka gane me RAMADAN yake nufi
Musamman da hancinsu ya jiyo musu wani mahaukacin turare wanda Sam bashi da dadin shaqa
Yarigada ya fece RAMADAN ya barsu dasu…
KHAMIS ya gyara tsayuwa cikin Murmushi Yace dama tambayarku xamuyi
Cikin gajiyawa wata cikinsu taqara cewa “Allah yasa munsani.
“Yauwa zama ku sani. Watace anan unguwar wai Aisha tana da ‘dan tsayi haka. Shine muke so muji ko wata tasanta acikinku
Tace aa muma can qasa muka fitoh gidan yayarmu zamu gida muba ‘yan unguwar bane
“OK mungode cewar FAWAS
Ganin hakan yasa suka juya sukaci gaba da tafiyarsu
KHAMIS yayi murmushi Yace “naxata fa ‘yan hannune. Ashe tsamayene
FAWAS Yace “aitunda kaga ya barmu dasu babanza ba
RAMADAN Yace “bakaji yanda suke wani tsami ba kamar sun sha giya
“Kai turarene qamshin ne dai baixo ba, cewar KHAMIS
FAWAS Yace “shiyasa Aunty LUUVAH da Aunty XEE sukayi arayuwa. Qamshinsu na musamman ne
RAMADAN Yace “kunga na nafara jin bacci kodai xamubar futannan ne yau.
FAWAS Yace “aidama bawai ni na damu bane
KHAMIS Yace “toh waye ya damu. Kasani Aunty XEE ce dai kuma kasan xan jita idan na miqe a gado na…
RAMADAN Yace “toh tunda haka ne pls mubarma gobe komai
FAWAS Yace “da sharadin qarfe 1pm xamu qauyen takai
Murmushi RAMADAN yayi Yace eh mun yarda.
Gida KHAMIS yake qoqarin shiga yana cewa “yau bame saukeni tunda akofar gida nake. Sai Allah ya tashemu
FAWAS Yace “Allan ya tashemu lafiya…..
Motar FAWAS RAMADAN ya shige shima FAWAS din ya shige da tadata
Sanda FAWAS ya sauke RAMADAN agida sannan ya nufi gidansu
Daran ranar kasa bacci RAMADAN yayi. Tsoransa karya kwanta shege Junior🤣 ya qara zuwa ya 6ata masa tunaninsa.
Dan haka ya tashi yadinga kai kusanka gun mahaliccinmu me dukka😭
Lokacin kusan biyu da rabi ne na dare………
Ahankali yajawo wayarsa yakira SAILUBAH
Ita ‘dinma bata da’de da kwantawa ba idanta biyu. dan yancy ta idar da tata sallar.
Tana ganin Kiran nasa tayi saurin dauka tana cewa “QANINA yadai bakayi bacci ba.
Ahankali Yace Auntyna nakasa yi
Jan numfashi SAILUBAH tayi tace “meyasa toh
“Tsoro nakeji Aunty… Karna kwanta wannan baccin ya qara xuwamin
Murmushi tayi Tace “zan shiga tashin hankali QANINA idan ya qara xuwa. pls karka bari hakan taqara faruwa.
Ashagwa6e Yace “ba nine da kaina ba Aunty….
Afusace tace “aina sani… pls kayi xaxxafar addu’a kafin ka kwantan
“Nayi fah…… Ya katseta da faɗin hakan….
Shuru tayi can tace toh yanxu yaxa’ayi….
Lumshe ido yayi tare da janyo filonshi yana me jan bargo jikinsa Yace “kawai bara na kwantan duk yanda Allah yayi dani ina so….
Atsorace ta katseshi da cewa “me kake San cewa…😳
Murmushi yayi jin yanda tayi maganar Yace “cewa xanyi Aunty *I LUV U* ❤ yana fad’in hakan ya kashe wayar gabaki d’aya yana murmushi…
Fad’i yake aransa ko ba komai yaji muryarta hankalinsa ya kwanta
Kiran sallar asuba ne ya tasheshi. Nan yayi salati ga annabi ya godema Allah daya nufeshi da tashi kafin yayi alwala yaje yabada farali
SAILUBAH ko rikicewa tayi. Yayinda hankalinta ya tashi. Nan tadinga kiran wayar tasa taji akashe
Tsaki taja tana mita aranta… Yaran nan so yake yasa mata hawan jini. Yanyu yanxu ya wani kirata ya 6ata mata tunani. Kuma ya kashe wayan dan iskanci
Jikinta ne yabata abinda yafaru dashi baxai qara faruwa ba. Hakan ne yabata damar sakin ranta tana cewa zasu had’u gobe.
Harta kwanta saidai tatashi tafara roqar Allah ya kare mata shi
Kafin takoma ta kwantan
~~~
Washe gari bata tashi da wari ba sai kusan gama da rabi tatashi
Tana break ne ya shigo tsaf dashi cikin shirin zuwa skull. Yayi kyau sosai cikin shigar qananun kaya sai qamshi yake
“Aunty nayi kyau. Yace da ita
Nan ta gallamai harara yaje ya xauna kusa da ita Yace am so sorry my Aunty kinji
Shuru tayi mishi
Yaci gaba da fad’in “me yasa baki shirya ba bayan kinsan shaɗaya muke da lectures yau
Nima KHAMIS ne yake gayamin ‘dazu dana kirasa na tambayesa shine ya tambayi Abdul dan yakira Aunty XEE tace bata sani ba. Wai meyasa Auntyna bakusan skull ne
Abin da zai amfaneka ya amfani xuri’arka…….
“Dallah yimin shuru. Idan kafara magana baka tsayawa. Kawani isheni da surutu kace kace sai kace wani aku…
Yaushe nasamu kaina dahar xaka faramin wani maganar skull
Ana saura sati biyu bikina nadena zuwa skull kai kasani
Sannan kaxo ka kwanta baccin ba gaira ba dalili harna tsawan kwana huɗu…
Koba jiya bane kasamu kanka
Dake karatun yana ranka basai katafi ba
Nidai baxani ba saina huta.
Shuru RAMADAN yayi can Yace “Amma ai jiya kunje wajan maza shine yau xaki kasa zuwa ga abinda xai amfaneki
Harara tasakar mai tace “idan naqara jin kace naje gun maxa wallahi saina murɗe bakinka
Tashi yayi yana turo bakin Yace toh ai shikenan akwai ranar in dillanci inji hausawa. wallahi duk ranar da rayuwa tajuye miki kika kawomin kukan San karatu sai tosheki…..
Yana faɗar hakan yaficce daga gidan yana mejin takaicinta
Itako binshi tayi da kallo tana mamakin yanda akayi ya rainata
Can taja tsaki haɗe da taɓe baki tana fa’din xatayi maganinsa
Shabiyu da rabi suka fitoh daga lecture. Direct gida yayo yayi wanka yana qoqarin leman abinci ne FAWAS ya shigo yana cewa har yanxu KHAMIS bai samu kansa ba
RAMADAN Yace “naji wata by due budurwar sadeeq Jamila tana cewa zasu’dau awa d’aya da rabi nan gaba kafin sufito
Yace “hmm damuwata HAMEEDAH
RAMADAN yayi Murmushi Yace “mujirashi kad’an dai
FAWAS Yace “ai jira ya xama dole…..
Momy ce tashigo ɗakin tana cewa toh ga abinci can kan dining kwaci ni nafita
FAWAS ya gaidata RAMADAN Yace toh. Kafin ta ficce
Gwatan doya ne wanda yaji kifi d’anye na mangyad’a. Kaɗan yaci dan FAWAS mah cikinsa acike yake sai dirink da yasha kawai…..
SAILUBAH ce tashigo tana cewa “ina momy take samareen banah
FAWAS yayi dariya Yace “kai aunty LUUVAH
Tace “Allah FAWAS ba qarya nafaɗa ba. Ku SAMAREEN BANAH ne bana baɗi ba😀. Kugayamin inda momy taje pls
“Aunty kinyi kyau….
Kallan kanta tayi daga sama har qasa doguwar rigace ajikin nata ta yane kanta da qaramin gyale sai wata ‘yar fus qarama ahunnunta
Murmushi tayi da kallansa RAMADAN ɗin Tace hmm “nagode ina momyn inata tambaya kunyimin shuru
FAWAS ne Yace “tafita tun ɗaxo. Jin hakan yasa taficce
Wasa wasa KHAMIS bai samu kansa ba sai wajan qarfe uku
Baiyi tunanin zaikai wannan lokacin ba
Kai karatu da wahala idan kuma ka iya da daɗi
Gudu gudu sauri sauri yayi wanka yayi sallah da shirya kansa yana murmushin mugunta yau ya jiqama FAWAS taba….
Wayarsa ce tayi qara yana ‘dauka FAWAS ya haushi da matsifa yana cewa kai wane irin mutum ne wai. Kana kallan lokaci kuwa
“Kayi hakuri dan Allah abinci xanci yanxu. yace dashi hakan
Yanda yakecin abinci da sauri shiyasa momynsa cemishi “wai saurin me kakeyi ne haka kamar tashin bubuwa
Ina xaka ne haka
Murmushi yayi Yace “wlhi momy wani gu xamu nida RAMADAN da FAWAS suna mota suna jirana
Shuru tayi mai taci gaba da karanta jaridarta
Shidai RAMADAN koda yaga fitowar KHAMIS murmushi yayi Yace da FAWAS toh gashi ya fito saika tada motar ko
Baice komai ba har lokacin da KHAMIS ya shiga motar sannan ya tada motar yana wani cika yana batsewa
RAMADAN ya nunama KHAMIS FAWAS da ido.
Murmushi KHAMIS yayi da talle qeyar FAWAS
Jin hakan yasa FAWAS Murmushi da cewa “kai ‘dan iska ne wlhi
Dake basu taso da wiri ba shiyasa suka isa qauye kusan qarfe huɗu da rabi
Basu samu yaran aike ba harna tsawan minti 10
FAWAS sai Jan tsaki yake… Can saiga wannan yaran nan da suka aika tun ranar farko… Yana ganinsu yaxo garesu da sauri yana Murmushi ya kalli RAMADAN Yace “in kira muku ita. Yace “eh….
Aiko da gudu ya shiga gidan lokacin HAMEEDAH na wanke wanke tana ‘dan rera waqarta ahankali Ahankali sai ganin Yaro kawai tayi akanta ya sunkuyo da kansa gareta Yace “HAMEEDAH wai kije inji wa’yannan kyawawan SAMAREEN NAN na ranar….
Shuru tayi tana tunanin can tace “oho su FAWAS ko
Yace “eh mana. Kina da masu zuwa gunki ne imba suba
Murmushi HAMEEDAH tayi Tace ya’u kenan kai dai ba’a rabaka da surutu jeka kace ina zuwa….
Da gudun ya fitta yaje gasu KHAMIS Yace “wai tana zuwa. Ku kan kuna cin sa’ar innah bata nan lokacin da kuke zuwa da baxata barta ba.
Miqa mishi ɗari biyu RAMADAN yayi akaro na biyu Yace “kaqara siyan wasu littattafan kaji
Yace “nagode yayah Allah ya saka. yanxu xata fitoh.
Naga mishi kai RAMADAN yayi sannan ya tafi da gudu abinsa
Batafi minti biyar ba tafitoh cikin shigarta na atamfa riga da xani
Kallo ‘daya xaka musu kasan sunsha jiki
RAMADAN ya qare ma HAMEEDAH kallo. So yake yaga ta’inda xata xama bala’i ga FAWAS. Anya ba qarya Junior yayi masa ba kuwa
Saidai baisan dalilin dayasa farkwan ganinsa da ita gabansa ya faɗi ba
Gashi yanxu mah gaban nasa ya qara faɗuwa
Qura mata ido yayi sosai sai yaga kamar tana da buɗewar ido kaɗan…..
Tunanin FAWAS ya ɗauke cak ganin masoyiyar tasa
“Assalamu-alaikum….
“Amiien-wa’alekissalam yabata amsa cikin murmusawa
“Ai nayi tunanin baxaka dawo bah
“Ban dalilinki kad’an naji
“Duba da nayi da kwanakin daka d’auka sun kusa sani in rasa nutsuwata
“Idanko hakan ne ba shakka nafiki shiga wani hali
“Baxan musaka ba idan kabani haske
“Hmm RAMADAN ne baiji da’di ba shiyasa baki ganni ba
“Haba mana… ninasan babanxa ba ciwo ne kawai xai hanaka zuwa gareni… Dalilina kuwa shine idan nayi duba da qaunar da nahangu a tare dakai ranar farko
“Gaskiya ne kin 6ata tunina.
Wan nan bai isheki ba sanda kika 6ata xuciyata…. Fatana kisoni dan Allah Ki qaunaceni da Gaskiya danna rigada na baki amanar kaina
Shuru HAMEEDAH tayi tana qarema fuskarsa kallo. Kyakkyawane ajin farko gashi Yaro meji da kansa. Ga wayewa tamkar tarayu dashi. Ga iya magana. Tamkar yasan tana San me da’din kalamai. Taji tana sanshi dan tun ranar da suka had’u xuciyarta taqi mantawa da shi….
Kiɗan tsagaita tunaninnan yayata dan ina gudun shigowar sheɗan cikinsa
“Kullun ina neman tsari dashi. Dan haka kar kayi tunanin xai shiga cikin tunanina
“Hmmm “tonaji gayamin
“Na kar6i amanarka xanyi qoqarin riqeta amana
“Kingama min komai yayata
“Anya wannan sunan baxai fitta daga bakinka bah
“Ai dashi ya dace dake
Murmushi tayi da cewa hmm ka daɗa cin sa’a yaumah
“Yace name fah.
Nayi ɗam malele
Saurin waro ido😳 FAWAS yayi yace “Wlhi na qoshi dam dam😀
Kallansa tayi da sauri cikin mamakin rikicewar da yayi tace “toh miye na rantsewa kodan baka san ci ne
Saurin girgixa mata kai yayi da cewa “ko kad’an yayata. Kawai dai na kwashin ne kamar cikina xai fashe haka nakeji Amma idan kin saka wani xargi aranki toki kawo min inci koxanyi amai na rantse miki baxanqi cin abin hannunki ba….
Murmushi tayi tace “na yarda da abinda kace. Karkaji komai….
Bata qarasa ba wayarshi tafara ringing yana dubawa yaga dadynsa ne
Dan haka Yace “ina xuwa yayata bara na amsa wayar Dadyna
Tace toh
Yana barin gun RAMADAN ya fito daga cikin mota ya nufuta yana qare mata kallo
Tace “ya jikin
Yace “naji Sauqi
“Kamar da magana abakinka
“nayi mamakin yanda akayi kika gane
“na lura da hakanne kawai
Murmushi yayi Yace “kamar kina da wayewa…..
Da sauri ta kallesa. Kana kuma tayi saurin ɓoye yanayin tana me cewa “ina wata wayewa agun mutumin qauye
“Kinsan wasunsu suna suka tara. ‘yan qauyen…..
“Toh me kakesan cewa. Ta katseshi da fad’in hakan.
Murmushi yaqe yayi sannan Yace “haɗu warmu dake tafarko nagamsu da cewa ke ‘yar qauye ce
Sai dai yanxu dajin kalaman da kikayi amfani wajan ba FAWAS amsar maganganun da kukayi shiya tabbatarmin da cewa da wiya idan ke ba ‘yar birni bace
Kallansa tashiga yi dakyau kana tagyara harshenta da cewa “baka da hankali…..
“Biyu kenan. Ya katseta da fad’in hakan yana me cigaba da cewa. “Hmm tsakanin ni da ke za’aga babbance mara hankali.
Duk abinda xanyi ina aiki da hankali
Abinda xance miki anan kawai shine. kina da wani sirri wanda kike tunanin ba kowa bane xai ankare dake
Saidai kin haɗu dani
Abokina ya kamu da MASEEFAR SONKi na tsakani da Allah
Baxan hanaki abinda kike San aiwatarwa ba
Amma kisani idan har xakiyi agabana wlhi saina 6ata miki shiri. Ki rubuta Ki ajiye…… Ya qarashe maganar da kallan FAWAS wanda yake waya hankali kwance. kana ya maida kallansa gareta yacigaba da cewa “Ki duba yanda yake cikin farin ciki yanxu.
hmmmm Na roqeki dakar kiyi kuskuran cutar dashi……..
Yana fa’din hakan ya shige cikin motar
KHAMIS Yace “kana bani tsoro RAMADAN tayaya kake tunanin HAMEEDAH xata kasance wayayyiya.
Murmushi yayi Yace “xarginta kawai nakeyi saidai bakaga yanda tashiga tashin hankali ba. Ina tunanin akwai wani abu atare da ita
Shuru KHAMIS yayi yana kallanta
Can Yace “aikuwa gashi nan kam tafad’a tunani. Gashi kuma Santa FAWAS yake da gaske. Idan kanuna mishi wani abu bayarda xaiyi ba
“Barma batun nan xargi kawai nake. Fatana karya tabbata…..
“Ina waya naga kuna magana da RAMADAN kiyi hankali dashi yana da saurin 6ata tunanin mutum
Murmushin yaqe tayi Tace “ainaga alama saidai me kagani
“Abubuwa da dama mana. Natafi nabarki da sakewa yanxu kuma nataddake cikin tunani. Kuma nasan tunanin yana da nasaba da xancikan da kuka tattauna
Murmushi yaqen taqara yi Tace “koma dai miye nayarda da abinda kace akansa yanxu.
Wai magana yake akan insoka tsakani da Allah dan kaima irin wannan San kakemin
Murmushi yayi Yace “ai gaskiya ne ya fad’a miki. Shikenan abinda yacemiki
Tace “adunqule dai shikenan
Yace “toh yayata xani gida…
“Har naji gabana ya faɗi.
Dan Allah karka barni yanxu wlhi ban gaji da ganinka ba.
“Abu me sauqi ne yayata. Kawai kibani ɗaki na shiga ciki mukwana muna hira
“Dama ace ni watace danayi yanda kace
“Toh kixama watan mana
“Toh tayaya
“Kice infitoh. Wlhi xan fitoh in ɗaukeki daga gidan nan in kaiki gidana. in killaceki. Ki koyamin yanda ake xaman aure
Rufe fuskarta tayi cikin jin kunya tace “Allah suɓutar baki nayi ranar. Kadena faɗin hakan.
Murmushi yayi Yace “wlhi baxan dena ba. Sannan kuma nayi alqawarin idan kika xama mallakina ke xaki fara bani haske kan wannan abubuwan…….
Juyawa tayi da gudu tashige gidan nasu Cikin nuna matuqar kunyarta
RAMADAN yaja tsaki Yace “Allah da bayani akan yarinyarcan
KHAMIS yayi murmushi Yace “hmmm naga alama
FAWAS ko da murmushi ya juya yashige motar
Suna cikin tafiyane wayar KHAMIS tayi qara. Ya ɗauka yana me lumshe ido ganin XEE ce
Yace “my baby ya gida
XEE dake kwance agadanta ita da SAILUBAH Tace “ina kaje ne.
Yace “waje me nisa… Tace “shiyasa naji duk hankalina ya tashi. Murmushi yayi Yace “toh ya kwanta dan gamu akan hanya. Tace “toh madallah kaxo min da abu me daɗi dan dama kwaɗayi nake ji shine nace bara in nemoka nasan duk inda kake xaka nemomin abin kwaɗayin
Yace “angama my wife my Aunty my baby
“Duk ni kad’ai
“Yace eh mana
Tace “toh kakulamin da kanka pls
Yace “insha Allah xanta kulamiki da kaina ina miki tattalinsa harsai randa kika mallakeni.
Dariya tayi tace “wato daga ranar sai insan nayi kagama naka ko
Yace “kwarai mah kuwa. Kina sakaci dani akwai mayun da suke bibiyata
Tace “aikowa baxan basu damar daxa su ɓatamin tunaninka ba. Yanxu nabaka minti 30 kayi qokarin ganin mun kasance da junah
Waro ido yayi 😳 cikin sauri Yace “haba Aunty XEE. tace “haba me sona.
dafe kansa yayi yana cewa “yanxu fah muka taso ALLAH xan xarce wannan lokacin.
Tace “kai kasani. Waya sani ma ko daga gun wata kake.
Wlhi idan ka xarce wannan lokacin saina hukuntaka
Tana fa’din hakan ta kashe wayanta
Lumshe ido yayi da buɗewa alokaci ɗaya sannan yace da FAWAS da yake tuqi cikin nutsuwa “kaga malam tsaya……
Tsayawa ko FAWAS yayi agefan titi… Ganin hakan yasa KHAMIS fitowa yana cewa “kaima fitoh.
Ba gaddama FAWAS ya fitoh.
Yana fitowa KHAMIS ya shige maxaunin Direba yana fad’in komacan naga baka sauri kuma minti 30 tabani taganni kusa da ita……
RAMADAN yayi Murmushi yace duk bala’inka kuma saimun biya na siyama Auntyna ice cream…..
Muguwar harara KHAMIS ya auna masa xaiyi magana sai kuma yatuna duk acikin minti 30 ɗin tace mishi tanajin kwaɗayi… Tuno da hakan da yayine yasa bai cema RAMADAN ɗin komai ba dan yasan dole nema yanxu saiya biya ta wajan.
FAWAS ko taɓe baki yayi yashige inda KHAMIS din ya fito sannan KHAMIS ɗin yajah motar da wani banxan gudu……….
RAMADAN ya waro ido😳 ganin dugun da KHAMIS yakeyi Cikin tsoro yace “Ka tsaida tunaninka dan Allah karka yima Auntyna asarana😰 dan ALLAH
Ya qarashe da damuwa
Me FAWAS xaiyi imba dariya ba 😂
Aiko KHAMIS bai tsaya da wannan gudun nasa ba har sanda suka je sukayi siye siyensu ya qara figarsu bai tsaya ako ina ba. Sai a qofar gidansu XEE
Ahankali ahankali yake sauke numfashi cikin wani hali ya kira numbar XEE Yace “my luv gani na iso.
XEE tanumshe ido tare dayin murmushi tace dts gud my baby Allah ya temake ka saura minti uku daka xarce daka sani
Shuru yayi mata da kashe wayan
SAILUBAH taja tsaki tace “Allah dai ya sauwaqe miki ‘yar iska kirasa da wanda xakiyi luv saida qaramin yaro…….
Dariya XEE tayi tace “kema ai qaddarar na kanki. kijira xuwan lokaci kawai. Tafad’a tana me ficcewa daga d’akin
Ta fitoh falon kenan RAMADAN da FAWAS suka shigo falan suna gaida mamah
Tace ” ya jikinka RAMADAN
yace ” da sauqi Mamah na ware.
“Toh masha allah dama anjima nakeso naje in qara duboka sai kuma gaka
Yace “naji sauqi sosai dan yanxu mah daga wata unguwa muke
Tace “haka ake so. yauwa dama nace niko bana ganin KHAMIS yanxu ina yashige ne ko yayi tafiya ne
Da sauri RAMADAN ya kalli FAWAS shima kallansa yayi yace “ai Mamah…….
Saurin katseshi XEE tayi wajan cewa yayi tafiyane Mamah
Tace “haba mana shiyasa bana ganinsa….
SAILUBAH ce tafitoh tana murmushi Tace wlhi Mamah ba’inda KHAMIS yake yananan……….
Har suna had’a baki wajan cewa “wlhi Mamah da gasken yayi tafiya
SAILUBAH takalli RAMADAN wanda ya rantse da kallan FAWAS shima daya rantse ta kalli XEE itama data rantse saita maida kallanta ga Mamah tace “toh shikenan Mamah xan tabbatar miki da cewa sune suke qarya dan xan kawo miki KHAMIS har gida kigansa
Mamah tace toko wani abu ya faru ne
RAMADAN yayi Saurin cewa ba komai Mamah kidai bartan takawo miki shi ɗin
“Toh nabari. Ta fa’da da barin falan tana girgixa kai
XEE ta gallama SAILUBAH harara da ficcewa daga falan xuwaga masoyin nata
FAWAS yayi Murmushinsa cikin shauqin so dan jin daɗin ganin HAMEEDANSA kana ya ficce shima daga falan
RAMADAN ya matso kusa da SAILUBAH Yace “hmm kinsan miye Aunty….. Tayi banxa dashi. Saiya kama hannunta yacigaba da cewa “Yau KHAMIS ya kusa kashe miki ni…..
Da sauri takallesa haɗe da waro ido😳…..
by RAHEEMAT
[9/6, 3:05 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*4
Kisa…..
Kisa wane iri RAMADAN.
“Wlhi Aunty gudu yadinga yi damu muna ce mishi ya tsaya Amma ina sai qarawa yake
Murmushi SAILUBAH tayi da cewa “hmm indai gudun mota ne ai kaima kanayi. Amma pls kudena yi dan banaso. Kasani ai….
“Toh Aunty ambari Amma me yasa kikaso gayama mama gaskiya….
“Yauwa yaushe kakoyi qarya.
“Karewa nayi Aunty kinga baidace mufad’i gaskiya ba
“Yayi maka kyau ai da qaryatani
Kiyi hakuri baxan sake ba
“Nayi… sarkin ‘yan bada hakuri
Murmushi yayi da cewa ga ice cream na siya miki
Da murmushi Tace “wow nagode sosai.. kamarko kasani naji sha’awarsa d’axo
“Ai naji ajikinane my Aunty.
“Kin kyau sosai my luv
“Hmm wakayima wannan wankan
“Akwai wata ne bayan ke
“Eh mana. Meya kaiku guri me nisa
“Wata ce takwarema FAWAS
“Dafatan Gaskiya ka fad’amin
“Wlhi Aunty XEE baxan miki qarya ba
“Nayarda yanxu.
“Nasan xaki yarda tunda na rantse miki
“Toh karkasa indena yarda fah
“Baki isa ba ai…
“Ko
“eh mana.
“To naji bani abinda ka siyamin.
Miqa mata kayacicin daya siya mata yayi
Cikin farin ciki ta kar6a tana cewa “SAILUBAH taso tona mana asiri yau…..
“Dan Allah fah.
Tace “wlhi
“Dama ta tona dan sufara sanin komai
“Hmmm zaka sani. Idan suka kunno matsala nixan fika shiga tashin hankali. dan kasan nina faro
“Hmm kibari lokacin yayi kigani cikin ni dake waxaifi shiga tashin hankalin
“Wai kana so ne kabani mamaki
“Ai ko daga yanxu ya kamata kifara tantancewa. Dan bakiga gudun haukan da nadinga yi bane
RAMADAN cewa yayi kar nayima Auntynsa asararsa….
Dariya tayi da cewa toh gayamin.
Kama hannunta yayi cikin wani yanayi Yace “nayi missing d’inki jiya wlhi over
“Nima haka
Toh gayamin mafarkin da kikayi akaina
“Nayi mafarki kana tayani girki a qayataccan kitchen d’ina wanda akayi mishi ado da kalmar I luv u
“Naji dad’in hakan sosai
“Toh kai gayamin wanne kayi akaina
“Hmm ganinmu nayi a wajan shaqatawa wanda muka yima kanmu ado da yara masu kamarki kamata kyawawa…
“Wayyo dad’i. Bar gayamin.
“Xan sake fad’a
Watoh in shiɗe kenan dan daɗi
Xanso hakan sosai Amma ba a irin wannan lokacin ba
“Alamu sun nuna xakaji dani
“Kallanta yayi dakyau na tsawan wani lokaci kafin yace “Ki jira lokaci Aunty XEE. Xanyi qoqarin baki madara dan naga kinfi Santa
“Wacce aciki
“Tawa mana. Tunaninki xan baki ta wani ne
“Naji. Gayamin ya kalarta take
“Hmm… Kidai ban lokaci
“Abubuwan da kace im baka lokaci akansu suna da yawa my baby.
“Ina sane so nake in tarasu da yawa. Kinga lokaci d’aya saina baki mamaki akansu
“Badai iya magana
“Ke kika koyamin ai. Kinsan ni salihi ne ada
“Xan kulle bakinka da xarar kaxo hannuna
Murmushi yayi da sakar mata hannunta yana cewa “ina xumuɗin xuwan ranar da xan shiga hannunki my baby
Murmushin itama ta mayar masa kana tace “kaga tafiyata. Ina tsoran sharrin SAILUBAH
“Itama tsoran naki ai take
“Xanso injika sosai wajan baccina
“Xanyi qoqarin baki mamaki sosai wajan baki kalamai masu sanyaya xuciya. Farin cikin Ki shine nawa. Kuma nasan xaki samu.
Murmushi tayi da ficcewa daga motar tana cewa bye my baby
Binta yayi da kallo har tashige
FAWAS naganin shiganta ya nufi gun motar da shigewa yana cewa kagama 6ata tunaninta da yawa fah😳
Ga RAMADAN canma yana xubama Aunty LUUVAH shagwa6a
Murmushi KHAMIS yayi yace. “Bari kaga sallar magrib ce kawai xata Sa ya fitoh
Dariya FAWAS yayi da gyara xamansa ya kalli KHAMIS dakyau Yace “wlhi KHAMIS ina matuqar San HAMEEDAH. Bansan yaushe hakan tafaru dani bah. Bansan ta ina xan fara ba. Yanxu dana ganta wlhi ji nayi kamar an xaremin ciwan shekara guda.
Ina mata wani so Wanda yafi qarfin da akirashi da MASEEFAR SOO
Sai mamakin kaina nake KHAMIS. Ji nake cikin xuciyata kamar idan na rasata xan shiga wani bala’i.
Kaduba iyayanmu baxasu kallemu da batun aure ba yanxu
Ni kuma Gaskiya shi nakeso yanxu. kuma da HAMEEDAN wlhi KHAMIS aure nake so…….
Da sauri KHAMIS ya kallesa… Bakinsa na rawa Yace “Aume
Yace “aure
Shuru KHAMIS yayi… Xuwa can Yace tab eh jan
Gaskiya ka d’auko aiki. Kuma tunaninmu d’aya. Amma jira shegen can ya fitoh kasan akwai basira
Lumshe ido FAWAS yayi cikin gamsuwa. Yace toh muje gida dan jikina qaiqayi yake min wanka nakesan qarawa anjima mayi maganar in Mun had’u ko gobe.
Tada motar KHAMIS yayi yana cewa tunda Aunty LUUVAH taxo da mota muje kawai xai biyota. Nima yanxu ina wanka nayi sallah kwantawa xanyi
“Yauma ba zuwa club kenan. FAWAS Yace hakan
“Eh. KHAMIS ya bashi amsa
Sanda ta shanye ice cream dinnan tas sannan tace da RAMADAN “ban rage maka bah kaga na manta
“Hmm Aunty kenan… Ai idan ice-cream na tare dake mance kanki kike….
Yanxu dai tashi muje gida naga kinxo da mota. Agajiye nake sallah kawai ta raqemin in kwanta
“Cin abincin fah
“Banajin yunwa
“Wai me yake damunka ne RAMADAN. So kake ciwo ya kamamin kai. Baka da maqiyi aduniya irin abinci. Sam baka d’auki abinci da wani mahimmanci ba. Ga cucuka kala kala suna kama mutane sanadinsa………
Shuru tayi dayi mishi kaɗan dan ganin yanda kawai ya xubama bakinta ido
Ganin ta tsaya da maganar yasa ya sakar mata murmushi Yace “Aunty bakin ki yana kyau da jambaki
Harararsa tayi cikin damuwa tace “pls katemaken kadinga cin abinci mana RAMADAN
Tashi yayi tare da gyara mata d’aurin d’ankwalinta Yace “toh naji Aunty… tashi muje kinji amfara kiran sallah
Murmushi tayi ganin yanda yake janta tamkar wata makauniya
Sunkai qofa ya jawo mata takalminta da saka mata a qafartata yana cewa “wow kullun qafarki qara kyau take my Aunty
Murmushi tayi
“Kaga bamu ma mamah sallama…. Bata qarasa ba Maman tafitoh tana cewa “xaku tafi
“Eh Mamah sai da safe. Cewar RAMADAN
“Toh Allah ya tashemu lapia
“Amiin. Fadin SAILUBAH
Awajan hutawan gidan sukaga XEE tabaje sai shan ice-cream take. Tamiqa ma SAILUBAH wani da cewa “Ga naki
“Kina can nasha nawa ai
“OK
“Nina tafi sai goben idan kin fito
“Toh..
RAMADAN akula da kyau pls karka qara yin wannan baccin
Murmushi yayi da fa’din “Aunty XEE kenan.
“Allah gaskiya tafad’a ai
“Hmm toh muje Aunty dare fah nayi
“Wlhi RAMADAN kana da futuna. Katafi abinka mana… Koda ita kaxo. XEE tafa’di tana me harararsa
Kama hannun SAILUBAH yayi yana janta… Ganin hakan yasa SAILUBAN ta biyema tafiyar tashi dan karya kayar da ita suka ficce daga gidan….
Murmushi XEE tayi RAMADAN ko futuna cewar xuciyarta
Tayi parking kenan wayanta tafara ringing…. Kanta d’aga RAMADAN Yace “Aunty waye kuma Najib
“Wani ne na had’u dashi d’azo
Kallanta yayi kaɗan itama kallan nasa takeyi tana so taga me zaiyi.
Ganin hakan yasa Yace “toh bana sanshi Aunty Ki rabu dashi.
“Yanxu me kake San nace mishi
“Kiran ya katse ai
“Xai sake kira. Idan ya kira ince mishi me
“Kice karya qara kiranki dan baki sanshi
Tsayar da kallanta tayi sosai akansa sannan tace “daga nan kuma sai me
“Saiki kashe wayan
“Idan ya qara kira fah
“Saiki Qara d’auka Ki zageshi Kawai😔
“Allah ko
Kallanta yayi tare da saurin kawar da kallan nasa daga garetan
Shuru tayi ganin wani kiran nasa ya qara shigowa
Ya qara kallanta a karo na biyu
Tayi murmushi da cewa “d’auka kai ka gaya masa dan baxan iya bah
Murmushi yayi da d’agawa yana me cewar “Wai tace in gaya maka Kayi hakuri tana da sadakinta ahannu kaga bedace ta yaudareka ba
“Kai qaninta ne. Cewar Najib d’in
“Eh… Fad’in RAMADAN
“Toh nagode kace mata naji dad’in gaskiyar data fad’amin
“Insha Allah xan tabbatar mata da cewa bakaji dad’in hakan ba. Amma dake ba yanda xakayi kana mata fatan alkairi
“Dako nagode.
“Karkaji kamai
Saiya kashe wayan kana ya goge number sannan ya kalli SAILUBAH wacce tunda ya faro maganar idanta yake kansa. Tace “Toh bani wayata
Ahankali ya miqa mata cikin sanyin murya Yace “am so sorry my Aunty kiyi hakuri xan dena miki hakan kinji
“Lumshe idanta tayi tabud’e kafin tace “watoh haka kakesan kaganni ba kowa atare dani ko…
D’aga mata kai yayi da cewa “Eh Auntyna
Da mamaki taqara tsaida idanta akansa Tace “eh fah kace
Shuru yayi mata
Ganin hakan yasa tafitta daga motar tayi cikin falan nasu
Murmushi yayi sannan shima ya ficce daga motar yayi gidansu yana me rayawa aransa matsalarsa qalilance
Wannan shine dare na uku kenan wanda arayuwar HAMEEDAH takasa bacci
Ni dai Rahamat ganinta nayi tanata juyi da alama tana cikin damuwa
Tunani tafara akan RAMADAN wanene shi dahar xai kaifin tunaninsa yake San tarwatsa tunaninta
Ta gaske taji tana san FAWAS karo na farko arayuwarta…..
Tashi tayi daga kwancen da take…. Abayyane take fad’in ina sanka FAWAS duk da kai qaramin Yaro ne xanyi qoqarin mallakarka cikin lokaci qanqani😟
Da qar bacci 6arawo yayi awan gaba da ita
Shima FAWAS din bacci yayi wannan dare cikin shauqi da farin cikin yau ya gana da masoyiyar tasa
Haka KHAMIS bai bar XE tasamu kanta wajan bacci da wuri ba
Dan Sanda ya gama kunce mata tunaninta kaf sannan ya kashe wayarsa yana me rayawa aransa wlhi duk bala’in daxai fuskanta agun iyayansa xai jure indai xai samu Aunty XEE👈🏼
Itako takasa tunanin komai dan tasa aranta kawai RAMADAN so yake ya kasheta da ranta
Yaqi barinta da kowa yanxu har abin ya kaisu da cewa so yake ya ganta ahaka ba kowa🙅🏼 tare da ita👈🏼
“Kai wallahi da sake. Anya ba asiri RAMADAN yake min ba. Tafad’i hakan abayyane cikin damuwa
Ganin da tayi tunanin baxai kaita ko ina ba shiyasa tayo alwala tahau sallah
Lokacin 1 ne na dare
RAMADAN ko xaxxafar addu’a sosai yake aikawa da Auntyntasa
Illah yake mata cikin dare Amma bata sani ba
Shiyasa yake samun yanda yake so akanta batare da wata matsala ba
*NI DAKE DA KAI MUTASHI TSAKAR DARE MU HANA IDAN MU BACCI MU ROQI ALLAH BUQATUMMU WLHI SHINE ME BAYARWA KUMA ME HANAWA ME KASHEWA*
RAMADAN Yana ji da SAILUBAH tamkar su koma ciki🤰🏼tare da ita👈🏼 Joyi yake a gadansa yana yana addu’ar Allah ya kaishi inda yakesan ganinsa shi da Auntynsa💋
*BARKA DA SALLAH SISTERS🙋🏼*
[9/9, 11:12 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*5
Washe gari antashi da ruwa agarin na kano
Hakan yasa kowannansu yana nad’e agado
Wani kira ne yasami Dadyn RAMADAN lokacin da yake dining yake breakfast
Inda ya kara wayan nasa a kunne yana fad’in “Assalamu-alaikum Assalamu-alaikum dawa nake magana
Daga can 6angaran wata sanyayyiyar murya ta bashi amsa da cewa “kana magana da *Alhaji Abdullahi*……..
Afurgice Dadyn ya tashi cikin matuqar ka’duwa Yace Ranka ya dad’e amin afuwa bansan dakai nake magana ba
“Nasani ai. Bai kyautu ka damu ba.
Dama na kiraka ne in shaida maka da cewar lokacinka ya kusa qarewa.
Sannan inasan ganin “dana acikin wata biyu nan gaba
Inasan in dinga ganinsa na tsawan watanni
Kuma ba’a nan qasarku ba. Acan qasar England
Saboda wani harkar kasu wanci ce xata kaini gun.
Saboda haka make San inyi amfani da wannan damar inga d’ana
Soran dabara tarage maka.
Gumine ya fara wanke fuskar Dadyn. Cikin wani yanayi Yace “Amma ranka ya dad’e lokaci baiyi ba da har xaka nemi ganinsa. Da xaka bari lokacin ya cika daxaifi min……..
“Kaga dakata. Kasan ba qaramin hakuri nayi ba arayuwata
Dan haka wlhi baxan iya canja wannan bayanin nawa ba….
Yana gama fad’in hakan ya kashe wayansa
Jagwab Dady ya xube kan kujera hankalinsa amatuqar tashe…..
Momy tace “lafiya naji ka ambaci me martaba
“Eh shine wai yana san ganin RAMADAN nan da wata biyu a England
Momy Tace “innalillahi’wainna’ilaihirraji’un… Me xanji ni Amina
Dady ya goge guminsa Yace “xanje ga Habibu yanxu mu tattauna dan yaban shawara….
Da sauri momy Tace “Yakama kam
Daga yanayin tuqin da Dady yake xakasan yana cikin wani hali
Haka dai yasamu ya isa ga office d’in Dadyn KHAMIS da damuwa ya xauna a kujera yana cewa Habibu komai ya kwance min yanxun nan…..
(Dake haka ainiyin sunan Dadyn KHAMIS yake Habibu)
Dan haka ya kallesa da mamaki Yace “ai tunda na ganka haka nasan ba lafiya ba. Meya faru ne
“Maimartaba ne ya kirani yanxu yanxu. yana me cemin yana San ganin ɗansa RAMADAN anan qasar England dan wani kasuwanci ne xai kaisa qasar nan da wata biyu kuma shi kansa xai kai kimanin wata biyun.
Atakaice dai yana San nan da wata biyu yaga RAMADAN a England……
Duk da kasan ba fitowa xaiyi gaba da gaba suga juna ba
Jan numfashi Dadyn KHAMIS yayi cikin matuqar damuwa Yace “akwai matsala. Banyi tunanin hakan xata faru ba. Tunda lokacin da ya iba bawai yayi bane…..
Da sauri Dady ya katseshi da cewa “aishine nima na gani
“Toh ga shawara
Mexai hana ka datse karatun shi RAMADAN din kaneman mishi gurbi a England da sunan kanasu ya qarashe karatunsa acan… Nasan dake yana da basira yaran. Xai tuhumeka akan meyasa xakayi masa hakan. Tunda yana ganin ya kusa gamawa. Kaga sai Kayi amfani da wannan damar kace mishi kana so karatun nasa yayi xurfi yafi hakan ne. In acanne baifi ya d’auki shekara hud’u ba ya gabama gabaki d’aya anan ko xaifi hakan tunda kanaso sone yaci gaba….
Da murmushi sosai akan fuskar Dady ya miqama Dadyn KHAMIS hannu sukayi musa baha yana me cewa “Gaskiya naji dad’in wannan shawara taka. Da gaske idan ba hakan akayi ba komai xai iya faruwa
“Hakane
Gyara xama Dady yayi ya fuskanci Dadyn KHAMIS dakyau yace “Saidai fah wani hanxari ba gudu ba.
RAMADAN baxai yarda arabashi da KHAMIS da FAWAS ba
Dan sanin kankane sunyi matuqar shaquwa da juna.
Murmushi Dadyn KHAMIS yayi Yace “aini shaquwarsu mamaki take bani. Sai kace sunsan daga rashe d’aya muke
Yanxu dai abinda yadace anan shine mu tuntu6i shi Mustapha (Dadyn FAWAS yake nufi) awaya yanxu sai muqarasa tattaunawar dan kasan shima yana aiki da nutsuwa
Shuru Dady yayi da fara neman Dadyn FAWAS awaya
Yaci sa’a ya samesa Yace mai yana so su had’u office d’in Dadyn KHAMIS dan akwai magana me mahimmanci da xasuyi
Jin hakan yasa Yace dama yanxu yana hanyarsa ne ta xuwa office tunda hakane bara kawai ya biyo
Cikin murna Dady ya kashe wayan yana mayarma da Dadyn KHAMIS yanda sukayi
Bai dad’e ba ko ya baiyana garesu
Nan Dady ya kashe komai ya gaya masa
Yayi mamaki sasai daga bisani Yace “ina ganin duk muhad’a kan yaran mu fiddasu karatun
Kunga idan akai hakan xa’a samu yanda akeso
Amma koya kuka gani
Shuru sukayi. Can Dady Yace hakan yayi Gaskiya naji dad’in hakan sosai
Dadyn KHAMIS Yace dama nalura da kan KHAMIS na rawa kwana biyun nan
Kamar Wanda ya fad’a soyayya
Dady yayi murmushi Yace “ai in ita d’ince mah ya fad’a ba mamaki dan nima naga soyayyar SAILUBAH a idan RAMADAN…..
Da sauri Dadyn FAWAS Yace kaji ja’irin Yaro ina xaikai SAILUBAH
Murmushi Dadyn KHAMIS yayi Yace yaran nan kana kallansu kabarsu yanda kagansu kawai
Dan inda kake tunanin zasu kai kansu ba nan suke hari ba. Sai inda bakaiyi tunani ba saika gansu agun
Dan idansu a abu’de tar muka haifesu
Murmushi dady yayi yana me miqewa Yace “yanxu a ina mukabar xancanmu
“Karka damu akwai wani Abokina acan England
Yaransa cikin shekaran nan suka fara karatu acan d’in. ina tunanin ma kun wayeshi Abdulsamad
Xan mishi magana yanxu idan naje office nasan xaiji da komai na nema musu qurbi da komai da komai kafin nan da wata d’aya
“Ayya Abdulsamad ai bashi da matsala kawai atura mishi da kud’i nasan kam kamar ma anyi komai an gama. Cewar Dadyn KHAMIS
“Toh tunda hakane yanxu hankalina ya kwanta xanje office yanxu sai min had’u kawai.
“Madallah. Nima bara mufita tare… Cewar Dadyn FAWAS
Nan sukama Dadyn KHAMIS sallamah suka ficce
Inda Dady yayi ma’aikatarsa shima Dadyn FAWAS yayi tasa
*Wannan kenan*
Wuraran qarfe biyu ne na rana wasu samari biyu way’anda baxa su wucce shekara ishirin da takwas ba suke jingine a jikin motarsu a qofar gidansu SAILUBAH suna masu hira da juna. kallo d’aya xaka musu kasan aminan junane……
Fitowar khairat ne daga gidansu SAILUBAH ya tsayar musu hirar tasu.
D’aya daga cikinsu Yace “Allah yasa sunanan
Khairat tayi murmushi kana tace “Suna ciki har sunce kushigo cikin
“Toh madallah mungode ‘yan mata ga wannan
Fur khairat taqi kar6ar kud’in nasu tayi cikin gidansu
Suko sukayi murmushi tare da shigewa ciki
Wasu kujerun robane gudu hud’u 4. table d’in tsakiyan na d’auke da drink kala kala da danginsu kayan fulawa
SAILUBAH da XEE suna xaune akan biyu daga cikin kujerun
Ganin hakan yasa SAMAREEN xama akan sauran biyun suna masu gaisar dasu
Da jan aji da yanga suke amsa musu……
Duk RAMADAN da KHAMIS da FAWAS suna kallansu
Dan suna barandar saman d’akin RAMADAN ne suna hira da junansu
RAMADAN yakai kallansa ga harabar gidansu inda khairat take takusa shigewa falo kenan ya kwalla mata kira
Da sauri tanufi shi tana cewa “Ya RAMADAN gani
Wata shegiyar harara ya auna mata
Kafin Yace “Na rantse da Allah daga yau na qara ganin wani ya aikeki Kikira mai Auntyna kikaje kuma na rantse da Allah saina ji miki ciwo dan duka xan miki bana wasa ba.
Ahankali Tace “Toh yayah idanga ce musu me
Wata shegiyar hararar ya qara auna mata Yace “kice musu ammata miji
Da sauri khairat ta kallesa tace “toh yayah waye mijin nata dama Aunty ta fidda miji ne😀
D’auke kansa yayi ga kallanta ya maidashi ga FAWAS…..
Ganin yanda kishi ya fara aiki akansa shi yasa FAWAS ce mata khairat jeki ai kinji dai me Yace miki ko
Da sauri tace naji ya FAWAS imma banyi aiki dashi ba ai jikina ne xai gayamin Amma waye Wanda Aunty ta fidda mijin nata……
“Bar nan gurin…..
Da gudu tabar gurin dan ganin yanda kamannin yayan nata yanda ya canjah
Murmushi FAWAS yayi ganin yanda KHAMIS ya xubama XEE ido yanda ta dage tanata hirarta da d’aya daga cikin SAMAREEN kallo d’aya xaka musu kasan saurayi da budurwa ne
Ya maida kallansa ga RAMADAN shi Kam kallan wani gu yake ba kallan SAILUBAH ba saidai kishi xaka hango 6ace 6ace ya 6ata mishi kyakkyawar fuskarsa…….
Gyaran murya yayi duk suka juyo suka kallesa
Yace “xaman me kuke kuna gani anacan ana muku 6arna musamman kai KHAMIS Aunty XEE tasake da yawa fah.
Dan wlhi idan kabari wancan ya 6ata maka tunaninta xakasha wahala wajan setata dan ba qarya ya had’u
Tsaki RAMADAN yajah….
FAWAS ya kwashe da dariya yana me cigaba da cewa hmmm kai baka da matsala RAMADAN tunda mukullun xuciyar Aunty LUUVAH na hannunka. Akowane lokaci idan wasu suka xuba dattinsu kakan iya bud’ewa kashiga kashare tas harda wankewa
“Sai aka gaya maka nima mukullun xuciyar Aunty XEE baya hannuna……
Idan kana tunanin ban mallakeshi ba. Toh kadena dan wlhi yanxu ganin idanka xanje in 6ata tunaninta….. Cewar KHAMIS
Murmushin yaqe RAMADAN yayi
KHAMIS ya tashi a fusace ya gangara qasa can suka ganosa har ya shige idansu SAILUBAH……
XEE naganin d’an kyakkyawan saurayin nata wanda ya gama 6ata mata tunaninta ya cakuɗa mata tarbiya ya hanata ganin kyawun kowa a xuciyarta gabanta ya fad’i
Ahankali ya qarasu garesu
Yaje kusa da XEE tare da sunkuyar da kansa dai dai kunnanta Yace “My luv xo kiji
Ahankali tace mai “bafah saurayina bane😔
“Makawo ne kawai xaki gayama hakan ya yarda shima dan baya ganine
Wlhi ko kitashi kona 6ata tunanin mutum yan xun nan
“Idan nawa ne ai gadad’e da 6ata shi.
“Ina nufin na qazamin saurayin naki.
Allah in baki tashi ba xan baki kunya
Yana fad’in hakan ya miqe daga cakuɗa mata lissafin da yayi
Ahankali XEE ta sakar ma saurayin da suke hira murmushin yaqe. Ganin yanda ya kafesu da ido daga shi har na SAILUBAH
Ganin hakan yasa taqara da cewa “xanxo in ɗan jishi kad’an👌🏼
“Qaninki ne. Saurayin ya katseta da fad’in hakan
Ahankali cikin in i na tace
“A….. ina… nufin aa… Shi wannan ina ne
“Shi miye naki….
Rintse idanta tayi tace “shine wanda xan……
“Haba XEE miye haka me kike San cewa….. Cewar SAILUBAH
Kallan KHAMIS XEE tayi ahankali…. Ganin yanda yayi kicin kicin da fuska shi yasa duk tarasa nutsuwarta
Baxata yaudari kanta ba..
Dan San KHAMIS take da gaske
Bata san 6acin ransa
Dan haka sai kawai tatashi da kama hannunsa tace “muje ka gayamin
Murmushi KHAMIS yayi cikin farin ciki Yace “muje ciki gun kakah dan kijini dakyau
Aiko ba musu KHAMIS na gaba XEE na binshi a baya tamkar raqumi da akala haka su SAILUBAH suka bisu da kallo har suka shige falo……
Suna shiga falan KHAMIS yace “Miye haka my luv bakisan xan iya kisa akanki bako
Shafa kansa tayi cikin wani hali tace “Sorry mana my baby
Ba gashi ka tasoni kuma nataso bah
“Kar kiyi wani min dad’in baki.
Dan wlhi ba fahimtarki xanyi bah
Ke kinsan yanda naji axuciyata ganinkin da nayi dashi kuwa
“Ya Allah…… Nifah bani san mita
“Ai kinyi abin amiki ne da bakiyi ba ai ko kusa baxan miki
“Toh ya isa haka ai naga ya wucce ko
“Ni bai wucce aguna ba. Harsai kinyi min alqawarin baki sakewa
“Wannan shine kawai abinda yasa annurin fuskarka d’aukewa
Harararta yayi da cewa “Allah xan hukuntaki
“Allah baxaka iya ba
“Danna damu dake ko
“Ko shakka babu
“Toh kidena haka pls
“Nace maka nadena ko
“Anya my luv xakimin ladabi idan kukayi aure kuwa
Harararsa tayi da cewa “Dubawa xakayi
“Idan nace xan duba yanxu ba shakka xan tabka aika aika
“Idanko hakane ba makawa sainasa an kullemin kai
“Idan aka kulle miki ni kiyi rayuwa dawa
“Inyi da wancan qaxamin saurarayin mana
“Toh ya isa haka malama muyi hira can
“Angama my baby…….
SAILUBAH Ko tari ne ya kamata tayimah samarin murmushi yaqe dan duk haushin XEE ne ya kamata…….
Kanta tattaro abin cewa sai ganin RAMADAN tayi yana shigowa aiko nan take gabanta ya bada dam….
Dan tafi kowa sanin sharrin RAMADAN yanxu saiya canja tunaninta
“Auntyna hira kikeyi…
“Eh menene
“aa ba komai ina Aunty XEE
“Tana ciki… Je kace mata ana jiranta
“aa
Da mamaki SAILUBAH ta kallesa jin yanda yace mata aa
D’aure fuska tayi tace “Baxa kaje ba
Aiko nan take yayi kicin kicin da fuska Yace “Ni dai gaskiya baxani ba…..
Waro ido SAILUBAH tayi 😳 cike da mamaki tace “me kace
Turo baki yayi gaba cikin rashin kunya Yace “ai Abba yace idan kikayi baqi kidinga kirana ina tayaki hirar
Shine yanxu da baki kirani ba naxo Amma kuma saiki korani ciki bayan Aunty XEE bataxo gidan nan ba…….
Salati SAILUBAH tasaki tana me tafah hannu cikin mamaki dajin kunya Tace “wai yaushe kakoyi qarya ne RAMADAN yaushe kukayi haka da Abbah..
Harararta yayi ya ta6e baki xaiyi magana saiga Abba ya shigo
Cikin sauri RAMADAN yaje ya tar6i Abban yana cema Abban cikin d’aga muryar yanda su SAILUBAH zasu jishi “Abba kaga wa’yancan ‘yan iska ne kuma sunxo wajan Aunty ne dansu 6ata mata tarbiya wlhi y’an iska ne Abba
Tsura musu ido Abba yayi yanaso ya fahimcesu dakyau
Eh lalle ba masu hankali bane
Dan da sun gaishesa dan ko makawo ne ya yafa fuskar SAILUBAH ya shafa tasa. To ba shakka nan xai gano kamanninsu
Toh bare su masu ido ai ya dace suyi aiki da hankali
Suko mamakin RAMADAN ne ya kamasu.
Eh da gaske su y’an nanaye ne
Amma sun fahimce idan SAILUBAH da XEE abud’e yake. Dan haka suka nemi canja salo. Amma kafin su cimma burinsu KHAMIS ya d’auke XEE. Ga RAMADAN kuma ya jefesu da wata kalma. Kodai ya sansu ne
Cikin nutsuwa Abban Yace musu “kuyi hakuri na bada y’ata bani san qara ganinku a cikin gidan nan.
Ke kuma Ki sameni aciki
Yana fad’in hakan ya shige shashinsa
Ahankali cikin mutuwar jiki SAMAREEN NAN suka ficce daga gidan
SAILUBAH da tayi suman xaune ganin ficcewarsu ta farfad’o idanta cikin na RAMADAN tatashi da qaraso gabansa Tace “hmmm wato kai AMAKURCIN KA saika rabani da kowa ko
Girgixa mata kai yayi alamar aa ba haka yake nufi ba
Wata shegiyar harara ta auna masa kana tace “toh me kake nufi
Ahankali Yace “Aunty kiyi hakuri baxan qara ba……
“In bakamin shuru ba wlhi saina makeka
Kaxauna ka shararamin qarya. Da makirci kala kala Amma daga baya kadinga bani hakuri
Toh wlhi bari kaji idan ka qara ganina da wasu samareen kaxo ka rabani dasu narantse da Allah saina maka abinda baxaka ta6a mantawa ba
“Auntyna baxanma Qara ba dan Allah kiyi dariya inji dad’i kinji
Harararsa taqara yi xata juya dan barin gun yayi Saurin riqo hannunta yana me marairai ce mata Yace “pls mana my Aunty
“Da sharad’in har cikin xuciyarka baxa ka sake ba.
“Eh Aunty na yarda baxan sake ba
Jan hancinsa tayi tare da sakin murmushi tace “toh nayi
“Toh naji dad’i
“Kajirani bara inje gun Abba naji shi kad’an👌🏼dan akwai maganar da xanyi dakai
“Akan miye Aunty
Waifah wani d’an abokin Abban ne yake sona
Shine Abban yake gayamin d’axo har yana cewa in ban amince ba wlhi xai aurar dani sadaka ga duk Wanda Allah ya nufah
Waro ido😳 RAMADAN yayi cikin tsoro Yace “kinsan fah wannan karan abin xaiyi tsanani fah
Kinsan halin Abba sarar
“Tsoran da nake yi kenan QANINA duk kaine ummulaba’isan komai ai
Kai kake cutar dani akan hakan
“Aunty nadena daga yau kije kiji me xai ce miki anjima da daddare xanxo mushirya komai
“Owkie….. XEE na ciki in kana neman KHAMIS
Tana fad’in hakan tayi part d’in Abban nata
Ganinsa tayi yana safa da marwa. Tanemi gu ta xauna Cikin ladabi tace “gani Abba kayi min afuwa bansan haka suke ba
“Na yaba da hankalin RAMADAN baxai min qarya ba
Wannan shine maganata ta qarshe dake
Wlhi wlhi wlhi Fatima kifuta daga idona
Bar ganin wancan ya mutu kiyi tunanin xansa miki ido sai yanda kikayi……
Hmmmmm tunda ke haka Allah yayiki da jaye jaye…. Toh na baki nan da sati hu’du ki kawomin wanda yayi miki
Kika xarce hakan xan aurar dake ga d’an aminina ai namiki maganarsa d’axo kinjini ai….
D’agamai kai SAILUBAH tayi
“Toh sai ki tashi kibani guri ai
Ahankali SAILUBAH tatashi taficce daga d’akin
Rahamat Nalele💋
[9/11, 3:51 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*6
RAMADAN ko gurin FAWAS ya koma
FAWAS Yace “naga sunfice batare da sunce komai ba
“Eh sharri na qala musu gun Abba shine Yace su fitan masa agida yayima ‘yarsa miji
“Wai dan Allah In tambayeka San Aunty LUUVAH kake da kake korar mata samari
Kallansa RAMADAN yayi yana murmushi kana Yace “hmmm dubawa xakiyi
“Ai naduba ne shiyasa na tambaya.
Yanxu idan aka baka Aunty Luuu sai ka iya mata kishiya gaba ko. Dan nalura kamar xakayi futuna. Duk da ba alamu ka nuna ba.
Dariya RAMADAN yayi sosai 😀 yace
“Alamu sun nuna sam HAMEEDAH baxata… maka yawa ba ko.
“Hmmm ina tunanin ko ukunta nasamu baxa sumin yawan ba… Dan inaji ajikina kamar nid’in me lafiya ne
Murmushi RAMADAN yayi Yace “Idanko haka ne nafika lapia yanda nakeji a jikina
Murmushi shima FAWAS d’in yayi da cewa d’an iska. Ila irinku ne wa’yanda idan anyi kuke kasa saka kwai a kwana uku kud’au shekaru ana abu d’aya
Kallan FAWAS sosai RAMADAN yayi da Murmushin dai akan fuskar tasa Yace “dake ba Aunty XEE bace taka ta KHAMIS ce da xan iya ce maka idan hakan ta faru na samu Auntyna ila a daran farko in iya jefawa takira matarka tana me ce mata dama haka RAMADAN yake😭….
Dariya FAWAS yayi sosai Yace “wayaga daran farkwan FAWAS da HAMEEDAH yana me gyara tunaninta
Tashi RAMADAN yayi yana dariya Yace “shegen nawa. Har ka hangoka ko. Toh tsaida tunaninka dakyau….. idan kamantane in tunatar dakai. Cewa tayi ita xata nuna maka yanda aure yake.
Kaga ko xama xakayi ka fuskanceta dakyau cikin wannan daran ta gyara tunaninka da setashi tad’uraka akan hanya
Yana fad’in hakan ya bar shi nan
Sai hakan yayi dai dai da qarasowar KHAMIS
WlHi kidena San KHAMIS da yawa…. Kisani fah duk wannan abun da kuke iyayanku ba yarda zasuyi da maganar auranku ba
Kawai ya wani xo ya tadaki kina hira da wa’yanda suka dace dake. Wlhi kiyima kanki fad’a Sam abinda kike tunani baxai tabbata ba
Yanxu ke bakijin kunyar Ki fito kice wai KHAMIS shine wanda xaki aura
Idan ban manta d’axo ba kamar hakan kikaso cewa
Tashi XEE tayi cikin takaicin maganganun SAILUBAH Tace “kinga malama kibarni haka pls
Akan wane dalili xaki sakani gaba da fad’a kullun dan kawai ina soyayya da qaramin yaro
Ko kin manta cewa annabi Muhammad sallallahu alaihiwasallam shugaban manxanni ya auri Nana khadija shekarunsa basu kai nata ba
Gaskiyane Allah yayi Gaskiya dan ya nuna mana hakanne danya tabbatar mana da cewa babu illa akan hakan halak ne ba haram ba
Ina San KHAMIS ina qaunarsa over
Pls kigyara tunaninki Ki fahimce me nakeji Ki tausayamin dan bani nayi kaina ba. kiso soyayyata da KHAMIS sannan kiduba rayuwarki da yanayinki dan kindad’e da faɗawa tankwan dana fad’a
“Ban bahimci me kike nufi da qarshen furucunki ba
Harararta XEE tayi tace “haka xaki qare ai
Gwarani nasamo bakin xaran harna magancema kaina. Fatana Allah ya dubeni ya mallakamin shi matsayin mijin aurena
Tsaki SAILUBAH taja tace “Baki da hankali
Tace “Naji d’in🤷🏼♀
Can naganosu ni Rahamat a qauyan takai KHAMIS RAMADAN suna cikin mota kamar yanda tsarin nasu yake
FAWAS ko ya tasa HAMEEDAH a gaba yana 6ata tunaninta
Itako tayi shuru sai d’aukar darasin nasa take
Can ta kallesa dakyau tace “kasan miye
Yace “saikin fad’a
“Yau da safe kawummun yaxo yanata min fad’a akan wai ina xaman banxa naqi fudda mijin aure
Dan haka ya yanke shawara akan in fidda miji nan da sati d’aya
Idanko ban fitar ba. Toh ba shakka xai auramin aure da wani abokinsa
Sainace mishi ni bani da samari sai Yace shikenan xai bani kawai abokin nasa
Dan haka nan da sati biyu xa’a d’aura min aure dashi
FAWAS naji tsoran karna ambaceka ne dan xaice Kayi qaramin Yaro
Amma bayan futansa saina lura da innah ta tausayamin karo na farko a rayuwata ni da ita
Duk da…. bataso hakan ba dan tunaninta waye xai dinga yima bauta amma ta tausayamin dan sanin halinsa ya fita mugunta
Ta tabbatar xai aurar danine ga mutumin da xai dinga cutar dani
Dan haka saita tacemin ko ina da wanda nakeso
Na gaya mata labarinka kuma ta jinjina dan kasan cewarka qaramin Yaro
Ta tambayeni ina sanka ahaka
Na tabbatar mata da hakan
Tace tunda hakane in gaya maka katuro iyayanka xatayi magana da kawunnamu
Amma kafin nan tana so taganka ku shiga kugaisa
Na tambayeta dalilinta
Ta tabbatarmin da cewa tadena cutar dani arayuwa kuma xata shige gaba wajan ganin kaxama miji agareni
Bata d’auki lokaci ba ko takirasa tace mai ina da wanda nakeso amma qaramin Yaro ne
Nan ya hau fad’a wai shi baxai aurar dani ga qaramin Yaro ba. Kalan mutan qauyan nan sufara yi dashi dan yaga bashi ya haifini ba
Tayi qoqari sosai wajan ganin tashawo kansa
Daga bisani yayi jam alamar ya shiga tunani
Sanda ya kammala tunaninsa tsaf Yace min yaran d’an birnine
Nace mai eh
Yace toh ince maka katuro iyayanka nan da kwana uku
Idan baka turosu ba wlhi xai aurar dani ga amininsa…,..
FAWAS ya fad’i maganar ne da dariyar mugunta
Ganinsa baxaka iya turo iyayanka ba.
Tana kaiwa nan a xancanta ta durqusa gaban FAWAS d’in cikin xubar da hawaye tace……
“Katemaken FAWAS
Kaji tausayin qauna
Ka rufama xucita asiri
Kamin sitira da bargwan qauna
Kayi qoqarin killaceni a bayan xuciyarka
Karka barni inje hannun wanda xai cutar dani
Kasani ni marainiyace
Tun farkwan ganina dakai ka kwarema xuciyata karan farko a rayuwata
Wlhi idan baka maidani ‘yar gatanka wajan aureni a wannan lokacin ba xan fad’a cikin quncin rayuwa
Nasani iyayanka baxasu yarda su maka aure yanxu ba. amma karoqesu kace ni marai niyace
Kuma idan suka rabani dakai ba shakka mutuwa xanyi
Kace musu alhakina ya rataya a wiyansu
Ina maka wani s……..
“Kina min wani SOO Wanda bakisan yaushe bane hakan tafaru ko…… FAWAS ya katseta da fa’din hakan
Cikin sauri ta d’agamai kai.
Da Murmushin yaqe Yace “hmmm HAMEEDAH kenan. Tunaninki ban sanki ba……..
Gaban HAMEEDAN ne yayi wani mummunan fad’uwa… Taqara kallansa a furgice tace…..
“Me kake San cewa
“Abin da nake San cewa shine. Nariga da na sanki tun ranar gamuwarmu dake
Tun ranar nasan na kware miki
Tun ranar nasan nayi nasarar sace xuciyarki
Xanso kitashi Ki shiga cikin gida
Dan xuciyata ta fara rayamin in kama fuskarki in lashe hawayan da kikamin asarar xubansa
Bayan kin wanke fuskarki inaso kicema inna gamunan shigowa gaisheta
Sannan ina miki albishir da cewa kwanakin da kawu ya ibar min Sha Allahu baxasu qareba iyayena zasuxo gareshi……
Saukar da wata naunauyiyar ajiyar xuciya HAMEEDAH tayi ha’de da Murmushin samun nasara… Tace
“Har narasa ta ina xan fara murna
Murmushin luv ya sakar mata had’e da shafa gefan fuskarta Yace kifara tako ta ina yayata
Tashi tayi tana cewa “Da kai mijina ne dana aiwatar da wani abu gareka yanxu
Waro ido yayi😳 kad’an👌🏼 yana mai cewa “kwana nawa ne ya ragemun yayata
Pls aiwatar kawai
Cikin shagwa6a tace
“Xa’a d’aukeni ‘yar iska ne ai
Kuma kaga bai dace ba
Yace “hmm ai bangani ba. kedai Jeki dan naxaqu in ganni agida yanxu
Shigewa cikin gidan nasu tayi tana Murmushin samun nasara
KHAMIS ya kalli RAMADAN Yace “tajefah FAWAS cikin tashin hankali fah😳
“Wlhi kuwa……..
Xanso kaji yanda ta kulle tunanina🤔…. RAMADAN ya fad’i hakan cikin damuwa
“Kadubo mukullinka ka bu’de dan wlhi na fara tsorata da ita…. Cewar KHAMIS
“Namanta na baro mukullin a gida
(Yana nufin sai yayi tunani akan lamarin dakyau kenan👌🏼)
“Idan mun koma gidan pls kadubashi dakyau
(Irin yayi naxari akan lamarin sosai kuma cikin gaggawa)
“Ai wannan basai ka fad’a ba…… RAMADAN yabashi amsa da damuwa
Kan KHAMIS ya qara fad’in wani saiga wata qaramar yarinya tafito daga cikin gidansu HAMEEDAN tana cema FAWAS wai su shigo
Jin hakan yasa yaxo gasu RAMADAN masu yi masa la6e a soyayyarsa Yace suxo su shiga ciki dan gaida innah
“Toh suka cemai cikin sauri da fitowa🙂
BY RAHEEMAT NALELE
‘YAR MUTAN FULANIN KHATSINAWA
Hajju💁🏼
[9/12, 8:47 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*7
Koda suka shiga gidan ganin taburma sukayi a tsakar gidan shinfid’e xamansu kawai take jira
Dan haka suka xauna ga taburmar suna masu gaida innan wacce take xauna akan kujerar tsugunno
“Madallah samari Allah yay muku albarka
Wanene FAWAS din cikinku dan naga duk kusan kamannin naku d’aya
Dake duk kan nasu a sumkuye yake shiyasa KHAMIS da RAMADAN d’agowa suka kalleta tare da nuna mata FAWAS wanda ya qara sunkuyar da kan nasa qasa
Masha Allah…..
Yanda nayi xatanku ashe ba hakan kuke ba
Gaskiya ne baxa a kiraku da yara ba
Dan da a qauyan nan kuke ba shakka da kuna da yara uku zuwa hud’u…..
Wayar KHAMIS ce tayi qara ya duba me kiran nasa yaga momyinsa ce hakan yasa ya kalli innan da Murmushi yace “Toh innah xamu tafi
“Kai haba tun yanxu har ina sawa a sako muku d’an malele…..
Saurin tashi RAMADAN yayi yana cewa “ai innah yanxu ana jirammu ne idan muka kuma xuwa maci😆
Ya fad’i hakan da ajiye mata dubu biyar….
“Tace toh nagode Allah yay muku albarka Ku gaishemin da iyayan naku da kuma fatan kai FAWAS HAMEEDAH tagaya maka saqo
“Eh innah tafad’a insha Allah zasuzo
“Toh Allah yasa saika hanxarta dan kawun nata bashi da Sauqi
“Insha Allah komai xaixo yanda ake so….. yace da ita hakan da tashi shi da KHAMIS suka ficce
Da gangan RAMADAN ya tsaya gyara takalminsa
Sai hakan yayi dai dai da jeruwarsa da HAMEEDAH wajan fitowa
Baiyi nauyin baki ba wajan ce mata…..
“Kamar kinji tsorona
“Akan wane dalili xanji tsoranka
“Gani nayi dan kawai ina xarginki bai dace kinemi amiki auran daba shiri ba
“Wai miye tunaninka akaina RAMADAN
“Kawai dai ban yarda dake bane
“Saboda kana da wani kwulli acikin xuciyarka
“Ko kad’an… Xuciyar ce dai batayi na’am dake ba
Kallansa tayi dakyau kana tayi murmushi da cewa “Abin mamaki
Toh idan duba kake ka dena
Dan wlhi baxaka ta6a yin nasara akaina ba
“Wow dama abin haka yake….. Ai banyi tunanin da gaske ked’in bame gaskiya bace
Xan baki shawara idan kin d’auka ta amfaneki idan kinqi kifad’a tarkona
Wlhi idan kika sake kika cutar min da aboki nayi rantsuwa da Allah saina d’auki mummunan mataki akanki……
Yana fad’in hakan yabarta nan xuciya cike da mamakinsa
Yana lura da yanayin da RAMADAN ya fito dashi
Ba shakka akwai abinda yake faruwa da shi da HAMEEDAH
Musamman itama da yanayin da tafito dashi
Tunanin hakan da FAWAS yayi ne yasashi sakar mata murmushi da cewa “Nadai gaya miki kiyi hankali da RAMADAN dan duk inda kikayi xatansa ya wucce nan
Gayamin me kuma yanxu yace miki wanda ya d’aukemin farin cikinki da annushuwarki
“Hmm abokinka RAMADAN bashi da kirki
Tunaninsa kamar xan cutar da kaine
Na lura kamar baya sona dakai
“Kingani ko
Ko anan ya rigada ya 6ata tunaninki
RAMADAN yafi KHAMIS bani qarfin gwiwa asoyayyata dake
Shege ne….. Nasan akwai dalilinsa na damunki akan kiriqeni amana……
Pls karki cutar dani HAMEEDAH…..
Ina miki wani soo Wanda bansan ya akayi ya shigeni ba
Yafi qarfin akirashi da MASEEFAR SOO
Ki gayamin da wane suna ya dace in kirashi dashi…….
“Na shiga uku ni HAMEEDAH… Me xanji daga bakinka FAWAS
Yanxu daga wannan maganar har xuciyarka ta fara shiga shakku akaina…..
“Ko kad’an tauraruwata…
Na rigada nayi nisa asanki
Ban ta6a kawo wani mugun tunani akanki ba
Karki damu da RAMADAN
Shiba me duba bane dako yaushe komai yayi harsashe saiya kasance
Wlhi sanki dai nake da gaske yayata
Ba wani abu me suna kalma ko akasin hakan da xaisa yardar da nayi dake tasami tangard’a acikin xuciyata
Jan ajiyar numfashi tayi cikin gamsuwa da kalamunsa Tace “nagode mijina……
“Naji dad’in sunan sosai👌🏼
“Ni kuma naji dad’in yanda kaji dad’in hakan
Dan har naji kwad’ayin in qara fa’din maka wata Kalmar wacce xatafi wannan yimaka dad’i
Murmuahi yayi da cewa “aa kibarta
dan natabbatar xaki fad’i wacce xata hanani kaiwa gida lafiya ne
“Toh miye amfanin wa’yan can…. Basai su xama direbobinka ba
D’aya na tuqaka d’aya nayi maka hira me dad’i da dad’ad’awa
“Gaskiya yayata…. Mijinki kawai kika sani
Kinga KHAMIS yana da Aunty XEE
Haka RAMADAN yana da Aunty LUUVAH
Duk suna ji dasu
Barni dai in lalla6a ahakan inkai gida lafiya….
‘Allah kabari in gaya maka….. Namaka alqawarin idan aka samu kuskure ganina xakayi kawai gefan gadanka ina meyi maka fifita da mayafina da kuma shayar dakai …
Waro ido FAWAS yayi.
Ganin hakan yasata rufe fuskarta Da shegewa gidan nasu
Murmushi yayi da shigewa motar tasu yana mamakinta
RAMADAN ya ta6e baki dajan motar
Komadai miye FAWAS yaji xuciyarsa tana masa rawa akan dagula lissafin da RAMADAN yakema tunanin HAMEEDANSA
Ya sani sarai RAMADAN sai ya hangi wani abu yake cusa kansa ga koma miye
KHAMIS ko harga Allah yanxu HAMEEDAH tafara ficce mishi arai
RAMADAN ko yana tsintar kansa a fad’uwar gaba idan yaga HAMEEDAN kamar yanda na gaya muku a baya
Yana kuma jin qaunarta aransa irin na kamar ‘yar uwarsa haka
Sannan kuma xuciyarsa taqi yarda da gaskiyar soyayyar da takema FAWAS
Bai daiji tsanarta aransa ba
Amma yasani yafi kowa sanin kansa
Tunda ya fara jinta a hakan
Ba shakka wata rana xai iya jin tsanartan
Murmushi FAWAS yayi yana me kallan RAMADAN Yace “kadena 6ata min tunanin matata
Murmushi RAMADAN yayi da cewa “Xanso naji me tace akaina
“Toh baxakaji ba.
Amm yauwa nasan kunji komai daya wakana tsakanina da ita.
Pls Ku gayamin ta ina xan fara
” Kafara ahankali. Dan nalura tagama 6ata tunaninka gabaki d’aya…. Cewar KHAMIS
Murmushi RAMADAN yayi da cewa “kaje kasa Dadynka agaba
Dake yanaji dakai fiye da momy wala Allah mudace.
Allah yasa mudacan dan jinake idanna… rasata mutuwa xanyi Wlhi
Ina Santa over
Shuru suka masa har suka iso gida..
Bai damu ba dan yasan iskansu ne ya motsa
*Wannan kenan*
“Kaji abinda Abbana yace min RAMADAN
Kuma wlhi na yarda da xancanka wannan karan da tsanani yamin maganar
Ina jin tsoran kar ya had’ani da d’an aminin nasa kamar yanda yace…
Nifah Sam baiyi min ba
Wani baqi dashi
Bai cika kyau ba
Kuma gashi gajere
Saidai yana da dad’in murya
“Toh ya akayi kika san hakan atare dashi bayan ba ta6a zuwa gareki yayi ba
“Bayan fitanku d’axu naji wayata na ringing
Ina d’auka ya tabbatar min da shine
Sainace mai ya turomin da pix nashi ta Facebook
Wlhi tsabagen takaici baisani bari kadawo ka gansa ba na goge hotan
Jan mufashi RAMADAN yayi
Cikin wani hali Yace “Aunty akwai sauran lokaci.
Karkiji komai dan ina tare dake
“Kana nufin kar in tada hankalina
Kuma in saki baki inyi bacci har sai randa lokaci ya quremin sannan kaxomin da burkitaccen labari
Wanda na tabbatar da sai xuciyata ta buga dan takaicinsa
Gaskiya ina……
kabani shawara kawai yanxu…. tunkan dare yamin in rasa hanyar 6ullewa
Saukowa yayi daga kan kujerar da yake
Ya durkusa a gabanta tare da kama hannunta yana me Kallan kwayar idanta
Cikin wani hali Yace “Aunty kiyarda dani
Inasan inyi xama na musamman dan baki farin ciki
Kisani Aunty baxan miki wasa a wannan lokacin ba….
Ya qarashe xancan nasa da aika mata da wani shu’umin kallo wanda yake da tabbacin koda xata qara masa wata magana toko baxata wucce cewa ina jin bacci ba…..😍
Kamar yanda yasani ko hakan ce ta kasance dan Jikinta ne yafara mutuwa
Yayinda takejin wani abu yana yawo acikin jikinta
Ga wani xare da yake futowa daga cikin kwayar idansa yana shigowa nata.,…
Ji takeyi xuciyarta na muntsininta sakamakwan shu’umin kallan da yake aika mata dashi
Cikin wani hali tace “Me yasa naji wani abu na yawo acikin jikina sakamakwan wannan kallan da kake aikamin dashi…..
Murmushi yayi da sakar mata kiss a hannun nata Yace “ban San dalili ba Auntyna.
Fatana dai Allah yasa lapia kike…..
Yanda ya sakar mata kiss d’in taji hakan har cikin xuciyarta
Hakan yasa tayi saurin rintse idanta
Sai hakan yayi dai dai da kammala furucinsa
Cikin matuqar shagwa6a tace mai “Bacci nakeji…..
Murmushi yayi da sakar mata hannun ya miqe yana me shafar fuskarta cikin Murmushin Yace Ki kwana lafiya my Aunty
Sannan kiyi mafarkina
Dan hakan xai faranta raina sosai…..
Yana fad’in hakan ya ficce daga falan
Rintse idanta tayi had’e da dafe kanta.
Tana me cewa na shiga uku ni SAILUBAH
Meyake shirin faruwa dani.,..☹
Bana jin hakan ga kowane d’a namiji me yasa nakejin hakan ga RAMADAN
Wayyo🤦🏼♀ Allah ni SAILUBAH Allah kamin maganin RAMADAN danya fara fitinar ruhina…..
Khaka ce tafito tana ce mata “ke kuma miye haka..
Kina daga xaune ke d’aya kina sambatu
Shuru SAILUBAH tayi mata da tashi ta shige d’akinta
Dad’inta tayi sallar i’sha da wanka.
Dan haka canja kayan bacci kawai tayi da miqewa akan gadanta……
KHAMIS ne ya kira RAMADAN wanda fitowarshi kenan daga wanka
Kallan agogo yayi yaga qarfe gama Sha d’aya ne na dare
Cikin tsokana Yace mai “Kaga malam kaje kaji da Aunty XEE yauma ba zuwa club
“Kasan dai tunda bature yayi waya kobanje gareta ba yanxu zanji muryarta dakyau
Am ba wannan ba
Nakiraka ne naji kayi tunani akan waccen ‘yar wasan can
Dariya RAMADAN yayi sosai kana Yace “wai kana nufin HAMEEDAH
“Eh mana
“Hmmm har kasa mata suna da ‘yar wasa
“Ta iya bugawa ne ai
“Nayi tunani sosai
Kamar tana sone tasamu FAWAS cikin gaggawa dan qaramin tunaninta da ganin kamar xai iya kufce mata.
Tana da wani nufi akansa wanda ni baxansan miye ba
Wannan shine kawai labarin
“Zako taci ubanta idan Tace da nufi xata auresa….. KHAMIS ya fad’i hakan
“Na lura tana da wayo amman bata da dabara. Yanda dai na fahimta
“Koma dai miye lokaci xai bayyana kansa
“Ina fatan ya bayyana mana alkairinsa…. Fa’din RAMADAN
“Amiien…. Cewar KHAMIS
FAWAS ko bayan ya kammala shirin baccinsa…
Nufar Dadynsa yayi cikin tsoro
Yako taki sa’a momynsa na tare da Dadyn nasa
Ganin hakan yasa tsoransa ya qara tsananta
Ahankali yaje ga Dadyn nasa ya lafe ajikinsa Cikin nuna qaunarsa ga mahaifin nasa
Kana ya kwantar da kansa a cinyar mahaifin nasa yana me kallansa a d’an tsorace
Murmushi momy tayi da cewa “Yaran nan da ana komawa ciki na tabbatar da komawa xaiyi cikinka
Murmushi Dadyn yayi yana me shafa kan FAWAS d’in Yace wai haka my son
Shuru FAWAS yayi yana me nuna alamun damuwa
Ganin hakan yasa Dadyn nasa tsayar da kallansa sosai akansa yana me cigaba da cewa……
“Me yake damun yarona naga kamar yana tare da damuwa……
Cikin dauriya FAWAS ya kama hannun Dadyn nasa Yace “Pls my Dady….
Dan Allah xan roqeka wani abu ina rokwanka da Allah kamin shi
Cikin nuna tabbaci Dadyn ya rufe idansa ya bud’e kana Yace ina jinka my son fad’i menene
Ahankali ya kalli momynsa sannan ya maida kallansa ga Dadyn nasa Yace “Aure nakeso kamin Dady dan soyayyarka da Allah da Manzansa annabi Muhammad sallallahu alaihiwasallam………….
BY RAHEEMAT NALELE
‘YAR MUTAN FULANIN KHATSINAWA
Hajju💁🏼
[9/15, 2:53 PM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*8
Saurin tashi momy tayi… Cike da mamakin d’an nata
“Aure Aure… Aure kakeso FAWAS
kallanta yayi da d’aga mata kai……..
Dadynsa ko rintse idansa yayi da fad’awa tunanin me yasa hakan yaxoma d’an nashi lokaci d’aya
Lallene baka tara sani da Allah. Banda haka da yasan yaran nasa xai fad’a soyayya da wuri haka da tun da wurin xai d’auki mataki
Afusace momy tadallah masa harara da cewa “tashi kabama mutane guri
Kama hannun Dadyn nasa yayi cikin matuqar damuwa kamar xaiyi kuka Yace “zakamin Dady
Ahankali Dadyn ya shafa kansa damuwa qarara akan fuskarsa Yace “kayi yaro my son. Kuma shi aure anayinsa ne da aiki da hankali
“Dady kai kad’ai ne xaka fahimceni. Dakai na dogara
Wlhi Aure nake so….
Ina san HAMEEDAH irin sannan da ake kira da maseefa
Dady idan na rasata mutuwa xanyi
Wlhi ina Santa
Dan Allah karka bari na rasata. Dan Santa nake da gaske.
Xan iya rasa rayuwata idan ban aureta ba…….
“A ina take… Wacece ita… my son
Kuma yaushe kuka fara soyayya da har kaxo gareni ba kunya kake cemin aure kake so
Lumshe ido FAWAS yayi hawaye ya xubu masa cikin matuqar tashin hankali
Yafi kowa sanin Dadynsa idan xaiyi maka abu kaji yana jero maka tambaya akan wannan abun toko ba shakka ko baxai maka wannan abun ba
Tunanin hakan da yayi ne yasa shi fidda hawaye
Wlhi San HAMEEDAH yake da gaske
Ji yake idan ya rasata mutuwa xaiyi da gaske
Dan haka baisan lokacin daya fashe da kuka ya tashi dayin part d’insa ba….
Binshi da kallo momy tayi cikin matuqar mamaki
Lalle in kana duniya xakaga abu iri iri
Yaran nata kwaya d’aya wanda taci burin San ganin bikinsa bayan ya kammala makaranta da xama cikakken Namiji shine yanxu xaixo ya 6ata mata shirinta lokaci d’aya….. Ina…. Da sake wlhi….. Kuma wacce shegiyace ta 6ata masa tunani saidai tabar mata d’anta dan ubanta…..
Afusace tatashi dan taje taci masa mutunci dan in wasa yake to yadena….
Kama hannunta taji Dadyn nasa yayi mata
Cikin nutsuwa Yace “Ina San Yaro na. Kuma kinfi kowa sanin ina mutuqar qaunar farin cikinsa
Tunda har kikaga yaxo yace aure yake so… Toh xan masa…. dan baxan bari d’ana Wanda na mallaka kwaya d’aya ya lalace bah
Kinfi kowa sanin FAWAS yana da nutsuwa da hankali
Ki godema Allah daya axurtaki da kamarsa….
Kisani xamani ya lalace
Ba kamar yanda kika sanshi a xamaninmu bane
Idan naqiyi masa na tabbatar xai shiga shashanci ne da matan banxa
Bana fatan hakan taxo daga xuri’ata
Ina umartarki da amatsayina na mijinki da karki qara cewa komai akan auran da xan masa
Yanxu kibini muje garesa inji a ina take yarinyar……
Fashewa da kuka momy tayi
Ranta yayi MASEEFAR 6aci jin furucin mijin nata
Taji tsanar HAMEEDAH sosai acikin ranta
Babu amfani da tsaya tana sa’insa da mijin nata dan tafi kowa sanin waye shi
Idan yasa abu aransa xaiyi…. Ba wanda ya isa ya hana Sa sai ubangijinsa
Sannan ko wacece wannan HAMEEDAN tacuceta
Kuma baxata ta6a qaunarta ba
Sannan badai suxauna mata a gida ba
Wai wannan wane irin cud’add’an al’amari ne…..
“Ba kuka xaki tsaya kina min ba kawai muje inji ta bakinsa
Batayi musu ba ta goge hawayanta sannan suka nufi part d’in FAWAS
Shiko FAWAS kuka yake sosai
Dan Sanda hakan tafaru sannan ya dad’ajin MASEEFAR SON HAMEEDAH taqara mamaye xuciyarsa
Har wani abune yaji yaxo ya tsaya masa a qirjinsa….
Jin an ta6ashi shi yasa ya kalli wanda ya ta6ashin
Ganin Dadyn nasa yasa ya rungumeta yana cewa “WIhi ina Santa Dady
“Naji my son… Gayamin a ina take…..
Da sauri FAWAS ya kalli Dadyn nasa Yace “Dagaske Dady xaka auramin ita
“Koda xan aura maka ita my son aisai naji bayanai akanta ko
“Gyara xama FAWAS yayi yashiga ba Dadyn nasa labarin HAMEEDAH tiryan tiryan bai 6oye mishi komai ba….
Aiko yana kaiwa aya momy ta wanke shi da mari
Tana fad’in kayi qarya ka Auro wacce ta xarce shekarunka
Ashe kai Sha Sha Sha ne sakarai ne ban sani
Karasa wacce xakace kana so sai wacce ta girmeka
Toh wlhi bari ji…….
“Bance Kiyi shuru bane akan wannan lamarin
Kwafah momyn tayi jin furucin mujin nata
Dadyn ko shuru yayi na wani lokaci
Kana Yace “kace a QAUYEN TAKAI Take ko…
FAWAS wanda yasha marin baxata gun mahaifiyarsa d’agama Dadyn nasa kai yayi cikin matuqar damuwa
Dan tunda yayi wayo baxai iya cewa ga ranar da d’aya daga cikin iyayan nasa wani yakai masa duka ko mari ba
Amma gashi *SANADIN SOO* momynsa ta bashi cikakken mari
“Toh ai shikenan
Tunda iyayan nata sunce jibi sukesan ganinmu. Xamuje Allah yay mana jagora
Cikin sauri momy tace “Idanko kabiye masa xaka aura masa itan
Toh badai suxauna anan gidan ba.
“Ba damuwa sai suje su taya Adda Jamila xama…….. Dadyn ya bata amsa da fad’in hakan cikin kulawa
Aiko jin hakan yasa ranta dad’a d’aukar xafi taficce daga d’akin amutuqar fusace
FAWAS da Dadyn suka bita da kallo
“Yauwa my son ka kwantar da hankalinka kaji
Dama ina San magana dai akan karatunka
Ina San turaka qasar England dan kaci gaba da karatun acan
“Wayyo Dadyna……😳 FAWAS ya fad’i hakan a tsorace sannan yaci gaba da fad’in
Bana San rabuwa daku da RAMADAN da KHAMIS ga HAMEEDAH pls Dad kace min kafasa turanin pls…..
“aa my son baxan iya ba. Baxan iyaba Gaskiya
Xandai yimaka auran
Amma maganar tafiyarka karatu yaxama dole ne
Shuru FAWAS yayi yana tunanin anya xai iya rayuwa ba RAMADAN ba KHAMIS kuwa
Kawai xai cema Dadyn nasa ya yarda idan yayi masa auran in lokacin tafiyarsa karatun yayi saiya bijire masa
Kammala wannan tunanin nasa ne yasa ya dubi mahaifin nasa da murmushi Yace “nayarda dady inhar xaka nemamin auran HAMEEDAH
Ina Santa da yawa Dady.
Make qeyarsa Dadyn yayi cikin xolaya Yace watoh soyayyar HAMEEDAH tasaka ka xama mara kunya ko
Murmushi ya shiga yi yana me sunkuyar dakansa qasa da cewa
“Dady muje muba momy hakuri kaga tayi mummunan fushi dani
“Kamanta momynka ne idan tafara fushi ba’a tunkaranta alokacin. Koso kake ta rufe min kai da duka
Murmushi yayi da girgixa kansa da rungumar mahaifin nasa yana cewa “Ina matuqar sanka Dadyna
Shafa kansa Dadyn yayi Yace nagode yarona
RAMADAN ko wajan sallar asubane bayan sun dawo Dadynsa yake gayamai maganar qarashe karatunsa a qasar England….
Araxane ya kalli Dadyn nasa Yace “
“England… England fa kace Dady😳……
Pls dad kabarni na Aqarasa abina anan kawai. Dan baxan iya rayuwa awata qasa babu kai ba momy ba Auntyna ba FAWAS ba KHAMIS ba.
Dan Allah Dady ka temaken kajanye wannan furucin naka
“Baxan iya ba my son
Hakan shine xaman lafiyata da kwanciyar hankalina inhar ina sanka kusa dani.
Banasan kabarni ina matuqar sanka my son amma haka dole xaka qarashe karatunka acan
Jan numfashi RAMADAN yayi cikin matuqar tashin hankali Yace
“Dad ina maka ladabi akan komai amma wannan xai hanani nutsuwa da kwanciyar hankali
Kuma kaga bana san rabuwa Auntyna
“Ka kwantar da hankalinka my son idan xamu kai maka xiyara tare da ita xamu dinga zuwa
Dafe kansa RAMADAN yayi cikin matuqar damuwa batare da yaqara cewa komai
Ganin hakan yasa Dadyn rungumarsa yana me shafa kansa cikin matuqar so da qauna Yace “karka damu kaji yarona. Ina sone kayi ilimi me xurfi ka had’e komai da komai acan dan anan kasan d’aukar lokaci xakayi
“Dad wanda xanyi ma anan d’in ai yayi tunda ba sauri nake ba
“Inaso kayi da saurin ne
Dan incika *ALQAWARIN QANWATA* nasan Kayi karatu dakyau……
Tun bayau ba nake da niyar kaika kayi karatun acan… Toh Allah baiyi ba dan sona dakai kusa dani
“Wacece ita hakan wacce ban Santa ba. Ko bata raye ne
“Karka tambayeni magana akanta yanxu.
Ina so anjima nayi breakfast dakai
“Toh kawai RAMADAN yace mishi yana me faɗawa tunanin Wacece qanwar Dady wacce shi bai Santa ba
Shiko KHAMIS yana breakfast ne da iyayan nasa
Dadyn Sa Yace mai
“Inaso inkaika England ka qarasa karatunka acan dan ina so kayi ilimi me xurfi Cikin lokaci qanqani….
Atsorace KHAMIS ya furxar da ruwan tia d’in dake bakinsa ya miqe cikin tashin hankali Yace… “Wlhi Dady na hakura da karatun acan
Kabarni anan pls😰 dan Allah dan soyayyarka da manxan Allah
Da murmushi Dadyn ya kallesa Cikin mamakin tashin hankalin daya shiga lokaci ‘daya Yace “Xauna mana my son…
Gayamin miye matsalarka menene….
Cikin sauri da su6utar baki Yace “Aunty XEE wlhi Aunty XEE itace matsalata Dady
Santa nake da gaske. Idan na rasata mutuwa wlhi xanyi
Santa nake da Aure ina so kamin aure Dady……….
Shuru falan ya d’auka kamar ba abu me numfashi a cikinsa
Ganin yanda iyayan nasa suka xuba masa ido shine abinda yasa shi yin sak👌🏼
Hmmmm magana dai xarar bunu ce kuma ya rigada ya fad’eta
Shi kansa baisan lokacin daya fad’i hakan ba
Kawai maganganun sunxo mishi ne
Dake dama aransa suke
Ahankali ya kalli momyn Sa wacce tabala’in xuba masa ido
Ya maida kallan nasa ga mahaifin nasa shima yaga yanda yake kallansa
Saiya sunkuyar dakansa qasa cikin ladabi yaci gaba da fad’in
“Am so sorry my Dad mum
Yana fad’in hakan yabar falan xuwaga bedroom d’insa
Momy ta kalli Dadyn nasa tace “toh fah😧
Idan kunnena ya jiyemin xancan da yaran nan yayi yanxu yana nufin ya fara soyayya
Cikin wani yanayi Dadyn Yace “Ga xahiri nan kingani tunda har yana maganar Aure
Tashi momy tayi cikin tashin hankali Tace “kuma naji yana ambatan Aunty XEE
“Eh yana cewa ita yake so idan ya rasata mutuwa xaiyi ba
Dafe girjinta momy tayi cikin tashin hankali tace bafah wata bace yake kira da Aunty XEE baface Zainab ‘YAR Alhaji Murtala Y’a ga memunatu……
Da sauri Dady ya kalleta Yace ” Y”AR Murtala fa kikace
Tace “ko shakka babu ita yake nufi
Tashi yayi cikin sauri yayi bedroom d’in KHAMIS din ganin hakan yasa itama tabi bayansa
Shiko KHAMIS sauri sauri gudu gudu yake shirin ficcewa daga gidan dan yasan halin iyayan nasa sarai saisun biyosa
Musamman daya tafka wannan ta’asar da hausawa suke fad’in magana xarar bunu
Tab😌 yaushe xai iya barin RAMADAN da FAWAS…. Wlhi imma bacci su Dad dinsa suke saidai sudena danshi dai baxai je ko’ina ba…..
Wannan xancican da yake yine axuciyarsa
Da gudu ya shequ dan barin bedroom d’in nasa….. Aiko nan take sukaci karo da Dadyn nasa…. Yayi saurin ja da baya yana cewa “Sorry Dady
“Koma kaxauna muyi Magana ne….. Cewar Dadyn nasa
Kamar KHAMIS xaiyi kuka haka ya koma ya xauna kan bedsat
Dadyn ya xauna kusa dashi…..
Momy ko tana tsaye dan jira take hasashenta yaxama gaskiya taci qaniyar d’an nata
“Sonake ka gayamin Wacece Aunty XEE
Shuru KHAMIS yayi mai yana tunanin yafad’a mai ne ko yayi shuru da bakinsa
Kai gwara ya fad’i abinda yake ransa tunda ya faro.
Yana gama wannan tunanin sai yayi saurin durqusawa qasa ya kama qafar mahaifin nasa Yace “Kamin rai Dady karka rabani da Aunty XEE ina santa kuma munyi alqawarin aure ni da ita
Sannan ita ce Zainab ‘YAR Alhaji Murtala…..
Yana kaiwa nan. Ya fashe da kuka wiwi yana cigaba da cewa wlhi Dady in ban auri Aunty XEE ba mutuwa xanyi
Rintse idansa Dadyn nasa yayi….. kanya bud’e aiko saiji yayi……
Dim didi dim. Dim didi dim….
Momy tarufe KHAMIS da duka tako ta ina
Ranta ya bala’in 6aci… Kallo d’aya xaka mata kasan takai qarshe wajan 6acin rai
Daqar Dady kwaci KHAMIS a hannunta yana mece mata “Wai meyake damunki ne
Wannan bai isheki ishara ba
Wanna ai had’in Allah ne
Kuma baxanyima Allah budulci ba.
Idan har da gaske sukesan junansu shi da ita Zainab d’in toko na amince da soyayyarshi dan baxanqi aura mishi ita ba
Jin hakan da momy tayi shiyasata fashewa da kuka wiwi….. Tana me cewa “Aidama da hakan xaka fake
Tunda har yanxu kana San uwarta…..
Waro ido KHAMIS yayi yana kallan momynsa
Dadynsa ko cewa yayi “Subhanallahi…. Kedai bansan ranar da xakiyi hankali ba
Matar auran… Gaskiya baki da hankali
“Eh naji… Kafad’i koma miye dai dai da kaine
Tunda akwai wani abu aranka
Banda haka wane irin xalinci ne wannan da xaisa kace xaka aura masa wacce tagirmema shekarunsa haka
Toh Bara kaji narantse da Allah idan har nice na haifi KHAMIS baxai ta6a auran XEE ba. Idan uwarta tabi malamai tacusama d’ana soyayyar ‘yarta wlhi saitasha mamakin yanda xan wulaqantata
Dan idan ita sammako tayi toni ahanya na kwana………
Tana fad’in hakan ta karkata qeyarta taficce daga d’akin……..
“Dady gayamin meyake faruwa ne…..😳 Cewar KHAMIS
“Lokacin muna samari na ta6a neman mahaifiyar Zainab wato XEE kamar yanda kake ce mata
Toh dake ni da momynka had’in xuminci aka mana shine yasa ban samu na Aureta ba
Alokacin munsami rashin jituwa tsakanina dashi mahaifin ita Zainab XEE d’in taka
Dan har ya mallaki mahaifiyarta bata dena nuna mai tsana ba
Dan kasan bashi take so ba ni take so
Hakan yasa kishi ya shiga tsakanina da shi mahaifin nata
Yanda na nuna soyayyar ta qarara axahiri shiyasa momynka tayi mata mummunan tsana
Har yanxu a haka ake
Ba lefi idan na had’u da shi mahaifin nata yanxu muna gaisuwa sama sama
Wannan shiyasa kaga hankalin ita momyn naka ya tashi
Shuru KHAMIS yayi yana hararo matsalar da xai fuskanta nan gaba
Can ya kalli mahaifin nasa Cikin matuqar damuwa Yace
“Ina Cikin matsala….
Dan Allah Dady katemakeni kasan halin momy tana da matsala akan komai
Ba tsayawa take tayi naxari akan wasu abubuwan ba saikaga taxartar da wukunci……
Murmushi Dadyn yayi cikin matuqar qaunar d’an nasa
Yace “karka damu komai xaixo da Sauqi
“Na amince da tafiyata karatu Dady amma pls ka auramin Aunty XEE idan na dawo koma mai xai faru ya faru
Shuru Dadyn yayi
Can Yace “kasan yanxu fah dole asamu matsala da mahaifin ita Zainab my son
“Duk abinda xai faru dan Allah Dady karka bari nayi missing d’in Aunty XEE kaga har xaxxa6i ne yanxu ya kamani Dady…. KHAMIS yafa’di hakan hawaye na xubo masa
Shafa kansa Dadyn yayi yakoji yanda ya d’auki xafi cikin sauri da damuwa Yace “karka damu komai zaixo da Sauqi
Yana fad’in hakan ya fita daga D’akin yana tunanin duk yanda xaiyi xaiyi dan baxai bari d’ansa ya kamu da ciwo bah
Koda yaje part d’in momyn bai ganta ba
Dan haka baibi takan lalle saiya San inda take ba
dan haka dubama KHAMIS magani kawai yayi ya koma ya bashi yasha sannan ya shafa kansa Yace “yau kana da lectures ne
“Girgixa masa kai KHAMIS yayi alamar babu
Murmushi yayi da ficcewa
Jan numfashi KHAMIS yayi cikin damuwa. Dole yaje yasamu FAWAS da RAMADAN yanxu
Momyn KHAMIS ko. Futanta gyalanta taxara tayi gidansu XEE dan bala’i😳
Dadyn baisan nan tanufa ba haka KHAMIS d’in mah
BY RAHEEMAT NALELE
‘YAR MUTAN FULANIN KHATSINAWA
Hajju💁🏼
[9/21, 10:31 AM] Rahamat Nalele✍🏼: *SAMAREEN BANA*
(Tasu salan soyayyar)
Book 2
Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele
*Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara ko kana saurayi koka ta6ayin aure kukaranta min littafi ba. Nayi shine kawai dan ma’aurata badan Ku ba.*
♻EXCLUSIVE WRITER’S FORUM♻
🌐FURE MOMENT OF LIFE WRITERS
💮 DUNIY🅰R M🅰RUBUT🅰 💮
FASAHA ONLINE WRITERS💤
LEEKITAN ZUCIYAH GROUP NOVEL💔
” بسم الله الرحمن الرحيم
*Page*9
Tuqin ganganci take hankalinta baya jikinta
Burinta taganta kawai agidansu XEE
Cikin sa’a ko Allah ya kaita gidan lafiya
Afusace tashiga gidan tana me daku d’aya bayan d’aya cikin isa da taqama…. Sai cika take tana batsewa
Yanda tatura qofar falan ya isa yabaka tabbacin ba lafiya ba
Toh bare kuma kayi toxali da fuskarta
Da mamaki Maman XEE tatashi ita da mijinta da XEE suna masu kallanta
Cikin maseefa ta nuna Maman XEE da yatsa tana me cewa “Idan kina cin qasa Kikiyayi tashuri
Bakin jiriya ba wajan wasan makawo bane
Banyi mamaki ba idan kaga kan mage ya nace dasan saiya waye
Watoh adole ke…. Saikin had’a xuri’a da *MASARAUTAR ABEE* ko
Ha ha ha ha ha….. Ban hanaki hakan ba
Dan ba’akaina kike ba
Daga dukkan alamu kina neman Ki rainamin hankali
Da yanda kika xubamin ido kina kallona
Kedai kam bakiji dad’in halinki ba…….
Jan kunne naxo namiki da babbar murya….
Idan kinbi boka kinbi malam kinje kinjefama d’ana soyayyar ‘yarki…
Toh kiyi maxa kije Ki warware wannan kwullin
Na rantse da Allah idan ‘yarki bata futa daga harkar d’ana ba….
Wlhi bake ba.. Kaf danginki sai sunsan da xaman Murjah……
Tana kaiwa nan tajuya dan barin falan….
Cikin sauri mahaifin XEE ya sha gabanta yana cewa “Haba Murjah me yayi zafi haka shi ba wutta
Fahimtar dani menene yake faruwa….
Murmushin takaici tayi. Cikin 6acin rai tace kasan acan baya ma. Ina ganin mutuncinka
Har gobe mijina bai mantataba
Wlhi kullun qarajin tsanarta nake
Akan wane dalili xatabi ta had’a d’ana da ‘yarta
“Har yanxu bangane me kikesan cewa ba
“Abinda nake San cewa shine ‘YARKA Zainab ce take soyayya da d’ana KHAMIS
Yanxu mukasan komai
Wlhi idan xanyi yawo tsarara KHAMIS baxai ta6a Auran Zainab ba…..
Rintse ido mahaifin XEE yayi cikin matuqar damuwa ya bu’de idan nasa
6acin ransa ya ninka na momyn KHAMIS…….. Yace
“Kamar yanda kikace ko xakiyi yawo haka baxaki ta6a bari KHAMIS ya aure Zainab ba…
Haka nima ko Zainab xata mutu wlhi wlhi wlhi baxan bari ta Auri KHAMIS ba
Kisa aranki na tsani mijinki fiye dakowa da komai arayuwata
Kamar yanda kikace haka nima har gobe takasa mantawa dashi cikin ranta…… Bani da wani maqiyi aduniya kamar mijinki…..
” Yauwa yanxu naji batu…
Sai dai karka tsaya sanya
Dan idan kayi wasa sai su binneka
Momy na fad’in hakan takarkad’e geyarta taficce daga gidan
Mahaifin XEE ya koma dining yaci gaba da karya warsa
Mamah da XEE ko suna tsaye qiqam🕴🏻 kowa da abinda yake saqawa aransa………..
Dafe kanta Mamah tayi danjin yanda yay bala’in Sara mata
Tayi saurin rintse idanta
Ranta ya gama 6aci iyakar 6aci… Ashe ba banxa ba take tsananin San KHAMIS dashi dasu RAMADAN…. Kallan XEE tayi Cikin matsanancin 6acin rai tace…
Abinda Murjah tafad’i Gaskiya ne…..
Sunkuyar da kanta XEE tayi hawaye ya xubo mata cikin sanyin rai tace……
“Kuyi hakuri iyayena… Na kasa control d’in kaina ne
Wlhi San KHAMIS nake da gaske…. kuyi hakuri Ku sanyaye xukatanku karku wargaxa mana farin cikinmu…….
Ji kake fauuu….. Tassss. Tatatasss…..
Mahaifin XEE ya bata wannan mahaukatan Marikan
Iya gigicewa XEE tagigice dan bata ta6a tsintar kanta cikin irin wannan yanayi ba
Har wani wulgawar wuta tagani a idanta
Marikan sun shigeta sosai….
Agigice tace “Ya Mahaifina kaji tausayin qauna
Karka bari zuciya ta d’ebeka karasani….
Ni kad’aice dakai
Kar kama Allah budulci kaqi kar6ar qaddarar daya abko maka
Wlhi ina San KHAMIS ina qaunarsa bana ji bana gani duk abinda xakuyi ayanxu kun makara dan mun rigada munyi nisa *_A SO_*
Tana fad’in hakan tasheqa bedroom d’inta da gudun tsiya ta kullo qofah
Ran Mahaifin nata ya bala’in 6aci da xancican da tai masa
Hakan yasa ya shiga kaiwa da kawowa xuciyarsa na tafasa
Hawaye ne ya xuboma Mamah tayi saurin sharewa. Tare da yin nata d’akin
Ganin hakan yasa Mahaifin XEE d’in binta d’akin nata
Tana xama abakin gado yana shigowa
Nan ya hauta da bala’i
Ta’inda ya shiga batanan yake futaba
Fad’i yake “Baku isa ba yanxu… Kunyi qarya daga ke harshi
Na rantse da Allah baxan aurama KHAMIS Zainab ba
Saidai su mutu… Wannan rainin hankali dame yay kama
Qilama dama can kungama shirya komai ke dashi…. dan munafunci yanxu kina ji ana magana kunyima matane shuru
Toh kiji dakyau ina dai dai daku
‘Yan iska kawai shashashai…….
Kallansa Mamah tayi da sauri…. Tunda take dashi bai ta6a kuskuran xaginta ba sai yau….. Gashi Y’a taja mata
Bata damu da yanda shi da Murjah suke tunanin wai har yanxu suna da wani abu ita da Dadyn KHAMIS ba
Dan tasan wannan dama har abada in ba wani ikwan Allah ba baxai bar xukatansu ba
Tunda sudai tsinannan kishine yay musu yawa axuci da bayyane…. Dan haka sai suje sutayi
Damuwarta ‘yarta Zainab XEE…..
Ita kad’aice da ita
Batasan abinda xaixo ya jefa mata ‘ya acikin damuwa
Tana San ‘yarta…. Duk da taji rashin dad’i akan yanda suke soyayya da KHAMIS…
Ba yanda xatayi dan aikin gama ya gaba
Kuma baxatama Allah budulci ba
Dan tayarda da qaddara mekyau da Mara kyau……
Haka dai ya qaraci sauke mata bala’insa sannan ya ficce yana me cewa
” Yana jira yaga Wanda xaixo mishi da batun ya d’au ‘yarsa ya aurama KHAMIS qaramin Yaro mah
*Wannan kenan*
FAWAS ko da gari ya waye shida dadynsa ne kawai suka kasance a dining
Momy taqi yi musu breakfast
Gashi su bacin na ‘yan aiki suke ba
FAWAS ya kwantar da Kansa akan kafaɗar Mahaifin nasa Yace “Dady kaga momy taqi yin breakfast ko…..
Kan Dadyn yay magana saiga momyn tafitoh da qatan faranti ahannunta tana cewa fushina bai shafi cin abincinku ba
Kuskure d’aya xakuyi kai da dadyn naka shine Ku kwasota Ku kawumin ita nan
Wlhi hakan tafaru ranku baqaramin 6aci xaiyi ba
Tana fad’in hakan ta jera musu komai kamar yanda tasaba sannan tajuya da niyar barin gun……
FAWAS yanemi yay mata magana sai Dadyn nasa ya hanashi da ido. Ganin hakan yasa shi yin shuru har Sanda tabar gun sannan Yace dashi “Fushi take har yanxu ka’yaneta baxata wucce akan hakan ba tunda ta ranse
Murmushi FAWAS yayi cikin rashin damuwa tunda Dadynsa ya d’aure masa gingi ai bashi da wata matsala.
Yasani akan batun kam baxata qara yimusu maganar ba tunda kam tarantse
Bayan sungama Dadyn nasa ya fitta saiya lalla6a yaje ga momyn nasa yako sameta tana xaune tana waya da qanwarta da alama batun take gaya mata
Ganin hakan yasa yaje ya xauna akusa da qafarta yana me d’ora kansa akan cinyarta duk da yasan wayar take hakan bai hanasa cewa ba. “Kiyi hakuri momyna…. Ina San HAMEEDAH…. Kema xaki sota insha…
Yana fad’in hakan ya d’ago da kansa da kama hannunta ya sakar mata kiss tare da miqewa ya ficce abinsa.
Binsa tayi da kallo duk da haushinsa bai bar xuciyarta ba amma kallo d’aya xaka mata kagano qaunar da takema d’an nata
*wannan kenan*
Kamar yanda Dadyn RAMADAN ya buqaci yin breakfast dashi hakan ce ta kasance
Suna breakfast d’in ne cikin qauna da soyayyah Dadyn yana ba RAMADAN shima RAMADAN na bashi momy sai kallansu take cikin so da sha’awarsu……
Wayar Dadyn ce tayi qara… Yana dubawa yaga Dadyn KHAMIS ne
Nan ya d’auka suka gaisa cike da nutsuwa
Ba 6ata lokaci Dadyn KHAMIS ya kwashe duk abinda ya faru ya gayama Dadyn RAMADAN
Hankalinsa yad’an tashi
Daga bisani Yace kar komai ya dameshi su had’u anjima
Bayan sun gama wayanne
Sai kuma kiran wayan Dadyn FAWAS ya shigo masa… Nanma shima ya gaya masa yanda sukayi shida FAWAS jiya
Abin ya bama Dadyn RAMADAN mamaki yace mishi yanxu mah Dadyn KHAMIS ya kirasa… Amma ba damuwa duk xasu tattauna anjima
Bayan ya ajiye wayan ne ya kalli RAMADAN dakyau Yace “wato my son bakya karatu ko
Da sauri RAMADAN ya waro ido Yace “Wlhi Dad muna karatu…. Wani abu ya farune….
“Eh mana tunda ‘yan uwanka sunsa iyayansu agaba waisu Aure suke so…..
Saurin kwarewa RAMADAN yayi da ruwan tia d’in daya kwur6a……..
Dady yayi murmushi Yace sha ahankali karyayi maka illah… So kawai nake nasan kai kuma Wacece wacce kakeso
Dan nasan KHAMIS da FAWAS baxa suce abu kai kaqi fad’a ba… Qila ma Kaine ka shirya musu komai
Sosa qeya RAMADAN yayi ya kalli momy wacce idanta yake kansa
Sai duk yaji kunya ta kamasa
Dalilin hakan ne yasashi cema Dadyn nasa “Share kawai Dad…
“Baxan shareba my son sai naji komai…. Gayamin Wacece
Me makwan yayi magana sai kawai ya miqe ya xaga bayan Dadyn nasa da rungumosa….
Cikin sanyayyiyar murya me tafe da shagwa6a Yace kasanta Dady. Kuma na kasa fad’a mata…. Sai wahalar da ruhina take
Pls my Dad ka tayani addu’a taxama tawa
Dan tarigada tayimin illah
Xanso in sameta kafin ka hankad’ani karatun da kace xani………
Yana fad’in hakan yaxare hannunsa daga rungumar da yayima Dadyn nasa ya ficce
Murmushi dady yayi ya kalli momy da cewa “sun shirya komai ne yaran nan
Girgixa kai momy tayi kawai
RAMADAN na komawa part d’insa yaga KHAMIS yana safa da marwa
Harararsa RAMADAN yayi da cewa Ku ‘yan iskane wlhi
FAWAS yaje yatadama Dadyn Sa hankali Ashe kaima kana bayansa
Kan KHAMIS yayi magana saiga FAWAS ya shigo yana ‘YAR waqarsa
_Zan rayu dakE…. Zan mutu dakE….. Abadan dani dakE xamu xaunA…._
Kallansa KHAMIS da RAMADAN kawai suke.
Yanda yake waqar ya isa ya tabbatar maka da cewa lalle duniyar tamai dad’i
Sanda ya kwanta agadan sannan ya kallesu yace “Samaree… Dady fa ya d’auremin gingi
Bakuga yanda hankalin momy ya tashiba 😳
Saidai ya xatayi… Dan d’anta Aure yake so🤣
RAMADAN Yace “da gaske 😳
Yace “wlhi
“Kai amma na tayaka murna😀 kace yauma akwai zuwa QAUYE kenan dan bada gudstory
“Sosai mah
“Kuji dani plsss…… Cewar KHAMIS
“Xo mu goyaka toh…. Cewar FAWAS
KHAMIS ya harareshi cikin damuwa ya xauna ya juye musu duk abinda ya faru. Ya qara da cewa “Kunsan Allah har yanxu xaxxa6i nakeji. Na shiga tashin hankalin da tunda nake arayuwata banta6a shiga ba…..
Cak annurin fuskar FAWAS ya d’auke.
Sosai damuwa ta baibaye shi
Hakan tsarinsu yake
Idan dai d’aya daga cikinsu yana cikin damuwa rasa sukuninsu suke
Ahakan RAMADAN ya gaya musu yanda sukayi da Dadynsa
Shima FAWAS gaya musu komai daya faru tsaninsa da mahaifan nasa
Hankalin RAMADAN da FAWAS komawa yayi ga KHAMIS
Dan sunsan ayanxu yafisu shiga wani hali
RAMADAN Yace “kaci gaba da addu’a kadage sosai Allah xai kawo mafuta
FAWAS yaja numfashi Yace “duk Sai narasa sukunina jin hakan
KHAMIS ya dafa kafaɗar shi Yace “ina ganin kiran Aunty XEE naqi d’auka
Bansan dalili ba
Ji nake kamar inta kuka ko hankalina xai kwanta
Dana gwada yin hakan d’axu sai naji qaramin damuwa da ciwo yayi
Pls brothers kutemaken wlhi idan na rasa Aunty XEE bansan wane hali xan fad’a ba
Bansan yaushene tayimin illah ba
Bansan haka soyayyar gaskiya take ba
Banyi tunanin xan jike asanta haka ba
Banyi xaton haka ba Sam……
Tashi RAMADAN yayi yana me cewa muyi sallah raka’a biyu mutoqi Allah akan lamarin
Na tabbatar xai dubemu
Kuma xai sanyaya zuqatansu
Basuyi musu ba😌 dan sunsan basu da mafutar da tafi abinda Yace musu
Dadyn RAMADAN ko da Dadyn KHAMIS had’i dana FAWAS sun had’u sun tattauna akan batun yaran nasu…
Dadyn RAMADAN ya nuna mamakinsa sosai
Yayinda Dadyn KHAMIS Yace “Shi matsalarsa Mahaifin XEE dan kar tasan kar tsakaninsu
Dadyn FAWAS Yace insha Allah xasu sami nasara
Sun yanke shawarar gobe zasu QAUYEN TAKAI
Amma kafin suje can xasu fara zuwa wajan Alhaji Murtala wato Mahaifin XEE sunemi iri suga ko zasu dace……
Kuka takeyi sosai hankalinta ya bala’in tashi.
Ba qaramin so takema KHAMIS ba
Ya xatayi
Sanda tasha kukanta takira number nasa dan taji shi dakyau meyasa ya bayyana soyayyarsu yanxu amma yaqi d’auka
Ganin hakan yasata kiran SAILUBAH…
Yanda taxubama TB ido sai Kayi tunanin kallo take.
Nanko tunanin RAMADAN ne yay mata cah akai 🤦🏼♀
” Yaran nan fah yana san 6ata tunanina… Kumadai ya 6ata ne
Mexaisa in kasa bacci saboda shi
Akan wane dalili idan na rufe idona bani ganin kowa sai shi
Jiyafa kwana nayi ina juyi na kasa bacci saboda tunaninsa 🤔
Wai me yake shirin faruwa danine….
SAILUBAH kenan me karatu itace me wannan xancikan acikin xuciyarta……
Qarar da wayanta yayine shi yasa tadawo daga duniyar tunanin da tashiga
Ganin XEE ce me kiran shiyasata d’auka batare da Jan aji ba😌