SANADIN SONKI CHAPTER 3
Da gudu Aliyu ya shiga cikin gidan Babaa Lantana yana kuka sosai, Babaa Lantana mak’obciyar su fatima ce, mutunci sosai suke yi, tana tsananin tausayin Fatima da yaran ta, ita da mijin ta shi yasa wani lokacin suke taimka musu da abin da Allah ya hore musu, don su ma ba wani kud’i suke dashi ba sai rufin asirin Allah, suna da yarinya d’aya mai suna Aliyah ta d’an girmi Suhaima da kusan shekara hud’u, ita kad’ai Allah ya basu rayayyiya cikin duk yaran da take haihuwa suke mutu.
A madafa Aliyu ya tarar da Babaa Lantana tana sauke abinci daga kan murhu, d’ago kanta tayi da sauri ganin yanda aka shigo mata gida kai tsaye babu sallama, mamaki ne ya kamata ganin Aliyu ne ya shigo yana kuka, cikin mamaki tace
“Aliyu lafiya, mai ya faru kake kuka? ”
Cikin rawar murya da hakin gudun da yayi yace
“Babaa Lantana ki taimaka mana, Inna ce bata da lafiya gashi ji…… ‘
Kafin ya k’arasa maganar da yake yi ne, tuni Babaa Lantana ta d’auko fallen zanin ta na atampa a saman igiyar shanya ta lullu6a shi a kanta, ta fita da sauri shima Aliyu ya bi bayan ta, har suna rige rigen shiga gidan.
Cikin d’akin suka shige da sauri inda Fatima da Suhaima suke, Fatima sai murk’uk’usun azabar ciwo take tana hawaye, yayin da Suhaima take zabga kuka da k’arfi don ganin halin da Innar su take, da sauri Babaa Lantana da Aliyu suka k’arasa inda take, ganin halin da take ciki ne ya sanya Babaa Lantana cewa
“Subhanallah Fatima 6ari ne sannu Allah ya baki lafiya ”
Kallon Aliyu tayi tace
“Aliyu kama hannun Suhaima ku fita tsakar gida ”
Girgiza kai Aliyu da Suhaima suka yi lokaci d’aya, kafin Aliyu ya iya cewa
“Babaa Lantana kiyi hak’uri ki bar mu a wurin Innar mu ”
Itama girgiza kai tayi tare da cewa
“A’a Aliyu kayi hak’uri ku je waje ”
Dakyar Babaa Lantana ta shawo kan Aliyu ya kama hannun Suhaima suka fita waje, suna waiwaiyar Innar su, da batasan halin da take ciki don ta fara fita a hayyacin ta.
Bayan fitar su ne Babaa Lantana ta fara yiwa Fatima dabarin su irin na zamanin da, ganin abin yana kok’arin gagarar ta ne ya sanya ta fito waje inda Aliyu suke raku6e waje d’aya, kallon su tayi wani tausayin su ne ya kamata dakyar ta iya cewa
“Aliyu kayi sauri kaje ka kirawo Ladi ungozoma ”
Gid’a kanshi yayi sannan ya fita da gudu, ita kuma Babaa Lantana ta koma cikin d’akin wajen Fatima, ta bar Suhaima anan zaune tana kuka.
Babu dad’e wa Aliyu ya dawo Ladi ungozoma tana bin shi a baya, d’akin da Fatima take ciki ya iya nuna mata da d’an yatsan shi, Ladi ungozoma kuwa wadda ke d’auke da k’aramin buhu a hannun ta na kayan aikin ungomanci irin na zamanin da, ta shige cikin d’akin.
Duk yanda suka yi kok’ari wajen kada cikin Fatima ya zube, sai da cikin ya zube sai dai jini yak’i tsayawa sai zuba yake, nan dai ungozoma ta bayar da maganin da za’a jik’a mata ta sha, sannan Babaa Lantana ta biya ta kud’in ta, ta had’a kayan nata ta tafi.
Babaa Lantana sai da ta gyara jikin Fatima tsaf da d’akin, sannan ta kirawo Aliyu da Suhaima don su zo wajen ta, sannan ta tafi gida don d’ebowa Fatima abinci don ba k’aramin gala6aita tayi ba sosai, tun da ba wani abincin kirki take samu ta ci ba, da sannu Allah zai saka ita da yaran ta a wajen Umaru, tabbas yaci amana bai rik’e amanar da Allah ya bashi ba ya azabtar da su, duk don son rai irin shi nashi.
Suna shiga d’akin wajen Fatima suka nufa, zama suka yi a gefen ta gaba d’aya sun zuba mata suna kallon ta tamkar yau suka fara ganin ta.
Kallo d’aya mutum zai mata yasan bata da ishashshan jini a cikin jikin ta, saboda yanda tayi wani fari sosai, gashi ta rame sosai dakyar take iya motsi ma, kallon yaran nata tayu tana daga kwance, wani tausayin sune ya kamata, a hankali wasu hawaye suka shiga zubowa daga idanun ta, bud’e bakin ta tayi wanda ya bushe saman le6en yayi fari tace
“Aliyu ga Suhaima nan koda na mutu ka rik’e ta cikin amana, ina horan ka da ka tsaya tsayin daka ku nemi ilimi, don zama da jahilci bashi da amfani, sannan kada ku ce zaku ji haushin mahaifin ku, ku cigaba da yi mishi biyayya koda ya dawo wajen ku, ku kasance cikin yi mishi addu’a Allah yasa ya gane gaskiya, yasan ‘ya’ya rahma ne, komai runtsi ina son ka kasance da Suhaima kada ka guje ta, duk laifin da tayi maka kayi hak’uri kai babba ne ”
D’an dakatawa tayi ta had’iyi yawu sannan ta d’an yamutsa fuska saboda jin yanda marar ta take wani murd’awa wa, cikin kuka Aliyu ya kamo hannun ta yace
“A’a Inna baza ki mutu ba, zamu rayu tare da junan mu, don Allah ki daina wannan maganar Inna, hankali na yana tashi wani tunani yana d’arsuwa a zuciya ta sannan gaba na yana fad’uwa ”
Wani d’an murmishi Fatima tayi tare da cewa
“Kayi hak’uri d’ana ni kaina bansan dalilin yi maka wad’annan maganganun ba, ina son duk lokacin da mahaifin ku ya dawo ku sanar dashi na yafe mishi duk abin da yayi min, nima kuma ya yafe ni idan nayi mishi wani laifin a zaman mu, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya raya min ku ya baku ilimi mai amfani ya kuma kare min ku a duk inda kuke ‘ya’yana, ku rik’e Babaa Lantana da Baba Adamu a mataayin iyayen ku, don mutanen kirki ne kuma zasu rik’e ku tamkar Aliya ‘yar su, duk abin da suka baku shawara kuyi amfani da ita don nasan baza su baku mummunan shawara ba Allah yayi muku albarka ”
Fatima ta k’arasa fad’in haka tana hawaye sosai, nana Aliyu da Suhaima suka sake fashe wa da kuka sosai, ana cikin Babaa Lantana ta shigo d’akin turus taja ta tsaya ganin su da tayi suna kuka, jikin ta ne yayi sanyi sannn wasu hawaye na tausayin su ya zubo mata, wayance wa tayi tare da fakar idon su don kada su ganta ta goge nata hawayen sannan ta k’arasa inda suke tace
“Haba Fatima taya zaki na saka su a gaba kina kuka suna yi, ke da zaki rarrashe su ki kwantar musu da hankali ”
Murmishin yak’e kawai Fatima tayi, nan Babaa Lantana ta rarrashe su dakyar suka yi shiru, sannan ta basu abincin suka fara ci hannu baka hannu kwarya.
Sannan ta d’ago Fatima a hankali ta kara mata kofin madarar shanu mai d’umi a bakin ta, a hankali Fatima take kur6a har ta gama shan kusan rabin kofin, sannan ta zame bakin ta a bakin kofin tana girgiza wa Babaa Lantana kai alamar ya ishe ta.
Sauke kofin tayi a k’asa ta ajiye, tukunna ta d’auko kofin maganin da aka jik’a ta bawa Fatima tasha, bayan ta gama ta kwanta tana mai mayar da ajiyar zuciya, ita kad’ai tasan abin da take ji cikin jikin ta.
Babu dad’e wa bacci ya d’auke ta, fito wa suka yi zuwa tsakar gidan gaba d’ayan su don kada ayi hayaniya ta tashi, Babaa Lantana da Suhaima suka fara kimtsa gidan da yake Fatima bata sangartar da ita ba, tana d’an sata aikace aikacen da zata iya wanda baifi k’arfin ta.
Aliyu kuwa fita yayi a gidan don zuwa neman wani aikin da zai siyo wa Inna lemo da kankana don tasha, tun da yasan mara lafiya yafi son cin kayan itatuwa fiye da komai.
Babaa Lantana tana wanke wanke ne Aliya d’iyar ta ta shigo gidan, nan ta kar6i aikin da Babaa Lantana take yi ta cigaba da yi, gefe d’aya Suhaima nayi mata dauraya.
Lokacin da Farima ta farka daga baccin jikin ta da d’an dama don ta iya tashi taje band’aki da kanta, sai dai har zuwa lokacin jini yana zuba a jikin ta, amman ba mai yawa sosai ba, sai bayan ishsha Babaa Lantana ta tafi gida, ta bar Aliya anan wurin Fatima ko zata na taimaka mata da wani abin a yafi k’arfin Suhaima.
Bayan tafiyar kenan Aliyu ya dawo gidan da yankan kankana a hannun shi k’arami sai lemo mai 6ayo guda biyu, dakyar ya same su bayan yasha wahalar ferar lemo mai tarin uban yawa da mai siyar da lemon ya bashi, sannan ya bashi wannan kankanar da lemon tare da nera ashirin, cikin farinciki ya taho gida.
Bayan ya shigo gidan duk suna d’aki don haka ya shiga kitchen ya d’auko silver da wuk’a ya yanka su k’anana sannan ya shiga d’akin da sallama, Fatima, Aliya da Suhaima suka yi amsa mishi, da sauri Suhaima ta mik’e tana rik’e shi cikin shagwa6a tace
“Yaya shine kayi zaman ka ina ta jiran ka, kasan bana son ka fita ka dad’e ”
D’an murmishin yak’e yayi tare da shafa kanta yace
“Yi hak’uri ‘yar k’anwa ta aiki ne ya tsare ni ”
“Toh Yaya na ”
Fatima kallon su take kawai, kafin wasu hawaye su zubo mata, da sauri ta sanya hannun ta, ta goge su don kada su Aliyu su gani, don ma babu wadataccen haske a d’akin.
K’arasa wa yayi inda take ya zauna tare da mik’a mata silver d’in yace
“Inna gashi kisha, ya sauk’in jikin naki? ”
“Da sauk’i Aliyu nah, nagode Allah yayi muku ya albarka ”
“Amin Inna”
Aliyu ya amsa, nan ya fara bata a baki a hankali, bayan ya d’an sanwa Suhaima don Aliya k’in kar6a tayi.
A hankali yake bata har ta shanye tas, sannan ya d’auke silver d’in ya bawa Aliya takai kitchen, shi kuma ya fara jera wa Fatima tambaya akan yanda take jin jikin nata, Fatima kuwa amsa mishi kawai take da sauk’i, har zuwa lokacin kwanciya bacci, har ya tafi Fatima ta kirawo shi tana dad’a yi mishi nasiha tare da k’ara bashi amanar ya kula da kanshi da Suhaima, jiki a sanyaye Aliyu ya fito ya shige d’akin shi.
Can cikin dare wajen asuba ne jini ya tsinke wa Fatima kafin kace me tuni ta fara fita daga hayyacin ta, aikuwa Suhaima da gudu ta shiga d’akin Aliyu ta taso shiga, daman ba baccin yake ba, don gaba d’aya ji yayi baya jin bacci a idanun shi, ganin Suhaima tana kuka ba k’aramin d’aga mishi hankali yayi ba, ko tambayar ta bai tsaya yi ba ya fito daga d’akin nashi ya fad’a d’akin Fatima.
Yana shiga yaga abin da ya gigita shi, ya rud’u iya rud’ewa kamar wani babban mutum, da sauri ya k’arasa wajen Inna Fatima ya rik’e ta yana fashe wa da kuka yace
“Inna don Allah kada ki tafi ki bar mu, ki bud’e idanun ki ”
Ya fad’i hakan ganin yanda take lumshe ido tana jan numfashi da dakyar, gashi ta kasa magana sai kok’arin bud’e baki take tayi magana ta kasa bud’e shi, kallon Aliyu kawai take da Suhaima.
“Yaya Aliyu ka kirawo Babaa mana ”
Yaji saukar muryar Aliya a kanshi, sai lokacin ya tuna hakan, aikuwa ya ajiye Inna a hankali ya fita da wani irin gudu.
Fatima bin shi da kallo tayi Sannan ta mayar da kallon ta kan Suhaima, sai kuma a hankali ta bud’e bakin ta zata yiwa Suhaima magana, amman sai kawai taji ta tsinci bakin ta da furta kalmar shahada, a hankali ta k’arasa fad’a sannan Lokacin d’aya kuma numfashin ta ya tsaya da aiki, idanun ta kuma a lumshe suke har zuwa lokacin da zuciyar ta tabar bugawa komai na jikin ta ya tsaya cak da aiki ya daina motsi, ta koma tamkar wadda ta mutu ko irin ta suman nan.
Da iyakacin k’arfin shi yake bugun gidan Babaa Lantana yana d’aga murya da k’arfi yana kiran Babaa Lantana da Baba Adamu, sam kamar Aliyu baya cikin hayyacin shi yama mance da wani dare ne Saboda tsabar rud’ewa.
Da sauri Babaa Lantana da Baba Adamu suka fara rige rigen bud’e kofa, jin muryar Aliyu, Baba Adamu ne yayi nasarar bud’e kofar saboda Babaa Lantana zaninin jikin ta da kunce yana kok’arin sullu6e wa k’asa.
And rikice Aliyu ya rik’e hannun Baba Adamu yana cewa
“Ku taimaka min Inna ta ”
Abin da ya iya furta kenan, aikuwa tsakanin Babaa Lantana da Baba Adamu tare da Aliyu suka kasa tsere don shiga gidan.
D’akin Fatima suka fad’a dukanin su, kallo d’aya Baba Adamu yayi wa Fatima yasan bata numfashi, ganin haka ya sanya korar Aliyu, Aliya da Suhaima daga d’akin.
Suna fita Baba Adamu ya kalli Babaa Lantana ido jawur yace
“Sai dai mu yi hak’uri Lantana Fatima ta rigamu gidan gaskiya ”
Hannu Babaa Lantana ta sanya a kanta dukka hannun tare da zaro ido tace
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, Malam da gaske Fatima ta mutu ko suma tayi ne ”
Cikin dauriya Baba Adamu yace
“Haba Lantana ki kalle ta da kyau, ai kina kallon Fatima kinsan gawa ce ”
Lokaci d’aya Babaa Lantana ta rushe da kuka sosai, yayin da Baba Adamu ya sanya zani ya lullu6e ta tun daga saman kanta har k’afar ta, Sannan ya kamo hannun Babaa Lantana suka fito waje tsakar gida, ina Suhaima da Aliyah suka yi tsuru tsuru suna kuka, yayin da Aliyu ya kasa zama waje d’aya sai safa da marwa yake yi.
Ganin fitowar Babaa Lantana da Baba Adamu jikin su a sanyaye ga Babaa Lantana tana kuka, yasa Aliyu tahowa wajen su da sauri yana cewa
“Ku fad’a min meke faruwa, ina Inna ta, kada ku ce min ta mutu don Allah ”
Babu wanda yayi karfin halin yi mishi magana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai d’akin Lokaci d’aya kuma gaban shi na bugawa da k’arfi sosai……
Sai kun yi hak’uri da wannan page d’in banyi editing ba.
5/6