SAWUN BARAWO
CHAPTER 7
Misalin karfe biyar da rabi na asubahin ranar data ke daidai da kwana shidda da b’atan ramlahnne hajiya ta doko wa safwan din waya da farar safiya. 1
Harga Allah batasan miyasa jikinta yak’i yi mata dad’i ba tun kwanaki hud’un dasuka wuce, sannan dad’in dad’awa ga wasu muggayen mafarkai da ita kanta in an tsareta bazata iya kawosu ba dasuka bi suka addabi rayuwar baccinta matuk’ar zata sanya hakarkarinta domin yin bacci
Hakan yasa a wayewar garin na yau, tai hanzari gami da yin hobb’asa domin jin awani mataki diyar tata take kota sami peace if mind, karin mamakin ta shine yanda yau kusan kwana bakwai kenan tun barin su safwan d’in daga gidan, amma ko waya babu wanda yayo musu, hana karya kwanaki biyar dasuka shige inna tace sunyi waya da safwan d’in. 1
Cikin baccin dayasamu ya dauke shi bayan ya idar da sallar asubahi neh yaji wayar shi na neman agaji, a kasalance ya mik’a hannu domin ganin isashshen dake mishi wannan kiran da farar safiya. 2
A zabure ya mike zaune sakamakon ganin sunan hajiyar dayayi a kan screen d’in wayar tashi, hakan yasanya take ciwon kan daya d’an sarara mishi yanemi dawowa babu shiri, take kuma gabanshi yacigaba da faduwar rashin sanin abinyi, hakan ya janyo har kiran ya katse batare da yasami ikon dauka ba. 1
Ko kafin yasake sanin abinyi, wani kiran yasake shigowa wayar, zuru yayi yana mai cigaba da kallon wayar nata ringing, harga Allah baisan mizai ce wa hajiyan inya dauka, domin kuwa tabbas yasan k’arshen ta tace mishi da diyar ta takeson magana.
Wannan karonma kiranne ya yanke batareda yasami kuzarin dauka ba. Hakan yasa ya dafe kanshi yana mai rattafo addu’o’in samun sauqi bisa lamarin dake nema ya girmi tunani da hankalin sa, ba shakka idan da wani zaice mishi zai tab’a shiga mawuyacin halin kwatankwacin wannan dayake ciki, toh hak’ik’a daya karyata hakan, diba da irin hali irin nashi, dakuma d’imbin damammaki da Allah yake bashi aro. 1
Tunanin sa neh ya datse sakamakon sake shigowar kiran, wanda wannan karon shahada yayi gamida tattaro sauran kuzarin daya rage mishi ya dauki kiran.
“Safwan Mainasara on the line….” Kamar kullum ya furta abinda yasaba furtawa matuk’ar zai dauki waya.
“Ina ka aje waya nake ta faman kira ba’a dauka?” Ta fad’a a dan zafafe.
“Kuyi hak’uri bana kusa neh, dafatan kuntashi lafiya?” 2
“Lafiya lau, ina ramlahn take? Bani ita zanmata magana, tunda wani sabon salon iskanci kuka koya baku iya neman mutane ba.”
Ji yai kanshi yayi wani mugun sarawa, hakan yasa ya hadiye wani miyau ba shiri, take kuma ya shiga neman karyar daya kamata ya yayi wa hajiyar domin gujewa tambayoyin ta ayanzun d’in
Kasantuwar shi mutum wanda baisaba k’aryaba, hakan yasa gaba d’aya yarasa ma yaya zai fara k’ak’alo zancen bogin dazai rufe bakin hajiyar, hakan yasa yafara sosa keya yana in’ina. 1
“Ammm dama….” sai kuma yai tsaki domin rashin sanin inda zai dosa.
“Kai banson shirme, kanka k’alau? Malam wuce kaje ka kai mata wayar ni inbaka da abin fad’a.”
Da sauri yace “Nifa bana gida neh, sai dai inna koma sai inkiraku.” yasamu ya shirga mata wannan karyar, wacce tasaka har gumi neh keh tsiyayo mashi sakamakon rashin sabo. 1
“Toh gidan ubanwa kaje da asubahin nan? Watoh safwan va dai zaka canza hali ba koh? Na dauka zuwa yanzu ansamu cigaba cikin iskance iskancenka, ashe ba haka bane, ashe bazaka tab’a canzawa ba ko safwan? Bakomi Allah ya shiryaka.”
Ta karasa maganar da alamun baccin rai a sautin muryar tata, harga Allah da tunanin ta naga cewar komin yayane yanzu kila asami sauyi daga halayen safwan d’in, kodaon albarkacin aure dake rataye a wuyan shi yanzu, ashe ba haka bane, hasashenta na banza neh kenan, tunda kuwa gashi har yanzu bai fasa fita galgal d’in shi ba. 1
Shafo sumar kanshi yacigaba dayi cike da rashin sanin abinyi, lokaci guda yanajin tamkar laifukan shi na k’ara ninkaya neh, ba shakka hajiya na daga cikin mutanen da baza su tab’a fahimtar shi ba a yanzun, amma ya aka iya da k’addara?
“Kuyi hak’uri, danakoma zan kiraku, amma inason kusan cewa ba abinda kuke tuntunani bane ya fitar dani, don Allah kurika yi mani kyakkyawan zato hajiya.” 5
Jitai jikinta yayi sanyi, amma batareda tabari ya fahimci hakan ba ta datse kiran bayan ta tabbatar mashi da cewa tana nan tana jiran ji daga gare su.
Komawa yayi ya jingina da allon gadon yana mai lumshe idanun sa, lokacinguda yanajin wani abu mai nauyi ya tokare kirjin shi,”shin waye zai fahimce shi?….. Waye zai yadda dashi? Haka zalika waye zai tayashi neman ta? In fact ta yaya ma zai fara neman nata?”
Ya runtse idanunshi cike da godewa Allah bisa wannan shafin k’addarar tashi da’aka bud’o….”Allah gani gareka!” ya furta a hankali.
***
Cikin awanni biyu da isowar bilal garin, abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda kai cigiyar ramlan gidajen labarai dasuka had’a da gidajen redio, television, da gidan jaridu, wanda hakan na d’aya daga cikin shawarar da bilal d’in yafara badawa tun isowar tashi.
Daga nan basui kasa a guiwa ba suka nufi duk wasu division division na police suka mik’a report, wanda zuwa wannan lokacin har anfara gudanar da binciken musamman ta kafafen yad’a labarai.
A daidai lokacin da suke hanyar tafiya gidan su safwan d’inne domin sanar dasu abinda keh faruwa neh kuma a daidai wannan lokacin nabila da kakus keh zaune a main falon gidan suna kallon labaran kasa a tashar ta NTA, wanda ba karamin daga akasha ba da inna akan sanya tashar NTA d’in, diba da yanda tai bake bake ta hana nabilan kallon tashar bollywood datakeyi k’iri da muzu, wai ita labarai zataji, wanda saika rantse da Allah jin turancin take bare kuma harta fahimci abinda ake cewa. 1
Takaici yagama kashe nabila diba da irin yankar k’aunar da innar tai mata, wanda alokacin ta k’ara jin takaicin lalacewar plasma d’in ta dake dakin ta, da menene ma zai fito da ita nan, bare har kakus ta nuna mata karfin mulkin mallaka.
Tsaki tayi tacigaba da danna wayarta, domin ita duniya idan da akwai abinda ta tsani kallo, toh bai wuce news da ball ba, sam basa gabanta kuma bata tab’a jin tana ra’ayin kallon su ba.
Ihun da innah tayine da karfi ysa nabilan cire ear piece d’in data makala a kunne, tajuyo tana harar innar, ba shakka kakus bazata tab’a canza hali ba, domin kuwa matuk’ar zata zauna kallon tv toh hak’ik’a sai ta addabi jama’ah da iface iface, musamman intaga abinda ya d’an danganci abinda tasani neh.
Dauke kanta nabilar tayi batare data kalli fuskar tv d’in ba, inda sabo yaci ace tasaba da halin innah, amma ga mamakin ta sai taga har yanzu kakus d’in bata dena tafi ba gamida wangale baki cike da jin dad’i ba, lokaci guda tana mai k’ara gyara zama tana karewa fuskar hotunan ramlan da aketa haskowa a fuskar akwatin talabijin d’in, tareda zuba zantuttukan dasuka shafi hoton cikin harshen turanci, wanda sam bawai nabilan ta maida kai bane ballantana ma ta lura taji me reporter d’in ke b’ab’atu akai
Dad’i neh yagama kashe innah a inda take zaune, domin kuwa har alokacin baki wangalau take sake gyara zama tana mai kura wa tv din idanu, meya kai wannan abin farin ciki, ka hango wanda kasani a fuskar akwatin talabijin? Ai ita kau yau take sallah agareta, jikanyarta ce haka take ta zuba murmushi a cikin tv. 2
Shigowar su safwan falon yayi daidai da gama zuba rahoton bacewar Ramlah tafidan, wanda alojacin idan ka dubi fuskar innah kai ka e yau taje sallah neh, duba d ayanda dukkan farin cikin duniyar nan ya isheta, hakan yasa tundaga sallamar su safwan d’in dataji yasa ta mike tana masu lale lale da zuwa, bakinta kuwa sam yaqi rufuwa, gaba d’aya ta k’osa su zauna domin basu wannan dad’d’an labarin, domin kuwa gani take kaf zuri’ahr tasu ita kad’ai Allah yabaiwa damar ganin rablatun a akwatin tabijin d’in.
“Lale lake da zuwan yaran kirki.” inna ta rik’a fad’a cike da jin dadi, wanda hakan yasa sam bata lura da yanayin jikan nata ba,burinta kawai su zauna tahau rattafo zancen dake cinta a rai.
Nabilan ce tashige domin kawo wa bilal d’in abin sha bayan ta gaishe su, wanda a zuciyarta kuma ta rik’a mamakin abinda ya ramar da yayan nata haka, domin kuwa idan ba idanunta ke mata gizo ba, har wata suma yatara akai, ga kuma kasumbar data ke nema ta mamaye dukkan fuskar shi sakamakon rashin samun kwanciyar hankalin dazai tsaya gyaranta ma. +
“Inna munsameku lafiya?” cewar bilal kenan yana d’an k’ak’alo murmushin dole, domin kuwa tabbas yasan babbar k’alubalen su ta farko inna ce.
“Lafiya k’alau bilalu, ince duk mutan gidan na lafiy dai ko?”
“Duk kowa lafiya innah, suna gaisheku.”
“Madallh aiko muna amsawa.” Ta ida zancen da zallar murna a sautin ta, wanda hakan yasa safwan dake gefe kanshi a sam ya dafe kannashi mamakin abinda keh sanya sweetheart d’in tashi jin dad’i haka, wanda take yanke ya rik’a jin sabon bacin rai domin tuna yanzu wannan murnar tata zata koma bacin rai.
“Yaron kirki, ai tundazu na k’osa inabaka labarin abunda nagani a talabijin yanzun nan ba dadewa.”
Da sauri yadago kanshi gamida gyara zamanshi, wanda dukkan numfashin dayakeyi na tafiya neh da faduwar gaba,amma mamakin shine ya datse ganin babu alamun masifa ko bacin rai akan kyakkyawar fuskar kakar tashi, hasalima wani jin dad’i ya lura na haskowa daga fuskarta, diba da yanda take ta wangale baki.
Bilal neh yasami kuzarin tambayarta abinda tagani d’in.
“Kai dai bari, ai ingaya muku rablatun mu tanan gidan nagani a cikin talabijin sai doka murmushi take, abun bazai k’ara birgekaba sai irin yanda aka rik’a hasko hotunan rablatun ana kwararo turanci cike da iyawa da kwarewa, dake waccan takwalar nabilan wawiya ce, bata da rabon ganin rablatun diba da yanda ta maka wannan zaren wayar a kunne, duk don nace ni labarai zan kalla, ashe zanci karo neh da wannan abin burgewar, ohh ni rakiyya dad’i kasheni yau naga rablatu a talabijin.”
Gaba d’ayansu shiru sukayi aka rasa maj bakin magana, hakan yasa dariyar datake ta fara raguwa, kana ta rik’a binsu da kallon ni zaku bada wa kasa a idanu?
Kici kici tayi da fuska, ganin duk yanda ta dage d’innan tana basu labari mai dad’in sauraro basu maida hankali sun nuna farin cikin su ba, hakan yasa ta sake dak’una fuska akaro na biyu, gamida kallon su shekeke tace….
“Amma ku d’in nan anyi kafirai kuma mashahuran yan wulakanci, inbanda baku da mutunci yaron kirki iyyye, indage ina baku labari irin wannan mai dad’in gaske amma ku kasa nuna jin dadin ku sabida kafirar hassada data yi maku yawa? Mussaman kai yaron kirki, ashe dama bak’in munahuki neh kai, tunda abin murna da farin ciki yasami matarka ka kasa koda tafi neh ko murmushi da zai nuna kana maraba da wannan cigaban data samu, ba shakka kaji haushi wallahi ahi tallahi kabani mamaki yaron kirki, kodayake ni meye ma nawa, tunda nidai harga Alllah nasan ni babu digon hassada ko misk’ala zarratin a cikin wannan tsohuwar zuciyar tawa, banzaye kawai.”
Sai kunga yanda take huci kamar wacce ta had’iyi kunama, gaba d’aya idanunta sun rufe bata ko lura da yanayin zaratan mazan dake zaune a gabnta kai a sunkuye, inbanda gumi babu abinda suke, mussaman safwan dayakejin tamkar yatashi ya tsere, domin kuwa jikin shi yagama bashi irin ubanshin da zai ci ahannun kakus da zarar ta fahimci abunda takewa b’ab’atu ba gaskia bane. 3
Dauke kanta tayi tana cigaba da huci, lokaci guda ta rik’a jin haushin wannan irin bakin hali na su safwan d’in, ace mutum sam babu abinda suka sanya agaba sai tsabar hassada da bak’in ciki? Tai kwafa cike da jin tamkar ta tashi ta musu tsinannen duka.Sake hasko hotunan ramlan da akayine, yasanya takuma wangale baki wangalau tana sake gyara zama, wanda zuwa wannan lokacin harta manta da haushin su safwan d’in datakeji, kira take “Yawwah yaron kirki, kagani, kaga abinda nake gaya muku koh? Oh ni wai yaushe ramlah ta shahara neh haka bamu da labari yaron kir…..”
Zubewar farantin dake dauke da abubuwan sha a hannun nabila ya taimaka wajen datse maganar da innar keyi, wanda gaba d’ayan su suka waiga ta inda nabilan keh tsaye a sandare, idanu a waje, hannu dafe da kirji.Innalillahi wa’inna ilaihirraju’oon” kawai safwan keh ambata, sanin musabbabin abunda ya firgita nabilan har ta ke zubar da tiren hannun ta. +
Innah ce ta rik’a watsa wa nabilan harara, domin kuwa har yanzu bata dena jin haushin biris d’in da nabilan tai mata ba, dad’in dad’awa ga wannan b’arnar data k’ara bugawa yataimaka wajen k’ara hasala innar. 3
“Amma dai nabila bantaba ganin shashasha irinki ba, halan talabijin d’in neh baki tab’a gani ba har kike tuntube tamkar sabuwar makauniya?” 1
Nabilan ma tasan tanayi, gaba d’aya idanuwan ta a zare suke, kafe bisa fuskar tv d’in, lokaci guda kuma kunnuwanta da idanuwanta nasake shaida mata abinda keh fitowa daga bakin mai rahoto na tashar NTA.
“A young girl of 19 years of age bearing the name RAMLAH TAFEEDA(Mrs) has been kidnapped six days ago, at her matrimonial home in kaduna state nigeria. Please incase of any information concerning the victim, we hereby request you to please contact us or any of her family members via the following details…… “
“Wayyoh Allah na, innalillahi wa’inna ilaihirraju’oon…. Mun shiga uku, ya safwan garin yaya? Garin yaya aka sace ramlah? Yaya…. Wayyoooh….” sai kuma muryarta ta sarke sakamakon kukan da yaci karfin ta, wanda zuwa wannan lokacin ta riga ta dade da kaiwa k’as tana gumshekan kuka cike da tashin hankali.
Zuwa wannan lokacin innna ta riga data fara rudewa ganin irin ihun kukan da nabilan take, lokaci guda kuma idan ba kunnuwanta neh keh jiyo mata karya ba taji nabilan na ihun sace ramlah? Yoooh me ake nufi da sace ramlah? Inbanda iya shege ta yaya za’a sace d’an mutum kamar wani kiyashi?
“Keh dallah banson hauka, halan kisami tabin hankali neh? Kuji min shegiyan yarinya da janyowa mutaneh alkaba’i ana zaune kalau!ke kam dai kinji haushi, haka kurum muna cikin nishadiin mu zaki tayas mana da hankali,’yar jakar uba mai suffar ‘yan ruwa….Dallah tashi kibar….. ” 1
Fadowar kabeer falon tamkar anjehoshi yasanya innah dakatawa, lokaci guda su safwan dasuka gama sandarewa a zaune sukai hanzarin kallon kabeer d’in dake ta zabga zufa tamkar wanda yasha tseren gudu.
Kallon dayake bin safwan d’in dashine yasanya safwan d’in bajintar dauke kanshi gefe, ba shakka yasan ba k’aramin tashin hankali neh keh dumfaro shi ba, daga dukkan kallon da yayan nashi keh jifanshi dashi yasan yagama tsintar abinda keh faruwa shima.
Cikin kakkausar murya yace….. “Safwan meh nakeji na faruwa? Me kunnuwana suke jiye mani?wane irin banzan zance neh haka nake tsinta?Ansace ramlah? Garin yaya aa sace ramlah har cikin gida? Kana ina aka sace matarka safwan?” ya ida zancen yana mai kafe safwan d’in da wani irin kallo mai cike da ma’anoni
“Nikaina tambayar danake yi wa kaina kenan, har yanzu nagaza samun amsoshin tambayoyin dasuke barazanar fasa kaina, bansan garin yaya aka shigo har gida aka sace ramlah ba kabir,ku fahimce ni.”
“Kai jaaa can shashasha…. Lahaula wala kuwwata…. Yau nake jin abinda yafi karfina!yaron kirki sata fa naji kuna magana akai? Sata?garin yaya za’a sace dan mutum haka har ba’a saniba? Kana ina aka zo har gida aka sace yarinyar mutane safwan? Shege kana can yawon gantalinka na bin matan banza bayan ga halalinka nan a gida, amma dayake kai d’in dan banza neh mai mance alheri katafi kabar er mutane a guda har aka shigo aka sace ta! Yau munshiga uku mun lalace. ” habawa ai sai innah aka b’arke da kuka, wanda zuwa lokacin harta kai kasa tana shirin fara birgima.Bilal neh yai k’ok’arin tallafe kakus d’in, lokaci guda yana mai k’ok’arin fahimtar da ita, amma inah…. Kakus bata jin kira inbanda kuka babu abinda take, lokaci guda tana zubawa safwan d’in kwandunan zagi iri iri.
“Duk inda ka kaimani yarinya, ina mai shawartarka daka hanzarta zuwa kaa fito mani da ita, nabaka daga nan zuwa yamma!”
A firgice kowa dake falon yadago kanshi gamida bin mai maganar da kallo.
Tsaye take ta wajen corridor d’in dazai sadaka da falon, fuskar nan a had’e tamau tamkar hadari, wanda inba mugun sani kai mata ba zaka dauka bata tab’a wani abu waishi annuri ba.
Daga haka bata k’ara cewa komi ba ta juyaah fuuu kamar kububuwa ta bar su gaba d’aya cikin tashin hankali, mussamamn safwan dayakejin wani zafi na taso mashi daga kirjin sa.
“Shin mi hajiyarsu keh nufi da ta bashi nan da zuwa dare ya kawo mata diyarta? Idan da yana da wannan ikon suna tunanin da tuni ba’a dade da wuce wurin ba? Shin da wanne ma tukunna ake so yaji? Daga dukkan alamu danganta b’atan ramlan ake akanshi!” 1
Zuwa wannan lokacin bakajin sautin komai inbanda kuka innah da nabilah, yayin da safwan, bilal, da kabir d’in suka rasa kuzarin basu baki, toh mema zasu ce neh? Tashin hankali yakai tashin hankali.
Innah har lokacin bakinta bai mutu ba, kira take…
” Munahukin Allah ta’alah, haba, ashe da walakin goro a miya, yau kusan sati d’aya kenan rabonka da gidan nan, ashe kasan abinda ka k’ullah…. Yaron banza yaron wofi, kaikam dai sai kaci uwarka a cikin gidan nan matuk’ar baka fito mani da jikata ba, bak’in mugu mai bak’in hali….. ” ta cigaba da rera kuka tamkar mai shirin shid’ewa.
” Don Allah innah kuyi shiru hakan nan, in sha Allah za’a ganta, tunda har munsaka cigiya gidajen redio da jaridu, addu’ah kadai yakamata mudage dayi, domin ganin al’amura sun daidaita, kuyi hak’uri inna don Allah…. Kuyi hak’uri.” cewar bilal duk don ganin ya kwantar masu da hankali.
” Toh naji, dama ai addu’ah tazama dole bilalu, addu’ah tazama dole, oh ni ‘yasu duniya ina zaki damu? Yarinya salaha irin wannan, ga hak’uri da kawaici, amma b’arawo yarasa wa zai sace sai ita? Bayan ga mashahurin k’atoh nan, ai dashi suka sungume ba wannan siriryar yarinyar ba… Saboda Allah fa iyyyiiih” 4
“Hakane innah,duk abinda kukace hakane tabbas, saidai kamar yanda nace d’in neh mucigaba da addu’ah, bi’izinillah komi zaizo da sauk’i.”
“Amin dai d’an nan, Allah dai yai maka albarka yaron kirki yaron albarka, mungode kaji ko?” tanayi tana zubawa safwan harara, wanda zuwa wannan lokacin bayama fahimtar duk wani abu daake cewa a falon, komi ya tsaya mishi.. Babban tashin hankalin sa shine yanda zaiyi da hajiyar sa.
” Allah kakawo mani d’auki” ya rik’a maimaita hakan a kasan zuciyar shi. 1
***
BIRNIN IKKOH, LAGOS NIGERIA.
Zuwa yanzu data kai kimanin kwanaki shidda da wabzuwarta cikin garin na lagos, a cikin wata unguwa da har yau bata da masaniyarta, hasalima dalilin dayasa ta gane cewa a lagos d’in take shine ta hanyar ganin location d’in da wayar ta ya nuna mata tun lokacin data farka daga dogon baccin daya dauke ta tun bayan fara tafiyar su zuwa gidan hajiya ita da safwan d’in.
Mamakin taneh ya k’ara karuwa lokacin da ta farka ta tsinci fuskar safwan d’in na zaune gefen gadon datake yana kare mata kallo, bakin shi dauke da murmushin da har yau takasa sabawa da shi daga gareshi…. This is unlike him.
“Babyna ta farka kenan?” 4
Saida ta yamutsa fuska gamida d’an dafe kai sabida wani guntun ciwon kai dake barazana da ita, kanta ta d’aga alamun eh, kana ta bukaci sanin dalilib daya sa sukazo lagos a maimakon gidan hajiyan.
“Wani kiran gaggawa neh yasameni, batun aiki neh, kinsan bazai yiwu yanzu tunda nauyi ya hau kaina ba inzauna babu aikin yi, we have to survive you know?”
“Amma yaya ko kaya fa bamu dauko ba, yanzu haka i want to change kuma babu abun canzawar.” ta fada tana mai k’ara kallon shi, ya canza mata k’warai dagaske.
“Nasan da haka, shiyasa na tsaya na sama mana abubuwan dazamu bukata har zuwa lokacin da zangama abinda yakawoni mukoma, ban manta bama harda pad na siyo maki”
Ya ida zancen yana mai janyo wata fara k’al d’in leda mai dauke da tambarin wani shopping mall datafi tunanin may be a lagos d’in yake, don bata san sunan ba.
Sunkuyar da kanta kasa tayi tana dan murmushi, ba shakka kamar yasan abinda keh ranta kenan.
“Oya jekiy freshen up, kafin nan na nema mana abinda zamuci.”
Gyada kai kurum tayi tana mai bin dukkan wani motsin shi da ido, “He’s ao different now.” ta ambaci hakan a kasan ranta. 4
Hanyar fita yayi, kafinnya karasa ficewar sai ya dakata gami da waigowa yana mata wani irin kallo, wanda zata iya rantsewa da Allah bata tab’a ganin mahalukin daya tab’a yi mata irin kallon ba.
Hakan yasa tai hanzarin sadda kanta k’asa tana maijin yanda kallon nashi keh bin dukkan sassan jikin ta.
“Inafatan period dinnan yana gab da kaucewa? Coz I’m dying to start my angwanci very very soon.” ya ida zancen yana mai dage girar shi guda, wanda zuwa wannan lokacin tafara sabawa da sabon halin na safwan. 9
Harararshi tayi k’asa k’asa batare da tace komi ba, lallaima ya safwan d’in nan yama latsa ta, shi harma tunanin wannan abin yake? Allah ya kyauta mata ita kam, domin kuwa alk’awari tayi babu ita babu wani d’a namiji a duniyar nan, har yaushe take da wannan guts d’in na sakar ma wani da namiji jikinta da sunan having sexual intercourse? Haba har abada wallahi.Anyway, Tunda bazaki bani amsaba, nidai just make sure bak’on nan yakama gabanshi as soon as possible, because somebody here is dying of hunger…..” Daga haka yasanya kai gamida karasa ficewa daga dakin.
Binshi da kallo dai tayi har zuwa lokacin data daina hangoshi, lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya, lallaima mutumin nan, dalilin dayasa yataho da ita lagos d’in kenan? Lallai namiji ma baida ta ido, amma inba haka ba duka duka yaushe suka shirya da har zai fara batun neman hakki? Da sake…. Itakam baza ai wannan iya shegen da ita ba wallahi, garama tun wuri ya rik’e kirkin shi dayake yi mata, wanda sai yanzu ta fahimci dalilin sauyawar tashi, ashe da abinda yake dako a birnin zuciya? Aikam zaiga karyar rashin kunya matuk’ar yace zai dameta da wannan zancen, ita ashirye ma take da ta wareh takoma gida abinta , ai ba dole bane zaman nata a nan d’in.
Haushi neh yakamata data ga babu wayarta a gefen ta, tuna zancen shi na dazun tayi…. “Yawwa bani wayarki, coz banason wani ya damemu, irin su kakus da nabilah, honey moon namu zamu fara soon.” 1
Daga haka ya dauke wayar tata ya kasheta gaba d’aya, wanda a lokacin shiru kurum tayi tana mai binshi da idanuwa, gamida tabe baki jinnya ambaci honeymoon.
Ganin tunanin babu inda zai kaita yasanyata nufar band’akin domin yin wanka, dukkuwa da cewar tana tunanin zuwa anjima ma ko gobe kila tasamu tsarki, domin kwana uku zuwa hud’u takeyi intana fashin sallah.
***
GARIN GWAMNA, KADUNA NIGERIA
Zuwa wannan lokacin sun dade da baro can family house d’in nasu safwan, wanda da k’yar da ya Allahu aka samu innah tayi shiru ta daina surfawa safwan din kwandunan zagi, a cewar ta dashi aka had’a baki aka sace rablatun, ai dama baya sonta sam, kuma dama ya furta cewar zasui danasanin had’a auren nan da hajiyar tayi. 2
Koda suka koma gidan na safwan d’in ba wani abu suke iya tabukawa ba, gara ma bilal yayi k’ok’arin fita yaje yayo masu takeaway domin kuwa har laasar na neman sanyo kai basu samu sanya wa tumbinsu komiba tun wayewar garin.
Ko kallon abincin safwan d’in beyi ba, gaba d’aya tunanin shi yatafi a inda zaiga ramlan, ba shakka duk ranar da Allah yabasu sa’ar samun ramlan bazai gusheba wajan jaddada godiyar shi wajen ubangiji ba, sa’annan kuma bazai tab’a jinkirtawa ba wajen cin uban duk wanda yake da hannu bisa bacewar matar shi ba. 1
Tunanin sa neh ya katse sakamakon jin karar intercom d’in gidan, ko kafin subada izinin shigowa, har surar mutumin ta bayyana cikin falon.
Wanda kallo guda zakai mashi ka tabbatar da hak’ik’a yau ran emmaza ya b’aci, duba da irin wulakantaccen kallon dayake bin safwan d’in dashi.
Abutalib Neh.
Bilal neh yai yunkurin bashi hannu, amma ko bi takan hannun na bilal d’in beyi ba, yanemi kujerar dake fuskantar wacce safwan d’in yake ya zauna gamida daura kafa d’aya kan d’aya.
Saida yaja fasali kana ya dubi cikin idanun safwan d’in dake binshi da kallo yace……
“Nasan zuwa yanzu kasan musabbabin abinda yasanya ni takowa zuwa gidan mutumin daya zama shine abu na farko dake sanya katangar karfe da dukkan farin ciki na, lemme go straight to the point mr mainasara, karka dauka labarin bogin daka mik’a gidan jaridu da televisions zasui tasiri akaina? Karka dauka rainin hankalin dakaiwa sauran al’umma zaiyi tasiri a kaina! Karka dauka dukkan wannan fad’i tashin karyan dakake zaiyi tasiri akaina? Sam bakai nasaraba ta bangarena mr safwan, domin kuwa zan sanya a daureka har sai igiya tayi rarah idan bakai hanzarin fito mani da kanwa ba! To hell with you and your fuckin lies safwan! To hell with you nace, bari in fad’a maka abinda bakasan munsani ba….. “Ya numfasa cike da bala’in dake tattare dashi, kana yacigaba….” Let me tell you, maigadin gidanka ya tabbatar mani da cewa kaine mutumin da ramlah ta fita dashi last a cikin gidan nan! Basai na tambayeka hakane koba haka bane? Domin ni dakai da kuma CCTV cameran dake manne da main entrance d’in gidan nan sun shaida hakan.
Daga haka ya mike tsaye gamida yura dukkan hannayen shi a aljihu yace….. “Nabaka zuwa wayewar gari, kamaido mani da kanwata, idan bahaka ba…. Idan ba haka ba safwan, shariah nida kai yanzu muka fara.”
Daga haka ya sanya kai yajuya domin ficewa daga gidan, amma sai yadakata yayin daya rike handle din kofar falon gamida juyowa.
” Remember zaka amsa laifuka biyu neh a kotun! Na farko as a rapist ! Na biyu kidnapper! Get ready for the upcoming trauma Mr Safwan Mainasara.”
Garam ya buga kofar yayin da yabar safwan da bilal suna mai bin bayanshi da kallo….. Kallo mai cike da dimbin tashin hankali.Sautin suratul sajda keh tashi daga k’aramin dec din dake zaune a dakin baccin nashi, wanda tun wayewar garin yakasa tabuka komi tun bayan massalaci daya ziyarta domin gabatar da sallar asubahi. 3
A hankali yake bin karatun cikin kasan ranshi, wanda hakan ba karamin sauki yasamawa rikitacciyar zuciyar shi ba kwarai da gaske, hakika idan da wani zaiyi gigin gaya mashi cewar watarana rayuwar shi na iya juye mashi irin haka, toh hakika da ya karyata hakan, diba da yanda Allah yake bashi aron damammaki bila adadin, kuma yarika amfani da damammakin bisa gurbatacciyar hanyar da shi kanshi yasan ba mai b’illewa bace.
“Astaghfrullah” ya furta hakan a bayyane, lokaci guda yana mai sake juyawa bisa girkakken gadon italian din dake dakin baccin nashi, ba shakka yana hango tashin hankali gamida rikitaccen al’amari na tunkaro rayuwar shi, abin tambayar anan shine….. Shin ta yaya zai tserewa dukkanin masifun nan dake bibiyar shi? 1
“Komawa ga Allah, tare da tuba izuwa gareshi, taubatun nasuha, wacce zakayi ta don shi Allah din, dakuma nadama bisa shud’dd’un zunuban ka.”
Wani sashi daga sashukan zuciyar shi yayi azamar tuna mashi….. Sai dai me? Shin Allah zai yafe mashi bisa dimbin kura kuran daya tafka a iya tsahon rayuwar shi? Ya sake tambayar kanshi, wanda hakan ya janyo faduwar gaba mai tsanani tareda jin wani tsoron mahaliccin shi na shigar shi tamkar walk’iyah.
“Ubangiji mai yawan gafara neh, haka kuma shi din yakasance rahamar shi bata da iyaka….. Hakika Allah na yafe laifukan bawa koda yawan shi sunkai yawan teku neh, matukar shi bawan zaiyi tuba neh dawwamammiya kuma don Allah d’in, tare da alkawarin baza’a sake komawa sab’on ba har abada…. Allah mai tsaanin tausayi neh ga dukkan bayinsa salihai.”
Muryar shaikh Aminu Daurawa kenan daya tuna yatab’a ji yana waazi kan Tuba da sharud’d’anta, hakan yasanya jikin shi kara yin sanyi, lokaci guda kuma ya sami kanshi da tsananin jin kunyar mahaliccin sa, bisa dogon zangon da ya d’auka yana sab’a mishi.
“Allah na tuba, Allah na tuba, Allah na tuba ka yafemani.” Ya rika maimaita kalmomin sau ba adadi, a yayin da wasu hawaye masu zafi keh ziyartar kuncin sa. 1
Lumshe idanuwan sa da suka dade da kodewa yayi, zuciyar shi kuma na cigaba da samun nutsuwa bisa kintsatstsen tunanin dake k’ara mishi kusanci ga mahaliccin sa, lokaci kuma ya kara sakankacewa bisa yarjewa dakuma rungumar kaddarar dake bibiyar rayuwar shi….
Hak’ik’a bashida wata mafita ko shaida face ubangijin shi, wanda ya riga ya sakankace cewar shi d’in yana saneh dashi, kuma Hak’ik’a hakan na nufin wata jarabta ce daga shafukan k’addarorin shi aka bud’e.
Mik’ewa yayi zaune gamida sanya fuskar shi gaba daya cikin tafukan hannayen shi, yayin da zuciyar shi keh yanke mashi hukuncin dayake ganin hakanne daidai a gareshi, dakuma iya tsawon lokacin daya d’auka yana zaluntar rayuwar tasa, gamida sanya kunci da bakin ciki cikin zukatan mafi soyuwar mutane a gareshi.
Jinjina kanshi yacigaba dayi, yayin da jiki da ruhin sa suka aminta da hukunci dayake ganin shine daidai wa rayuwar shi, kila hakan da zaiyi yakara sanya mashi kusanci da ubangijin sa, kila hakan yazama sanadiyar da Allah zai karbi dukkanin tuban sa, kila hakan yazamo silar hucewar dimbin zukatan daya b’ata mawa.
Daga haka bai k’ara minti daya ba yamike gamida dauko diary din shi yayi wasu ‘yan rubuce rubuce masu k’arancin yawa, kana kuma a hankali ya shiga kimtsa jikin shi domin zuwa ya fuskanci sabuwar rayuwa mai cike da k’alubale dake fuskanto shi.
***Gaba d’aya ahalin gidan nasu yasama a tafkakeken main falo na gidan, kallo guda zakayi wa fuskokin su ka hango zallar damuwa da tashin hankali, mussaman hajiya dakuma nabilah dake kwance saman kafarta tana mai zubar da k’wallah.
Sallamar shi cikin falon yasanya duk suka maido da hankulan su gareshhi, da’alama zancen shi suke, sai gashi kuwa ya bayyana.
‘Yan mazanne sukai kokarin amsa sallamar shi,wanda yanayin kallon dasuke binshi dashi ya sanya yakuma himmatuwa domin son ganin yaje ya ida nufin shi kowa ma ya huta.
Kusa da salim yasami guri ya zauna, domin kuwa yau sam babu annuri ko fuska a gurin sweetheart din tashi dake ta balla mashi harara tun bayyanuwar shi a falon,wanda juyawar bayan na innah yakara taimakawa wajen kara afkawar shi cikin damuwa.
Hannu yabaiwa salim dake kusa dashi, kana ya mimmika wa kabeer da saeed sukayi musabaha, wanda hakan yazame masu bak’on al’amari, diba da baudadden hali irin na safwan, wanda ko wace iriyar haduwa zakuyi dashi a da, ba dai yabaka hannu ku gaisa ba tsabar iskanci da iya shege dake d’awainiya dashi a wancan lokacin.
Yuuuuu haka suka rik’a binshi da idanu tamkar sunga sabuwar halitta, domin kuwa gaba d’aya safwan din ya canza masu akan yanda suka sanshi a da…. Idan aka cire tsabar rama da duhu da yayi, sassanyan hali gamida wata iriyar kamilallaiyar fuska daya aza wa tsohuwar fuskar shi ma’abociyar d’aurewa da masifa da kowane mahaluki yasanshi da ita yanzu ta kau, babu ita sam bisa wannan sabuwar fuskar mai dauke da tsantsar damuwa da dimbin tashin hankali mabayyani.
Tun bayan gama gaisawa da mazan falon yakoma yazauna gamida sauke kanshi k’asa, hakika shi din mai laifi neh, hakan yasa gaba daya nauyin hajiyar shi yasa duk ilahirin jikin shi yin la’asar, amma batare da wani jinkiri ba ya dubi sashen inna dake hakimce bisa kujerar kusa data hajiyar tana wurgo mashi saqonnin harara, tamkar mai shirin tashi ta rufe shi da kafirin bugu.
“Sweetheart ina wuninku? Dafatan kuna lafi….”
“Uwar ma lafiya ce ba lafiya ba” ta katse shi gamida jefo mashi dak’uwa.
“Nace uwar lafiya ce ba lafiya ba, fitsararre mara mutuncin, inbanda tsabar baka da mutunci yaron kirki? Kadubi tsabar idanuna a irin wannan yanayin daka jefa mu kace muna lafiya? A ina zamuga lafiyar ma tukunna don uwarka? Shege mai bak’in,kadaiji haushi wallahi, karasa da wa zakaje kai kud’i saida matar ka, er uwarka yaron kirki? Shin kanason gamawa da duniya lafiya kuwa safwanu?
Ta ida magnar yayin datake rik’e hab’a, lokaci guda tanaji tamkar ta tsage da kukan bakon ciki, ba shakka ba’a son ranta takeyi wa jikallen nata wannan tijarar ba, amma dolece tasa tunda yariga da ya b’ata rawar shi da tsalleh
Tunda innah tafar rattafa ruwan masifar tata ya sunkuyar da kanshi k’asa, yayin dayake jin girman laifukan shi na k’ara yawa, hakika koda ace bashida hannu cikin sace ramlah, toh ba shakka amma yana da alhaki cikin takura wa rayuwarta tun batasan meke mata ciwo ba, hakkin hakan kadai ya isa yarik’a d’awainiya dashi, shin ina zai kai wannan hak’k’i? Ba shakka ya cancanci duk wasu cin kashi daga dukkanin bangare na mutane.
Ganin innar tayi shiru ne yasa shi fuskantar mahaifiyar tashi da tun shigowar shi falon bata kalli ko iskar data d’ebo shi ba, gaba daya hankalinta na kan akwatin talabijin d duk bayan awanni biyu sai sun nanata sanarwa gamida cigiyar diyarta.
“Hajiya ina wuni,don Allah kuyi hakuri, in Allah ya…..”
“Kai dakata mani mana, hala kamanta abinda na gaya maka jiya a gidan nan? Mena gaya maka jiya safwan? Mena gaya maka? Bance nabaka zuwa dare ba ka kawo mani yarinyata? Amma dayake kaidin maras mutunci neh, kuma baka daukeni abakin komi ba kai biris da maganata, sabida ka nuna mani kai cikakken dan duniya neh koh?”
” Bahaka bane hajiya, don Allah don sonku da annabi ku fahimce ni, wallahi talla… “
“Malam rufe mani baki, kakuma rik’e rantsuwar ka, wacce babu komi cikin ta sai zallar k’arya da son kai, jibeka bakaji kunya ba safwan, sabida tsabar zalunci, dakuma son ka nuna mani iyakata akan auren dana danai maka shine zaka je ka salwantar da rayuwar marainiyar Allah! Bakaji tausayi ba gamida duba iri amanar dana baka, kasanya k’afa katake gamida nuna mani kai d’in yaron zamani neh maras neman albarkar iyayen shi, ka nuna mani cewar dama ka rantse ko dawa nake yawo bazaka tab’a zama da ramlah ba ko safwan?” +
Ta numfasa yayin da muryarta ta fara rawa” Ka nuna mani kuskurena safwan, ka tunasar dani cewar uwa bata isa tayi wa danta abinda yakamata ba, dukkuwa da cewar d’an yakasance fand’ararre kuma maras tausayi ga mahaifiyar shi, ka tunasar dani cewar kai d’in nan ba mai biyyayar iyaye bane, haka zalika kayi nasarar wanzar da dana sani gamida bakin ciki mai d’orewa cikin zuciyata, amma fa kasani, ni bazanyi maka baki ba safwan, abinda nasani shine kaje wannan tsakaninka da ubangijinka neh, katashi ka b’ace manj da gani safwan, bana buk’atar sake sanyaka a cikin idaniyata, domin.kuwa kai d’in kazame mani ciwon a ido dukkan cikin y’a’yana,katashi kaje…. Katashi kaje naceeeeh……!” 4
Ta k’arasa maganar cikin kuka da k’araji, wanda ya sanya bama safwan d’in kadai ba, dukkan sauran mutanen dake falon tsorota…. Hakika basu tab’a ganin mahaifiyar su cikin tsananin fishi irin wannan ba, hakan yasa dukkaninsu sunkuyar dakai gamida sharar k’wallar dake sulmiyo masu a idaniyan su.
Zuwa wannan lokacin kuka sosai safwan yake sharb’a, kuka neh irin wanda tunda uwar data kawo shi duniya bai tab’a itin shi ba, kuka yake cike da sarewa da gaba d’aya rayuwar, kuka yake cike da jin zafin furucin mahaifiyar tashi a gareshi, kuka yake mai cike da dimbin tashin hankali da dana sani. 4
Rayuwa kenan….. Rayuwa juyi juyi, hakika da wani zai fada wa wani daga cikin yan gidan cew akwai watarana mai kaman ta yau da safwan zai zauna ya rika kuka kashirb’an haka, toh da sun k’aryata hakan.. Domin shi din yakasance mutum neh mai matukar taurin rai da zafin zuciya, yakasnce mutum mai wuyar sha’ani, haka nan yakasance mutum neh mai kafirar kafiya da jajircewa, hakika ba karamin abu bane zai saka shi kuka haka ba.
Guiwa bibbiyu yazube gaban mahaifiyar tashi a yayin da hawayen fuskar shi basu fasa rige rigen sauka ba, wanda dama basu samu damar samu a kula suba bare su dena fitowar.
“Hajiya na kasance mutum na Farko daya fara sanyaku kuka a dukkanin zuriar gidan nan, na kasance rai d’aya k’waya tal daya kasance mutumin banza a dukk kafatanin gidan nan, nasani hajiya nasan da haka, nasan da cewar laifukana masu tarin girmane da yawa, laifukana masu wahalar mantawa neh, laifukana masu daci neh da tsananin ciwo, amma duk da haka hajiya inaso kuyi mani wata alfarma guda d’aya a duniyata, inaso koda wannan alfarmar itace abu na karshe da zaku iya yi mani a doro kasa yazmana kunyi mani ita, ba donni ba hajiya, bakuma don mugayen halayena ba, sai don wannan alak’a dake tsakaninmu ta tsakanin ‘DA DA UWA!….. Domin wannan kadai hajiya nake so ku dubeni ku yafe mani dukkanin laifukana a gareku, kuyi mani wannan alfarmar hajiya don ya rasulillahi…. “
Kuka ya sark’e muryar shi wacce take tsananin rawa yayin dayake furta kalaman zuwaga jigon samuwarshi a doron k’asa.
Inbanda sautin kukan nabila bakajin komi a cikin falon, domin kuwa sautin nata ya danne na safwan d’in, wanda shi dama hawayene masu tsananinin rad’ad’i keh sauka bisa kuncin sa, innah kuwa dama ta dade da fara share majina sabida tsabar tausayin yaron kirkin nata, zata iya rantsiwa da Allahm daya halliceta bata tab’a ganin shi a irin makamancin halin dayake ciki ba yanzu, ba’a maganar su kabir da gaba daya jikin su yai laasar, tsananin tausayi da kaunar dan uwan su keh raysa dukkanin gabbansu.
Runtse idanuwanta hajiyar tayi gamida jin wata sabuwar soyayyar guda jinin nata na rufto mata, wanda yanzu haka dayake zube a gabanta takeji tamkar ta kamoshi ta lallashe shi neh bisa bayyanananen kuncin dake bisa fuskar shi, sai dai kaash! Laifukan shi masu tarin yawa ne! Laifukan shi masu tsananin muni neh! Laifukan shi masu mashahuran girma neh! Lallai laifukan shi ba ababen yafewa bane.!Hakan yasa ta kauda kanta gefe gamida cewa cikin kakkausar muryah “Safwan bazan tab’a yafemaka ba har sai ranar da ka bayyana mana ramlah! Ba zan tab’a yafe maka ba har sai randa idanuna sukai kicibis dana ramlah! Bazan tab’a yafe maka ba sai anbi mani hakk’in yarinya ta safwan, sabida haka katashi ka b’ace mani da gani.” +
Kirjinnshi neh yai mashi nauyin da bai tab’a yi mashi irin shi ba, sanin cewa kenan hajiyar shi bazata tab’a yafe mashi ba har gaba da abada kena? Domin kuwa bashida masaniya nisa inda zaiga ramlah….. Sai dai me? Tunawa da furucinta na karshe yasanya mashi kwarin guiwa, kenan sai bayan babu shi neh sannan zata iya yafe mashi?
Sassanyar ajiyar zuciya yasaki tuna hukunci da dama yariga ya yanke wa rayuwar shi, wanda yake ganin hakan neh kadai fansa bisa laifukan day dade yana tafkawa a doron kasa. Daga haka yace wa hajiyar tasu “Nagode da alfarmarki a gareni mammy, zankuma dawwama ko bayn babu ni ina gode maki bisa tarin alkairanki agareni.”
Kana daga nan yajuya ya fuskanci yan uwanshi gamida sake basu hannu sukai musabaha yana mai sake neman yafiyar su.
Kafin yakama hanyar fitane ya tsugunna gamida rike hannayen kakus, lokaci guda yana mai sakaye fuskar shi da wani marayan murmushin da bai kai zuci ba, wanda zuwa wannan lokacin inbanda tsiyayar hawaye babu abinda innah keyi, batasan meyasa jikin ta keyi mata wani iri ba, bata san meyasa take hango wani babban al’amari na tunkaro su ba a karo na biyu ba, batasan meyasa take jin tsananin tsoro na mamaye zuciyar ta ba, hakannyasanya takasa cewa uffan ta kurawa kyakkyawar fuskar tilon yaron da tafi so da kauna kaf zuriar su.
“Zantafi sweetheart, kisamani albarka.” ya furta yayin dayake matse hannayen ta anashi. 8
Tsananin hawayen datake yasa takasa magana, sai afkin kallonshi datakeyi, yayin da ta rik’a sanya mashi kwandunan albarka ta can kasan zucciyarta.
Mikewa yayi da azama, zuciyar shi cike da tarin al’amura yanufi hanyar ficewa daga mutanen dayafi kauna kaf duniayr shi, yanajin tsananin kewar su tun yanzu tana shigar shi, batareda ya saurari kwalla kiran sunan shi da innah keyi ba, ya tunkari hukunci gamida sakamakon abinda shafukan kaddarorin sa suka bud’o mashi.BIRNIN IKKOH.
Zuwa yanzu ramlah tafara sanya alamar tambaya akan safwan din dake tare da ita, ba komai ya jawo hakan ba, illah sabbin dabi’un dake bayyana a tattare da wannan din wanda suka sha banban da na asalin safwan din da tasani a da.
Dad’in dad’awa yanda wannan din yake yin mirsisi da idanun shi ya rik’a soko mata zantukan soki burutsu da kan shallake tunanin ta a lokuta da dama, sai dai kuma wani abin mamakin shine yanda mutumin kuma ya dena yi mata zanceb son kasancewa da ita kamar yadda ya fara a tun farkon zuwan su lagos din, domin kuwa zuwa yanzu da suke neman tasarwa kwana takwas a garin na ikko bai kuma gigin kara kusanta kanshi da itaba tamkar wanda akai wa baki.
Kamar kullum idan garin Allah ya waye, shi keh fara zuwa dakin data ke ya gaisheta tareda jin lafiyan ta, daga nan kuwa idan ya sanya kai ya fice, sai kuma dare gab da lokacin da take shirin sanya hakarkarinta domin hutawa, daga lokacin da yai mata sai da safe kuma shikenan, sai kuma garin Allahn ya waye su sake haduwa
Da farko abun baya damun ta,amma zuwa wani dan takaitaccen lokaci saitaji ta gundura da irin zaman da suke, gaba daya rayuwarta sai takejin ta tamkar a gidan yari, dukkuwa da cewa duk wani jin dadin rayuwar duniya akwai shi a cikin gidan, babban abinda yafi bata mamaki shine yanda kiri kiri ya rabata da wayar ta balle ta kira gida taji muryoyin su, hakan ya sanya mata tsananin kewar su fiye da tunanin mai karatu. 2
Kamar kullum dai yauma kwance take a dakin da yazama mallakinta neh tun isowar su garin, agogon gefen gadon ta kalla, a inda ya nuna mata karfe goma sha biyu saura kwata, ganin yanayin lokacin baisa ta fasa jin son tunkarar safwan din ba a yau domin amsar wayar ta dake hannun shi, hakikanin gaskia tana matuqar son jin muryar mammynta, nabila, kai harma da kakus, ga kuma oga kwata kwata her beloved yaya talib da kewar shi keh barazanar tafiya da ragowar juriyar ta.
“Shin mi ya tsaida ya safwan din yau haka da har yanzu kusan karfe sha biyu bai dawo gida ba?” Ta cigaba da tambayar kanta, domin kuwa yau kam tasha alwashin jiran shi komin dare domin amsar wayar ta, koda hakan na nufin zai doketa neh.
Ganin har sha biyun ta gota yasanyata yanke shawarar tunkarar dakin nashi domin ta bincika wayar tata da kanta,duk kuwa da warning din da ya bige mata akan shigar mashi daki kai tsaye, amma tsananin buqatar son jin muryoyin y’an gida yasanyata watsi da warning din nashi ta nufi dakin nashi kanta tsaye. 2
Dama akwai wani corridor daya raba tsakankanin d’akunan baccin nasu, hakan yasa akwai y’ar tazara kafin kaje nashi dakin, mamakin ta neh ya dad’u yayin da ta ga haske daga cikin dakin nashi ma’abocin duhu a koda yaushe,koda kuwa yana gidan neh, amma hakan bai dakatar da ita ba, sanin shikenan ma wanda take zaman jiran ma ashe ya dawo bata sani ba.
Kanta tsaye ta tura kofar dakin tareda sallama a bakin ta, ga mamakin ta babu kowa cikin dakin, illah kayan shi dayasa yafita da safe yashe akan marble din dake shimfide a dakin,ga kuma brief case din shi itama yashe bisa gado.
Cigaba da wurga idanuwan ta ta rik’a yi cikin dakin, da zummar ko zata ga wani abu daya danganci abinda yafito da ita, garin kalle kallen neh sai take ganin kamar d’igo d’igon jini a kan fari qal din marble din dake dakin, hakan yasa ta sake wara idanuwan ta domin son tabbatar da zargin ta. 1
Ilai kuwa jinin neh ya d’idd’iga har hanyar dazata sadaka da toilet din dake manneh da dakin, batasan meyasa taji kamar gabanta ya soma faduwa ba, shin meyakawo jini cikin dakin yaya safwan kuma? Ta rik’a tambayar kanta yayin da take bin jinin domin isa cikin makewayin.
Turo kofar bayin kawai kurum tayi taga ta bude, wanda budewor kofar bayin yayi daidai da juyowar mutumin dake tsaye a gaban mirror yana kokarin yage wani abu daga kan fuskar shi.
Turus tayi, yayin da haduwar kwayoyin idanun su yayi daidai da wata azababbiyar faduwar gaba da ta ziyarce ta, wanda abinda idanunta ya hango mata a tsaye yana kallon ta ya sanyata yin baya taga taga tamkar zata kifa k’asa.Tsaye yake daure da towel a qugun shi, gefen kafadarshi kuma nannade da wani farin bandeji, da’alama sabon rauni neh a gurin, diba da yanda jini yana dan bullo ta gurin. +
Shi kanshi da yake namiji sai da gaban shi ya dan fadi, dalili kuwa bai taba tunanin bayyanuwar ramlan ba a cikin dakin nashi, diba da yanda ya bige mata warning akan shigar mashi daki.
Sank’are take a jikin bango, yayin da gaba daya notikan kanta suka kwance, suka kuma dena aiki, duk wata jijiya dake sadar da saqonni ga gangar jikinta suka sami hutun takaitaccen lokaci, a yayin da kwakwalwarta ta samu kwancewar wucin gadi, sakamakon abinda idanuwan ta sukai arba da a yanzun din.
Fuskar fatar dake hannun shi mai dauke da fuskar safwan mainasara ta rika bi da kallo tamkar mutum mutumin, yayin da kuma dayan sashe na tunanin ta ya rik’a tariyo mata mutumin dake tsaye a gaban ta yana mata wani irin kallo. 1
Kana lokaci guda ta rik’a shak’o wannan nataccen turaren da har ta koma ga mahaliccin ta bazata kasa tamtanceshi ba cikin dubu,ba shakka tana fatan ace inama mafarki take ta farka daga wannan masifaffen al’amarin dake tunkaro duniyar ta, idan kuwa idanh biyu neh take hango fuskar mutumin da bata tab’a tsammanin zaiyi badda kama ba ya rik’a cutar rayuwar ta har haka ba fatan inama zata iya maida hannun agogo baya domin gyara inda ta gaza a rayuwarta da har wanan mutumin zai afka wa duniyar ta har haka! 2
“Kaiiii…… Kaineeeh da…. Damaaah?” muryarta mai cike da gargada tasami kwarin guiwar yin magana, yayin da hawayen dake maqale a kwarmin idaniyanta suka shiga rige rigen sauka.
Wani malalacin murmushin da bata tab’a sanin shi dashi ba ya sakar mata, yayin da ya shiga tunkarota gadan gadan yana mai kwashewa da wata mahaukaciyar dariya, dariya yake mai tattare da ban haushi da ban tsoro, hakan yataimaka wajen daduwar makyarkyata da jikin ta keyi tamkar mazari, take ta rik’a yin baya baya domin tsere wa azzalumi kuma maha’inci mutum irin wannan
“Nine ramlah…… Nineh nan, duk da banso kika fahimci koni waye ba a yanzu, domin that wasn’t my plan for now…. But ya muka iya da kaddara?” Ya rausayar da kanshi yayin da yake dakatawa daga kusanto ta. 1
“Yes…. My plan was totally ruined ramlatu nah, and all thanks to you in ruining my whole plan ramlatu nah, why? Why? I mean how comes kika shigo privacy dina despite all the crucial warnings that i gave you ramlatu nah? Uhuuummm? Meyasa haka ramlatu nah?” ya ida zancen muryar shi dauke da wani boyayyen alkaba’i a cikin ta, haka zalika kallon shi gareta kallo neh mai dauke da tarin ma’anoni masu wuyar fassarawa.
Girgiza kanta kurum take, yayin da ta sanya dayan hannunta tana mai toshe bakinta da kuka, ya kwace mata, lokaci guda tana jin wani irin tsoro mai girma na ratsa dukkanin gabban ta, hakan yasa ta rik’a jin inama zata iya rugawa a guje ta tsere wa munafiki kuma algungumi irin wannan, shin dama a duniayr nan akwai mutane irin wadannan?
Kamar yasan meye a ranta yai haramar takowa gamida yimata runfa da kirjin sa maras riga, hakan yasa takuma toshe bakinta, yayin da hawaye suka cigaba da tsartuwa bisa fuskar ta, ba shakka tsoron Allah yakara kama ta.
“Duk da irin son danake maki ramlatu nah hakan bazai hanani hukunta ki bisa karya dokata da kikayi ba, how dare you zakiyi merging into my territory kanki tsaye ramlatu nah? I didn’t gave you that freedom yet! Therefore i must punish you for breaking my rules honey, i surely must punish you honey…… ” 3
Yanda yake zancen tare da shafa ilahirin fuskarta shi yakara tsurar da ita, hakan yaqara tuna mata da lallai wannan mutumin shine rai kwaya daya tal daya keta.mata haddi a wannan daren, domin kuwa wannan shine action dinsa a yayin daya sanya qyalleh ya toshe mata baki, kana kuma ya rik’a bin fuskarta yana shafawa tareda kai wa labban nata sumba ya tsohon mayeh
Toh yanzunma abinda yake maimaitawa kenan, domin kuwa hannau bibbiyu yasa ya tallabo fuskarta gaba daya, kana ba tareda bata lokaci ba ya sanya kafarshi guda ya tadiye ta tayi kasa kamar za zube, ammah hakan bai samu ba sakamakon yanda ya sanya jikin shi ya tokareta ta mannu da nashi jikin, cikin zafin nama ya dumfari bakin ta da niyyar yi masu shan aka tsine uwar mai karya. +
Karar da ta kwallah mai dauke da kalmar sunan shi ya dakatar da shi, kana kuma kafinn kace kwabo jikin ta yasaki idanuwan ta sunyi sama gami da kakkafewa alamun babu sauran numfashi ko rai a tattare da ita. 5
A hankali ya furta “Noooo…. Ramlatu nah don’t you dare leave me.”
Hawaye masu tsananin dumi suka gangaro bisa kuncin sa.
***
GARIN GWAMNA.
Tun bayan tafiyar safwan daga gidan, komi ya ja tunga gami da dakatawa daga sauran kuzarin da ya rage wa ahalin gidan, mussamman innah da nabilah, domin kuwa ita hajiya expression din ta is blank, duk nacin mutum bai isa ya fahimci meh zuciyarta keh ciki ba.
Idan ka debe ragowar yan mazan gidan da suka watse suka koma gidajen su cike d alhinin abinda keh wanzuwa a familyn nasu maras dadi, ba shakka sukam wannan shekarar sunga jarabtar rayuwa, abinda ya rage shine fatan cin jarabawar da suke kan sha.
Washegari kamar kullum, innah da khalil harma da nabilah neh da hajiya a zaune a main falon na gidan da zuwa yanzu sun maidashi matattarar zaman su, domin haduwa gaba dayan su su kalli tashar NTA da AIT domin kawai suji snarwar batan ramlatun koda ansami wani cigaba.
Sai dai kuma meh? Yau zancen news din yasha bamban, domin kuwa kai tsaye suke snarwar cewa a jiya neh aka samu barawon Ramkah Tafidan, dadin dadawa kuma b’arawon ya bayyana cewar shine dai kuma mutumin daya taba yi mata fyade a wasu shudaddun lokuta, kana kuma daga karshe kuma still b’arawon beyi kasa a guiwa ba ya shaida wa hukumar tsaro cewar a yanzu hakan shi din MURDERER neh domin kuwa ya dade da aika ramlahn barzahu, tsoron Allah neh ya sanya shi kawo kanshi gami da mika wuya ga hukuma domin a yanke mashi hukunci gwargwadon laifin sa, daga karshe mai news din ya rufe da cewar yanzu haka mai laifin na hannun state C. I. D na jaha, saboda haka ‘yan uwan mariganyiya ramlah tafida su hanzarta zuwa domin kwatar wa yarsu hakkin ta.
Gaba daya falon baka jin sautin komi inbanda kuka da sheshekar nabila, zuwa yanzu kam kakus neman hawayen tayi ta rasa, inbanda gumi babu abinda take, yayin da takasa dauke kanta daga fuskar akwatin talabijin din, muryar khalil dake fassara mata abinda dan jaridar keh cewa yaciga da yi mata ruri da amsa kuwwa a cikin tsaffin kunnuwan ta.
“Allahu akhbar rablatu, Allahu akhbar rablatu, Allah yajikan ki ya amshi baquntarki, Allah kuma yasaka maki akan dukkan mugun daya sanya katangar karfe tsakanin ki da duniyar ki, Allah ya saka maki rablatun innah…. Wayyoh Allah na”
Aifa innah daga haka muryarta ta hau karkarwa sai kawai ta tsage da wani irin kuka mai ban tausayi, sosai zata baka tausayi a kallo guda da zakayi wa fuskarta, ga tsufa ga tashin hankali.
Shigowar salim gidan a sittin ya sanya gaba dayan su jiyowa suna kallonshi, batareda yace masu komi ba ya dauki remote gamida canza tashar NTA dake kai zuwa tashar AIT.
Abinda idanun su suka hango masu ya sanya hajiya sulalewa kasa a sume.
Ga abinda headline din yace “A YOUNG MAN OF 32 YEARS OF AGE,BEARING THE NAME SAFWAN MAINASARA, SUBMITTED HIMSELF TO THE STATE C. I. D YERSTERDAY AS HE CLAIMS TO BE THE RAPIST, KIDNAPPER AND THE MURDERER OF HIS MISSING WIFE.”Cikin halin tashin hankali khalil ya nufi kitchen a sukwane gamida dauko robar ruwa,salim dake rungume da hajiyar tasu ya karbi ruwan gamida shafa mata a fuska, sai da yayi hakan kusan sau biyar sannan cikin ikon Allah numfashin ta yadawo, kana lokaci guda ta farka labbanta dauke da kalmar innalillahi wainna ilaihirraju’oon. 1
A hankali salim ya taimaka mata ta kwanta bisa three sitter, a yayin da gaba daya zukatan su keh cunkushe da tashin hankali mai girma, kaka kam zuwa yanzu bata ko iya magana, ikon Allah kawai yake sata sauke nunfashi ta yanda ya kamata
Salim dinne yai yunkurin tambayar hajiyan tasu in akwai inda keh mata ciwo?
Girgiza mashi kai tayi a hankali, a yayin da hawaye keh cigaba da wanke ilahirin fuskar ta, kokarin dauke kanshi salim din yayi, yayin da yake jin wani mugun tausayin kansu gaba daya na kara mamaye shi…. Allah gamu gareka! Ya ambaci hakan a kasan ranshi.
“Salim kirawo mani kabeer, inason ganin shi yanzu!” nabila dake kusa da ita ce kadai tasami ikon jin furucin bakin nata.
“Yaya wai kakira mata yaya kabeer.” nabilan tai kokarin isar da saqon hajiyar tasu.
Sai dai yai tsaki kana yace….. “Narasa abinda keh damun ya kabeer kwana biyun nan, gaba daya he wasn’t himself, nakasa fahimta abubuwan dayasa a gaba.” ya ida zancen yayin da yake kokarin dialing numbern kabeer din.
Shiru gaba dayan su sukai suna kallon shi, yayin da shikuma yacigaba da neman numbern kabeer din, amma ga mamakin shi har yanzu daya doka mashi almost seven missed calls bai dauka ba. 1
“Inajin baya kusa da wayar neh, na mashi kusan missed calls bakwai no answer.” 2
“Kacigaba da neman shi salim, yayi maza yazo ina bukatar ganin shi, mussamman sabida safwan, inafatan ka fahimci me nake nufi?”
Gyad’a mata kai kurum yayi gamida cigaba da neman layin na kabeer din.
***
Zaune yake a inda aka tanada domin ganin masu laifin dake tsare a hannun hukuma, tun daga wayewar garin na yau daya tsinci labarin halin da aminin nashi yake ciki bai kuma samun nutsuwa ba, zuciya da ruhin shi sunkasa gasgata mashi abinda idanuwan shi abinda yagani a jaridar daily trust ta yau din.
Shin meyasa safwan zai sanya rayuwar shi cikin garari irin wannan? Meyasa zai yanke wa kanshi hukunci da bai dace dashi ba? Ba shakka da yasan da wannan plan din a zuciyar safwan din, toh da hakika ya sanya katangar karfe tsakanin shi da abinda ya aikata. 2
Shigowar wani kurtun dan sanda inda yake zaune ya katse mashi tunanin sa.
“Yallabai ka shigo daga cikin wannan dakin, yana ciki, sannan kuma mintuna ashirin aka baka kugama ganawa.”
Godiya yayi mashi gamida bin bayan dan sandan zuwa inda yake tunanin nan safwan din yake.
Kwanaki uku kacal da basu hadu ba, amma saida canjin daya gani a tattare da surar ta safwan din ta firgita shi, wanda tunda sukayi ido hudu yaji wasu hawaye na taruwa a kwarmin idon shi.
“Ya ilahi, safwan neh yakoma haka cikin kankanin lokaci.” ya ambaci hakan a qasan ruhin shi.
Da hanzari ya isa inda safwan din keh zaune, hannu da kafa daure da ankwa, ba lallai bane inba kayi mashi mugun sani ba a duba na farko ka gane shi ba, domin kuwa hakika ya sauya, sauyawa ta ban mamaki, wanda kumburi da fuskar shi tayi, da kuma gefen idanon shi na dama da wani kakkauran jini ya taru zai tabbatar maka da cea ba k’aramin buguwa yayi ba a hannun hukumar. 1
“Aboki…. Kaine haka?hasbunallahu wani’imal wakil, don Allah idan mafarki nake wani ya gaggauta tadani.” bilal din ya ida zancen yayin dayake yin zaman dab’aro a gaban safwan, wanda tun shigowar bilal din yake zuba mashi wani irin murmushi wanda yafi kuka ciwo.
“Aboki kaga yanda rayuwa ta juya mani koh?” Safwan din ya furta muryarshi dauke da wata iriyar juriya da dakiya a cikin ta.
“Meyasa? Meyasa safwan? Sabida Allah menene yasa ka zabi kuntata rayuwar ka akan laifin da baka da hannu ciki? Why… Why? For heaven’s sake safwan meyasa zakayi haka?” 1
Murmushin neh dai har yanzu bisa labban shi dasuke dauke da bruises, yayin da yacigaba da kallon bilal din cikin halin banida wata mafita.
Kar Kara rike hannuwan safwan din bilal din yayi, yayin da zuciyar shi takasa daure tukukin zafi da tausayin aminin nashi, hawaye masu tsananin dumi suka kwararo daga idaniyan shi,kana lokaci guda ruhi da gangar jikin shi suka shiga kokawa mutumin da yafi so kaf duniya bayan iyayen shi. +
Safwan dinne yake da juriyar baiwa bilal din hakuri, a yayin da kalamen ban hakurin suke kara tunzura fitar zafafan hawaye daga idanun shi.
“Stop it don Allah bilal, kataimakeni ka kara mani karfin guiwar fuskantar shafin kaddarorin da aka bud’e mani, kataimakeni kabani kwarin guiwar da zan rungumi kaddarorina da hannh bibbiyu, ka taimakeni kabani courage d’in da zan nunawa ubangiji na ni dinnan mai godiya neh bjsa jarabobin sa a gareni, wata kila hakan yazame mani hanyar tsirah, wata kila hakan yazame mani hanyar da ubangiji zai amshi tubana? Ko ka manta neh intuna maka bilal? Ka manta wannan safwan din mai tarin laifuffuka neh?
D’ago fuskar shi bilal din yayi yana mai duban safwan din, wanda zuwa yanzu har idanuwan shi sun canza launi sabida tsabar hawayen daya zubar a yanzun nan.
Murmushi yakuma yi kana yacigaba” Yea bilal ni din mai tarin laifuka neh ma’abota girma, nasan kasani, kamar yanda duniya kanta zata shaidi hakan a gareni, shin bazaka duba iya lokacin dana dauka a rayuwata ina sabon ubangiji na ba bilal? Shin baka ganin wadannan jarabobin da aka jarabcenj da su su zama sanadiyar amsar tubana? Hakika idan da za’a kimasta yawa da kuma tsayin lokacin dana dauka ina zalintar kaina, wannan abin da ya fada mani banajin zafi da ciwon shj yakai munin abubuwan dana aikata a duniya ta bilal…… “
Ya numfasa, kana ya cigaba “Sabida haka bilak nake rokon ka daka taimakeni ka kara mani qarfin guiwa domin ganin na fuskanci abinda duniyata ke fuskanta a yanzu, hakan neh kadai zai tabbatar mani da amintar mu.”
Shiru bilal din kawai yayi yana mai kallon bakin safwan din, gamida jin zantuttukan nashi tamkar sarar takobi, dukkuwa da cewar lallai dukkan abunda ya fada din gaskia neh, sai dai duk da haka baiga dalilin da zaisa shi safwan din ya amsa laifukan da bashi ya aikata su ba! 1
“Na fahimci dukkan bayanan ka safwan, sai dai abinda nakeso ka gane anan shine, shi Allah mai tsananin tausayin neh ga bayin shi, haka zalika shi din mai son bayin sa neh masu tuba, hakika Allah mai gafara neh, kuma mai jin k’aine, domin kuwa rahamar shi ga bayin shi mai tarin fad’i ce maras iyaka….. Amma meh? Ba lallai saika amshi laifukan da bakai ka aikata su ba neh Allah zai yafe maka safwan, sabida bakai ka aikata abinda ake tuhumarka dashi ba! Safwan baka da hannu cikin dukkan abubuwan da ke faruwa, don me zaka zalinci kanka, iyayenka da abokan ka kanemi salwantar da rayuwar ka bisa abinda baka aikata ba?”
“Kwarai bani na aikata su ba bilal, amma waye yasan cea bani na aikata ba inba kai kadai ba bilal? Tell me, duk duniayr akwai wanda yakamata ya yarda dani sama da mahaifiyata bilal? Babu koh? Toh har mahaifiyata bata yadda dani ba,yan uwana basu yadda dani ba, tamkar yanda duniya ma zatai mani wannan shaidar yayin da aka tuntubeta, ka gaya mani duk wannan din laifin waye? Laifi na neh bilal, yau komenene ya afka wa rayuwata nine nan na jawo abina, meyasa nace haka? SABIDA DAMA CAN BANI DA SHAIDA TAGARI A IDON DUNIYA! hakan keh nuni da koma meye neh akace na aikata toh tabbas ansan zanyi fiye da hakan….. Ashe hakan bazai tunasar dani cewar duniya ta shaideka da kyakkyawan zato ba ma wani abu bane? Shaidar jama’ah shaida ce dakan bi dukkan bawa har a ranar gobe kiyama, wanda ni nayi wasa da dmata tun fil’azal bilal….. “
Zuwa yanzu hawaye neh keta tseren gudu bisa kuncin safwan din, yayin dayakejin bakin ciki gamida danasanin irin rayuwar daya aikata a baya,ba shakka da koda hakan zai faru, toh hakika da abubuwa sunzo mashi da sauki, amma ina yayi wasa da dimbin damammakin da Allah keh bashi aro a lokuta da dama da suka shude.
“Alfarma guda nake nema a wajen ka bilal, ko bayan babu ni Allah zaisa a ga ramlah, don Allah make sure you tell her everyteverything, kai kasan komi Aboki, kasan komi….. Let her know that ni dinnan zan mutu neh zuciya da ruhi na gode mata, zan tafi neh ina mai farin cikin kasantuwar ta dalili kuma babban jigo na daidaituwar rayuwata, kamar yanda nasan fata da burin mahaifiyata da kai kanka bilal kenan, zan dawwama ko bayan babu ni ina godewa kaunar ta dake kasan raina, wacce ba shakka itace ta zame mani duhu da haske na daga shafin babin rayuwata, ka kuma rokar mani yafiyar ta bilal, domin nasan na kuntatawa duniyarta sau ba adadi, wanda yin hakan danayi shine tsira a gareni…. Tell her that all my life i live for her….. Kamar yanda zuwa wani lokaci i will soon die for her…. Son ta yazame mani weakness dina kamar yanda kasani neh bilal….. Don Allah let her know that all what i become in my life was because of her.. And I’m glad she did play the bad and now the good role in my life…… Kagaya mata I’ve been loving her from the very fist day i set my eyes on her! And zan mutu ina son ta fisabilillah…… ” 9
” Time up! ” kakkaurar muryar dan sandan ta doki kunnuwan su.
Mikewa bilal yayi, yayinda harshen sa bai fasa ambaton zanyi dukkan abinda kace safwan, kai kasani aboki, ko babu kai ni d’in mai biyayya neh ga dukkan cewar ka, sai dai inason kasani cewar ba yanzu zaka barmu ba, muna nan tare, muna nan tare safwan….. Kamar yanda nake alwashi gamida fatan da yardar ubangijin talikai saika rayu da ramlah tafida kamar yanda nai maka alkawari a baya…… Yanzun ma nayi wannan alkawarin safwan, zaka rayu in Allah ya yarda….. I promise you that aboki na. 1
Ya ida zancen yayin da kofar dakin da safwan din keh ciki keh karasa rufewa,a hankali ya juya ya domin ficewa daga division din, ruhi da zuciyar dauke da tarin al’amura masu wuyar fahimta.
***
Cigaba da kallon wayar yayi tana ringing, haka nan zuciyar shi keh azazalar shi da son daukan kiran amma ya kasa.
“Yanzu ba lokacin ku bane salim.” ya ambici hakan a bayyane, sanin irin takurar da salim din ke sonyi mashi cikin kwanakin nan da dukkan mafarkan shi suke a hanyar gangara na cika.
Tsaki yayi gamida jin sabon bacin rai, kana can kasan ranshi yacigaba da danne al’amura mafi muni da suka taimaka wajen maidashi mutumin da yake a yau! Hakan yasanya shi runtse idanun shi, yayin da zuciya da ruhin shi keh fatan ganin ranar da zai tarwatsa rayuwar mutumin dayai mashi karan tsaye tun wasu shudaddun lokuta masu tarin tsayi. 2
Nishin kukan ta ya maido shi daga tunanin da yake, hakan yasa a zabure ya mike ya nufi gadon datake shimfide, hanun ta kuma dauke da drip dukjuwa da cea ba’a asibiti suke ba a gida suke.
Ganin muguwar fuskar shi a gabanta ya sanyata hanzarin rufe idanunta da suka kode cikin kankanin lokaci, yayin da zuciyarya har yau takasa daukar abinda idunwanta suka gane mata! Ba shakka zata dawwama tana mamakin ha’inci, munafinci da mugunta irin ta wannan bawa dake tsaye a kanta. 2
Lallai mutum mugun icce neh, kamar yadda bahaushe beyi karya ba yace “MAKASHIN KA NA GINDINKA” Yau ita kam ta shaida hakan. 2
Cikin siririyar muryashi da ada kan burgeta, harma take kara sanyawa ta kara girmama shi da bashi dukkan kulawa sabida kasantuwar shi cikin jerin mutanen da bazata manta halaccin su da dimbin kaunarsu ba a gareta,yace…..
“Alhamdulillah ramlatu na is all wide awake!” ya ida zancen yayin da yake yi mata rumfa bisa gadon da take, lokaci guda yana mai kai hannayenshi saman fuskar ta.
Murya a zafafe ta furta “Banaso YAYA KABEERRRRRRR…….”Ambatar sunan shi kadai da tayi sai da zuciyarta ta jagule, wani k’ullutun bak’in ciki ya cika mak’oshinta, wanda ta ke jin tamkar k’irjinta zai tsage tsabar takaicin da wannan bawa ke bata, ba shakka shi d’in ya kasance wani b’angare na daga mutane ma’abota ha’inci! Kaico! Kaico da mutum irin KABEER MAINASARA! 10
“Stop it Ramlatu na, stop those precious tears of yours from fallen, kinsan yaya tasirin hakan ke da shi a gareni?” 7
Ta tsinkayo muryar shi yayin da yake sanya d’an yatsan shi guda manuniya yana mai d’auke hawayen da ke rige rigen sauka bisa kuncin ta.
Zuwa yanzu zuciya da gangar jikin ta sun fara gajiyawa gami da sarewa da dukkan sabbin al’amura da ta keh fuskanta daga wannan mutumi da yake tamkar wani bangare na rayuwar ta a da! Hakika a yanzun ba ta tunanin akwai wata halitta mafi muni da ta ke iya hanga a dukkan tsawon rayuwar ta, duk kuwa da cewar har yanzu akwai mashahuran tambayoyin da ke barazanar fasa kwakwalwarta da ta ke bukatar samun amsar su daga gareshi.
Murya a raunane,haka kuma ba tare da ta dago kanta ba tace, “Menene yasa haka ya kabeer?” 4
Zuru yayi mata da rinannun idanuwan shi masu shegen girma, domin kuwa asali duk gidan nasu yafi su manyan idanuwa, amma kuma shine kusan na karshen baya wajen kyawu, kila hakan na da nasaba da siranta da yake da ita, wanda hakan ya kara taimakawa wajen bayyanuwar tsawon shi matuk’a gaya. 9
“Menene yasa mene? Nayi wani abu ne maras kyau?” 2
Ji tayi tamkar ta watsa wa banza mari, amma tasan hakan ba mai yiwuwa ba ce, hakan yasa bacin ranta ya kara yawaita, da karfi ta sanya hannuwan ta ta hankade shi daga rumfar da ya yi mata a ka, kana ta diro daga gadon gami da cisge kanular dake sanya a hannun ta, sosai ta ke so ta manna mashi hauka.
Cikin kiftawa da ido ta fara wurgi da dukkan wani abu dake zaune a dakin nashi, da karfi take zunduma ihu gami da yin ball da duk wani abu dake gaban ta, bakin ta kuwa bai fasa ambatar “Yaya kabiru tambaya ta ka ke mene mene? Kayi wani abu ne maras kyawu? Ni ka ke tambaya ko kayi wani abu ne maras kyawu Ya Kabeer? Ni kake tambaya? Amma kai din kacika dan tasha Ya Kabeer, wallahi ka cika tantirin maras kunya, wayyoh Allah… Ku ji fa jama’ah, ku ji mani wannan maha’incin wai tambaya na yake?
Zuwa yanzu muryar ta har ta dena fita sabjda ihu da kuka, ga kuma mashahuriyar gajiya da tai mata rubdugu, wanda hakan ya kara taimakawa wajen zazzabi da ciwon kai yi mata rubdugu, hakan yasa ta duk’e a gurin ta na mai zuba kuka maras sauti. 8
Gogan naku na gefe a tsaye, kallo yake bin ta dashi tun lokacin da ta fara tsallen drama din ta, haka kawai ya tsinci zuciyar shi da yi mashi zafi, shin meyasa yarinyar nan bazata fahimci dukkan abubuwan da ya yi, ya yi su ne duk don sabida ita kadai? Mi yasa bazata gane cewar ita d’in ce silar abin da ya zama a yau? In fact ta yaya zai fahimtar da ita cewa gaba dayan ta an halitta ta ne domin shi shikadai ne? Yaushe za ta gane cewar safwan ba komi ba ne a rayuwar ta face wani bigire ko kuma wani bango da ya taimaka wajen hauhawar ta zuwa gareshi? Hakika tana bukatar ta fahimci cewar shi d’inne asalin mutumin da ya dace da yazama miji a gare ta ba k’annin sa ba! 3
Cigaba da kallon ta yake tana mai rusa kuka, kuka take mai cike da zallar bakin ciki, wanda tsabar kukan har yasa ta kwanta shabe shabe a k’asan sassanyar marble din dakin, dukkuwa da sanyin da ake zurarawa, hakan bai sa ta mike ba, illah ma sake bajewa da ta keyi tamkar wata marainiya. 2
Ji yayi shima hawayen na taruwa cikin kwarmin idanun sa, hakan yasa ya karasa inda take, ba tare da sanin ta ba sai ji tayi ya sanya hannayen shi biyu yai sama da ita, ihun ta cigaba da zundumawa lokaci guda ta rika shure shure da bige bige akan ya sauke ta, bai saurare ta ba sai da ya dangana ta da gadon, a hankali ya aje ta dukkuwa da irin yanda take mauje mashi fuska da naushi.
Zaune ta tashi bisa gadon tana mai kunduma mashi wasu gima giman ashar, wanda ita kanta bata san ta iya su ba, gaba daya ta fice daga hayyacin ta.Allah ya isa, d’an iska mugu mara imani, Allah ya isa da fyaden da kai man! Allah ya isa da sato ni da kayi! Allah ya isa da tab’a wa mijina jikina da ka ke yi! Allah ya isa da dukkan muguntar ka a gareni! kai Allah ya isa bazan tab’a yafe maka ba Ya Kabeer! In sha Allah nice ajalinka! NICE AJALINKA KABEERU! 1
TA karashe maganar cikin k’araji, ba shakka ita zatai ajalin wannan tsinannen, ko ba dade ko ba jima sai ta kashe shi, kamar yanda ya kashe asalin Ramlatun da kowa ya sani, haka itama zata kashe sabon Kabeer din da ke tsaye a gaban ta yana mai zuba mata idanuwan shi cikin nata, gaba daya babu alamun bacin rai ko jin haushi bisa furuciin da ta gama yi a kanshi, asalima wani mischievous smile ke bayyanuwa bisa salahar fuskar shi, wacce kwarai da gaske babu mahalukin da ya isa yace shi d’in wani irin monster ba ne. 1
“Seems har yanzu baki fahimci inda na dosa ba Ramlatu na, har sai yaushe ne zaki gane cewar baki da wani miji a duniya in ba ni ba? Sai yaushe zaki gane cewar safwan ba komi bane face wata katanga da ke tsakanin mu, yakamata zuwa yanzu kingane cewar i have taken back what is rightfully mine! And idan duk duniyar za su had’u wallahi tallahi babu shegen da ya isa ya rabani da ke! I am addicted to you Ramlatu na, i am possessed to you, and dole ne ki aminta da hakan Ramlatu, dolen dolen ki ki amshe ni a matsayin possessive mijin ki, dolen ki ki rungume ni Ramlah, You were mine since from day one, and zuwa yanzu nasan kin fahimci dalilin da yasa nai maki fyade, nayi maki fyade ne to OWN YOU ALL BY MYSELF ALONE! I raped you just t make you mine, and duk duniyar nan babu mahalukin da ya isa ya rab’i jiki da zuciyar ki bayan ni! You are MINE, MINE AND MINE ALONE Sugar. 10
Ya karasa zancen da wani irin dominance a tattare da muryar shi, da wani irin iko da isa a muruar shi, wanda kallo guda zaka mashi ka hango zallar gaskiya cikin dukkan abin da yace d’in, ba shakka Kabeer Mainasara ya bambamta daga sauran mutane da zaka iya cin karo dasu a duniyar ka, domin kuwa shi din yakasance wani irin mutum ne mai tsananin sanyin hali da nutsuwa, mutum ne introvert d’in gaske, mutum ne maras hayaniya a dukkan kafatanin gidan su,tambayar a nan itace, shin menene ya canza wancan Kabeer d’in zuwa wannan azalumin? 6
A hankali ta sauke nata idanuwan daga nashi, tanajin duniyar ta na tangal tangal, ta na jin duniyar ta na tseren gudu da ita, tanajin asalin duniyar ta ta da nayi mata bye bye, hakan yasa ta sauke wata ajiyar zuciya kana kuma labbanta suka fara ambatar “Allahumma ajirni fi musibatiey, wa akhliefni khairun minha.”
Ganin yanda jikin ta yai lakwas yasanya shi karasowa bisa gadon da take, tunanin sa zantukan shi sun fara tasiri ne a gare ta, ba tare da jinkiri ba ya shafi abinda yafi k’auna a dukkan sassan jikin ta, wato labb’anta ma’abota laushi da taushi, hakika ba zai tab’a mance daran da ya fara had’a bakin sa da nata ba, kusan ya wanzar da dukkan lokutan shi ne wajen tsotsar bakin nata, dukkuwa da irin mutsu, mutsu da cizon da ta rik’a kaiwa nashi bakin da sunan son k’wacewa, amma a hakan yayi wa labb’an nata shan ala tsine uwar mai k’arya, kafin ya sami damar amshe budurcin ta cikin mawuyacin hali, domin kuwa kamar yanda yasan yabata wuya haka shima ya kwashi tashi azabar mai tattare da nutsuwa da kafirin dad’in da bai tab’a jin irin shi ba, ba shakka ita din ta kasance wata RAI guda daya tak da ta tab’a sanya mashi nutsuwa, duk kuwa da cewar ba cikin nutsuwa da dadin rai d’in ya tara da ita ba, tambayar shi anan itace, shin wace iriyar nutsuwa kuma zai samu idan ya sake kusantar tare da yardarta, goyon bayan ta da kulawar ta? 5
Runtse idanun shi yayi, yana jin canjin da jikin sa ke samu a duk lokacin da yai gigin tunawa da dad’in da ta jiyar dashi a wannan daren, hakan yasa nan take duk kofofin jikin sa suka bude, tsigar jikin shi suka mimmike, kana ruhu da gangar jikin shi suka fara tawayen son samun irin nishadin da ya tab’a samar masu, duk kuwa da alkawarin da ya dauka na kin sake kusantar ta har sai da aminceamincewar ta, domin kawai ya tsinci aminci da nutsuwar dak tattare da jikin ta. 1
“Idanuwan shi da suka kad’a sukai jawur ya bude gami da zuba su a kan fuskar ta dake kallon shi cike da tsana da tsoro kuma, labb’an nata da yake murzawa da dan karfi ya rik’a bi da kallo kamar sabon maye, yayin da zuciyar shi ke azalzalarshi bjsa son ganin ya karya wancan alkawarin.ko da kuwa hakn na nufin sake yi mata wani fyaden ne a karo na biyu! 4
Murya a raunane kuma a shak’e, dauke kuma da wata iriyar makauniyar shaawa a cikin idaniyan shi yace….. 2
“Please sugar, ki taimake ni in samu nutsuwa dake a karo na biyu.” 2
Zaro idanuwan ta tayi ta k’ara baje su bisa fuskar shi dake kallon ta ta, yqyin da zuciyar ta ke sake tambayar ta da anya Ya Kabeer na tsoron Allah? In fact wannan mutumin kuwa yasan addini shi ma, kuwa? Hakan yasa ta budi baki a hankali tace.
” Ya Kabeer shin wane irin jahilin farko ne kai?” 3
Murmushin nan nasa mai nuni da zallar kamewar sa ya sakar mata, kana a hankali yace “Bari in nuna maki kalar jahilcin na wa da baki gama sani ba.”
Wani razannanen ihu ta saki ganin ya haye ruwan cikin ta.
***
“Saratu na gajii da jiran wani banzan Kabeeru da ake a cikin gidan nan, nagaji da wannan banzan hukuncin naki, nagaji da jiran gawon shanu saratu, idan har ke baki tunanin halin da d’anki yake ciki, ni nan tunani da tashin hankalin da jikana yake ciki ya hanani nutsuwa, ya hanani runtsawa, ba shakka idan yau baki tashi mun tafi domin k’wato yaron kirki ba toh ba shakka zanci ubanku gaba daya ‘yan gidan nan, aikin banza aikin wofi kai. ” 9
Kakus kenan keh surfa ruwan bala’i a yau asubahin washegarin ranar da suka ga sanarwar safwan na hannun hukuma.
Sake sunkuyar da kanta hajiyar tayi, yayin da take sanya hannayen ta tana dauke hawayen dake ta zarya a idanun ta tun jiya, murya a raunane tace, “Innah don ya rasulillahi ku yi hakuri ku fahimci nufi na nayin hakan mana, ko kuna tunanin cikin dadin rai nake zaune a haka? Ko kuwa sai yaushe ne ma zaku fahimci cewar nafi kowa shiga damuwa bisa halin da safwan yake ciki, wanda Kabeeru ne kadai zai shaidi hakan, yakuma fahimci hakan,don Allah kuyi hakuri Kabeer din yazo tukunna. 10
Irin hararar da innah ke bankawa ne zai ba mutum dariya da tausayi a lokaci guda, domin kuwa idanuwan ta da suka gama jmewa da hawayen kukan da ta sharba take kuma zubawa hajiyar harara, da’alama gab take da wanka wa hajiyar mari, diba da yanda take huci tamkar ruwan zafi, hakan yasa ta mike gami da nuna hajiyar da yatsan ta manuniya tace,
“Yoooo ni ina ruwana da wani kabiru can saratu? Wannan ba damuwa ta bace, abinda na sani shine yanzun nanba anjima ba nake so a tashi maza maza a dangana ni da gurin yaron kirki, idan ba haka ba Saratu, Saratu idan ba haka ba wallahi summa tallahi zakiyi danasanin wayewar garin na yau! Domin kuwa zan tabbatar da kowa na cikin gidan nan yaci uwar shi la’ada waje, nabaki awa biyu in ganni a gaban yaron kirki,banzaye marasa imani” 10