SAWUN BARAWO
CHAPTER 11 THEND KARSHE
“Ramlah! Keh Ramlah bude idonki ki kalleni nan” muryar Hajiya ta doki kunnuwan ta, a hankali ta rika bude idanuwan nata da hawaye yakasa daina fitowa daga cikin su, har yanzu kunnuwanta basu daina jiyo mata muryar Safwan ba lokacin da yake datse igiyar aurenta dake kanshi. +
“Ya salam!Hajiya,Innah, Nabilah, ku taimakeni, meyasa Ya Safwan zai mani haka? Meyasa zasu rik’a wasa da rayuwata kamar wata yar tsana? Uhmm Hajiya ki gaya mani, menene yasa mutanen nan biyu bazasu bar zuciyata ta huta haka nan ba? Sabida Allah Innah menai masu har haka da bazasu barni inyi farin ciki ba? Ki duba kigani Nabila daga wannan sai wannan, dame suke so inji? Nagaji, nagaji, Hajia, wallahi nagaji da yawa.” 2
Ta ida zancen da wani irn matsanancin kuka, ba shakka duk mai sauraren ta a lokacin dole ne ma tabashi tausayi, dole neh ka tausaya mata, hakika rayuwa nakan yin tangal tangal da ita, amma sai dai? Hakuri d yanda rayuwa tazo wa bawa shine kawai mafita. 1
Cikin lallashi Hajiya ta rika fad’a mata maganganu masu sanyi, ta hanyar yi mata nasiha, tare da yi mata da tunin cewa duk abinda yasamu bawa mukaddari ne daga Allah, abin kyautatuwa a gurin bawan shine yayi kokarin rungumar kaddarar tashi da hannu bibbiyu, tare da godewa Allah bisa dukkanin jarabawar da kuma fatan cin jarabawar.
Cikin ikon Allah,maganganun Hajiyan suka rika samun tasiri a zuciyar Ramlan,kamar yanda tunda abin yafaru halshenta bai yanke daga ambaton “innalillahi wainna ailaihirraju’oon ba.”
“Nagode Hajiya da kulawarki a agreni,amma inaso ki sani wallahi koda maza sun kare a duniyar nan bazan tab’a iya auren Ya Kabeer ba,shine mutum na karshe da zan iya sake hada inuwa guda dashi, ki gafar…. “
“Ya isa Ramlah!” Hajiyan ta dakatar da ita fuskarta kunshe da murmushi.
“Karki damu kanki akan Kabeer, domin kuwa koda ace zaki amince ki auri Kabeer a son ranki ma hakan ba mai yiwuwa bane matukar Safwan na da rai,kin manta ne intuna miki? Kabeer fa shakikin Safwan ne,sabida haka aure a tsakaninku haramtacce neh har sai in babu sauran nunfashin Safwan a doron k’asa, k’warai nayi mamakin hukuncin da Safwan ya yanke, wanda nasan yayi hakan ne out of sadaukarwa, ba tare da sanin cewa yin hakan da yayi din ga Kabeer bashi ne zai bashi ikon mallakar ki ba!” 8
Ta numfasa, kana a hankali ta waiwaya inda Kabeer keh zaune tun bayan afkuwar lamarin, ko kusa bai motsa ba tun bayan fitar kalaman daya dade yana son ji daga bakin danuwan nashi, sai dai abinda zai baiwa mutum mamaki shine, gaba daya kalamen da Safwan din yayi, sunyi nasarar debe duk wani sauran kuzari dake tattare da Kabeer din,al’amarun da yasa ya zama tamkar mutum mutumi,inba kayi masa kallon kurullah ba, zaiyi wuya mutum ya fahimci yana motsi ko baya yi.
Hajiyar na shirin magana ne,Kakus din ta amshe ta hanyar cewa, 2
“Toh Kabeeru dangin shed’an,burinka ya cika, kayi nasarar raba Yaron kirki da matar shi, duk sabida shegen son kai, da son zuciyah irin taka, toh amma sau dai kuma wani hanzari ba gudu ba, ga dai Rablatun nan an sakar maka, sai kazo ka aura mu gani idan kana da iko,afff ashe fa na manta da kasungurmin jahili nake magana, yoooh jahili mana, inba jahili ba, wane mai hankalin da ilimi ne zai rika bibiyar matar kannen shi kamar a zamanin jahiliyyah? Ai sai kai din jahilan farkon zamani.” 3
Hajiya samun kanta tayi da runtse idanuwan ta sakamakon jin zantuttukan da Innar keyi wa Kabeer din,ba shakka komi duniya ta gaya wa Kabeer ya cancanci a gaya mashi dinne,tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka!”Keh kuma, ta waigo kan Hajiyar, gara ma ki tashi yanzun nan ba sai anjima ba ki kintsa yarinyar nan, yau dinnan ba sai gobe ba zata koma gidan mijin ta, nagaji da wadannan abubuwa, zance yaki ci yaki cinyewa, toh gara su tattara su koma gidan su, suma safi sakewa da juna, amma nan ina yan hana ruwa gudu irin su Kabeeru zasu barsu su huta,wanda ni nasan duk iya bakin cikin mutum nan da wata tara da kwana tara sai na dauki gudan jinin Yaron Kirki a hannayen nan nawa!”
Ta d’aga hannayen nata sama tana nunawa Kabeer da baisan ma tanayi ba yayin da take kai karshen maganar ta ta.
Da mamaki suke kallon Innar, halan ta manta da furucin Safwan dinne kafin yabar dakin? 1
“Meye kuke kallona kamar naci ban biya ba?” Innar ta katse kallon kallon mamakin da suke bin ta dashi.
“Innah kun manta ne, yanzun nan ba jimawa Ya Safwan din ya saki Ramlan?
Nabilah tayi hanzarin tunawa Kakus din, a tunanin su ta manta ne.
Amma sai me? Wani mugun tsaki suka ji taja, kana tace,
“Ku kuka dauki wannan abun saki,ansaka Yaro a gaba ba dole yai sub’ul da baka ba yace ya saki abar son shi, kinga Saratu kina b’ata man lokaci wallahi.” 6
“Duk da haka ta saku Innah,ku kunsan hakan kamar yanda kowa yasan hakan.”
Hajiyar ta bata amsa.
Zuwa yanzu anfara kai Innah bango, hakan yasa ta mik’e tsaye gamida nuna Hajiyan da yatsa, rai a bace tace,
“Keh Saratu ki fita daga cikin idanuna,nace Rablatun bata saku ba koh? Ko kuwa dole ne sai na yadda da soki burutsunki? Toh naji inma ta sakun, ni na maida ta, keh inma ni bani da ikon maidata,toh yanzun nan zan nuna maku ikona ta hanyar sanya wanda ke da ikon maidata ya maidata din, aikin banza kai, har ni za’a gaya wa ba sukari?
Daga haka ta juya fuuu ta fice daga dakin, a yayin da dukkan su suka bi bayan nata da kallo,bakunan su a bude, girgiza kai Hajiyan tayi gami da yin wani sihirtaccen murmushi, yakamata zuwa yanzu al’amuran Kakus sudaina ba mutum mamaki.
Sake maida idanuwanta tayi kan Kabeer da har yanzu bai motsa ba,al’amarin da ya so ya dan baiwa Hajiyan tsoro, hakan ya sa ta taso gami da nufo inda yake.
“Kai banson shirme, tashi ka bar man d’aki.”
Babu alamun yaji ta, ko kuma iya shege ne yasashi yin biris oho. Hakan yasa ta kara daga murya, wannan karon harda kai mashi bugu a kai, a hankali ya dago idanuwan sa da suka rine zuwa kalar jaa ya zuba su akan mahaifiyar ta su, a yayin da yake jin wani nauyi a kasan zuciyar sa,take halshen sa yai masa nauyin da yakasa ce mata uffan, illah idanu da ya zuba mata k’uri.”Ka tashi nace ka fice man daga daki koh? Halan ka kurmance ne? Ba kaji abinda kake son ji ba? Sai ka tashi ka bace man da gani.” +
Kamar an tsunguleshi ya samu harshen sa dayai masa nauyi samun ikon motsawa, hakan yasa da sauri ya kamo hannayen Hajiyar ya rik’e tamau, duk ilahirin jikin sa babu inda baya rawa, murya da kyar kamar zai shide yace,
“Mammy!”
Da sauri Hajiyar ta kalleshi, rabon da ya kirata da wannan sunan, tun bayan lokacin da Safwan yafara iya magana, tun suna yara, wanda sai ayanzu ne ta fahimci, haushin Safwan din nakiranta da sunan ya sanya shi dena kiranta da shi,hakan yasa ya k’ak’aba mata Hajiya, wanda daga baya Hajiyan ya bita mammyn ya bace.
“Ba zance ki yafe man ba yanzu,sabida nasan fadar hakan tamkar wani sabon son zuciyar ne, haka zalika ba zan iya neman gafarar Safwan ba a yanzu,yin hakan tamkar son zuciya ne irin wanda nasaba, amma duk da haka, bazan fasa neman alfarmarki ba mammy,nasani ke kadai ce zaki iya fahimtata a yanzu, upon all my mistakes,ina rokonki da girman Allah mammy,ko bayan bani, ki rokar mani gafarar Safwan!ki hada ki rokar mani gafarar Ramlah, ban cancanci in roke su yafiya dakaina ba Mammy,bani da wannan karfin a yanzu, bani da wannan iyawar a yanzu,domin kuwa mutum mai tsananin son kai irin nawa ba abun ayafe masa bane kai tsaye!” 7
Zuwa yanzu, mamakin maganganun Kabeer din ya bayyana a fuskar Hajuyar, hakan yasa ta rika bin bakin shi da kallo tan mamakin jin wannan furucuin nashi kamar daga sama, shin menene ya canza wancan Kabeer din zuwa wannan yanzu yanzu?
“Kina mamaki koh Mammy?” Ya katse mata tunanin ta.
Ba tare da ta iya cewa komi ba ta daga mashi kai, murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo, kana yace,
“Mammy a yanzu yanzun nan bayan fitar wadannan kalamen daga bakin k’anina ne hankali da tunani samun shiga kwakwalwata, kinsan meyasa?”
Ba tare da ya jira amsarta ba yacigaba, “Sabida yanzu anan Safwan ya nuna mani girman zumunci,yanzu anan ya nuna mani shakikin so duk kuwa da irin muzgunawar da nai mashi,mammy ki duba ki gani,Safwan ya sadaukar mani da abinda yafi so kaf duniyar nan duk domin ya faranta mani bisa laifukan da nake ikirarin yayi mun, ashe akwai irin wannan soyayyar tsakanin danuwa da danuwa? Ashe duniayr nan akwai sauran mutane irin Safwan mammy?bantaba tsanar kaina ba rayuwata kwatankwacin yanda natsani kaina a yau,ashe tunda Safwan zai iya sadaukar da farin cikin sa domin nawa, ni meyasa tuntuni nakasa yi masa haka, saima bita da kulli da na rika bibiyar rayuwar sa da shi?ban cancanci wannan alkairin ba daga mutum irin sa mammy,ki taimakeni ki gaya mani ta yaya zangyara kuskurena akan danuwa nah”
Zuwa yanzu kuka kurum Hajiyar take, harma dasu Nabika dake zaune kan gado ita da Ramlah suna masu jin su.
Janyo shi tayi jikinta ganin yanda. Cikin kankanin lokaci ya canza kamanni tsabar kukan da yake, bayan shi ta rika bubbugawa a hankali,amma halshen ta yai mata nauyin da bata iya cewa komi,ruhu da gangar jikinta ne kadai suka san irin farin cikin dake ziyartar ranta, ba shakka Allah mai girma ne da daukaka, shi yakan shirya wanda yaso, a lokacin da yaso, yakuma batar da wanda yaso, a lokacin da yaso, Allah mai girma ne da daukaka! Alhamdukillah ta rika ambata a can kasan ranta
“Mammy ki gaya mani,Safwan da Ramlah zasu yafe mani? Don Allah karkice mani ah ah!”
“Me zai hanasu yafe maka Kabeer? Ko wane dan adam fa ajizi ne, haka kuma babu wanda baya mistake a rayuwar shi, abin godiga ne ga Allah ta yanda shiriya tazo maka tun kafin kurewar lokaci,ina mai tabbatar maka da cewar zasu yafe maka Kabeer, koba yanzu ba, ko ba dade ko ba jima, zasu yafe maka, kmar yanda ni dinnan na jima da yafe maka, nima kuma ina rokon ka gafara bisa fifikon da muka rika nunawa a tsakaninka da danuwanka,kwarai hakan zai zama darasi garemu da kuma yan baya, fatana yanzu Allah ya yafe maka Kabeer, ka dage da neman gafarar Allah, gami da neman gamawa da duniya lfya Kabeer, Allah yai maku albarka gaba daya.” 1
Hawayen farin ciki ne suka rika gangarowa bisa kuncin sa, hakan yasa ya dauki lokaci mai tsayi bisa cinyar mahaifiyar tasu yana kuka, bata hanashi ba, domin ya cancanci yayi kukan, sai da yayi ma’ishi kana ya doga kanshi ya kalli mammyn yace,
“Zantafi, zanyi nesa daku mammy, karkice mani ah ah,idanuwana baza su jure ganin danuwana ba bisa batancin danayi masa a rayuwata ba,ki tayani basu hakuri mammy, zantafi, bansan randa zan sake ganinku ba, amma idan Allah yayi mana tsawon rai, wata rana zamu hadu, nagode da kulawarku a agareni Mammy, kiman addu’ah, kuma ki taimakeni kimun alkawarin neman yafiyar su.” 2
“Nayi maka Kabeer, nasani kai ba Yaro bane, idan tafiyar taka itace alheri Allah ya sake hadamu da akheri, ka kula da kanka Kabeer,Allah yayi albarkaa.”
Daga haka ya mike yana goge sauran hawayen shi, labbanshi basu fasa furta kalmar godia zuwa ga mahaifiyar ta su ba, a yayin da ya gaza daga idanuwan sa ya kalli Ramlan, sai bayan da zai fitane yace,
“Ramlah ki rike Safwan da hannu bibbiyu, baki dace da kowane namiji a duniya in bashi ba, ga amanar k’anina nan a hannunki,zancen yafe mani kuwa, ban tsaurara ba,fatana dai ki yafe mani duk lokacin dakika ga dacewar hakan, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi, goodbye.”
Kuka sosai suke bayan ficewar sa daga dakin, sosai zukatan su ke rawa bisa wannan al’amarin, ba Shakka babu yanda Allah baya ikon sa.
“Na yafemaka Ya Kabeer.” Ta ambaci hakan a kasan ranta. 3
***
Kwance ta sameshi can karshen gadon nashi ya duk’unk’une tamkar maijin sanyi, haka zalika daga inda take tana iya jiyo sheshshek’a alamun ajiyar zuciyar ansha kuka an koshi. 4
Da hanzarinta ta k’arasa gami da hayewa bisa gadon tana mai kiran sunanshi, a zuciyarta kuwa mamaki take, domin kuwa zata iya cewa a rayuwarta wannan shine karo na farko da taga kukan Yaron kirkin nata tun bayan girma.
“Kai, Yaron Kirki, lafiyanka? Meyasameka?”
Ta jero masa tambayoyin a yayin da take birkitoshi daga cukuikuyewar da yai pilllow, jin muryar kakus din ya sanyashi juyowa da sauri gami da rugumeta, lokaci guda yana sakin ajiyar zuciya, batayi kasa a guiwa ba ta rik’a shafa kanshi alamun lallashi,kana kuma ta rika girgiza kanta cike da alhinin wannan hali na jikan nata, wannan shine yayi abin yasha masa kai kuma.
“Sweetheart,Kitaimakeni kigaya mani wani hali kazar mayu take ciki?” 7
Sai da ta harareshi kana tace “Bansani ba, ba dai ka riga ka saketa ba, kai ga sarkin “yan kirki da iya kyauta koh? Matar taka ma bata tsira ba, anya Yaron Kirki kana da hankali kuwa?”
Sake maida kanshi yayi bisa cinyarta yana hawaye, yayin da yakejin zuciyarsa tamkar zata fice daga kirjin sa ne, shin ta yaya zai fahimtar dasu dalilin sa nayin hakan?
“Sweetheart ki fahimceni don Allah, banyi hakan don wani abu ba, sai don neman sulhu tsakanina da Kabeer, idan har kasantuwar Ramlah a wajen shi ne zai kawo mana mas’ala gami da fahimtar juna, da kuma dorewar dangantakarmu, toh hakika hakan danayi ban fadi ba, fatana Allah ya bani hakurin jure rashin ta.”
Ya ida zancen,zuciyar sa na wani irin bugu, shi kanshi har yanzu yakasa yadda bisa hukuncin da ya yanke akan matar tashi.
Make masa k’eya da akai ya maido shi daga tunanin da ya fada, hakan yasa ya daga kanshi yana kallon fuskar kakus din dake ta zuba mashi kwandunan harara.
“Kai dai bantaba ganin shashasha irinka ba Yaron kirki, a tunaninka hakan dakayi ne zaisa Kabeer din ya auri Rablatun? Toh ai inka kwantar da hankalinka ma da baka sha wahalar sakin nata ba, domin kuwa sam babu aure a tsakanin su har sai bayan babu ranka.”
Murmushi mai kama da kuka Yayi,kana yace “Sweetheart waye yace maki babu aure tsakanin Ramlah da Kabeer matuqar ina raye? Ba haka bane,Allah bai haramta wa ya auri matar da kaninsa ya aura ba ko da yana da rai, sai dai domin abinda hausawa ke ce ma ana barin halas ko don kunya, ammah har ga Allah akwai aure a tsakanin su sweetheart”
“Kai da Allah jaaa can kabani guri, kana nufin Saratu kenan k’arya take da tace hakan haramun neh? Wai kai don Allah me ma kadaukeni ne Yaron kirki?”
Rik’o hannayenta yayi, a yayin da yatashi zaune yana fuskantar ta.
“Ni bance Hajiya tayi k’arya ba Sweetheart, kawai dai ina fada maki gaskiyar magana ne, wanda abune da nasani tuntuni, amma idan baki yarda ba, zankira maki wani kawun Bilal, babban malami ne sai ki k’ara tambayah kiji”
Dauke kanta tayi alamun zancen ne dai bata so, hakan yasa yasake juyo da fuskarta yana kallonta.
“Sweetheart, kiyi man addu’ah, inaso a yau dinnan zanbar k’asar nan, bazan iya jure ganin Kabeer da Ramlah tare ba, zuciyata zata iya fashewa.”
Wata dariya Kakus din ta kwashe da ita kana tace, “Kkwantar da hankalin ka, dama maganar da ta shigo dani kenan, maza maza ku hada kayanku kaida matarka kubar gidan nan, nayi matukar gajiya da masifun nan da suka ki ci suka ki cinyewa.”Wace mata kuma?” Ya jefo mata tambayar fuskar shi da alamun mamaki. +
“Kaci uwarka, kana da wata matar ne da ta wuce Rablatu? Yaron kirki ka fita daga idona tun ban fusata ba wlhy.”
“Sweetheart nakan rasa inda hankalinki ke tafiya atimes,kinmanta ne na riga da na saki Ramlan?”
“Mtsw,kai kake ta wannan, ai yanzun nan ba sai anjima ba nakeso ka maidata, sannan kana cewa ka maidata, banaso ku k’ara koda minti talatin ne a cikin gidan nan, ku wareh kawai ku bamu guri.”
Kallonta yake, yakasa cewa komi,ba shakka zaifi kowa jin dadin ganin Ramlan shi ta dawo gareshi, sai dai babban tashin hankalinsa shine,yaya Kabeer zai dauki al’amarin? Zai cigaba da kallon shi a matsayin mutum mai sonkai kuma maras cika alkawari kenan? Sannan kuma yaya makomar dangantakar su kenan?
“Stop stressing your self akan Kabeer Safwan.” Muryar hajiya ta doki kunnuwan su, a tare suka kalli kofa shida kakus din, yayin da Hajiyar ta karaso zuwa cikin dakin tare d neman guri ta zauna, ganin kallon da Safwan din ke bin ta dashi yasa tace,
“Eh haka nace,kadaina damun kanka akan maganar Kabeer, ina mai tabbatar maka daga rana mai kama ta yau, magana kwatankwacin abinda ya faru sai dai kuma labari, kamar yanda Innah tace dinne,katashk ka dauki matarka ku koma gidanku, ni kaina kun fara isata.”
“Yawwah gaya masa dai Saratu, dama yanzu yagama karyataki, wai ai akwai aure tsakanin Kabeeru da Rablatun, kiji soko fa.”
Murmushi hajiyan tayi, kana tace “Ba k’arya bane Innah, tabbas akwai aure tsakanin Ramlah da Kabeer, na fadi hakanne a lokacin domin koda Kabeer din zaiyi wata magana, idan da ace ma zai fito ya nuna mani Allah bai haramta ba, ni da kaina zan haramta hakan, wanda shine abinda nayi din, na haramta auren Kabeer d Ramlah ko bayan babu raina ne,sai kuma ma al’amarin ya juye zuwa wani babban al’amari kuma, kunji abinda yafaru bayan barowarku dakina……………. Tafara basu labari” 3
Sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya Safwan din yayi, a yayin d yakejin tausayi gami da kaunar dan uwan nashi na ratsa shi, hakan yasa take yake ya furta kalmar yafiya a gare shi, tare kuma da fatan Allah ya sake hada fuskokinsu da alheri.
Tabe baki Kakus take ta faman yi tun bayan gama jin labarin na Hajiya akan Kabeer, hakan yasa Hajiyar tace, “Lafia dai ko Innah? Naga sai faman tabe baki kuke, ko akwai wani abu ne?” 1
“Keh rufa ni ki saya ni, ninan garas nake, kawai dai zancen tuban Kabeerun ne be gamshe ni ba, sai kace a film? Daga fita ta har ya tsattsara ku haka, kuma kun hau kun zauna? Toh Allah yasa dai ba tuban muzuru yayi ba, kila ma don yaji ance babu aure tsakanin su ne yasa yace haka, yasan bazai samu ba, ahappp mu har a gaya mana salo.” 2
Ta dauke kai gami cuna baki gaba tana cigaba da tabe baki. 2
“Nifa Sweetheart banason haka, meyasa bazaki rika kyautata zato ba akan mutum? Ni nan danake zaune ban isheki ishara ba? Kokuwa ni da Allah yatashi shiryar dani,ba dare daya na shiryu ba? Duk d munsan shiriya daga Allah ce, amma komi yana da sanadi, kuma dukkanmu nan sanadi ne ya wanzar damu bisa tafarkin shiriyar, kawai ki mashi addu’ah tare da fatan dacewa, bawai ki rika fadin haka ba sweetheart,gaskia i don’t like it.”
“Dallah tafi can, nima ai i don’t like it din,wa zaka rika yi wa karyar turanci? I don’t like it, i don’t like it, nima na fad’a eheeeee!”Dariya ce taso subucewa Hajiya ganinnyanda kakus din tai kicin kicin da rai ita a dole tana turance jikan nata, amma sai ta dake gami da basarwa, zatai magana kenan Nabila ta shigo dakin. +
“Hajiya kizo, ga Ya Talib yazo, yana main palour a zaune.”
Da sauri Safwan yatashi zaune gami da cewa “ke zonan,what? Talib?where the hell is Ramlah?”ya jero mata tambayoyin a dan rude.
STORY CONTINUES BELOW
Da mamaki take kallon shi, ta ma kasa cewa komi, tsawar daya buga mata yasata rudewa, da sauri tace,
“Ammmm, tana, tana parlor, au tana dakin Hajiya,errrmm kamar tama fita ne ina….. “
“Are you stupid?get the hell outtaf here.” Ya sake katseta.
Kana ba tare da b’ata lokaci ba, ya mike gami da nufar wardrobe, jar shirt mai laushi ya daura bisa bakin jeans din dake jikin sa, kana ya rarumi keys din motar sa yayi hanyar fita daga dakin, sai bayan yaje k’ofa ne ya tuna da su Inna da Hajiya dake ta faman binsa d a idanu.
“Hajiya,Sweetheart thank you for everything,na maida Ramlah tun dazu bayan gama jin bayaninku,yanzun nan zamu wuce gidan namu kamar yanda kuka bukata,see you some other time.”
Bai jirayi abinda zasu ce ba ya fita da mugun sauri, domin shi kadai yasan yanda yakeji idan yaji koda ambatar sunan Talib ne akai, mutumin yayi masifar yi mashi karan tsaye a duniyar shi.
Hanyar parlor din yabi, koda tsautsayi zaisa yaga Ramlan a parlor din, sai kuma babu ita a ciki, hakan yasa ko kallon inda Talib din yake beyi ba, duk kuwa da hango Nabila da yayi a gabansa tana zuba mashi lemun exotic a cup.
Binshi da kallo Talib din yayi yana dan murmushi, kana a hankali kuma ya girgiza kai tuna baudadden hali irin na Safwam din, muryar Nabila ce ta dawo dashi daga kallon da yabi Safwan din da shi.
“Ya Talib, ga drink din kasha don Allah, and pls stop minding Ya Safwan, kaima nasan kasan halin shi.”
Murmushin nan nashi mai k’ayatarwa ya sakar mata, kana a hankali ya sassauta muryarshi yace, “Anything for this beautiful damsel” 3
Ya kashe mata ido daya, hakan yasa ta sunne kanta a cinyoyinta tana dariya a hankali.
***
Tura k’ofar dakin baccin Hajiyar tasu yayi a hankali, lokaci guda yana ambatar “Babyn Safwan where are you?” 6
Kasantuwar dakin da duhu yasa yafara laluben kunna switch, yana kunnawa haske ya gauraye dakin,can ya tsinto mak’ure a bakin toilet,karamin towel din wanka ne a jikin ta tun na dazu,kanta sanye yake tsakanin cinyoyinta,jinyo muryarsa da tayi yasa ta kara cusa kanta cikin cinyoyin nata, kwata kwata bata son ganin shi, har yanzu she couldn’t believe bakinsa zai iya furta mata kalmar saki ba, upon all the promises he made to her when he was making love to her, ashe duk karyace tunda gashi daga wayewar gari har ya dirka mata saki. Tai k’wafa a hankali ba tare da ta dago ba, duk kuwa da jin takun sa da ta yi ya nufo ta.
“Hello, what’s wrong with my baby?” ya tsugunna gamida son tattaro ta jikin sa, hakan yasa cikin zafin nama ta goce, lokaci guda ta dago rinannun idanuwan ta da tasha kuka ta rika gabza mashi harara, bakin ta na rawa tace,
“Don’t you dare touch me again, i hate you.”
Zuru yayi yana bin dan bakinta da kallo, haka kuma babu alamun jin haushin abinda tace mashi yanzu din, asalima picturing lips dinta ya rik’a yi bisa nashi, hakan yasa ba tare da b’ata lokaci ba ya janyo kafafunta k’iiiii ta fado jikin sa.
Ihu ta saki da dan karfi, domin ya shammace ta, dalilin da yasa ta rika bugun shi akan ya sake ta bata so.
“Please kabari Ya Safwan bana so, nifa ba matarka bace yanzu, meye haka kakeyi?” 6
Ba tare da ya dakata dga abinda yake ba yace, “Shhhhhhhhhhh,nasamu brain problem neh dazu honey,but alhamdulillah na dawo hayyacina yanzu.” 2
Hararshi takuma yi ganin rainin wayon da yake son yi mata, wato Innah taje ta tilasta shi ya maida ta shine zai raina mata wayo.
“Da Allah ni ka cikani, zuwa yanzu its high time da zaka gane cewar na wuce ajin matar cushe, kawai ni ka karasa mani sakina in huta.” 3
“You must be mad,wancan ma da akayi ki dauke shi a matsayin mummunar kaddara,wacce da izinin Allah ba bazaa sake maimaita wani abh kwatankwacin hakan ba, koda hakan na nufin sadaukar da numfashi na ne, i promise you that honey,please now accept mg bunch of kisses😘” +
Ko kafin ta numfasa, ya hade bakunan su, wani irin passionate kiss yake zuba mata, wanda hakan ba karamin effect yake samu ba akan ta, sosai take manta kowa da komi ta rika maida masa martani,ganin yana shirin zame mata tawul yasata zame bakin ta wanda yafara dan kumbura tsabar tsotsar da Safwan din ke mashi,tureshi tayi gamida yin baya tana kakalo hawayen k’arya. 12
Zuba mata idanuwansa da suka fara canza launi yayi, a yayin da mak’ogwaronshi ke ta sama da k’asa da sauri da sauri, ita dinma zumbura baki tayi tana mai k’ura mashi ido, sai take ganin ya k’ara yi mata kyau, ko meyasa? Shirun da sukayi suna kallon juna ne ya kara azalzala wutar shaawarta a zuciyar sa,hakan yasashi mikewa da sauri kafin yayi aika aika a tsakiyar dakin mahaifiyar tashi, ba tare da ta luraba, ya janyo zumbulelen hijabin sallar hajiya da ta cire dazu ya sanya mata.
Bai bata damar magana ba, ya sunkuce ta gaba dayanta bridal style yayo hanyar waje da ita. 3
Kira take, Yaya put me down, haaaan don Allah put me down, ni ka ‘aje ni, ina zaka tafi dani, wayyyooooh Hajiyaaaaah!”
Ta wage murya ta rika kwalawa Hajiya kira.
A parlor suka jame da su Hajiyan, Inna na gefen Talib sai zuba surutu take,ganin Safwan din dauke da Ramlah yasata mikewa tana washe baki.
“Ah ah yaron kirki har anfito kenan? Toh ku gaida gidanku kunji koh, don Allah karku sake zuwa gidan nan sai ka tabbatar akwai ciki a jikin Rablatu, bana ciki da iskancin ku atoh, ko kuwa me kace Dalibi?” 18
Ta waiga baki washe tana tambayan Talib, murmushi kurum Talib din yayi gamida gyada wa Kakus din kai, a yayin da yai hanzarin dauke kansa daga kallon sashen da Safwan din ke tsaye yana baiwa Nabila Saqon kayayyakinsu da suka bari, akan gobe Khalil yakawota da kayan nasu.
“Sweetheart,consider all your wishes done in sha Allah, Mammy mu mun wuce,see you some other time.”
Kunya ce kawai ke dawainiya da Hajiya, mussaman sabida Talib dake zaune a parlor din, duk kuwa da dama yanzunnan suka gama tattauna akan abubuwan da suka farau, kuma ya nuna mata da cewar komi ya wuce a wajen shi, domin kuwa yasan cewa haka Allah ya qaddara Ramlah ba matar shi bace.
“Bye sweetheart.” Muryar Ramlah ta doki kunnuwan su, hakan yasa suka kwashe da dariya dukan su, ganin yanda ya sab’ata a saman kafadar shi tana masu bye bye, fuskarta dauke da wani irin annuri wanda babu wanda yataba ganin ta da irin shi. 19
“Be happy baby am”
Talib ya ambaci hakan a kasan ranshi, yayin da yake bin su da addu’ar zaman lafiya mai dorewa.
***
Yayaah don Allah ni ka sosa man.” Ta fad’a muryarta da’alamun son yin kuka. +
Cikin magagin bacci ya lalluba inda yazame mashi tamkar karatu tsabar haddace shin da yayi, wato cikinta, a cikin baccin da ya riga yaci qarfinsa ya sanya hannun shi guda yana sosa mata tulluwar cikin nata mai kimanin wata bakwai a hankali. 7
Ture hannnun nasa tayi gami da sanya kuka da d’an karfi tare da cewa “Ni banan ba, nan nace.”
Da sauri ya karasa bude idanunsa domin fahimtar inda tace din, duk kuwa da duhu dake gauraye da dakin, mussaman idan mu kai la’akari da talatainin dare ne, wato a kalla karfe biyu da rabi na dare.
Sosai inka dubi Safwan din zai baka tausayi, mussamman yanda sam baya samun wani isashshen bacci, sakamakon tsirfa iri iri da cikin na Ramlan yazo musu dashi, balle ma da cikin yanzu ya dauki hanyar gangara, sai yayi da gasken gaske yake samu tayi bacci, daga nan shima sai yasamu ya dan runtsa, da kuwa ta bude ido, tofa shikenan karshen baccin sa shima yazo, daga tace ya sosa mata nan, sai ya danna mata can, sai kuma yai mata abu kaza, babu kuma sauran sauqi sai gabanin asubah, hakan yasa idan yaje office(yasamu aiki da reshen CBN dake nan kaduna) ya rik’a gyangyadi kenan,sai yayi da gasken gaske yake iya yin abinda ya kaishi. 3
Yana dawowa kuwa nan ma ba hutawar zeyi ba,da zarar yasamu yayi sallah kuma shikenan, wankan ta, cin abincin ta,duk aikin sa ne, daga nan kuma sai ta kwnta ya hau yi mata massage, itakuwa yar laushin tana zuba shagwabarta kala kala, thou ita kanta wani lokacin yana bata tausayi, hakan yasa take kokarin yin wasu abubuwa d kanta, duk kuwa da cewar ba da sanin sa ba, amma da tsautsayi yasa yakamata shikenan zai haut da masifa, shifa bayason haka,angaya mata baya iya yin duk abinda take so ne, daga nan kuma sai yahau zuba mata kashedi, bayaso kar ta sake yaqara kamata tana haka,inkuma wani abu yasameta ita da babynshi kotu ce zata rabasu. 15
Zuwa wannan lokacin ta riga da ta dena mamakin irin so da kulawar da Safwan din ke musu ita da yaron cikin ta,a duniyarta she never knew cewar people like Safwan do exist, mussaman idan mukai duba da irin baudadden halinsa, sai dai kuma me? He is very soft inside, mutum ne mai tsananin tausayi, haka kuma when he loves, he loves with all his heart, ktautatarwar shi da soyayyar sa a gareta yataka muhimmiyar rawa wajen kara daukaka darajar sa a idaniyanta,wanda hakan yasa a koda yaushe bata fasa godewa mai duka bisa bata sahihi kuma ingarman miji irin Safwan dinta, Allah abin godiya!
***
“Yayaah gaskiya ni wando nake son sawa, haka kake so inyi jogging din sa zulumbuwar riga?” Ta ida maganar tana mai k’ura masa ido alamun rok’o.
“Allah bazaki sa wando ba, i mean are you crazy? Babyn nawa kike son takura mawa ko kuwa me kike nufi?” 3
“Haba ni na isa, kawai dai Yayaa naga zanfi sakewa ne a track suit din.”
“Toh ban yarda ba ban amince ba,wannan rigar zaki saka.”
Ya k’arasa janyo wata armless doguwar riga silk maras nauyi,kana ya hado da wata er light sweater mai budadden gaba,ya aje su a gefe, daga nan ya koma gurin inda safunan su sake, ya dauko mata, kana ya nufi inda take jera vails dinta, nan ma ya dauko mata wani mai dan girma kadan amma maras nauyi. 1
Ita dai kallon shi take, har mamakin shi take a wani lokacin, yanda yasan takan zaba mata kaya, kuma ikon Allah duk lokacin da yace abu kaza din zata sanya, sai ta samu knta da zama comfortable a cikin su.
Yana tsaka da shiryata ne wayar aa dake aje bisa gado ta hau b’urari,ita ta zura hannu ta dauko wyaar, sakamakon tafi kusa da ita, “Sweetheart” ta gani bisa screen din, hakan yasa ta hau dariya, sanin dalilin kiran na kakus,hararta yayi gami da amshe wayar daga hannun ta, kana ba tare da bata lokaci ba ya danna malatsin rejection, yayi rejecting call din, yana shirin kashe wayar gaba daya wani call din ya shigo, wannan karon “Hajiya ce”.Shiiiiit!” Ya ambaci hakan a kasan makoshin sa, sanin cewar ko giyar wake yasha bai isa yayi rejecting call din ta ba. +
“Assalmu alaikum, this is Safwan Mainasara.” 7
Sallamar kawai ta amsa, kana cike sa masifa tace, muna cikin harabar gidan naku, idan kagadama kazo ka bude mana k’ofa, tan kaiwa nan ta datse kiran, domin ta riga da tasan ta shammace shi.
Sakato yayi da waya a hannu yana kallon ta, ba shakka daga dukkan alamu Hajiya da shirinta tazo gidan nan, idan beyi da gaske ba, yanaji yan gani zasuyi mashi sakiyar da ba ruwa, k’wafa yayi a cikin ransa, kana ya kara daura aniyar cewa babu mai rabashi da matar sa, ha’aan antaba dole? Shi bai taba jjn inda akace dolen dole sai mace ta koma gida don ta haihu ba, wai ma angaya masu shi be iyawa ne da matar sa da har sai ance ta wanj koma gida, shifa wallahi bayason tsirfan nan, kuma yasan duk iyayin nan daga waje kakus zai fito. 3
Jin cikinta da yayi yana zungurarshi ta baya ya sanar dashi rungumar da tayi mashi, hakan yasa da hanzari ya juyota gami da rungumeta tsamtsam, duk kuwa da cikas din da tirtsetsen cikin keyi masu wajen rungumar junan nasu.
Halshenta ta sanya cikin kunnuwan shi a hankali tana juyawa, sanin abinda yafi so kenan idan ranshi ya baci, sosai take manna mashi wasu k’ananan peck a tsakankanin wuyanshi da fuskar shi,wanda hakan yayi sanadiyar birkicewar shi gaba daya ya shiga yamutsa ta da zafin gaske, sosai ya manta da wasu su Hajiya a waje suna jiran su.
Yana gab da fara mai gaba dayanne wayar shi takuma canyara kara,hkna yasa yaja wani mahaukacin tsaki yana mai mirginawa daga kan Ramlan, shi har ga Allah ya manta da wata Hajiya a waje, da sauri ya mike gamida gyara zaman wandon shi,kana itakuma Ramlan ya gyara zaman blanket a jikin ta gamida manna mata peck a goshi ya fice da sauri babu ko riga.
Bude kofar yayi daidai da kwad’a mashi jaka da akayi, kana ba tare da tabari yace wani abu ba ta tureshi gami da kutsawa cikin gidan tana kwala kiran Rablatu.
“Rablatu, ina take er tusan itama? Zakici ubanki ke dadi miji koh? Kinzauna yana ta zungurarki ko a jikin ki, hmmm toh inbaku da hankali mu muna da shi, wai ina take neh?” 9
Ta durfafi hanyar dakin Safwan din tana cigaba da mita.
“Hajiya sannunku da zuwa.” Ya ambata bayan ta samu guri ta zauna.
Kalar hararar da ta maka mashi ya sanya shi saurin maida kanshi k’asa, a zuxiyarsa kuwa dariya abin ke son bashi, ganin wannan karfin hali irin nasu.
“Rike sannu da zuwanka, saboda ka maida ni yar iska nace maka muna waje shine sai da ka mula ka mule zakazo ka bude mana koh? Wato ga yan iska marasa aikinyi sunzo maku gida koh?”
“Ba haka bane Hajiya, kuyi hakuri, Ramlan ce nake k’arasa shiryawa, kunsan bata cika iya yin komi da kanta ba.”
Ba sai ya kalleta ba, yasan wata sabuwar hararar yake sha, hakan yasa yaqi kallon nata, sai faman suaaunkuyar da kai yake.
“Shiyasa mukeson dauke maka dukkan nauyin, amma dake kai din ba dan goyo bane kake neman maisa mutane abbokkan wasan ka.”
“Ni wallahi Hajiya sam bata takura mani, asali ma nasan ku din bazaku jure da wasu abubuwan nata ba, ni din dai ne ke iyawa da dukkan rigingimun ta, don Allah Mammy ina hadaki da Allah kibar mani kayata zan iya da ita.” 5
Galala tayi da baki tana kare mashi kallon anya wannan yaron na da hankali? Girgiza kanta tayi gami da dauke kanta ba tare da tace komi ba, hakan yabashi damar samun guri yacigaba da antayo zantuttuka masu tsabar nauyin ji wai shi nan a dole iya gaskiyar sa yake fada.
Ganin bai san katobarar da yake saki ba yasanya Hajiyar yaka mashi burki ta hnayar daga masa hannu alamun ya isa, kana ta sake daure fuska sosai taci magani tace,
“Ban tambayeka dukkanin zantuttukan nan ba, inace ba haka mukayi dakai ba, tun last upper week mukayi dakai akan zaka kawota, dake ka maidani kakarka sai ka rika man yawo da hankali, toh yanzu ba labari na tambayeka ba, tashi maza ka fito man da yarinya inada abinyi, koda ka ganni nazo gidanka.”
Marairaicewa yayi alamun son ganin ya lallasheta, wanda dama dakyar yake tunanin samun nas samun nasara a irin wannan lokacin, yana shirin sake magana ne ya jiyo muryar kakus din na fadin, +
“Au kuka ma kike koh Rablatu? La’ilahaillalahu ni jikar mutum hudu, toh wai ni duka duka ma yaushe kikasan dadi miji har haka iyyyiii? Saratu kizo ki gane mani wannan badala da rana tsaka.”
Zumburo baki gaba tayi,tana hawaye tace, “Toh ni dai kome zakice Allah babu jnda zanbiku, waye kukeso ya kular man da miji? ” 8
“Yau nashiga uku ban lalace ba ni Rakkiya!kai ina Yaron kirkin? Don ubanka garin yaya ka lalata yarinyar nan? Saratu kinajin er banzar yarinyar nan? Ana ga gabas yana ga yamma, ita ga me miji, toh don uwarki, tun kafin uwarki ma tasan zatazo duniya nasan meyw aure, har zaki tsaya kina man wani kilibibin banza da wofi, kuma gida babu fashi, ku hadiyi zuciya ku mace kawai!”
Tana bambamin fadan ta tiso qeyar Ramlan zuwa cikin falon, hakan yasa da sauri Safwan din ya mike ya taro ta jikin sa ganin yanda take hawaye, ga kuma masifar kakus dake ta kara rudata.
“Its okay ya isa nace, sorry honey, Kakus ce ta miki hayaniya?”
Tana malalar da hawaye ta daga mashi kai alamun Eh.
“Kiyi hakuri, kinsan ta yar hayaniya ce, Allah zai saka mamu kinji koh? Don’t mind her, i got you.” Ya ida zancen yana shafa sumar kanta dake a hargitse. 2
Bai dago kai ba ballantana ya lura da irjn kallon banzar da Kakus din ke binsu da shi, hakan yasa sai dai yaji saukar throw pillow a kanshi tana kundumo masu zagi.
“Ni naga laila da majnunu ma karewa,nakuma ga tip da taya, haka zalika na kuma ga kashin awaki karewar mannewa,ba hayaniya nayi mata ba ai, bata gaya maka sauran ba? Kamata nayi nai mata tsinannen duka a can cikin kuryar dakin naku daka boyeta, azo nima a dake ni, nace azo a dakeni, sannan ne zansan kaji haushi.”
Ramlan ce ta dago kanta daga kirjin Safwan din tace “Oho ai dai Allah ne zai saka mamu.”
Bata rufe baki ba, kakus din ta kuma jefota da pillow, hakan yasa ta saka kukan shagwaba.
Da sauri Safwan din ya dubi kakus din yace, “Nifa sweetheart wallahi kinfara kaini bango, haka kukeso inbaku matata kina zuwa kina cin zalin ta? Tun anan ma kenan, inaga inkun tafi inda babu mai ganin ki? Gaskia ni Mammy abar mani matata, zan iya da kayana.” 1
Ba tare da sanin sa ba, sai tsintar Hajiyar yayi a gaban shi, fuska babu alamun wasa ta mika hannunta ga Ramlan gami da cewa “Keh banson shashanci, tashi ki wuce muje kafin in sab’a maki.”
Sanin duk iskancin su basu isa suyiwa Hajiyan ba yasa jiki a sanyaye ta mika wa Hajiyar nata hannun ta kama, hawaye kuwa sukace bani guri, ai sai kawai ma ta bude mak’oshi gami da wage baki ta rika zunduma ihu, kamar wacce akace shikenan an rabata da mijin. 14
Kakus in banda salati tana sanar da ubangiji babu abinda take, kira take, “Yau mu munshiga uku, munga ta kanmu, keh saratu anya yarinyar nan kalau take kuwa?”
Ba tare da hajiyar ta juyo ba tace wa Safwan din ina jiranka, ka biyo ni da dukkan kayan bukatun ta, nasan kasan me nake nufi, daga haka ta cigaba da tafiya da Ramlan, suka fice daga main parlor din gidan, Inna na gefenta tana sababi. 3
Malam Safwan kuwa yanda kasan mutum mutumi haka yakoma, gaba daya notikan kansa ne suka samu go slow, hakan yasa yai zugudi yana mai jiyo muryar abar son sa tana burarin kuka, al’amarin da yasa ya runtse ido zciyar sa na bugu.
Take yanke ya yanke shawarar hada yanashi yanashi shima, da gangan ma ashe yake ta bata wa kanshi lokaci, bayan ga mafita nan ma. 10
Gama tunanin hkan yasashi mikewa da sauri domin zuwa ya hada masu kayan nasau, shima gidan zaikoma ya tare,badai sun iya rabashi da matar sa ba
? Toh gashi nan zuwa gidan, anyi 1-1 kenan.
***
Misalin qarfe shidda saura na yamma ya isa family house d’in nasu, sanya hancin motar sa cikin harabar gidan nasu, yayi daidai da fitowar Taleeb da Nabeela, kallo guda zakai wa fuskokin su ka karanto tsantsar soyayyah da bata iya boye kanta a fuskokin su, mussaman in mukai duba d yanda Nabilan ke ta nonneke kai, shikuma yana dubanta k’asa k’asa yayin da labbanshi ke motsi hankali, itakuma murmushi yagaza daukewa daga bakinta, da’alama wani abin yake fada mata. +
“Kai kam dai anyi babban kawai, ka tasa yar cikin ka gaba kana ta faman washe mata hak’ora, har bakujin maganar mutane a kanku.” 10
Be saurari hararar da Taleeb din ke maka masa ba, ya dubi Nabilan data qara sunkuyar da kanta tana turo baki gaba, yace,
“Zaki b’ace man da gani ko kuwa?”
“Heyyy, hang it there man,nikam wai ina ruwanka da Matata ne Damisa?kafa fara kaini bango, dan iska kai.” Talib din ya katse shi yana hararar shi.
“Say whatever you feel like saying dude, bani iya jure kallon tatsitsiyar nan a gabana, kana bada maza wallahi. “
Ganin bata wuce ba, yasashi sake cewa,
“Don ubnki yaushe nafara wasa dake?” 7
“Kai Yaa Safwan,invitations din fa zan karb’a a wajen shi.”
Bai sake bi ta kanta ba, ya dan bigi kafadar Talib dake tsaye yana banka mashi harara,
“Angon next week yi hakuri karka had’iyeni, kawai banason ganin yanda kake washe wa yarinyar nan baki ne,kasan mata da iya raini.”
Ya ida maganar yana dan tapping shoulder din Talib din, ture hannun sa Talib din yayi yace, Shege har kana da bakjn magana, kasan nasan komi koh?karka dena sa wa matata ido, wallahi zan rama ne, and me and you knows that.
Dariya Safwan din yacigaba dayi, yayin da yake dage hannuwan sa sama in surrender, kira yake, “Sorry man, i surrender!” Kana yai hanyar cikin gidan.
“Baby girl, don’t mind this your brother,daga next week dai yagama sanya mana na mujiya, oyaaa muje ki karbi invitations din.”
Murmushi ta sakar mashi, gami da gyada kai, yayin da zuciyarta ke cigaba da godewa Allah bisa zab’a mata nagartaccen miji irin Talib. 2
***
Da Khalil yafara cin karo a parlor.
“Kai zonan” ya yafito Khalil din, key din motar shi yabashi, kana yace mashi, ya bude boot din motar ya kwaso dukkan kayayyakin dake ciki yakai masa su dakin sa.
Karbar key din Khalil din yayi, a zuciyar sa kuwa fadi yake, dama ni nasan zaa rina, ta yaya ma su mammy zasu dauko Ramlah suyi tunanin Ya Safwan din zai zura idanu ya kyale su, dariya yayi a hankali gami da kara jinjina halin yayan nashi. 2
“Kazo kenan.”
Ya tsinkayo muryar Mammy daga wajen sashen cin abinci na gidan(dining area).
“Eh nazo Mammy, duk na kwaso kayan dakika buqaci in kwaso makk, harma da wadanda baki ce ba.”
Sanin abinda yake nufi yasa bata nemi jin ba’asi ba tace, “Hakan na da kyau bita zaizai.”
Shiru yayi, yayi kamar beji me tace ba, a zuciyarsa kuwa kira yake, “Mammy kirani da kowanne suna kika gadama indai akan Kazar Safwan ce, na amsa sunan da hannu bibbiyu, ni MAYEN TA NE.” 13
Tana shirin shigewa Kitchen ta waigo gamida bashi warning din karshe,
“Kabar ganin bance maka komi ba, bisa tarewar da kake shirin yi mana a gida,kar inji, kar ingani ka nemi takura wa yarinyar nan,infact sau biyu na yarda ka ganta a rana, da Safe in zaka wuce office ka shiga dakina ka dubata, sainkuma da dare in zaka kwanta, shima na yarda ka shiga kai mata sai da safe, inafatan ka fahimceni?” 6
Ta ida maganar babu alamun wasa a fuskar ta.
“Angama Mammy, yanda kike so haka za’ayi.”
Ya bata amsa, fuskar shi dauke da murmushi.
Kafin ta ida shigewa yai zumbur ya mike,gami da cewa, “Mammy bari infara ganin nata yanzu, tunda ban gantaba tun safe, kinga an fanshe na safen kenan.”
Ba tare da ya lura da kallon banzan da take watsa mashi ba, ya juya da azama ya nufi dakin Mammyn ta su.
Girgiza kai kurum Hajiyar tayi, ranta tan kara godewa Allah bisa samun canjin rayuwa da Yaron nata ya samu, indeed in every hardship, there comes a relief.
Allah abin godiya.
***
December, 2017
Hidimar bikin Nabeela da ake ra fama dashi, ya Nabeela da ake ra fama dashi, yasa sai yayi da gasken gaske yake samun ganin Kazar tashi, babu kunya, yake kutsa kai duk yawan mutane yaja Ramlan dakin shi yagama lagudata gami da jagwalgwalata son ranshi, wani lokacin ma har shammatar yake ya amshi kamu guda kafin ya barta ta koma,duk kuwa da irin matakan tsaron da Hakiyar ta sanya mashi, a cewar sa, sauki yake nemar wa Ramlan wajen haihuwa, mussaman in Ramlan ta so bijirewa bukatar tashi,daga nan ne zaibi ya kalailayeta da dadin bakin cewar ta hakanne Allah zai kawo haihuwar da sauki. +
Yau asabar ake daura Auren Abu Taleeb Tafeeda tare da amaryarshi Nabeela Mainasara, daurin auren da ya tara dubban jama’ah daga fannin ango da amarya, mussaman in mukai duba da abun duka tuwona maina neh. 3
Tunda suka baro wajen daurin auren,gaba daya abbokan ango da sauran mutane sunka rankayo sukayo gidan su amarya,domin daukar mutane zuwa inda za’ayi reception, kamar yanda abokan angon suka nuna rashin son yin african time.
Amarya Nabeela dama ta dade da gama cancarewa cikin wani arnen turquoise blue din code lace dinta, wanda aka sanya maroon ashoke aka nada mata head dashi,fuskar nan ta sha dankaren makeup, sai walainiya take tamkar wata ranar daren goma sha hudu. 3
Rukayya Sadauki ce ke faman taya Ramlah saka rigar ankon su na wani danyen tissue yard mai kalar zuma da sukayi, duk da dinkin maternity gown aka mata, hakan bai hana wajen sanya zip din wahala ba, mussaman yanda daga sama rigar ta dan kamata, daga kasa kuwa cikin nan yafiti zungurgur kamar zata iya haihuwa yau ko gobe.
“Ruky, tayani kiran Yaaayana please.” Ta mika wa Rukayyan waya yayin da take kokarin sanya sarka da dan kunnenta, sosai tayi kyau ba dan kadan ba, mussaman yanzu da cikin jikinta yasamu nasarar hurata tai k’iba sosai, ko ina na jikinta ya cike, gwanin ban shaawa,sosai cikin ya amsheta,mussamn yanda bai sakata muni ba, saima wani haske da fatarta mak duhu ta qarayi, hakan yasa kamarta da Rukayyan Bilal din sake bayyana sosai, tunda munsan cewa ita Rukayyan Fara ce tas, kuma chubby mai dan jiki.
“Kin ga ma My Bilal is calling.” Rukayyan ta fada yayin da fuskarta da tasha make up ke bayyana jin dadin gnin rabin ran nata akan waya.
“Okay,toh fara amsawa, nasan karshenta ma Yayaana ne, kinsan tun dazu wayan nawa ke a kashe.” Ramlan ta bata amsa.
“Eh ba mamaki kuwa,” Ta amsa, yayin da take cewa “Hello dear na.”
“Heeyy lover, I’ve missed you alot.” Muryar Bilal din ta doki kunnuwanta, hkaan yasata sakjn dariya kasa kasa tace,
“Kai dear, ko awa biyu fa bamuyi da rabuwa ba.”
“And so? Those two hours felt like an eternity to me kinsan hakan ai?”
Tana dariya kasa kasa tace”Nasan hakan angon Rukayyah in two weeks coming in sha Allah.”
Daga k’asan makoshin sa yace “In sha Allah lover, and i can’t wait for that blessed day to come! Ya rabbi!”
Sun shagala suna ta zuba zance har ya manta saqon Safwan din, da kuma ma musabbabin kiran, hakan yasa jin basu da niyyar hada shi da matar shi ya fizge wayan daga kunnen Bilal din yace,
“Sorry to interrupt lovers,hope you don’t mind sticking me with KAZAR SAFWAN?”
Dariya ce ta subuce wa Rukayyan, kana cikjn dariyar tace “So sorry Mayen Ramlah, here she is.”
Daga haka ta manna wa Ramlan wayar a kunnenta ta juya domin karasa shiryawa.
“Assalamu alaikum, this is MAYEN RAMLAH.” 3
A hankli, cikin siriryar muryarta mai kunshe da zallar kaunar mijin nata tace, “Wa’alaikumssalam,and this is KAZAR SAFWAN.” 2
A tare suka sanya dariya, wanda ko wannen su cikin zukatan su sun rasa wanene yafi son dan uwanshi.?
***
February, 2018
“Anya Saratu bazamu kira yaron kirki mu fada mashi halin d yarinyar nan ke ciki ba? Kinga fa har yanzu fama take.” Cewar kakus cike da damuwa.
“Ah ah Innah, kyaleshi, kinsan halin Safwan, yanzun nan sai yabaro exams din dake gabanshi yazo gurin nan,kuma jarabawa ce me muhimmanci yakeyi, banason abinda zai sa ya samu matsala, in sha Allahu zata haihu lafiya, mudai mu cigaba da yi mata addu’ah.
Cikin jimami Kakus din tace “Amin amin.” Sanin hakan ne kadai mafita a gare su yanzu.
Rufe bakin Innar yayi daidai da fitowar wata nurse,ta nufo su.
“Mrs Mainasara ta samu bouncing baby boy,the mama and the baby are in a good situation.” 5
Gaba dayansu suka mike, fuskokin su da zukatan su fal farin ciki, ba shakka yau Allah ya nufi Safwan da zama BABA, Ramlah kuma MAMA.
Allah abin godiya ne.
Rige rigen daukan kyakkyanwan babyn suke, Rukayyah da isowarta asibitin kenan ita da latest ango Bilal, Nabeela kam sai dai waya da ake ta faman yi da ita, sakamakon ba’a kasar suke zaune ba, tana can Amsterdam ita da ogan ta Taleeb, har da dan tayin cikin ta na wata daya da sati daya.
“Masha Allahu, wannan ai Yaron kirki kika haifa mani Rablatu, Saratu zokiga fuskar jaririn nan, tamkar lokacin da kika haifi Yaron kirki.” 7
Cewar Innah tana washe baki, gaba daya ta kwakume jaririn, tun bayan shiryashi da aka gamayi, ta hana kkwa ya taba shi, hatta uwar jaririn, sai leken shi kawai da take faman yi, babu halin magana. 2
“Aikuwa wallahi Kakus kamar Abokina sak babyn, dan kawoshi in mashi addu’ah.” Cewar Bilal yana murmushi.
Sosai take ganin girman Bilal din, hakan yasa sam bata iya yi mashi rashin M, hakan nan ba don ranta ya soba ta mikawa Bilal din katoton babyn da yai k’urrr da ido yana kallon kowa. 2
“Wai kaci sa’a Bilal” cewar hajiya a cikin zuciyar ta. 1
Ko minti biyar babyn beyi ba, ta mika hannu akan abata shi nan, Rukayya kamar ta fasa ihu, sakamakon ta samu ta amshi babyn daga hannun Bilal din.
Tana k’unk’uni ta mik’a mata shi, kamar ta sanya kuka, gaba daya babyn yagama yi mata kyau, ji take inama nata ne.
“Namu na nan tafe very soon lover.”
Ta tsinkayi muryar Bilal din na rada mata, hakan yasata sakin dariya a hankali.
“Ramlah, maza ki shanye tea dinnan mu wuce gida, tu da dai doctor din yace babu wata matsala, kinga kema kina bukatar hutu sosai.”
Cewar Hajiyan,toh kawai tace wa Hajiyan, a zuciyarta kuwa duk tabi ta kosa mayen nata yazo ya kwatar masu yancin su wajen kakis, wannan karfin hali har ina? Mata tabi ta kwakume baby ta hana kowa, har ita da take uwarshi ta hanata tajk dumin kayanta, kamar ita tai mata nakudar, ta ida tunanin tana hararar inda kakus din ke zaune sai zubawa baby surutu take, kai kace jin me take cewa yake.
Bata gama shan tea din ba, aka shiga dakin da sauri, sai da ya karaso ma ya tuna da wata sallama, bai bi ta kan kowa ba sai matarshi dake ta faman doka mashi murmushi tunda ya shigo, hayewa yayi bisa gadon gami da tallabota jikin ta, kana ahankali ya manna mata peck a goshi, kan kuma ya lalubi kunnenta yace,Thank you a million times for completing me honey,Allah yai maki albarka Kazar Safwan.” +
Sake lafewa tayi a kirjin sa, kana a hankali tace “Ameen my hayateey,”
Babu wanda yakulasu, domin inda sabo yaci ace ansaba da wannan kalar rashin kunyar ta Safwan, wanda sannu a hankali sai da yasamu nasarar koyawa Ramlan itama. 4
“Where is my blood?” Suka tsinkayo muryar Safwan din yana tambayar Ramlan.
Sai da ta cuno baki gaba tace, gashi can hannun Kakus, kuma wallahi Yayaah tun dazu fa Kakus dinnan ta hana kowa daukar shi, kaji fa har ni dana haife shi tayi kanekane ta hananj koda ganin shi ne.” Ta ida maganar tana kunkuni. 19
“Yoooh akan me? Ita tai mamu nak’udar da zata nuna mana fin karfi?”
Wannan shine harara cikin duhu, domin wacce sukeyi don utama batasan wainar da ake toyawa ba, tana can hira tai nisa tsakanin ta da sabon Baby, shima gulmammen babyn ko ehem baiyi ba, ballantana a sa ran zaiyi kukan neman abincin shj, saima ware idanu da yayi yana bin bakin Kakus din da kallo, kai kace yasan me take cewa.
“Excuse me sweetheart, in babu damuwa Daddy nason ganawa da Babyn shi.”
“Yaron kirki ba dai gandoki ba, toh ai sai ka bari sai munje gida, yanzu kam baka gani hira muke?”
“Eh ai nima hirar nake so muyi, ko baki gane bane? In maki gwari gwari?”
Safw din ya fada cike da kosawa, Sweetheart din tashi tafara kaishi bango.
“Kai nifa kasan banson damu Yaron Kirki, nace bazan bayar ba koh? Ko kuwa so kake ka gwada mani cewar kai kai cikin?” Tafada a fusace tana hararar Safwan din. 10
Shima hararta yayi kana yace, “Kuji man Sweetheart dinnan fa, toh da ke kikai cikin? Kinga ni kibani dana, nida matata muna son ganawa da abin mu, ha’an wannan masifa har inah?” 10
“Kunci ubanku ku duka, karfi yaci daru ya danne, idan kuna da karfi kuzo ku k’wata.” 4
Ta bashi amsa tana fici fici da ido.
Sanin bala’in kakus yasashi sassauto da murya yakoma lallashi, domin yafi dan dakkn tasha sanin babu wanda ya isa yasa Kakus ta bada babyn nan in har batai niyya ba, sabida haka masifar shi ba wai yimata zatai va, gara ya lallabata, kila a dace.
Anci sa’a da ya langabar da kai kamar maraya, kuma ya nuna shi din ba komi bane, kana kuam ya hada da cewar huduba kawai zai mashi ya maido mata shi, ta bayar da babyn, dake shima babyn dan daru neh yana shiga hannun Safwan din ya dage ya tsala ihuu, kamar an mintsine shi. 2
Dariya kowa na dakin ya kwashe da ita, ganin yanda Shi kansa Safwan din ya rude gamida saurin maida wa Kakus Yaron, wanda yana dorashi kan hannunta yai tsit yana sake warwara idanuwan shi kan Kakus din, al’amarin d yasa kakus din wangale baki gaba daya tace,
“Sabon Yaron Kirki, barka da zuwa duniyar mu.” 8
Gaba daya akasa dariya, ana al’ajabin wanna qauna data wanzu tsakanin Kaka da Tattaba kunnen ta.
A hankali kuma Safwan yace, “Alhamdulillah, Allah ya raya mana BILAL MAINASARA, yakuma raya shi bisa tafarkin sunnar manzo (SAW). “
Fuskar Bilal ce kawai dauke da mamaki, sabanin sauran mutanen dakin da suka amsa da amin amin, yayin da farin ciki mabayyani ke fita daga fuskokin su.
“Nagode Aboki, kagama mun komi, Allah ya akbarkaci Rayuwar namesake dina, ameen.” 1
Safwan din ya dubeshi gami da cewa “You deserve more than this Aboki, kai din Amini ne nagari.” 7
Duka dakin suka hada bakunan su wajen cewa wannan haka yake, Alhamdulillah.
Rungume Ramlan yayi suna murmushi, yayin da idanuwan su ke cike da so da kaunar junan su, ba shakka komi yai farko zeyi karshe.
***
Tammat bi hamdullah!
MU HADU A WANI BOOK