SANADIN RAGON LAYYAH COMPLETE

 SANADIN RAGON LAYYAH COMPLETE

🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        1-5

Assalamu alaikum, salamu alaikum hajara, hajara ina kika shiga ne nake ta sallama ko kin zagaya makewayi ne, Malam kabiru ne ya shigo yana kwalawa me dakinsa kira, fiddausi ce ta fito daga daki hannunta dauke da kayan wanki sannu da zuwa tayiwa mahaifin nata ya amsa sannan ya shiga tambayarta, ” fiddausi ina mamanku ne ko bacci take banji motsinta ba” baba tana cikin daki dazu dai naga idanta biyu bansani ba ko bacci ya dauketa, to shikenan jeki kiyi wankinki, ya bata amsa sannan ya shiga dakin da hajara take ciki.+

Duk wanda ya kalli yananin mlm kabiru sai ya fahimci irin farin cikin da yake ciki, fuskar sa da walwala ya shiga dakin yana kara maimaita sallama.

Ledar hannunsa ya ajiye a gefen kujera, hajara na mik’e akan doguwar kujera mlm kabiru ya shiga, amsa sallamar sa tayi ciki-ciki kamar batayi niyya ba, da mamaki ya kalleta yace, ” hajara idan ki biyu ko yanxu kika tashi? ” dan dago da kanta tayi sannan tace, ” ban dade da tashi ba” to taso ki gyara mana kayan miyan nan bari na tsallaka gurin nasiru me nama in karbo mana dan k’ashin miya” ko kurar sa bata kalla ba yana gama magana ya fice.

Kai tsaye tsallaken titi yaje ya samu nasiru me nama na hura wutar balangu cikin barkwanci mlm kabiru ya fara yi masa kirari,  ” kaga sarkin nama ko ince kafi giwa nama ya kasuwar ya harkoki? ” washe baki nasiru me nama ya farayi yana fadin,  “kwarai kuwa mlm kabiru suya za’a baka ko danye kai ko duka kake so yanxu zaka ga aiki da cikawa, dariya mlm kabiru yayi yace a’a sarkin nama wane ni da siye duka wannan naman, ay nama dari biyar zaka yankomin ungo kudin amma fa dubu ce dan nasan yanxu kace mun canji wuya yake” nasiru me nama karbar kudin yayi yana fadin, ” mlm kabiru kasan kasuwar ce sai godiyar Allah kawai amma abun ba’a cewa komai.

Yanka masa naman yayi yana shirin nad’e takardar, mlm kabiru yace, “kai sarkin nama yanxu naman dari biyar haka ya koma haba kai kuwa ka dan kyauta mana sai kace naman dari uku”  hmmm mlm kabiru kenan karfa ka manta yau sallah saura kwana uku kasan dai yanda dabbobi suke tsada, wallahi wannan naman daka gani kawai dai karfin hali ne, haka zamu daddagira har zuwa bayan sallah.

Hakane kam Allah ya iyamana wannan tsadar rayuwa talaka dai yana cikin wani hali, mlm kabiru ya bashi amsa ya karbi naman ya wuce gida.

Yana shiga gida hajara ya samu a inda ya barta, cikin mamaki yace, ” hajara wai nikam ko akwai abunda yake damunki naganki duk wani iri”  dan ya mutsa fuska tayi sannan tace, ” a’a ni lafiya ta klau me ka gani? kawai  yanayi ne yasa ni hakan”

To shikenan Allah ya kyauta tashi ga nama na kawo ki hada kayan miyan cen akai markade yamma tanayi.

Bata bi ta kan zancen sa ba ta jeho mai tambaya.

Wai ni mlm tun dazu bayan fitarka ina ka je ne? naji ka shiru banji kukan rago ba, ni nayi tunanin ma ko kasuwa ka tafi tunda naga dai ay kunsami albashi ga alama nan na gani kana cikin walwala.

Hmmmm hajara  kenan wai meyasa kinfiya gutsira magana kamar wata karamar yarinya, inace yau kusan kwana biyu kenan dayin maganar mu, ko so kike muyita abu daya agaban yara suna ji, wannan be kamata ba sam kinsan ni naki jinin gutstsira magana.

STORY CONTINUES BELOW

Au Allah mlm da gaske kake yau naga ikon Allah, lallai mlm abun naka kara gaba yake tsakani da Allah ga kudin ka samu kake shirin kayi mana keta, yanxu dududu sallah saura kwana uku makota kowa ya tirke ragonsa masu shanu duk sun adana amma yanxu ka nemi ka jamun raini a unguwa, kana gani mlm duk shekara na wuce gori da raini agun makota sannan wannan karan ka bullomun da wannan maganar.

Au hajara dan banyi layya ba shine za’ay miki gori ki gayamun waye zai rainaki wai ma intambayeki zaman wa kike a unguwar nan? ke wato bama dan Allah kike so muyi layyar ba sai dan mutane ko, to ni ban iya aikin riya ba nace miki bani da halin yi idan ke wata ce har zaki iya budar baki kice wani abu amma wallahi kin bani mamaki hajara.

Haka nace maka ba dan Allah nake so kayi layyah ba, dakata mlm kabiru karka hada ni da ubangiji na nidai ina gaya maka irin kallon da za’a yi mana ne, kai yanxu kodan yaran kar suji kamshi a makota ay ka siyo mana ragon nan mutum da kudi a hannunsa sai mammakon tsiya gaskiya duk abokin da ya baka wannan shawarar ya cuceni Allah ya isa tsakani na dashi.

Abinda baka sani ba mlm wallahi ko rance ne sai kayi ka saya mana rago shine samun kwanciyar hankalinka, hajara ta karasa magana cikin tsiwa da jin haushi.

Tabdijam lallai hajara wuyanki yayi kauri au rainin har yakai ki dinga fadamun irin wadannan maganganun, ni mijinki ni kike gayawa haka, sai kace da yaronki kike magana wai kin manta da layyah nufi ne na Allah, tunda na aureki tsawon shekara dai-dai-dai har goma sha bakwai bantaba fashin layya ba sai wannan karan,  amma wai yau saboda nace bazanyi ba kike neman kicinmun mutumci, mlm sani ya fada cikin bacin rai ya dora da, ” hajara kinsan yanda rayuwa take kara tsada ga kudin hayar mu kina gani watan gaba zan basu kudin su, ga kudin magungunan inna banda ma Allah na rufa asiri.

Yanxu zainabu idan baki tallafeni kin kwantar mun da hankali ba ya kike so nayi?

Kayi duk yanda zakayi mana kabiru aykasan yanda zaka bullowa lamarin karka maidani wacce batasan me takeyi ba, karka manta karamar sallah kaya kala dai-dai kayi mana, babbar sallah bara ma so kayi kaki yi mana layyar nan, wai akanmu talauci ya kare ne?  Wallahi duk masu zugaka zasu kaika su baro.

hajara ni bance ana zugaki ba sai ni zaki ce ana zugawa, ki dinga gode Allah fa idan baki godewa ba zaki godewa azabarsa.

Auzubillahi insha Allahu bazanga Azabar ubangiji ba, wato kabiru har fatan azabar Allah kake mun.

Ni ba fatan azabar Allah nake miki ba kece kika dauko wata hanya daban, amatsayina na mijinki muddin bazaki sake dabi’ar da kika dauko ba to kuwa zaki gamu da azabar ubangiji.

Tashi zaune hajara tayi tana fadin, ” Ahayye wai da nayi magana sai ka fara zancen miji miji, wai kabiru rahamar nan a hannunka take ne? Rahama ay ta Allah ace shi ke bawa wanda yaso kuma a sanda yaso.

    Bari kaji wallahi idan fa har ka kafe akan bazakayi layyar nan ba, barar nama zan tafi cen unguwar Alhazawa zan shirya inshiga, sallah guda ace mutum yana zaune sai dai yaji kamshi na tashi, tunda dama abun ay zama biki yimun inmaka ne, to mukuwa da bamuyi ba waye zai bamu.

Hmmmm, mlm kabiru murmushin takaici yayi, sannan yace, ” lallai hajara girman ne da shekarun suka zo miki amma hankalinki da saura.

Gaskiya ban tabbatar da baki da hankali ba sai yau Allah ya shiryeki yasa ki gane, amma ki gyara tunaninki idan  ma bacci kike ki farka ga naman nan ki tashi ki dora mana girki inkinga dama” yana gama maganar ya tashi ya fice ransa a b’ace.

Aykuwa kamar ya watsawa hajara ruwan zafi, cikin hassala ta fara magana.

” wato mlm ni kake cewa mahaukaciya ko, ka daukeni bansan me nakeyi ba lallai kaci abinci akaina, wallahi sai na nuna maka asalin haukan da kace inayi, har yanxu baka gama sanin halina ba nan gaba labarina zaka fara bayarwa, kuma girki bazan dafa ba, ehe bazan girka ba, kasa yara suyi ko ka dora da kanka”

STORY CONTINUES BELOW

Tana cikin bambamin fada fiddausi ta shigo dakin kusa da ita ta zauna tana fadin,  ” haba umma dan Allah meye haka kikeyiwa baba tunda kikaji yace bashi da kudi wallahi bashi da shi kinsan dai baba idan yana kudi basai ance yayi ba, komai fa lokaci ne kuma layya fa ba kanmu ne aka fara rashin yi ba dan Allah kiyi shiru karma makota suji……”

Katse ta hajara tayi cikin tsawa, ” ke ki kiyayeni yanxun nan ko jikinki ya gaya miki, har ni zaki xo ki samu kice zaki gayamun wasu maganganun banza da wofi, tashi ki bani guri inba haka ba ranki yayi mummunan baci.

Dan Allah umma kiyi hakuri banyi haka dan ranki ya kara b’aci ba naga baba ya fita ransa a bace ne, kuma kinsan baba bashi da fada sai abu yayi mugun b’ata masa rai amma idan na b’ata miki rai kiyi hakuri, fiddausi ta karasa maganar tana kokarin tashi aykuwa cikin fada hajara ta kara rufeta da fada.

          ” to me uba wato bashi da fada sai ni da kika maida karya ko? yar kishiya rukon me hakuri wannan da ace a asibiti na haife ki kuma da bakya kama da mlm wallahi cewa zanyi canje akamun, shashar banza wacce bata kishin uwarta, komai mahaifinki yayi shine yayi dai-dai kuma me gaskiya, zaki fice mun kosai na janyoki na sauke miki ragowar b’acin raina akanki, sakarya duk yakin da nakeyi idan aka yanka ragon kuma inace daku za’a ci, har zaki zo ki wani kalallame ni da dadin baki”

Sum sum sum fiddausi ta wuce bata kara tankawa mahaifiyarta ba, dan tasan idan tace zata kara magana to tabbas tana iya hucewa akanta, kai tsaye ta wuce ta sauki ledar kayan miyar da mahaifinta ya kawo ta fita tsakar gida ta fara gyarawa, dan tasan tunda mahaifiyar ta ta tace bazatayi ba ya zauna din, bare yanda taga kowannen su ya dau zafi sam abin bai mata dadi ba.

Salamu alaikum, salamu alaikum kawata, dago da kai fiddausi tayi fuska a hade dan sarai ta gane muryar me sallamar, ciki-ciki ta amsa kamar bata so ba, a’a fiddausi yan mata gyaran kayan miya akeyi ne  ina umman taki ko bata nan, matar da ta shigo take tambayar Fiddausi.

Kasa-kasa ta bata amsa, ” tana ciki ” dan fiddausi ta tsani hanne saboda duk wasu abubuwan da hajara takeyi hanne ce take zugata, sai kace uwarta duk hudubar da zatayi mata da muguwar shawarar da zata bata hawa take dass ta zauna.

Hanne irin matan nan ne munafukai, massada, masu kyashi, san abun duniya da zagwan kasa, uwa uba ta iya kissa da kisisina, bata da aure mijinta yafi shekara goma da rasuwa ya barta da ‘ya daya tun bayan rasuwarsa bata kara aure ba, tana sharbar duniyarta da romo.

Dakin hajara ta fada tana fadin, “kawata lafiya ko laifi nayi inata sallama aka mun shiru to idan ni ce kaina bisa wuya na ta mlm kabiru ikon Allah”

Hmmm ki bari kawai hanne wallahi yau nida kabiru ne ya mugun bata mun rai, shiyasa ma kika shigo kika jini ina mita, ” au yau bama mlm din kenan hajiyata da gani yau ya tab’o ki da yawa” hanne ta fada cikin sigar sonjin labari.

“Ke kinji yau shafin wulakancin daya budemun wai bashi da halin yin layya, ga kaza ga kaza yake tamun lissafi wai bana sai dai muyi hakuri dan Allah jiki rainin hankali…….”  katse ta hanne tayi da, ” haba hajara kema kinsan wasa yake miki kila irin barkwancin nan ne na mata da miji, kamar mlm kabiru har yace bazaiyi layya ba inba dai son zuciya ba, au ki yafeni karfa kiji haushi na”

Ke hanne kabiru fa da gaske yake, wai kinga irin tufka da warwarar da mukayi dashi, wallah sam ba alamun wasa acikin maganganunsa…… ” hanne ce ta katse ta, to ke kuma wane mataki kika dauka ta shawai dan nasanki da sakarci, yooo Allah na tuba namiji ma baka sakar masa ba yaya bare kuma ya samu guri, Allah sa ma ba kudin aure yake tarawa ba dan na lura komai kika ce sai dai yace miki bashi da kudi, hmmm namiji duk yanda zaka bullomai sai Allah”

Buhun uban nan wallahi karya ne, karya ne kabiru yayi kadan yace zai mun wannan lalatar, wai kin mata dawa kike magana ne, ki tuna ko kura ta rame karyar karnuka su kawo mata wargi, ni hajara wallahi kabiru yayi kadan yace zaimun wannan rainin hankalin.

Sai kace wacce ta rako mata duniya, haba ay wargi ma guri yake samu.

Kawata kenan ay idan kikace zaki cigaba da zama kina zuba ido, to kina nan zaune zakiga  zama wallahi sai dai kiji yaxo yana ce miki kinsan komai mukaddari ne Daga Allah bakiyi aune ba zakiji kishiya……..

Cikin tsawa hajara ta katseta,  ” kinsan duk duniya ba abinda na fi tsana sama da kishiya, wannan zancen da kikemun kamar kina hura wuta ne acikin zuciya ta ki iya bakinki, dan wallahi da kabiru yayi mun kishiya gwara ni dashi duk awayi gari mun mutu kowa ya rasa, kinsan yanda na tsani kishiya kuwa?”

Shewa hanne tayi tana kara dan muskutawa da gyara zama tana fadin,  ” Da kyau ta hannun dama na haka nake san ji shiyasa nake kara sanki, bakida sanya amma wani hanzari ba gudu ba kinsan dai maza zuma ce ko, kuma kinsan sai ana danne kawunansu ta karkashin kasa, hanne ta karasa maganar kasa-kasa tana dan waige.

Ban fahimceki ba hanne ni nafisan ki fito sarari ki mun bayani, yafi wannan zaurancen da kike mun.

Fiddausi ce ta shigo dakin daukan hijabi zata kai markad’e, da sauri hajara ta dan zunguri hanne da kafarta, tuni hanne ta dauke karatun aykuwa ta wayance da.

           ” oh hajara kullun yara na gida ba makaranta, kinashan bari-bari danma ga fiddausi nan wani abun basai kinyi magana ba, ni tun zuwa na ma banga iyalan naki ba.

Kedai bari ay wannan cutar sai dai Allah yayi mana maganinta, yau na dan samu suntafi gidan inna gaba daya suka tarkata nayi sauki kafin su dawo.

Ita kanta fiddausi jikinta ya bata ba wannan hirar suke ba, hijabinta ta dauka ta fice daga dakin.

Hajara ce ta fara magana, ” kinsan halin yarinyar nan yanxu tana jin hirar da mukeyi bayan ki tafi tazaxo ta isheni da nasiha”

Ummm bari ay naga alama ita ce sak mlm kabiru, hanne ta fada tana murmushin gulma ta dora da, ” to hajara sai fa kin tashi kuma kin bude bakin aljihu”

Bangane ba hanne.

Eh, gurin wani mutum zan rakaki shi yake yiwa furaira aiki, wallahi aikinsa ba karya kamar yankan wuka yake.

_Muje zuwa🤣 sisters_

_Vote_

_Comments_

_Share_

    _*MOM ASLAM Ce*_ 😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        6-10

Allah hanne? Shafamun inji a wace unguwar yake? Cikin zumudi hajara take tambayar hanne, murmushi hanne tayi sannan tace, ” wallahi wani dan kauye ne sai kin shirya sai muje, saboda shi aikinsa sai kana kudi, inda kudinki to zakiga aiki kamar yankan wuka sabon wa shi.

Hanne kara zugoni fa kikeyi ji nake kamar nayi tsuntsuwa muje gurin, amma to kamar nawa yake yin aikin?

Ehto, ki tanadi kamar dai dubu goma zuwa goma sha biyu, na gaya miki shi kudi sune agabansa, idan kinada uwar kudinki to bakida matsala saboda shi duk sabon da kukayi dashi na tsahon shekaru indai baki da cash to ranar ba magana, amma ki gwada ki gani zaki bani labari dan idan yayi miki aiki wallahi sai kin juya malam kabiru kamar waina a tanda, ke abinda baki sani ba wallahi ko kashi da fitsari inbaki bashi umarnin zuwa ba saidai yayi shi agurin.+

Ayyiriri nanaye ahaayye kawata shiyasa nake sanki ta wajena, amma wani hanzari ba gudu ba, wallahi kudin gurina basufi dubu takwas da yan kai ba, yan kanma bance sunyi dari biyar ba, hajara ta karasa magana tana kallan yanayin hanne.

Kallan tsaf hanne tayiwa hajara sannan tace, haba hajara dubu takwas fa kikace me dubu takwas zatayi mana ga kudin motar ma Allah zamuci dubu daya da dari biyar, hajiya ta ki ware bakin aljihu kiga aiki da cikawa.

To shikenan hanne bani zuwa nan da gobe da safe zan nemi cikwon kudin, ke gobe ma zamu je kinsan da zafi-zafi kan daki karfe, hajara ta karasa maganar tana mikawa hanne hannu suka tafa.

Haka nake san ji da zaki wani bada mata, kamar ba mace ba akwakulo da yawa daga hannun mlm kabiru, uwar gida sarautar mata.

Kan hajara ne ya kara girma ta fara murmushi, sannan tace,  ” hanne kedai ki zauna cikin shiri goben nan fa zamu je.

Haba hajara meye naki na jadadda mun nida ba miji ba, ba tsayayyen farka ba ay ko da dare kika xo muje ni banida matsala.

Cikin dariya hajara tace, ” kwarai kam shiyasa kike tsula tsiyarki san ranki”  dan canja fuska hajara tayi tacewa hanne, ” Kin dai tabbatar da aikinsa na ci ko dan gaskiya banasan nayi asarar kudina, kar inzo indunkule kudina inkai masa azo aiki be ci ba.

Mtsssswww dan Allah kiji zaki b’ata mun rai muna zaune cikin jin dadi, idan aikinsa baya ci zakiji nace zan rakaki ne? Ke yanxu samarin da suke dafifi gurin furaira na banza ne, kin manta da ba shegen da yake zuwa gurinta kamar wacce akayiwa asiri da jab’a, amma yanxu ko ke Shaida ce basai nace komai ba ko ke kin isa ki bawa wani labari.

Dariya hajara ta kwashe dashi tace,  ”  kai kawata gaskiya baki da kyau hanne, ga gidanki nan sai layi ake kamar asibiti.

To ke banda abinki hajara wa yace miki ana zama haka inba sakarai ba, zama haka ay sai Shashan mata, ke bari na zo na gudu yamma tanayi.

To shikena hanne nagode kwarai Allah bar zumunci, sai kinji ni.

Yanxu hajara takaninmu harda godiya? Ni nayi tunanin tun tuni mun zama daya.

Eh mun zama daya hanne amma ay hausawa suka ce yaba kyauta tukwici.

Wannan haka ne hajara, to Allah bamu alheri ina jiranki sai kinzo.

STORY CONTINUES BELOW

Hanne tana fita hajara ta fito ta fara kiciniyar dora girki lokacin fiddausi har ta kunna risho ta dora tukunya da mai, hajara ta shiga kitchen ta karbi girkin.

Fiddausi kallan mahaifiyarta take da mamaki, dazu kamar ba itace take ta banbamin fada ba, cikin zuciyarta take fadin.

         ” oh ga umma kamar ba itace d’axu take ta fada ba amma zuwan wannan shu’umar matar ji yanda ta sake kamar ba ita ba, Allah sa dai ba wata banzar shawarar ta bata ba.

Hajara ce ta leko ganin fiddausi a tsaye tace, au ke kuma kina nan tsaye, to tsaiwar me kike yi kije ki karasa wankin man tunda na karbi girkin.

Da sauri fiddausi ta wuce gurin da take wankin kayanta.

Cikin zuciyar hajara tunani take ta yanda zata bullowa malam kabiru gurin karbar kudin zuwa gun mlm me dogon zaure, ita kadai sai sak’a da warwara take yi, tana cikin aiki wata shawara ta fado mata saboda jin dadi har ji take kamar ma taje gun malamin ta dawo.

_BAYAN SALLAR ISHA._

Hajara na zaune suna hira ita da fiddausi, ibrahim, khadija da muhammad, biye musu da hirar kawai take yi amma Allah-Allah take malam kabiru ya shigo har gani take lokaci baya sauri.

Suna nan suna hira malam kabiru ya shigo, A tsammaninsa ko sannu da zuwa bazai samu agun hajara ba amma ga mamakinsa, yana shigowa ta taso tana mai varka da zuwa.

Mlm kabiru shi kadai yake mamaki  ganin fuskar hajara washar kamar gonar Auduga, cikin zuciyarsa yake magana, ” kamar ba ita ce d’azu take zazzaga rashin mutumci ba, wata zuciyar tace a’a kayi mata uzuri kila dai tayi karatun tanutsu taga abinda tayi be kamata bane shiyasa ta sauko….

Malam muje ciki ka ci abinci ka huta man, hajara ta katse shi.

Ba musu ya tashi ya shiga daki, abinci aka jera masa ya fara ci, hajara harda yi masa fifita anayi mai hira me dadi.

Bayan su fiddausi duk sunyi bacci, malam kabiru na zaune suna hira, hajara ta fara koro masa bayani, ” malam dazu aka kira ni ake cemun habu ( _kaninta_ ) bashida lafiya, Ashsha me yake damunsa? mlm kabiru ya tambaya da sauri.

Basu gayan me yake damunsa ba amma sunce mun yana jin jiki.

      Subhanallahi Allah ya bashi lafiya, idan Allah ya kaimu gobe sai kije kiji ya jikin nasa.

Dan Allah mlm ka taimaka ko rance ne ka vani na dubu hudu, kasan idan naje nice me siyan maganin, kuma kwandala banida ita  kuma idan naje zasu sa ran zan tafi da Dan wani abun.

     To kudin gurina dai basu kai dubu hudu ba sai dai inbaki abinda ya samu kiyi maleji, kudina dubu biyu da dari biyar ne zan baki su sai kiyi hakuri.

Dan yatsina fuska hajara tayi tana juya kudin da hannunta sannan tace, ” yanzu mlm duk acikin kudin nan zanyi ba mota da wanda zan je insai masa magani gaskiya idan da wasu karo dan wadannan bazasu isheni ba”.

Iya kudina kenan hajara abunda ka samu dashi kake amfani, yanzu kenan kin raina abinda na baki ko? Kikasan uzurin da zanyi dasu na kwashe duka na baki.

Juya kudin tayi tana musu wani kallo sannan tace, ” to angode madallah” ta karasa maganar tana ninke kudin tana yin hanyar uwar daki.

Idanu ya zuba mata yana kare mata kallo cikin zuciyarsa yana mamakin hali irin na hajara, san kudinta Yayi yawa ga rashin godiyar Allah.

_CIKIN DARE._

Bacci ne ya gagari idan hajara sai d’okin tafiya take, ji take tamkar ta janyo safiya suyi su tafi gun malam me dogon zaure.

Tinowa tayi da cewar kudin da zata tafi dasu basu cika ba, sannan ta tino da cewar ance malamin bashida mutumci akan kudi, waigawa tayi gefe taga mlm kabiru baccin sa yake hankali kwance, a hankali ta yunkura ta tashi zaune, sadaf sadaf ta sauka daga kan gado ta lallaba ta tunkari rigar da mlm kabiru ya cire ya rataye.

STORY CONTINUES BELOW

Hannu ta zura cikin aljihunsa tana yi tana dan waige, hannu taji ta duma cikin kudi zuciyarta fes ta zaro dubu uku ta kalmashe su, cikin drower ta bude ta hada da sauran kudadenta ta koma luf ta kwanta kamar  munafuka.🤣

Motsi taji mlm kabiru yayi ta yi kamar ne bacci harda jan munsharin karya, juyi taji yayi ya kara gyara kwanciya ita dinma wannan karan baccin ne ya fara daukanta zuwa wani lokaci tayi bacci.

Washe gari duku-duku hajara take ta kiciniyar aiki, wajen karfe takwas da rabi na safe bayan ta fito daga wanka mlm kabiru ya shigo ya fara mata magana,  ” yanxu hajara har yanxu baki gama shiri ba ga rana kara yi take yi kefa kika cemun da wuri zaku tafi asibiti, ke kin cika na wa kamar me, haba kiyi ki tafi yaro yana cen   yana jin jiki” eh wlh mlm ay na gama ma dan kaya kawai zansa sai inci abinci.

To ya kamata ki hanzarta kuwa rana na karayi.

Bayan hajara ta fito zata tafi sallahun duk abinda za’ayi a gidan ta barwa fiddausi, ta kuma shaida musu ta tafi kai habu asibiti, cikin hadin baki sukayi mata addu’ar adawo lafiya akuma duba me jikin.

Hajara na fitowa sai waige take tana juye-juye, da sauri tayi ta fada gidan hanne, dan kar mlm kabiru ya biyo bayanta yaga inda ta shiga.

Da sallama hajara ta shiga gidan hanne, lokacin suna karin safe ita da furaira lafiyayyan shayi da biredi suke sha sai dankwaleliyar kaza a cikin leda, murmushi hanne ta saki ganin hajara da farar safiya.

Bayan sun gaisa, hanne ta kalli hajara, ” oh mutuniyata baki da sanya yanxu har kin yunkuro kinganni ni ko wanka ma banyi ba, kinga janyo flask  gashinan ki zuba ruwan shayi Allah yayi da rabonki ga kaza kema kya taba, Alhajin furaira ne ya hadota da shi ko minti talatin batayi da dawowa ba, wai Abuja ta rakashi wani taro”

Ayfa shiyasa nakesan zuwa gidan ki hanne baya rabo da dan kwalam da makwalashe, bari naja cinyar dan yawuna har ya fara tsinkewa.

Furaira na danne-dannen waya ta dago idonta daya yasha eyelashes, ta gaida hajara, ” ummansu fiddausi ina kwana ya gida?”

   Cikin washe baki hajara ta amsa, ” lafiya kalau furaira ya kuka baro Abujar nasan kinsha sanyin AC, kai garin dadi na nesa Allah yayi mana arziki” 

         Wallahi AC kam har ki gaji ay arxiki yana inda yake, furaira ta bata amsa ta cigaba da latsa wayarta.

_BAYAN WANI LOKACI._

Tsaf hanne ta shirya , bakar abayar furaira hajara ta saka ta dauko nikab shima tasa suka fito dan kar malam kabiru ya ganeta.

Fitowarsu yayi daidai da fitowarsa daga gida, sai dai kowa hanyar da yabi daban, kirjin hajara har bugawa yake, ta zaci zai gane ta sai da suka bar layin sannan hankalinta ya kwanta.

Adaidaita sahu suka tara ya kaisu tasha, zuwansu keda wuya suka shiga motar wudul, mutum biyu kawai suka samu aciki wasu mata biyu akujerar baya suma suka shiga ta bayan suka zauna.

Sannu a hankali motar take samun passingers, zuwa wani lokaci motar ta  cika suka wulla titi.

Tafiya  sukeyi sosai har sun fara shiga kauyuka, motar ce ta fara kauri daga wajen injin hayaki ya fara fita, cikin zafin nama driver ya taka birki kwandastan da sauri ya bude musu kofa kowa ya fito.

Bayan fitowarsu driver yayi yan tabe-tabe da dube-dubensa ya kara shiga dan ya kunnata, amma mota taki tashi.

Kwandasta ne ya kalli passingers din yana fadin, ” Alhaji dan Allah kuyi hakuri hajiya kudan bamu lokaci kadan oga zai gyara ta mu karasa.

Wani mutumi ne ya fara magana cikin fada, ” kudai kunada matsala wallahi haka kuke diban passinger kara zube, bakwa duba lafiyar motarku kudai burinku a baku kudi ku karbe”

        Haba master wallahi motar mu lafiyarta kalau kasan dai karfen nasara baida tabbas.

STORY CONTINUES BELOW

Duk yanda driver yaso ya tada motar taki, shawara ya yanke zai tsaida musu da wata motar inyaso ko bakanike sai ya kira yaxo ya gyara masa.

Wata mota data zo wucewa aka tsaida su hanne suka shiga, mutum hudu ne suka samu guri su hanne da wata mata sai wani saurayi, kudi drivern su hanne y dauko ya bawa me motar, sukuma sauran wadanda basu samu guri ba ya basu hakuri.

Su hajara kujerar baya suka samu kusa da wasu mata guda biyu.

Bismillanku ga dabino da gyada, daya daga cikin matan tayi wa su hajara tayin gyada da dabino, hanne tace ” kai haba mungode wallahi “

A’a ba ayi haka ba ga leda daya sai ku taba kunsan gyada marau da farin jini, dayar matar ta kusa da hajara ta fada tana miko musu, ba musu kuwa suka karba suna godiya.

Nan fa hira ta shantake a tsakaninsu , idan ka gansu sai ka rantse dama cen sunsan junansu, sosai suka cika motar da hayaniya har sai da wani mutum yayi ya juyo yayi musu magana, amma kamar ma kara zigasu ya keyi.

Gidan mai motarsu ta shiga, suna shiga  Hajara ta sai musu pure water kowa dai dai, aykuwa nan da nan wani sabon ya kara shiga tsakani.

Bayan fitowarsu daga gidan mai ko tafiyar minti ashirin basuyi ba, matan nan suka ce zasu sauka, badan su hajara Sun so ba.

Tafiya suka yi me dan tazara sannan suka karasa tashar wudul, motar su hanne parking tayi kwandastan ya bude motar yana fadin,  ”  To Alhamdulillah Allah ya kawo mu dadin mota ya kare, Alhaji bismillah”

                   Mutanen gaban motar ne suka fara fitowa, sannan yan baya hajara ta yunkura zata tashi ta kalli hanne tace, ” Hanne ina jakata ne ko na miko miki ita?”

” jakarki kuma hajara? Yooo jakarki da take saman cinyar ki kya tambayeni ita”

Yan dube-dube hajara ta shiga yi da leka kasan kujera wayam babu, cikin fargaba hajara tace, ” wallahi kinga hanne na duba ko ina babu sai wayata dake hannuna”

Kan uba hajara kardai matan nan ne da suka sauka sune suka yashe ki, kara dai dubawa ki gani ko wani gun ta fada tunda acinyarki take, hanne ta fada tana dan leka kasan kujerar.

Sunkuyawa hajara ta karayi tana dubawa idonta ya fara raina fata, zuciyarta na kuna saboda bakin ciki, kwandastan ne ya leko yake musu magana, ” haba hajiya sauka daga mota kamar masu sauke farali tun dazu fa ku muke jira zamu karayin wani lodin, kano kano Alhaji zo ka hau ba jira ba b’ata lokaci”

Azalzalarsu ya cigaba dayi ba shiri hanne ta sauko, hajara ma bayanta ta biyo tanayi tana dan waige.

Gefen wata bishiya suka koma suka tsaya sukayi carko-carko, hajara duk wanda yaxo wucewa idan ta zura mai ido har sai ya sha kwana,  kamar wacce take neman jakarta agurinsu.

Idan badan kayan jikinta ba sai ka dauka sabon kamu ce domin kallan da takewa mutane ya wuce misali.

Hanne ce ta katse shirun da, ” hajara wai yanxu meye abun yi wannan tsaiwar bazata kaimu ba”.

Hanne kaina ya kulle, hajara ta fada kwallah na zubo mata, amma dan Allah idan kin fito da kudi da yawa ki aramun inmun koma gida zansan yanda zanyi.

Kinsan Allah hajara kwandala banida ita yau da dari biyu na tashi, dari aka siyomun kati sauran darin nacen na barta kan window, kinsan kwana biyu furaira bata gida kuma yau data dawo ban karbi komai agurinta ba.

Wani malolon bakin ciki ne ya tokare hajara, sai ga hawaye shaarrrrr, kuka take me tsuma zuciya mutane har sun fara kallansu kasancewar har zuwa lokacin suna cikin tasha.

Hajara ki daina kuka kinga idan mutane na kanmu, azafafe hajara ta katse hanne, ” ba idon mutane ba Allah sa duka fuskar mutane ne akanmu, hanne dole nayi kuka wannan mata da ta sacemun jaka Allah ya isa tsakanina da ita.

Nidai dan Allah ki yi shiru zaki tara mana mutane hanne ta fada tana yiwa hajara magana kasa-kasa, aykuwa kamar ta watsa mata ruwan zafi hajara ta fara fada.

        ” hanne idan banyi kuka ba dariya kike so nayi, kudi sama da dubu goma anyashe ni babu, kina gani ko kudin da zamu koma gida babu, duk duniya kudin nan ke gareni ba kudin ba biyan bukata, ki gayamun me zanyi hanne? ” sai kuwa hajara ta kara fashewa da wani kukan.

Hanne shiru tayi ba baka sai kunne, suna nan jugun-jugun wata me awara taxo tana musu tallah.

      ” hajiya ga awara ci ko tsaraba tawa ta dabance bana sa mata yeast, tanawa za’a zubo muku ne?” shiru sukayi ba wanda ya kulata.

Matsowa tayi kusa da hanne ta cigaba da tallanta, ” awarere awareriya aci a ware gida, ga gardi ga dadi awarata tafi nama dadi, hajiya ku duba ku gani wannan awarar ko balangun dan tani albarka, ta nawa zan zubo muku?”

Hanne na shirin yin magana kan kace me hajara ta riga ta, ” ta uwarki da ubanki shegiyar yarinya me nacin tsiya, kinxo kinyi tallah anmiki shiru ubanki ne ya bamu kudin?

🤣🤣🤣🤣🤣 hajara me awara dai ba ita takar zomon ba🤣🤣

_BARKANMU DA SHIGOWA WATA ME DARAJA ME ALFARMA, ALBARKAR DAKE CIKI ALLAH YA BAMU SHARRINSA ALLAH YA KAREMU._

_Vote_

_Comments_

_Share_

    *MUM ASLAM Ce*😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        11-15

Harararta me awarar ta farayi, ta tsugunna tana kokarin daukan bokitin ta, gunguni take yi  kasa-kasa tana fadin, ” wallahi badai tawa ba sai dai taki haka kawai zaki dinga zagina “

          Au zagina kikeyi shegiyar yarinya mara kunya, mara tarbiyya kawai.+

Sai da me awara ta juya idanu kasa da sama, saman idan nan yasha eyeshadow ga uwar jagira, murgud’a baki ta kara yi sannan tacewa hajara.

              ” Ay ba’a  mara kunya daya, ki kara zagina inlissafo miki su” ta karasa maganar tana barin gurin.

Hajara zabura tayi zata dank’o wuyan me awara, da sauri hanne ta dafe mata cinye tace.

            ” haba hajara meye haka kike yi ne, wannan yarinyar fa ba sa’ar yinki bace, kina ganin kalubalen da yake gabanmu, ya kamata mu tsaya mu fuskanci matsalar dake tattare damu”

To shikenan, hanne yanxu ya zamuyi? Dan Allah mu karasa gidan malamin nan ki rokar min shi ko bashi ne yayi mun aikin, tunda kinga kun dade dashi, kinga ay na rage zafi”

” Kudin mota kuwa nasan idan mukaxo tasha, nasan zamu samu dan na Allah basa karewa ” hajara ta karasa maganar cikin marairaicewa.

Ummmmm hajara banaki ta taki bane, akwai abunda nake hangowa, malamin nan bashi da mutumci ko kadan, indai akan kudi ne baya ji baya gani, kinga mun shafe shekara bakwai tare, amma wallahi akwai lokacin da naje masa da bukatar yayi mun wani aiki akan rabon gadon mu, wallahi ki yayi sai da na koma na ciko masa kudinsa casss sannan yayi mun.

            Bare aikinki yana cikin jerin ayyuka masu tsada da yake yi, aikin miji dana kishiya da yayan miji yafi tsada aduk cikin ayyukan da yake yi”

“To yanxu hanne haka kike so muzo abanza mu koma awofi ga asarar kudin dana tafka, yanxu kina ganin zanji dadi ko nan gaba zaki kara yimun jagora inbiki? “

“A’a ba’ayi haka ba, mu jarraba hajara amma wallahi jikina yana bani mutimin nan bazai miki aiki ba, dan sanin hali yafi sanin kama” hanne ta fada tana gyara tsayuwarta.

Hajara tace, ” haba hanne kinji irin mugun bakin da zaki ja mana, tun kafin muje dan Allah kiyi mana adduar Allah ya doramu akanshi.

Hanne dan jim tayi sannan tace, ” to ” muje ay mutum baya k’in ta mutane, sai angwada………..”

Hanya suka mik’a suna ta tafiya, sai wuce gidaje da shaguna suke, sannan suka yanka cikin wadansu ciyayi, sun dan jima suna tafiya cen cikin wani daji suka nausa ba gida gaba ba gida baya, sannan suka karaso wani dan madaidaicin karamin gida.

Kofar gidan cike yake da manyan motocin masu kudi, da mashina kekuna basu fi guda biyu ba.

Soron gidan suka shiga maza ne sunkai takwas, bayan sun shiga ciki suka samu mata sunkai goma sha hudu, zaune suke atsakar gida kan tabarma, su hajara na shiga matan suka bisu da idanu.

Sannu hanne tayi musu sannan tace, ” dan Allah wace karshe?” wata yar matashiyar mata ce da bazata wuce shekara talatin ba tace, ” ni ce karshe amma kunsan k’a’idar malam idan yaga mace daya to namiji daya ne zai shiga”  eh, nasani, hanne ta bata amsa tana kokarin zama a tabarma, itama hajara guri ta samu ta zauna.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan zamansu kowannen su, tunanin yanda zasu tunkari malam da maganar suke.

Fargabar hanne daya kar malam ya dizgasu cikin mutane, saboda indai bakaxo da cikakkun kudi ba idan ya koroka ya dinga kunduma maka zagi kenan har na soro ma sai sunji, aykuwa hanne na cikin wannan tunanin taji malam me dogon zaure ya koro  wata, kuma karshen zancen baza wuce bataxo da isassun kudi ba.

Hajara ce ta kalli hanne, suka hada ido kasa furta komai sukayi, cikin kowannen su ya d’uru ruwa sai muzurai sukeyi, ga yunwa ta fara addabar su.

Suna nan zaune akayi Azahar, sallah suka tashi suka gabatar duk sunyi wuri-wuri kamar marasa gaskiya, koma wa sukayi suka zauna suna jiran gawon shanu, sai uwar hamma suke rafkawa, yunwa kara sasuk’arsu take yi da k’ishirwa, ga basu da kudin koda siyan pure water ne, ruwan rijiyar kuwa da sukayi alwala dashi sam bazai shawu ba, jajir yake da tab’o haka suka zubawa sarautar Allah ido.

Basu samu damar shiga dakin malam ba sai da sukayi sallah la’asar, suna shiga yana zaune adan dakinsa, kan buzun sa na fatar damisa, gefe ga wani zabgegen carbi sai kwarya, mudubi, wuk’a, wuri, k’ahon barewa da kofaton giwa da dai sauran abubuwan sa na aiki.

Zama sukayi a sanyaye, hanne ta dubi malam ta zayyana masa duk abinda yake tafe dasu.

” Ke kalleni nan, matsalarki me sauki ce, ba wani lokaci za’a dauka ba, sai shi mijin naki yana da dan taurin kai saboda yawan ibadar sa, amma zamu dan kwankwasa shi kila inhadashi da yar buzaye, ungo rike nan ki dauki daya” malamin ya karasa magana yana watso mata carbi.

Dauka hajara tayi ta mik’awa malam, karba ya yi ya jujjuya shi, sannan ya dunkule shi  ahannunsa , zuwa wani lokaci ya bude sannan yace, ” shi mijin naki shine wani dan dogo haka ruwan tarwada? Yana da dan gashin baki ko?  Ay gashi cen ma yana zaune gun mahaifiyarsa da carbi a hannu,”

Karaf hajara tace, ” eh shine”

Mudubi ya dauko, ya zuba ruwa acikin kwarya ya dora mudubin akai, zuwa wani lokaci kadan ya dago mudubin yana kallansa tsaf sannan yace, ” kunyi sa’a fulani tana nan vata da wani aikin dan haka inajin ita zan dora akan aiki ki.

      Zaki bada dubu hudu kudin yanka za’ayi mata yanka na bakin zakara da ja, sannan sai kudin gero wanda za’akai shi gidan tururuwa, shi kuma dubu daya ne, sauran kudin kayan aikin dan kayan sai na nemi aljanu sun je cen taikun kwara, suma yanka za’ayi musu”

Gaba daya dai zaki bada dubu goma sha biyar, ya karasa maganar yana mik’o mata hannu alamar yaji dumus.

Hada ido da hanne sukayi, hajara ta yi mata alama da ido, hanne ce ta karkatar da kai gefe ta sunkwi da kai kasa ta fara wassafo masa bayani, ” Allah ya taimaki aikin malam Allah ya karawa malam lafiya, wallahi mun shigo mota……… Tas hanne ta bashi labarin duk abunda ya faru dasu acikin mota.

Lokaci guda malam me dogon zaure ya hade girar sama data kasa ya tsuke fuska, cikin tsawa ya fara yiwa hanne magana, ” hanne sai kace bakisan doka ta, kinsan dai ko kallan mutum banayi sai ya zube mun kudi, sanin bakya mun wasa da kudi yasa na shiga yi muku bayani kai tsaye, ashe bakuda ko kwandala kuka sani nake ta surutu abanza da wofi”

Hajara ce ta dan kara kwantar da murya tace, ” malam dan Allah ka taimakeki ba dan ni ba kayimun aikin nan, na maka alkawari nan da kwana uku zan kawo maka……………

Azafafe malam ya katse hajara, ” ke dallah rufe mun baki, naga alama ke bakuwa ce wallahi kika kara magana sai na maida kafafuwanki wuya, shashasha kawai munafuka kinsan da Allah kika xo nan? Ku tashi ku fice mun   ko inhada ku da Aljani dan kanannad’o ya nad’e mun ku”

Sum sum sum jiki na rawa suka fito daga dakin, mutane suka zubo musu idanuwa, kasa-kasa wasu mata suke gulmarsu, takalmansu suka saka suka fice daga gidan.

Tunda suka fito daga gidan malam suke zuba sauri, ko waige bameyi acikinsu, daka gansu duk sun fita hayyacin su sunyi fik’i-fik-i dasu duk sunsha wahala, babu wanda yace wani uffan acikinsu har sai da sukaje tasha.

STORY CONTINUES BELOW

Hanne ce ta fara magana, ” hajara dama na gaya miki mutumun nan sam bashida mutumci, indai akan kudi ne to shi bashi da sabo, ni na rasa hali irin na malam yau da gobe ay tafi karfin wasa, ay yaci ace nida shi mun saba”

Ummmm hanne kenan kinaji yana zai turo mana wani aljani, ya nade mana kafafuwa, nidai dan Allah kiyi shiru kar muxo ko yana jin mu, muje ya turo mana da aljanu su halaka mu.

       Sosai hajara taso ta bawa hanne dariya, ganin yanda hajara duk tabi ta tsure lokaci daya, dan karta kara kular da ita tasa tayin shiru da bakinta.

” Hajara wai ya zamuyi da batun tafiya gida ne? ” yooo hanne ya zamuyi bara zamuyi har mu samu kudin mota ko amaleji ne akaimu?

” BARA fa hajara, kina gani magriba na kawo kai, nidai shawara zan bayar me zai haba muje gurin masu motar mu rokesu alfarma, ko a maleji ne su kaimu” hanne ta fada.

To shikenan hanne muje Allah ya d’ora ku akamsu.

Haka suka rankaya gurin da ake lodin motoci, kwandastan motar suka samu suka dan jashi gefe, rokonsa  sukayi akan ya rage musu hanya, amma yace suyi hakuri idan ogansa yaji ya dau mutane kyauta fada zai masa.

Zama sukayi har motar ta tashi a gabansu, sannan suka kara jarraba motar da aka fara yimata lodi itama ba sa’a, duk motocin da zasu tsaida babu wacce suke samun dacewa aciki.

Masu mutumci ne ma suke gaya musu magana me dadi su basu hakuri, amma wasu sai dai su kyaresu ko suyi musu banza.

Gajiya sukayi suka koma gefen wata bishiya suka zauna, hanne ce ta kalli hajara tace, ” hajara yau munga ta kanmu kiga mutanen nen kamar ba musulmai ba, kayita hada su da Allah suna dauke kai, amma Allah wadaran naka ya lalace”

Ummhumm hanne ni narasa bakin magana, wallahi cikina ya kulle ga wata kishirwa da nake ji, ko zamu tambaya cikin tashar nan koda rijiya me dan kyau muje musha ruwa………”

Katse ta hanne tayi cikin sauri, ” ki sha dai ni kinga idan kinganni a lahira kaini akai, rijiyar tashar zaki sha ruwa tab Allah bada sa’a, bakiji ance indare yayi ba, kashi suke a leda suna wullawa cikin rijiya, ki bari mu samu wani mutumim wanda yayi shigar kamala sai mu tambaye shi”

“To shikena hanne” hajara ta bata amsa.

Suna nan zaune jugum kowannen su sai sak’a da warwara yake cikin zuciyarsa, wani mutum ne yaxo wucewa cikin manyan kaya, hannunsa rike da igiyar ragonsa yana ja, hajara ce ta kalli hanne tace, ” dan Allah kiga wani magidanci gwanin sha’awa ya saiwa iyalinsa ragon layyah, banda nawa mijin yanxu da mlm kabiru ya siyo mana _*Ragon Layyah*_ da me zai fito dani gurin wani malam me dogon zaure har yana wulakanta mu, gashi nan _*Sanadin Ragon Layyah*_ ankwashe mun mak’udan kudina ajaka, mun yi wunin yunwa da kishirwa, kai gaskiya Allah wadaran hali irin na mlm kabiru”

Hmmmm hajara kenan dan Allah banasan ki da saurin karaya, haba kamar bakisan tsautsayi ba, wadannan kudin fa da kin fito da baki fito ba wallahi tunda Allah ya rubuta sai sun b’ata ba makawa, ay kisha kurumunki wallahi yanda mlm kabiru ya kwasa miki takaici zaiyi bayani, ni bari ma naje na rokar mana shi pure water naga ya tsaya kofar shagon me cajin cen” hanne ta karasa magana ta nufar mutumin.

Da sallama ta isa gurunsa, cikin kwantar da murya take rokonsa ya sai musu ruwa, ba musu yace ta karbi guda hudu agun me cajin, dayake yana sai da ruwa dasu drinks, godiya tayi masa sosai sannan ta karba, har ta juya zata tafi ta kara komawa cikin alamar tausayi ta fara kai masa kukanta.

               

Duk abinda ya samesu tas ta gaya masa amma banda zuwansu gidan malam me dogon zaure.

Ya tausaya musu mat’uka sai dai naira dari ya dauko ya basu, ya kuma basu hakuri da cewar kudin hannun sa na motane kawai sukayi saura, sai naira darin da ya basu.

Godiya hanne tayi gwiwa a sanyaye sannan ta juyo, ta dawo gurin hajara ta yi mata bayani.

Hajara bata iya bawa hanne wata amsa ba sai idanu data zurawa mata, ta kuma zabga wani uban tagumi.

Kiraye-kirayen sallah magariba aka fara, jama’ar dake cikin kasuwar duk sun fara watsewa masu rumfuna duk sun fara hada kayan su, masu kashin kaya irinsu kayan miya, albasa, yalo, dabino da dai sauransu duk sun fara kwashe kayayyakin su, hadari ne yake haduwa ana dan kad’a iska gari ya fara duhu.

Hajara ta kalli hanne tace, ” hanne zama be ganmu bafa kinga garin nan kara rinewa yake, muje mu jarabba sa’a ko zamu samu wani ya dubi Allah da ma’aiki ya rage mana hanya, amma idan mukace zama zamu cigaba dayi wallahi sai mu kwana agurin nan”

” kuma fa zancen ki yana hanya wallahi tun lokaci bai kure mana ba muyiwa kanmu lamuni mu nemi mafita, ke idan ta kama ko cen babban titi sai muje mu fasa kuka mu nemi taimako, tashi muje kinji” hanne ta karasa maganar tana sanya takalminta.

Gurun lodin motocin suka kara komawa, zuwansu keda wuya suka tarar da motar ta cika, har driver ya tada motar gefe suka koma aka turo wata mota wadda itace ta karshe ajerin layin gurin.

Kwandastan suka kira gefe  suna yi masa bayani.

Wani mutumi ne yaje wucewa ta gurunsu yaji suna magiyar arage musu hanya, akan kunnensa yaji kwandastan yana kafta musu rashin mutumci, hajara har tana durk’usawa kasa tana rokonsa.

Dawowa mutum yayi ya fara tambayarsu, ” Bayin Allah lafiya me yake faruwa ne?”

      Hanne har tana tuntube ta karaso gurin mutumin da sauri tana kara yi masa bayani tace, ” bawan Allah wallahi kaga tun azahar muke gurin nan munxo kasuwa siyan raguna aka yashe mu tun acikin mota, jakar tamu gaba daya aka dauke ko biyar bamu da ita, shine muke rokon mutumin cen ya taimaka ya rage mana hanya ko da a maleji ne” hanne ta karasa bayani tana zubda kwallah.

Ya tausaya musu sosai musamman yanda yaga duk sunyi zuru-zuru, ga hadarin da yake kara hadowa, dan jim kadan yayi su hajara har sun fara fidda rai, sannan ya kallesu yace, ” wani hanzari ba gudu ba, nima kano na nufa amma maganar gaskiya mota ta akori kurace, kuma shanu da tumakai ne abayanta, idan kuna ganin zaku iya shiga  to naga akwai sauran guri bata cika ba”

   Hajara ce tai karaf cikin zumudi tace, ” me zai hana malam, mungode kwarai Allah jikan mahaifa, muda muke neman mota ido rufe Allah saka da alheri”

Hanne ce tayi dagalo tana jinta, cikin zuciyar ta take ayyana, ” yanxu inba kaddara ba me zai kaimu cikin motar shanu da awakai daga nan har kano kamar wasu dabbobi, wannan masifa dame tayi kama wai ni hanne yau ni ce zan shiga motar shanu ” mttswww dan guntun tsaki taja kasa-kasa sannan tace mai mungode malam Allah raya zuria.

” Aamen ya rabbi, to ku dan zauna sun kusa gama lodin ragunan, suna karasawa zamu tafi”  ya basu amsa yana dauko goro daga cikin aljihunsa.

Gefe su hanne suka koma suna jiran agama lodin raguna su tafi, amma kowacce da magana abakinta.

_Vote_

_Comments_

_Share_

*MUM ASALM Ce*😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        16-20

Hanne fakar idon mutumin tayi ta dan zunguro hajara kasa-kas ta fara yi mata magana, ” hajara yanxu motar dabbobi zamu shiga    kodai zamu ce masa mungode mu nemi wata motar ne? “

Wani kallan baki da hankali hajara tayi wa hanne sannan ta bata amsa, ” lallai kekam hanne bansan da wane suna zan kiraki ba, yanxu mu wuni a wahale muna neman motar sannan yanxu Allah ya rufa mana asiri mun samu za’a rage mana hanya sannan kice mu bashi hakuri mu nemi wata, ni kam yau ba abinda zai hanani hawa motar nan sai dai idan shi yace ya fasa daukanmu”+

“To shikenan Allah ya sauke mu lafiya” hanne ta bata amsa.

mutumin na cen gefe sai gartsar goro yake, bayan ya gama ci ruwa ya bula ya kurkure bakinsa ya watsar gefe, yana nan zaune wani matashin saurayi yaxo gurinsa ya dan rissina yace.

       ” me gida ankammala lodun ragunan akwai sauran abunda za’ayi? “

A’a shikenan kacewa Isa ya karaso da motar nan, akwai matan da zamu ragewa hanya, ya hanzarta da Allah kaga garin nan k’ara haduwa yakeyi” mutumin ya karasa maganar yana mikewa tsaye.

       Ba’adauki wani lokaci ba Isa ya karaso da motar, saukowa yayi yaxo ya mik’awa ogansu mukullin.

Motar irin akori kurar nan ce bayan ta abude yake, shanu biyu ne aciki sai raguna da tumaki masu dan dama.

Kallansu ogan nasu yayi ya umarcesu da su shigon sha’aibu su dauko masa buhunhunan shinkafa guda uku daya siya.

       Debo buhun shinkar sukayi suka loda su agaban motar kusa da mazaunin driver, bayan sun rufe suka dawo bayan motar suka d’ane suka hau.

Ogan nasu ne ya leka gurin da su isa suka haye yace, ” isa ku dan tura ragunan nan gaba sai kusa musu gora na nan akasa, kudan matsa kuma gaba kunga da bayin Allah nan zamu tafi”

     “Hajiya bismillah ku zo zamu wuce” ogansu isa ya fada yana haye gaban motar.

Su hajara ne suka karaso gurin motar, hanne ce ta kalli dan tudun bayan motar da alama dai ya musu tudu bazasu iya hawa ba.

Magana ta farayiwa isa.

      ” saurayi dan Allah taimaka mana bazamu iya hawa ba motar ta mana tudu”

Yooooo wane taimako zan muku ga dai benci cen ku dauko ku taka sai ku hawo.

Ba musu hajara taje ta dauko musu benci ta ajiye, hanne ce ta fara takawa ta haye sannan hajara tabi bayanta suka d’are saman motar, sai ga su hanne cikin raguna.🤣

Atsaye suka tsaye isa yasa hannu ya sa sakatar motar, sannan su hajara suka samu suka jingina.

Magana su isa suka yiwa ogansu sannan ya tada motar suka dau hanyar kano.

Sun danyi tafiya me nisa ba me yiwa kowa magana, suna hanya aka fara yayyafi da walkiya kafin wani lokaci ruwan sama ya dauko.

Ruwa ake tafkawa kamar da bakin kwarya, andan dauki lokaci ana ruwa daga baya ruwan ya tsagaita sai iska da take tashi.

STORY CONTINUES BELOW

Su hanne sunyi zumu-zumu duk sun jik’e kamar ansaka kaza aruwa, hajara har ta fara rawar d’ari kayan jikinsu sun jik’e sharkaf, kafafuwan su duk fitsari da kashin raguna ne, gaba daya gurin da suke ya jagale abun kyankyami.

Suna tafe iska tana dan kadasu, har suka kusa karasowa cikin gari, adaidai na’ibawa motarsa ta yi parking, saukowa yayi ya zagayo gurunsu hajara yace.

      ” Hjy ni anan zan dakata domin akwai sak’on da zan bayar”

Bayan su hajara sun sauko, dari uku ya dauko ya mik’a musu, yace su yi kudin mota da ita, har rige-rigen karba suke suna zabga masa godiya, tsallaka titi sukayi kowacce jiki yayi likis saboda gajiya.

     Sun dan jima atsaye sannan suka  samu adaidaita sahu, tafiya me dan tsayi sukayi dan sahu ya kaisu unguwar gaida.

Bayan sun sauka tafiya suke ahankali saboda yanda kafarsu tayi tsami, murnar su daya da garin yayi dubu, bare yan sa’ido su kare musu kallo.

         Suna zuwa kan layinsu kowacce tayi gida ko kyakykyawar sallama ba suyi ba.

Hajara na shiga gida ta samu su fiddausi su kadai suna hira, suna ganinta suka tafi ta gudu suna mata oyoyo.

Fiddausi ta fara jero mata tambayoyi, ” umma jikin kawun ne ya matsa mukaji shiru baki dawo ba ko ruwan sama ne ya tsaida ki, dan naga duk kin jike kunje asibitin me suka ce? Ya karfin jikin nasa?”

Sam hajara ta manta ma da tace musu asibiti zata je kai habu, cikin duburburcewa tace, ” umm iyi to jikin nasa da sauki wai maleria da typod ne sukaci karfinsa, amma anyi masa karin ruwa da allurai, ya warware jikin nasa”

“To Allah bashi lafiya” fiddausi ta fada.

Hajara ruwan zafi tasa fiddausi ta dora mata, bayan yayi zafi wanka ta shiga tayo alwala ta gabatar da sallolin da ke kanta.

     Ruwan tea me kauri ta hada tasha, ko minti goma batayi ba da haye gado baccin wahala yayi awon gaba da ita.

Bayan Malam kabiru ya dawo yaso ya same ta ido biyu,  amma ganin kamar a gajiye take yasa ya kyaleta da maganar da yaxo yi mata zuwa safiya.

Washe gari da safe, bayan sun gaisa malam kabiru ya fara mata magana, ” hajara na shigo jiya da dare naga kina bacci da alama kingaji da yawa, ya kika baro me jikin? “

   Hajara ba kunya ta amsa da, ” wallahi malam jiya na gaji ne likis jiki da sauki sunyi mai allurai da karin ruwa, jikin ma tunkan na taho yayi kyau kasan zazzabin nan baya kama mutum ta dadi”

     ” To Allah ya kara lafiya”

Hajara ta amsa da ” Aameen”

  Mlm kabiru ne ya kalli hajara yace, ”  shekaran jiya da dare nazo da kudi gidan nan, wadanda na hadasu zan biya malam mudi kudin hayar mu, dubu saba’in ne cas na sasu a aljihu, amma abun mamaki jiya na kaimasa yana irga kudi yaga ba dubu uku……”

     Da sauri hajara ta katse shi, ” bangane ba malam  kana nufin sata akayi maka kenan, acikin gidan nan? “

A’ a ni bance sata akamun ba, amma ina mamaki ne dan Allah idan kingansu ki bani, inajin ko da zan cire kaya ne suka dado.

        Azafafe hajara tace, ” bangansu ba idan kuma ni kake zargi shikenan nagode malam Allah saka da alheri”  ta karasa maganar tana fashewa da kuka.

Hajara karki mum mummunar fahimta, ni ba nufina kenan ba amma tunda baki fahimceni ba dan Allah mubar maganar, ni banasan ayi ta kace-nace.

” Malam ay kaine da wata magana yanxu yaushe zankai hannuna aljihunka, naga cemun kayi ma kudin gurinka kenan, kuma ka nemi ka zargeni ka tuna dai inda ka zubar da kudin” hajara ta fada tana juya kai gefe kamar ba ita ta dauka ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Shikenan maganar ta wuce hajara”

hajara cikin zuciyar fes dan tasan dama, mlm kabiru va mutum ne me hatsaniya ba, idan ta murje idanta shikenan zai ce abar maganar.

Hajara kallan mlm kabiru tayi sannan tace, ” malam ya maganar ragon namu tunda dai ka biya kudin hayar mu, ay nasan komai ya warware yooo banda mlm mudi baida mutumci, idan shi wani ne ba ya daga mana kafa zuwa nan da wata biyu ba, ka sai mana ragon inyaso daga baya inka samu ka biyashi”

” Hmmmm hajara kenan, idan kina abu kamar karamar yarinya sai kiyi ta shirme, wani abun ma yarinyar cen fiddausi bazata yi ba, ni bari nazo na wuce” mlm kabiru ya karasa maganar yana mik’ewa tsaye.

” To Ay shikenan malam, yauwa hanne batajin dadi zan dan shiga induba bata wai har karin ruwa itama akayi mata”

” Ki duba ta amma karki dade agidan, dan banasan wannan zaman na gidan mak’ota banda gulma ba abinda ake kullawa ” mlm kabiru ya bata amsa yana fita daga dakin.

Agurguje hajara tayi abun da zatayi ta fada gidan hanne, da sallama ta shiga ta taradda hanne zaune tana ninke kaya.

Da murmushi hanne ta kalli hajara tace, ”  yar halak yanxu nake zancen ki azuciya ta, wallahi yanxu nake cewa zan shigo muyiwa juna bangajiya, to ya gajiyar ta mlm kabiru ikon Allah”

Dan murmushin jin dadi hajara tayi tace, ” kai hanne bakya rabo da abun dariya, wallahi gajiya tabi lafiya amma gajiya kam ay munsha ta, nikam wannan tafiyar dan ba kara”

    ”  wallahi ni kaina hanne dana kwanta sallah asuba sai takwas da rabi nayita, dan tunda uwata ta haifeni bantaba yin tafiya me wuya irin ta jiya ba” hanne ta fada.

Hajara ce ta tambayi hanne, ” wai ni ina furaira n banji motsinta ba ko bata tashin daga bacci bane?”

” wallahi nima ban dawo na sameta a gidan ba sai da na kirata tace mun wani Alhaji ta raka bude meeting kaduna dare yayi musu shi ne suka kwana, amma tace mun yanzu haka suna hanya, dan munyi waya da ita d’azu kafin shigowar ki” hanne ta karasa maganar tana yashe baki.

Hajara kallan tsaf tayiwa hanne sannan tace, ” Anya hanne baki wauta ba, yanxu furaira har fita take da samari tana kwana awaje, bakya tsoron halin mazan wannan zamanin, furaira fa ita kadai ce yarki dan Allah idan mafarki kike hanne ki tashi”

“Dakata hajara ina ganinki da mutumci ya zaki bullo mun da haka, ko kema biyewa gulmar yan unguwa zakiyi? Yanxu furaira akirata da karamar yarinya, yar shekara ashirin da biyu ay ba yarinya bace tasan fari tasan bak’i ta kuma san me ke mata ciwo, na tabbata babu wani namiji da zaiwa furaira dabara, kuma kullin zata fita sai na mata addu’ar Allah ya tsare ya kare, dan Allah hajara karmu fara haka dake kinsan yanda nakesan furaira kamar raina” hanne ta karasa magana cikin tsuke fuska.

     A sanyaye hajara tace, ”  Dan Allah hanne karki mun mummunar fahimta, kiyi hakuri idan magana ta ta bata miki rai”

“Shikenan komai ya wuce amma ki kiyaye gaba” hanne ta fada.

Hanne ce tace, ” Hmmmm hajara tsegumi ne abaki na fa, yau da safe nake jiyi kukan rago agidan lami me kosai, wallahi dan intabbatar da tsegumi na har sai da na sab’i naira hamsin naje siyan kosai, Abun mamaki ina shiga na hango rago antirkeshi sai cin harawa yake, kuma wallahi baki ganshi ba dan madaidaici dan baza’a kirashi kafi zuru ba…………”

Da sauri hajara ta katse hanne da, ” kan uban nan hanne badai gidan idi me wanki da guga ba? “

   ” Yooo cen mana muna da wata lami me kosai a layin nan banda abinki inba lami matar idi me wanki ba, nima  furaira rannan take cemun wannan sabon Alhajin da ta hadu dashi yace sallah bana raguna biyu zaiyi mana, amma kuma tunda bangansu ba banga ta magana ba, shiyasa ko ke banyi wa hirar ba karnazo baiyi mana ba naxo naji kunya, duk da dai nasan ko baiyi ba furaira zata yi mana” hanne ta bata amsa.

STORY CONTINUES BELOW

Nannauyar ajiyar zuciya hajara ta saki cikin damuwa tacewa hanne, ” tabdijan lallai kice ina cikin tsaka me wuya, yanxu su har su lami suyi layyah amma ace gidana babu labari, hanne kinsan yanda layin nan namu yake idan aka kafa gulmarka, dan Allah meye mafita hanne ki bani  wata shawarar”

“To nidai ayanxu shawarar da zan baki itace, ” ki nemi rancen kudi ki je ki sayo muku rago, ki tirke shi ke ko hirar ma karki masa kice wai zaki ranto kudi, kiyi gum da bakinki idan yashigo yaga rago na tabbata zai tambaye ki, inyaso sai ki gaya masa nasan dai duk abun mlm kabiru bazai ki biya ba, kinga idan kika yi haka wazai ji bare asaki abakin duniya”

Cikin damuwa hajara tace,  ” to ni hanne bank’i ta taki ba amma a ina kike ganin zan samu yancen kuma kamar nawa zan ranxi kudin? “

Eh to, ki ranci kamar dubu talatin da biyar zuwa arba’i , kuma rance karki damu zan rakaki gidan lubabatu me adashi, muna abin arziki da ita nasan zata bak’i dan tana ganin mutumcina, kinga idan kika karba sai inraka ki unguwar yan awaki ta unguwa uku muje ki tarxo santalelen ragonki, wanda da anganshi ansan ba karya” hanne ta karasa maganar cikin murmushi.

Hajara wani farinciki ne ya lullubeta ji take kamar taje ta siyo ta dawo gida, cikin jin dadi tacewa hanne, ” naji dadin shawarae nan taki, yanxu dama kina da wannan shawarar kika kaimu jiya mukaje mukasha bakayar wahala”

     ” yo hajara idan Allah ya yanka maka kazarar wahala ay sai ka fige”  hanne ta karasa mafanar suna kwashewa da dariya.

Suna zaune suna hirarsu sukaji sallamar furaira ta dawo, tun daga tsakar gida take kwallawa mahaifiyar tata kira, da gudu hanne ta tashi ta je ta taro ta tana mata oyoyo, ledojin hannunta hanne ta karbo furaira ta biyota suka shigo cikin dakin.

” Wash Allah na inna wallahi duk na gaji kai kaduna itama ba laifi akwai nisa, kafafuwana duk sunyi tsami dan Allah doramun ruwan wanka inna” furaira takarasa zama tana cire dankwalin kanta.

Cikin sakin fuska take gaida hajara, ” umman su fiddausi ina kwana?”

” Lafiya klau furaira ya gajiyar hanya” hajara ta amsa gaisuwar tana karewa furaira kallo, ganin yanda duk tabi ta kara kwailewa ga kan nan yasha uban k’arin gashi, hannuwa farce zak’o-zak’o kamar ba yar musulmai ba.

Wasu daka-dakan kaji ne acikin leda hanne ta fito dqsu, dayar ledar fresh milk ne da hollandia da dai sauran tarkacen drinks.

Dan yatsina fuska furaira tayi tanawa mahaifiyarta magna, ” inna dan Allah ki doramun ruwan wankan wallahi jikina duk ba dadi”

Cikin rawar jiki hanne ta amsa, ” to yar albarka bari na tashi” hanne ta tashi taje dorawa furaira ruwan wanka.

Bayan hanne ta dorawa furaira ruwan wanka, kaji ta baje musu da drinks, sai da suka ci suka yi kat dasu sannan suka tashi suka rankaya gidan lubabatu mai adashi.

Da sallama suka shiga, atsakar gida suka samu lubabatu tana tatar gasarar koko, tana ganin su hanne da murna ta tarbe su, kallan hanne tayi tace.

        ” lale maraba yau na ciri tuta hjy hanne kwana da yawa kinsani kwandan shara, ya gari ya harkoki naji ance kin danne wasu manyan kaya”

     Dariya hanne tayi tace, ” nifa dadi na dake kenan iya shegenki kara yawa yake, idan na danne manya kaya kya ganni ina yawo akafa”

” A’a yoooo wannan abu a duhu, kawata ku shiga daga ciki bari na kara sa” lubabatu ta fada tana karasa matse dutsar geron.

Bayan lubabatu ta gama tatar gasara wajen su hanne ta shiga, ruwa ta kai musu a jug bayan sunsha ruwa sun gaisa hanne ta farayiwa lubabatu bayanin duk abinda ya kawo su.

   Dan jim kadan lubabatu tayi kamar bazata yi magana ba, hanne tace, ”  haba kawata ko bazamu samu bane, nina dauka mun riga mun zama daya, yanxu ko banxo da kaina ba na ce hanne taxo inji ni ay zaki bata bare kuma tare da ita kuma xo, kinsan sha’ani na kudi wata matsala ce ta taso mata kuma ba wadatattun kudi a hannunta, shi ne nace mata inada ke amma naga kamar bazamu samu ba”

STORY CONTINUES BELOW

” Hanne kenan ni bank’i ta taki ba gaskiya ina jin tsoron kar azo asami matsala, kinsan adashi na dan wata-wata nakeyi kuma yawanci ma’aikata ne sukeyi, banasan mutum yaxo yana zuba kudinsa sai dauka yaxo ince mai kudi basu cika ba, hanne kinsan ni bana shiga sabgar jama’a amma akan kudi bana d’aga kafa, idan na baka bashi nace ma rana ita yau nake so to nafisan na same su saboda idan bansame su ba kayan kudi nake d’auka, cikin biyu za’ay daya ko kudi ko kayan kudi” lubabatu ta karasa magana tana kallan hanne.

      Hanne tace, ” Lubabatu karki ji komai kinsan bazan kawo miki wacce zata miki wasa ba”

”  To kamar nawa za’a bata? Kuma yaushe zata biya ” lubabatu ta fada tana kallan hajara.

  Sai alokacin hajara ta samu bakin magana tace, ‘” ehto, kamar dai dubu talatin nake so “

  Hanne ta karaf tace, ” kin tabbata dai dubu talatin zata isheki, karfa sai mun tafi kice bazasu isa ba”

    ” A’a ay ina ganin kamar zasu isa ko, kokuma abani dubu talatin da biyar ina ganin zasu isa”

   Lubabatu tace,  ” to nidai ki tsaida magana daya, kuma ni bana bada bashi fa sai munyi rubutu atakarda kinsa hannu na saka hannu na yarjejeniya, idan kin amince shikenan”

  ” Eh na amince a bani dubu talatin da biyar din ” hajara ta fada.

   Daki lubabatu me adashi ta shiga ta debo kudi ta k’irga su tabawa hajara ta kirga itama, takarda da biro ta dauko ta kwalawa nasiru kira ( _Babban d’anta_) bayan ya shigo, lubabatu tace, ” hajara, hanne ita zata zama shaidarki nikuma ga nasiru shine shaida ta dan haka ga takarda ki sa hannu”

  Ba musu hajara tasa hannu, ta karbi kudin sukayiwa lubabatu godiya, antsaida magana akan kwana arba’in hajara zata biya kudi, da wata daya lubabatu tace suka nemi akara yan kwanaki, daga baya ta karawa hajara kwana goma sannan suka taso suka fito daga gidan.

Bayan fitowar su hajara cikin farin ciki tacewa hanne, ” wallahi karkiji yanda naji dadin kudin nan yanda kikasan kyauta aka bani su, kai hanne nagode miki Allah bar zaman tare”

    ” Ameen hajara, meye abin godiya ay anzama daya sai dai kinsan matsalar lubabatu bata da mutumci akan kudi idan baki bata kudinta akan kari ba, to kuwa zakiga aynihin kalar ta” hanne ta fada.

   ” Haba Ay haka ma bazata faru ba, hanne yaushe zaki rakani kasuwar yan awakin ne? ” hajara ta tambayi hanne.

  Hanne tace, ” kai hajara sai dai zuwa gobe dan wallahi har yanxu jikina ciwo yake mun, kamar wacce akayiwa duka”

  Hajara tace, ” To Allah ya kaimu, nima ay ba yau zamu ba tunda ban tamvayi mlm kabiru ba, hanne bari na wuce sai mun hadu goben na bar yara agida. “

   Daga haka sukayi sallama kowa ya kama gabansa.

Bayan hajara ta koma gida cen kasan kayan ta tura kudin, tana tunanin wacce karya zatayi wa mlm kabiru dan ta samu ta fita siyan rago.

    Da daddare bayan mlm kabiru ya shigo gidan, suna zaune hajara sai janshi da hira takeyi, cikin hirar take  gaya masa washe gari zata kara komawa ta gano jikin habu, da farko mlm kabiru ya hanata tunda tace jikinsa yayi kyau, sai data hada da karya sannan ya kyaleta, murna fal zuciyar hajara tana zumudin gari ya waye.

   Washe gari, wajen karfe sha daya na safe hajara taje ta biyawa hanne suka tafi kasuwar yan awaki dake unguwa uku.

    Kasuwar cike take da mutane kowa sai hada-hadarsa yake, su hajara ne suka fara cinikin wani rago, ba laifi yana girma kuma jikinsa ba yunwa, dubu talatin me ragon yace musu da kyar cini ya fada akan dubu ashirin da bakwai.

   Igiya, harawa da kowar wake, hajara ta siya suka rankayo basu suka dawo gida ba sai kusan azahar, turke tayi masa awajen bandaki aka zuba masa abinci da ruwa yana ci.

   Hanne ce ta kalli hajara tace, ”  yanxu dan Allah hajara bakya jin zuciyarki fes cikin jin dadi? “

   ” Hmmmm bari hanne ay wallahi farin ciki ne ya hana ni magana, gaskiya samun mutuniyar kirki kamar ki sai anduba, kawata nagode kwarai”  hajara ta fada cikin jin dadi.

   Hanne tace, ” ni idan kina mun godiya sai indinga jin wani iri hajara ay mun riga mun zama daya, ni bari na karasa gida sai anjiman mu”

      Sallama sukayi hanne ta tafi, hajara sai karajin kaunar hanne take axuciyarta tana kuma alfahari da ita, hajara ta dade a tsaye tana shafa rago tana jin dadi, shikuwa yayi luf kamar ba shi ya cika su da kuka ba farkon xuwansu.

Da daddare bayan mlm kabiru ya dawo daga gidan mahaifiyarsa suna zaune suna hira da hajara, yanayinta kadai ya kallah yasan tana cikin farin ciki, abinci ta zubo ta kawo masa mlm kabiru yace.

        ” hajara na lura kina cikin farinciki meyake faruwa ne? Matso muci abincin mana ko ke kinci naki? ” mlm kabiru ya fada.

  Murmushi ne a fuskar hajara ta matso tace, “a’a banci ba dama tare na zubo mana”

   Tashi tsaye mlm kabiru yayi yace, ” to bari na kewa bandaki nayo fitsari, wannan fara’ar ba banza ba bari naxo ki bani labari”

      Buta mlm kabiru ya sab’a yayi hanyar bandaki yana haska fitila, turus yayi ganin rago akwance cikin mamaki ya furka, _*RAGO,*_ da sauri ya juyo gurin hajara yana kwala mata kira.

_kuyi hakuri banyi editing ba._

_Vote_

_Comments_

_Share_

     *MUM ASLAM Ce* 😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        21-25

_Sorry for not editing_👏🏼

” Hajara hajara, wai hajara ina ta magana baki amsa ba zo nan maza-maza ki fito” mlm kabiru ya fada yana kara haske rago dake kwance.+

   Da sauri hajara ta fito daga d’aki abayan katangar dakinta ta lab’e tana leken mlm kabiru, gabanta ne ya yanke ya fadi, ta fara fargabar abinda zata gaya masa.

    Jin hajara shiru yasa mlm kabiru ajiye buta ya nufi daki gurunta, hajara najin tahowar mlm kabiru ta fada d’aki ta koma mazauninta, sai raba ido takeyi kamar munafuka.

        ‘Dakin mlm kabiru ya shiga ya tsaya ya fara yiwa hajara magana yace,  ” hajara bakya jin ina kiranki ne tun daga waje nace a ina kika samu rago? “

    Hajara dauke kai gefe tayi zuciyarta na lugude, bata tab’a tunanin zataji shakkar gayawa mlm kabiru maganar rago ba sai yanxu daya tirketa da tambaya.

       Cikin tsawa ya katse mata tunanin da takeyi yace,  ” magana nake miki kina jina sai juya kai kike, nace a ina kika samu rago, wallahi hajara ki bude baki kimun bayani tun raina bai b’aci ba”

     K’asa-k’asa hajara ta bud’e baki tace,  ” d’azu ne na siyo shi bayan na fita”

     Kika siyo hajara? Dama kinada kudi har wanda zaki iya siyan rago, ke da ba aiki ba ba kuma kasuwanci ba, ko kina wani kasuwancin aboye bansani ba? “

      ”  Mlm jira nake fa dama ka gama cin abincin sai na maka bayani to kuma kazo kanata sababi, dan Allah ka kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ” hajara ta fada cikin karfin hali.

Hankalinsa gaba daya ya tattara akan hajara yace, ” ina sauraronki kimun bayani yanxu basai anjima ba “

       Kallansa hajara tayi taga fuskarsa ba alamun wasa, hakan ne yasa ta fara magana tace,  ” dama dazu ne dana fita na biya gidan lubabatu me adashi, na karbo rancen kudi dubu talatin da biyar nace mata idan ka samu albashinka na watan gaba zaka biya ta, to daga nan sai naje kasuwa na siyo……………. “

Cikin tsananin bacin rai mlm kabiru ya buga mata tsawar da har sai da ta sata matsawa cen karshen gado,   ” zaki rufemun baki hajara ko sai na tattakaki agurun nan, na rasa kedai hajara wacce iri ce idan kina abu kamar me kan tinkiya, na aike ki nace kije ki ciwo mun bashi, wato duk abunda nake acikin gidan kin raina ko baki da gashin wance kice sai kinyi kitson wance, tunda nake dake na taba zuwa gun wani rancen makudan kudi har dubu talatin da wani abu, hajara wannan tozarci har ina a wannan rayuwar da muke ciki wasu fa basa samun ci uku rana, amma ke me kika rasa akan nace miki bazanyi layyah ba duk kike mun wannan tonon asirin, wai kece harda zuwa rance ki sai rago sai kace ke kike aurena , ki bude kunnen ki da kyau kiji wallahi-wallahi ba agidana ba ko ki kai mata ragon ki cika mata kudinta ko kuma ki saida ragon ki maida mata kudinta, amma ni da kike gani biyar dina bazatayi ciwon kai ba “

Idanun hajara ne suka fara raina fata cikin firgici tace,  ” Dan Allah dan Annabi mlm ka taimaka ka rufamun asiri, dan Allah karkayi mun haka ka fiddani kunya tunda sai karshen watan gaba zaka bi……….

STORY CONTINUES BELOW

Katse ta yayi cikin fushi yace,  ” karshen watan ke zaki bani kudin ko kuma ajiya kika bani? Wallahi hajara kin bani kunya kin cuceni ko ince kin cuci kanki, _SANADIN RAGON LAYYA_ kina neman ki zubar mana da mutumci agaban yan unguwa, wannan abun da kika aikata wallahi yafi rashin yankan ragon da nayi, wallah bansan sanda kika kara lalacewa ba hajara, tir da hali irin naki “

     Cikin rawar murya hajara tace, ” wlh mlm a unguwar nan babu wanda ya sanda haka sai lubabatu “

     Mlm kabiru yace,  ” ita lubabatun alwashi ta ci miki bazata gayawa kowa ba, wato kin fi son inatafe ana nuna ni ana cewa na yi rance na sai _RAGON LAYYAH._

Cikin takaici mlm kabiru ya cigaba da magana, ” hajara banzaci rashin hankalin naki har ya kai nan ba wlh, tun wuri tun ban dauki mummunan mataki akan ki ba, kisan yanda zakiyi da ragon cen “

    Hajara ba baka sai kunne, zuru tayi fadan mlm kabiru na kara ratsata, tabbas me hakuri bai iya fada ba mlm kabiru yaje iya wuya, ransa ya gama b’aci fada yake sosai sanin idan ransa ya b’aci bashi da dadi yasa taja baki ta tsuke.

    Yana gama fadan kofar gidansa ya fita ya zauna yana huci, cikin zuciyarsa yana mamakin rashin hankali irin na hajara, dan karamin tsaki yaja afili ya furta, ” zan dau mataki akanki hajara gani kikayi na sa miki ido, kinxo dai-dai gabar da zan miki hukunci yanda ya dace dake “

    Yana nan zaune yana nazari makocinsa mlm sambo ya fito shima kofar gida, mlm sambo abokin mlm kabiru ne kuma makoci nagari yana da halin kwarai, cikin murmushi yace,  ” mlm kabiru barka da dare yau kaine da daddare akofar gida? “

   Mlm kabiru amsa ya bashi amma sam baya cikin walwala, mlm sambo ya lura da haka amma bai tambayesa ba dan yafi tunanin matsalar tashi ta cikin gida ce, shiyasa ya dinga kokarin kawo masa hira masu dadi, ahaka har mlm kabiru ya dan saki jiki suka cigaba da hira.

    Hajara na zaune inda mlm kabiru ya barta sai sak’a da warwara takeyi cikin zuciyarta, hanne ce ta fad’o mata arai ji tayi ina ma rana ce da tuni ta ayka ankira mata hanne ko ta bata wata shawarar.

       A hankali tace,  ” nashiga uku ni hajara yanxu idan mlm yak’i biyan kudin nan naga ta kaina, wallahi da masifar iya nida lubabatu zata tsaya da abun da sauki amma yanxu na tabbata ba iya makotanmu na kusa ba kaf unguwar sai anjini da ita, ni kam dana sani da ban ranci kudin nan ba dan nasan yanzu masifa zasu zame mun, nasan duk tsiya dai mlm zai sai mana naman kasuwa”

   Wannan shi ne karon farko da hajara taji _RAGON LAYYAH_ ya fice mata akai, har tana dana sani.

   Kukan ragon ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, tashi tayi taje ta zuba mai harawa da ruwa ta koma kan gado, jikinta duk asanyaye kamar mara lafiya.

MENENE ASALINSU?

     Hajara lawal  shine aynihin sunan ta asalinta yar garin karaye ce, iyayenta gaba daya ‘yan garin karaye ne, su uku ne kawai agurin mahaifansu hajara ita ce babba sai jamila take binta sai kuma habu dan autansu.

     Mahaifin hajara me suna lawal dan kasuwa ne, matar sa daya rakiya wato mahaifiyar su hajara, kasuwanci yake zuwa kano sarin kaya yana kaiwa cen garin karaye, akwana atashi har ya fara shawa’awar dawowa cikin garin kano kuma ya aminta da haka, rana tsaka ya cewa rakiya ta fara hada kaya sati na sama zasu koma kano.

” Mlm kano fa kace, yanxu garin nan zamu bari garin iyaye da kakanni, mlm nan ce fa mahaifarmu yanxu muna cikin dangi da yan uwa zamu tashi mu koma cen kano, mlm wa muka sani acen nidai na yafe, zan zauna nida yarana inyaso lokaci-lokaci sai ka dinga zuwa kana ganinmu, kana turo mana dan kudin da zamu dinga amfani dasu na yau da kullin ” rakiya ta karasa maganar tana kallan mlm lawal.

      Kallan tsaf mlm lawal yayi wa rakiya sannan yace, ” au rakiya kece mijin kenan ko, to bari kiji umarni ne na baki ba shawararki nake nema ba ki hada kaya asabar ta sama zamu koma kano” yana gamar maganar yasa kai ya fice.

STORY CONTINUES BELOW

    Rakiya kamar ta dora hannu aka ta fashe da kuka, hawaye ta shiga yi tana kuka, babu yanda ta iya haka ta hau hada kaya tanayi tana tunanin irin rayuwar da zasu yi a birni.

       _RANA BATA KARYA_

     Su rakiya sun dawo garin kano inda suka tare a unguwar sallari, sannu ahankali har suka fara sabo da unguwar da mutanen unguwar.

       Lokacin da su hajara suka dawo kano tana da shekara goma sha bakwai aduniya, jamila nada shekara bakwai sai dan autansu habu me shekara daya aduniya.

Sannu ahankali sukayi mak’otaka da gidan mlm hashimu ( _mahaifin mlm kabiru_) me itace, mutanen kirki ne kwarai da gaske zumunci me karfi ne ya shiga tsakaninsu,  makaranta aka saka su hajara ita da jamila, haka suka cigaba da rayuwarsu gwanin birgewa.

      Bayan wasu shekaru Allah yayi wa mahaifinsu hajara rasuwa, lokacin hajara na dakin mijinta har ta haifi fiddausi, mutuwar ta girgiza rakiya matuka alokacin ne yan uwanta suka bukaci ta koma karaye, mlm hashimu shi ya hanata tafiya ya koki alfarmar zai dinga tallafa musu matukar yana raye.

      Sam yan uwanta suka ki yarda sai da kyar ya shawo kansu suka amince.

     Mlm hashimu shi ya dauki ragar su rakiya ta yau da kullin tare da taimakon babban dansa, hatta gidan haya shi yake biyawa su rakiya, da farko mutane sun fara tsaigumi akan cewar mlm hashimu auran rakiya yake sanyi shiyasa ya dorawa kansa wahala, daga baya ne suka fahimci manufa da kyakykyawar niyyarsa.

         Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, akwana tashi ba wuya agurin Allah ance inba tsufa akwai mutuwa.

Mlm Hashim ciwon ajali ne na  b’arin jiki ya kamashi, ankashe kudi sosai, sai da ya shafe shekara biyu da rabi akwance sannan rai yayi halinsa, mutuwar mlm hashimu ta girgiza gidaje biyun nan, haka suka cigaba da rayuwa da dadi ba dadi har aka aurar da jamila.

      _Wannan kenan_

_B’ANGAREN MLM KABIRU_

    Kabiru hashim dan yaro shine cikakken sunansa dan asalin garin kano ne, iyayensa yan unguwar kurawa ce dake wajen gidan sarki, yayi makarantar sa ta boko da ta islamiya ya sauke alkur’ani yana da shekara goma sha tara, yayi karatun bokonsa daga primary har zuwa NCE, yana koyarwa a karamar secondary dake unguwar dorayi.

Auren zumunci akayiwa mlm hashimu da matarsa zuwaira, mlm hashim su biyu ne agurin iyayensu yayarsa me suna Amina itace babba sai shi mlm hashimu daga kansu mahaifiyarsa bata kara haihuwa ba, mahaifin mlm hashimu ya rasu gabannin za’ayi auren mlm hashimu da zuwaira hakan ne yasa aka d’aga bikin zuwa wani lokaci, bayan bikin su ne aka raba musu gadonsu shida yar uwarsa Amina shi ne silar siyan gidansa ya koma sallari da zama, anan kofar gidan sa yake sana’arsa ta itace.

  Suna Zaune da matarsa cikin kwanciyar hankali, har sai da suka shafe shekara biyu da aure sannan zuwaira ta samu cikin mlm kabiru, kwanci tashi Allah ya sauki zuwaira lfy, mlm kabiru nada shekara hudu zuwaira ta samu cikin khalisa itama tana da shekara uku ta kara samun wani cikin, Allah da ikonsan ta haifo yan biyu amma ba wanda yaxo da rai daga kansu sai da ta shafe shekara bakwai sannan ta kara samun wani cikin,  bayan wata tara ta santalo yarta mace me suna Amina daga kanta zuwaira sai da tayi b’ari biyu bata kara haihuwa ba.

Anyiwa khalisa aure tun tana da shekara goma sha takwas, inda mijin nata ya tafi da ita cen jigawa gurin da yake aiki.

       Wata rana suna zaune an aiki Amina siyan kayan miya tsautsayi ya auku wani me mota ya bigeta ko shurawa batayi ba rai yayi halinsa, bayan rasuwar Amina da shekara mlm hashimu ya auri wata bazawara me suna saratu, zaman zuwaira da saratu gwanin sha’awa ahaka suka cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali.

      Mlm kabiru yana matukar tausayawa mahaifinsa ganin irin sana’ar da yake yi, yayi iya yinsa dan ganin ya hana mahaifin nasa saida itace amma yaki yarda.

    Bayan lokaci me tsawo su hajara suka dawo kusa da gidansu mlm kabiru, ana cikin haka soyayya ta shiga tsakani aka daura musu aure.

Bayan auren mlm kabiru da shekara uku mahaifinsa ya kwanta ciwon b’arin jiki, ya shafe shekaru ahaka daga baya rai yayi halinsa.

Gaba daya dawainiyar da mahaifinsa yake yiwa su hajara ta dawo kan mlm kabiru, lokacin da mlm hashimu ya rasu rakiya (mahaifiyar hajara) har ta yanke shawarar komawa karaye mlm kabiru y hanata, sannan ya umarceta da ta koma gidansu kusa da mahaifiyarsa .

Hakan ce ta faru rakiya ta koma gidan su mlm kabiru ya cigaba da rikesu da dadi ba dadi, ana cikin haka wata rana rakiya ta tashi da ciwon kirji me tsanani kafin wani lokaci Allah ya karbi abarsa.

   Akwana atashi shekaru na kara tafiya tsufa na kara zuwa, inna zuwaira ce ta kamu da ciwon hawan jini, hakan ne yasa mlm kabiru yace zai dawo da ita gidansa amma sam taki yarda dole ya saida gidan da take ciki, ya sai mata wani karamin gida a unguwar gaida bayan gidansa.

Habu kanin su hajara shagon wani abokinsa ya samu suke kwana tare, har suka fara koyan gyaran motoci da mashina.

Hajara irin matan nan ne masu san wadak’a da harka faca-faca sai dai ko kadan batasan neman ko ince sana’a, hajara irin matan nan ne yan karya masu nuna san asani da nuna ita wata.

Mlm kabiru yana kokari iyayinsa dan ganin ya kare martabar iyalansa, ba abunda suka rasa sai dan abinda ba a rasa ba, nauyin gidansa dana mahaifiyarsa gaba daya yana kansa.

_Mukoma labari_

Cikin dare hajara na kwance fitsari ya tashe ta, fitowa tayi a falo taci karo da mlm kabiru ya yi shinfid’a ya kwanta, cikin zuciyarta take fadin, ” lallai mlm na yarda yayi fushi sosai, Allah kaimu safiya inshiga gurin hanne dole nasan abinyi”

Hannu takai zata tashe shi wata zuciyar tace, ” kinga ki kyaleshi karfa kije k’iru ta ja bauu”

   Ta gefen sa ta raba ta wuce har taje tsakar gida taga fitilar wajen akashe, touchlight ta koma ta dauko ta wuce toilet tana tafe tana a’uziya kasa-kasa, bayan ta fito  daga band’aki gurin rago ta karasa tana haska wajen tirken nasa wayam ta gani sai igiya cen gefe ga dusa da ruwansa nan.

    Gabanta ne ya yanke ya fadi cikinta ya karta ji kake ya bada wani sauti kuuuuuuu, jikinta har b’ari yakeyi, sawun kafar ragon ta gani har wajen kofar fita.

Hajara ta manta ma dare ne, aguje tayi kofar gida abun mamaki a bude ta samu kofar, cen karshen layinsu ta hango wasu mashina guda biyu, da wasu matasa guda bibbiyu akai kowanne suna dauke da rago daya akai, sun bawa mashin dinsu wuta .

Da gudu hajara ta bazama ciki gida ta dora hannu aka tana kurma ihu, kuka take tun karfinta tana fadin,  ” wayyo Allah na ni hajara yau naga ta kaina na sanya rayuwata cikin tasku na shiga uku, wayyo Allah ragona jama’a ku taimaka ku kamo mun ragona wayyooo rago wayyooo rago wayyooooooo Allah ragona”

       Cen nesa-nesa Mlm kabiru cikin bacci yake jiyo ihu ana kuma bubbuga abu kamar a mafarki, tashi yayi cikin salati yana murza idanu mamaki ne ya kamashi jin muryar hajara, wayarsa ya duba karfe uku saura na dare, haska bakin kofa yayi inda yake jiyo ihun hajara.

   Hango ta yayi kwance abakin kofa tana birgima, zaninta na gefe dan kwalinta na kan buta, daga ita sai dan kanfai da underwear, underwear din ma ya dawo cinya inbanda kalmar rago ba abinda take ambata, tana surutai marasa kan gado.

Mlm kabiru cikin tashin hankali ya tashi saboda tunda yake da hajara bata taba yi masa irin haka ba, gashi cikin dare ne nan da nan wani tunani ya fado masa.

Da sauri ya koma kusa da ita ya fara karanto mata ayarul kuriyyu yana tofa mata.

_mlm kabiru anya ayatul kursiyyu zatayiwa hajara kuwa_🤣

Barkanmu da sallah

*Vote*

*Comments*

*Share*

   _MUM ASLAM Ce_😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        26-30

_Shima wannan banyi editing ba kuyi sorry._😉

Bil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wari daya akafarta wari daya kuma igiyar ta tsinke, buta a tuntsire ruwan cikinta ya tsiyaye tas, surutai hajara ta cigaba dayi bakai ba fasali, hakan ne yasa mlm kabiru ya kara daga murya cikin azama yana karanto mata ayoyin kur’ani yana tofa mata.+

    Hajara cikin fusata tace, ” mlm wai sai tofeni kake yi ni kabarni inji da abinda yake damuna “

Dan dakatawa yayi da karatun yana karewa hajara kallo, tsab muryarta take da alama ba wasu jinnu da suke damunta, zaninta ya janyo ya rufe mata cinyoyinta dasu, yunkurawa hajara tayi ta tashi zaune tana zubda kwallah.

Cikin tashin hankali Mlm kabiru yace, ” hajara lafiyarki me ya sameki cikin dare kike wannan ihun, nasha gaya miki idan zaki kwanta ki dinga tofe jikinki da addu’a, kuma idan mummunan mafarki kikayi basai ki karanta addu’a ki koma bacci ba, idan baccin ya gagareki sai ki yo alwala ki gabatar da sallah ki fawwalawa Allah lamuranki, to hajara kodai gamo kikayi dan naga buta kusa dake ” mlm kabiru ya karasa magana yana kallan hajara da fuska ta hade hawaye da majina.

Hajara girgiza kai tayi sannan tace, ” babu ko daya malam “

Mlm kabiru kuluwa ya farayi cikin fada yace, ” amma ba abinda yake damunki kikaxo tsakar gida cikin dare kina wannan haukan salan mak’ota suce wani abun akai miki ko azaci aljanu kika hau, cire makota ma yanxu da yaran nan sun farka suka fito suka ganki da dan kanfai me zaki ce musu, sai ki tashi ki kamwashe tsummokaranki kiyi gaba, ina cikin baccin na me dadi kin tashe ni “

    Hajara bakin ciki ne ya cikata, zafi biyu ga na rashin rago ga sababin da mlm kabiru yake mata, rushewa tayi da kuka cikin kuka tace, ” mlm rago ne, wallahi ragon nan ne ” sai kuka yaci karfinta ta kasa karasa maganar.

    Guntun tsaki yaja sannan yace, ” yanxu hajara har kin fara sumbatu cikin dare saboda abun duniya, me akayi da rago da har zaki fara surutai mara fasali, badai  rago bane kin siyo to sauran mitar ba meye kuma ?”

    Cikin kunan rai hajara tace, ” mlm sun sace ragon sun gudu dashi”

Cak mlm kabiru ya tsaya cikin mamaki tace sun sace rago to su waye suka sace ?

Duk abinda ya faru hajara ta kwashe ta gayawa mlm kabiru, asanyaye ta nufi hanyar da rago yake, yana haskawa yaga wayam kamar yanda hajara gaya masa, cikin gida ya dawo lokacin hajara ta shiga falo ta zauna, mlm kabiru guri ya nema ya zauna cen nesa da ita yana kare mata kallo cikin takaici da bakin ciki.

Hajara kukanta ta sharba me isarta, sai da tayi ta gama ta goge hawayenta, sannan mlm kabiru ya ce, ” hajara, ki gaya mun ribar Abinda kika samu nawa kika kirga nawa kika samu, yanxu me ragon nan ya amfaneki dashi, wallahi duk wanda be godewa Allah ba zai godewa azabarsa kuma duk wanda beji bari ba zaiji hoho, hajara yanxu wa gari ya wa ya kin ranto kudin mutane kin siyo rago ansace shi, me zaki cewa me kudin idan lokacin biya yayi, duk irin abinda ake guje muku bakwa gani duk abinda zuciyarku ta baku shi kuke aikatawa, to hajara dabara ta ragewa me shiga rijiya sai kisan yanda zakiyi dasu, kinga _SANADIN RAGON LAYYA_ kinsa kanki cikin matsala da tasku, kina zaman zamanki kin jawa kanki ruwa, dama nasha gaya miki ki dinga godewa Allah inba haka ba zaki godewa azabarsa, wallahi kadan ma kika fara gani muddin bazaki canja tsarin rayuwarki ba ” yana gama magana ya ja fulo yayi kwanciyarsa.

STORY CONTINUES BELOW

     Hajara abun duniya duk yabi ya addabeta, wannan ake cewa rana zafi inuwa k’una, gaba daya hawayen idanta ma ya k’afe cikin zuciyarta take fadin wato kuka ma rahama ne, wannan shi ake kira da tashin hankali ba’a sa maka rana, hajara yanda taga rana haka ta karasa ganin darenta, zuwa safiya duk ta jeme ta bushe abunka da farar mace dokaci daya ta kwantsame, shi kuma mlm kabiru ko ajikinsa sabgar gabansa ma yakeyi.

        Bayan su fiddausi sun karya suka shiga tambayar hajara ina rago suna baya nan, hajara ji tayi kamar sun watsa mata ruwan zafi, ba wanda ta bawa amsa sai ma zagi tana rarraba musu, ganin haka yasa mlm kabiru ya ce duk su shirya zai su tafi gidan inna su taya ta zama, cikin murna da jin dadi suka hau kiciniyar shiri.

Basu suka fita daga gidan ba sai karfe goma sha daya na safe, tare da mlm kabiru suka fita gida ya rage sai hajara da take sak’a da warwara, abun duniya ya isheta kanta duk ya kulle.

    Hanne ce ta fado mata da sauri ta janyo hujabinta dake kan kyaure ta sa, ta shuri takalmanta ta fice, fakam fakam take wurga kafafuwa duk  wanda ya kalli yanayin hajara sai ya fahimci irin tashin hankalin da take ciki, gidan hanne ta fad’a ko sallama babu.

    Hanne na gyaran wake tsidik tashi fadowar mutum daki har sai da ta tsorata, afadance tace ” kai hajara da girmanki zaki shigo mana gida ko sallama babu kinji yanda na tsorata kuwa “

Hajara tace, ” hanna sallama ay sai da kwanciyar hankali “

Hanne tace, ” ke duk mu bar wannan wai kinshiga gidan sahura da balaraba kin musu jaje kuwa, wallahi kinga dawowa ta kenan da kamar na shigo miki nace kai yanxu safiya ce kar aga rashin hankali na “

    Yatsina fuska hajara tayi tace, hanne dan Allah ki barni da wannan zancen ki ajeshi agefe, ki saurari tashin hankalin da nazo dashi “

     Hanne kallan tsab tayiwa hajara tace,  ” hajara wai ni lafiyarki kuwa ji wani hijabi da kika sako duk jurwaye ga wata uwar jela zani kina tafe tana binki, wai kuwa kin kalli kanki a madubi kafin ki fito, ji takalmi wari da wari” Allah ya kyauta miki.

Kwallace ta zirarawo hajara cikin jimami da sanyin murya tace, ” hanne ina cikin tashin hankali wallahi tunda nake bantaba tsintar kaina cikin wani yanayi irin wannan ba, idan kika cire mutuwar mahaifana bantaba shiga halin ni ‘yasu kamar na yau, hanne ragon da muka siyo ansace shi jiya da daddare ” hajara ta fada hawaye na bin fuskarta.

        Azabure hanne ta dafe kirji tace, ” hajara dama harda gidanku aka shiga, jajen da nake tambayarki kinje gidan su balaraba suma fa jiya aka haura aka janye ragunan ashe abu na gindina bansani ba, innalillahiwainnailahirraji’un tabbas hajara kina cikin tashin hankali, kai wannan barayi Allah ya tsine musu, naji wai afadar mutane ance wai sa aka sace na gidan Alh D’an baba, oh ni hanne yau munga tashin hankali “

    Katse ta hajara tayi da,  ” hanne zuwa nai kibani shawara ki taimake da mafita mlm kabiru ya juya mun baya, ba yanda banyi ba akan ya taimaka ya biya kudin nan yaki kashe ma cemun yayi insaida shi inbiya kudin, wai bana gani ta biya kudin hayar gida watan gaba wai kayan abinci zai siya dasu, ke da na dameshi ba sai ya hada kan yaran sukayi gidan inna, hanne jiya kwana nayi ba bacci ina fargabar abinda zan cewa lubabatu intazo maganar kudinta, kuma ni yanxu babu wani abu fitacce nawa da zan d’aga ince inna siya alokaci daya zan samu dubu talatin dashi, sai dai ko katifata ko sif dita ta kaya, yanxu idan na sai dasu a ina zamu kwanta ko mu zuba kayan mu aciki, nikam yau naga ta kaina tsorona daya tijarar da lubabatu zatamun atsakiyar unguwa “

        ” Haba hajara dan Allah kibar batun saida kadarar ki insha Allahu ma ba abinda zaki siyar naki dole zamu nemo mafita” hanne ta fada.

Hajara tace, ” to hanne meye abun yi yanxu, kinsan dai ni ba sana’a nake ba bare nasa rai zan samu kudi inbiyata ba, wlh akudin jiya dubu biyar kawai suka ragemun, ina kike ganin zan cikon dubu talatin din dan ni tuni na hakura da wani ragon layya, insamu infidda kaina daga wannan masifar “

STORY CONTINUES BELOW

    Ajiyar zuciya hanne ta sauke sannan tace,  ”  to hajara wata shawara gareni amma bansan yanda zaki dauketa ba ko zaki amince, saboda ita kadai ce mafitar da zan kawo miki “

   Cikin zumudi hajara tace ”  fadeta  hanne ina jinki “

” ina wannan tak’adarin yaron nan, na cen kasan layin mu dan wajen huwaila ni yama sunansa salisu ne ko me ni na manta ma, amma dai gogarma ake cemasa kingane shi ? ” hanne ta tambayi hajara.

     Hajara tace, eh na ganeshi harisu sunansa ba salisu ba, amma ay gogarma aka fi kiransa dashi, hanne me zaiyi mana, nifa ina tsoron harka da irin ‘yan shaye-shayen nan “

Hanne kallan hajara tayi tace, ” ni dadina dake wutar ciki, bakya cin ribar zance ki bari kiji me zaiyi mana, kiranshi zamu yi ki dan yi masa alheri sai mu sashi yaje irin yan kasuwannin nan da ake cin kasuwar raguna ya sato mana rago ko zuwa bayan sallah ne sai muje mu saida ki biyata kudinta, kema kin huta da bala’inta inyaso ko nan gidana sai akawo shi a ajiye dan kar mlm kabiru ya kara tuhumarki “

Hajara dan jim kadan tayi tace, ” hanne amma fa gaskiya wannan shawarar tanada hatsari bakida wata mafitar sai wannan, nifa tsoro nakeji wallahi kar yaron nan yaxo ya tona mana asiri naxo na kara shiga uku gun mlm kabiru, dan Allah ki kawo wata shawarar ba wannan ba “

Shekeke hanne ta kalli hajara tace, ” to gaskiya banida wata shawarar inkina da gurin da zaki samo mata kudinta sai ki samo , kinsan dai alfarma ta kikaci ta baki rancen kudin nan ko, kiyi dai nazari hajara “

Hajara tace,  ” dan Allah hanne ki dan tambayar mun furaira man inzan samu kudi agurinta dan Allah taban rance”

   ” chab wallahi hajara bance zaki samu ba, dan yawancin samarin furaira bance suna bata kudi da yawa haka ba banki kayan kwalam da motsa baki ba , wannan kome take so suna siya mata amma kudi har dubu talatin dai bazaki samesu agurun furaira ba” hanne ta fada.

  ” to yanxu a ina zamu sami gogarma din” hajara ta tambaya.

” ehto, ina yawan ganinsa awani kango cen bayan shagon laminu, cen ne matattarar su idan mukaje zamu samesu acen” hanne ta bawa hajara amsa.

Basu dau dogon lokaci ba suka fice daga gidan hanne, kai tsaye gurin gogarma suka nufa, cikin sa’a kuwa suka samesu zaune lakadan suna sana’ar tasu ta zuke-zuke, suna karasawa gurin su uku suka samu zaune kowa da abinda yake sha, gaba daya gurin ya tirnik’e da warin kayan maye ba dadin shak’a.

Wani dan figigin cikin su ne ya diro daga cikin kangon ya fara magana irin ta yan daba yace,  ” kaaaaiiii meee kuka xo yi nan gurin ne ko kwalawa ne suka turo ku leken asiri ? ” yana gama maganar ya zaro wuk’a daga k’ugunsa yana nuna su hajara da ita.

Da sauri hajara taja gefe cikinta ya fara diban ruwa, hanne ce tayi karfin hali tace, ” dama gurin gogarma muka xo neman wata yar alfarma, gogarma lek’o ka ganni hanne ce babar furaira ka ganeni ?  Hanne ta tambaya cikin karfin hali.

Wanda aka ambata da gogarma d’ago da kansa yayi ya lek’o su hanne, idanuwansa jawur gefen fuskarsa yanka ne har guda biyu saman gishinsa ga wani tafkeken tabo nan shima alamar yanka ne agurin, cikin shak’akkiyar murya yace, ” yaaaaaa hanne me yake tafe daku ne, wa za’a yanka muku, sata ce ko kuma sara suka za’ayi masa ” ya karasa maganar yana tsare su da manyan idanunsa.

”  to to ummmm dama nace ko zaka dan taso muje gefe sai mu gaya maka abinda ke tafe damu ” hanne ta fada cikin karkarwa, ita kuwa hajara tayi tsumu sai zare idanu take kamar kamar ace mata kyet ta gudu.

   Tasowa yayi yana tafe yana layi kamar zai fadi har suka ganagara cen gefe.

Duk abinda yake tafe dasu saida suka zayya ne masa dan jim yayi sannan ya dago da kansa yace, ” idan zan maka aiki ya zama wajibi ka fara bani wani abin daga cikin kasona kuma idan na kammala ba’a sabamun alkawari, idan ka sabamun alkawari zaka iya rasa ido  daya, kunne daya, hannu daya ko kafa daya idan kun amince shikenan”

    Hanne tace, ” mun amince to nawa zamu biya ka “

” dubu goma zaku bayar, zaku bani dubu biyar kafin aiki bayan aiki ku bani dubu biyar saboda akwai yan shilolin da zan bawa dan wani abun muyi aiki dasu tare ” gogarma ya fada yana kunna sigarin hannunsa.

     Cikin sauri hajara tace, ” dan Allah adanyi mata sauki mana gogarma” hajara sai alokacin ta samu damar magana.

    Katse ta yayi da, ” wannan shine ka’idar aikina daga satar kaza zuwa zuwa satar abinda yayi dubu hamsin dubu goma ake biya na, daga satar sa ko saniya zuwa abinda yayi dubu dari ana biyana dubu ashirin,  sata ta mataki-mataki ce, kisan kai ne kawai ake bani dubu tamanin babba da yaro, idan jariri zan kashe miki dubj hamsin zaki ban inma babban mutum ne haka zaki bani, haka aiki na yake idan yayi muku shikenan inbe muku ba ku ware ku bani guri ” ya karasa maganar yana niyyar tafiya.

_Masha Allah damina ta sauka anshiga marka-marka, Allah ya bamu albarkar cikinta._

_Vote_

_Comments_

_Share_

    _MUM ASLAM Ce_😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        31-35

Hanne ce ta tsaidashi cikin lallashi tace, ” haba d’a na daga magana kuma sai ka tafi, to ba wani abu mun amince amma fa bamu fito da kudin ba, sai dai ko kazo ka karba ” bai juya ba ya bata amsa da,  ” karki damu zan turo k’ugiya yazo ya karba gidanki ne na karshen layi ko akwai wata yar hannu agidan ” hanne shiru tayi cikin tsawa gogarma yace, ” ba tambayarki nake ba, nace gidan akwai wata yar hannu aciki ko ” da sauri hanne ta amsa da, “eh nan ne “+

      ” Kuna komawa ku aje kudin zan turo akarba, ku sa aranku kamar ansato muku rago angama ” cewar gogarma.

Su hanne tafiya sukayi hajara tana yan sak’e-sak’e azuciyarta, hanne ce ta katse hajara tace, ” hajara ni sai yanxu nake ganin wawtarmu wallahi ” da mamaki hajara tace  ” wawtar me mukayi ” yooo da mukace rago daya zai sato mana mukasani ko ya sato mana dan karami wanda befi dubu goma sha biyu ba ” cewar hanne.

  ” ehh, kuma fa zancen ki na hanya hanne, yanxu meye abunyi ” inji hajara.

Hanne tace, ” ko dai cewa zamuyi ya sato biyu ” to hanne ina naga kudin da zan bashi nace miki dubu biyar kadai ta rage mun, ke cikon kudin ma fa saidai ki aramun ” cewar hajara.

      ” Karkiji komai na ara miki dan dai na lokaci bari muje Allah sa furaira ta dawo sai intambayeta ko zan samu yar dubu goma ko sama da haka rance ” inji hanne.

Suna tafe suna hira har suka karasa gidan hajara, hajara kudi ta dauko dubu biyar ta irgasu suka karasa gidan hanne shigarsu keda wuya sai ga k’ugiya ya danna kai ko sallama babu.

Daki hanne ta shiga ta dauko cikon kudin, saida suka irga kudin dubu goma cif sannan suka mik’a masa sukace ya irga, ba musu ya irga sannan hanne ta kora masa bayani akan sun sake shawara suna san asato musu raguna biyu, hanne har kara jadadda masa take akan su samo musu kato me tsoka, kamar wacce ta bada kudinta. 🤣

Cikin dakusashshiyar murya ya bata amsa, ” karku damu kunsan me gida bashi da wasa, kudai ku tanadi tirke da Abinci “

Bayan fitar k’ugiya hajara ta cewa hanne, ” to bari na karasa gida kinsan Allah yau ba abinda nayi, dama yaran nan mlm ya tafi dasu tun safe ke shimfidar dana tashi ma ban gyara ta ba, saboda tashin hankalin da rashin nutsuwa “

       ” banda abinki hajara komai aysai da kwanciyar hankali, yanxu kije kiyi aikin da zakiyi ki dawo kafin nan kinga sun dawo sai su sameki anan koba haka ba ” cewar hanne.

Sallama sukayi hajara ta tafi gida zuciyarta fess cikin jin dadi, hanne ce tabi bayanta da harara cikin dariyar keta da mugunta tace, ” waiwaiwai yaro man kaza hajara kenan amma ke kam anyi wawuya wawuyar ma ta karshe, hajara kin zamemun jari ko ince kadara, ay tunda mlm kabiru yaki amincewa ya aure ni na dinga doraki aturken keken b’era, kin dauka zan zuba muku ido yana nannan dake yana baki kulawa hmmm yanxu kika fara gani tunda ke baki da hankali ” hanne ta karasa maganar tana kara kecewa da dariyar mugunta.

Hajara na fita kai tsaye gida ta wuce, wannan karan yanayinta ba yabo ba fallasa sai dai har zuwa lokacin bata gama sakin jikinta ba, cikin zuciyarta take fargabar mlm kabiru idan ya tambaye wannan ragon  kuma tace masa me, fargaba ce ta cika zuciyarta tana ta fatan kamalla abinda zatayi ta koma gidan hanne kafin mlm kabiru ya dawo inyaso ko wata karyar ta shirya masa.

STORY CONTINUES BELOW

Wani tunani ne ya fado cikin zuciyar ta, ” ke hajara yanxu abun ya kaiki har kayan sata za’a sato miki kiyi biyan bashi, kinfi jin kunyar lahira akan duniya, ki tuna fa mutuwa zata iya riskarki akowanne yanayi, idan kika mutu da kayan sata kije kicewq Allah me, ko kin manta Allah baya yafe laifin wani akan wani, ya kamata ki sake tunani ” hajara jim tayi da tsintsiya ahannu tana yan zantukanta azuci, jikinta duk yayi sanyi taji wani irin tsoron Allah ya kamata, sauri tayi ta karasa aikin gidan ko wanka batayi ba, ta kara sa kai tafice gidan hanne wannan karan ta danfi kyan gani akan fitarta ta farko.

     BANGAREN SU GOGARMA

     Hayar Adaidaita sahu guda biyu sukayi shida yaransa guda bakwai, wadansu irin munanan makamai suka kwaso suka zuba cikin wani buhu kamar masu zuwa farauta, gogarma ne yake tambayarsu, ” kai wace kasuwar kuke ganin zamu fasa ne, ko muje hauren shanu “

     Wani yaronsa me suna duna yace, ” sa’a dai master sa’a dai, ni agani na kar muje hauren shanu kasan fa cen babban titi ne kuma suna da yawa zasu iya yi mana eh yane kadai gane, dan  suma shegun kansu ne sun tsaurara matakai “

  Cikin jin haushi  gogarma yace, ” kai dallah kana nufin sun yi mana zarrah ne “

   Sa’a dai me wuk’a me mashi me barandami da k’ugiya, ba nufina kenan ba master kasan ko iyaye na cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi banasan muyi jagwal ne, mu canja gurin zuwa kawai ”  cewar duna.

Jin dadin kirarin da duna yayi masa yasashi washe bakinsa da yayi wani baki-baki yace, ” kumafa maganarka na hanya duna, kai wai ku duk kawunan ku ba caji ne naji duk kunyi shiru karfa muje ku b’ata mun aiki “

      Wani daga cikin yaronsa me suna Almakashi yace, baabaah me zai hana mu danna dorayi wajen cirancin nan kasan akawai haja agurin “

     ” Kwarai haka za’ay mu afka dorayin ” inji gogarma.

Tun bai rufe baki ba suka d’ane adaidaita sahu, kamar gaske babu wanda zaiyi tunanin da wasu makamai atattare dasu, daga gaida zuwa dorayi ba wata tafiya me nisa bace, ba dadewa suka karaso, kallan tsab suka yiwa gurin rakuma, shanu da raguna ne kawai suke budurinsu agurin, wasu mutanen siyayyar raguna suka xo suna ta hada-hada kowa na sabgar gabansa, su gogarma na karasowa basuyu wata-wata ba suka afkawa mutane da sara suka kan me uwa da wabi duk wanda suka samu saidai su kai masa duka ko sara, ganin haka yasa mutane kowa ya fara ceton rai, sun dan daki lokaci kafin su samu nasarar diban manya-manyan raguna, akalla kowanne zaiyi dubu arba’in, cikin adaidaita sahu aka turasu suka fisgeshi  da gudu.

Sai bayan wani lokaci  sannan mutane suka dan fara dawowa da kadan kadan, raguna biyu  suka jiwa ciwo sai saniya daya da suka yanka tana dan zubda jini, kowannensu carko-carko sukayi cikin jimami suka fara jajantawa kansu jaje, wani daga cikin su ne yace, ” wai haka zamu sa ido bazamu kira hukuma akan wadannan fitsararrun yaran nan ba, wallahi muddin suka ga munyi shiru to sunga hanya haka zasu cigaba dayi mana dauki dai-dai “

    Hajara na shiga gidan ganne a sanyaye ta zauna jiki a kwari, hanne ce ta kalleta tace, ” wai ni kawata lafiya kuwa naga kin wani shigo sukuku dake “

    Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace, ” wani tunani nayi hanne anya bazan fasa harkar ragon nan ba, mu rika tunanin mutuwafa duniya ba matattaba bace, nikam hanne ko sun kawo nafasa karba su mayar kawai kayan wani ba kwanciyar hankali bane, kuma ba abinda zai amfaneka da shi “

Hajara ta cigaba da cewa, ” ko su rike kawai dan ni inajin tsoron inzo inmutu da hakkin wani akaina, wallahi hanne duk ji nake ba dadi anya nayiwa mlm kabiru adalci, gaskiya idan yasan abubuwan nan kashi na ya bushe, kema kinsan iya kokari mlm kabiru yana mun dan ko wata matar me kudin bazata nunamin komai ba, dan Allah hanne meye mafita “

Kallan tsab hanne tayiwa hajara sannan tace, ” lallai hajara kin raina mun hankali wai me kika dauke ni ne, kodan kinga duk abunda kika kawon ina baki ‘yan shawarwari, yanxu kina nufin kudin dana bawa gogarma sun tafi abanza kenan, to dame zaki biya lubabatu, yanxu munce mun fasa karbar rago acikin ku waye zai biyani kudina, kin kuwa san waye gogarma “

STORY CONTINUES BELOW

  ” hanne idan suka xo sai ya siyar ya biyaki kudinki dasu ita kuma lubabatu sai inje gidanta inbata hakuri, ni wallahi tashin hankalina daya akawo mun kayan sata na karba ” cewar hajara.

Shekeke hanne ta kalli hajara tace, ” wallahi ni bada ni ba bazan iya tarar gogarma da wannan maganar ba, haka kawai inje tsautsayi ya kwasheni ya saukemun kafad’a ko ido kibari idan yazo ke sai ki karbar mun kudina, Wai hajara wani sabon tsoron Allah ne ya shiga zuciyarki da har kikayi karatun ta nutsu, kinsan dai Allah gafurur rahimu ne idan kayi astagafurullah ay Allah zai gafarta maka, kawata karki bani kunya mana ki tuna lubabatu  kinsan dai ba kanwar lasa bace kiyi nazari “

Dan jim kadan hajara tayi maganganun hanne nayi mata yawo azuciya, wannan shi ake cewa gaba kura baya siyaki, ta nan tana nazari sukaji karar karafuna da kukan raguna yaran gogarma ne suka shigo janye da raguna hannayensu dauke da mugayen maka mai.

Hanne ce tayi musu iso ta nuna musu gurin da za’a tirke ragunan, bayan andaure ragunan har sun juya zuwa bakin kofa duna ya dawo yace,

         ”  ya ina sauran kudin master yace zaku ciko ehh yane, saura dubu goma kudinsa “

Hanne ta amsa, ” eh haka ne bari mu hado muku kudin inazuwa “

Hanne na zuwa gurun hajara tace, ” za’a samu dan wani abun agurinki “

Bakin zani hajara ta kama ta kunto dubu daya  ta mikawa hanne, itama hanne d’aki ta fada furaira ta samu har ta fara bacci, d’an tashin ta tayi ta karbi kudi ta fito ta mikawa duna, ko amsa be bata ba yasa kai ya fice.

   Hajara da ido tabi raguna da kallo cikin zuciyar tana ayyana wadansu maganganu, sauran kanzon dake cikin tukunya hanne ta kankaro musu ta zuba musu nan da nan raguna suka cinyeshi suka sha ruwa, wannan karan ko kadan wadannan ragunan basu burge hajara ba bare tayi murnar su.

      Tun bayan tafiyar su gogarma tsumma suka samu me girma suka daurewa saniyar da su gogarma suka yanka a k’afa, tattaunawa suka cigaba dayi akasn yanda zasu bullowa lamarin,  daya daga cikinsu ne yayi gyaran murya me suna Ayyuba yace,  ” nifa gaskiya badan ina tsoro ba da nace wani abu “

    Cikin zak’uwa duka suka ce, ” tsoron me dan Allah fadi muji “

”   To gaskiya waannan abunda zan fada kasada ce “

    Lokaci daya suka bashi amsa, ” dan Allah mu ka bar ja mana rai ka fada kawai muji “

   Yaran da sukayi mana abun nan yan bayan layinmu ne, sunan babban su gogarma, basuda imani ko kadan ina tsoron kar su gano ni suje su yi mana ba dai-dai ba nida iyalina.

Ya cigaba da ” sun jiwa dabbobin mu da mu kanmu ciwo acikin mu sun sassari wasu, kunga wannan babban tashin hankali ne dan bamusan gaba me zasuyi mana ba, amma ina kara jaddada muku dan Allah kar su fahimci ni ne na tona su, idan ba haka ba ana sako su kashina ya bushe “

      Wani daga cikin su wanda ya kasance kamar shugabansu shine ya fara magana, ” tabbas munji dadin wannan maganar kuma zamu kai rahoto gurin yan sanda sai dai Ayyuba ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru da kai da iyalinka, nine zan shiga gaba gurin aywatar da komai inasan ka nitsu, ko labari banasan ka bawa wani akan abunda ya faru kasan mutum sai Allah wani na iya cin amanar ka, kaja bakinka ka tsuke yanxu ina harisu da shu’aibu ” ya karasa maganar yana kallansu.

   Wasu mutum biyu ne suka fito daga cikinsu, sannan shugaban nasu ya cigaba da magana, ”  daku ya kamata muje police station muyi report ku kuma ku kula da gurin kafin mu dawo.

Ayyuba da su harisu wucewa sukayi suka tari dan adaidaita sahu, kai tsaye police station din sharada suka je basu dauki dogon lokaci ba aka dauki report dinsu.

Hajara ce ta kalli hanne tace, ” hanne yanxu wadannan raguna ina zamu kaisu mu sayar, ni tsoro nake ji kar mukai kasuwa azo agane mu “

    ” Haba hajara gaggawar me kike yi haka, ki bari ayi sallah asallame mana sai muje kasuwa mu saida su hankali kwance, kinga yanxu gobe ne sallah to ba gobe ba mu bari zuwa jibi kinga dai duk cikin shagalin sallah ne, sai muje muci kasuwar muna dawowa mu wuce gidan lubabatu mu bata kudinta sauran mubi ta kansu ” cewar hanne.

” to shikenan Allah ya nuna mana, hanne ki aramun kudi asiyo musu dusa idan komai ya warware zan biyaki ” inji hajara.

        Sallama hajara tayiwa hanne jiki a sanyaye ta tashi ta nufi gida, tana shiga gida atsakar gida ta samu mlm kabiru zaune akan kujera yara sun kewa shi suna mishi sannu, tsumma ne ahannunsa yana daure kafarsa daga wajen kwauri jini na zuba.

Da sauri hajara ta karasa cikin sallallami tana tambayarsa me ke faruwa, sai da ya kammala daure kafarsa sannan ya kalli hajara cikin tsuke fuska yace, ” wato hajara abun naki kara gaba yake yanxu har fita kike bada izinina ba “

    Cikin dabarbar cewa ta fara bashi amsa, ” amm na’am eh dama wallahi hanne ce ta ayko wai jikinta yayi zafi ga furaira bata kuma ga yunwa tanaji shine naje na dan dafa mata fara da mai danma fiddausi bata nan da ita zan ayka “

  ” Hajara wai yaushe zaki fita sabgar hanne ne nasha gaya miki hanne ba mutuniyar kirki bace amma sam bakyaji ko, yayi dai-dai kiyi duk yanda kika ga dama idan na gaji zan auro hannen sai ku cigaba da zumuncin agida “

Wata harara ta watsawa mlm kabiru bata ce uffan ba, daga baya tace, ” lafiya naga kafarka na zubar jini wannan ciwo haka garin yaya “

      ”   Wallahi yaran nan na kasan layin mu suka taho da adaidaita sahu, muna tafe suka make ni danma Allah ya takaita kurjewa ce nayi amma abu haushi ko waigowa basuyi ba bare su bani hakuri, dama kuma nasan baza suyi ba Allah dai ya shirya mana zuri’a ” cewar mlm kabiru.

  ” wane yaro ne mlm “

  ” yaron nan mana gogarma, kinsan yayi kaurin suna ” mlm kabiru ya fada.

   Rassss gaban hajara ya fadi jikinta har rawa yake, dakewa tayi ta tattaro nutsuwa tace, ” ay yaran ne sai addu’a Allah ya kara sauki malam “

     Motar police guda aka bawa su Ayyuba kai tsaye unguwar gaida suka nufa, duk inda motar ta shiga sai anbita da idanu, kangon da su gogarma suke zama  nan ayyuba ya nuna  musu, su gogarma suna zaune kowanne da abunda yake zuk’a wari da hayaki sai tashi yake agurin, gaba daya sunsha sunyi mankass, cikin sand’a yan sandan suka dunfare su lokaci daya suka cabke kugunsu suka tura su cikin mota.

_Kuyi hakuri da jina shiru na kwana biyu da kuka ji, ina godiya da kulawarku kwarai Allah ya bar zaman tare._

_Vote_

_Comments_

_Share_

   _MUM ASLAM Ce_😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        36-40

Zille-zille sukeyi suna niyyar direwa ta saman mota, wasu daga cikin su ma ko kwakkwaran motsi basayi saboda sunsha tayi musu karo, kai tsaye police station aka wuce dasu aka tura su cikin cell, inbanda warin wiwi ba abinda yake tashi idan mutum ya gifta ta wajen cell din.+

         Wani gabjejen police ne yaje ya tsaya ta jikin kofar ya buga musu tsawa yana tambayarsu, ” Kai uban waye yace kuje kuyi musu fashi da tsakar rana har kuke neman illa tasu suda dabbobinsu? “

       Kallan raini gogarma yayi masa cikin magana irin ta rikakkun yan daba yace, ” haka kawai zamu je musa musu kai ne, kai wadancen mutanen nan fa sun raina mana hankali, haka kawai zasu sa akamo mu adinga yi mana wata tambayar ehh yaaane, ni tinda nake ma bantaba ganinsu ba “

      Cikin fusata dan sandan ya buga mai tsawa, ” kai karamin dan iska banasan iskanci da rainin wayo, ina kuka kai musu ragunansu? “

        Harara gogarma ya kara watsa masa yace, ” babba nifa ban fahimci wasu ehh raguna da kake zance ba, wai ma mu me zamuyi da wasu raguna muda ba iyali ba bare muyi musu layya? “

Cikin fusata dan sandan nan ya kwalawa wasu police su uku kira, suna karasowa yace, ” kai Abinda nake so ku tambayi yaran nan har sai sunyi laushi, saboda naga sunxo da rainin wayo da alama zasuyi taurin kai “

   Tun kafin ya rufe baki suka juya dauko kulkinsu, ba b’ata lokaci suka bud’e cell din aka fara jibgar su gogarma sai ihu suke.

Hanne ce zaune ita da furaira suna hira, furaira tace, ” inna nifa wallahi kwadayin wainar fulawa nakeji ko insiyo fulawa ki soya mana? “

      ” Me zai hada furaira dan dai suyar wainar fulawa Allah na tuba anawa take ” inji hanne.

     ” Kai Amma gaskiya bacci nakeji kozan siyo sai na tashi tukunna ” cewar furaira.

Galala hanne take kallan furaira da mamaki tace, ” ke furaira me yake damunki ne ko awa guda fa bakiyi da tashi ba kice zaki kara komawa, nafa lura kwana biyun nan baki da aiki sai na bacci “

      Hamma furaira tayi tace, ”  to inna mutum na gida me zaiyi inba bacci ba “

    Wassafa wani abu hanne tayi cikin zuciyar ta nan da nan tsoro ya kamata, sai ta basar ta cewa furaira, ” kafin kije ki kwanta dakko mun tukunyar fatan waken nan inciye ta inyi wanke-wanke “

      Da “to” furaira ta amsa mata ta tafi tana lumshe ido alamar bacci na kanta.

           Tana dauko tukunyar faten waken taji wani wari ya bigi hancinta da sauri ta ajiye tukunyar tana toshe hanci, wani amai ne ya taso mata, da gudu ta karasa bakin rariya tana kwara uban amai awahale.

    Gaban hanne ne ya yanke ya fadi tsoro ya kamata, cikin firgici tace, ” ke furaira me yake faruwa dake ne? Ki gama aman kixo inasan ganinki “

A wahalce furaira ta yunkura ta taso bakinta duk ba dadi, tana tafe tana yatsina fuska ta karasa gaban hanne ta zauna tana dafe kai, kallan tsaf hannr tayi mata sai alokacin ta kare mata kallo, ganin irin d’ashewar da tayi ne yasa ta fara tambayarta, ” furaira yaushe rabonki da bakonki na wata? “

      Dan sosa kai furaira ta farayi tana  sinne kai kasa.

     Tsawa hanne ta buga mata ta kara tambayarta, ” nace yaushe rabonki da bakon ki na wata? “

     ” Ina ina inajin dai zanyi wata biyu ” furaira ta fada.

   

    Cikin faduwar gaba hanne tace, ” muga hannuki” duba hannunta hanne tayi tana duba idanunta, bata gama duba idan ta ba hanne tarufeta da duka.

       Cikin takaici hanne take fadin, ” yanxu furaira kina nufin ciki ne dake, oh ni hanne yau naga tashin hankali ” hanne saboda bakin ciki harda kwallah.

     Janyo furaira hanne tayi ta makureta jikinta har rawa yake saboda tashin hankali tace,  ” dan ubanki ki gaya mun waye yayi miki cikin nan, wane shegen ne ya lalata ki? “

      Furaira kokarin kwace kanta take, tana ihun neman agaji sai da taji jiki sannan furaira ta fara magana, ” Alhajin Abuja ne “

      Gwabe bakin ta hanne tayi tace, ” shi Alhajin Abujan dan ubanki mijinki ne iyee? ” hanne ta tambayeta cikin kumfar baki.

   ”  Ay yace zai aure ni ” inji furaira.

        Sai alokacin hanne ta tsagaida da dukan furaira sannan tace, ” too too yanxu naji batu, ayda kinmun bayani tun farko da bakiji jiki da duka ba, tashi kije kiyi wanka sai muyi maganar anutse ” hanne ta fada.

Bayan magriba mlm kabiru chemist yaje aka yi masa allura aka bashi magunguna, kwata kwata hajara bata da nutsuwa da ka ganta kamar ace keeet ta arce, duk tayi furkai-furkai da ita kamar wacce tayi amai da gudawa.

     Mlm kabiru ya lura da yanayinta amma da ya tuna sace ragon da akayi mata sai ya dauka ko satar ce take damunta, shiyasa yayi watsi da ita ko bi ta kanta baiyi ba.

*Washegari*

      Wacce ita ta kasance ranar idin babbar sallah, su gogarma dake cikin cell sun daku iya dakuwa tun suna gardama da taurin kai har suka zayyanewa yan sanda komai game da bukatar su hanne.

        Duku-duku da farar safiya police suka taso keyar gogarma amota tiryen-tiryen har gidan hanne, lokacin ma bacci suke kamar asama sukaji ana bubbuga gida kamar za’a cire kofar, afusace hanne ta fito tana fadin, ” bashin ko tara ko naci na wani banbiya ba, da farar safiya adinga mun bugun tashin hankali “

     Hanne na bude kofa tayi turus ganin yan sanda gefe guda kuma gogarma ne fuska ta haye tayi suntum, da sauri ta ja baya tana kokarin turo kofa wata macen police tayi sauri ta damko hannun hanne, furaira ce ta fito tana fadin.

        ” inna waye najiki shiru? “

   Turus tayi ganin yan sanda, suka tasa keyar hanne sukayi waje.

Da sauri furaira tabi bayansu cikin tashin hankali tace musu, ” dan Allah bayin Allah lafiya me mahaifiya ta tayi muku, me tayi da zaku tafi da ita? “

   Shiru ne ya biyo baya ba wanda ya tanka mata, kara shan gabansu tayi tana musu magiya.

    Daya daga ciki yace mata, ” zaki iya biyo mu station domin jin karin bayani “

Mota aka nufi hanne za’a sata aykuwa da sauri tace, ” yallabai nima ba nikadai bace akwai wata makociya ta ga gidanta cen tare da ita muka sasu aikin “

Aykuwa kai tsaye kofar gidan mlm kabiru suka nufa, buga kofa suke kamar yanda suka bugawa hanne kofa, zuwa wani lokaci mlm kabiru ya fito, da mamaki yake kallansu tare da fadin yallabai barka da aiki lafiya naga kun buga mun gida? “

    ” lafiyar ce ta kawo haka, fito mana da iyalinka muna gayyatarta a office dinmu ” police din ya fada.

  Da mamaki mlm kabiru yace, ” iyalina me tayi muku”

Cikin tsawa dan sandan yace, ” kai bafa hira ce ta kawo mu ba ka fito da ita ko insa ladi ta fito da ita “

       A sanyaye mlm kabiru yace, ” basai anyi haka ba, inane station din naku nida kaina zan kawo ta zamu xo tare, nayi muku alkawari “

    Kallansa police din yayi yace, ” ka tabbata idan baka kawota ba inmuka dawo zamu hada da kai, mun baka nan da awa daya kuje sarada division “

”  Ke wuce muce ” ya bugawa hanne tsawa.

_Zakusha kura-kurarai banyi editing ba._

_Vote_

_Comments_

_Share_

     MUM ASLAM Ce 😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        41_45

  _Not Edited_

Ku karbeshi da hakuri

Mlm kabiru kamar Wanda kwai ya fashewa aciki jiki a salube haka ya koma gida lokacin hajara na kwancen cen kuryar gado, sai da ya tsaya ya gama kare Mata kallo Yana wassafa abubuwa azuciyarsa sannan ya Fara bubbuga jikin gadon cikin takaici ya Fara yi Mata magana, ” hajara ke hajara tashi” murza idanu ta farayi cikin bacci tace, ” mlm Dan Allah ka barni indan matse wallahi barcin Nan bai isheni ba ” takaici ne ya Kara rufe mlm kabiru cikin jin haushi ya buga Mata tsawa, ” Ke dallah tashi baccin me Zaki karasa kunje kun jajubowa kanku masifa ki tashi mu tafi police station, idan munje sai inji takamaimai lafin da kuka aykata keda kawar taki “

     Rasss gaban hajara ya fadi cikin fargaba hajara tace, ” mlm police station Kuma, me zaikaimu police station? “

      Mlm kabiru kallan kin Raina min hankali yayi Mata yace, ” wato Baki San me Zaki je yi cen ba ko, da Kika samu zan tafi dake ta lallami idan sune yaushe zasu tsaya suna Miki magana har kina tambayar su, dama darajar aure Kika ci hajara wallahi da tuni na basu umarni sunyi gaba dake tunda ay duk tsuntsun Daya ja ruwa shi ruwa Kan doka ” mlm kabiru na gama magana ya fice ya barta zaune tana zullumin abinda zataje ta tarar a police station.+

    Hajara idanta ta wanke ta canja kaya ta zura hijabi, gaba daya taya aikin ne Amma hankalinta baya jikinta, bayan ta gama shiryawa rasa abinyi tayi haka ta dinga shiga tana fita kamar wacce taiwa sarki kaya yasa akamota, mlm kabiru gajiya yayi ta shige da ficenta ya rufeta da fad’a ba shiri ta wuce sum sum sum suka fita.

      Lokacin da aka Kai hanne cell gaba daya idanta ya Raina fata Bata taba zatan wannan harkar zata kwabe musu haka ba, tafi tunanin sanya hajara cikin matsala sai Kuma haka ta faru, mugun kallo suka dinga jifan juna dashi tsakanin hanne da dasu gogarma, kowa na aybata Dan uwansa acikin zuciyarsa.

     Mlm kabiru na zuwa ko bi ta kansa police din basuyi ba aka tasa keyar hajara cikin cell, dama tunda hajara ta hango hanne da gogarma ta saddak’ar da cewar kashinsu ya bushe, asirinta ya gama tonuwa, saboda tsabar fargaba jikinta har rawa yake yi, tana tsoron hukuncin da mlm kabiru zai yanke akanta, ita tafi tsoron hukuncin mlm kabiru ma da wannan badakar da suka aykata, yawun bakinta ne ya bushe makogaronta har d’aci yake, cikin zuciyarta take fadin ashe kuka ma rahama ne.

Mlm kabiru takaici hanashi magana yayi jikin bango ya samu ya tsaya Yana watsawa hajara muguwar harara, cikin zuciyarsa Yana mamakin yaushe hajara ta lalace da mugayen dabi’u haka, guntun tsaki yaja yaje ya samu wani police dake Kan kanta ya Fara yi Masa magana, ” yallabai barka aiki antashi lafiya?”  Lafiya klau Alhamdulillah meye matsalarka” police din ya bashi amsa.

   ”  Dama nine Wanda nace musu zan taho da baiwar Allah cen to kuma ansata cell banji laifin da ta aikata ba ” cewar mlm kabiru.

      Police din juyawa yayi y klli cell din sannan yace, ” ita Bata Gaya maka me sukayi ba? ” Eh bata gaymun ba yallabai ” cewar mlm kabiru.

    ” To zarginsu ake da ayken sata Kuma da tada tarzoma ba bisa ka’ida ba, sun tura wadancen yan daban sunje sunyiwa mutane satar raguna sun kuma sassaresu ” inji police din.

Mlm kabiru ji yayi kamar anbuga Masa guduma aka kansa ya Fara juyawa gefe ya nema Kan benci ya zauna ba tare da ya bawa police din amsa ba, hannuwa biyu yasa ta dafe kansa Yana jin wata irin hajijiya na fisgarsa, afili ya furta innalillahi wa’inna ilahirraji’una.

     Ganin yanayin da mlm kabiru yashiga yasa police din be Kuma bi ta kansa ba ya cigaba da yan rubuce-rubucensa.

      Hajara na cikin cell zuciyarta inbanda lugude ba abinda take yi Bata tabajin Dana sanin haduwa da hanne ba sai yau data kwabe Mata.

Bayan wani Dan lokaci mlm kabiru ne ya tashi ya koma gurin police din yace, ” yallabai ina masu ragunan suke “

   ” Basu karaso ba sai anjima ” police din ya bashi amsa.

    Bakin wata bishiya mlm kabiru ya koma ya zauna Yana tunanin irin hukuncin da zai yankewa hajara, kamar Wanda aka tsikara zumbur mlm kabiru ya Mike ya fice daga police station din Kai tsaye gida ya wuce.

    Yana shiga su fiddausi ya samu sunyi carko-carko suna jimami, suna ganinsa da sauri suka tashi sukayi gurinsa cikin hadin Baki suka Fara tambayar sa, ” Abba Ina kuka je kaida umma muna fitowa duk bakwa nan ? “

Dan Jim yayi ganin irin damuwar da yaran suka shiga Yana tunanin irin amsar da zai basu, dabara ce ta fado Masa yayi karaf yace, ” yau da asuba ne aka kirata daga karaye anyi rasuwa shine dazu na rakata Tasha ta hau mota, kuna bacci shiyasa ban tashe ku ba Amma bazata Dade ba kwana biyu zatayi ta dawo “

      Sai alokacin yaran suka Dan saki jiki fiddausi ce ta Kara tambayar sa, ” Abba ko goggo nene ce ta rasu Dan ta tsufa sosai gashi dama Bata jin Dadi “

    ” To da yake dai basu Fadi Wanda ya rasu ba, sunce dai taje anyi rashi Kuma banda abinki fiddausi ita mutuwa ay Bata kyale yaro ba Allah yasa dai mu cika da imani ” cewar mlm kabiru, gaba daya yaran suka amsa da Aameen.

   Daki mlm kabiru ya shiga ya kwanta Yana wani tunani afili ya furta, ” hajara wannan Karan kinkai ni bango Zaki dandana ba abinda zai maidani police station, Zaki ta zama acen har sai lokacin da kikayi nadama da kanki tukunna zanje inyi bellinki, idan inada Rana Zaki gani idan ma banida ita Zaki gani, samu ba abinda baya sawa jindadi ne yayi Miki yawa Amma wannan Karan zan barki da hannen zanga yanda karshen kawacen naki zai kasance, ay bahaushe yace shiru ma magana ce.

Hajara na  tsaye ta hada Kai da gwiwa tun shigarta ba abinda ta iya furtawa hanne saboda tsabar bakin ciki da takaici, sai ayanxu hajara ta iya samun sukunnin yin hawaye, hanne ce ta kalleta ta kece da dariya sannan tace, ” hajara meye abin hawaye Dan Allah……. ” Cikin tsananin bacin rai hajara ta bugawa hanne tsawa, ” dakata mun hanne wallahi na tsaneki hanne kin cuceni kin cuci rayuwa ta sai yanxu na tabbatar da ke ba kawar arziki vace, kin jefa cikin masifa Kuma yanxu kina tambaya ta kukan me nakeyi, nayi danasanin haduwa dake hanne zamantakewata dake bata amfaneni da komai ba sai tarin nadama, gaskiya hanne ke masifa ce kina gani yanxu aurena Yana cikin wani hali, Allah na tuba ka tafemun abunda na aikatawa mlm, Allah ka tausasa zuciyarsa, Allah karka bashi ikon yanke mummunan hukunci akaina ” hajara ta karasa fad’a tana fashewa da kuka me tsuma zuciya. 😭

      Kallan shekeke hanne tayi Mata sannan ta Kara fashewa da dariya sai da tayi me isarta harda rike ciki sannan ta tsuke fuska tace, ” hajara yanxu na tabbatar da Baki da hankali ke kina tunanin duk shawarar da nake Baki ta alkairi ce? Inbaki sani ba ki sani wallahi hajara ban taba yiwa wani kyashi ba sai ke, keni wallahi bazan iya fasalta irin haushin ki da nake ji ba, tun farko dawowa ta unguwar gaida na fahimci irin gatatawar da mijinki yake Miki da yanda yake nannan dake, sai na Fara jin inama mijina ne, da farko nayiwa mlm kabiru kallan sha’awa ne da zummar ya zama abokin hulda ta kamar yanda nakeyi aboye, hakan ne yasa na kasa boye bukatata har naje na sameshi, mlm kabiru cin mutumcin da yayi mun tunda nake ba’a taba mun irinsa ba, daga baya ne na fahimci tsantsar kaunar da nake masa, na Kara komawa da bukatat ta biyu Nan ma bai saurareni ba, ke har gurin bokaye Nasha zuwa da bukatata Amma ba nasara saboda tsantsar ibadar sa, wannan ne yasa na kuduri niyyar sai na Bata duk wata kyakykywar alakarku, shiyasa na tsiri shigowa gidanki idan mlm kabiru bayanan saboda nasan idan mlm kabiru ya ga Ina zaryar gidan sa zai dau wani hukuncin akaina, kuskure Daya mlm kabiru yayi Daya kyaleki muke ma’amala ta yau da kullin, na tabbata da nayi galaba, nasan babu wani hukunci da mlm kabiru zai dauka akanki da ya wuce saki, Kinga mun zama daya kenan ” hanne ta karasa maganar tana Kara kecewa da dariyar keta.

       Sororo hajara tayi kamar mutum mutumi tana kallan hanne kamar wata me matsalar kwakwalwa, da ace awaya taji wannan kalaman zatayi tunanin wani yake Mata magana amadadin hanne, da ace sako ne hanne ta ayko Mata dashi to zata zaton batan hanya akayi, ba mamaki ba har tsoro hanne ta fara bawa hajara, ja da baya hajara tayi cikin takaici da bakin ciki tana fadin, ” Allah ya isa tsakanina da ke kinci amanata Amma Allah baya bacci Allah zaimun sakayyah ” cewar hajara.

    Hanne dariya take zuciyarta wasai tana nuna hajara sai ta Kara fashewa da dariya, hajara takai bango a tsananin bakin ciki har Bata ganin gaban ta sosai, jin dariyar da hanne take yi Mata ne yasa ta Kara fusata, aykuwa hajara tayi kukan kura ta tafi da gudu ta damko hanne ta rufeta da duka.

Jibgarta take kamar Allah ya aykota duka take Mata iya karfi ta, ta ko ina tana dukanta, jin dukan da hajara take Mata ba na kare bane yasa hanne ta fara ihu tana neman dauki, kafin police suje tuni fuskar hanne ta haye tayi suntum.

_Vote_

_Comments_

_Share_

     _MUM ASLAM Ce_😉🐏🐏🐏

       *SANADIN*

               *RAGON  LAYYA*

           🐏🐏🐏

              🐏🐏

                    🐏

                  _By_

         *Ameera Adam*

    *AmeeraAdam60*

      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

               46-50

   🔚🔚🔚

Wani police ne ya karaso bakin cell din da suke ya buga Musu uwar tsawa cikin masifa ya Fara magana, ” ku wad’anna irin mahaukata ne da girmanku kuke irin wannan shirmen jibeku yanxu idan yaranku sukaga Kuna irin Haka kallan me zasuyi muku Amma wlh kun bani mamaki, ko Kuma ay ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin laifin da kuka aykata shashan banza da wofi, dubesu kamar masu hankali Amma Kan ashe na tinkiyoyi ne dasu”

    Hanne ce ta Fara sauke ajiyar zuciya da kyar tace, ” yallab’ai ka taimaka ka cireni daga cell d’in Nan wallahi zata iya lahantani ji irin dukan da tamun yanxu haka bana gani sosai jiri ne yake d’ibana”

     ” Anki acireki din ay kawarki ce laifinku d’aya Kuma tare aka kawoku, idan kuka cika mun kunnene zan d’auki mataki akanku” cewar police din.

    Gaba daya tsit sukayi kowa da abinda yake sak’awa zuciyarsa, hajara abun duniya ne duk yabi ya addabeta tsoron had’uwarsu da mlm takeyi.+

    Masu raguna basu suka iso police station din ba sai kusan karfe goma Sha biyu na Rana, su hanne haka suka dinga rokonsu suna magiya, zuwan masu raguna keda wuya sai ga mlm kabiru ya shigo, gaisawa sukayi ya gabatar Musu da kansa sannan ya nemi asanta akashe maganar tun ba’aje ko inaba, da kyar da sid’in goshi mlm kabiru yashawo Kansu suka amince, kudin asarar da akayi Musu suka buk’ata atake mlm kabiru ya biya Wanda akaci tarar hajara, alokacin kuma aka fito da ita hanne sai rok’onsa take ko ta kanta baibi ba, su hajara sunje fita suka had’u da furaira taxo Kan maganar mahaifiyarta, tambayar hajara furaira takeyi Amma ko kallan arziki hajara batayi Mata ba tunaninta Daya yanda zasu kwashe da mlm kabiru.

     Suna fita mlm kabiru ya kalli hajara cikin tsuke fuska yace, ” bayan wannan wane Abu Kika aikata Wanda bansani ba?” Sunne Kai k’asa hajara tayi tace, ” kudin lubabatu Mai adashi ne ya rage” tambayar ta yayi nawa ne ta Gaya Masa zaro kudi yayi ya irgasu ya ware na lubabatu yasashi a aljihu daban, ita dai hajara da ido take bin mlm kabiru har suka karasa titi, me napep ya Tara Kai tsaye Tasha yace ya kaisu, suna xuwa ya wuce wajen lodin motocin karaye umarni ya bawa hajara ta shiga, jikinta ne yayi sanyi har ta budi baki zatayi magana mlm kabiru ya dakatar da ita.

Mlm Kabiru zama yayi shida ita bame cewa wani uffan hajara nasan yin magana tana tsoron jin ta bakin mlm kabiru, bayan sunje karaye Kai tsaye gidan kakannin hajara suka wuce duk kakannin nata sun rasu saidai irin y’an uwan Nan na dangin,  sai wani tsohon ne kawai ya rage me suna mlm Alto shima wani Dan uwan kakanta ne da suke abokan wasa, mutanen kauyen na ganinsu suka Fara murna ana ga hajara ta zo, sai dai ta bisu da yak’e Wanda yafi kuka ciwo, gurin mlm Alto sukaje suka gaisheshi mlm Alto murna yake inakasaka inaka aje, har ya bada kudi asiyo Musu abinci  mlm kabiru ya dakatar dashi, sannan ya Fara yi masa bayani, ” baba Ina San kamun alkawarin duk hukuncin da zan yanke bazaka tambayeni dalili ba ” rassss gaban hajara ya Fadi jikinta har karkarwa yakeyi ta gama saddak’ar wa zamanta da mlm kabiru ya k’are, mlm Alto yace, ” kabiru inajinka nasan halinka Sarai bazakayi wani Abu ba tare da wata hujja ba me yake tafe dakai Fad’i kanka tsaye”

     ” Yauwa, dama inasan hajara ta zauna agarin Nan na D’an wani lokaci idan lokacin yayi ni zan dawo da kaina na d’auketa” sai alokacin hajara ta D’an ji dama-dama, mlm Alto na Shirin tmbyr mlm kabiru sai ya tuno da alkwarinsu Amma ba makawa yasan ruwa baya tsami banza, D’an kudi mlm kabiru ya deb’o ya bawa mlm Alto sannan yayi Mai sallama ya fito, hajara ce biye dashi idanunta sun ciko tana rok’on sa Amma kamar baimasan tanayi ba, ganin mutane sun Fara kallansu yasa hajara komawa cikin gida tayi turus tama rasa makamar dafawa sai hawaye da yake bin fuskarta.

    Mlm kabiru badan yaso ba ya yankewa hajara wannan hukuncin saidai yasan wannan shine yafi dacewa da ita, acewarsa bazai iya rabuwa da hajara ba, ko tayi hankali ta gane muhimmancin sa yana hanya ta kirashi yafi a irga kamar bazai d’auka ba yasa hannu ta d’auka yace, “lafiya Kika isheni da Kira?” Dan Allah mlm kayi hkr…….. Katseta yayi da, ” dakata hajara tuni nagama magana, Ina komawa Kano zan nemi auren kawarki hanne, Kuma idan Kika sake Kika baro garin Nan ba tare da ninazo na taho dake ba wallahi kinji na rantse abakin auranki” Yana gama maganar k’it ya kashe wayar.

     Hajara batasan lokacin da ta rushe da matsanancin kuka ba,matan gidan ne suka rugo da gudu suna tambayar ta me yake faruwa.

STORY CONTINUES BELOW

    Furaira na shiga police station din itama suka kamalla abinda zasuyi sannan aka Kara gargad’arsu akan su kiyaye gaba, sukuwa su gogarma kotu aka turasu kasancewar su masu tsofaffun laifuka ne.

        Su faraira na komawa gida ciwon ciki ya rufe ta kamar wacce zata mutu arude hanne ta d’auketa suka tafi asibiti, gwaje-gwaje akayi Mata sannan likita ya tabbatar wa da hanne cewar ciki gareta, magungunan da allurai aka basu, ko kadan hanne batayi mamaki ba sai dai suna fitowa ta hurawa furaira wuta akan cewar sai ta Kira shi wannan Alhajin ta sanar dashi, haka kuwa akayi ta kirashi ta sanar dashi, ko dar Bai nuna alamun ya damu ba saima cemata yayi da zaixo suyi wata magana da ita.

         Da daddare Alh yaxo gurin furaira bayan sun gaisa ya deb’o kud’i dubu d’ari yace taje asibiti acire Mata, da farko Taki amincewa sai da taji yace bazai aureta ba matukar Taki bin umarninsa, gida ta shiga ta sanarwa da hanne aykuwa da daddaren hanne ta tasa furaira agaba suka tafi gurin wani Emanuel me chemist domin yayi Mata duk abinda ya kamata, dubu Ashirin ya bukata atake suka zaro suka mik’a Masa sannan yashiga cikin wani Dan d’aki shi da furaira.

   Lokacin da mlm kabiru ya dawo Kai tsaye gidan lubabatu me adashi ya nema sallama akayi Masa da mijinta bayan sun gaisa ya zayyane Masa duk abinda yake tafe dashi, magana yayiwa lubabatu sannan yayi mata bayanin mlm kabiru, Sarai ta fahimci mijin hajara ne karbar kudin tayi sannan ta shige gida, shima sallama yayiwa mijin lubabatu sannan ya wuce gida.

A sanyaye Emanuel ya fita Yana goge gumin fuskarsa kallan sa hanne tayi tace, ” likita inafatan ankamalla komai kenan Ina fatan dai cikin ya zube?” Cikin gurbatacciyar hausarsa yace, ” Ajiya akwai masalafa yarinyanki ta mutu fa” azabure hanne ta mik’e tsaye tana Fad’in, ” Kai me kake cemun ne bangane ba?” Emanuel Kara shafa kansa yayi yace, ” I mean ur daughter don die ooo, sai dai kiyi akuri Kixo da mota ki dauketa” hanne cakumar wuyan ema tayi tana zage-zage cikin kuka har duka take Kai Masa, da kyar ya samu ya kubce aykuwa ya fita da gudu Yana fita kuwa mota ta banke shi ko motsawa Bai karayi ba.

      Hanne tana kuka Haka ta fita take Kiran samari duk Wanda ta gayawa da irin taimakon da take san yayi mata sai dai ya zame ya gudu, har kafa ta Fara daukewa ganin dare ya farayi yasa hanne ta tafi gidan mlm liman buga Masa gida takeyi cikin tashin hankali, bayan ya fito da mamaki ya kalleta yace, ” baiwar Allah lafiya” hanne fashewa tayi da kuka sannan ta zayyanawa mlm liman duk abinda yake faruwa, ya jima Yana jimami sannan ya wuce yaje yafara Kiran jam’a sai da mlm liman yayi da gaske sannan mutane suka Dan taru aka fito da furaira har zuwa lokacin jini Bai daina fita daga jikinta ba, gida aka kaita sannan  mlm liman yayi shela akan zuwa safiya za’a yi Mata sutura akaita gidanta na gaskiya.

       Hakan kuwa akayi da safe aka sallaci furaira aka binneta, hanne duk ta fita hayyacinta mutuwar furaira ba karamin tab’a hanne tayi ba ko abinci Bata iyaci, gaba Daya tayi nadamar rayuwar ta tayi Dana sani yafi a irga gaba Daya duniya da rud’unta sun fice daga ranta, duk y’an unguwa sun fahimci sauyin halin hanne, ta kame kanta kamar ba ita ba, duk Wanda yasan hanne ya ganta awannan lokacin sai yayi mamaki.

   _Bayan wata takwas_

    Hajara na hango ita da wasu Mata suna tafe sun dawo daga wani D’an kauye kowwcce da abinda ta roro wasu ciyawa, wasu tafasa, harda masu kabewa, kayan jikinta duk sun kece takalminta ma wari da wari ne, gaba Daya tayi duhu kamar ba ita ba duk ta rame suna shigowa gidan hansa’u ta mik’awa hajara talatin tace, ” hajjo ungo kudin tafasarki wai saura naira hamsin lami zata ciko miki” afusace hajara tace, ” cab lallai wallahi ba ta Isa ba sai ta cikomun kudi na ba dare ba Rana Ina cikin dawa Ina roro inyo itacen indafa na Dora Mata tallen ta turon da naira Ashirin wallahi tayi karya” fuuuuu hajara ta sa Kai ta fice, fad’a ne yarincab’e da hajara da lami akan naira hamsin, abun ya kusa zama da kokawa kowa na zagin D’an uwansa, mlm kabiru ne ya shigo cikin kauyen da niyyar ya zo ya taho da hajara, Daga Dan nesa ya tsaya Yana karewa fad’an nasu kallo shi abunma dariya ya bashi wai hajara ce da fad’a akan naira hamsin, wani yaro ya Kira Mik’a Masa d’ari biyu yace ya kaiwa hajara, aykuwa har rige-rige sukeyi Allah ya bawa hajara sa’a ta karbe kudin, aykuwa lami ta rufe hajara da masifa har tana Mata gori wai mijinta ya sakota ya kawota kauye ya kyaleta ko yaranta Bata da iko dasu maganganu dai marasa dadin ji.

     Hajara ta juya da niyyar ta tafi gida saboda duk fad’an da kukeyi da ita da ka farayi Mata wannan gorin tuni jikinta zaiyi sanyi, inba’ayi Wasa ba har hawaye takeyi, idanunta ne suke Mata gizo kamar mlm kabiru ta hango Yana tsaye ya hard’e hannuwansa cikin kananan Kaya, murza idanunta ta yi tana Kara kallansa ganin ba gizo takeyi ba yasa ta tafi da gudu taje ta rungume mlm kabiru tana fashewa da kuka me tsuma zuciya, murmushi mlm kabiru yayi sannan ya Fara bubbuga bayanta, goge hawayenta tayi sannan ta d’ago da kanta tana kallansa cikin muryar damuwa tace, ” mlm ashe zaka iya mantawa Dani ka barni cikin damuwa kana cen kana cin Amarcinka da wannan tsinanniyar matar” sai alokacin mlm kabiru ya tuno da yace Mata zai auri hanne, murmushi yayi yace ki daina zagarmun Amarya ko ba komai yanxu matsayinku daya wuce muje ki shirya yau kafata kafarki.

     Haushin maganar sa taji Amma Bata nuna ba ta wuce suka tafi ta waiwaya tana watsawa su lami mugun kallo, duk sai sukayi shiru bame magana sai da su hajara suka wuce sannan suka Fara San tsegumi k’asa-k’asa.

     Saboda zumudi hajara Bata tsaya tayi wani wankan arziki ba, Dan ihsani mlm kabiru yayi wa mutanen gidan sannan suka sa kai suka wuce Kano, lokacin da su hajara suka shiga gida ba karamin farinciki su fiddausi sukayi ba, ita kanta tayi missing dinsu gaba Daya daga mlm har yaran nata Hira sukayi sosai kowa da irin labarin dayake Bata.

     Washegari mlm yake sanarwa da hajara rasuwa furaira, sai alokacin take tambayar sa Ina yakai hanne ba karamin dariya ta bashi ba daga Haka ta fahimci dama tsokaranarta yakeyi, mlm ne yace ta shiga tayiwa hanne gaisuwa da farko taki yarda sai daga baya ta shiga hanne na zaune tana Jan carbi taji sallamar hajara, kunyarta ce ta kamata bayan sun gaisa hajara tai Mata gaisuwa, akunyace hanne ta nemi gafarar hajara agurguje hajara tace ta yafe manata daga Haka tayi Mata sallama ta wuce gida.

            Hajara ce da mlm kabiru suke Hira cikin hirar hajara take bayyana Masa nadamar ta Kuma take rok’on gafararsa akan duk abubuwan da tayi Masa Wanda ya sani da Wanda Bai sani ba, cikin farinciki yace, ” hajara ayni na Dade da yafe Miki sai dai ki kiyaye gaba” gyada Masa Kai tayi tana murmushi.

     Wata Rana hajara na zaune hanne ta shigo, cigam ta mik’awa hajara take sanar Mata da daurin aurenta ranar asabar ta samu wani mutum da matarsa ta mutu sun dai-daita zasuyi aure, murna ta tayata da Allah Sanya alheri, mlm kabiru na zuwa hajara ta bashi labarin auren hanne cikin zolaya yace Mata, ” lallai mutumin nan da zafinsa yake tafe tunda har ya doke ni, Amma Kuma ta wani fannin tamun tsufa na duba ko akawayen fiddausi ne” hararar Wasa hajara ta watsa Masa tace ” ayda na bar maka gidan na koma karaye “

   Dariya mlm kabiru yake yi harda rike ciki yace, ” kice da kin koma damben naira Ashirin tunda kwanaki na naira hamsin kikayi, waini kudin meye ma kuke fad’a akansa?”

      Ita kanta hajara dariya tayi sannan tace, tafasa ce nakeyowa acikin dawa Ina dafawa sai indorawa lami talla, dasu nake samun D’an kudin kashewa” aykuwa gaba Daya suka kwashe da dariya.

           _Alhamdulillah Alakullihal_

     _Tammat bi hamdulillah_

   _Anan na kawo karshen wannan littafin na SANADIN RAGON LAYYA darussan da suke ciki Allah ya Bamu ikon d’auka kura-kuran da suke ciki Allah ya yafemana._

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *