SAWUN BARAWO
CHAPTER 4
Bata jirayi yak’ara wata kalma ba, ta nufi hanyar ko’fa jiki a sanyaye, haka kuma wani sashe na zuciyar ta na ingizata ga wani abin daban. +
Bata Kara’sa ficewa ba daga dakin ta tsinci muryar shi yana cewa “Keh kazar mayu make sure you jam the door.”
Ilai kuwa tana Kara’sa ficewan ta janyo qofan tai musu jamming, take kuma a gurin ta rasa tudun dafawa, domin kuwa sam bata san inda zata dosa ba a cikin wannan daren, dad’in dad’awa a guri irin wannan da ba ruwan kowa da kowa, in short kowa na mahallin shi a gark’ame.
Da yake akwai d’an tazara tsakanin wannan d’aki zuwa wani d’akin, hakan ya sanya tasami wqni d’an passage da taga wata er resting chair a gurin, hakan yasa ta nemi guri ta zauna, diba da yanayi na sanyi da garin ke ciki ya taimaka wajen assasa jin sanyin ta.
Hakan ya sanya ta dage k’afafun ta sama, gami da had’e su guri guda ta takure, alokaci guda kuma tana k’ara jan k’aton farin mayafin kanta, domin ya rage mata jin sanyin. 1
Hawaye yacigaba da sauka daga cikin idanuwan ta, a lokaci guda kuma ta rik’a godewa Allah bisa irin wannan jarabtar da ya jarabeta da ita,Allah abin godiya.
Daga nesa take jiyo d’an hayaniya kadan kad’an, hakan yasa ta k’ara saurarawa domin tabbatar wa kanta abinda kunnuwan ta keh jiyo mata, ba shakka wannan kukan samirah neh, to amma lafiya lau ta baro su a d’akin, ko wani abu ne ya sami safwan d’in? Tarik’a jeri wa kanta tambayoyin.
“Raamlaaah!” Tajiyo muryar safwan din na k’walo mata kira, kasak’e tayi domin sake gasgata kunnuwan ta. 1
Takun tafiya ta jiyo ta wajejen da take, lokaci guda kuma tana jiyo muryar shi yana kwala kiran sunan ta, da’alamun tashin hankali a sautin muryar ta shi.
Had’a ido sukai daidai lokacin da ya k’araso inda take a takure, da hanzarin shi ya k’araso, ko kafin tayi wani yunk’uri yasanya hannayen shi gaba d’aya ya sunkuce ta, a inda al’amarin ya taimaka wajen shud’ewar wasu sakanni na tunanin ta.
Bai iya cewa komi ba har ya k’arasa da ita zuwa cikin d’akin nashi, wanda itama kanta mamaki ya hanata yin katab’us, a inda mamakin ta ya linku sakamakon ganin babu b’urb’ushin samira a d’akin.
Sai da ya dire ta bisa gado kama ya kwanta ta gefen ta a rgingine yana kallon silin, daga saa ta jiyo maganar shi cikin wani irin yanayi da bata tab’a ji ko gani ba a tare da shi.
“Kin tayar mani da hankali” ya furta a hankali ba tare da ya kalle ta ba. 2
Sai da ta waiwaiga cikin d’akin ko zata sami ikon gano samira, amma bata ga ko jakkar ta ba, hakan ke nufin da ita yake kenan?
“Me yasa kika tafi? Kinaso ki k’arasa kashe ni neh? Ta sake tsinkayaro muryar shi a karo na biyu, ba shakka da tana da iko, da ta tashi ta tsere daga d’akin nan, domin kuwa al’amuran sun zame mata wani banbarank’wai wai namiji da suna hajarah. 6
” Uhhhmmm talk to me please.” Ta sake tsinkayo shi a karo na uku.
Bakin ta na rawa tace “Kayi hak’uri don Allah”
“Karki k’ara yimani haka.” 2
“Amma kai kace in fita ai” Ta fad’a muryar ta da alamun sake yin kuka.
Sai da yayi tsaki, kana a hankali ya ce “I know, amma ba hakan ke nufin ki tafi ba, innemeki in rasa ba” 2
Ta cigaba da k’walalo ido ba tare da ta sake magana ba, domin kuwa al’amarin na nema ya girmi shekarun ta.
“Bazan yafewa kaina ba in wani abu ya sameki, ki kulah” wannan Karon da alamun warning a muryar shi. 2
Samun kanta tayi da gyad’a kai tamkar k’adangaruwa,lokaci guda kuma jikin ta na bata akwai wata a k’asa.
“Kinci abinci”? Ya cigaba da tambayan ta ba tare da ya kalleta bah. 6
Shiru tayi sakamon rasa abin cewa, yau take ganin sabon ikon Allah! Shin menene ya hau kan ya safwan?
“I said kinci abinci”? Ya daka mata tsawa, ba shiri tace “Ah ah banci ba, amma nak’oshi…….. “
“K’arya kike baki k’oshi ba” Yaa katse ta, lokaci guda kuma ya mik’e gami da janyo wayan land-line dake girke a kan durowan gefen gado.This is room 99″ Ya furta a hankali yayin da yake bin ramlan da kallo, a zuciyar shi kuma yana mamakin rashin nauyin ta, anyaa yarinyar na cin abinci kuwa? Ya tambayi kan shi. 3
Cikin en mintuna yayi musu list d’in abubda suke buk’ata, kana yayi hanging call din.
Gama wayar shi, yayi daidai da banko kofar da akayi, samira ce a furjajan, gashin nan duk ya mik’e tsaye tamkar sabon kamun hauka.
Gadan gadan ta nufi inda ramlan take, ko kafin yayi yunk’urin yin wani abu ta zuba mata mari, kana cikin zafin nama ta fizgota ta buga da k’asa, lokaci guda kuma ta nemi hayewa saman cikin ta.
“Wallahi nice ajalin yarinyar nan mainasara, ni mainasara, ni zaka wulak’anta akan wannan mai kama da muciyar? Ta cigaba da ambata rai a b’ace.
A sukwane ya iso inda samiran ke haye da ramlan, wanda a lokacin ramlan ma ko hawayen ta kasa tsabar firgita da azaba da take sha, ita kam yau take ganin bala’i iri iri.
“Keh samira are you out if your mind? Kina da hankali,? Zaki kashe musu yarinya neh? Ya furta cikin bacin rai yayin da yake fizgo samiran daga saman ruwan cikin ramlah.
A lokaci guda kuma ta cigaba da k’ok’arin fizgewa, asson ta koma taje ta jibgi ‘yan kayan ta.
“Dallah malam ka sake mani hannu, ashe ma kai k’ aramin d’an akuya neh, ashe ma burgar banza ce da ta wofi ake mana, wa billahillazil summa tallahi sai kasan ka wulak’anta ni akan wannan matar cushen taka, aikin banza ainkin wofi ma malam” 1
Ta cigaba da fizge fizge tana zuba ruwan tijara da bala’i, abin mamaki kuma safwan din kwata kwata beyi yunk’urin casa ta ba kamar yanda ya saba, hasalima lallab’ata ya cigaba da yi don son ganin ya bata hak’uri.
“Keh, keh samira listen to me, kinsan dai bakya bina bashin rantsuwa koh? To wallahi yarinyar nan is not behind abinda ya faru, ki yarda dani please” ya furta da alamun son ganin ya kwantar mata da hankali.
“Qarya kake mainasara, nace K’arya kake yasin, ni zaka maida y’ar iska mai shan taba ta k’eya?” Tasaki dariyar jin haushi, kana kuma ta d’ora da cewa….. 2
“Wallahi baka isa ka tozarta ni ba don kana ikirarin an d’aura maka aure da wannan mai kama da kazar mayun, wallahi sai ka k’arasa mani abinda ka fara ko zaka sami kwanciyar hankali eheee!”
Keh wace iriyar jarababbiyar tunkiya ce keh? Bakyajin uzuri neh? Ko baki da fahimta ne? , i told you nikaina bansan miyasame ni nakasa tab’uka komi ba, may be banda lafiya neh” Ya ida maganar cike da gajiya da halin na samira, ba shakka dole so take sai ta tona mashi asiri a gaban yarinya.
“Ina ruwana, wannan matsalar kace, nidai abin da nasani shine a biya mani buk’ata ta, tsabar baka da mutunci sai da komi yazo gangara zaka wani ce baka iyawa baka da lafiya? Tsabar iskanci da munafinci irin naka” Ta zak’ale ta rik’a rattafa ruwan masifa, tare da manta waye asalin Safwan mainasara. 1
Ya runtse idanun shi cike da jin sabon bacin rai na ziyar tar zuciyar shi, ba shakka samirah ta gama da shi, amma yanzun nan zai gwada mata kuskuren ta.
Daga haka baice komi ba ya nufi inda ramla.keh yashe a k’asa tanajin maganganun da suka girmi tunanin ta, toilet yaja hannayen ta ya saka ta, kana ya rufeta daga waje.
“Remove your filthy clothes right now” Ya fada muryar shi babu alamun wasa. Lokaci guda kuma ya fara kwabe belt din jeans d’in dake k’ugun sa, wanda dama wanon neh kad’ai a jikin shi. 6
Ganin hakan yasanya ta sakin murmushin samun nasara, daga haka ta salub’e shegiyar doguwar rigar dake jikin ta, ya rage daga ita sai pant da bra.
Tana k’okarin cire su ya dakatar da ita gami da cewa “Let me do the rest,” Hakan yasan yata nufo shi tana babbank’aro k’irji gaba,gamida kashe shi da idanuwa, ita a dole ga wacce taci ribar masifa. 5
Tana k’arasowa gaban shi ya sanya k’afar shi d’aya ya kwasheta ji kake, tiiiiiimmmm gardiya ta je k’as, ba tare kuma da b’ata lokaci ba ya janyo belt d’in da ya aje a gefe ya shiga kilar banzaaa.Ihuuu take tana k’arawa, lokaci guda kuma tana had’awa da ban hak’uri, idan bangon d’akin ya kula toh safwan ya kula, dukan tsiya,dukan kawo wuk’a yake mata.
“Don ubanki gobe zan k’ara yin magana ki tsaya kina maida mani, Ni sa’anki neh don uban da ya haifi uwarki shegiya er iska,nace ni sa’an kineh? Eyeeeh?” 3
Tana kuka tana ihu take bashi amsaa, “Wayyoo na shiga uku, wallahi na tuba safwan kai mani rai, wayyooo Allah naah” Ta kwaye baki ta rik’a kurma ihun neman dauki, wanda ko tari bata ji ba, Ballantana ta sanya ran a kawo mata d’auki.
Sai da yagaji don kanshi, kana ya ya rik’a ball da ita har zuwa bakin k’ofa, batare da ya damu da tsiraicin jikin ta ba, ya bude k’ofar gamida da sanya k’afa yai ball d’in karshe da ita zuwa waje, daga haka ya maida k’ofar ya datse bam yana huci.
Ramkah dake bayi Tarik’a sakin fitsari a wando, dominnkuwa har hango ta take gata nan tana amsar nata kason dukan, hakan ya sanya ta koma chan k’arshen bath ta boye, bakin ta kuma bai fasa ambaton “Allahumma ajirni fi musibati, wa akhkifni khairun minha” ba.
***
***
Yafi mintuna ashirin yana kwance tun bayan k’aramin exercise d’in da yayi a jikin samirah, a inda kwanciyar tashi tazame mashi wata hanya ta baje kolin tunanikan da suka addabi kwanyar shi. 1
Hak’ik’a shi kanshi mamakin yanda al’amuran suka juye haka yake yi, domin kuwan har yanzu yakasa gasgata abinda yafaru mintuna kadan da suka gabata.
Ya sauke wata kasalalliyar ajiyar zuciya, cike da son k’ara gasgata abinda zuciya da gangar jiki keh wanzar mashi.
“Shin mi hakan keh nufi”? Yacigaba da neman amsar da shi kanshi baya da ita. 1
Akwai k’amshin gaskiya cikin wasu zantukan na samira, wata zuciyar ta raya mashi, domin kuwa idan ba haka ba, mizai sa yakasa ida abin da ya fara, ma’ana how comes ma ya nemi dukkan kuzarin shi da sha’awar shi yarasa?
“Rashin kyautatawa, da kuma cin mutunchin aure da kake shirin yi” Wani sashe ya bashi amsa. 1
“Damn” ya furta a hankali, lokaci guda kuma yana mamakin yanda a yau kad’ai kalmar nan ta “Aure” ta keh nema ta wargaza duk wasu al’amura nashi. 1
“This is outrageous” ya furta yayin da yake shafo kwantacciyar sumar kanshi da ta sauko ta had’e da sajen shi mai matuk’ar kyawu da daukar hankali.
Fad’uwar wani abu a cikin toilet ya ankarar da shi gami da tuna mishi ramlan da ya datse a ciki, hakan yasa shi yayi hanzarin mik’ewa ya nufi toilet d’in. 1
Bud’e k’ofar bayin yayi daidai da sake sakin wani marayan kuka da ramlan tayi a hankali, domin kuwa da dukkan karfin ta ta sanya hannayenta wajen toshe bakin ta, a son karya jiyo sautin kukan bare kuma har ya gano ta. 1
Idanuwan shi yaciga da watsawa cikin fankacecen bayin mai kama da d’an madaidaicin sitting room, lokaci guda kuma yana mamakin inda yarinyar ta shige da har bai hangeta ba.
“Kazar Mayu where are you”? Ta tsinkayo muryarshi yana fad’e. 2
Sai da ta turo baki gaba, gami da jin sabon b’acin rai, domin kuwa duniya yanzu babu abinda ta tsana sama da sunan nan.
“Where the hell are you ramlah”? Wannan akaran a d’an zafafe yayi maganar.
Banza ta sake yi da shi, domin jikin ta yagama bata, matuk’ar sukai ido hud’u itama shirgarta zaiyi kamar Allah ya aiko shi.
Jin takun tafiyar shi yasa tak’ara lafewa gami da boyewa jikin bath din bayin, wanda ya kasance a gewaye cikin jacuzzi.
Ta mirror d’in dake manne jikin bangon bayin ya hango gyalenta ya lek’o, diba da yanda tai shiru gamida lafewa a gurin, ya tabbatar mashi da shi take b’oye mawa, hakan yasa ba tare da yin wani kyakkyawan motsi ba ya k’ara gurin gami da sungumarta gaba d’ayan ta.
Baki ta bud’e zata kurma ihu, hakan bai samu ba sakamakon had’e bakin sa da yayi da nata, wanda hakan ya sanya gaba d’aya notikan kanshi tsayawa chak! Lokaci guda kuma jikin shi gaba d’aya ya d’auki wasu jolts d’in vibration da bai tab’a ji ba tunda uwar data kawo shi duniya. 4
Hakan yasa ya dire ta gamida mannata jikin bangon bayin, yana mai k’ara wawurar bakin nata ya tsohon maye. Da’alama wannan ba safwan bane, domin kuwa wannan sabon safwan d’in gaba d’aya kallo guda zaka mashi ja hango tsananin obsession a tattare da irin rik’o da kuma sumba dayake wa bakin rablatun hajiya.Ido zare a waje, haka tarik’a mutsu-mutsu, al’amarin yazo mata a bazata, lokaci guda kuma wani sabon tsoron ya mamayeta, a take kuma jikin ta yacigaba da karkarwar tsoro, lokaci guda matsar da yayi mata a daren da yayi mata fyad’e yadawo kanta. 1
Tunanin hakan ya taimaka wajen sanya kukan da tayi, lokaci guda kuma tarik’a k’ok’arin hankad’eshi daga jikin ta, ba shakka bazata manta azabar datasha ba a hannun shi a wannan mugun daren, a inda tafi danganta azabar da yankan wuk’a. 1
Toh mutumin ku fa gaba d’aya nema yake ya fice daga dan sauran hankalin da yayi mashi saura, diba da yanda yake fidda numfashi daki daki, lokaci guda kuma yana nema ya cinye wa ‘yar mutane baki, hakan zai tabbatar maka da cewar hak’ik’a bai tab’a samun bakin da yatafi da ruhin shu ba irin wannan d’in. 4
Ganin ba shi da niyyar sakar mata baki ya sanya, tayi karfin halin sanya hannunta ta bayan shi da ya kasance ba riga ta manna mashi wani kyakkyawan tsunguli, wanda nafi zaton kamar harda fatar bayan nashi ma ta had’o diba da yanda gurin yayi jawur. 2
Bai bi takan abinda tayi mashin ba, wanda hakan ma gani nayi kamar yataimaka wajen k’ara assasa wutar sha’awarta dake nema ta kifar da shi a inda suke.
Da k’arfi ta chafki harshen shi ta ganna mashi wani azabebben cizo, wanda a take yanke ya sake ta gami da sauke kanshi da yayi bisa wuyan ta yana maida numfashi. 3
“Ba shakka yau ya tapka babban abin kunya” Wani sashe na zuciyar shi ya raya mashi, a yayin da d’ayan sashen ya dakatar da wancen sashen ta hanyar ce mashi “Kai share, ai matarka”. 4
Shi kan shi banbarank’wai kalmar tai masa a zuciya, lokaci guda kuma yaji wata iriyar kunya na neman rufto mashi, ba shakka ya siya wa kanshi raini, toh shi me ma yakaishi tab’a wannan k’wailar yarinyar.? 2
“Don Allah ni ka sake ni” Muryar ta ta dawo da shi daga wucin gadin da ya shiga, lokaci guda kuma yanemi nutsuwar shi ya rasa.
“So kike in sake kih”? Ya tambayeta ba tareda ya d’ago da kanshi daga wuyanta ba.
A hankali ta d’aga kai gamida cewa “Eh don Allah ka sake ni.”
Bugun zuciyar shi naeh ya k’aru, lokaci guda kuma sai yaji kamar wani tsoro na neman shigar shi, A take kuma ya tuna da hirar shi da bilal.
“Safwan, ko a mafarki bana yi maka fatan sakin ramlah, shin ina yarda da k’addarar ka yake,? Kadai sake wata shawarar amma banda batun saki.” Muryar bilal d’in tacigaba da yi mashi ihu a kunnuwan shi. 1
“Don Allah kasake ni, nagaji” Wannan karon cike da k’osawa tayi maganar, hakan yasa shi dago da kanshi yana mai tsura mata idanuwa, ba shakka yarinyar nan mayya ce. 1
“Idan na sake ki mezaki gayawa su hajiya”? Ya zura mata ido yana k’ara mamakin abubuwan da yarinyar keh sanya shi ji.
Fuska dauke da mamaki tace, “Ban fahimcekaba.??”
“Tunda baki fahimceni ba then forget.” ya furta yayin da yake sakin hannuwan ta gamida juyawa domin fita daga bayin.
Kallon mamaki tarik’q bin shi da shi, ahin wani irin baud’add’en mutumi neh wannan, ko yana tunanin da tace ya saketa, sakin aure take nufi? 1
” Ikon Allah” mutumin sai Carol’s wasu abubuwan kamar ba bahaushe ba, tq girirgiza kai cike da mamakin wannan sababbin halayyar ta safwan d’in.Wanke fuskar ta tayi, sa’annan ta fito, zaune tasame shi ya chanza kaya cikin wasu t-shirt da boxer mai adon kanfanin Louis voitton, lokaci guda kuma ya tasa abinci a gaba yana zubawa tumbin shi. Ba shakka tasan shi dama mutum neh maras wasa da cikin shi. +
Fuskar nan kamar hadari ya gangamo yace mata tazo ta dauki abincin ta, jiki a d’arare ta janyo plate d’in abincin ta rik’a tsakurah, ba shakka mutumin nan dak’yar inba ya had’a alak’a da jinnu ba, wannan irin bone fuska kamar tashin hankali. 2
Cikin en mintuna yagama cin abincin ya shige bayin, da’alama brush yayi, koda ya fito bai kalli inda take ba, ya nufi gadon shi gami da jan duvet d’in dake bisa gadon ya rufa, a take kuwa bacci yayi awon gaba dashi.
Asubar farko alarm d’in shi ya Tadashi, ga mamakin shi can ya tsince ta saman couch a makure tana bacci, duk da sanyin da ake makakawa haka ta kwanta babu bargo, sai mayafinta maras kauri ta lullube jikin ta dashi, a inda kallo d’aya zaka mata tabaka tausayi diba da yanda take a mak’ure sanyin a.c da sanyin gari suka taru suke cin k’aniyan ta.
Kawai sai yaji kamar tausayin ta ya tsirga mishi.
“Ko uban mi ya hanata hawa gadon oho.” 1
Samun kanshi yayi da tadata, “Heyyy, heyyy wake up.” A take kuwa ta bude idanuwanta gamida sauke su ana shi, a hanzarce ta tashi zaune, duk tunaninta wani laifin tayi.
“Keh me ya hanaki zuwa ki kwanta a can”? Ya nuna mata gado.
Cikin mamaki tace, “Kayi hak’uri naga kamar gadon yamana kad’an neh” ita knta tasan wannan uzurin nata beyi ba, diba da irin makeken gadon, wanda a kalla ba’a kasara ba yaci mutum hud’u manya lafiya lau.
Sai da ya balla mata harara kana ya daga girar shi guda sama yace “Oh really? Stupid nawa kike dazaki kalli gadon can kice yamana kad’an?” Yai tsaki kana ya juya ya nufi bayi, lokaci guda kuma yace “Ogarki samira ma bata isa tace wannan gadon yayi kad’an ba, Ballantana keh kazar mayu”. 4
Sai da tabi bayanshi da harara kana tace k’asa k’asa, “Oho nidai wallahi ba mayya bace”, Daga nan ta juya tacigaba da baccin ta ganin tafara fashin sallah a cikin daren.
***
“Wallahi samira ban tab’a ganin wawiya ba irinki, bariki hauka eh dazaki tsaya k’ato kullum ya rik’a jibgar ki kamr jaka?” wata kawar samiran da ta kawo mta dauki a daren na jiya da Safwan ya jibgeta.
Har yanzu takasa magana tun bayan faruwar al’amarin daya daguka dukkan lissafan ta.
” Wannan shine ga mari, ga tsinka jakka”.
Zuciyar ta tacigaba da wanzo mata mummunan hukuncin da ta gama yankewa a kan safwan din.
“Ba shakka daga kanta bazai k’ara d’aga hannu yadaki wata mace ba, zata shayar dashi ruwan mamaki!” Tai kwapa cike da son ganin gari ya waye taje ta ida mummunan nufin ta. 1
***
“Keh nabulaaa, nabulaaa? Yaki nan” ina ta kwallo wa nabila kira, yayin da take k’ok’arin shiga kicin. 4
“Ungo nan danno mani yaron kirki, inji ya suka kwana” Ta mik’a wa nabila waya da tayi kini kini da rai, sanin dama dalilin kiran da kakus d’in keh mata dama baya wuce akan yaron kirkin nata, inji ta.
Yana fara ringing ta mik’a wa innar ta juya tai wucewar ta abin ta, domin kuwa kad’an daga aikin inna neh yanzu ta tanb’aro mata wani aikin.
“Alo, Aloo yaron kirki kana jinah”?
“Sweetheart inajin ki, ya kika tashi”? Ya fad’a muryar shi dauke da alamun bacci.
Lafuya lau d’an albarka, ya inaa rablatun fa? Dafatan kabita a hankali koh? 2
Sai da ya yamutsa fuska, kana yace “Keh matsalata dake so jin gulma sweetheart.”
“Kai tafi chan, inbanji halin da yarinya take ba, me kake so inyi”? Tayi fici fici da ido kai kace yana gabanta neh.
“Pls sweetheart kibar ni inyi bacci, a gajiye nake wallahi , bansamu bacci ba sosai daren jiya.”
Aifa shi kenan, sai hajiya innah aka hau kyalkyala dariyar jin dad’i, harda su tafi, lokaci guda kuma tace “Dakyau yaron kirki, haka akeso ai, ince dai bakaji mata ciwo ba dai koh”? Ta cigaba da tambayar shi bil hakk’i da gaskia. 13
Tsaki yayi k’asa k’asa sabida haushin da innar ke neman bashi, hakan yasa ya mata gatse yace “Gata nan kwanche bata motsi,sabida faffarke ta danayi” 10
“La’ilaLa’ilahaillahu kai yaron kirki, amma kai dai anyi maras mutunci, yanzu baka tausaya wa siririyar yarinyar nan ba kabita a hankali ba…… Wannan ai zalin……” +
Bata idaba ya datse kiran, hakan yasa tarik’a “Aloh, aloooo yaron kirki kana jina?” jin babu alamun shi yasan ya tai wurgi da wayar, gamida nufar hanyar dakin hajiya tana sababi.
“Ina saratun? Keh saratu fito kiji aika aikar da maras mutuncin d’anki yayi, ohhh ni rakiya, yau nake ganin abinda yafi k’arfina.”
A dan firgice hajiya ta fito jin irin salallamin da innar ta nufo dakin tana yi.
“Lafiya innah miyafaru neh haka kuke ta salati”?
“Yoooh meye ma bai faru ba, eyeeee, ayii yaro shi sam bashi da hak’uri da mutunchi saboda Allah?”
“Inna kuyi mani bayani, wallahi duk hankali na yatashi.” Cewar hajiya cike da son jin minene keh faruwa.
“Waye ba yaron kirki ba, toh ai gashi nan abinda ake gudu yafaru, yanzu da bakin shi yace mani rablatun gata can kwance bata motsi sakamakon kaca-kacan da yayi mata.” 2
“Ya salam” hajiya ta dafe goshi cike da tararrabi.
***
Kikayi shiru kina dafe kai, ai tashi zakiyi mutafi in dubo halin da yarinyar mutane keh ciki,kai wannan yaro anyi dan banzaa ni ‘yasu!” Kaka keh fad’in hakan cike da tashin hankali mabayyani. +
Hajiyan bata ce komi ba yayin da take k’ok’arin juyawa takoma daki, hakan ya k’ara harzuk’a inna tace,”wai saratu ba magana nake ba, kikai shiru kika kyaleni?”
“Inna kuyi hak’uri waya zan d’auko inkira khalil yazo ya kaiku, ni kunsan ba binku zanyi ba.” 2
“Dama kyace haka mana, tunda danki yariga da yayi aika aika, ni yi maza ki kira mani khalilun yakaini indibo yarinyar mutane.” innar ta amshe cike da jin haushin hajiyar, takaicin ta d’aya da tace bazata bisu a dibo rablatun ba. 1
***
Wak’ar ‘Oyaah ooo’ ta olamide keh tashi da d’an k’arfi a cikin 406 d’in da khalil d’in ke tuk’awa, innah na bayan mota sai zabga sababi take akan khalil bashi da hankali, domin kuwa bayan volume da ya k’ure na motar, lokaci guda kuma yarik’a had’awa da rough driving duk don ya baiwa innar haushi sakamkon tadoshi da akayi yana baccin safen shi mai dad’i. 9
“Don ubanka idan kagadama katashi sama, sannan neh zansan baka da hankali, fitsarar……..
Bata k’arasaba ta saki ihuuu gamida sanya salati da iya k’arfinta, lokaci guda kuma sai ga inna na wuntsil wuntsil a tsakanin window da window, sakamon yanda khalil d’in yataka wani shegen break, lokaci guda kuma yatake shi gamida kwasar motar a dari da sittin. 5
Zo kuga innah yarda take zabga gumi, lokaci guda kuma ta rik’a kwashe mashi albarka, gaba d’aya ta tsorata sai zuba sababi take, domin kuwa duk wuyar nan datake sha bai sa bakinta ya mutu ba. 4
Ai suna shiga cikin harabar hotel d’in ta b’alle murfin motar tayo waje, zani a hannu, gyale a hannu, hakan yasa batayi kasa a guiwa ba da khalil d’in ya fito, ta sanya takalmanin k’afarta ta rik’a k’wala mashi, lokaci guda tana zuba mashi kwandunan zagi. 2
Sai da tagaji don kanta ta kyaleshi tana maida numfashi, sa’annan ta daura zaninta da gyalenta da suka salub’e.
“Inkin gama gyare gyaren sai ki wuce muje in kaiki, domin ni ba jiranki zanyi ba.”
“Kafirin maza, ai k’aryarka tasha k’arya kak’i jirana yaro, ko dayake ma yi tafiyar ka abinka, safwanu ya maido ni.” Tafad’i hakan sakamakon tunawa da bala’in daya sanya ta yanzun nan ba dad’ewa. 3
Reception suka isa, khalil din ya fad’i gurin wanda sukazo, hakan ya sanya aka kira wayan dakin domin a tabbatar da sanin wanda akazo gani d’in.
Cikin bacci yadauki wayar dake faman ringing a gefen shi, hakan yasa ranshi a b’ace yace “What?”
“Sir you have some visitors….” ya waiga ya kalli su kalil yace, “Sunan ku fa?” Da hanzari inna tace “Kai kace mashi kakar shi don masu garin su.”
Ko kafin mai kiran ya ida sak’on safwan d’in yace “Let them in.” kana ya katse wayar cike da mamakin abinda ya kawo kakus d’in, kardai gatsen da yayi mata neh ta hau kai ta zauna? Dariya yayi gami da girgiza kansh, lokaci guda kuma ya maida hankalin shi ta inda ramlan keh kwance tana zuba bacci hankalin ta kwance. 3
K’ura mata idanuwa yayi, inda kallon yafi ta’allaka bisa ‘dan bakin ta, data turo shi kadan cikin baccin,take sai yatuno da yanayin da ta sanya shi a jiya daya had’e bakin shi da nata duk a son ya katse mata ihun datake shirin sanya mashi.
Komi ya tuna ya tashi da sauri ya nufi inda take kwancen, batare da b’ata lokaci ba ya dauketa a hankali, ya shinfid’eta bisa gadon, lokaci guda kuma ya lallab’a ya rabata da mayafin dake kanta, hakan yataimaka wajen bayyanuwar tumulin gashinta da yake a tsefe kuma a d’an hargitse sakamakon ups and downs d’in data fuskanta tsakanin daren jiyan.Komawa yayi gefen ta ya kwanta gamida janyota jikin shi a hankali yanda bazata iya farkawa ba, sosai ya rab’ata da jikin shi, kana kuma ya sanya hannun shi dake tallabe da kanta yana shafa sumar tata. +
“Ga d’akin nan sai ki shiga, ni kinga tafiya ta.” Bai jirayi komi ba ya juya da sauri, don gudun had’war shi da yayan nashi, yasan k’arshen ta ranshi ya b’aci kafin su bar hotel d’in.
“Bam bam bam” Inna ta rik’a bugun k’ofar da iya k’arfin ta, lokaci guda kuma tarik’a k’wala wa safwan d’in kira.
“Kai yaron kirki, yarooon kirki don masu garinku zoka bud’e mani k’ofa, munafiki azzalumi.” Ta rik’a surfa mashi zagi.
Banza yayi da ita, yacigaba da dariya k’asa k’asa, lokaci guda kuma yana k’ara jinjina rashin kirki da hak’uri irin na kakar tashi.
Wani bugu da ta kaiwa k’ofar saida yayi sanadiyar farkawar ramlah a firgice tana zare ido, lokaci guda kuma ta zabura gami da mik’ewa zaune bisa gadon, fuskar ta bayyane da tsoro gamida mamakin yanda ta tsince ta bisa gado a maimakon kujera.
Ganin ta mik’e zaune yasa yabita da kallo, lokaci guda kuma yana mai watsa mata sak’onnin harara. 2
“Meye haka kikeyi?”
Shiru tayi gamida sunkuyar da kai k’asa, ganin haka yasanya shi mik’ewa ya nufi k’ofa, wanda a lokacin kakus ta riga tagama cika, fashewa kawai take shirin yi.
“Kaci ubanka nace yaron kirki, wani irin shegen bacci kuke haka nake ta bugun k’ofa babu wanda ya ji ni?”
Ba tare da tajirayi amsar shi ba tai shugewar ta cikin d’akin, lokaci guda tana surfa masu zagi, akan sun maidata ‘yar iska.
“Kai sweetheart kincika mita wallahi, abeg keep shut.” Cewar safwan bayan ya maida k’ofar ya rufe.
“Kai jaaa chan shashasha, gardi kamar ka baka tashi bacci ba,k’arfe tara na safe,ka dai ji kunya wallahi.”
Ramlah da tagama tsurewa a kan gado,ganin inna yak’ara tayar da hankalin ta, a tunanin ta wata tijarar tabiyo ta tai mata.
Hakan yasa da sauri ta mike da niyyar sakkowa daga bisa gadon, ba tareda lura ba ta bige da katakon gadon a ta wajen dugadugin k’afar ta, hakan yasa ta sanya k’ara a hankali, wanda safwan din neh kad’ai ya lura. 2
D’angyashi ta rik’a yi yayin da take k’ok’arin k’arasowa wajen inna da ke hakimce bisa kujera, bakinta yaqi shiru, tama manta abinda ya fito da ita daga gida, sai sababin anbarta a waje take yi.
Lura da yanda ramlan ta taho tana d’angyashi ya tuna mata musabbabin zuwan nata, hakan yasa bada b’ata lokaci ba ta chanza akalar fad’an nata.
“Yi a hankali kinji, oh ni rakkiya yau nake ganin abinda yafi k’arfina, sannu rablatu, sannu kinji,” ta rik’a jero mata sannu har ta k’arasa kusa da ita ta tsugunna domin gaisheta.
“Tashi tashi zo nan ki zauna kusa dani, ince dai jikin da sauk’i?”
Ita dai ramla ba tareda sanin abinda ke faruwa ba ta d’aga kai alamun ‘Eh’.
“Sannu kinji, tashi muje inyi maki wanka, nasan bakiniya yi da kanki koh?” 4
Dariya ta kusa sub’ucewa safwan dake gefe yana kallon su. Ba shakka babu wanda yakai inna b’aud’d’en hali, yanzun nan ta chanza daga wannan zuwa wanchan.
“Lah innah wallahi lafiya ta lau , zan iya wanka ai” ramlan ta bata amsa cike da mamakin dalilin innar nayi mata wadannan tambayoyin.
“Keh tafi can, so kike sai kowa yasan abinda keh damun ki? Na tabbata in aka barki kiyi wankan nan ke d’aya bazaki gasa kanki yanda yakamata ba, amma inni nayu miki tsaf zaki koma ki lik’e kamar da.”
Lokaci guda kuma ta waiga ta dubi safwan d’in dake tsaye jingine da bango yana kallon su.
” Bak’in mugu, idan kagama kallon namu sai ka tashi kaje kahad’a mani ruwan zafi a band’akin, kuma tafasashshe nake buk’ata, shashasha mara kan gado. ” ta ida zancen tana zuba mashi harara. 3
Bai jirayi ta k’ara wata kalma ba ya juya ya nufi toilet d’in yana dariya k’asa k’asa.The drama is getting awesome” ya furta yayin dayake kunna water heater d’in bayin. +
Ramlah dai tai tsiru tana jin ikon Allah, toh ita miyasameta daza’a ce za a yi mata wanka? Al’amarin daya kasa daina d’aure mata kai.
“Tashi ki tub’e kayan ki mazaa, nasan jikin ki ba k’aramin tsami yayi ba.” 2
Sanin masifar ta innah yasata mik’ewa domin yin abinda tace d’in.
Mikewar tata yayi daidai da saukar idanun innah bisa mazaunen ramlan ta k’asa da tayi staining sakamakon fashin sallah da take, kuma ikon Allah sosai tayi staining d’in,sa’anan kasantuwar material neh a jikin ta mai kalar haske ya taimaka wajen bayyanuwar jinin sosai b’aro b’aro.
Ai atake inna tahau salati tana sanar da ubangiji da iya k’arfin ta, wanda hakan yayi daidai da fitowar safwan daga toilet d’in.
“Tsakani da Allah yaron kirki ban k’ara tabbatar da rashin imaninka ba sai yau, sabida Allah diba kaga irin rashin imanin daka gwada akan yarinyar nan.” Ta rik’e hab’a tana mitsi mitsi da ido.
Da sauri ramlan ta rik’a bin jikinta da kallo, domin gano mai innan keh bala’i akai,lokaci guda kuma ta k’ara shiga rud’ani sakamakon fara fahimto abinda innar keh nufi.
Hakan yasa ta juyo da sauri tace wa innar “Inna wallahi ni lafiya ta k’alau, babu abinda yayi mani.” Ta ida zancen tana mai kallon safwan d’in, wanda shima kallon nata yake cike da wani irin gingimemen yanayi a tare da kallon nashi.
“Keh jaaa caan,inaso ana so a gyara ki, kina neman kawo mani k’auli da ba’adi, ki tsaya kina kallon shi yakaiki ya baro.”
“Innah wallahi wannan abinma da kuke gani ma fashin s…..”
“La’ilahaillahu….” innar ta katse ta yayin da take tafa hannu,Kana kuma ta cigaba.
“Yau ga shegiar mata, idan wankan neh bakyaso inyi maki ai basai kin doka wannan shegiyar k’aryar ba.” 1
Ta juya ta dubi safwan d’in gami da cewa “Tunda kai kayi b’arnar saika wuce kaje kayi mata wankan, tunda ni bata son nawa.”
Ai bata san lokacin da ta kwasa a guje ba ta nufi innar tana bata hak’uri.
“Keh don ubanki kibi a hankali, ko so kike ki k’arasa yagewar? Wannan gudu dakike kamar ba mara lafiya ba?” innar ta riketa duk don wai kar ta fama raunin ta. 6
Hawaye tafarayi da iya gaskiyar ta, gami da ba innar hak’uri akan ta barta tayi wankan ta da kanta zata iya.
” Qaryarki kuma yarinya, wallahi sai dai ki zab’a ko ni ko mijin ki, don ban yarda kiyi da kanki ba, haka kurum ki rub’e mana mu shiga uku.”
Shiru ramlan tayi tana nean mafita, ita kam bata jin zata zab’i ko da’ya, shin ta yaya a zata tsaya babba da ita ana mata wanka, rashin sanin abin yi yasanya hawaye fara tsartuwa bisa fuskar ta, lokaci guda tana mai jin tamkar ta sanya ihu ko zata huta da wannan sabon bala’in dake neman kunno mata.
“Kai yaron kirki shige kayi mata wankan nan, naga alama har yanzu yarinyar nan bata san ciwon kanta ba.”
Ai tanajin haka ta kwasa a guje tayi cikin bayin gami da banko k’ofar tasanya key.
Kallo yabi bayin ta dashi, yana son yin dariya ganin yanda innah ta dafe kai tana jin tamkar ciwon a jikin ta yake.
“Anya yaron kirki baka sabauta yarinyar nan ba?”
Hak’ura yayi ya saki dariyar dake nuku’rk’usar shi tun d’az,kana lokaci guda yace “Sweetheart sau nawa zangaya maki cewa mace irin ramlah bata cikin irin kalar matan danakeso ballantana, har sukai ga burge ni.?” yai tsaki gami da d’orawa da,
“Common yaaawaah kike wallahi”
Tsaki tayi gami da cewa “Aikin banza, wazakai wa borin kunya bak’in munahuki.” ta dauke kanta cike da jin haushin yara na neman raina mata wayau.
Mik’ewa tayi ta nufi bakin k’ofar bayin ta bude.murya yanda ramlan zata iya jiyo ta, kana tace “Fitsararriya ki tabbatar da kin gasa gurin nan da kyau, inbahaka wallahi kece a ciki.” 2
Banza tayi da innar tacigaba da wankan ta lokaci guda kuma tarik’a hararar k’ofar toilet d’in.
“Wannan matar bata yi ba wallahi.”
Chan kuma kamar daga sama tajiyo innar na cewa, “Ni tsakani da Allah ma yaron kirki bawai na yadda da kai bane,tafiya zanyi da ita har sai ta warke kazo ka d’auke ta daga baya.”
“Kun rufawa kanku asiri.” Safwan d’in ya fad’a cikin halin ko in kula, sai ma yataya innar fad’a wa ramlan yandda zata iya jiyo shi.
“Kazar mayu hurry up and get the hell out of here.”
Sabida tsakani da Allah dama ta tsare mashi gaba, ta hana shi nutsuwa, k’ila in bata nan nutsuwar shi ta dawo.Horn guda yayi a daidai isowar su gidan nasu, inna dake bayan mota tana ta rattaba zance har suka iso babu mai kulata, gara gara ma ramlah takan amsa da ‘eh’ ko ‘ah ah’. +
Shigar su parking lots d’in yayi daidai da lura da wata fara k’al d’in Lamborghini da safwan yayi, lokaci guda kuma yana mamakin wani bako mutanen gidan sukayi, sabida dai babu mai irin motar a dukkan gidan. 1
Fitowar ta ramlah yayi daidai da b’ullowar wani sangirin ingarman saurayi,kyakkyawa neh sosai, haka zalika diba guda zakai mashi ka hango zallar kamala da kamewa bisa baqar kyakkyawar fuskar shi. 3
Ai da gudu ramlah ta saki murfin kofar motar ta safwan ta ranta a nakare ta nufi mutumin tana ihun murna, daga dukkan alamu ba k’aramin jin dad’in ganin mutumin tayi ba. 1
“Keh don ubanki kibi a hankali, yau ga y’ar banzar yarinya maras kan gado.” cewar inna yayin da take dafe kai, gami da tararrabin ciwon dake jikin rablatun. 4
Ko kafin kace mene ta mak’alk’aleshi tana tsallen murna. Wanda shima a take ya sanya hannayen shi ya d’agata sama yana k’yalk’yala dariyar sake ganin y’ar k’anwar tashi a bangare guda kuma wata jigo daga cikin jigogin rayuwar shi. 2
“Yaa Talib” Ta ambaci sunan shi cikin matsanancin farin cikin sake ganin shi, a karo na barkatai na rayuwar ta, haka zalika muryar ta dauke take da zallar jin dadi da annushuwa da zai k’ara tabbatar maka da jin dadin ganin nasa a yau din. 4
“Baby am.” Sassanyar muryar shi ma’abociyar taushi da dadi ta furta sunan da shi kad’ai neh ma’abocin kiranta da hakan. 1
“I missed you.” Ta fada muryar ta na dan rawa, lokaci guda kuma tana sake lafewa a faffadan kirjin sa, wanda hakan ya taimaka wajen shako wani daddadan turaren da bazata tab’a mantawa da shi ba a kaf rayuwar ta, ta nan gaba in Allahu ya nufa. 2
Ko kafin ya bata amsa ta d’ago da sauri tana mai son k’ara gasgata kamshin turaren, hakan ya taimaka wajen tariyo mata wannan bak’in daren da shafin k’addararta ya bud’o mata. 4
“No may be irin turaren neh” Wani sashe na zuciyar ta yayi azamar tuna mata, domin kuwa wannan mutum dake tsaye a gaban ta, shine mutum na uku a duk duniyar nan mafi soyuwa a gareta. 2
“Heyy baby am” ya hure mata idanuwa, sakamakon halin fita hayyaci ta hanyar tunani daya fahimci ya tafi da ita.
“What is wrong, tunanin me kike?”
“Uhmmm nothing ya talib.” Ta bashi amsa a yayun da take sakaya fuskar ta da murmushin ganin shi.
“Good girl, kinsan na hanaki tunani anyhow right?” Ya dage girar shi guda yana kare mata kallo.
“I know ya taleeb, kayi hak’uri kaji.?”
“Anything for my fav gurl.” Ya bata amsa yayin da yake ruko hannayen ta gaba daya cikin nashi, lokaci guda kuma zuciyar shi na tseren gudu bisa allon kirjin sa, ba shakka yayi missing yarinyar nan. 6
Basu ji takun tafiyar shi ba,illa deep husky voice din shi dake razana zukatan yammata,amma wannan karon muryar dauke take da wani irin sauti mai nuni da zallar bacin rai.
“Well, hello Mr Abu Taleeb,idan kagama rungumar mani mata can i have her now?” 11
Da sauri ta dago kanta gami da sauke kwayar idanuwan ta cikin nashi, wanda a take yanke tayi gaggawar janye su gami da hanzarin yin baya daga kusanci dake tsakanin ta Abu Taleeb din.
Har ga Allah ita tama manta da wani safwan. 1
” Idan kagama rungumar mani mata, can i have her now?”
Kalamaen suka cigaba da yi mashi kururuwa cikin sako da lungu na kunnuwan shi, lokaci guda kuma yana k’ok’arin karyata abinda kunnuwan nashi suka jiyo daga bakin mutumin da yafi tsana kaf rayuwar sh. 1
” Well i hope you are not mistaken Mr Safwan Mainasara,? Because this girl right in front of me is no one else, but Ramlah Tafeeda.”
Ya ida zancen a yayin da yake maida kallon shi bisa kyakkyawar fuskar ta ramlah, lokaci guda kuma wani murmushin da shi kanshi ba zaice ga dalilin yin shiba na subuce mashi.
Dariyar da bai shirya fitowar ta ba ta subuce mashi, hakan yasanya lokaci guda ya maida kallon shi bisa ramlan da kanta keh sunkuye, ba tare da sake wani tunanin ba a karo na biyu ya mika mata hannun shi guda gami da cewa….
“Shall we.?” +
Sabida har ga Allah bashi da lokacin tsayawa baiwa taleeb d’in amsa, amma yana tsammanin hqkan da zaiyi, zaiyi matuk’ar taimakawa wajen fahimtar da shi amsoshin sa.
Jiki a salube ta mik’a nata hannun, lokaci guda jiki da ruhinta na jin kamar bata kyauta ba, hak’ik’a yaa talib ya kasance wani bangare na rayuwar ta.
Hannayen nasu yaciga da bi da kallo, wanda a lokaci guda kuma batare da ya dawo daga wannan mamakin ba ya qara lulawa cikin wani, sakamakon yanda safwan din ya mannata a gefen kafadun shi da suka shallake kanta sabida tazarar tsayin su. 2
Kallon su yacigaba da yi har suka shige cikin main entrance d’in kofar falon gidan, wanda a lokaci guda kuma Waiwayowar da ramlan keyi idanuwan ta dauke da boyayyen al’amari ya taimaka wajen kara dagula sauran lissafin shi.
“Shin me hakan keh nufi?”
Ya tambayi kanshi, ba tareda nasarar samo amsoshin su ba, yabi bayan su, zuciyar shi dauke da tarin hargitsi gami da mashahuran tambayoyi cike da kwakwalwar sa.
***
Isowar su falob yayi daidai da wurgi da yayi da ita cikin tsakiyar falon, hakan yasa ta tafi da karfi ta bugi gefen kujerar three sitter dake chan tsakiyar katafaren falon. 1
Lokaci guda tasaki k’ara, wanda keh nuni da zafin buguwar da tayi, ta wani bangare kuma,gabanta yaciga da luguden bugu sakamakon gainin yanda safwan d’in ya juye yadawo mata asalin safwan din da ta sani a da.!
Wannan mugun safwan din.
“Ai bantaba sanin dabbancin ki yakai haka ba.”
Ya sami guri ya zauna gamida fuskantar ta,fuskar nan a tamke kamar hadari, domin kuwa har wani ja ja ja takeyi sabida bacin rai.
Sake lafewa tayi a gurin jikinta na b’ari, lokaci guda kuma ta rik’a addu’ar samun dauki daga koma waye. 1
“Get your small ass over here nonsense.” 5
Ya daka mata tsawar da tasa ta rarrafo da sauri kusa da shi, bakinta dauke da addu’ar neman tsira daga lillahi.
“Ubanwa yace ki rungume shi, don ubanki kinmanta matsayin ki neh a yanzu.?” Ya zaro mata idanuwan shi da suka gama rinewa da b’acin rai.
“Ka…. Kayi… Kayii Hak’uri don Allah.”
Ta fada muryarta dauke da sautin in’ina, wqnda hakan keh nuni da tsurewa da tayi, domin kuwa hak’ik’a bata shirya cin najaki ba a yau din.
Hannu yasa yabige bakin dake bashi hak’urin, lokaci guda kuma ya rik’a surfa mata ruwan masifa tamkar zai mammake ta. 1
Ikon Allah kuma babu mahalukin da ya biyo ta falon bare tay tunanin samun dauki.
Kanta sunkuye, bata jiyo tafiyar shi ba, sai dai kamshin turaren nan da tunda ta shake shi yake sanya mata faduwar gaba. 1
Zama yayi a kujerar dake fuskantar ta safwan din ba tare da yace musu uffan ba, saima dora kafa kan daya da yayi yana kare masu kallo.
Ganin talib din a falon yasa yadakata da fadan dayakeyi, wanda shi kanshi ya rasa dalilin da yasa yakejin b’acin ran da bai taba tsammanin jin irin sa ba, kila hakan nada nasaba da abi ya faru ne sakamakon ganin mutumin da yafi tsana kaf rayuwar shi. 1
Hak’ik’a Abu talib yadade da son yi mashi karan tsaye a duniyar shi,amma zaiyi maganin shi for real.
Sai yanzu ta samu kukan ya subuce mata ganin Abu talib d’in a gaban ta, hakan yasa tacigaba da kallon shi tana hawaye, lokaci guda ta rik’a fatan mammy ta fito domin ceto ta daga wannan yanayin da take ciki.
Janyo ta yayi jikin shi gaba d’ayan ta da niyyar ganin yacigaba da kuntatawa mutumin dake zaune yana kallon su, sanin babu abinda keh matuk’ar kunna shi irin abinda yake shirin yi.Keep shut, and hold your mouth.” Ya umarceta yayin da yake nutsa idanuwan shi cikin nata idanuwan da suka k’walalo waje sabida kukan da takeyi. +
Ba tare da musu ba tayi tsit tamkar ruwa ya cinyeta, lokaci guda kuma ta kama bakinta ta ri’ke da dayan hannun nata. 3
Mamaki yacigaba da kashe abu talib d’in a inda yake zaune, lokaci guda kuma ya rik’a fatan bayyanuwar hajiyar cikin falon, sanin ita kad’ai ka iya bashi dukkan amsoshin tambayoyin shi. 2
Kallaon su yacigaba da yi, haka nan kuma zuciyar shi bata fasa tseren doki ba bisa allon kirjin shi.
“Ya Allah kasa ba abinda nake tunanin bane.”
Zuciyar shi ta ambata a can kasan ranshi.
“Oh ni duniya, inbaka mutu ba kasha kallo!” 1
Dukkan su suka tsinkayi muryar kakus tana nufo falon, lokaci guda kuma tana tapa hannuwa duk sakamakon ganin ramlah da tayi zaune share share bisa cinyar safwan, lokaci guda kuma tana mamakin yanda takama baki ta rike, yayin da shi kuma yake bjn fuskar ta da kallo ya tsohon maye. 3
“Yanzu kai yaron kirki a cikin gidan ma bazaka sarara wa yarinya ba? jibi yanda ka nanike ta ka aza bisa cinya kamar wata mage, ko kunyar idanun jama’ah baka ji.? ” Ta rike hab’a alamun mamaki.
Kiciniyar sauka ramlan ta farayi amman yasanya hannunya maidata, wannan karon gaba dayanta ya rungume, ya manne ta gamida cusa ta cikin can tsakiyar kirjin shi, kana ba tareda ya damu da kallon hadarin kajin da bakon nasu ke mashi ba yakama hannayen ta gaba daya ya kwak’ume. 1
“La’ilahaillahu yau ga dan iskan yaro,maidata ciki kake shirin yi neh yaron kirki? Jibi yanda kabi ka kwak’ume masu yarinya kamar kasamu katifa” 3
Baibi takan surutun innah ba ya soma kici kicin tura fuskar shi cikin wuyanta da yakasance babu mayafi, sakamaon zamewa da mayafin yayi daga kanta. 8
Muryar ta na rawa tace” Don Allah yaa safwan kabari,Natuba.” domin kuwa gaba d’aya al’amarin nashi nema yake ya girmi tunanin ta.
” Keep still” Ya furta daga can kasan makoshin sa, domin kuwa ita kanta saida tayi da gaske tasami ikon jiyo abinda yace dun.
Jitayi gaba daya gashin jikinta sun mimmike sakamakon yanda ya furta maganar a can karkashin wuyanta,a lokaci guda kuma yana k’ara dannata a kirjin shi, tamkar mai shirin sanyata ciki.
Idanuwan shi dama sun dade da canza launi, hakan yasa ko da yaji muryar inna a kusa kusa dashi bai d’ago kan shi ba. 1
“Wallahi yaron kirki idan baka sakar masu yarinyar mutane ba yanzun nan zan tara maka jam’ah, yau nake ganin jaraba da rana tsaka.”
Ganin baimasan tanayi ba yasanya ta juyawa wajen Talib dake zaune can baice musu ci kanku ba, illah yanayin shi da gaba daya ya jirkice yakoma wani abin tsoro, zuciyar shi kuma tana cigaba da bugawa fat fat fat.
” Dukkan alamomi sun nuna cewa safwan has win over him.”
Take yaji wani ciwon kai na barazana da rayuwar shi, hakan yasa ya runtse idanuwan shi da karfi, gamida fatan Allah yasa mafarki yake ya farka.
Inna da ta juyo da nufin Taleeb d’in yakawo mata dauki ai sai tai saranda gamida kama baki tana maiyin galala da ido, hanci da baki tana kallon yanda hawaye keh tsere bisa kuncin sa. 2
“Yau anshiga uku, kai D’alibii lafiyan ka, kake hawaye haka? Ikon lillahi!” 5
Kakus tacigaba da salallami cike da mamaki mabayyani, domin kuwa har ta ma manta da bad’alar da safwan keyi a can gefe, diba da yanda taka ingarman namiji irin Talib d’in ke kwararar da hawaye kamar anbude pampo.
Zama tayi dabas bisa kujera tana k’ara hangame baki gamida kallon ikon Allah.
“Toh shi kuma wannan halan ciwon farfadiya gare shi?” Tacigaba da tambayar kanta.
Ramlah da hankalin ta yagama tashi ganin yanda hawaye keh surfafowa daga rufaffun idanuwan yaa abu talib d’in ya taimaka wajen assasa nata kukan, dadin dadawa yanda safwan din ya cumuimiyeta ya hanata koda motsin kirki neh. 2
“Allah kakawo mani dauki.” Ta ayyana hakan a ranta, lokaci guda tana mai sake fashewa da kukan rashin sanin abin yi.
Kafin kace me, inna ta fice da saurin ta zani ahannu ta doshi kofar da zata sadaka da dakin hajiyar, lokaci guda kuma ta rik’a surfafo mata kira tana ccewa…. 4
“Saratu? Keh saratu kina ina? Yau nake ganin abunda yafi karfina!”
Tsakanin ta da Allah a rude take. 5
***