SAWUN BARAWO CHAPTER 6

SAWUN BARAWO 





CHAPTER 6





Cikin awannin da basu shige biyu ba yagama clearing komi na hotel din, kana suka rankaya gidan dayazama mallakar shi neh cikin gadon shi da mahaifin su yabari.

Gida neh madaidaici mai matuk’ar tsari, wanda yake kunshe da madaidaitan falo guda biyu, sai dakunan bacci guda uku kowanne dauke da toilets, sai kuma dangin su kitchen, store, dining area da kuma dakin bak’i.

Yanayin tsaruwar gidan neh kad’ai abinda ya birge ramlan har taji tana dan bukatar sanya hakarkarin ta bisa shiryayyen dakin baccin data ke tunanin nan neh nata, ganin yanda tun shigowar su gidan, safwan din ya shiga dayan dakin na can dake k’arshe.

Dayake dama anriga da an shirya komi a cikin gidan, hakan yasa bata wani samu matsala ba wajen shiga toilet domin ta watsa ruwa, dama tunda maigadi ya shigo masu da akwatinan su falo ta janyo nata ta shigo dashi dakin.

Bayan gama wankan nata neh, ta had’a da d’aura alwalar sallar azahar, duk kuwa da cewa kusan la’asar ma na gaf da yi, amma rashin zama baisa tasamu ta gabatar ba. 2

Bata bata lokaci ba wajen shafe shafe, bayan d’an lotion kadan data mutsuka wa jikin tane, ta had’a da sanya roll on da sauran sprays masu sanyin kamshin dadi. 2

A gurguje ta shirya cikin wata doguwar armless riga fara, wacce ta kasance cotton mai dan karen laushi, hakan yasa ta zumbula zumbulelen hijabi ta fusaknci alqibla domin gabatar da sallolin ta. 1

Bayan idar da sallolin nata neh ta dan bata lokaci gurin yin addu’o’i, da gamawarta kuwa ta ninke kayan sallan ta,kana a take tai sufa ta dare gadon ta da yasha lallausan shimfida.

Lumshe idanuwan ta tayi, lokaci guda tanajin wani nishadi na ziyartar zuciyar ta tamkar bata da sauran damuwa a duniya, lallaikam babu abinda yafi aure ta wani fannin dadi, mussamman idan ka waiga ko ina kaga komi fa dake gidan mallakin kane…. Madallah da wannan daraja ta aure

Batare da sanintaba wani shahararren bacci ya lallabo yai gaba da ita, wanda kallo guda zakayi mata kasan ba karamin dadin baccin takeji ba, diba da yanda tai daidai tasaki jikin ta, ta rik’a kwasar baccin ta hankali kwance, batare da ta tuna ma da wani abu wai shi safwan ba a gidan

Ta bangaren safwan d’in ma dai kusan ma iya cewa hakance tafaru dashi, bacci sosai neh yasami damar kwasar shi, hakan yasa shima ya manta da dukkan wasu al’amura na damuwa, ya maye su da sharholiyar baccin sa mai shegen dadi.

A inda baccin ba karamin daukar su yayi ba, domin kuwa ta sashen ramlah kiran wayar ta neh, yataimaka wajen katse baccin nata.

Cikin kasala irin ta mai bacci ta lalubi wayar domin son ganin wake kiran nata.

Sunan nabila ta gani a kan screen d’in.

Da d’an hanzari ta dauka gami dacewa, “Ni nayi fushi, habawa nabila sai yanzu zaki neme ni?”

Katseta nabilan tayi tana mai bata hak’uri, kana kuma ta k’ara da cewar ai itakam space ta basu suci soyayyan su da yaa damisa, ta ida maganar tana dariya

“Koba soyayya ba, wallahi nabila ki fita daga idanuna tun muna mu biyu.” Ta bata amsa a kufule.

Idan banda iskanci nabila, harma wata soyayya take hango mata a gidan nan? Tabbb gaibu kenan.

“Munafinci….” nabilan ta cafe, kana ta cigaba.

“Ai nagama jin komi a baki kakus, kike nema ki maida ni wata sauna, bayan angama shan mintin soyayya da yaya damisa.” 1

Tunda ta fara maganar ramlan keh hararar wayar, wanda sai ka rantse da Allah gaban nabilan take, lokaci guda takaicin abinda innar tai mata a dazun yak’ara dawo mata, hakan yasa ta bud’e mak’oshi ta hau zubo ruwan masifa da iya qarfin ta.

” Ai wallahi kibar innar nan,na rantse da Allah inkinsan haushin da ta bani dazu koh? Hmmm Allah neh kurum zai saka mani.”

Dariya kurum nabilan keh kwasa abinta, domin kuwa ita gani take duk borin kunya ramlan keyi, bayan ta riga tabada kai bori ya hau.

” Kedai fadi gaskia yarinya. ” Nabilan ta fada cikin dariya.

Ganin dagaske dai nabilan ba kama zancenta take ba yasa tace… “Amman gaskia nabila kinbani ma dariya, kina tunanin akwai wani abu da zai shyga tsakanin na da yaya safwan bayan duk cin mutuncin shi a gareni? Haba nabila, ta yaya kike tsammanin zan yadda da mutumin daya yaga mani rigar mutunci farat d’aya haka? Allah yakyauta har abada wallahi. +

Ta karasa maganar tare da sabon bacin ran dake barazanar faso kirjin ta, hak’ik’a bazata tab’a yafewa ya safwan ba, koda kuwa abu na k’arshe kenan dazatayi a doron kasa.

Cikin sanyi murya nabilan tace” Hakane ramlah, amma don Allah kiyi hak’uri mana ki manta komi, tunda mai hadawa tariga da ta had’a ku, ki tuna aure fa ba wasa bane? “

“Mtsw kinga kina b’ata mani lokaci, idan kinsan irin maganganun dazaki rik’a manu kenan inkin kirani, don Allah ki rike gaisuwar ki bana bukata, aikin banza aikin wofi, kuma na rantse da Allah koda wa yake yawo sai ya sakeni.”

Nabilan zata sake wata maganar ta datse kiran tana hucin bacin rai, lallaima nabilan nan, wato ita mai dan uwa har ta manta abubuwan dayayi mata a rayuwar ta?

Kwafa tayi cike da takaici, kana ta juyo domin sakkowa daga gadon taje tai alwalar sallar magariba.

Ido hud’u sukayi yana tsaye jingine da kyauren dakin, hannayen shi bisa kirjin shi yana kare mata kallo.

Kallo guda ta mishi, tai hanzarin dauke nata kan gabanta na tsananta bugu, diba da irin mugayen kallon dayake watso mata yabata tabbacin yaji dukkan abinda ta tattauna da nabila a waya yanzun.

Gaggawar sauke kanta kasa tayi tana gunguni a hankali, domin kuwa ta riga ta rantse da da yanzu ba d’aya bane, domin kuwa sam bazata k’ara daukar cin kashin dayai mata a baya ba, bayan ayanzun tana da tabbacin akwai mai daure mata gindin iya shegen ta.

Bataji sautin tafiyar shi, sai dai ta hangi takalmin wankan dake kafarshi a kusa da ita, hakan yasa ta k’ara danna kanta k’asa tana cigaba da gunguni a hankali.

“Keh kazar mayu dago mani kanki nan.” Ta tsinkayi muryarshi yana mai bata umarni.

Banza tai dashi gamida k’ara dauke kanta, dukkuwa da cewa gabanta bai daina faduwa ba, domin tafi dan dakon tasha sanin yanzun nan tsab sai yaci mata uwa babu abinda yadameshi.

Hannayen shi kawai ta tsinta bisa hab’ar ta, ko kafin kace mene ya dago da kan nata data ke ta faman sunnewa k’asa.

Direct idanuwan shi nan nashi ya sanya cikin nata, hakan yasa take taji wani abu maigirma ya wuce ta mak’oshin ta, ji kake ‘K’uut’ ta had’iye abinda bata da masaniya akai

“Maimaita abinda kike fad’a wa nabilan.”

Shiru tayi tana zare ido, ga fuskarta gaba d’aya a tafin hannun shi babu dama ta juya tai kunkuni, hakan yasa tai shiru tana mai cigaba da dauke idanuwanta daga nashi.

“Karki bari in k’ara maimaita magana makamanciyar wannan kazar mayu.” Ta k’ara tsinkayo muryar shi yana bata umarni.

Da sauri tarik’a had’iyar miyau, lokaci guda kuma hawaye na neman taruwa cikin kwarmin idanuwan ta, k’ara marairaice fuska tayi ko zai ji tausayin ta, domin kuwa batajin zata maimaiata abinda tace d’in dazu.

“Ka… Kayi hak’uri ni babu abinda nace.” Ita kanta data zambad’a karyar sai da taji babu dad’i, domin kuwa halayen safwan kakaf babu wanda basu sani ba, mussamman na mugunta, dad’in dad’awa tasan yanda baya shiri Sam da makaryaci.

Zafin dataji a saman leb’en tane yasanya ta sanya ihun azaba, hawaye suka cigaba da tsartuwa bisa kuncin ta, lokaci guda kuma ta rik’a jin tamkar ta saki fitsari a wando, ba shakka ya safwan bak’in azzalumin neh.

Kamar ba shi keh mutsuke mata labb’a ba, kallon ta yacigaba da yi batare da ya saki fuskar tata ba, hakanan ya tsinci kanshi da sin kare mata kallo, mussamman idan hawaye na silalowa daga idanuwanta masu sanya mashi faduwar gaba.

“Uhmmm, inajinki, me kike gaya wa nabila a waya?” Ya k’ara tambayar ta a karo na biyu, wannan karon bakin daya murje, ya sanya yan yatsunshi yana shafasu, gamida murzasu a hankali, batare kuma da ya dauke idanuwan shi da suka fara canza launi daga kanta ba.

Jikintane ya soma rawa a hankali, hakanan sai taji kamar wani abu na fizgarta, ga daishi azaba ce yagama dandana mata a yanzun bada jimawa ba, amma kuma sai ta tsinci wani abu nabin ilahirin jikin zul zul yana shigewa har k’arshen kwanyar ta, lokaci guda ita kanta tanemi nutsuwar ta ta rasa, hakanan ta tsinci kanta da kasa bude baki tayi magana, gaba d’aya wata shegiyar kasala ke bin lungu da sako na jikin ta. +

“Uhuumm, talk!” Ta k’ara tsinakayo muryar shi cikin wani irin sauti da bata tsammanin baiyi nasarar tsinka sauran daskararren jinin dake gudu cikin jikinta ba, hakan yasanyata yin baya luu.

Shi d’in ma batare da sanin shi ba, ya tsinci kanshi da kura wa labb’an nata idanu, hakanan lokaci guda ya rik’a jin wani abu mai shegen girma na fizgar shi, wanda take yanke yafara neman sauran tunanikan shi yarasa, babu abinda yake gani a lokacin inbanda k’aramin bakinta dake ta shan murza a hannun shi, tsinatar kanshi yayi yana binta a hankali yayin datakeyin baya domin dangana da katifar gadon datake zaune.

“Talk…. Please.”

Ya k’ara maimaitawa daga kasan mak’oshin sa, wanda daga dukkan alamu shi kanshi bashi da masaniyar abunda keh fitawa daga bakin shi, diba da yanda gaba d’ayan su suka fice daga sauran hayyacin su batare da sanin su ba.

Ji tayi kamar ansanya makulli andatse mak’oshin ta, domin kuwa gaba d’aya neman yanda ake bude baki ayi magana tayk ta kasa, numfashi kurum take saukewa a hankali, wanda hakan yayi nasarar hadewa da nashi numfashin, sakamakon irin rumfar da yayi mata.

Zuru yayi yana cigaba da kallon bakin nata, lokaci guda kuma numfashin nata na samun nasarar sauka bisa kirjin shi dayakejin tamkar wani gingimemen abu yai mashi tsaye bisa kai, hakan yasanya sauaran kuzarin shi yin sallama dashi.

“Talk….. Plea… sse”

Shi kanshi bazai ce ga dalilin dayasa yake ta wannan nacin ba,gaba d’aya babu sauran tunanin daya rage a kwanyarshi wanda yawuce ya rarumi bakin ta daya sanya wa na mujiya tun dazun.

“Ban… Bance ko… mi……”

Gaba d’aya kafin ta k’arasa rawar bakin nata, taji duniyar ta na juya mata, haka nan lokaci guda taji abinda batajin ta tab’a jin irin shi a dukkan tsawon rayuwar ta.

Irin cafkar daya kaiwa bakin nata neh zaiba mutum mamaki, domin kuwa zaka iya rantsewa da Allah his life depends on it neh, diba da yanda yake zuba mata wani irin passionate kiss d’in dashi kanshi bayajin yasan sanda ya iya irin shi, hakan yayi nasarar mantar dasu dukkan wasu matsaloli ba rayuwar su, mussaman wata kalma ta “K’in juna” da suke ikirarin sunai wa juna.

Duniyar su ce ta rik’a mirgina mirgina dasu, domin kuwa ba sumba ba na wasa yake wa ramlan ba, sumba ce mai matuk’ar zafi yake mata, wanda hakan kad’ai ya isa ya tabbatar maka da cewar su dukka biyun sun dade suna muradin hakan a rayuwar su.

Gaba d’aya ya nanik’eta yana shirin cinye mata baki, dama armless rigarta ta dade da barin kafadun ta, diba da yanda yake yamutsa ta, yanayin da dukkansu suka shiga d’in yazame masu wani gingimemen al’mari wanda atake yanke zuciyoyin su suka cigaba da bugawa a tare, a lokaci guda kuma suka k’ank’ame juna kamar wasu magnet

Kiran wayar safwan data dade da fadowa k’asa neh yasami nasarar tsinke dukkan wasu shudewar tunani da suka yi, hakan yasanya shi sakin bakin nata a hankali, wanda yin hakan dayake yaji tamkar raba rayuwar shi da wani bangare na jikin shi yake.

Rabuwar bakunan nasu, yasanyata jin waata iriyar kad’aita na mata sallama, hakanan sai takejin kamar maraici na shirin afka mata, gaba d’aya jikinta ya rik’a jin tamkar yayi rashin wani bangare babba na daga gareshi neh.

Idanuwanta a rufe suke ruf, amma duk da haka bata fasajin yanda idanuwanshi keh hora bear skin d’in ta ba, hakan yasanyata k’ank’ame jikin ta, lokaci guda kuma ta rik’a tariyo abinda ya faru tsakaninta dashi sakanni kadan da suka wuce.

“Kazar mayu you win in seducing me abi?”

Take taji wata shegiyar kunya da haushi sun lullubeta,lokaci guda tarik’a danasanin yanda akima ta biye mashi,hakan yasa ranta yai matuqar b’aci da kalmar daya gaya mata, tarasa me zatayi mashi ta huce.

Batare data k’ara tunanin komi ba, ta tattaro dukan miyan bakin ta ta tofa masa duka a bisa fuskar shi dake samnta yana kallon ta. 1

“What the fuck?”Don Allah ina neman afuwarku bisa kuskuren da aka samu a chaptern baya, inda nasanya ramlan tayi ramuwar sallolin ta, bayan kuma a baya nariga dana ambaci cewar tafara fashin sallah a wayewar garin na yau. Ajizanci neh irin na dan adam, afuwan pls. Love you all fisabilillah💞😘
***
“Lashe shi.” 1

Kwalalo idanunta tayi waje, tana mai k’unk’uni, lallaima wallahi bazata lashe ba.

“Kazar mayu don’t make me repeat myself… zuro halshenki ki lashe miyan ki.”

Mirgin kanta gefe ta kuma yi, alamun bafa zata lashe ba, waye yace ya fad’a mata bakar magana. 2

Cikin sakannin da bata sami ikon kirga su ba, ya tattaro ta gaba daya gamida maida hannayen ta baya ya murd’e, lokaci guda ya bankaro ta gaba d’ayan ta

Ihun azaba ta sanya, gamida ambaton yayi hak’uri yayi mata rai, bai kula ta ba, illah fuskar tashi daya k’ara matso mata da ita daidai saitin bakin ta.

Ai da gudu ta sanya halshenta tana mai sud’e miyan data kwab’a mas a fuskar, cikin kankanin lokaci ta tande miyan tass yazamana babu ko digon saura akan fuskar tashi. 12

Saida ya sanya rigarta ya k’ara share fuskar tashi kana ya yai wulli da ita tsakiyar falon, hakanbyasa ta k’ara bajewa a kasan tana cigaba da kukan azaba, a zuciyar ta kuma tana cigaba da ja mashi kwandunan Allah ya isa.

Sai da ya sanya k’afa ya k’ara shure ta kafin yayi ficewar shi daga dakin, batare da jin koda digon tausayin ta ne ba, ballantana ya tsaya ya lallashe ta, ganin ihun kukan data ke kwararawa harda su birgima.

***
Ganin ya karade dukkan inda yake tunanin zai sami samiran neh bai sameta ba yasanya shi yanke hukuncin kiran ta kawai, duk da dai da yasone yayi mata dirar mikiyah.

“Mr Tafeeda is that you?” Ya tsinkayo sautin muryar samiran bayan ta dauki wayar.

“Numbern wa kika gani?” Shima ya tambayeta.

“Mamaki nake neh, yaushe kashigo k’asar?” Ta tambaya muryar ta da alamun damuwa.

“Bayan kingaya mani inda kike, sannan sai muyi maganar.”

“Ina gidanmu.” Ta bashi amsa a takaice.

“Kina ganin gidan  nakun is that safe dazamuyi maganar dake tafe dani?”Sai da tadanyi nazari kadan, kana tace…. +

“Okay mu had’u a gidanka  mana kawai.”

“Ki sameni a can.” Daga haka ya datse kiran yana mai Allah Allah ya had’u da samiran domin ta fad’a mishi how comes tai failing d’in shi. 9

***
Ganin babu mai lallashin tane ya sanya ta mike ta fada bayin ta sake yo wanka, kana ta fito gamida k’ara kintsa jikin ta sabida fashin sallar datake.

Cikin tane ya fara kugi, hakan ya tabbatar mata da cewar yana bukatar agajin gaggawa.

Da sanda ta shigo falon, kana tacigaba da yin sandar harta dangana da kitchen d’in gidan, bude bude ta rik’a yi tare da fatan samun abunda zata sanya wa cikin nata dake ta faman ihun yunwa.

Babu wani abun ci a kitchen din, kasancewar komi danye neh, gashi kuma kayan wutan na girki, ba’a hadasu ba bare ta dora koda indomi neh.

Drinks kadai tayi nasarar samu a cikin fridge din, hakan yasanya ta sunkuci guda gamida hanzarin budeshi ta tuttula wa tunbin ta.

Ji tayi kamar ansake yi mata yasa a cikin, hakan yasa ta fito kitchen din da saurin ta ta doshi dakin da take tunanin nan neh na safwan din.

Knocking tafara yi da d’an karfi..

“Who the hell is that?” Ta tsinkayo muryar shi a fusace.

Saida ta harari kofar kana tace itace.

“What?” Ta sake jiyo shi yana tambayar ta.

Kara dallah wa kofar harara tayi, gamida jin inama zata iya kama gayen nan ta mishi tsinannanen duka, kila ta huce takaicin da yake k’unsa mata.

Ganin irin yunwar datakeji yasanya ta murguda baki gamida cewa…..” Toh ni ba yunwa nakeji ba”

“And so? Uban mi zan miki dakike gaya mani?”

Taso tace ubanka zakai mani, amma tai hanzarin maida maganar diba da cewar marigayi uban nashi, itama d’in hak’ik’a uba yake a gareta.

Tana k’unk’uni tace… “Toh ni banga abinci ba a gidan, atoh kuma ni nan yunwa nakeji.”

“Toh ba mayya bace keh dama, shigo ki cinyeni kawai.” Yabata ansa cikin halin ko inkula. 1

Gaba d’aya yagama k’ule ta, watoh mutumin nan bazai daina danganta ta da mayu ba koh?

Shiru tayi tana mai cigaba da harar kofar, ganin aikin banza take harara cikin duhu yasanta sanya kafar ta ta hauri kofar da karfin ta, kana lokaci guda tace.

“Kaga mayyah a tsakiyar gadon ka, mugu azzalumi, kuma wallahi koda me kake tak’ama sai ka sakeni nakoma wajen masoyina kuma mijina abin alfaharina in Allah ya yar……” 2

Maganar ce kawai ta tsaya a makoshin ta sakamakon jinta datayi a tsakiyar dakin nashi a yashe a kasa, wanda wurgotan da yayi saida yasami nasarar buguwar kanta da gefen girkakken italian bed din dake dakin nashi.

Ihun azaba tacigaba da zubawa, lokaci guda ta rik’a kiran mammy da dukkan karfin ta, domin kuwa yau tariga datasan k’arshen rashin kunyarta tazo.

“Da sannu zanci ubanku daga keh har wannan bak’in yayan naki mai bak’in hali, zaki baiwa masu garin ku labari.”

Mirginawa tayi can k’arshen bangon dakin tana cigaba da makyarkyatar tsoro, domin kuwa kallo d’aya taiwa fuskar nan tashi tainmaza ta dauke kai, domin kuwa a asalin safwan damisan shi yake.

” Matso nan stupid. ” ya daka mata tsawa.

Ai batasan lokacin data matso ba da sautin ta, lokaci guda kuma ta rik’a rokonshi akan yayi hak’uri ya yafe mata sharrin yunwa neh. 3

Zama yayi bakin gadon nashi gamidacewa, karta damu zaiyi mata maganin yunwar yanzun nan.

Shiru tayi jikinta na cigaba da mazari, zuciyar ta kuwa kamar ta fado kasa sabida zullumi da tsoro, Allah gani garEka ka kareni daga sharrin wannan bawa naka, ta rik’a addu’ar hakan aranta.

“Komawa yayi ya kwanta bisa gadon, lokaci guda yaciga da danne danne a wayar shi batare da yakara kallon gefen inda take ba.

Hakan yasa tafara tunanin kila zai yafe mata neh, tunanin hakan yasanya fitowar ajiyar zuciyar ta a hankali, kana ta rik’a sharce kananun gumin da suka fara feso mata a goshi.

“Kneel down, raise your hands up and close your damn eyes.” ta tsinkayo muryar shi in a serious tone yana fad’a.

Saurin daga kai tayi ta kalle shi domin sake gasgata abunda kunnuwanta suke jiyo mata, kwata kwata hankalin shi baya kanta, illa wayarshi dayake ta daddanawa hankalin shi kwance.Don’t make me repeat myself, you will regret it.” Yasake fad’a batareda ya kalli sashen da take ba.

Ai da sauri ta mike gamida yin yanda yace d’in, hawaye kuwa sukace salamu alaikum, babban abinda yafi bata takaici shine armless rigar dake jikin ta, wacce d’aga hannun datayi yataimaka wajen bayyanuwar hammatar ta dakuma gefe da gefe na boobs d’in ta.

Inda ta godewa Allah ita d’in ba mai barin koda digon gashin hammata ba ne, hak’ik’a da yau ta kwashi kunya da takaicin da bazai taba gushewa a ranta ba, amma duk da haka ranta bai fasa kuna ba bisa wannan cin mutuncin da yake mata.

Tafi minti ashirin da bakwai a hakan, wanda zuwa wannan lokacin hannayenta sungama sagewa, inbanda radadin azaba babu abinda suke mata, bayaga uban gumi datake ta zubawa duk kuwa da a.c din dake kunne a dakin.

Shiru tayi tana mai cigaba da karkarwar azaba, hakanan kuma taki bude baki ta bashi hak’uri, sanin kitayi hakan inba yagadama ba ba kulata zaiyi ba.

Ta gefen idanunshi yake kallon ta, kana kuma akaikaice ya rik’a bin jikin ta da kallo, idanunshi neh suka sauka bisa gefen nononta da suka dan bullo ta gefen hammatar ta, dan kwala ido yai waje yana mai mamakin dama yarinyar nan nada boobs, domin kuwa shi duk daukar shi flat f9 kirjin nata yake. 2

Cigaba yayi da kallon kirjin nata batare da yasan yanayi ba, domin kuwa wannan karon gaba daya daina satar kallon nata yayi, saima juyo dayayi sosai yana kare masu kallo bil hakki da gaskia.

Fahimtar abinda yakeyi ya sanyata turo baki gamida dura mas zagi a zuciyar ta, kana lokaci guda ta sauke hannayen ta tana mai kakkare jikinta.

“You must be very stupid ramlah”

Kara nannade hannayenta tayi a kirjinta tana mai gunguni a hankali, yadade bai ce mata stupid ba, wannan ai salon iskanci neh zaa rik’a kallon mata nono kamar anbata a jiya.

Lallaima yarinyar nan tafara rainashi, ya ambaci hakan a cikin ranshi, lokaci guda ya yanke hukunci me zaiyi mata, sai yaga ta karyar boye boyen datakeyi,nonsense kamar wata mai nonuwan arziki, yai kwafa.

“Sabida kin rainani koh kazar mayu? Nace ki sauke hannayen ki neh eyeeeh?”

Kara zumburo baki tayi gaba gamida dauke kanta gefe.

Tsawa yadaka mata wacce tayi snadiyar sanyata sakin tusa a firgice, domin kuwa batayi tsammanin mutum zai iya irin wannan tsawar ba haka. 5

” Tashi kifara tsallen kwado useless.”

Ai tunkafin yarufe baki ta tsugunna gamida fara tsallen kwadon, lokaci guda kuma tana zunduma ihun kuka, domin kuwa ba shakka yau safwan yagama ci mata sauran mutuncin ta dake idanunshi.Komawa yayi ya kwanta yana mai fuskantar ta, domin kuwa wannan karon aje wayar yayi ya maida kacokan hankalinshi bisa kanta dake ta faman buga tsallen kwadon.

Kallonta yacigaba dayi kamar maye, hakanan idanuwanshi basu fasa kallon yanda kirjin nata daya rainanke tsalle ba shima sakamakon tsallen da ilahirin jikin ta keyi.

Relaxing yayi gaba d’aya yana mai enjoying girgizar da jikinnata keyi, domin kuwa har wani lumshe idanu yake tareda jin yanayin jikinshi na canzawa. 2

“Wow” ya rik’a maimaitawa a can kasan makoshin sa, lokaci guda yana k’ara mamakin yanda akai bai tab’a lura da yanayin kirjin nata ba,a take kuma yarika mamakin abinda yasa bata sanya breziya ba, domin kuwa da da bra din a jikin nata zaifi tunanin kila acuci maza ta sanya wato push up irin wacce samira keh sanya wa.

Ihun kifawarta neh yamaido shi hayyacin sa, hakan yasa ya mike da sauri ya isa inda take kwance warwas tana maida numfashin wahala, irin nishin datake sai mutum ya dauka cutar asthma gareta.

Tuni dama jikin shi yagama mutuwa, hakan yasa yana isa inda take ya kwaaheta gaba d’ayan ta ya mannata da kirjinshi dake ta bugawa fat, fat, fat kamar  shima yayi tsallen kwadon. 1

Lakwas tayi a jikinshi, domin kuwa batama da sauran karfin dazatai gaddamar raba jikinta da nashi, hakan yasa tai surrender gamida sanya kukan bak’in ciki, lokaci guda tarika jin tamkar kafafun ta suntashi aiki, diba da yanda takejin tamkar ansanya gora neh an bibbige mata guiwowinta.

Matseta yayi a jikin shi yana jijjigata ahankali, lokaci guda kuma yarika  ambatar “Ya isaa, it’s okay…. Nine koh.?

Cigaba tayi da kukanta, ranta na suya, ba shakka yau d’innan ta k’ara tabbatar da cewar shi d’in yakasance wani irin mugun azzalumi na bugawa a jarida, batai kasa a guiwa ba ta rik’a ja mashi kwandunan Allah ya isa bata yafeba a can kalkashin zucciyar ta.

“Ya isa nace, I’m sorry kinj?” Ya furta can ckin kunnenta a hankali, hakan yasa ta k’ara sautin kukanta jin yana k’ok’arin lasar mata kunne.

Sunkutar ta yayi gaba d’aya ya aza bisa gadon nashi, kana ya sanya duvet din dake bisa gadon ya lullube mata kafafu, bakinshi batareda ya yanke daga ambatar sorry nine ba koh.

“Bari nije insiyo miki abinci okay? Jirani yanzu zandawo.”

Juya mashi keya tayi gamida cewa “Ba’acin abinci.”

“Naji kiyi hak’uri, give me few minutes.” Ya ida zancen yayin da yake surar keys d’inmotar. 3

Peck ya manna mata a goshi, ko kafin tazuba wani action din ya fice da sauri gamida cewa “Pretty ina dawowa yanzu.” 10

Juyowa tayi gamida bin k’eyar shi da harara, kana ta maida kanta tana cigaba da maida ajiyar zuciyar wahala.

Fitar shi da baifi mintuna sha biyar ba taji alamun motsi a falon, lokaci guda kuma ta rik’a jin alamun tafiya hankali tamkar ana sand’a.

Kasak’e tayi tana mai k’ara kasa kunnenta domin gasgata abinda kunnuwan ta ke jiyo mata, hakan yasa ta fahimci soaai takun tafiya keh k’ara yawa, hakanan kuma sai taji kamar ana shiga sauran dakunan baccin nasu.Kafin ta farga da menene sai jitai an bude dakin safwan dindatake ciki, sannan ko kafin tagama sanin waye sai gani tayi ankashe wutar dakin duhu ya mamaye.

Take gabanta yai wata iryar mummunar faduwa, sakamakon jin wannan kamshin turaren da yazame mata tamkar wani tuni neh ko fami ga daren da yazame mata sanadin tashin hankalin ta. 4

“My Love Longest Time.” Ta tsinkayo siririyar muryar mutmin ta ambata. 9

Tsirrrrr taji kamar fistari ya kufce mata.

“Wayyyoooo Allah naaaaaaaaaaaa…… ” Ta kurma wani razanannen ihu.Ta sake tsinkayo muryar tashi wacce tai matuk’ar yi mata kama data wani data sani, amma kuma ikon Allah takasa tunawa. +

A hankali yaciga da matsowa inda gadon keh girke, wanda a lokacin tariga data gama jikewa da zufa da fitsari, yanda jikinta keh karkarwa kuwa kai kace lokacin hunturun sanyi neh tai wanka da ruwan sanyi irin mai k’arara d’in nan. 2

Duk da cikin duhu neh hakan bai hanata fahimtar yazo saitin inda take ba, diba da yanda kamshin turaren ya yawaita a hancin ta, dama ta dade da sandarewa sabida tsananin tsoro, domin kuwa ko ynkurin yin wani abu kasawa tayi.

Batare da saninta ba taji saukar yan yatsun shi bisa fuskar ta ya shafo, ai da gudu ta k’ara sakin ihu gamida wuntsula can k’arshen gadon tana mai cigaba da karkarwa, haka nan kuma zuciyar ta bata fasa bugawa ba busa tsananin mamakin jin muryar mutumin datake tunanin shi yai mata fyade a wancan karon.

Hak’ik’a inbata manta ba, ko a wancan karon bataji muryar shi ba, wanda a iya saninta babu dalilin sanin muryar ma, domin kuwa ita ganau ce na cewar tabbas fuskar safwan tagani bayan yagama tsiyar shi zai fita, safwan mainasara shine wanda idonta ya hasko mata, hak’ik’a zafin ciwo ba zaisa ta kasa tantance fuskar safwan mainasara ba, a kowanne hali kuwa take ciki.

Amma yanzu wannan fa? Miya kawo wannan kuma gidanta? A tunanin ta rapist d’in ta take aure yanzu, toh don menene kuma wani daban zai fara bibiyar rayuwar ta? Shin me tayi wa jama’ah neh suke son ganin k’arshen ta?

Hayowa gadon dayayi yayi sanadiyar maidota daga tunanin wucin gadin datayi, hakan yasa takuma takurewa jikin bangon dakin wanda keh tabbatar mata datazo mak’urar gadon.

“Don….don Allah kayi hak’uri, menayi maku kukeson ganin rayuwata ta tagayyara?” Ta fada cikin sautin kuka mai tattare da bak’in ciki da tsoro.

“Heyyyy, kar insake jin kin ambaci tagayyarar nan? Ni d’in mai sonki neh har gaba da abada, just hushhh and come here.”

Sake barkewa tai da kuka a karo na biyu tana rokonshi.

“Malam kom wanene kai na tabbatar kasan yanzu ni matar aure ce? Kuma hak’ik’a nasan kai d’in musulmi neh, kuma tabbas nasan kasan hakkin cin mutunchin aure, shin darajar auren danake da ita bazaisa ka kyaleni ba?”

Wata deep dariya ya saki a hankali, wanda saida yayi ta ishe shi kana yace…..

” What are you saying? Nine mijin ai, haba I’m not that bad dazanke neman matar mutane, Godforbid I’m too good for that babe.” 15

Kasak’e tayi tana mai kara son fahimtar muryar, amma hakan yaci tura, amma kuma yak’ara rudata, shin mi yake nufi da shine mijin?yau ita kam ta shiga uku, taje ta rik’a addu’ar bayyanuwar safwan domin yakawo mata dauki, dukkuwa da sanin cewa shi d’in ma halin su guda da wannan d’in, but at least tasan wannan karon zai iya tausaya mata ko don kasancewarta matar shi a yanzu. 1

Kafin ta ankara sai ji tayi anjanyo kafafunta k’iiii, ko kafin tayi wani yunkuri yayi azamar sanya hannayen shi ya sanya wani kyalle ya rufe mata bakin ihun,idanuwa a waje ta rik’a mutsu mutsu gamida harbe harben kafafu,hauka sosai ta shiga zubawa duk don ganin ta kubuta daga wannan salihin mugun.Keh kehhh banason hauka, nine fa…. Ko baki yadda ba? Safwan neh, just calm down okay?”

Tsayawa tayi da bigebigen, ba shaka wannan anyi dan duniya, yana tuananin sai ya raina mata wayo neh zai samu nasarar samunta? Ai ko mutuwa tayi ta dawo muryar safwan bazata tab’a gushe mata ba, in short a iya saninta duk duniya shi kad’ai keh da irin muryarshi, bata tunanin akwai wani wanda zaibawa ikon imitating irin muryar ma tashi, ballantana har ace muryar ce exactly. 1

Ganin bata da niyyar daina kuka, yasanya ya nufi inda switch d’in dakin yake ya kunna hasken dakin, take duhun dakin ya gushe, haske kuma yabayyan dau.

Bai matsa ba daga inda ya kunna switch d’in, tsaye yayi gamida juya mata baya, ta yanda bayan shi kawai take iya hangowa sai ko keyarshi.

Dagasken gaske ta kura wa bayan nashi ido tanason tuno irin bayan, amma sam haka ya faskara, dogo neh shima,wanda sirantar shi ta taimaka wajen bayyanuwar tsahon nashi sosai.

Ganin tayi shiru neh tana k’are wa bayan shi kallo yasanya shi juyowa sosai yana facing d’in ta.

Dararaam taji gabanta ya rufta, wqnda tsananin faduwar da gaban nata yayi yataimaka wajen fidda sautin da kirjinta keyi fat fat kamar zai faso kirjinta. 1

“Yaa saf…. Safwan?” halshen ta ya dauki karkarwar kiran sunan shi.

Murmushin gefen bakin nan nashi ya saki gamida d’age girar shi guda sama.

“Matsoraciya kawai.”

Ya fadi hakan yayin da yake k’arasa takowa zuwa inda yake.

Kallon shi ta rik’a yi da zallar ikon ta, hakanan sai ta rik’a jin kamar wani al’amari na kusantoto neh yayin dayake nufota,har yanzu kwanyarta ta gaza gasgata mata abinda idanuwanta keh hango mata,domin kuwa mashahuran tambayoyi neh suka nemi sark’e mata k’wak’walwa har takejin tamkar kwanyar tata ba shirin tarwatsewa neh.

Har lokacin da safwan d’in ya k’araso inda take  zaune bata fasa binshi da kallon mamaki ba, idan dai ba haukar wasu en awanni tayi ba, to hak’ik’a tafi kowa sanin cewa wannan ba muryar safwan bace, na biyu kuma, gaba d’aya yanayin kirar jikin su ma ba d’aya ba sam sam,abu na uku kuma wannan kayan dake jikin shi ba irin su bane a jikin  da zai fita ba, abu na hud’u shi wannan d’in ya kasance babu digon gashi ko daya a fuskar shi, a shaven ta take, sannan kuma sumar shi ma a sake take, sai wasu en tsirarun gashi kadan bisa kan nashi. 9

Amma daga ba wannan ba, komi dakuka sani na fsukar safwan shine a fuskar wannan d’an tahaliki, in short inbama ita da suka rabu dashi ba yanzu, to kam hak’ik’a babu wanda ya isa yace wannan d’in ba safwan mainasara bane.

Abu d’aya dazaka k’ara tantancesu shine yanayin attitude da personality d’in su, kallo d’aya zakayi wa wannan ka fahimci cewr mutum neh mai fara’ar gaske, in short smiling face gareshi ma, yayin da wancan safwan d’in ya kasance complete opposite d’in wanan, domin kuwa shi sai yafi wata ma baiyi dariyar minti daya ba, bash shi dai in abu yabashi dariya ya murmusa da gefen labban shi.

“Yanzu kinfahimci cewa ni d’in neh koh? Tsoron ya k’are?” ya ida maganar yayin dayake kashe mata ido daya, lokaci guda yana sake sakin Murmushin nan nashi dayazame mata bakon al’amari.

“Ba shakka ya canza.” Ta ambaci hakan a ranta.

“Amma miya canza shi har haka?” ta shiga tambayar kanta.Oyaa tashi muje gida mammy na son ganinmu.” 2

Kallon mamaki ta k’ara bin shi dashi, dazun nan fa suka baro gidan, kuma ma yanzu da dare yayi neh mammyn zata bukaci ganin su? Da mamaki kuwa.

“Muje inraka ki kicanza kaya, kinga yanzu kusan to eight, inaso zuwa ten mundawo.” Ya ida zancen yana zura mata dakwalan idanuwan shi masu shegen haske.

Idanuwan ta rik’a kallo, dama ya safwan nada idanuwa haka yake masifar lumshe su, domin kuwa tsaf zaka danganta shi da masu fici ficin ido, diba da yanda kodayaushe suke a lumshe kamar na mashaya.

Rakata yayi dakin nata, ganin yayi mata tsayene yana kallo yasanya ta dauki kayan ta shige toilet ta shirya, zuciyarya kuwa bata fasa yi mata wasiwasiba bisa wannan canjin datake gani tattareda safwan d’in. 3

Koda suko zo harabar gidan babu motarshi a gurin, a cewarshi a waje yayi parking sabida kar su bata lokaci.

Malam sada mai gadin dake zaune a kofar dakin shi yana jin redio sukai wa sallama.

“Baba zamu fita muje mudawo, duk wanda yazo kace bama nan.” cewar safwan kenan.

“Angama yallabai, a dawo lafiya.”

Daga haka suka fice daga gidan, inda ta hango wata mota kirar fomatic ash colour sabuwa dal sai shek’i take.

Kasa rike mamakin ta tayi, domin kuwa a saninta motar safwan benz ce baka wuluk mai tinted glass, hakan yasanya tace….

” Ammm ya safwan ka canza mota neh yanzu daga fitarka?” 3

Tayi tsammanin zai gwasaleta kamar yadda ya saba, amma sai yak’ara jibga mata d’imbin mamakin sa yace…

“Motar bilal ce fa, kinsan yana hotel nan zai kwana,mechanic ya wuce da tawa dazunn nan.”

A ranta tace oh mutumin nan kirkin ma baiyi. Maka kyau ba, kafi kyau a maras kirkin ka. “

” Shall we? ” ya ambaci hakan yayin da yake bude mata gaban motar.

Tabbb mamakin safwan yau zai kasheta, kirkin nan yayi yawa, tsakani da Allah abin yafara yi mata baraza a zuciyar ta. Kar kuga laifin ta, bata saba bane.

Bayan ya tada motar neh ya juyo ya kalleta, ganin yanda tasaki baki take ta k’ara binshi da kallo, ta tsammani zai harareta ko yadakamata tsawa kamar yanda yasaba, amma ga mamakin ta sai jitayi yace….

“Babe na canza maki neh yau?”

Baki a hangame take girgiza kai…. Hak’ik’a safwan yau bazai kasheta da mamakin sa ba.

“Here w we goooo….” Ya kwashi motar a sittin. 3

***
Horn mai karfi guda daya yayi a kofar get d’in gidan nashi, a zuciyar shi kuwa Allah Allah yake ya karasa gidan domin kai mata abincin, ba shakka yasan taji yunwa sosai, diba da irin tsallaen kwadon dayasata dazu, ko shi kad’ai yaci ya wawuahe ragiwar abincin dake tumbin ta. 4

Malam sada dake jin redio yayi hanzarin lekowa ta k’aramar kofa domin son tabbatar da hirn d’in da kunnuwanshi suka jiye mashi, domin a iya saninshi ko minti goma basu rufa da fita daga gudan ba.

Ganin safwan dinne yasanya yakoma daga ciki domin wangale get d’in, a ranshi yana ambatar kila mantuwa sukayi.

Saida ya aikawa malam sadan harara bayan ya shige farfajiyar gidan, hakanan daya fito saida ya dubi malam sadan dake mishi sannu da zuwa yace…

“Malam sada badai zaka dena yin jinkirin bude mani get ba koh? Idan kagaji da aikin neh sai in sallameka akawo wani?”

“Ayi hak’uri yallabai, wallahi banma dauka kai bane, sabida naga ko minti goma bakayi da fita ba, shiyasa natsaya leke domin tabbatar da meyin horn din, ayi hak’uri yallabai.”

Hararar shi yayi gamida cewa shikenan yawuce, amman yaringa lura.

Godiya malam sada yayi yakoma bakin aikin shi, yayin dashikuma ya dauki ledojin siyayyar abincin da yayi musu ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, dama gashi ya dan dade a wajen diba da yanda yabata lokaci a hotel din da bilal ya sauka suna tattauna maganar yanda zai fara aiki, acewarshi tunda yanzu yazama. Me iyalin karfi da yaji, toh hak’ik’a yana bukatar aikin dazai yi domin sui surviving.

Aje ledojin yayi bisa dining table din, kana yaiwa dakin shi tsinke, ganin bai sameta anan ba, ya sanya shi nufar nata dakin.Bata nan ma, hakan yasa yai tunanin ko tana toilet neh, tunanin hakan ya sanya shi knocking toilet d’in gamida cea, ya dawo, idan tagama ta sameshi a falo, ga abincin can. +

Jin bata tanka shi ba yasanya shi hararar kofar tamkar tana gabanshi yace “keh bakya jina neh?” 1

Wannan karon ma shiru yaji,kunsan mutumin naku da saurin jin haushi, hakan yasa ya bud’e kofar a fusace, mamakin shi neh ya karu dayaga still bata ciki, saima rigar dazu dake jikinta daya gani yashe a kasan tiles d’in bayun..

Baisan miyasa ba sai yaji kamar gabanshi na faduwa, hakanbyasa da zafin nama ya kuma juyawa gamida bin ko ina na gidan yana dubata, lokaci guda yana ambatar sunan ta da iya karfin shi.

Kardai ganin ya dade yasanyata fita daga gidan nan? Idan ko hakane ba k’ara min sab’a mata zaiyi ba, besides da izini wa zata fita daga gidan nan, kuma ma da daren nan ina zataje?

Ganin ya karade gidan bai gantaba, ya sanya shi fitowa domin tabbatar da zargin shi wajen baba mai gadi, yasan dai dole sai ya bude mata kofa neh zata iya fita.

“Baba, baba sada ji mana….” ya yafito maigadin.

Da sauri baba ya karaso gamida dan dukawa, kana yace “Yallabai gani.”

“Da yaushe matar gidan nan ta fita, kuma ina tace maka zata?”

Mamakine ya dan bayyana a fuskar baba sada, amma sai yai tunanin kila mantuwa ce irin ta dan adam, hakan yasa yace….

“Yallabai ai ni tun fitar da kuka yi dazu tare mintuna ashirin da suka wuce bankara ganin hajiyar ba.

Saida ya harari malam sadan sabuda jin soki burutsun shi, ba shakka doke ya canza maigadi, bazai iya da wannan rudadden tsohon ba.

” My friend will you shut the fuck up, awanni kusan biyu da fitata kana gaya mani mintuna ashirin dasuka wuce na fita? Ka  san mekake cewa kuwa? 1

Da sauri baba sada yace” Wallahi tallahi Yallabai ko minti ashirin bakuyi da fita ba kaida hajiyar, shiyasa nayi mamakin dowowarka kuma yanzun nan, sai nayi tunanin kila mantuwa kayi kadawo.”

Gabanshi neh yau wata iriyar faduwar da bayajin yataba jin irin hakan….Kasak’e yayi yana k’ara kallon baba maigadi, irin kallon nan da zai tabbatar wa wabda ake kallo d’in, ba kallon hankali bane. +

Shima dai malam sadan sunkuyar da kanshi kasa yayi, zuciyar shi cike da wasiwasi.

Can kuma kamar an tsunguleshi yai firgit, gamida komawa cikin gidan da saurin shi, yayin da malam sada ya dage kai gamida binshi da kallo.

“Allah yasa dai lafiya.” cewar malam sada yayin dayake juyawa zuwa bakin aikin shi.

Koda ya shiga falon, zuciyar shi bata fasa bugawa ba, hakanan kuma koda ya dauko wayarshi baiyi mamakin yanda yaga kamar hannun shi na rawa ba, ba shaakka jikinshi nabashi wani babban al’amari na tunkaro rayuwar shi. 1

Numbern inna ya latso, sanin ita kad’ai ce mutum ta farko dazai fara tabbatar da zuwan ramlan ko rashin zuwanta.

Saida yakira sau biyu, ana ukunne Allah ya bashi sa’a ta dauka.

“Alo… Alo wayene.” Ya tsinkayo kakus d’in na fadi da karfin ta,wanda saida ya damtse idanuwanshi gamida jin tamkar ya aje wayar duva da yanda sweetheart d’in tashi ke zuba karad’in gaske a wayar.

“Please ki sassauta muryarki mana sweetheart.” Ya fad’a a dan kufule.

“Af yaron kirki wai kaine dama? Ai bansan kai bane shiyasa ma naki daukar wayar a kiran farko dakayi, ince dai lafiya koh?ina ita rablatun? Inafatan tana shiga ruwan zafi yanda yakamata?”

Shikenan kuma ai, kalamen innar sun tabbatar mashi da bataje gidan ba, toh ina ta tafi? Ya sake tambayar kanshi, yayin da wani azabebben ciwon kai keh barazanar tarwatsa kwanyarshi.

“Ya ilahiii…..Allahumma ajirni fi musibatiey, wa akhliefni khairun meenha.” Ya rik’a maimaitawa sau ba adadi,ba shakka yana cikin garari. 7

Da azama yamike gamida ficewa daga gidan, a sonshi yabi cikin unguwar ko Allah zaisa yasami dacewar ganinta.

***
A tsaye yake tunda ya iso gidan nashi, bayan yayi masauki neh a tangamemen falon gidan mai dauke da kayan alatun more rayuwa na yau da kullum.

Kiran wayarshinne ya tsaida shi daga zaryar dayake tayi a falon tun bayan shigowar shi gidan nashi, da’alama dama kiran wayar yake jira, domin kuwa umarnin shigowa kawai yayi ya datse kiran, kana kuma lokaci guda yasami guri ya zauna yana mai jiran bayyanuwar sameeran.

Da sallama ta shigo falon, hakanan kuma shigar dake jikinta shiga ce ta mutunci k’warai dagaske, domin kuwa a kallo guda dazakayi mata, ba lallai bane ka danganta ta da waccan samirar ta safwan daka sani. 2

Tsura mata idanuwa yayi har alokacin data samu muhallin zama a kujerar dake fuskantar tashi, lokaci guda kuma tana k’ara mamakin yaushe Talib d’in yadawo kasar bata da masaniya.

“Nayi matuk’ar mamakin ganinka mr tafida” Ta fad’a a hankali yayin datake k’ara kare mashi kallo, wannan shine ganinta dashi na biyu, tun bayan zuwan datayi can Canada d’in lokacin daya bukaci ganinta.

“K’warai nasan dama dole zakiyi mamakin ganina, amma banyi tsammanin a iya mamaki kawai zaki tsaya ba.” Ya ida zancen yayin dayake k’ara zura mata idanuwa.

Sauke kanta tayi kasa tana mai hasaso badak’alar dake gabanta tana jiranta, ba shakka she failed him, amma tayaya zai fahimci cewar ba laifinta bane?

“I thought zaki gujewa haduwar mu samira, diba da yanda gaba d’aya kika sanya mafarkina yazamo labari, ko zaki iya gayamani meyasa kikai failing dina?”

Gabanta neh yacigaba da faduwa, hak’ik’a datana da ikon canza komi to tabbas da tuni an dade da wuce gurin, amma bata da wannan ikon….

” Will you come back to your senses and explain everything to me.” Ya datse mata tunanin datake.

Sauke ajiyar zuciya tayi, kana lokaci guda ta dago jajayen idanunta da tun bayan bugun da cin mutuncin da safwan yai mata baisa sundawo normal kala d’in suba, diba da yanda ta rik’a kuka batareda ta sassauta wa kanta ba, hak’ik’a bazata yafewa mainasara ba.

“Kayi hak’uri don Allah…. Hak’ik’a nasan nayi kuskure, haka zalika na gaza bisa alk’awari dakuma aikin dakasani, wanda tabbas halshena bazai iya yi maka tak’amaimain bayanin yanda al’amura suka juye haka ba.”Cigaba yayi da kallon ta, har yanzun dai bata yi mashi k’wak’waran bayanin dazai gamsar dashi ba, shin ta manta cewar da rayuwarshi take tempering? +

“Hak’ik’a nayi kuskure bisa afkawa cikin soyayyar safwan ta gaskia ba bisa yanda muka tsaraba,taleeb ba laifina bane, domin kuwa zuciyata bata nemi shawarata ba yayin dataje dauko mani wannan magana, wabda a yanzu zaman nan danake ina wanzuwa neh cikin danasani gamida takaicin abinda zuciyata ta janyo mani. ” Ta ida maganar yayin da hawayen bak’in ciki keh kara gangaro mata. 1

Yamutsa fuskar shi yayi bisa jin soki burutsunta, shi ina ruwan shi da k’aunar gaskiya data farayi wa safwan a maimakon ta karya daya hayeta tai mishi, shi yana ganinma son gaskiyan nashi data afka yakamata yak’ara taimakawa gamida tallafawa bisa k’ara janyeshi daga ajiyar shi dake zaune a gidan su, amma duk da haka batai nasara ba, batai k’ok’arin ganin ta dauke hankalin safwan d’in ba, har saida yasami iko gamida damar afkawa kanwarshi kuma rabin ranshi, bai tsaya ahakan ba saida yasamu damar da babu wani mahaluki daya isa ya shiga tsakanin shi da ita yanzu.(Aure)

Ya runtse idanunshi yayin dayake k’ara hasko hoton safwan d’in k’wak’ume da abinda yafi so kaf rayuwar shi….. Hak’ik’a bazai barshi ba, bazai tab’a yafe ma safwan bisa yi mashi karan tsaye cikin rayuwar shi ba, zai tabbatar da yadauki fansar cin mutuncin wacce yake ikirarin mata ce a gareshi yanzu

“Don Allah ka gafarceni Mr tafeeda, ni kaina nan daka ganni ina cikin bak’in ciki da gararin abinda mainasara yayi mani akan wanan yamusashshiyar matar tashi.” 1

Mugun kallon dayake watsa mata yasanyata tunawa da kasassab’ar datayi, hakan yasa da sauri ta gyara zancenta gamida cewa…

“Yarinya k’arama irin wannan, gata very cute and tiny,banyi tunanin tana da effect akan safwan ba har takai ga yayi mani dukan da tunda uwata takawoni dunuya ba’a tab’a yi mani irin shi ba, safwan ya wulakanta ni a gaban kanwar ka taleeb, yaci mutunci na, yakuma yi nasarar dasa tsanar shu a cikin birnin zuciyata, hak’ik’a kuma ko ba dade koba jima sai na dau fansar wulakancin dayai mani.” 2

Hawaye suka cigaba da gangaro wa da kwarmin idanunta,, wanda kallo guda zakaiwa dakwalen idanun nata kai hanzarin mirgina kai gefe, diba da yanda suka k’ara firfitowa sukayo waje sabida kukan data sha.

Baiyi tsammanin zai iya yi mata uzuriba, shin idan yayi mata uzuri shikuma yaya tashi makomar kenan? Shikenan ana nufin ya rasa dukkan burin da ya girma yana gina shi? Ana nufin sai dai ya hakura ya rungumi k’addara kenan? Ana nufin safwan has win over him kenan?

Ya sake runtse idanunshi cike da jin sabon tashin hankali, lokaci guda kanshu yacigaba da bugawa tamkar maishirin tarwatsewa, idan ko ya hakura yabar safwan yatafi free of charge toh hak’ik’a yacia babban dolo, sakarai, shashashan farkon zamani!

“Samira banajin zan iya yafe wa safwan, haka zalika keh kanki danake tsammanin ina da hope daga gareki kinyi failing dina, idan zakiyi wa kanki adalci, tabbas kinsan idan na kyaleki kika tafi free of charge banyuwa soyayyar ramlah adalci….” Ya numfasa kana yacigaba.

“Taimako guda zan iya yi maki, shine kizabi irin hukuncin dakike ganin yadace dake, nikuma nayi alk’awarin yi maki sassauci ta hnayar yin abinda kika zaba d’in, shi kuma safwan i will make sure he regrets his whole damn life, for tempering with mine, zan shayar dashi ruwan mamaki, domin kuwa har yanzu baisan asalin ko waye Abutalib Tafeeda ba.” 1

Jikin samira babu inda baya rawa, a dan iya tsirarun shekarun data fara sanin abutalib tasan waye shi , tasan abinda zai iya aikatawa dama wanda bazai iyaba,tasan abutalib ciki da wajenshi, kuma hak’ik’a tasan shi d’in baya yafiya ga dukkan wanda ya shiga hurumin shi, dukkuwa da kasantuwarshi mutum mai matuk’ar kirki da sanyin hali, matsalar shi d’aya kashiga hurumin shi, toh in sha Allahu a sannan neh zaka tantance zare da abawa.

Yanayin yanda jikinta keh rawa dakuma yanda zufa keh keto mata ta ko’ina bai sanya yaji koda burbushin tausayinta bane, hasalima ji yake tamkar yasanya k’afa yamata bugun da bazata sake koda motsi bane, girman laifinta agareshi ba mai gogewa bane. +

“Kataimakeni taleeb kamar yanda Allah yataimake ka, naaan bazaka tab’a yafe mani abinda nayi ba, domin kuwa laifina mai tarin girma neh agareka, amma duk da haka ina neman sassauci daga sashen sassanyar zuciyar ka, katausaya mani koda wannan shine agaji na k’arshe dazaka iya yi mani a rayuwata, hak’ik’a a ashirye nake da inyi dukkan wani abu dazaka bukaci inyi maka a yanzu, kuma ina tabbatar maka zanyi shi batare da mishkila ko samun akasi ba, don Allah give me this one last chance, zan kasance mai bin umarninka batare da haufi ba.”

Ta ida zancen yayun datake zukunne ri’ke da kafafun shi, lokaci guda tana wani irin kuka mai d’aga hankalin mai sauraro.

“Tashi kizauna.” Iya abinda ya furta kenan batareda ya k’ara kallon fuskarta ba data rine tai jawuur sabida tarin tashin hankali da yawan kuka.

Zama tayi d’in kamar yanda yabukata tana mai k’ok’arin tsaida hawayen dasuke ta tsere bisa kuncin ta, hak’ik’a tafi kowa sanin abu talib yanzu, he has money, power and everything that can take someone down in an instance! Shi d’in wani gwaska ne mai zaman kanshi.

“Sameera zanniya yafe maki laifukan ki agareni, idan har kikai k’ok’arin yin abinda zan sanya ki idan bukatar hakan ta taso, amma mark this at the back of your mind, wallahil azeem i will never ever halt in making your bitchy life miserable idan kika kuma failing dina a karo na biyu ba, agreed?”

Da saurinta take d’aga kanta alamun ta yarda, kana kuma tai amfani da makoshin bakinta wajen k’ara jaddada mashi cewar she is willing to risk her life domin ganin ta faranta mashi a wannan karon.”

Jinjina.kanshi yayi alamun fahimta, kana batareda b’ata lokaci ba yabata umarnin tafiya, akan zaineme ta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

This is Mr Abutalib Tafeeda.

***
Wasa wasa saida safwan ya share sama da kwanaki biyar yana bulayin neman ramlah batare da yabari kowa yasan da b’atan ta ba, zuwa wannan lokacin zamu iya danganta rayuwar safwan a wata iriyar bahaguwar rayuwa mai dauke da tarin kalubale da matsaloli, wanda izuwa wannan lokacin kallo guda zakai mashi, kasake waigowa kamashi kallo na biyu diba da yanda gaba d’aya ya sauya, tashin hankali yasanya ko abincin kirki baya iya tsayawa yaci, wanda yake ci din ma don dai yayi surviving neh, har yasami damar nemo ramlah.

A kwana na biyar d’in neh yai k’ok’arin sanya bilal cikin iftila’in rayuwar dayake ciki, a inda taahin hankalin da bilal  d’in yashiga yaso ya zarta na safwan d’in diba da irin k’aunar dake tsakanin su.

Yayi fad’a, yayi fad’a sosai da sai da aka dauki kwanaki sannan safwan d’in ke sanar dashi wannan babban tashin hankalin.

“Aboki ka fahimceni, bansan tayaya zanfara gayawa wa mutane cewar matar ta was kidnapped by someone claiming to be me, saboda Allah bilal ta yaya zanfara fuskantar su hajiya da maganar nan, hak’ik’a ina cikin tsaka mai wuya bilal, my life is about to get shattered, sabida me za’a zo har cikin gidana asace mani mata? Menayi wa koma waye wannan yake k’okarin tarwatsa mani ragowar rayuwa bilal? What have i done for heaven’s sake?”Zuwa wanna lokacin, fad’ar irin tashin hankalin da zaratan mazan keh ciki ma b’ata baki neh, bilal d’in neh yake da sauran courage d’in dayake kwabtar wa da safwan d’in da hankali.

” It’s okay safwan, in sha Allahu everything will be okay kajiko? Abinda nakeso dakai ka yawaita amabaton innalillahi wa’inna ilaihirraju’oon, da yardar Allah komi zaizo da sauqi,gobe zanbiyo flight d’in karfe takwas domin musan ta ina zamu fara,su hajuya kuma don’t tell them anything yet har sai nazo, zamusan yanda zamuyi su fahimci komi okay?mucigaba da addu’ah, indeed with every hardship there is relief.” 4

“Shikenan bilal, zanyi  yanda kace d’in, and i hope and pray komi yazo da sauk’i ta bangaren hajiya, domin yanzu itace babban tashin hankali nah, inafatan su fahimceni kamar yanda ka fahimce ni bilal.”

“Karka damu komi zaizo da sauqi, just keep on praying, ina tareda kai aboki, akowanne hali ka tsinci kanka, kaikasan hakan.”

“Nasani bilal, zandawwama ina godewa Allah da kasantuwar ka amini nagari agareni….” 4

“Allah abin godiya.” Suka ambata a tare.



Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *