SHAUKIN SO COMPLETE
Saurayine dan kimanin shekara 30yrs yake Jan mota kirar Accord 2016, cikin kwanciyan hankali yake tuki cikin motan kuma wani kidine mai sanyi yake tashi wakar Jennifer Lopez _what is love_ shi yake tashi, shikuma sai faman kada Kai yake alamar yana jin dadin wakar”.
“Parking yaja a daidai harabar _Sahad_ dake garin kano, sanye yake cikin fariin yadi Wanda yasha aiki kana ganin kayan zaka San mai tsadane, kafarsa kuma wata takalmi mai kyaun gaske shima fari, hannun sa daure yake da agogon axurfa kirar campanyn Rolex,yasha kyau iya kyau fuskansa dauke da murmushi ya shige super market din.”+
” yana shiga ya fara binciken abinda zai saya, yana cikin duba kaya ya ga wata Yarinya kyakkyawa ya kalleta sama da kasa amma bai ce mata komai ba, ya ci gaba da sayayyarsa har ya kammala ya zo aka yi masa total din kayan ya biya ya fita, yana zuwa wurin motarsa ya bude bayan boot ya saka kayan da ya siyo, sannan ya dawo gaban motarsa yayi tsaye yana jiran wannan yarinya ta fito.”
“Bai fi minti bakwai ba, sai ga yarinyar ta fito tare da sayayyarta ta tsaya bakin titi tana jiran mai taxi domin ya dauketa, yayi sauri ya shiga motarsa ya je ya faka kusa ga yarinyar ba tare da ya fito ba, ya sauke glass din motarsa tare da cewa “Assalamu alaiki ‘yan mata” sai ta amsa masa “Wa’alaikas salam” ya ci gaba da cewa “‘yan mata ina zaki, kuma naga kamar kina jiran taxi ko?” tace “eh taxi nake jira” sai yace “to gani nima direbane kuma biyana ake sai ki shigo muje ko?” sai tace “a’a nagode” sai yayi dariya yace “aini ba godiya nake so ba, dan biyana zakiyi, in kai ki inda kike so sai ki biyani, ke ga ko ai baidace kiyimin godiya ba, ki shigo muje” tace “ni ba irin wannan mota nake son shiga ba, taxi nake bukata dan haka kaje kawai wallahi nagode” sai yace “karki yimin haka dan Allah! Ai ci gaba ne nasamu shiyasa kika ganni ina yin taxi da wannan mota, amma can asali ‘yar taxi ce gareni, ki shigo kawai muje dan Allah karki yimin walakanci, ai duk dayane dani da dan Taxi, bai dace ace kamarki kina tsaye a titi ba rana tana dukanki” da kyar ya samu ya shawo kanta, sai ya fito ya kwashi kayanta ya saka Mota, sannan ya dawo ya bude mata kofar mota ta shiga ya rufe ya dawo ya shiga suka tafi.”
” Suna cikin tafiya kowa bai cewa wani uffan ba, sai tafiya suke can sai ya dubeta yana murmushi yace “au nayi mantuwa ban tambayeki inda muka dosa ba, sai faman tafiya nake”.
“Murmushi tayi kan tace “Borno avenue zaka kaini” yace “ok” daga nan bai sake cemata komai ba har suka kai kofar gidan ya fito ya dauko mata kayanta, ta dauko kudi zata bashi sai yayi dariya yace “ai bada wannan zaki biyani ba” sai tace “to dame zan biyaka?.”
” sai yayi murmushi yace “bazan gayamiki ba yanzu, amma kibani lambar wayarki dan idan natashi karba sai nakira ki, sannan kifadamin sunanki dan nayi saving dashi”.
” sai tayi murmushi mai alamar mamaki tace “hmm lamba kuma me zakayi da ita?”.
” sai yace “ai nariga na gayamiki abinda zanyi da ita, zata yimin amfani duk ranar da natashi karbar bashina agurinki zan kira ki na sanarda ke, kuma inason nasan sunanki dan nayi saving”.
STORY CONTINUES BELOW
“Tana murmushi a ranta kuma tana mamakinsa irin yadda yamaidata yarinya kawai sai tabashi lambar wayarta sannan tace “Suna kuma ka saka wacce kake biya bashi”.
“Da sauri yace “a’a gwara dai ki gayamin sunanki dan baki sani ba ko wadan da nake biya bashin suna da yawa”.
“sai tace “hmm idan suna da yawa sai ka sakamin sunan da zaka iya gane ni” sai yace “duk da haka zan so naji sunanki domin saka sunan yafi muhimmanci”.
“Cikin sanyin muryanta tace “nima sunana na sayarwa ne” yayi murmushi yace “tow, amma duk da haka bai kai tsadar driving din da nayi miki ba, dan haka sai ki cire daga ciki, in yaso sauran na biyoki” tace “ai sunana ya zarce kudin driving din da kayimin ba” sai yace “ke dai tsadar naki kika sani, dan haka ki gayamin idan nakira ki zamu warware” ta dan ja aji, sannan tace “sunana Maryama amma ana kirana da Mama”.
“Dan guntun murmushi yayi tare da cewa “sweet name, ni kuma sunana Abdallah amma ana kirana da Abdul.”
“Murmushi tayi tace kaima sunanka mai dadi “.
” sai tayi masa bankwana tace zata shige cikin gida.”
” shi ma bankwana hade kuma da shige wa motarsa cikin farin ciki ya ja motan sa zuwa gida…..
*NEERATLURV*😍
&
*ABDUL AZIZU AAJ*✍
(Na England)..
_Dedicated to Maryam (mama)
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*Abdulazizu AAJ*✍
Da
*Neeratlurv*😍
Via O.H.W📚
*6-10*
Abdul na driving yana murmushi shi kad’ai Kai da Ka gansa zakaga tsatsan farinciki tattare dashi har ya karasa gidan su dake sharada phase 2, da Isar sa gida yakunsa kansa cikin falon bakinsa d’auke da sallama Mummy ce (matar kawunsa) ta amsa masa, zama yayi kusa da ita yace Mummy wlh yau am lucky fitan da nayi da sa’a na fita ya kare maganan fuskansa fal murmushi.”
“Lalle sirkina (haka take cemasa Dan yana d’auke ne da sunan kakansa, itakuma sunan baban mijinta) wacce sa’ace haka? Kodai kayi gamone da da surkuwata takare maganan tana kallonsa.”
“Keyaa yasoma tsotsawa alamar yaji kunya yace ehh Mummy wlh sai kin ganta yarinya mai hankali da tarbiya, amma fa har yanxu ni bancemata ina sonta ba kawai number’n ta na karba.”
“Ah hakanma yayi sirkina amma kayi saurin gabatarmata abinda ke ranka tun kan katsaya kallo kwad’o yama kafa.”
“Insha Allah Mummy zanyi yadda kika ce d’an baxan so na rasataba ina sonta sosai in narasata tamkar rayuwata narasa.”
“Ja’irin yaro ta wurgamasa tro &donnot pillow dake kujeran falon maras kunya.”
“Da gudu yayi hanyan d’akinsa yana dariya yace Mummy wai kunya hooo ai banajin kunya indai akan mama ne.”
“Yana karasawa daki yafad’a gado yana mai jin kansa cikin farinciki a hankali ya shafi fuskansa yafurta I love you Mama.”
“Kwanciya yayi nan bacci yayi awon gaba dashi….
Mama ma haka ya kasance da ita tana barin wajen Abdul tana murmushi har ta shige gida, a cikin gida ta tarar da ummanta tana hura wuta a kitchen tace yarnan lapiya kike murmushi ke kadai?.
“Babu ummina kawai dai wani abune yasani murmushi tabata amsa a taikace tana shiga cikin d’aki.”
“Allah ya shiryeki inji umma da fad’i.”
“Amen tafad’a tana mai kwanciya kan katifar dakinta murmushi tacigaba da tana Abdul kawai take ganin Funny guy ta furta a hankali.
*** ***
Da daddare ya kira wayar Mama, bayan ta dauki wayar sun gaisa sai ya fara yi mata bayanin ko wanene, tace ta gane shi, sai suka fara fira harma take ce masa “halan katashi amsar bashinka ne” sai yace “a’a ba yanzu ba, dalilin kiranki yanzu shi ne dan naji lafiyarki kuma na rinka waya dake dan karki gudanmin da bashi” tayi dariya suka cigaba da waya har suka gama. “
“Suna tsinke wayan yaringa dariya shi kadai Yakuma jin farinciki na shigarsa dawata zazzafan *SHAUKIN SO* na mama a haka har bacci ya daukesa….
STORY CONTINUES BELOW
“itama Mama haka kawai ta tsinki kanta cikin farinciki Wanda bata San dalili Ba, a zuciyarta kuma tace maybe it just d way funny he’s shiyasa yasani farinciki da bark’wancinsa,, da ire iren wad’anan tunanin b’arawon bacci ya k’washeta……
_*2 days later*_
Haka Abdul ya rinka kiran Mama suna gaisawa amma bai gayamata abinda zata biya shi dashi ba, saida suka yi sati biyu suna waya ya fara samun kanta, sannan ya fada mata abinda zata biya shi dashi, bakomai bane face zuciyarta kuma Mama ta amince da soyayyarsa. Sun fara soyayya da Mama cikin jin dadi ba tareda sun samu matsala ba.”
“Soyayyarsu sai habaka datake kullum suna manne cikin waya kamar Abdul ya had’iye Mama yake ji itama haka tana cikin *SHAUKIN SO* tanaji idan bata mallaki Abdul tarasa wani babban bangaren na rayuwanta. SO! SO!!..
_Abdul azizu na kalla nace allah ya mallakawa kowannesu juna_
_Ameen yafad’a sannan yace ke neeratlurv yi sauri kidauko mana rohoto kibar surutu haka, okay nace dashi nan muka ci gaba da aiki_
“Wayan mama ne dake gefenta yasoma ringing _Sweery_ ne yafito kan screen d’in nan tadauka tasa a kunne hade da cewa.”
“Assalamu Ala’ikum .”
“Daga dayan bangaren kuma akace wa’alaiki salam yake ma’abociyar kyau da wannan zazzakan muryan.”
“Cikin zazzakan muryanta tace Kai sweery kanafa fasa min Kai “.
“Uhm toh bbyna Ba gaskiya nafad’ava by d way hope kinyini lpy.”
“Lpy lau sweery and u?.”
“Cikin muryan so da kauna yace Baby Ba lpy va.”
“Sweery what happen, Ba d’azu mukayi wayaba, zazzabine koh meye? Tayi maganan cikin voice na tausayi da so.”
“Huuhh babyna not something bad fa kawai dai am baldy missing ur pretty face and that smile of yours.”
‘Cikin shagwa6a tace wlh sweery har Ka tsoratani I think wani abinne ya sameka, uhmm nima am missing you so badly fa.”
“Okay gobe zanzo toh koya kikace.”
“Yeah kazo kawai sweery na in ganka.”
“Tohm Allah ya kaimu.”
“Amen tace.”
“Daga nan kuma suka sha kiransu ta soyayya sai wajajen karfe 11:00 dare suka yi sallama hade da So da Kaunar juna kowanensu yayi bacci.”…….
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England)..
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*Abdul azizu AAJ*✍
Da
*Neeratlurv*😍
Via O.H.W📚
*11-15*
*** *** ***
Washe gari da misalin karfe goma sha daya na rana,Abdul ya shirya tsaf ya shiga motarsa yaje gidansu Mama, yana zuwa ya kira wayarta ya sanar da ita yana bakin kofar gidansu.
“Yana tsaye sai ga Mama ta fito tana taku daya-daya, cikin yanayin Annashuwa Abdul ya rinka kallonta ko kifta ido baya yi, a hankali ta iso wurinsa tare da yin sallama, amma bai samu amsa mata sallamarta ba, cikin kallon mamaki Mama ta Dubi Abdul tare da kada masa hannu awurin idanuwansa, firgit ya dawo da hankalinsa wuri daya, sai kuma ta dubesa tace “Me kuma kake tunani haka, nazo wurinka ina sallama amma baka amsamin ba?” gyara tsayi yayi, sannan ya dubeta yace.”
“zaki iya ganina a kowanne yanayi, saboda idanuwana sun tsinci kansu awurin kyakkyawar halitta wacce basu taba gani ba, kyawo mai gwarjini tareda tafiyarda hankalin mai kallo, wurinki nazo amma kyakkyawar fuskarki ta tafi da tunani na zuwa kallon fararen idanuwanki wadan da bansan dame zan misalta farinsu ba, naga adonki wanda ya zarce na dawisi, kunnuwana kuma suka ji zazzakar muryarki wacce ni ban taba jin sauti mai dadi irinta ba” sai ya kara zura mata ido tare da cewa.”
“shin wannan kyawun da kwarjininki kina tunanin bazai iya zautar dani ba, nifa ina ganin kyawonki ya yiwa idanuwa yawan kallo zasu iya makancewa da ganin kyawon kowa wanda ba ke ba” murmushi ta saki tare da cewa.”
“ai kuwa da zan samu haka da nafi kowa jin dadi, domin bazan so kaga kyawon wata wacce ba, wadda ba ni ba” sai ya sake sakin murmushi yace.
“in dai wannan ne baki da matsala, kafin ganinki naga ‘yan mata da dama amma banga wacce takai ki ba, ban kuma samu wacce ta mallaki zuciyata a ganin farko irinki ba, sannan bana jin SHAUKIN SON kowacce mace in bake ba, ni fa kasancewa ta tare dake a yanzu sai nake jina tamkar wani basarake wanda yake sarautar duniya”.
Mama ta fuskancesa tare da kallon so zuwa garesa tace “.
“ni tunda nake a rayuwata ban taba sanin dadin kalamai ba, sai da na hadu da kai, tunda nake ban taba jin abu mafi saurin magance damuwar zuciyata ba irin kalamanka ba, a rayuwata bana banbance kamshi da wari, amma zuwanka a kusa dani sai nake jin daddadan kamshi yana shiga hanci na tare gamsar da zuciyata, tabbas ina da yakinin zaka zamo jagora a rayuwata wanda zai zamo mafi kawo taimakon gaggawa acikin zuciyata, wanda zai zamo mai kore dukkanin dattin da yake zuciyata”.
“Abdul cike da SHAUKIN SO yace “ai ni da ke mun yi bankwana da dukkanin wani bakin ciki, na zamo fitilar zuciyarki mafi kawo haske a koda yaushe acikinta, sannan ke kuma kin zamo farin ciki acikin zuciyata wacce ta mamayeta tare da rufe dukkanin kofofinta babu yadda bakin ciki zai samu hanyar shiga, dan haka nake rokon Allah da yabarmu acikin aminci da son junan mu tare da yimasa godiya koda yaushe na babbar kyautar da ya bani wato ke!.”
“sai Mama tace “ni kuwa ina fargaba acikin zuciyata, saboda wannan farin ciki da nake ji a zuciyata mafin dadi kar wata rana ya zamo min bakin ciki mafi kuna a rayuwata”.
” cikin yanayin razana Abdul yace “haba Tauraruwa me yasa kike wannan tunani?”.
sai tace “saboda ina tunani ne akan Abbana, bana tunanin zai iya baka aurena”.
” da hanzari yace “saboda me?”.
” tace “saboda kai ba yaren mu daya da kai ba, dangin mu basu aurar damu ga wani yare wanda ba namu ba, haka zalika dan dangin mu baya auren wata wacce ba yaren mu ba”.
” jikinsa a sanyaye yace “in dai wannan ne ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu ni da ke ba zamu taba rabuwa ba”.
” sai tace “Allah yasa haka”.
” ya amsa da “Amin” sannan suka cigaba da hirarsu cikin farin ciki da jin dadi.
STORY CONTINUES BELOW
“Sai da aka Kira sallah ‘n magriba tuku Abdul ya Mata sallama ya tafi zuciyarsa fal cike take Da *shaukin sonta* haka itama Nata zuciyar.”
*** ***
Bayan wasu kwanaki soyayya mai karfi takara kulluwa tsakanin Abdul da Mama, duk tsananin tsoron da Mama take yiwa mahaifinta sakamakon ya dauki alwashin bazai aurar da ita ba, sai ga dan danginsu wanda suke yare daya wato FAKANCI kamar yadda suka saba, amma tsananin soyayyar da ta shiga tsakaninta da Abdul yasa ta debe dukkanin wani tsoro ko fargabar mahaifinta, hakan yasa ta baiwa Abdul damar ya turo iyayensa dan a tsayar da Magana wato ayi musu baiko. Wannan Magana tayi matukar saka Abdul cikin farin ciki sosai. “
“Amma yacemata da zarar yaje gida can wajen mahaipainsa zai sanar dasu inyaso ko bayan ya koma gidane sai ya turo.”
‘”Mama tayi na’am da zancen masoyinta.”
“Rayuwa tana tafiyar musu cikin kwanciyan hankali suna zuba soyayyarsu yadda ya kamata, soyayyane tsabtatatce Ba irin na zamaniba.”
“Abdul ya sanar da kawunsa sun yanke shawaran da zarar Abdul ya koma gida zai sanar da abbansa inyaso suji daga garesa akan wannan shawaran suka zauna.”
“Haka itama Mama duk fargaba da tsoron mahaipinta datake hakan batajin zai iya hanata tunkarar sa da maganar Abdul duk da tasan abune mai wuyan yuwa amma zata gwada fasaharta ko Allah zai sa a dace.”
“Dan ita a gaskiya idan aka rabata da Abdul toh tamkar anrabata ne da numfashinta dan son sa shine bugun zuciyarta, fatan ta da addu’arta Allah yasa mahaipinta ya janye zancensa na aurar da ita wa FAKANCI yan uwan su, kuma ya mallaka Mata Abdul matsayin mijinta.”
_Masu karatu nasan kun matsu kusan waye ABDALLAH (Abdul) da MARYAM (Mama ) toh Ku biyo neeratlurv da Abdul AAJ dan sanin asalinsu_.”
*NEERATLURV*😍
&
*ABDUL AZIZU AAJ*✍
(Na England)..
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*Abdulazizu AAJ*✍
Da
*N££ratlurv*😍
Via O.H.W📚
*16-20*
*** *** ***
_*Asalinsu da taikaitacen Labarinsu*_
Abdullah wanda akafi sani da Abdul Hausa/Fulani ne mahaipinsa bahaushe mahaifiyarsa kuma Fulani.”
“Yan garin Bauchi ne, mahaipinsa Adam su biyu ne wajen iyayensu dashi da kaninsa Ibrahim, sun taso cikin kulawar iyayensu, Kama daga nursery, primary, har secondary school sunyi maikyau, jami’ar su kuma a waje sukayi fannin business duk suka karanta, koda suka gama karatu suka dawo gida nejiriya nan suka Kama business gadan gadan shi Adam nakula da dukinyansu a garin bauchi inda sukeda da shaguna a kasuwanni da babban company’n su na sarrafa (pata). shikuma Ibrahim wajen sa kano yadawo da zama dan kula da company’n su na garin kano wato company’n sarrafa maganin sauro da company’n atamfofi.”
“Business d’insu natafi cikin yardar Allah watarana Adam yafita zuwa kasuwa dan duba shagunansu na kasuwa k’wasam a cikin wata shagonsu na saida mayuka da costemetics yaga wata kyakyawar yarinya tunda yashiga shagon yake kallonta har saida tagama sayayya taxo biyan kudin yace tabari yabiyamata da farko yarinyar taso kinyarda amma ganin yadda ya nace yasata amincewa,har tasoma tafiya ya tashi ya bita yace tabasa lambar wayanta kuma dan Allah tafad’a mai sunanta.”
“Batayi gardamava ta sanar dashi sunanta hadiza tavasa lambar wayan ta tafi.”
“Ranar da dare ya kirata bayan yamata bayanin waye shi dakuma abinda ke tafe dashi.”
“Cemasa tayi zatayi tunani akai, bai musataba ya yarje Mata kan tayi tunani nan sukayi sallama.”
“Itama hadiza Yar garin bauchi ce amma ita Fulani suna zaune da iyayenta kuma sunada rufin asiri daidai Gwargwado.”
“Bayan kwana biyu da yin haka hadiza ta amince da soyayyar Adam, Soyayya suke yi sosai kuma So mai tsapta Adam ke Mata.”
“Vasu Kai ga jimawa Ba kowa nasu ya San da maganar su har manya sun shiga an tsaida ran aure.”
“Bangaren Ibrahim shima kasuwanci Yana tafiya daidai kuma shima yasami nasa budurwan acan kano sun tsaida magana shima ya turo manya tare za’ayi aurensu da Adam duk lokaci daya.”
“Wata daya maganar aka daura aurensu dukka inda shi Adam nan garin bauchi zasu tare da matarsa shikuma Ibrahim can kano zasu.”
Kowannensu ya tare da matarsa zaman auratayya suke cikin jin dadi da kwanciyar hankali duka Mata yensu nasamin kulawa wajen mazajensu.”
“Shekarar su daya da aure Allah ya alabarkacesu da samin ciki, duka hadiza da Asiya matar Ibrahim Nada ciki, sosai suke samin kulawa daga wajen Mazajensu.”
“Cikinsu Nada wata Tara Allah ya saukesu lpy, inda hadiza ta sukuto da namiji itakuma Asiya Mace, ranar sunsha murna, haka aka yita zuwar musu barka yan uwa da abokan arziki.”
“Ranar suna yaro yaci sunan kakansa Abdullah ake kiransa da Abdul, itakuma yarinya taci sunar kakar ta mace Zainab ake kiranta da hafiza.”
“Abdul da hafiza sun taso cikin kulawar iyayensu gata sosai suke samu barin Abdul da yake namiji makarantar yayan masu shi aka sasu.”
“Sun gama nursery,primary har secondary, suka zana jamb acan Nile university dake abuja suka sami admission dan can suka cika.”
“Sun soma karatu lpy Abdul na karanta accountancy itakuma hafiza bsc nursing take.”
“Abdul ya kasance namiji kyakyawa ajin farko a jerin maza, bayida hasken fata dan chocolate color ne yanada faffafan kirji, sumar kansa a kwance take kamar na larabawa, gashin girarsa a cike take kamar Mace yanada idana masu kyau da daukar hankali vakinsa a tsuke kamar mace gashi jajir abdul ya hadu na karshe.”
‘Gashi Sam baida tsiwa ko surutu inka gansa yana surutu toh da abbansa ko ummansa sai ko asiya matar Ibrahim, Mata dayawa na sonsa amma shi ko takansu baya bi.”
“Sun kammala karatu sunyi vautar inda har sun soma aiki hafiza har tayi aure ta auri wani course mate dinta suna zaune a Kaduna.”
“Abdul na aiki a UBA bank dake bauchi Yana samu sosai amma har yanxu ko budurwa baiyida.”
“Hutu yaje wajen baffansa Ibrahim kano kuma da aikin da zai tayasa dan suna son hada company’s din ya dawo duka garin bauchi shiyasa yaje yatayasa wasu abubuwa. “
“A wata alhamis ne yacewa umma asiya zai je siyayya store ya fita toh acan ya had’u da Mama.”
STORY CONTINUES BELOW
_wannan kenan_
_*Sai kubiyo mu danjin wacece mama? kuma mai kudiri babanta da baxai yarda aurar da ita wa wani yare Ba sai FAKANCI*_
Amsoshin suna tare da Muneerat da Abdulaziz Ku biyomu a asannu zakuji……
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England)…
_Dedicated to Maryam(Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*Abdul azizu AAJ*✍
Da
*Neeratlurv*😍
Via O.H.W📚
*21-25*
*** ***
_*Mama*_ yace ga Isma’il da rufaida, ita kad’ai Allah ya basu.”
“Isma’il mahaifin Mama asalin dan Garin _*Bagudu*_ ne san’a ce ta dawo dashi garin kano da zama.”
“Isma’il da matarsa rufaida duk yan garin bagudu ne auren hadi aka musu, sabida su a al’adance da kuma yarensu wato _*Fakanci*_ basa auren bare shiyasa aka had’a su aure.”
“Wani alhaji ne da Isma’il ke saida masa kaya ya dawo da isma’il garin kano da zama bayan yabasa jarin naira dubu Dari biyar.”
“Isma’il ya kasance mutum mai rikon gsky da amana, suna saida wa alhajin kaya ne a manya manyan shagunan sa idan isma’il ya dage yazauna tsayin daka wajen rikewa alhaji amanar da ya bar musa na shagonsa.”
“Ire iren kyawun halayyen isma’il da tarbiyyansa yasa alhaji jin son isma’il har ya kaiga basa nasa jarin bayan ya daukesa ya kaisa kano ya budemasa shagon sai da atamfa, Sanadiyar barinsa garin _*bagudu*_ kenan ya dawo nan kano.”
“Dawo warsu kano da diyarsu wato Mama nan akasata makaranta, makaranta mai kyau akasata tundaga primary har secondary duk a private school tayi.”
“Isma’il na samu Ba laifi dan shagonsa yayi albarka ya cika dam da kaya ga customers dayake samu alhamdulillah.”
“Mama ta kasance kyakyyawa ajin farko dogowace, wankar tarwad’a tanada gashi mai tsayi, bakinta karami kuma a tsoke yake kalansa launin pink color, akoi manyan idanu ga uban eyelashes haka kuma tanada cikan eyebrow (gira) har suna Neman had’ewa, figure 8 ce ita mai kirar kalangu shape na coca kola, kirjinta a cike yake dam da dukiyar Fulani gasu a tsaye kamar an hura balu, mazauninta (hips) shima Masha Allah tanada shi dadai gwargwado, Mama kenan matashiya yarinya mai jini a jika Yar 18yrs ce.”
“Ta gama secondary school inda take diploma a BUK ta Fannin biochemistry.”
“Tun lokacinda Mama ta Kai Mace mahaipinta ke kwabarta da karta sake ta kula samari,.”
“Dawannan kalamai da mahafinta ya Mata ya sa kwata2 Bata bi takan samari ko sun Mata magana sai dai tabasu hakuri ta nuna musu an Mata miji haka suke hakura da ita.’
“Da farko a B.u.k akoi wani Gaye dayayi approaching dinta ta nuna masa bata yi.”
“Amma sabida naci irinta gayen har yasa tasoma kulasa.”
“Tun basuyi nisa da soyayyaba, watarana gayen yaje gidansu zance nan mahaipinta ya gansu ya cima gayen mutunci kuma yaja masa kunne da ya fita hanyar yarsa dan da mijinta, jiki sanyayye ya bar kofan gidansu Mama.”
“Koda baffanta yashiga gida duka yamata ranar na fitan hankali har saida yaga numfashinta ya soma daukewa kan ya barta.”
“Taci kuka sosai har ta godewa Allah ranar “
“Washegari baffanta yahanata zuwa school, va yadda ummanta batayiba amma yaki Yar jemata haka saida tayi good one week a gida kan ya barta ta soma zuwa bayan ya ja Mata kunne da ginda yamata sharudansa.”
“Yakuma sanar da ita baxai yarje da aurenta wa wani yareba face _*yaren fakanci*_ “
“Tundaga wannan lokacin mama ta daina kula samari har kawo Rana ita yau da Allah ya hadata da Abdul.”
“Lokacind Abdul yafurta yana sonta taso taki amincewa saidai ina tuni zuciyarta ta aminta da soyayyar Abdul.”
STORY CONTINUES BELOW
“So! So!! Cuta, So bala’i, so matsifa ,so guba, So dafi, Mama tayi nesa a son Abdul bata jin Kira, yanxu tana ganin zata iya tunkarar mahaipinta da maganar Abdul duk tasan akoi aiki babba amma yazatayi.”
_wannan kenan_
_Kubiyo AAJ da neeratlurv danji yazata kaya_
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*ABDULAZIZU AAJ*✍
DA
*NEERATLURV*😍
Via O.H.W📚
*26-30*
_*cigaban lbr*_
Abdul ya koma garinsu na bauchi da yake daman gurin kanen mahaifinsa ne ya je, a can ne ya hadu da Mama wato garin kano, bayan Abdul ya dawo gidansu bai bari yayi kwana koda daya bane ya je ya sanar da mahaifinsa zancen Mama, ya kuma gaya masa dukkanin abinda ya shafi rayuwarta. Mahaifin Abdul yana matukar son abdul hakan yasa yake masa komai yake so, bayan yaji zancen Abdul ya kuma amince da abindaAbdul ya zo masa dashi.
Mahaifin Abdul ya tura kannensa wurin neman auren d’ansa Abdul da Mama. Bayan iyayen Abdul sun je gidansu Mama neman auren Mama, mahaifinta yayi musu walakanci sosai wanda kare ma bazai daukaba, yakuma sanar dasu kancewa baxai bada auren ‘yarsa ga wani yareba face yaren FAKANCI.”
” bayan sun dawo sun sanar da mahaifin Abdul abinda duk ya faru shima kuma ya nuna bakin cikinsa sosai da faruwar wannan al’amari tare da sanar da Abdul halin da ake ciki, hade da Jan kunnnsa kan yaxama dole yafita hanyan Mama inyanason farincikinsa, toh kawai Abdul yace amma bayajin zai iya.”
Abdul yaje dakinsa ya kwanta yana jimamin wannan al’amari, yana kwance ya dauko wayarsa ya kira masoyiyarsa Mama, kamar jira take yana bugawa sau daya wayar tayi ringing Mama ta dauka, tana dauka abdul yaji ta tana shesshekar kuka, cikin yanayin damuwa shima yace da ita “Tawa me yasa kike kuka?” muryarta a sarkake tace “me zaisa bazan yi kuka ba, daman zuwan wannan rana nake gudu a rayuwata, da ganin wannan rana dama mutuwa tazo ta daukeni kafin zuwanta…” “kidaina fadan haka, ai ni bana tunanin rabuwa dake saboda nasan rabuwa dake abune wanda bazai yuyu ba, tunanina kawai ya za’ayi mu kasance a tare, ni da ke tamkar haduwar gulbi da teku ne wadanda ba zasu taba rabuwa ba” Abdul ne ya katsewa Mama Magana tare da fadan haka, sai kuma ita tace “raba rayuwata da kai tamkar raba kifi ne da ruwa wanda babu tabbacin rayuwarsa idan ya fito ruwa, haka nima idan akace a raba zuciyata da soyayyarka to tabbas zan iya mutuwa” sai yayi murmushin karfin hali yace “ai rabuwa takan zo ne ga masoya a bisa kaddara, mu kuma tamu soyayya babu kaddarar rabuwa acikinta, kaddara daya itace mutuwa, amma raba zukatan mu da soyayyar junan mu abune wanda bazai yuyu ba, wallahi Mama ko ni akace na ciro soyayyarki acikin zuciyata bazan iya ba, ballai wani daban ya cireta, gangar jikin mu ne suke son rabawa amma bazasu iya raba soyayyarmu ba, ki daina zubar da hawayenki domin kuwa ni naki ne” sai tace
“wannan dalilin yasa zuciyata take alfahari dakai, domin kaine ka zamo sa gudun duk wani bakin ciki da ya tunkaro zuciyata tareda maye farin ciki a gurbin bakin ciki, tabbas kafin nayi waya dakai zuciyata tafarfasa take tamkar ana gobara acikinta, amma yanzu sakamakon jin kalaminka da tabbacin zaka kasance dani komai tsanani. Lokaci daya naji zuciyata ta dawo tamkar ba wani abu da yake damunta tare da bayarda jin dadi ga sassan jikina yanzu banjin komai yana damuna” “kawo wayar nan ‘yar iska” Mahaifinta ne yayi mata wannan Magana cikin tsawa lokacin da ya tarar da ita tana waya da Abdul, ya karbe wayarta tare da cigaba da yimata fada daga karshe yayi mata sharadin kada ta sake fita waje.
“Jikin Abdul ne yayi sanyi lokacin da yaji sautin mahaifinta yayi wannan Magana tare da karbe waya ya kashe. Lokaci daya Abdul yaji ya kasa tsayuwa da kafafunsa ya shiga tunani iri-iri, sai kuma ya tashi ya yunkura zuwa waje don tunkarar garinsu Mama, yana kai bakin kofar dakinsa ya tarar da mahaifinsa a tsaye, sai mahaifinsa ya dubesa cikin harara yace “bani makullin motar nan” ya mika hannunsa zuwa ga Abdul, cikin sanyin jiki Abdul ya dauko makullin motar daga cikin aljihunsa ya bashi, sai kuma Babansa ya sake cewa.”
STORY CONTINUES BELOW
“yanzu sai kaje duk gidan uwar da zaka je, kuma ina mai shaida maka cewa daga yau babu kai babu zuwa ko ina, idan kuma ka fita, idan ranka dubu ne sai dukansu sun bace” sai yayi tsaki ya juya ya tafi.”
” Abdul ya koma cikin daki yana zubar da hawaye tare da sake kiran Mama amma yaji wayarta a kashe, lokaci daya ya shiga damuwa, a haka ya kasance cikin damuwa da bakin ciki.”
“Tsakanin Abdul da Mama kowa ya kasance cikin bakin ciki da damuwa tare da tunanin halin da dayansu yake ciki, amma babu mai jin labarin wani saboda kowa yana gidan an tsare”.
“cikin haka kawun Abdul na kano ya dawo bauchi da zama duka.”
“haka rayuwarsu taci gaba da gudana cikin yanayin bakin ciki da rashin jin dadi, duk Abdul yashiga wani yanayi, ga gidansu an daukemasa wuta, aunty asiyace kadai ke kwantar masa hankali da sasa cin abinci dan tana matukar tausayawa sirkinta Abdul.”
“Haka Mama duk gidan jiyane itama….
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England..)
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*ABDULAZIZU AAJ*✍
Da
*NEERATLURV*😍
Via O.H.W📚
*31-35*
_*BAYAN WASU KWANAKI*_
“Mama ce ta shigo cikin gidansu Abdul tana zubar da hawaye, tana shigowa ta tarar da Mahaifin Abdul zai fita, sai ta durkusa agabansa tana kuka, ta dubesa tace.
“Abba dan Allah ku taimaki rayuwarmu wallahi bazan iya rayuwa babu abdul ba, idan kuka rabamu hakan zai sanadiyar halakarmu, ka tausaya muna”.
“cikin yanayin fushi Mahaifin Abdul ya dubi Mama yace “Wai ke bazaki ji maganar iyayenki bane, tunda har suka nemi su walakanta mu, ba zamu yarda da wani zancen auren ku ba, mu Hausawa bamu ce D’an mu bazai auri Fakanci ba, amma su zasu ce ba zasu aurar da ‘yarsu ga hausawa ba, dan haka ki tashi kibar gidan nan”
” sai Mama tace “Abba kayi hakuri da duk abinda suka gayamuku, wallahi acikin rashin sani ne, basu san irin wahalar da zuciya take ba, aduk lokacin da ta rasa abinda take so, ni zan zauna tare daku, bazan iya komawa gida ba.”
“Kibar gidan nan nace tun kafin raina ya sake baci” Mahaifin Abdul ne ya fadi haka cikin fushi.
“Abdul na daki kwance ya jiyo muryar masoyiyarsa Mama, da hanzari ya fito ya tarar da Mahaifinsa yana korarta, sai yayi sauri yaci gaban Mama, sannan yazo inda Mahaifinsa yake ya durkusa tareda Mama, ya kalli mahaifinsa yace “Abba ka dubi irin halin da wannan yarinya take ciki, ka dubi irin halin da na shiga a lokacin da kazo ka gayamin iyayenta sun ce ba zasu bani aurenta ba, ka dubi irin azabar da zukatan mu suke ciki na rashin amincewarku. Dan Allah ku daina zancen Yare atsakanin soyayyarmu, wallahi ina sonta kuma bana tunanin zan iya sake son wata bayan ita, dan Allah Abba kabarta ta zauna anan har lokacin da iyayenta suka gane kuskurensu suka amince da auren mu” sai Mahaifinsa yace “idan kai bakada hankali to ni inada, sannan yanzu koda iyayenta sun amince da aurenku to ni bazan amince ba, kuma babu kai babu ita, idan kuma kace sai ita zaka aura to sai dai ka sake wani uban amma bani ba” sai kuma ya dubi Mama yace “ke kuma kibar gidan nan nace tun kafin ki fuskanci walakancin da baki yi zato ba” sai Mama ta tashi tsaye da nufin fita daga cikin gidan, amma kafin ta fita sai ta dubi Abdul tana Kuka tace “Abdul Duka ko Zagi basa fitar da sonka daga cikin zuciyata koda a bangarenka ne ballai bangaren iyayenka, dan haka zan tafi amma kasani tafiyata bata nufin rabuwarmu dakai ba, dan kuwa nasan rabuwarmu dakai abu ne wanda bazai taba yuyuwa ba har abada, sannan wannan korar da iyayenka suka yimin bazan ga laifinsu ba, kuma bazan tafi da haushin su ba, na dauki wannan abin kawai yana daga cikin kaddarar rayuwata” sai kawai ta juya ta tafi……..
STORY CONTINUES BELOW
“Bayan ta fita Abdul ya dubi Mahaifinsa, sannan ya dubi Ummarsa dake gefe tana kallonsa cikin yanayin tausayi, bai cewa kowa uffan ba ya shige daki. Mahaifin Abdul ya dubi Mahaifiyar Abdul yace “Hajiya kada ki yarda yaron nan ya fita daga cikin gidan nan, dan nasan idan ya fita zai iya bin bayanta su tafi tare” sai Hajiya kada kai tace “to Alhaji insha Allahu zan kiyaye” sai Alhaji ya fita cikin gidan fusace.
***BAYAN SATI DAYA***
Alhaji ya fito firgice daga cikin dakin Abdul inda ya tarar da Hajiya tana shirin shiga dakinta, cikin kakkaurar Murya yace da ita “Hajiya shin ina Abdul ya shiga kwana biyu bana jin motsinsa, yanzu kuma na shiga dakinsa ban gansa ba?” sai Hajiya tace “wallahi Alhaji bansani ba, dan ni nayi zaton yana nan, kasan tun lokacin da abin nan ya faru Abdul ya daina fitowa waje ko abinci daina ci yayi, amma yana yuyuwa ya tafi wurin abokansa ne” sai Alhaji yace “Amma idan yaron nan guduwa ne yayi tabbas saina bata masa rai, ni zai rainawa da wayo, nace kada ya fita amma ya fita” Batare da Alhaji ya sake cewa wani abu ba, sai ya shige cikin dakinsa, itama Hajiya takarasa shigewa dakinta.
“Abdu ne acikin wani karamin Daki wanda da kagansa kasan dakin gaye ne, ko gayen wanda bayada ko sisi. Abdul na cikin dakin abokinsa mai suna Usman a kwance, sai ga Usman ya shigo cikin dakin yana tsaki, batare da yayi sallama ba ya je ya samu wuri ya zauna yaci gaba da tsaki, cikin yanayin mamaki Abdul ya taso zaune ya dubi abokinsa Usman yace “Wai abokina me yake damunka ne kake ta wannan tsakin haka?” sai Usman ya juyo da hankalinsa wurin Abdul yace “Wallahi Madam din nan ce ‘yar rainin wayo naje wurinta karbar bashin Garin Kwaki Naira Ashirin amma taki bani, kuma abin haushi agaban jama’a take fadan wai ina cin bashinta kullum amma bana biya”
Sai Usman ya nunfasa sannan yaci gaba da cewa “Allah Abokina in badan jama’a na kusa ba, dana mammake ta, abinda ya hanani aikata haka kuma ina tsoron nayi mata rauni narasa wanda zai bani bashi gobe” sai Abdul yayi dariya yace “To kai in banda abinka me zai sa kayi fushi da wanda ke taimakama yana baka bashi, ai dole kayi hakuri kabita a hankali” sai Usman yace “Yauwa abokina akwai Hamsin awurinka?” Abdul yace “Wallahi yau kwana biyar kenan ba kudi a aljihuna” sai Usman yayi tsaki yace “Ai kaji tsiyar, inama gudun haka amma baka gani, yanzu gashi awurinka an rasa Hamsin kaida kullum ‘Yan Dubu-dubu bugun Abuja ake gani a aljihunka, amma yau gashi ko Hamsin bakada. Na gayama ka koma gida ka hakura da wannan yarinya, sai kace ita kadai ce Macce a duniya, duk matan nan da suke duniyar nan karasa wacce zaka so sai ‘yar wani gari kuma wacce ma ba bahausa ba” sai Baffa yayi murmushi yace “daman ina jiran zuwanka dan muyi wata magana” sai Usman ya gyara zama yace “Yauwa Aboki ai daman nasan idan Talauci ya isheka zaka koma gida kadaina zancen yarinyar nan, dan yanzu wa yake ta soyayya ana ta Kudi” sai Abdul ya sake wani guntun murmushi a karo na biyu, sannan yace “Abokina ba wannan bane, kadai ga irin halin da nake ciki, kullum kunci baya fita daga zuciyata, so nake ka taimake ni ka rakani garin masoyiyata Mama, ko zan samu sukuni a zuciyata” “Wa! Ni zan raka ka, tab gaskiya banyi mafarkin na mutu ba, mu je gari bamuda kowa acan, sannan bamu da kudi, ka dubi yadda suka yiwa iyayenku da suka je ballai mu kananan alhaki, wallahi abokina nikam ina tsoron zuwa” Usman ne ya fadi haka yana zare idanu, sai Abdul yace “to miye kake tsoro da mutuwa, wallahi koda zasu kasheni ne sai naje, bazan hakurin rashin ganin Mama ba tsawon kwanaki, wai me yasa mutane basa fahimtar wanda ya fada tarkon soyayya, me yasa mutane suke tunanin cire so acikin zuciya haka yake da sauki kamar yadda ake cire sutura daga jiki, me yasa mutane suke tunanin masoyi zai iya hango wani wanda yafi masoyinsa bayan zuciya ta riga ta makantar da idanuwa daga hango kyawon wani wanda ba masoyinta ba, sannan ta toshe dukanin kofofin jin dadin sautin wani wanda ba masoyinta ba, Usman wallahi duk wanda yake cewa nabar Mama naso wata ji nake tamkar yana sambatu a barcinsa wanda bai san yana yi ba”.
Sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Ban damu da zuwa da kudi don yin guzuri ba indai har zan samu kudin mota, dan na tabbata idan naje can nasamu ganin Mama to na wadatu da komai, ni fa koda yaushe idan natuna Mama sai naji damuwa ta yayemin, amma kuma idan natuna bata kusa dani sai naji tamkar ana dibar naman zuciyata, zan tafi idan kai bazaka rakani ba, kuma da yardar Allah zanyi nasara” sai Usman yayi ajiyar zuciya yace “Abokina shin ya akayi kayi nisa acikin soyayyar wannan yarinya kuma me yasa bazaka iya cireta a zuciyarka ba dan kasamu salama a rayuwarka tunda iyayenta sun ce bazasu baka aurenta ba” sai Abdul yayi murmushi yace “Wai abokina kai kuwa me yasa bazaka daina wannan sambatun ba, wa ya gayama Son Mama shiga zuciyata yayi, ai soyayyar Mama itace Zuciyar tawa gaba daya, sannan yanzu babu wata kofa a zuciyata ta karbar wata magana ko shawara ballai nace na tsaya nayi nazarin shawarar da kabani, sannan kwakwalta bata daukar zancen kowa a yanzu don ganin take ba dai dai bane, zancen Mama kawai take dauka dan shi ne dai-dai, kunnuwana kuwa basa tantance kowane irin yare mutum yake fada ballai su fahimci abinda ya fada, in ba maganar Mama ba, idanuwana kuma basa gane kalar kowa a yanzu ballai nagane muhimmancin mutum awurina in ba Mama ba, dan haka kayi hakuri da wannan sambatun naka saina dawo” sai Abdul ya fita, bayan ya fita Usman ya rinka kada kai yana magana shi kadai yana cewa “Lallai wannan yarinya ta mallake Abokina wannan So haka tab Allah ya kyauta” sai kuma Usman ya dawo tunanin yadda za’ayi ya samu kudin sayen garin Kwaki.”
STORY CONTINUES BELOW
“Hajiya ce ta isko Mahaifin Abdul zaune a dakinsa, itama tasamu wuri ta zauna, sai ta dubi Alhaji tace “Alhaji tsawon kwana biyar fa Abdul baya gidan nan, me zai hana aje anemo inda yake koda hankalin mu zai kwanta?” cikin fushi Alhaji ya dubeta yace “kwanciyar hankali kuma, ai sai in kece hankalinki yake atashe, ni kam hankalina akwance yake kuma ba inda zan je nemansa tunda ba karamin yaro bane, yaje duk gidan uwarda zashi, ai dai bayada wasu uwayen bayan mu, dan haka ki kwantar da hankalin ki duk inda yaje shi ne mai dawowa” sai Hajiya tace “Amma….” “Amma me?, ki canza zance idan zaki canza na gayamiki kidaina zancen aje anemo shi, shi da kansa zai dawo ya iske mu” Alhaji ne ya katsewa Hajiya magana ya fada mata haka. Sai Hajiya tayi tagumi batare da ta sake cewa komai ba.
Daga alkalamin:-Baffa yaje wurin Abokinsa Bashir ya ranto kudin mota wadan da zasu kaishi garin masoyiyarsa Mama wato Garin kano, Abdul ya shiga motar zuwa Kano tun daga Bauchi ba tareda yanada kudin cin abinci ba ya kama hanya. Suna tafiya acikin mota Abdul baya cewa kowa komai har suka isa garin Kano misalin karfe Goma Sha Daya na dare.”
“Bayan an Sauke Abdul tashar mota sai yayi tsaye yana tunani, ya rasa inda zai dosa, gashi dare yayi kuma gashi bai san kowa ba agarin sai gidan kawunsa gashi sun koma bauchi saikuma gidansu Mama, shi kuma gidansu Mama koda yaje ba zai samu shiga ba dan yana tsammanin sun kulle kofarsu. Yana cikin wannan tunani ne ya yanke shawarar yaje masallaci wanda ya hango a kusa dashi dan ya kwana in yaso idan gari ya waye yaje gidansu Mama dan ya ganta, haka kuwa yayi yaje masallacin ya iske shi a rufe, sai yayi kokarin budewa, yana budewa ya tarar an kashe wutar masallacin ya sussuda dan samun inda zai kwanta, yana zaunawa kafin ya kwanta ji kawai yayi ance “Ihu ga Barawon na kama” sai kawai aka kunna wutar masallacin, Abdul yaga mutane da yawa kowannensu da sandarsa, batare da bata lokaci ba suka farmasa da duka, Sahahu yana ihu yana fadan “Wallahi ni ba barawo bane” amma basu daina dukansa ba.
Bayan sun ga Abdul ya jigata, sai wani daga cikinsu ya dubesu ya daga hannu alamun su dakata, sai yace “Mu barshi a haka kunsan Liman yace kada mu dauki hukunci da kan mu, idan kuma muka kashe shi to lallai za’a yi muna hukunci mu ma, dan haka mu daure shi har gari ya waye mu nunawa Jama’a shi” sai su duka suka ce “hakane, kuma wallahi sai ya biya duk abinda ya dauka” sai kuma suka ajiye sandunan su suka dubi abdul suka ce “Barawon banza, kullum aka ajiye kaya saika dauka, to yau dubunka ta cika daman ance rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya” sai suka je suka samu wani ginshikin masallaci suka daure Abdul.
“Abdul yana daure jikinsa na zubar da jini, ba abinda yake tunani face wannan yanayi daya shiga, wani bangare kuma yana tunanin halin da zai tsinci kansa gobe, amma sai yayi addu’a ga Allah dan neman sauki.
Washe gari da Asuba an kammala sallar Asuba sai wani saurayi yazo kusa ga kunnen Liman yace “Allah gafarta Malam jiya da daddare an kama Barawon nan” sai Liman ya idar da addu’arsa, sannan ya dubi saurayin yace “Jeka ina zuwa”.
Liman ya fito waje don ganin Barawon, sai ya tarar da Yara da Manya sun zagaye Abdul, yana isa gurin suka bude masa hanya ya isa kusa ga Abdul. Yana zuwa ya dubi abdul sama da kasa yaga jikinsa jina-jina da jini, sai ya dubi nakusa dashi yace “me yasa kuka yi masa wannan dukan, to idan da ace ya mutu fa?” sai saurayin dake kusa ga Liman din yace “Allah gafarta Malam, wallahi saida nace adakata da sai dai aji mummunan labari” sai Liman ya dawo da kallonsa wurin Abdul yace “Kai kuwa me yasa kake wannan mummunan dabi’a, karasa abin sata sai kayan Dakin Allah, ka kuwa san mummunan zunubin dake tattare da aikata hakan?” Abdul na shessheka ya dubi Liman yace “Wallahi ni ba Barawo bane bako ne ni, jiya jiya na sauka a garin nan, na shiga masallaci ne dan nasamu wurin kwana ba dan sata ba, sai gashi wannan kaddara tafaru dani” sai Liman yace “Ta yaya zamu tabbatar da kai ba Barawo bane?” sai Abdul yace “Ni bansan yanda zani tabbatar muku da hakan ba, amma kuyi imani da Allah da cewa ni ba Barawo bane, idan kuma kuna shakka akan zancena, to kubarwa Allah idan har ni ne mai yi muku sata kada Allah ya bani abinda nakeso sannan ya debe muku alhakinku tun anan duniya kafin lahira, wallahi Malam ni ba Barawo bane” sai Liman ya dubesa yaga idanuwansa sun yi kwalla, sai Liman ya dubi saurayin dake kusa dashi karo na biyu yace “A yadda naga siffar yaron nan bangansa da alamar Barayi ba, kuma da nayi la’akari da maganganunsa na tabbatar da hakan, ku sake sa idan ma shi ne Lahira zai biya hakkin mu” sai Saurayin ya kwance Abdul.
Bayan an kwance Abdul sai ya dubi Liman yace “Nagode sosai kuma ina rokon Allah ya bayyana muku mai yi muku sata, sannan idan ya bayyana muku shi dan Allah kada kuyi masa yadda kuka yimin, domin kuwa kowane bawa da yadda Allah yake tsara rayuwarsa kuyi masa addu’ar shiriya awurin Ubangiji koda Allah zaisa sanadiyar addu’arku ya shiryu” sai Liman ya dubi wannan magana ta Abdul nan ya sake tabbatar da abdul ba Barawo bane. Sai Abdul yayi bankwana dasu, amma kafin ya tafi sai Limamin yace “Dan Samari naji kace kai bako ne kuma gashi jikinka ya jigata kuma tufafinka sun lalace sannan nasan kana bukatar abinci, dan haka muje gidana kayi wanka ka canza tufafi sannan kaci abinci” sai Baffa yayi guntun murmushi yace “Nagode Allah yasaka da alkhairi” sai Liman ya shiga gaba Abdul ya bi bayansa domin zuwa gidansa.
STORY CONTINUES BELOW
Da Abdul ya kammala komai na wanka da canza tufafi da cin abinci, sai yakara yin godiya ga Liman tareda yi masa bankwana ya tafi.
Tun da Abdul yabar gidan Liman bai tsaya ko ina ba sai kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya yana murmushi shi kadai yana jin farin ciki a zuciyarsa tun bai ga masoyiyarsa Mama ba, yana tsaye yana jiran yaron da zai aika, sai ga wata yarinya ta gifto Abdul ya tsayar da ita ya aika ta cikin gida don takira”
” amma gabansa faduwa kawai yake don tunanin abinda zai faru dashi idan mahaifinta ya gansa, amma kuma sai ya kawar da duk wani tsoro da fargaba acikin zuciyarsa. Soyayya mai sauya tunani da nazari, Soyayya mai hana mutum ganin duk wata wahala ko walakanci akan masoyinsa, kamar yadda Abdul ya manta da dukan da yasha awurin mutanen gari sakamakon tuhumarsa da suke akan shi Barawo ne, duk wannan abin ya manta dashi abinda kawai yake tunani yaga fitowar masoyiyarsa.
Yana tsaye yana gyare-gyare, sai ga yarinya ta fito tace masa “an ce tana zuwa” sai Abdul yayi murmushi ya laluba aljihunsa da niyar yabata kudi amma sai bai ji ko sisi ba, sai dai yayi godiya gareta. Bayan yarinyar ta tafi sai ga Mahaifin Mama ya fito dan ganin mai kiran Mama.
Yana fitowa yayi ido biyu da Abdul, da hanzari Abdul ya durkusa kasa cikin ladabi ya gaida shi, amma yaki amsawa, sai ya dinga yiwa Abdul kallon takaici sannan daga bisani yace dashi “daman kai ne ka dawo, lallai yaron nan ko kai maye ne sai ka bar Mama, halan kunnuwanka basa jin abinda ake gayama ne, kai bakada zuciya ne?” Abdul na kasa batare da ya dago kansa ya dubi mahaifin Mama ba, sai yace “Baba kayi hakuri wallahi bana jin duk wata magana wacce ta danganci na rabu da Mama kuma bana gajiya da duk wani walakanci da zan fuskanta akan Mama haka kuma bana gajiya wurin rokonka dan Allah kabani Mama wallahi ina sonta” cikin fushi mahaifin Mama yace “to lallai kana tare da wahala, dan kuwa yau zaka fuskanci walakancin da ban taba yimaka ba, kabar kofar gidan nan tun kafin nasaka yara su koreka da jifa” sai Abdul yace “Baba wannan bazaisa naki sake dawowa ba, dan muddin ina lumfashi to bazan daina kasancewa duk inda Mama take ba koda za’a dinga yanka nama na” sai Mahaifin Mama ya kada kai yace “to shikenan zaka gani yanzu”. Sai kawai yabar Baffa ya shiga cikin gari domin kira yara.
Bayan wasu lokuta da tafiyar Mahaifin Mama cikin gari, Abdul na tsaye bakin kofar gidansu Mama bai je ko ina ba, sai ga mahaifin Mama yazo tareda gungun yara suna biye dashi, yana zuwa ya dubi yaran yace “kun gansa nan shi ne nakeson ku korar min shi da ruwan duwatsu” “Tau Baba” yara ne suka amsa da hakan, sai kawai suka dinga tsintar duwatsu suna jifar Abdul”
Abdul na tafiya yara na binsa da duwatsu suna kiran “Mahaukaci, ga Mahaukaci” haka suke fada suna jifarsa, bayan sun yi nisa da gidan su Mama. Abdul yana kare fuskarsa suna jifan jikinsa sai ga wani Mutum ya gifto yaga yara suna yiwa Abdul wannan aiki, sai yayi sauri yaje wurin tare da tsayar dasu, bayan sun dakata da jifar Abdul sai yace dasu “ku wadan mi irin ‘ya’ya ne haka, cewa akayi kuyiwa mahaukaci haka, dubi yadda kuka jimasa ciwo, ko tunda yana mahaukaci kashe shi zaku yi” sai suka yi dariya suka gudu batare da sun ce komai ba.
Bayan sun tafiyarsu, sai mutumin ya juyo dan ganin halin da Abdul yake ciki, sai ya tarar da Abdul ya suma, da sauri ya dauki Abdul ya tafi dashi gidansa, yana zuwa ya samu ruwa ya yayyafawa Abdul, bayan Abdul ya farfado sai mutumin yace “a’a kada ka tashi kwanta ka huta dan jikinka akwai rauni garesa” sai Abdul ya koma kwance, sannan mutumin yaje ya samu wasu magunguna ya jikawa Abdul ya kawo ya baiwa Abdul ya sha, sannan kuma ya samu Bandeji ya daurewa Abdul duk inda suka ji masa rauni.
Mutumin nan yayi dawainiya da Abdul sosai kuma ya bashi wasu tufafi ya saka bayan yayi wanka, sannan daga baya ya fahimci Abdul da hankalinsa, haka yasa ya tambayi Abdul yace “Bawan Allah me ya Hadaka da wadannan yara suka biyo ka sunama wannan aiki tareda kiranka Mahaukaci” sai Abdul yayi murmushi yace “Bakomai Bawan Allah, kasan halin kurciya wani abu ne nayi wanda ko mahaukaci bazai iya yi ba amma acikin kuskure na aikata shi, shi ne suka rinka yimin haka” Abdul ya boye wannan sirri ne saboda baya son kowa yasan halin da yake ciki, ba dan komai Abdul baya son kowa ya sani ba, sai dan gudun abashi wata shawara wacce zata danganci yayi hakuri da Mama, sai mutumin yace “to Allah ya kiyaye gaba” “Amin” Abdul ya fada, sai mutumin yace “to amma kabari gobe da safe sai ka tafiyarka, tunda kaga yanzu dare yayi sosai” Abdul ya amince da hakan yayi kwanciyarsa a gidan mutumin…
STORY CONTINUES BELOW
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England)..
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*ABDULAZIZU AAJ*✍
DA
*NEERATLURV*😍
Via O.H.W📚
*41-45*
_*Second to the last page*_
**** ****
Tun da safe Da Abdul yayi sallar Asuba, ko tsayawa karyawa bai yi ba yayi bankwana da mutumin ya tafi.”
” Bayan Abdul ya baro gidan mutumin sai kuma ya dawo kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya wurin wata bishiya batare da ya aika kowa kiran Mama ba.
Yana zaune sai ga Mahaifin Mama ya fito zai tafi cikin gari, wurin dube-dubensa sai yaga Abdul, ganin Abdul yayi matukar bashi mamaki dan bai yi tsammanin Abdul zai sake dawowa ba, kuma sai yaga raunuka ajikinsa amma hakan bai hana shi dawowa ba, batare da ya cewa Abdul komai ba ya kada kansa ya tafi, shima kuma Abdul bai cemasa komai saboda gudun fushinsa, shi dai kawai ya zauna ne koda Allah zai sa yaga masoyiyarsa.”
“Da Yamma Mahaifin Mama ya dawo gida, amma kafin ya shiga ya sake ganin Abdul batare da yace masa komai ba ya shige cikin gida.”
“Har dare yayi Abdul bai ga Mama ba, sai ya yanke shawarar kwana karkashin bishiyar saboda ba inda ya sani, haka kuwa yayi.”
“Washe gari mahaifin Mama zai fita ya sake ganin Abdul amma baice masa komai ba ya wucewarsa, da Yamma da ya dawo ya sake ganinsa, wannan karon ma baice masa komai ba ya shige cikin gida. Abdul kuwa mamaki ya ishe shi dan tsawon kwana biyu kenan bai ga koda lekowar Mama garka ba, amma kuma a zuciyarsa bai cire tsammanin ganinta ba, haka yasa ya sake kwanciya anan gindin bishiyar.”
“Tsawon kwana Hudu Abdul yana wurin ba abinda yake ci sai ruwan da yake sha a wani Fanfo da yake unguwar, ba abinda yake sa ya dauke idonsa ga kofar gidansu Mama sai Sallah amma duk tsawon kwanakin nan bai ga abar kaunarsa ba Mama. Kuma kullum sai mahaifin Mama ya gansa.”
“Mahaifiyar Mama ta kawo wa Malam abinci wato mahaifin Mama, sai ta zauna, bayan ya kammala cin abinci ya dubeta yace “Mamar Mama kin kuwa san wani abu da yake faruwa?” sai ta dubesa tace “Malam ai sanin abinda yake faruwa sai ku dake fita waje” sai yaci gaba da cewa “Yaron nan wanda Mama ta kafe shi take so, yau tsawon kwana hudu kenan yana bakin garkar nan, duk tsananin abinda nasa yara suka yi masa amma bai hanashi dawowa ba” sai tace “To Malam wallahi ina tausayawa yaran nan, ka dubi yadda suke son junan su, banga abin aibu ba idan kuka bari suka auri junansu ba, ka dubi yarinyar nan yau tsawon kwana shida bata gidan nan mun yi nemanta amma mun rasa duk inda ake tsammanin taje bamu sameta ba, yaron da kake kokarin aura mata yanzu yana can ko ajikinsa babu wata damuwa, amma mu gamu cikin damuwa ko zowa gidan nan ya daina”.
Sai ta numfasa sannan taci gaba da cewa “muna ta zargin ko tana wurin yaron nan, to gashi ashe ba can take ba, ni daman nasan bazata je can ba, dan tasan sai anje nemanta can. To amma Malam me yasa tun farko baka gayamasa bata nan ba” sai Malam yace “saboda shi nakeso ya nemo muna ita, in yaso idan ya dawo muna da ita saina koresa” sai tace “Haba Malam ai wannan daukar alhaki ne, baka tunanin Allah ya tambayeka?” sai yace “ke gafara ke kullum baki ganewa, shin ya za’ayi na baiwa Bahaushe auren ‘ya ta” sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Bari na fita nasan yanda zanyi” batare da ya jira amsa ba ya fita waje.
Yana fita waje yaje ya samu Abdul zaune yayi masa sallama, Abdul cikin rawar jikin murnar ganin Mahaifin Mama yazo wurinsa ya amsa sallama, ya durkusa ya gaishe sa, sannan mahaifin Mama ya dubi Abdul yace “Nasan na walakantaka amma kuma hakan baisa kayi fushi damu ba, sannan munyi kokarin rabaku, to amma yanzu nagane lallai idan muka yi haka, to muma zamu dawo nadama, dan haka in dai ni ne na amince da aurenka da Mama” cikin fara’a da murna Abdul yace “Baba nagode sosai, tsawon lokaci kunnuwa basu ji kalma mafi dadin saurare ba irin wannan, ina Mamar take?” sai Mahaifinta yace “Yau tsawon kwana shida Mama tabar gida bamu san inda taje ba, duk inda muke sa ran mu ganta munje amma bamu ganta ba” sai Abdul yayi zaune cikin sanyin jiki, sannan ya dubi mahaifin Mama yace “Baba kada kadamu insha Allahu duk inda Mama take saina nemo ta indai tana duniyar nan” sai yace “bakomai nagode, Allah yabaka sa’a” “Amin” Abdul yace haka, sai mahaifin Mama ya shiga gida.”
“Bayan ya tafiyarsa sai Abdul ya dawo tunanin inda zai fara neman Mama, gashi Mama ba waya bace da ita ba yanzu, sakamakon mahaifinta ya karbe, gashi shima kuma mahaifinsa ya karbe wayarsa ballai yayi tunanin zata kirasa. Yana cikin wannan tunani sai ya runtse idanuwansa, yana nazarin inda zuciyarsa zata bashi Mama take. Can sai ya bude idanuwansa sakamakon zuciyarsa ta gayamasa inda Mama take.
Kafin Abdul ya tafi yaje gidan bawan Allah nan wanda ya taimakesa lokacin da Yara suke jifansa domin ya samu taimakon kudin mota awurinsa, bayan yaje ya nemeshi taimakon kudin mota cikin nasara ya dauko kudin ya bashi, sai Abdul yayi godiya ya tafi.”
Abdul yazo bakin titi ya tare motar zuwa garin Fakai nan yake tunanin somota gidan kawunta dake fakai ya shiga motan. Bayan sun iso Fakai aka sauke shi ya biya, bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawun Mama don nan zuciyarsa ta gayamasa masoyiyarsa taje, yana zuwa ya samu yaro ya tare sai yace dashi “Dan Allah shiga gidan nan kace Abdul na kiran Mama” sai yaron ya shiga cikin gidan ya isarwa mutanen gidan sakon da aka aiko shi, sai yaro ya fito ya sanar da Abdul ya isar da sakon da ya aikesa, Abdul yayi godiya ga yaro, sannan yaron ya tafi.”
” Yana tsaye sai ga Kawun Mama ya fito a firgice, yana zuwa Abdul ya durkusa ya gaishe shi, sai Kawunta yace “Kai ne Abdul?” Abdul ya kada kai yace “Eh ni ne Kawu” sai yace “Wallahi tunda Mama tazo gidan nan kwananta biyu tabar gidan bamu san inda taje ba, saboda ana yawan yimata zancen ta hakura da kai” cikin firgita Abdul yace “Kawu nan ma bata nan kenan, Inalillahi wa’inna ilaihir raju’un” sai Kawunta yace “Daman ba gurinka taje ba, dan nasan bazata koma gida saboda dalilinka tabaro gidan” sai Abdul yace “Bata wurina naje gidansu akace kwanan ta shida bata gida, shi ne nazo nan, amma baraz an bincika wani wuri” sai Kawu yace “dan Allah kataimaka ka nemo muna ita bamu san halin da take ciki ba” “Bakomai” Abdul ne yace haka, batare da ya jira Kawunta ya sake cewa wani abu ba, kawai yabar kofar gidan.”
STORY CONTINUES BELOW
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England)…
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*NEERATLURV*😍
Da
*ABDULAZIZU AAJ*✍
Via O.H.W📚
*46-50*
_*Last page*_
**** ****
Bayan ya bar kofar gidan sai kuma ya sake runtse idanuwansa domin nazarin inda zai sake zuwa don ganin Mama, bayan wani dan lokaci ya bude idanuwansa ya doshi cikin wani babban daji, don nan zuciyarsa tabasa masoyiyarsa Mama tana nan.”
Yayi tafiya mai nisa acikin daji gashi yunwa da kishirwa na damunsa amma bai hangi kowa ba acikin jinsin mutane ballai ya nemi taimakon koda ruwan sha ne. Can yana tafiya yakara yin nisa sosai cikin daji sai ya hango wasu mafarauta sun zagaye wata yarinya, tun yana nesa ya hango su, bai tsaya bata lokaci ba ya karasa inda suke, yana zuwa koda ya kalli yarinyar dake tsakiyar sai yaga Mama dinsa ce, cikin karfin hali yayi sauri ya tsallaka tsakiyarsu ya isa wurin masoyiyarsa, Mama na ganinsa tayi wata irin murna wacce ta jima bata yi irinta ba, sai daya daga cikin,mafarautan yace “kai wanene kai da zaka shigo tsakiyar mu muna kan aiki” Abdul bai samu damar mayar masa amsar tambayarsa ba saboda tunda ya fado tsakiyarsu kallon Mama kawai yake har ya manta da akwai wasu akusa dasu.”
“Cikin yana yin fushi dayan Mafarautan yakai masa duka wanda yayi sanadiyar faduwar Abdul kasa, Abdul yana kasa ya dubesu cikin mamaki yace “ku kuwa su waye da kuka zagaye masoyita, me kuke so” sai suka amsa masa da cewa “ita muke so mu tafi da ita” cikin dariya Abdul ya tashi ya kakkabe jikinsa yace “au daman akwai wanda duniya zai iya daukar masoyiyata daga gareni, daman akwai wanda zai iya tabin jikin masoyiyata agabana, wallahi duk wanda yayi yunkurin tabin masoyiyata sai yayi nadama, abu mafi sauki ku tafi kawai kubarmu da abinda ya ishe mu” sai Babbansu yace “Lallai yaron nan ka raina mu, to bara ka gani” sai yaje da niyar rike hannun Mama, da hanzari Abdul yazo wurinsa yakai masa naushi wanda yakaisa kasa, sai saura suka farma Abdul daganan suka cigaba da fafatawa, cikin ikon Allah Abdul ya samu damar dokesu su duka, da suka ga alamun babu riba suka ruga da gudu suka bar Abdul tareda Mama.”
Bayan sun gudu, sai Abdul ya dubi Mama yana shesshekar gajiya yace da ita “Ke kuwa me ya kawo ki wannan gungurumin daji?” sai Mama tayi murmushi tace “Ni ne da mamaki ba kai ba, ya akayi kasan ina wannan dajin?” sai Abdul yayi murmushi yace “shin kesan cewa koda yaushe zuciyoyin mu suna tare gangar jikin mu kadai ne a rabe, aduk lokacin da na runtse idanuwana nakan ganki acikinsu da kuma yanayin da kike, sannan idan ina bukatar sanin inda kike zuciyata ita take gayamin inda ‘yar uwarta take ma’ana inda kike, nakan bi dukkanin inda lumfashin zuciyata yake bugawa dan na tabbata kina wurin, kuma sai yanzu nakara tabbatar da hakan, tunda ta gayamin nazo nan kuma nazo na sameki” sai Mama tasake yin murmushi a karo na biyu, sannan tace “tun lokacin da nabaro garinku, na dawo gida amma nakasa zama, shiyasa naje wurare da dama amma duk inda na zauna aka tambayan matsalata nakan fada, amma kowa abinda yake gayamin nayi hakuri dakai, ni kuma nagaji da jin wannan mummunar kalma, shiyasa nayi nesa da mutane, dan nahuta dajin wannan mummunanr kalma, wannan wurin da nake yana debemin kewa saboda soyayyarka ita kadai ce abar hirata, tunaninka kuwa shi ne abinci na, nazarin kalamanka su suke debemin kewa” sai yayi murmushi yace “to albishirin?” “Goro” Mama ce amsa haka tana cike da fara’a, sai Abdul yaci gaba da cewa “Mahaifinki ya amince da auren mu, shi ne ma yabani damar nemoki, dan haka mu hanzarta mu koma gida” Mama tana murna ta dauko mayafinta ta daurewa Abdul rauninda mafarautan nan suka yi masa abaya, suka kama hanyar zuwa gida.”
Bayan doguwar tafiyar da suka yi acikin daji har suka iso gida, suna zuwa Kawunta ya gansu ya kuma yi murna sosai tareda jinjinawa Abdul, sai kuma matarsa ta dauko mayafi ta baiwa Mama, sannan Kawu ya shiryo dan biyo su Mama gida tare. Sun je tashar mota sun shiga motar zuwa Kano cikin sa’a basu jima ba mota ta cika suka kama hanyar Kano.”
“Bayan sun iso Kano suka zo gida, suna isa cikin gida mahaifin Mama ya tarbesu cikin fara’a, mahaifiyarta ta rugo ta rungume Mama, sai Mahaifin Mama ya dubi Abdul sannan ya dubi kanensa, sai ya cewa Abdul “Mun gode sosai Abdul Allah ya biyaka kuma naso na baka auren Mama amma kuma sai gashi wata kaddara ta gifta?” cikin tsananin mamaki Mama ta saki mahaifiyarta ta dubi babanta tace “Baba wace irin kaddara kuma” sai ya kalleta yace “Kin fi kowa sanin bama baiwa duk wanda yaji rauni a bayansa auren ‘ya’yan mu kuma gashi Abdul yaji rauni agurin” Mama tana kuka tace “Baba wannan al’ada ai ba daga wurin Allah ta fito ba, sannan katuna awurin cetona ya samu wannan rauni” Abdul na tsaye sai jiri yake ya kasa cewa komai saboda tsananin mamaki, sai Mahaifinta yace “Nadai gaya miki” Mama bata kara cewa komai ba, taje ta nemo wuka ta yanka a bayanta, cikin Firgita Babanta yace “Mama miye haka, kin yi haukane kike yankawa kanki wuka” Mama na hawaye tace “Baba a wannan lokaci wallahi zan iya aikata abinda mahaukaci bazai aikata ba, na yankawa kaina wuka abaya ne saboda nima nayi irin raunin da Abdul yayi, idan kuma hakan baisa kuka amince da auren mu ba, wallahi saina kashe kaina” a lokacin Kawunta yace “Yaya kawai ka amince da aurensu in har ba so kake muyi hasararta gaba daya ba, na tabbata a yadda take ji a zuciyarta zata aikata abinda tace” sai kuma Abdul yace “Mama kada ki aikata hakan, ki bi umarnin iyayenki mu hakura da juna indai basa son auren mu” sai Mama tace “Wallahi bazan iya hakuri da kai ba koda kai zaka iya hakuri dani, kuma yanzu zan aikata abinda nace”.
Sai Mahaifinta yayi sauri yace “Mama ajiye wukar na amince ki auri Abdul, kada ki aikata wannan mummunan zunubi, bazan yi sanadin fadawar ‘yata cikin wutar jahannama ba, na amince” sai Mama tace “sai kayimin alkawari sannan zan ajiye” sai mahaifiyarta tace “Ki ajiye Mama basai yayi miki alkawari ba, nasan ya amince har azuciyarsa” sai Babanta yace “Nayi miki alkawari na amince da aurenku” sai Mama ta ajiye wukar ta rungume Mahaifiyarta.”
“Bayan amincewar Mahaifin Mama, sai kuma ya umarci Abdul suje dashi da Mamar da kuma kanensa, dan ya baiwa mahaifinsa hakurin abinda ya aikata musu, tareda rokonsa shima ya amince.
Sun shigo mota su hudu sun hawo hanyar Bauchi, Abdul da Mama murna kawai suke a zuciyarsu amma sai suka boye basu bayyana a fuskarsu ba, amma kuma da kagansu kasan akwai farin ciki atattare dasu.”
“Allah ya kawo su garin Bauchi
lafiya, sannan suka je gidansu Abdul, inda suka tarar da mahaifin Abdul yana batun fita, da sauri Abdul yaje ya durkusa gaban mahaifinsa yana kuka yace “Dan Allah Abba ka gafartamin laifina dana aikata muku wallahi banida zabi akan hakan ne” sai kuma yaje gaban Mamarsa yace “Hajiya dan Allah ku gafartamin” yana cikin kukan ne Hajiya ta riko hannunsa ta tasuwa shi tsaye batare da tace komai ba, itama ta dinga zubar da hawaye. Sai kuma mahaifin Mama yazo wurin Alhaji yace “Alhaji kayi hakurin abinda muka aikata, cikin rashin sani ne da sharrin shaidan, mun dade muna kyamar aurar da ‘ya’yan mu ga Hausawa, sai yanzu ‘ya’yan mu suka fahimtar damu wani abu wanda muka dade bamu fahimta ba, ashe shi SO babu ruwansa da Yare, sannan Allah yakan hada kauna tsakanin duk wadan da yaso, dan haka ina mai nemanka gafara ka yafemin abinda na aikata maka, na amince kuma inason kaima ka amince, ta yuyu ta wannan hanyarce zamu samu magance nuna banbancin Yare, sannan mu sakawa wadannan yara albarka shi ne alkhairi agaremu bamu yi kokarin rabasu ba” sai Alhaji ya dubi Mahaifin Mama yace “Babu komai, komai ya wuce Allah yakara ganar damu, a baya harna yanke shawarar ko ka amince ni bazan amince ba, amma yanzu ba abinda zance bayan Allah yasa ayi damu, sannan Allah ya albarkaci aurensu” sai kowa dake wurin yayi murna, musamman su Abdul da Mama.”
“Soyayyar Abdul da Mama ta dawo cikin farin ciki da jin dadi batare da wani shamaki ko fargaba ba, daman ita rayuwa mai hakuri yake da nasara, sannan kuma soyayya abu ce mai daraja wacce take da wuyar samu cikin sauki, haka zalika duk tsanani sauki yana nan zuwa. Yanzu gashi iyayensu sun amince da auren su wanda basu yi tsammanin samun wannan nasarar ba a baya, amma da yake komai na Allah ne gashi yanzu sun cimma nasara.”
“An saka ranar auren Mama da Abdul an yi komai da ake na aure kamar su, Lefe kudin Sadaki komai anyi har an saka rana.
Ranar Aure anyi biki cikin farin ciki da jin dadi, sannan an yi shi abin burgewa, an je Kano an daura auren Abdul da Mama,.”
“Da daddare abokan Ango su Usman da Bashir da Ibrahim da Mansur da dai sauransu sun kai abokinsu Ango wato Abdul dakin Amaryarsa wacce aka kawo masa tun sallar Isha’I da yake ba gari daya bane wato Mama. Sun yiwa Ango da Amarya huduba harma da zolayar da abokan Ango suke idan sun kawo Ango duk anyi suka tafi suka bar Ango da Amarya acikin daki su kadai.”
“Sun je sun yi Sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, sun zo sun zauna suka fara hirarsu, acikin hirar Mama ta kalli Angonta Abdul tace “Angona ashe daman zamu ga wannan rana a rayuwarmu?” cikin murmushi Abdul yace “Amaryata kenan, aini daman ban taba cire tsammanin ganin wannan ranar ba, saboda bana tunanin akwai wanda zai iya rabamu a duniyar nan in ba Allah ba” sai Mama ta lumshe ido cikin shagabawa tace “Hmm kaida kace ka yafe ni” “Wa! Hmm ai kawai fada ne nayi a baki amma ba haka bane a zuciyata ba, ya za’ayi na yafe wacce na sallamawa dukkanin lamarina, wacce kullum mafarkina itace, wacce zuciyata batasan kowa ba sai ita, ai ni dake babu mai rabamu” Abdul ne yace haka, sai Mama tace “to Allah yabarmu tare, sannan ya albarkaci rayuwarmu ya bamu zuri’a dayyiba” sai yace “Amin Amaryata shalelena” sai suka tashi domin kwanciya, a Daren ranar Abdul ya karbi hakkinsa wajen Mama Tasha wuya hannun Abdul shikuma sai faman zubamata Rowan, albarka yake, ya gasamata jiki bayan sunyi wanka suka haye gado rungume da juna haka bacci ya debesu.”
“Rayuwar auren Abdul da Mama ta kasance cikin farin ciki da jin dadi, don kuwa babu wanda ya taba jin kansu, shima kuma Usman ya samu wurin cin abinci koda yaushe, dan kullum acan yake zuwa yana kwasar girki ya huta da karbar bashin garin kwaki.
“BAYAN WATA HUDU”
“bayan wata hudu Allah ya azirtasu da samin ciki sosai sukayi murna kula na mussamman Mama ke samun wajen mijinta da dangi.”
.”Ciki Nada 9mnth ta haiho yan biyu duka maza, basai mun tsaya fadamuku farincikin da zasuyiba just imagine readers.”
“Ranar suna yara suka ci sunansu Anwar da a
Ammar, anyi shagali har mun hangosu xarah bukar, Yar Ficika, walliya,Maryam G,Anker, Belly badaru, asy Khallel,RAZ,da sauransu sunata kwasan rengem, bamubar su Mr smile, ililee, raheem jegs anyi shagali lpy an watse.”
“haka rayuwa taci gaba da tfy cikin jin dadi dakwanciyar hankali,yara suna girma suna kyau da wayo, Abdul yasami Karin girma a wajen aiki komai yana tafiya dadai ALHAMDULILLAH….. Muna wa Abdul da Mama fatan alheri a rayuwarsu Allah yasa mu dace ameen….
TAMMAT BI HAMDILLAHI….