SAWUN BARAWO
CHAPTER 3
A yau ashirin da biyu ga watan satumba, shekara ta dubu biyu da sha shidda, jama’a suka shaida d’aurin auren SAFWAN IBRAHIM MAINASARA tare da Amaryar shi RAMLATU HASHIM TAFIDA, bisa sadaki naira dubu hamsin, lakadan ba ajalan ba.
D’aurin auren ya wanzu ne bayan sakkowar masallacin juma’ah na almannar da ke nan unguwar sarki kaduna, duk da d’aurin auren yazo neh b’akatantan ba bisa shiri ba, hakan bai hana jama’ah halartuwa gurin d’aurin auren ba, diba da irin ranar da d’aurin auren ya kasance.
Bayan gama d’aurin auren neh, su kabir da sauran k’alilan dangi mafi kusa da suka sami halartar d’aurin auren neh suka rankayo gaba d’ayan su, suka yoh gida, fuskokin su cike da boyayyun al’amura masu wuyar fahimta.
Hak’ik’a kusan gaba d’aya mazan gidan basa amanna da wannan auren, amma ganin yanda hajiyar ta su tai tsaye bisa lamarin ya sanya su basar da lamarin ta hanyar bin auren da du’ah’i da kuma fatan dacewa a cikin lamarin.
“Lallai hajiya da gaske take fa” cewar sa’id wanda shi ne ke bin safwan d’in wajen haihuwa,sakamakon ganin wata er k’warya k’waryar walima ta cin abinci da hajiyar ta shirya a harabar cikin gidan nasu.
“Ni mamakin duk a yaushe hajiya ta shirya al’amuran nan nake fa,ka duba fa yanda mako’ota da jama’ah ke ta zarya cikin gidan nan, kai kace auren nan an dad’e da sanya ranar sa. ” cewar salim yayin da suke shigewa cikin falon bak’in dake ta farkon shigowa gidan.
“Kuma da abin dariya kuke, kamar ba ku san wacece hajiya tamu ba? Hajiya ce fa tamu, ko kun manta ne in sake tuna maku”? Cewar kabir babban yayan su namiji.
Gaba d’ayan su suka kwashe da dariya gami da had’a bakuna wajen cewa “Hajiya sharp sharp ka keji alaji”.
Zaman su keda wuya nabila ta shigo falon dauke da kuloli a hannayen ta, bayan ta kuma wasu mata neh biye da ita dauke da filet filet na serving abinci
“Wai don Allah ya kabir haka akai d’aurin auren babu ango a gurin”? Cewar nabila yayin da take k’ok’arin aje abubuwan hannunta a inda ya dace.
Sai da tasami tukuicin rank’washi a ka kafin ya bata amsa “Mi ya hana kije ki d’auko shi a dak’in hotel d’in da ya maida tamkar gidan uwale da ubale”?
“Washhh! Wayyo Allah ya kabir, ba kyau wallahi, Allah har kaina ya fara ciwo, daga tambaya zaka burma mani kai” ta ida zancen tana turo baki, da’alama rank’washin ya shige ta.
“Amma zancen gaskiya yaya kuke ganin za’a k’areta da damisa? Kun san safwan fa hanyar da mutumci ya bi, sam bai bi ba, abin na ban tsoro nikam” cewar sa’id.
“Nikam ramlan ce kawai ke bani tausayi wallahi, ina hango mata tashin hankalin da keh gaban ta neh, for God’s sake mi yasa hajiya zata dage kan lamarin nan neh”? Salim ya amshe cike da jimami a muryar shi.”Duk wannan surutun babu maganin da zaiyi, gata d’aya zamui mata mu bita da addu’ah, Allah na nan ai, sabida haka shi zai kareta daga kaidin safwan” inji kabir kenan.
“Allah sarki ramlah, wallahi yaya tun da abubuwan nan suka taso baiwar Allahn nan ke kuka, sai kunga yanda ta k’ara ramewa, dama ya lafiyar kura bare tayi hauka” cewar nabila yayin da hawayen tausayin ramlan suka gangaro daga idanuwan ta.
***
“Wooh keh innah, wannan irin cizo haka sai kace kece amaryar” Khalil ya fad’a tun bayan shigowar shi dakin na inna bisa aiko shi da hajiya tayi a kan yazo yagaya mata ramlan tak’i ta je ta yi wanka ma, ballanta na aje ga batun sauya kaya. 2
Aiko nan da nan saiga inna na dashe baki, dama ga bakin duk wawulo tubarkallah,cike da murna ta amshe, “Kai khalilu ai dole nake tsatso kyawu na tun na ‘Yammatanci, bikin yaron kirki sukutum, in banyi kyau ba nikuwa mizanyi”?
Ta ida zancen yayin da take k’ara danna dankwalin dank’areriyar super aura d’in ta da hajiya ta sanya mussamman aka je aka dinko mata domin ta ci bikin shalelen ta. 2
“Ah gaskia na shaida wankan nan kakus, billahillazi kin wanku, no homooo yasin” ya ida zancen yana k’yalk’yalewa da dariya sakamakon ganin yanda ta dage tana d’aura d’ankwali yana salib’ewa.
“Yau ga d’an jakar uba, ni ce hamagon?” ta dakatar da abinda takeyi, tare da yin mitsi mitsi da idanuwa cike da masifa. 2
“Ai kinji matsalar ki kakus, ni tsiyata da ke k’auyanci wallahi, da yaushe nace maki hamago? Homoo nace, wani slang neh na yabo, ki ganeh mana” ya ida zancen yana harar ta.
“Ja’iri kai kasan wani ‘salang’, ni amshi waya ka danno mani yaron kirki d’an albarka,shin bazai zo ya ga amaryar shi bane”?
Turus khalil yayi yana mai hangame baki, a lokaci guda kuma yana mamakin kakus yar tawaye, ya akai ta chanza haka.? 1
“Allah dai ya biya kakus ta mu, ashe kema kin bi bamu da labari” Woooh keeehhhh” yayi baya baya alamun sarawa da jinjina.
“Kai da Allah can, yooo tun yaushe nabi dama? Ai da yaron kirki ya kawo man wannan mai siffar inyamuran dajin, gara dai rablatun, nasan da ta gyagije zatai bulbul ta maida wannan shegiyar ramar ta ta.”
Khalil yaci gaba da shek’a dariya ganin yanda inna ta fututtuke ta rik’a durawa samira zagi ta uwa ta uba, kai kace samiran na gaban ta ne.
Ganin bata da niyyar shiru ya sanya shi dakatar da ita ta hanyar cewa ” Yooo ni surutun ki ma kakus yasa na manta aiken da hajiya tayi mani gurin ki”
“Shegen surutun ka yaza ai yabarka dama ka tuna, Ya ya ankayi”?
“Wai tun dazu ake fama da Ramlah taje ko wanka ne tayi ta k’iya sai faman zabga kuka take, shine tace ingaya maki kizo ki lallashe ta k’ila ta ji maganar ki”
“Yau ga shegiyar mata, yanzun dama har yanzu el banzar yarinyar na bata bar kukan nan ba haka? Shi yaron kirki beyi kuka ba, da aka k’ala mashi ita, sai ita ce mai bakin iya kuka zata ishi jama’ah da koke koken banza da na wohiii”.
“Tashi muje inje inga yar jakar ubah, tana fama da wuya kamar masangalin lema.” Ta Ida zancen tana mai gyara zanin atamfar ta.
“Gaskia ke kakus Allah atimes ba ‘M’ kika cika ba, kibar baiwar Allah kawai tasha kukan ta sin ran ta, duk wanda aka ce zai had’a inuwa guda, bama gida ba da ya safwan ai dole ya yini yana kuka, Haba don Allah” khalil d’in ya fad’a cike da jin haushi.
“Jaa chan kabani guri shashasha mai kan k’wandala, kayi da tsayi kamar daren jire gawa, ai duk layin ku d’aya da rablatun” Tai gaba tana cigaba da mita, ita a dole an tab’o shalelen ta.
“Ina rablatun take” ta rik’a d’aga murya tun daga nesa.Wata cousin dinsu mai suna safiyyah ta mik’e a hanzarce taja ramlan gaba d’ayan ta ta antaya band’aki, sanin irin tijarar da kakus ka iya sauke masu a take yanke.
“Sannun ku innah, ahhh innah wannan tsatso kyau haka,? gaskiya ba k’arya kaman wata y’ammata ahswear” cewar safiyyan bayan ta datse ramlan a toilet d’in.
Sai da ta dak’una fuska, kana lokaci guda ta watsa wa safiyan harara, sa’annan tace “Fitsararriya baki san hanyar dakina bane, sai yanzun da kika ganni anan zaki mani wani felek’en dad’in baki? Toh rik’e kayan ki ban so, dubun ki sunce nayi kyau, don haka ban buk’atar naki”.
“Kai innah keh kullum cikin fad’a wallahi, zuwa na fa gidan kenan nake shirin inzo ingaishe ki, amma ji abinda kike cewa, ai shikenan bakomi wallahi” safiyyan ta maida mata tare da yin kalar tausayi.
“Keh ni ba wannan na tambayeki ba, ina rablatun? Taje ta yi wankan, ko kuwa tana jira neh sai yaron kirkin yazo yayi mata?” 3
Safiyya ta kwashe da dariya gami da cewa, “Kai kuji innah da wani batu ma dai, Kai kakus Allah dai yabar mana ke muaaaahhh” ta jefo mata kiss
“Kinyi wa uwarki Fatima, Fitsararriya, lukutar wofi” ta juya tana cigaba da mita.
“Naji bakomi inna, banji haushi ba wlhy *inyyuuut*” ta kuma jefa mata wani kiss d’in tana dariyaah sosai,Ko banza ta koreta cikin ruwan sanyi.
1
***
“Innah wallahi na riga da na rantse, ramla ba ta sake kwana a gidan nan, ba dai ni safwan yake so ya maida ‘yar iska ba, toh wallahi bai isaba, ni na haife shi ba shine ya haifeni ba”. Hajiya ta ida zancen tana huci, bayan gama amsa wayar kabir da tayi.
“Nifa saratu bana son haka, abi yaron nan a hankali bawai abi a rik’a matsa mai lamba ba, naga da sai a hankali zai saba da wannan auren dole da kikai mai” innar ta amshe.
Hajiya ranta ya sake b’aci sakamakon jin furucin na inna a karo na sha biyar tun faruwar d’aurin auren.
“Toh amma inna ta yaya safwan zaice baiga uban da ya isa ya raba shi da kwanan hotel d’in nan ba, sabida Allah kamar gidan uban shi” ta fad’a tamkar ta fashe don haushi.
“Kinga laifin shi? Nace kinga laifin shi ? Ai ko nice aka bi aka sanya mani idanuwaa gidan nan, abinda zanyi kenan, yoo ina dalili abar yaro ya b’ararraje, dukiyar uban shi ce ai bata wani k’ato ba eheeeh!”
Haushi yacigaba da kashe hajiyar kamar ta kurma ihu, kwata kwata innah bata da dad’in shawara, yanzu ta yaya zata sa aje afara aje ramlah a wannan k’atoton gidan ita kad’ai? Ai ba zaiyiwu ba, kuma ta riga tasan kafiyar safwan, babu mahaluk’in da ya isa ya sa shi yabaro otel d’in kamar yanda yace.
“Toh yanzu meye abin yi”? Tacigaba da nemar wa kanta mafita.
Cikin mintuna tai reaching conclusion, hakan ya snaya ta mikewa da saurin ta, tabar inna a gurin tana hararar ta.
Kai tsaye dakin da su ramlan suke ta shiga, a shirye ta sami ramlan sun sanya ta ta kimtsa don dole, amma fa har alokacin hawaye ke kwarara daga rinannun idanun ta.
Ba tare da b’ata lokaci ba ta umarci nabila da ta dauko shiryayyun akwatin ramlan ta biyo ta dashi mota, lokaci guda kuma ta umarci saffiya da ta kama wa ramlan hannu ta kai mata ita cikin mota.
Cikin mintuna da basu shige goma ba, hajiyar ta shirya, kana kai tsaye ta nufi parking lots d’in gidan ta iske su a tsaye suna jiran ta.Dama ramlan na cikin motar, hakan yasa batare da b’ata lokaci ba ta umarci su nabilan da su koma ciki, ita kuma taja motar, mai gadi ya hangame masu get ta fita. +
Waya ta rik’a yi da kabir domin samun tambayoyin da take buqatar amsar su, hakan yasa basu dauki dogon lokaci ba suka isa HOTEL d’in da safwan din yake.
Reception ta fara isa, ta umarci da shigo da akwatunan na ramlah, kana a lokaci guda ta kama hannun ramlan dake ta sharbar kuka cike da tashin hankali sukayi sama, inda kabir ya gaya mata lambar d’akin.
Knocking ta farayi, amma hakan baisa antanka ba, hakan yasa tak’ara sautin knocking d’in da d’an k’arfi a wannan karon.
“Common the door is damn opened” ta jiyo muryarshi a hasale yana fad’i.
Hakan yasanya ta murd’a handle din k’ofar suka shiga.
Kwance yake a bisa doguwar couch d’in dake girke a makeken d’akin hotel din, babu komi a jikin shi sai tawul dake daure a k’ugun sa, da’alama wanka ya fito, domin kuwa har wani k’ara fresh yayi da kyau, daka ganshi kaga asalin latest ango
“WTF, Hajiya lafiya, me kikazo yi nan”? ya fada a hasale bayan ya watsa wa halittar dake bayan ta kallon banza.
“Ungo nan,” ta jefa mashi dak’uwa.
“Ba dai kace babu wanda ya isa ya rabaka da otel d’innan ba? Toh shikenan babu mai raba ka da shi, amma hakan na nufin zaman ka a otel din zai cigaba da wanzuwa neh tare da matar ka a gefen ka, ina fatan kasan girma da darajar hak’k’in aure daga yau.”
Ta numfasa, “Idan kuma kagadama ka sanya kanta gabas ka yanke, sannan neh zan san kai asalin mara mutunci neh.” Gaka ga tanan”.
Daga haka ta juya ta fice, batare da ta kalli bangaren da ramlan ke mak’ure ba tana gabza kukan fitar hayyaci, lokaci guda itama, hawaye suka cigaba da rige rigen sauka bisa kuncin ta. 1
“Kiyi hak’uri ramlah” abinda ta rik’a ambata kenan har ta fice daga hotel din cike da kewa da tausayin d’iyar ta ta.
Shiru yayi fiye da mintuna biyar ba tare da ya iya furta wata kalma ba, kana daga bisani kamar an tsungule shi ya juya fuska tamkar hadari yace,
“Keh Zo nan don ubankii.”Jikin ta ne yaciga da b’ari kamar yanda ya saba, a duk lokacin da zata yi ido hud’u da yayan nasu.
“Karki bari inzo nan insameki” ya sake fad’a, yayin da yake k’ara yi mata kallon ‘This fool here is my wife’.
“Damn” Ya furta a can k’asan mak’oshin sa.
Tamkar wacce aka bige wa guiwowi haka ta rik’a taku a hankali tare da sabon bugun kirji a kowanne taku da takeyi zuwa gare shi.
“Allah dai ya sawwak’e, shegiyar yarinya ko kuzarin kirki bata da shi” ya ambaci hakan a zuciyar shi, lokaci guda kuma yana tunanin yanda sukayi da bilal.
Nesa dashi kadan ta zuk’unna, kana lokaci guda ta sadda kanta k’asa, kai da ka kalleta kasan kiris take jira ta fece da gudu.
Sai da ya ya b’ata lokaci wajen zuba mata kwandunan harara, wanda a zuciyar shi ji yake tamkar ya je ya shak’e ta, ko ya huta da zafin da take kunnawa zuciyar shi.
Sai da ya share mintuna sama da goma yana binta da kallo, a inda kallon ita kuma yazame mata tamkar wani salon azabar neh, sakamakon yanda idanuwan nashi ke nasarar huda dukkan ilahirin jikin ta.
Hawaye suka cigaba da gangarowa bisa kuncin ta, a lokaci guda kuma ta k’ara tsinkewa da al’amarin na safwan, domin kuwa yasan hanya kala-kala da zai iya gasaka cikin ruwan sanyi. Ita d’in shaida ce.
“Keh kazar mayu d’ago kanki ki kalle ni”
Gaban ta neh yacigaba da luguden bugu, domin kuwa tun shigowar smta dakin ta ke k’ok’arin ganin bata k’ara kallon shi ba, sakamakon yanayin da yake ciki,don kuwa a duk kafatanin rayuwar ta bata tab’a ganin balagaggen namiji babu suturar kirki ba, hasalima ko lokacin da yayi mata fyaden cikakkun kaya neh a jikin shi.
Ta runtse ido tamau, yayin da hawayen bak’in ciki keh cigaba da tsartuwa bisa ramammiyar fuskar ta.
“You must be very stupid,Uwar uban mi aka miki kike mani kuka? Na bige ki neh?” ya tambaye ta a ahasale, domin kuwa gab yake da mauje ta.
Da sauri ta girgiza kai tace “Ah ah, kayi hak’uri don Allah.”
Baisan lokacin da ya sanya k’afafun shi biyu ba ya janyota gaba d’ayan ta, hakan ya sanya ta bude bakin ta da niyyar sanya ihun ban hak’uri, sanin me hakan keh nufi a duk lokacin da ya zargota da k’afafun na shi. (Duka)
“Don Allah ya saf………
” Shhhhhhhhhhhhhhhhhhhh” Ya katse ta, ta hanyar sanya danyatsan shi bisa labb’an shi.
” Silent. “
Jin hakan ya sanya ta kama bakin ta tayi tsit, lokaci guda kuma jikin ta na cigaba da b’arin tsoro, ba shakka safwan bak’in mugu neh, kadan daga aikin shi neh ya jibgi abar banza.
“Look at me ramlah” Karo na farko da ya ambaci sunan ta tun bayan faruwar al’amuran da suka taimaka wajen yi wa rayuwar ta rubdugu.
Jin yanayin yanda ya ambaci kalaman ya sanya jikin ta saki k’alau, lokaci guda kuma wani sashe na zuciyar ta na son gasgata abinda kunnuwan nata ke jiye mata.
K’ara matso da ita yayi,hakan ya k’ara sanya kusanci tsakanin su, ba tar da b’ata lokaci ba ya sanya hannun shi ya d’ago da fuskar ta, wanda a lokaci guda idanuwan su suka gamu.
“Innalillahi” zuciyar ta tabuga da k’arfi sakamakon yanayin da ta ga safwan d’in. Gaba d’aya kuma sai taji wani sabon yanayi na ziyartar ta, wanda kwata kwata ta kasa fahimtar asalin ma’anar abin. 1
Zuru yayi mata da ido kamar bak’in maye, lokaci guda zuciyar shi na tseren gudu bisa allon k’irjin shi, tamkar yanda ya saba, a duk lokacin da zaiyi gigin had’a idanuwan shi da ita. “Babban dalilin da yasanya ya tsane ta kenan”.
“Tell me, keh mayya ce”? 9
A take kuma sai ta hangame baki cike da mamaki da tashin hankali, “Shin dama mutumin nan da gaske yake da yake danganta ta da kazar mayu?”.
Sabon haushin sa da bak’in ciki suka lullube zuciyar ta, hak’ik’a duk duniya babu mutumin da ya tsaneta sama da safwan.
“Answer me, pleaseeeeee.” 1
Ikon Allah, ai saikuma yadena bata haushi, yakoma bata tsoro da mamaki, “Please” a bakin safwan? Tunda uwar da ta haife ta, bata tab’a ji ba. 1
A firgice ta girgiza kai, kana ta ce “Kayi hak’uri ya safwan, wallahi ni ba mayya bace.” Ta fadi hakan da zallar gaskiyar ta, domin ita bata taba ji ko ganin inda wani yakira ta da mayya ba.
Ya lumshe idanuwan shi, kana lokaci guda kuma ya bude su gami da zuba su a kanta, Yanayin da yake ji a duk lokacin da zaiyi gigin kallon ta, ko kuma a duk lokacin da ta bayyana cikin baccin sa, hak’ik’a ko k’ur’ani zata had’iya bazai tab’a yarda da cewa ita d’in ba mayya bace. 2
Shekaru sama da goma sha uku tana bibiyar zuciyar shi. 6
“K’arya kike, keh mayya ceh, and a daren nan nake so kidena bibiyar rayuwata, for the first and last time, don Allah ramlah ki bar zuciya ta ta huta haka nan.” 4
“Yau na shiga uku, ya safwan kayi hak’uri, wallahi bansan abinda kake magana a kai ba, na tuba kayi hak’uri don Allah.” Muyar ta ta cigaba da karkarwa, domin kuwa wani sabon tsoron ahi neh daya ninka na da ke ratsa ilahirin jikin ta.
“Ba shakka, mammy ta kawo ta ga hallaka”
Nan take ya murtuke fuska tamkar talatainin dare, lokaci guda kuma ya sanya hannuwan shi ya shak’ota. 2
“Don ubanki ki dena bibiyar rayuwa ta hakanan, idan har ke ba mayya bace, menene kike bibiyar rayuwa ta haka? Duk inda naje sai kin bini, a cikin bacci ma ban tsira ba, tell me, me hakan ke nufi? Tell me kafin na yaga ki a gurin nan.” idanuwan shi sunkada sunyi jawur sabida tsananin masifar da yake ciki. Jikin ta babu inda baya rawa, lokaci guda kuma hawaye na cigaba da sakkowa daga kwarmin idanunta, yau take ganin babban tashin hankalin da ya kere wanda ta shiga a da.!
” Wallahi summa tallahi ni ba mayya bace, asalima ni bansan ya ake yin ta ba ya safwan, kaimani rai, don Allah ka yafemani” ta ambata muryar ta da sautin kuka. 1
K’afa ya sanya ya ture ta daga kanainaye tan da yayi, lokaci guda kuma ya dafe kanshi cike da azaba, ba shakka yarinyar nan ce ajalin shi. 2
“Nooooo!” ya furta hakan da k’arfi, lokaci guda kuma ya Mike ya nufi ma’ajiyar kayan shi, ya suturta jikin shi.
Cikin sauri yake daura agogo, tare da son ganin ya tsinci rayuwar shi cikin club, ba shakka wannan mayyar bata isa taga k’arshen shi ba. “Hajiya this is all your fault.”
Tana chan gefe a takure tana rusa kukan tashin hankali, ya sunkuci keys d’in motar shi ya yi hanyar fita.
Da saurinta ta mik’e ta biyo shi, tsoro bayyane a fuskar ta, “Yaya don Allah, karka tafi kabar ni ni kad’ai anan” ta fad’a hawaye shab’e shab’e bisa kyakkyawar fuskar ta da ta yi fayau sabida kuka.
Sai da ya watsa mata harara kana yace “Idan kin isa ki sanya siraran k’afafun nan naki ki biyo ni,anan neh zakisan asalin ko ni waye.” Daga haka ya sanya kai ya fice ya barta tsaye tana rusa kuka. 6
***
Naf club yayi wa tsinke, duk da club d’in baya d’aya daga cikin clubs d’in da yafi so, amma hakanan yau zuciyar shi ta zab’i da yaje chan.
VIP yayi booking kamar yanda ya saba a duk lokacin da zai raya daren shi a club.
Tunda ya zauna yake tuttula wa tumbin shi sigari, yau da’ace shi ma’abocin shan giya neh, toh hak’ik’a da yayi mata shan ala tsine uwar mai karya,amma duk da hakan tumbin na shi bai tsira ba, domin Chapman ya rik’a bulbula wa tumbin duk don ya sami sa’ida. 2
A hankali take takowa corner d’in da VIP’S keh zama, wanda kuma a lokaci guda tana cigaba da mamakin abinda ya kawo mainasaran naf club, sanin bai cika son zuwa club din ba kwata kwata, inba da kwak’waran dalili ba.
“Hello there” ta fad’a yayin da take samawa kanta mazauni a kujerar dake fuskantar shi, lokaci guda kuma tana cigaba da kashe shi da dak’walen idanuwan ta masu kama da na mashaya.
Banza yayi da ita, sanin wacece mamallakiyar muryar, hak’ik’a samira tunkiya ma ta fita aji, ya ambaci hakan a ranshi yayin da yake sake kunna karan sigari na goma sha biyu tun zaman shi a gurin.
“Mainasara magana fa nake” tayi karfin halin tambayar shi.
Sai da yaja wani dogon tsaki,gami da hura mata hayakin tabar bisa fuskar ta, kana daga bisani yace “Samira miyasa baki da hankali neh, so kike ki k’ara mani ciwon kai neh?” ya ida maganar yayin da yake tsareta da ido.
“I’m sorry, naga neh tun abinda ya faru jiya baka nemeni ba, at least ni akai wa laifi, yakamata abani hak’uri ko yaya neh.”
“Sabida kina uwata”? Ya katse ta.
Shiru tayi, domin kuwa gab take da fashewa da kuka, ba shakka safwan tsohon dan iska neh mara mutunci, amma ba laifin shi bane, don yaga she cannot do without him neh shiyasa yake yarfa ta son ranshi.Toh shi kenan, ni nace kayi hak’uri” Ta fad’a a shagwab’e.
Basar da ita yayi kamar beji mi tace ba, ganin hakan ya sanya ta komawa bisa couch din da yake ta shige jikin shi, sa’annan ta k’ara sanyaya murya tace, “Pls baby I’m sorry, bazan k’ara ba”. 2
Dama a matse yake, hakan yasa shi sanye hannayen shi gaba d’aya ya k’ara kusanto ta da jikin shi ya matse gam, lokaci guda yana mai shinshinar wuyan ta, tare da sauke wahalallaliyar ajiyar zuciya.
“I missed you” Ta rad’a mai a kunne, lokaci guda kuma ta sanya halshen ta cikin kunnuwan nashi tana tsotsa cike da k’warewa.
Wata wawura da yayi mata sai da tasanya ihun shagwab’a, hakan yasanya shi k’ara kaimi wajen kaiwa dukkan ilahirin jikinta zazzafar sumba, lokaci guda kuma yana maijin tamkar ya wanzar da ita a cikin club din.
Sanin yanda safwan din ya iya sarrafata bisa shimfida ya sanya ta mik’ewa gami da taimaka mashi domin su isa makwanci, “Hak’ik’a bata shirya zuba ihuu ba a gaban jama’ah.”
Bai iya driving ba sakamakon yanda jikin shi keh a mace, samirah has that effect on him, shuyasa yakasa fatattakar ta daga cikin rayuwar shi, wanda yasha gwada yin hakan, amma in sha Allahu sai sun sake dinkewa kamar mayu.
Tundaga wajen hawa step ya sungumeta bridal style, duk kuwa da k’iba irin ta samiran, amma tamkar ya sunkuci ramlah haka ya rik’a tsallake stairs bibbiyu suk don su isa makwancin da sauri. 3
Kwata kwata ya manta da wata aba wai ita ramlah, hakan yasa yana zuwa yasanya k’afa ya tura kofan, zaune take gaban gado ta takure, ko kayan dake jikin ta bata sauya ba, hakan zai tabbatar maka da tunda yatafi ya barta a haka, babu abinda ya sauya daga gare ta.
“Oh shiiiiittt” Ya furta hakan yayin da yayi idanu hud’u da ita, ba tare da ya sauke samiran ba yace.
“Keh kazar mayu get the hell out of here”. Daga haka bai kuma cewa komi ba ya nufi gado da samiran ya dire ta, ita kuma a lokacin take k’ok’arin tabbatar da abinda idanuwan ta ke ganan mata. 11
“Shin mi wannan shegiyan figagaggiyar yarinyan keyi masu a d’aki?” ta ambata a zuciyan ta yayin da take jin kamar taje ta shak’e y’ar banza kowa,ma ya huta.
Ganin da gaske safwan din na kwab’e kayan jikin shi ya sanya ta k’ara tsorata, “shin me mutumin nan yake nufi da ita neh?”
“Ya safwan, kayi hak’uri bansan inda zanje ba inna fita” ta fad’a muryar ta na rawa.
“Wannan matsalar ki ce, as you can see I’m about to get laid, inkuma zaki iya kallon yayanki, oh i mean mijin ki na sauke konji, then you are highly welcome.” 15
Daga haka bai kuma cewa komi ba, ya haye bisa k’aton gadon da ke dauke da samira a kwance tana jiran shi.
Toh amarya ramlah asuba ta gari. 😭