SILAR AJALI CHAPTER C KARSHE
Tulin tsarabar da suka kaima Goggo ne ya rufe bakin ta fatanta a ce wani saurayin ne ya ma salma wannan kyautar ba ruwanta da ko da ace wani abin ne ya faru.
Haka rayuwa tayi ta tafiya babu daɗi sai godiyar Allah, wulakanci yau daban na gobe daban, burin ta dai a samu Salmah da wani mugun hali ta samu abin yayatawa. Ana haka rannan salma ta wanke kayanta, taje daukan dutse guga da yake goggo ta daukeshi daga dakin Salmah takai nata, nan kuwa tayi fir ta tace “ba zan ba da ba, wa’inda suka haifo ku basu san zaku yi guga bane, Shegiya da ido kamar na mayu”
Bata ce da ita komi ba ta saka hijabbinta na zuwa makaranta a yamutse ta tafi islamiyya, hakan ya kara kona ma Goggo rai don har ta dawo mita take akan zancen.
Washegari ta same ta bayan ta kammala duk wani aiki da ke gaban ta ta ce mata ” dan Allah inje gida Batulu mai nika in goge, kin ga goggo hijabbin ya kara yamutsewa da na wanke” Ta karasa tana marairaicewa abinka da dan makaranta ga shi tana ganin ta kai ga balaga dole a fita a tsabtace,+
Nan take ba musu tace ” eh”
Da murnarta ta shiga ta yo guga ba ta tsaya ko mi ba ta kamo hanyar dawowa.
Ta na shigowa zaure tana wakar ta da tafi so
Sarmadan ya masoyi Sarmadan sarmadan
Sarmadan har abada ni da kai..
Bata kai aya ba taji yakushi a fuska, ba ta dawo daga duniyar da taje ba ta hau dukanta da tsinuwa, take kayan ya zube a kasa faɗi take
“tsinanniya, ki zo ki fita ki bar min gida, mara godiyar Allah, mai farin kafa yaushe zaki samu mai kwasa, kar ki fara shigo min gida” Tana faɗi tana watsi da kayan salma, Har takalma tana jefa mata wasu jikinta
Sannan ta cigaba da “Allah ya Tsine miki Albarka idan kika doshi wani daga cikin dangina”.
Nan fa mutanen gari suka zagaye su suna kallo babu wanda ya yi yunkurin hana goggo abin da take. Take bakin ciki ya cika Salmah, tunani inda zata take don take ta dau alwashin babu ita babu wani dangi na ta. Tsugunawa tayi ta ranka tsince kayanta, anan ne wani mai shago kusa dasu ya miki mata jakar vivah kusan 7 yace “gashi ki sasu ciki” Ta amsa ba gardama bayan ta kammala kwashewa ne ta tarkata ta yi bayan gidan ta zauna, ba tare da ta san me zata yi ba.
Can mairo makwabciyarsu ta leko ta kirata, tace “Salmah tashi ki tafi kano ga kuɗin mota, ki je wajen Abbanku na Kano tun da ranar da ɗan saura”
Girgiza kai tayi ta ce “ban fa taɓa zuwa da kaina ba, kaimu akeyi shima sau ɗaya,”
Tace “to ungo waya kira abban, ba kwanaki naji ya baku lambar sa ba da ya zo,”
Shiru tayi ta tuna zuwan sa da yanda ya buda ma goggo wuta akan musgunawar da take ma Salmah. Abba shine babban ɗan Hajiya Aziza, aiki ya kai shi Kano, yana da son mutunta mutum, ya tsani zalunci. Tun farko jinin su bai haɗu da goggo ba, abin ya tsananta sa’ilin da ya ji labarin korar RAHANATU da akayi.
“Kin yi shiru toh” Ta sake faɗi
” ai banda shi ne” Ta amsa a ciki
“ina da lambar Asmau, matarsa, gashi ki kira ta kiyi mata bayani, in ya so sai ki kama hanya.” da rawar jiki ta amsa ta kira inna ta faɗi mata, ba tare da wani tunani ba tace maza ta taho gurinsu.
STORY CONTINUES BELOW

Ban yi wata wata ba ta tafi tasha ta shiga mota zuwa funtua sannan suka ɗauki hanyar Kano.
***
Tun komawarta Kano ta sami kwanciyar hankali, ba hantara babu kyara, sai dai babu zancen karatunta kuma, duk wani ladabi da sunkuyar da kai da take don a barta haka zata ga yaran gidan sun tafi duniya dawo amma ita ko oho. Ganin shekara daya ba labari ne wata rana ta tunkari Abban da zancen karatun. Budan bakin sa sai cewa yayi
“ki yi hakuri, har ki samu miji kiyi aure, fata na dai ki samu wanda zai barki kiyi karatun. Naso ko hadda ki cigaba don naji kuna shirin musabaqa ne, amincewar Goggo na ki zauna a nan sai da ta sani yin Alkawari babu ke babu makaranta. Ni kuma ki samu chanjin muhalli yasa nayi saurin amincewa. Ki je ki cigaba da hakuri ” Ya karasa yana mai tausaya mata.
” Tasan ba abinda nafi so sama da karatu, ashe shiyasa tayi saurin amsawa in zauna gunku, dan lokacin ina ta mamaki” Ta faɗi tana murmushi mai kona zuciya
Take zuciyar sa ta kamu da tausayin ta, nan ya tuna da wani abokinsa malam Abba(Adam Abdallah bn Abdallah) fari mai kyau, yana jan baki masallacin Sheik jafar lokaci lokaci, ɗan kasuwane harkar gwal. Kwanaki ya ke ce masa yana neman matan aure. Murmushi ya sakar mata ya ce
“Da yardan Allah kin kusa jin dadi Salmah” dariya tayi tai masa adawa lafiya ta koma dakinta.
Takakkiya yayi har zuwa wajen malam abba ya faɗa masa ya masa mata, bai yi wani tunani ba shi kuma ya amince ganin yardan da yayi ma sa.
Cikin kankanin lokaci malam Abba ya kamu da son Salmah, kuma baya kyashi ya nuna mata so, hakan ya sa ta bayan fage suka je suka nemi Hakimi har marke, shi kuma jin an ce malam ne ga gemu ga shi baya take wando nan da nan ya amince, yace masa ya ringa zuwa duk jumma,
Bayan zuwan su MARKE ne Abba ya saka Salma a hadda don ta cigaba da hadda, Ana haka sai aka bude Daura(islamiyya) da akeyi in an yi hutun boko nan ma ta shiga, karatun ta na ta tafiya. Goggo kuwa tun da Hakimi ya je mata da zancen Malam Abba take bakin ciki, nan ta dage akan lallai sai shekara mai kamawa za’a sa rana duk da cewa tun da ya ga Hakimi ya dage da naci shi sai ya turo iyayensa, Abba na cewa da sauran lokaci, azumi yazo yayi hidima fin zaton kowa, ana ta murna mahassada suka sa tushe, to sai ya zamana duk abinda M abba ya kai mats sai abba ya raba biyu ya kaiwa Goggo.
***
Kwatsam sai goggo ta yarda harsu malam abba su je, M abba yazo murna kamar me, kallon ta yake yana ayyana ya kusa mallakar ta a ransa.
“Wai ni ko wannan kallo na lafiya? ” Ta faɗi tana hure masa idanun da ya kafe ta da su.
” Kin kusa kwanciya a gadon da ya fi komi daɗin barci ne nake kallo in ga ko zan auno irin Barcin da zaki yi akai” Ya faɗi yana kashe mata ido.2
“Ya salam, gadon gidan miji har wani bambanci ne dashi da na gidan uba, ina ce duk katakai ne da katifa” Ta amsa tana masa kallon wanda ke shirme.
“Hmmmn ba wannan ba, kin ga gadon nan, in kika hau ko. Hmmmn wata sai ta manta Salman da Suhayl ” dariya ya sa mata ganin duk ta cukuikuya mayafin ta garin son ta rufe fuska.
” ina sonki sosai Salmah, ki rike wannan. Gobe Alhamis zamu je a sa mana rana, ba zan zo ba sai Asabar. Ki kula min da matata kin ji, ban da kamar ta” Ya faɗi fuskar sa sanye da farin ciki. Kamar ya kyafta ido yaji an ɗaura musu aure.
***
Sun je an sa rana sati uku bayan sallah, zai kama wata shida kenan a ka sanya, ranar Asabar ɗin da malam abba ya kamata ya koma wajen Salmah ne wani rikitaccen abu ya faru. Don shiru shiru tana jiran zuwan malam Abba babu shi ba alamun sa, sai chan da dare Suna zaune ita da inna matar babanta Abba suna gyara alaiyyahon miya sa ga Abba ya zo a fusace
“Salmah! Salmah kina ina, ana ganin Goggo na cin zalinki ashe ke ce Shegiya ban sani ba”
“lafiya abban yara” Ta tare shi cike da mamaki
“yanzu mu kai sallamah da malam Abba da kanin babansa, in ban da rashin ɗabi’a ace Salmah zata taka har gida ta ci mutuncin mahaifiyarsa, ni gaskiya ba zan ɗauka ba, tashi zatai ta koma marke” Ya karasa yana kumfar baki
Sakin baki tayi can tai kokarin daɗin
“Wallahi abban yara ba ta fita ba”
Take ta tare ta da ce wa “kikasan sanda ta saci jikinta taje, wannan ‘ya zata kashe mai rai”
Nan fa rikici ya kaure tsakaninsu Inna Asmau ta dage akan sam Salmah bata fita ko ina ba, don duk yinin ranar tare suka yi shi tana zaman jiran Malam. ABBA.
Tun daga lokacin wasu abubuwa suka fara bayyana a tare da Salmah ciki kuwa har da yawan kasala, faduwar gaba, yawan jin tsoro, da firgita ba gaira ba dalili.
Wataran ta buɗe ido ta ganta cikin mutane,
“lafiya kuwa? ” Ta tambaya tana waige waige
” Kyace lafiya mana, mahaukaciya kin ɗauki adda kin yanki titi kina ta gudu ai kya ce lafiya” faɗin goggo tana hura hanci
“Haba salame, wannan yarinya fa lallaɓa ta yaci muyi, dole tayi hauka kin irin wannan kunci da kika saka ta a ciki sanda take gidan ki” faɗin hajiya Aziza tana mai. Tausaya mata.
“ke dai hajiya bana gwaninta a idon ki in dai akan mayyar nan ne” faɗin goggo tana yake
IMRAN SALMAN
Tun bayan dawowar Salman Nijeriya ya ji duniya babu abin da yake so sama da yaransa, musamman Salmah da ta tsaya masa a rai. Ya wanke hotunan ta ya kafa su a bangon gidansa. Kullum sai ya shafa ya ce2
“kin fi kowa bukata na amma sabo da wani Kawa na duniya na zama Silar rabuwa da ke” kwallar sa kuwa kamar jira suke duk ya tunkari hoton sai sun zubo.
A dalilin haka ya shirya ya samu RAHANATU har ofishin ta kasancewar ta kammala karatunta na doktora (PhD) sai suka bata aikin malanta anan jami’ar tabuk ɗin da tayi.7
“lafiya malam, in har gaisuwa ya kawo ka mun gaisa ka bani wuri” Ta faɗi bayan sun gaisa a mutunce kamar da gaske.
“a iya sani na ko Allah ana ma laifi kuma ya yafe ko da kuwa laifin ya kai dutsen uhudu ne. Balle kuma mutum, ina kara neman afuwa a gurinki sannan ina rokon arziki guda ɗaya” Ya faɗa a sanyaye.2
Duk da jikinta yayi sanyi hakan bai sa ta nuna ba, illa ma kara tsuke fuska da tayi, ganin bata ce komi ba ya cigaba da cewa
“Na san na cutar da ke, na kawo ki duniyar da ba ki da kowa sai ni amma saboda ajizanci da nai miki sanadi na ki miki uzuri na yassar da ke a lokacin da kika fi bukatar kasancewa na tare da ke, ki yafe min, mu je Nijeriya a gyara mana auren mu, mu ɗauko yayanmu mu je Sudan sannan mu dawo nan mu cigaba da rayuwar mu kamar ko wane iyali. Yaranki na bukatar uwa, yarana na bukatar uba kuma babu wanda zai basu abin da suke bukata sai ni da ke. Don Allah ki duba kar ki ki” ya karasa yana mai durkusa mata hawaye na rigerigen fitowa daga idanunsa.
“in mafarki kake toh tun wuri ka tashi. Ni duniya in da wanda na tsana yana bayanka, ka san wahalar da Salmah ke ciki, mace mai rauni, ka zama sanadin da ya sa na kaita inda ba’a ɗauki mace a matsayin mutum ba, wallahi IMRAN da ba don ina tsoron hukuncin Allah ba da babu abin da zai sa in kashe ka ko a rage mugun iri”
“tsaya! Mugun iri har ya wuce uwar ki da ta gagara tarbiyyantar da ke, ke idanunki basa kallon miki alkhairin mutum ne sai sharri, ko ba gazawarki bane ya kaini ga aikata zina? Eh faɗa min da kika ganni a halaka kin yi yunkurin ceto ni? Duk naji ban kyauta ba amma ke ma har da ke a wajen ba da gudunmuwan rabewar gidanmu, yara ne ba ki kwada ki cinye na san dai komin daren daɗewa sai sun nemi uba, kuma ni ɗin ne zasu nema” tun daga nan ya sa kai ya fice ya barta da.2
***
Yana koma gida ya rubuta wasikar ajiye aiki, ya fara haɗa kayan shi waje ɗaya. Cikin kwana uku ya haɗe duk abin da yake bukata ya sa mu dilallai da ke harkan ba da hayar gida (estate agents) ya sa gidan shi shi kuma ya koka gidan baƙi na ma’aikatan jami’ar tabuk da zama.
Duk wani hannu da za’a sa masa an kammala cikin sati biyu, kuɗin sa ma haka bai tsaya komi ba, ya tattara yana shi ya bar Kasar Saudiyya zuwa Kasar sa ta gado wato Sudan.
***
Da faɗuwar gaba ya sauka a filin jirgin sama ta birnin Khartoum. Garin na nan yanda yake sai yan canje canje da aka samu na cigaba. Hawaye masu zafi suka sauka a kuncin sa. Tunawa da yanda ya tsallake mahaifarsa da iyayensa da duk wani dangi nashi saboda abin duniya. Gashi yayi bokon, ya tara kuɗi amma zafin rabuwa da nashi ya’yan ya hana masa zaman Saudiyya.
Dama masu iya magana kan ce “iskar da ta kaɗa yaro waje ita zata kora shi gida”.
Nan dai ya samu racsha (keke napep) ya ce da shi
” Inqazz za mu je”23
“Khamsa jinai” Ya amsa masa.
Bai ɓata lokaci ba ya shige suka tafi. Sunyi tafiyar da ya ke ganin ta fi komi tsawo ko don ya matsu ya ga irin tarbon da za’a masa ne ko yaya ne shi kan shi bai sani ba.
***
Gidan nasu na nan yanda yake, sai dai akwai wasu sashi da ya ga alamun an gyara yayin da wasu na nan sai ma kara lalacewa da suka yi. Haske ya wadatar da ko ina kasancewar dubun dare ya fara sauka
STORY CONTINUES BELOW

Zaune ya iske su da gani sun idar da magrib ne suna cikin abinci da shayi. Dattawa ne ciki babu wanda ya manta fuskar sa, mahaifinsa ne yan uwanshi. A hankali ya karasa cikin su ya tsuguna. Bai iya cewa komi ba sai kuka da ya saki.
“wane ne kai kuma da zaka zo cikinmu da kuka” faɗin yayan mahaifinsa cikin larabcin su na yan Sudan, murmushi yayi tunawa da yayi da mai maganar, duk cikinsu yafi su masifa.
“Dan ku ne IMRAN, na dawo gare ku ina mai neman alfarma, ku yafe min ku sa min albarka, na san na muku laifi”
Ya faɗi, duk suka tsaya cirko cirko kamar a ce da su cas su antari na kare.
Baban yayan mahaifinsa kuwa haska kafafunsa yake ko zai ga kofato don kuwa a sanin su IMRAN ya daɗe da rasuwa. Nan kuwa aka samu wani ya shiga cikin gida ya faɗa ma mata ga fatalwar IMRAN ya dawo. Mata duk suka tsure.2
Hawaye ya ke sauka a idanun wata dattijuwa, bata tsaya wajen masu hayaniya ba wajen wanda ya kira Salman din ta je. Haska keyarsa tayi don ta tabbatar da shi din ne, ta san ya taɓa jin ciwo da karfe, kuma tana da yakini tabon ba zai taɓa washewa ba.
Kuka ta saki haɗe da rungume shi, faɗi take “Na san zaka dawo, me ya sa ka guje mu” taas! Ta sakar masa mari,2
“Na ce mai ya sa ka guje mu” Ta kara faɗi tana mai kara wanke shi da marurruka. Sannan ta kara rungume shi. Nan fa mutane suka fara sharar kwalla don tausayin su.
“Ai duk wani so yana bayan son uwa zuwa da ya’yan ta” faɗin kanin Mahaifin Imran.
***
Ya ci ya sha, ya rama sallolinsa sannan ya kwanta yai barci. Ji yake kamar ya sauke wani nannauyar abu zuciyar sa.
Washe gari ya samu fiye da kwanuka ashirin na abinci, don har yan uwansa mata da ke aure a wasu unguwanni sun aiko masa da karin kumallo. Farin ciki sosai ya yi da ya ga kalar gatan da ya samu daga dangin sa.
Sai sa hantsi ne ya zauna da iyayensa maza da mata ya basu labarin sa bayan barinsa gida. Sunyi murnar karuwar zuriar su sannan sun nuna ɓacin rai akan yanda ya wulakanta RAHANATU.
“se ka shirya ka je ka Kwaso mana yayanmu, ai su dawo cikin mu kawai, in boko ne ma sun daɗe ba su yi ba” faɗin baffa. Shi dai IMRAN murmushi kawai yake yi don y ki yarda ya musu hanyar da zasu ɓata masa rai.
“ni kuma na tarbe shi da Auren Aisha. Ga sadaki ya biya a ɗaura aure, Aysha yar uwar ka ce, ni ne nan mahaifinta” faɗin wani kanin mahaifinsa. Wuri bai tashi ba sai da aka aura masa Aysha, aka tsaida lokacin biki.
***
MARKE 2014
“Kun ji min shaɗaniyar yarinya, ina ga in ta kashe ni zata huta” faɗin Goggo tana mai shigowa cikin gidan, dawowarta kenan daga gidan Hajiya Azizah anan ta tsinci labarin, ihun masifar da ta keyi ne ya dawo da hankalin Salman, Suhayl da da innarsu Amina wacce ta kawo ziyara, zaune suna hira.
“Ke kuma da wane ne haka Goggo” suka tambaya a tare duk da sun san in dai sun ji rigimar Goggo ne toh tabbas abin ya shafi Salma
“Salma ce mana, ta shirya ta saci hanya ta je har gida ta ci ma uwar malam Abba mutunci, Ace an samu wanda zai kwashe ta ba abin ta yi murna bane, shi ne zata je ta rusa abu. Yanzu da na shiga gidan Yallabai ne hajiya ke faɗa min ai Abba ya kira ya faɗa mata. Yarinya Shaiɗaniya wacce bata son kowa ya huta” Ta karasa tana mai jan tsaki
“ita Salman ce ta aikata haka” Salman ya tambaya cike da mamaki
“Don uban ku nayi muku karya ne ko kuwa ita Hajiya Azizah ce ta rattabo karyan. Ai in anyi duniya don manzo SAW sai Salmah tayi sanadin dawowar iyayenku babu shiri.” Ta faɗi tana share hawaye
“a ce ka haifi ya mace ko jaraba, uwarta ta yi cikin shege ita kuwa sai ta haifi Shegu da yardar Allah ” Ta ɗaura ganin ba wanda ya tanka mata2
“In dai zaki iya ɗaukar ciki toh akan ki za’a ga Shegu, wa ya sani ma ko in malam Tanko na gadi kwarto kike kawowa” marin da Salman ya sakar ma Suhayl ya sa shi yin shiru.
“Ba ka da hankali ne? Kana neman shegantar da uwar da ta haife ke ne ko me? Na sha faɗa maka abin da hakuri bai baka ba rashin sa ba zai baka ba. Ni tun da na dawo na ji korar da tayi ma Salmah kaji nayi magana? Ko kana nufin abin bai min ciwo bane? Amma tun da na tabbatar da tana hannu da ba za ta wulakanta ba sai na sa ido. Goggo ki ji tsoron haɗuwar ki da Mahaliccinki don zai tambaye ki amanar kiwon da ya baki” yana kaiwa nan ya fice ya bar su nan. Take Goggo ta sa sabon fagen zagin su da tsine tsine. Shima Suhayl ɗin gaba ya ci suka bar ta da masifar ta.
Tun bayan tafiyar Salmah take lallaɓa su, duk wani gata tana musu don a ganinta ya’ya maza su ne ya’ya, mata kuwa bala’i ne masu jawo ma mutum masifa. Ta ɓata Suhayl da rashin sanin babu, in har ya nemi abu wajen ta ko bata da shi zata je ta ciyo bashi don ta ba shi.
A dalilin haka Suhayl ya taso bai da kunya, ba ya kyashin daka mata tsawa kuma haka take lallaɓarsa yayi hakuri don ba zata juri ganin ɓacin ransa ba. Don a tunanin ta a wajen ya’ya maza kawai ake cin arziki, mace kuwa ka gama hidima wasu ne zasu ci moriyar ta. Hajiya Azizah ta sha faɗa mata2
“kin san dai mace Rahma ce ko, sannan ko duniya ne baza taɓa ci gaba in babu mata ba. Almuhim shine ka tarbiyyantar da ilmantar da ita, sannan ka koya mata dogaro da kanta. Hakan zai sa wani namiji ba zai hana mata abin kula da iyaye da yan uwanta ba. Amma in bata sana’a ai se ya bada ko? “
Ita kuma amsar ta a ko da yaushe itace “Haba dai Hajiya ai ita mace a kaskance take ko da yaushe, Allah bai ban ɗa namiji ba amma ya azurta ni da jikoki maza, wa me ake da mace”2
Ko da su Suhayl suka fice nan hankalinta ya kai kololuwa wajen tashi, sai ta fara da na sanin abin da tayi haɗe da kara jin tsanar Salmah a ranta, tashi tayi ba shiri ta bi su don ta shawo kan su.
Wannan kenan…..
KANO 2014
Tun daga faruwar zuwan gidan su Malam Abba abubuwa suka canza, sau da yawa Salmah kan tsinci kanta cikin tashin hankali da fargaba, ko kuma ta farka a firgice ta iske mutane kewaye da ita in ta tambaya sai a ce barci ta ke yi. Hankalin iyayen rukonta ya kai kololuwa a tashi.
Akwai ranar da ta shiga kicin don yin tuwo, inna ta barta tayi don ta ga anyi sati biyu ba tare da ta shiga matsala ba. Tana cikin tuka tuwon sai muciyar ta fara rinjayar ta, tun daga nan bata san inda take ba. Shiru shiru inna bata ji ta leqo ta ba sai ta fito ta ga ko lafiya, tun da ga kofar dakinta take jin kauri alamun tuwon na ƙone wa, cikin azama ta karasa kitchen ɗin wayam ba Salmah babu alamun ta. Sauke tuwon tayi a tunaninta ko ta kewaya bayi ne.+
Shiru shiru bata ba alamunta, anan ne hankalinta ya tashi ta nemi abba ta faɗa masa. Bai ɓata lokaci ba ya karaso gidan sun bincike ko ina basu ganta ba. An kewaya unguwar ba wanda ya ga gilmawar ta. Su Abba ne har gangare, shi da su Mahmoud (yaransa) da wasu samarin unguwa suka raba kansu wajen neman ta. Can kusa da makabarta aka tsinto ta yasshe gindin rimi.
“Ga ta nan” Aarif ya faɗa ma sauran. Nan aka kwashe ta babu ko alamun motsi a tattare da ita. Daga nan aka kaita wajen masu maganin hausa, nan ma dai ba wani labari.
“ina ga abin da zai fi ku mika ta zaria, gidan zuma in Allah ya yarda za’a dace” faɗin malamin da ke siyar da magungunar.
Shiru abba yayi yana tunani can ya sa waya ya kira RAHANATU2
“Gamu a Rahmaniyya Islamic center, Salmah ce ba lafiya ina tunanin jinnu ne ko kuma frustration ya jawo mata hauka, ki yi ma Allah ki dawo ki kula da ya’yan ki, ki kuma turo min lambar uban nasu” Ya faɗi ba tare da ya amsa gaisuwar ta ba.3
“Goranta min rikon da kake mata za ka yi ko tun yanzu har ka fara nuna gazawarka ” Ta faɗi a kuntace5
” kin san matsalar ki? Kin gagara cin jarabawar da Allah ya ɗaura miki ne, ki dawo ki kula da yar ki tana bukatar ki kusa” Ya faɗi yana mai kawar da maganar ka da ya ɓata masa duk da kuwa ya soke shi
“ina da aiki sosai a gaba na, ka san dai aiki a Saudiyya ba kamar naku na Nijeriya bane da za’a sa algus a ciki. Ko na dawo ma ai ba ni ke bada lafiya ba, addu’a ce ko, zan mata dawafi Insha Allahu. Allah kara sauki” Ta faɗi tana mai kashe wayar.13
Sakin baki yayi galala, a tunaninsa uwa ba zata iya hakan ba. Wani lokutan in malamai na faɗi a wa’azi ko ya ji a shirin jakar magori abubuwan da iyaye ke ma yayansu sai ya ga ai kamar kaharu akayi amma sai gashi a nan kusa da shi hakan y faru.1
“Mtsw! Allah ya kyauta” Ya faɗi a bayyane yana mi komawa ga inda Salmah take.
***
Duk gidan babu wanda ya runtsa, ga dai salma na numfashi amma hauka hauka kawai take. Kuka kuwa har na dabban da basu sani ba tayi, can ta zauna tayi shiru ba Um ba Um um, sai hawaye. A haka aka ɗauke ta zuwa zaria, sun samu tarbo na girmamawa da karamci kafin a fara aikin.
***
Satinta ɗaya amma bata san wa ke kanta ba, Gata dai ido biyu amma ba um ba um um , sai daga nan ne aka fara shawo kanta, zata yi hira ta fahimci mutane yanzu Anjima kuma ta rikice.
A sati na uku ne aka samu tayi garau, kamar ba abin da ya same ta. Sai dai tun da ga lokacin ta rage magana. Haka zata zura ido tayi ta kallon mutane. Bayan komawar su kano ne Abba ya shirya ya je marke ya ɗauko Salman da Suhayl, da sunan zai sa Suhayl a makaranta kasancewar Salman na karatu a jami’ar ɗan fodio. Hankalin su ya tashi kwarai ganin jikin Salmah.
“Na kira mahaifiyarku amma neman duniya ya rufe mata ido ta ki ta saurare ni. Yanzu so nake ka kira mahaifinku ka faɗa masa yar sa ba ta da lafiya. Kun ga bai kyautu ya ji abu daga sama ba” Abba ya ce da Salman da ya kasa sukuni ganin halin da Salmah ke ciki.
“Shima ya koma Sudan tun bara, ya ce min yayi yayi su maida aurensu amma ummi ta ki, bara na gwada lambarsa na Sudan din mu ji” Ya faɗi yana gwadawa amma lambar ta ki shiga. Ya faɗi a maraice.
***
A cikin wata uku Salmah tayi kyau tayi ɓulɓul Abinta, kwatsam sammaci ya iske abba da ga marke, ya je yayi kwana biyu ya dawo jiki a sanyaye, washe garin ranar da Salmah ta je gaida shi ne ya ce da ita
“shirya, zamu fita zuwa karfe takwas na safe” Ta fita tana murna don rabon sa ta Fita har ta manta.
Bayan ta shirya ne ta shiga dakin inna don yi mata sallama, sai ta iske tana goge kwalla.
“lafiya inna kike kuka” Ta Tambaya hankali a tashe don ta fi son inna akan uwarta
“kwaro ya shigar min ido, kada kiyi wasa da addu’a kinji har ki je ki dawo” Ta faɗi tana murmushi sa kallo ɗaya zai sa a gane bai wuce fatar bakinta ba.
“kin wani tasa ta gaba kina kuka, bari in je in dawo mu tafi Salmah” Ya karasa yana mai kallon Salmah bayan ya jefi Inna da harara
“ina zamu je ne Abba” Ta faɗi tana share kwallar da ya ciko idanunta2
“gidan mahaukata na dorayi zan kaiki, su rike ki kar muje wataran kiyi inda bazamu kara ganinki ba” Ya faɗa a tausashe yana shirin fita ne ta ce
” Abba dan Allah to zaka kaini boarding school in karasa karatuna in mun dawo daga ɗorayin” kawai ya zuba mata ido, idonsa rau-rau kamar mai shirin fashewa da kuka, sai ya fice ba tare da cewa uffan ba. Inna kuwa kasa kunshe kukanta tayi.7
Nan take Salmah tace “inna ki daina kuka ki sa min buttermint da madara mutafi” kasancewar ta da son buttermint. Tun lokacin kuka take har Abba ya dawo ya sanar mata za shi Kaduna wani taron gaggawa, amma kaninsa Gambo da dan sa Mahmood zasu kai ta.
***
Wajajen karfe biyu na ran ne suka iso don tafiya da ita. Rungume ta tsam inna tayi tana kuka, tana jin zafin abin da mijinta da dangin sa suke shirin yi. Take ta ji ta tsani RAHANATU, ace ka haifi ɗa ka watsar, duk da kwanaki a shirin Darajan mata da ke zuwa a rediyon firidom anyi hira da kungiyar sccvolunteers masu rajin kare hakkin mutane daga kowani irin cuta sun ce2
“yayin da akayi ma yar ku fyade, saurin aurar da ita ba shi ne mafita ba saboda akwai wani radadi da suke rayuwa dashi. In an san wanda ya aikata mika shi ga hukuma shine abin yi don kare wasu da ga shiga tarkon shi, sai a kai yarinyar asibiti don nema mata magani. Ba wai maganin jikinta kawai ba har da na kwakwalwanta domin fyade kan zare ma wanda aka yi ma sinadarin tausayi, yana busar masu da zukatansu hakan zai sa su kasance masu kafiya, da son kansu da yawa….. ” ranar hawaye ta yini tana yi tana sauraron shirin. Ta so ace mutane zasu dinga damuwa da halin da Yaransu ke ciki yayin da aka musu fyade, don iyaye damuwar su kawai su aurar da su kar ta jawo masu abin kunya.
” Allah na tare da ke Salmah, Kije zai kare ki kinji, ga buttermint ɗinki, zan dinga zuwa duba ki kullum” Ta karasa tana kuka, a haka suka rabu dukkan su shaɓe shaɓe da hawaye
***
Da isarsu asibitin ofishin shugaban asibitin suka isa kamar yanda Abba ya umurce su, bayan sun masa bayani, kallon Salmah yayi da ga sama har kasa sannan yace “ita ce Sani yace ku kawo min kuwa?” Ya tambaye su cike takaici
“Eh itace” faɗin Mahmood
” Wallahi bazan kar6i yarinyar nan ba, wannan wane irin rashin tausayine, ba ku san zama da mahaukaci yana maida mutum irinsu ba” Ya faɗa s fusace
Bai kara cewa komi ba ya sa waya ya kira Abba,
“Dr taimaka ka amshe ta yanda na faɗa maka, zan zo in karbe ta in lokaci yayi” Ya tare shi kafin ya masa wani maganar. Jiki a sanyaye ya sauke wayar, Ya Kalle ta yace “kina son zama anan ?”
Na daga masa kai kawai tayi, haka kawai ta ga ya kama kwalla yana fadin “Wallahi da ‘yata ce bazan iya mata haka ba” Ya faɗi yana Share kwalla, Salmah kuwa zuciyarta ya bushe ba ta ko damu da kwallar da su ke yi ba, kara rikon jakar buttermint dinta ta yi kamar kwace mata za’a yi.1
Sakatarensa ya sa ya kira masa wata likita mai suna Aisha, bayan ta gurfana a gaban shi ne yace
” dauketa amman karki hadata da sauran mahaukata, zai kyautu ki barta a wajenki har na zo.
Maimakon su fita sai ta fara auna ta haɗe da mata wasu yan tambayoyi, nan ta hasala tana kunci ta ce “ciwon yarinyar nan in ma da shi bana asibiti bane” nan kowa ya msta shiru, ganin haka ta ce salma ta bi ta su je.
Da suka fita ne ta tambaye ta “dama an taba kaiki ne, ko nan aka fara zuwa da ke”
STORY CONTINUES BELOW

“Eh, kwanaki da Goggo ta zo ta sa an kaini Dawanau, sai suka bani magani mai karkatar min da baki, da na faɗa ma inna tace kar na kuma sha” Ta faɗi a hankali kamar bata so a ji ta, sai ta kara da
“shine na zuba su a masai”
“Good! Kin kyauta Wallahi, ai se da haka, su basu san maganin nan da kin sha da yawa ai da Se sai a tsince ki a titi kin koma cikakkar mahaukaciya, gaskiya basu kyauta miki ba. Yanzu dai kar ki dinga barin kan ki a bude in ba haka ba, kwarkwata zakiyi” Ta gaya mata suna shiga dakin.
“zaki zauna nan kinji, dakin matron ne, kin ga ba zan haɗa ki da mahaukata ba, zan sa a kawo miki su detol da sauran ababen hana ɗaukan cututtuka ” Ta ce tana Shafa mata baya.
Bata bar ta ba sai da ta tabbatar da su Mahmood sun siya mata detol na ruwa da sabulu, ta ce ta dinga zubawa a wajen fitsari ta kore da ruwa kafin ta yi fitsari sannan ta dinga sa wa a ruwan wanka.
***
Washegari ta fito kofar dakin tana akllon mahaukata, wata in ta danna da gudu sai ta kai karshen gidan, Wasu dambe, wasu rawa, wata kuma kawai sai ta fashe da kuka
Can sai ga wata kamar ba mahaukaciya ba ta zo ta zauna kusa da ita tace “ya sunanki?” cike da murna ta amsa mata ganin ta samu yar uwa “Sunana Salma Imran”
Tace” kema kishiya ta kawoki nan kiyi karatu ko” kawai salma ta bita da ido can ta ce ” ke ya suna ki?”
Tace “fadima”
“suna mai dadi” salma ta ce, nan suka sake suna ta hira abin su, can fadima tace ,
“Salmah sai naji ina sonki”
” nima haka kin ga mun zama yan uwa”
ta sake cewa “kin san fadima Yar manzon Allah”
A tare suka ce “sallahu alaihi wa sallama”
“Eh mana na Santa a tarihi” faɗin Salmah da murnar ashe ita din ba mahaukaciya bace, don ta tsinci shirme a maganar ta hirar da suka yi
“Toh ai nice, yar sa matar umar alaihis salam” dariya salma ta fara har tana kwanciya, nan fa sauran mahaukatan suka yo gun su suna dariya suma. Salmah sai ta kalli fadima sai ta aza wani dariya, nan sai su ma sai su saki wani dariya.
“Salmah” shine tsawar da aka sai a kansu, Dr Aisha ce
“maza tashi ki shige daki, nace miki zaki zama su ko, gashi tun ba’a je ko ina ba” tashi tayi a tsorace ta shige ɗaki aiko fadima ta biyo ta tana fadin4
“Wallahi duk wanda ya ta6aki sai na sa takobina na sare masa kai” sai ta daga hannunta alamun shine takobin, hakan yasa salma murmushi
***
Cikin wata ɗaya salmah da Fadima sunyi mugun sabo, in haukan ta ya tashi babu mai iya rarrashin ta sai Salmah, amma duk abin ta in mijin ta ya zo sai ta make da shi a ɗaki. Salmah ba ta dago komai ba har sai ranar sa ta ji Dr Aisha na fadin
“shegiya dole kishiya ta haukataki ai kina cin nama a daki, ke me miji ko, nan in na kawo ma Salmah abinci tare kuke ci duk da ke kina cin abincin wajen nan, oh Fadima mai miji” nan ta rufe fuska ta ce
“masoyiya ta in babana annabi Muhammadu ya zo ai zamu je ki ganshi ko” Ta faɗa tana murmushi.
A haka suka koma hira, wanda akasari na Fadima shirme ne, don rayuwar sahabbai take juyawa tace ce ai da ita a wajen ko? Nan kuwa salma zata samu abin so tai ta kyakyata dariya.
***
A cikin wata na biyu da tafiyar Salmah ne Aasif, Haruna da Mahmood suka je marke haɗe da abba. Anan suka je gidan Goggo don su gaishe ta, ko amsa gaisuwar su bata yi ba tace
“Ta na chan cikin mahaukata ko?, na san yanzu ai ta zama su sak, don saadu ya ce matukar na birne komi ma zai faru” Sai da tayi furucin sannan ta ankara da wainda take Maganar, ta juya ta ga ai Suhayl ma ya fice.
“ai gara da akai mata hakan. Yarinya se kace mayya, kin ganta kuwa? Ai in ta samu dama titi zata bi” faɗin Mahmood
“kai ɗan Albarka, yanzu babu yanda za’a yi a sake ta. Yarinya sai shegen bakin jini, ni fa na tsane ta Wallahi “
” zan san yanda za’a yi. Ki kwantar da hankalinki kin kusa ganin gawar ta” Ya faɗa yana sakin muguwar dariya. Shigowar Suhayl da Salman ya sa suka yi sallama suka fice.
***
“Amma ya Mahmood ka san abin da kake faɗa kuwa” faɗin Aasif rai a ɓace
“Toh so kuke ta sake yin wani abin, nayi mamaki da abba ya amince farat ɗaya ashe asiri matar nan tayi. Yanzu dai Bara mu san yanda za’a yi mu ga Salman, don duk laifin shi ne, da ace basu da dangin uba ne sai su tsaya, amma tun yaushe nake ce masa ya kira shi ya faɗa masa yaki”1
“ai yanzu abin da za’a yi, mu san yanda za’a yi mu fito da ita, sai a san abin yi a gaba” faɗin Haruna
***
Ba su samu ganin Salman a keɓe ba sai bayan mangariba, nan suka tsare shi har sai da yayi waya da Mahaifin su, cikin sa’a kuwa ya same shi, bayan sun gaisa ya ke faɗa masa matsalar Salmah.1
“Ashe dai baka ɗauke ni a matsayin uba ba, yata ba lfy tsawon shekara amma a gagara faɗa min. Yanzu dai zan neme ka zuwa gobe.” Ya katse wayar yana mai bakin ciki.1
***
Cikin sati ɗaya da taimakon Dr Aisha suka shiga suka fita aka ba Salmah sallama, suna kuka suka rabu da Fadima, har sun kusa kofa suka ji Fadima ta ce
“Salmah yaushe za ki dawo” Ta karasa tana bye bye da hannu ɗaya sannan tana Share hawaye da ɗayan.
Duk da tausayin ta da suka ji Haruna yaji takaicin tambayar, a fusace ya ce
“lokacin da ubanki ya dawo gidan nan” dariya suka sa masa su duka.
Tun fitowar ta, suka maida hankali wajen mata ruqya da amfani da magani, sai a sannan Aljanun suka fara magana in da suka bayyana cewa turo su aka yi.
Tun da Mahaifin su ya turo kuɗin tafiya domin cewa yayi ta dawo Sudan zasu mata magani, Salman da Mahmood suka haɗu suka dinga nema ma Salmah tikiti, biza da fasfot na tafiyar ta Sudan. Cikon ikon Allah suka kammala lafiya. Jirgin su ya tashi sai birnin KhartoumIMRAN…
Tun da ya sauke wayar Salman ya shiga tashin hankali, hawaye ya fara zuba a idanunsa, takaicin kansa da RAHANATU ya cika shi. A sanyaye ya karasa sashinsa inda yake zaune da amaryar sa Aisha,
“Sannu da dawowa” tace da shi tana mai murmushi, ganin yanayinsa ya sa ta shan jinin jikinta. Zama yayi gefenta yana mata murmushi da ya fi kuka ciwo,
“Na faɗi jarabawar da Allah ya min na matsayin uba” Ya faɗi a cije, sai hawaye kuma shar! Tsam ta tashi ta kawo masa ruwa mai sanyi ya sha, ya saki ajiyar zuciya, a hankali ta ke tausa masa kafafunsa lumshe idanu yayi, hawayen ya tsaya amma sai sakin ajiyar zuciya.+
Sun fi karfin minti talatin a haka, can ta tashi ta kai masa ruwa yayi wanka, ya fito nan ne ya ji kamar ana sauke masa nauyin da kansa yayi. Zaman da yayi kusa da ita haɗe da cire mata tagumin da tayi ne ya ankarar da ita dawowa shi. Murmushi ta sakar masa ta kauda fuska.
“in karo maka ruwa kasha ko? Ta tambaya idanunta cikin nasa tana mai aika masa sakonni wanda yake ji tun daga kwanya har tafukan kafarsa. Janyo ta yayi jikinsa ya raɗa mata abu a kunne yana shafo cikinta da ya turo riga. Dariya tayi tana ɓoye fuska a kirjinsa. Shi ɗin ma taya ta yayi. Sannan yace
“ɗan ki ne ya kira ni, wai ashe Salmah bata da a lafiya ina matsayin ubanta ban nema mata lafiya ba. Har ya kai ga an mika ta asibitin mahaukata duk da ciwon ta jinnu ne” Ya faɗa muryar sa na nuna tsantsan haushin da yake ji.
“Subhanallah, inna lillahi wa wa inna ilaihi rajiun, mahaifiyarsu fa?”
“shi ya sa Allah ya ce mu nema ma yaranmu uwa ta gari kuma ku nema masu uba na gari, wannan hakkinsu ne da in ka kasa za’a muku hisabi akai ranar gobe kiyama, da ga ni har ita mun gaza anan. Bata zaɓa musu ba nima ban zaɓa musu ba” Ya karasa yana mai kukan da yafi jini ciwo.1
“ai ba kuka zaka yi ba, akwai masu magani da dama a nan, yanzu dai ka shirya dawowarta, in ta zo sai a nema mata magani a aurar da ita, ka ga shi kenan yar ka ta dawo kusa da kai. Ko a cikin yan uwa ba za’a rasa ba. Don Kaga akwai masu ilimin zamani ma a cikinsu. ” haka ta cigaba da karfafa masa gwiwa tana nuna masa ai gara ya dawo da yar sa kusa da shi don sauran dole su nemi dangin su kasancewar su maza.
A ranar ya cika da alfaharin samunta a matsayin mata, don shi ya san so ɗaya ne kuma rahanatu yake ma wannan so ɗin.
***
Tun da suka tsaida maganar dawowar Salmah Sudan ya shiga bincike akan malamai da zasu mata maganin jinnu, da ya tabbatar da ya samu ingantacce ba mai tsubbu ba a Unguwar Ma’amoorah. Gini nai ya ji gini na asibiti mai tsada, amma duk magungunan musulunci suke badawa. Nan ya shiga ya tambayi yanda abin yake suka masa bayani kuɗaɗen da irin magungunar. Bai bar asibitin ba sai da ya yi booking.
Washegari ne ya kira Salman ya tura masa kuɗin da zasu shirya ma Salmah tafiyar. Sannan ya faɗa ma iyayensa da sauran yan uwa Salmah na tafe. Nan murna ya karade zuriar, take aka fara shirye, ana aika ma yan uwa na nesa da na kusa.3
***
Ranar da aka kira shi kan cewa jirgin su Salmah ya taso nan ya cika da murna. Yar da rabon da ya ganta tun tana da shekara hudu zuwa biyar ce zai gani a yanzu. Can ya tuna da rabuwar su da RAHANATU, take zuciyar sa ta tunatar da shi kalaman su na karshe ga junansu. Take ya zaro waya ya danna lambobinta. Kara na uku ta ɗaga, zazzakar muryarta na masa sallama.
***
RAHANATU…
Zaune take, ta dawo daga wani taro da aka yi na yan asalin Kasar Nijeriya da suke zaune a Kasar Saudiyya. Hankalin ta ya tashi saboda wanda ta gani a wajen hakan ya sa ta barin wajen ba don ta shirya ba.
Suna zaune kamar an ce ta ɗaga kai nan ta haɗa ido da shi. Bata wani saba da shi ba ko san da ya ce yana son ta, amma ko ya siffansa ya chanza ba zata taɓa manta fuskar da ta ɓata mata rayuwa, fuskar da kan zo mata cikin kashi a 70% na Barcin ta tun faruwar abin. Fuskar da mamallakin sa ya zama SILAR AJALIn mahaifinta da ta fi so duk duniyar nan. Fuskar da ta hana ta tausayin ya’yan ta lokacin da suka fi kowa bukatar ta. Take ta ji ta tsani zaman Saudiyya, bata kai ga tantance abin yi ba taji muryar sa na faɗin.
STORY CONTINUES BELOW

“wasu a suna ne kawai suke zaune a Kasar nan bisa ka’ida amma in da mahukuntar Kasar Saudiyya ta san ɓarnar da suka yi a kasashensu da su suka kada ba tukuri ba. Wasu ya’yan su na chan ba gata, suna rayuwa a kauyukan mu na Nijeriya mai cike da talauci amma suna rayuwa da fiye da dala miliyan a Kasar nan. Wasu matan Tsabagen son abin duniya suna zaune su ba muharramai ba, su ba mazaje ba, su din kuma suna da yaya a wahalce a Kasar Nijeriya, wata ma anan yayanta Bara su ke. Wasu mazan sun bar iyalansu a can ba sa zuwa sai shekara shekara. Babu ruwan su da hakkin matansu da ke kansu na biyan bukata, in tayi magana ace jarababbiya in Shaiɗan ya rinjaye ta ga aikata zina a ce yar iska. Mu ji tsoron Allah mu san duk wanda ya ke zaune anan ba tare da iyalinsa ba ya je ya dauko su ko kuma ya koma gida da zama. “5
Nan take ta ji bata taɓa muzanta irin yau ba. Wato bayan ya illata mata rayuwa, har yan da bakin da zai aibace ta, bata jira ya kammala ba ta ja kayanta zuwa gida. Ta zauna kenan wayarta ta hau tsuwa. Kallon Numb ta yi, tabbas lambar Sudan ne.
” kar dai ace mutumin nan ya rasu me zan ce da yaran nan” Ta faɗa a bayyane yana mai ɗaga wayar. Tun da ta samu labarin ya bar Kasar bata ji daga gare shi ba
“Assalamu Alaikum warahmatullah” Ta faɗa gaban ta na faduwa,
“umm Salman” ya ce bayan ya maida mata da sallama.
Gaida shi tayi duk da tana jin muryar sa ne, amma a tsorace take, maganar da ya mata ya katse ta.
“Insha Allah nan da awa biyu zuwa uku Salmah zata iso Sudan. Ban sani ba da ranta ne ko gawar ta za’a kawo, na dai san sun tuna ba su gatan da ya wuce nan shi ya sa suka ga ya kamata ta iso nan ne bayan sun kuɓito da ita daga asibitin mahaukatan da marasa tunani suka kaita don su karasa haukatar da ita” bai jira amsar ta ba ya kashe wayar.
Hannu ta sa akai, yau da wani irin sa’a ta tashi da aka tozarta ta sau biyu a tare.” Su din basa duba matsala ta ne, ba su damu da damuwata ba” Ta faɗa cikin kuka.10
Wayar Salman ta fara nema, bata samu ba, nan tai tunanin aika masa sako ta WhatsApp, kunna data dinta ke da wuya sako ya shigo mata ta hanyar akwatin sakon gmail. Hannun ta na rawa ta buɗe ganin daga kamfanin da suka bata aikin ta ne. Wasikar dakatarwa ce daga aiki ne. Sun kuma bata awanni 48 ta dawo musu da duk wani abin da take rike da shi na kamfanin su sannan sun daskarar da akawun dinta na banki da duk bin da ta mallaka. Kuka ta saki, har da gunjin ta. Sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta fara baza kaya
“zan koma in rungume ya’yana, Imran kayi kaɗan ka kwace min su” tana kuka tana fadi kamar wata sabon kamu.
“Hmmmn! ” ajiyar zuciya kawai Salmah ta saki yayin da taji sanarwan saukar jirgin su.
” ko da wani fuska zasu karɓe ki” wani sashi na zuciyar ta ya tunatar da ita.
“Gbam! gbam! Gbam! ” Kawai take ji sautin bugun zuciyar ta da ke ɗaga rigarta.
” Allahu ga baiwar ka nan kada ka sa rayuwata cikin garari” kawai ta tsinci bakin ta da faɗi.
Bayan saukar su, sun bi dogon layin bincike da karɓan kaya wanda ya kai musu awa biyu cur. Nan ta jiyo kiraye kirayen sallah, kai ta ɗaga taga garin ya rufe luf alamun magriba. Kallon agogonta tayi ta ga karfe huɗu da mintuna arba’in. Kallon agogon da ke manne a bango tayi, nan ta ga shida da minti arba’in.
“Subhanallah, amma karfe biyu fa jirgin mu ya taso. Ji lokaci” Ta sa mu kanta da faɗin haka. Ɗalibai biyu da suka sauka tare Rukayya da Zahra, suka sa mata dariya. Itama se wayance ta ce
“Yoh ni dai naga dai bai isa muyi tafiyar awa huɗu ba, sannan kuma ga agogo na ya nuna min karfe huɗu, ko nan ma irin Turai ne da sukan yi magriba da karfe huɗu in yanayi ya chanza” Ta karasa tana mai nuna iyakar gaskiyar ta kenan.
“kin san haka amma kin gagara sanin akan samu bambancin lokutan tsakanin yankuna” Zahra ta faɗi, Rukayya kuwa dariya ta kara tuntsirewa kamar ta gano Ummu-Abdoul tayi kuskuren larabci.6
Sai a lokacin hankalin ta ya kai ga haka. Tabbas malamin english ya taba faɗa mata.
“Allah sarki ko yana ina, bawan Allah mai son mu amma tun da ya ce ta tafi aiki Kasar waje bai sake waiwayo mu ba” Ta faɗi a ranta2
“kika sani ko yazo bakya marke” zuciyarta ta tuna mata.
A haka har layi ya kawo kansu. Nan Rukayya tayi ajiyar zuciya tace
“Allah yayi, ni abin da ya sa na tsani Sudan kenan. Abba ya ce kowace kasa ana samun cigaba a wajaje musamman filin jirgi amma banda Sudan. Yace tun lokacin su na yara fa haka nan take sai sun kwashi layi kafin ka gama clearing komi tun daga arrivals har departure”
“Bara yan kasa su ji ki, ni ba ruwa na” kallon su sa salma keyi ya sa suka tambaye ta.
“ke me ya kawo ki Sudan? Mu Kinga karatu muke a jami’a.”
“Nazo wajen Mahaifin mu ne, shi dan kasar nan ne amma babar mu yar MARKE ce a Nijeriya, amma yanzu tana Saudiyya”
“Allah sarki. In kin amshi jakar ki, can zaki bi zai sada ki da inda ake jiran baki” suka faɗa mata. Da murna ta gode musu, lokacin aka kawo kanta.
***
Bayan ta gama komi ta je inda suka ce ta bi. Tana ta waige waige ga gari na kara rufewa. Can ta hango su zahra sun shiga taksi sun fice, kamar ance ta waiga nan ta ga wani mutumi dogo, ras! Gaban ta ya faɗi tayi saurin kauda kai.
“Daga ganin tsawon nan na mutanen Sudan ne ba MARKE ba, Marhabanbiki yaa Habibty” Ya faɗi yana ɗan rungume ta, tare da sumbatar goshin ta.
Wani daɗi da ni’ima ya sauka a gare ta. “Alhamdulillah” kawai ta iya faɗi sai kuka shar. Share mata hawayen yayi sannan ya rike hannun ta da hannun dama hannun hagun sa na rike da jakanta zuwa motarsa kirar Hyundai sonata 2.0t. Sai da ya tabbatar da ta zauna da kyau kafin ya rufe kofar, ya saka kayan a gidan baya sannan ya shiga gefen direba ya ja su suka tafi.+
STORY CONTINUES BELOW

Kalle Kalle kawai take ganin yanda hasken lantarki ya mamaye ko ina,
“ki gode Allah kakanmu ya baro kauyenmu Kasala, da ya tashi sauka kuma sai ya kafa tushen sa a inqaaz, inqaaz kashi 80 na mutanen yankin Hausawa ne yan Nijeriya, da wasu kakanninsu na uku ko huɗu ne suka shigo Sudan. Zaki samu dukkan abincin da kike so irin naku na Hausawa ” Ya faɗi cikin gurɓatacciyar hausar sa. Ai ko take ta tuntsire da dariya tace6
” har ka tuna min da ummitr, aminiyar kwarai” kallon ta yake cike da farin ciki, sam bata da bakonta.
A hankali yake tuki amma sai ga shi har sun isa gidan. Mutane ne fal kamar ana biki. Kafin ya kashe motar sukai masu yuuuuu. Kowa na son ganin Salmah. Haka dai ɗan da kyar ta iya fitowa har suka kai ga shiga gida.
Bayan ta rama salollinta ne aka gabatar mata da Asida haɗe da Eish. Asida abinci yan sudan ne da ake yi da bushashen nama, vegetables, madara da dankali. Ana girka shi ne kamar faten dankali, haɗe ake ci da Eish wanda yake wani naui ne na burodi ko gurasa.
A gefe daya kuma fura aka dama ya ji madara, can ga kayan marmari nan duk sai ta rasa Wanne zata ci Wanne zata bari. Take yan uwanta suka faɗo mata a rai
“ina ma duk kuna nan Kuga gatan da muka rasa” Ta ce faɗi a ranta.
Se da Taci rai qat sannan ta samu ta kwanta ta huce gajiya. Washegari taron mutanen sun ninka wainda suka tarbe ta. Nan ta kara gode ma Allah kasancewar su yan dangi.
Sai da tayi sati bata zauna ba, kowa na son ta kai masa ziyara. Itace har asalin kauyen su mahaifinta Kasala, anan ne fa hira ya zama matsala don kwatakwata ba sa ko jagwalgwalon da yan inqaaz ke mata da sunan hausa. Kwana biyu tayi sannan ta dawo gida.4
Sai a lokacin ta samu ta dan yi hira da mahaifinta, sannan aka kaita wajen magani. Cikin ikon Allah sai tayi sarai, bata ko jin ciwon kai balle kuma ace ta ji ta fita hayyacin ta.
Kwatsam sai wani abokin mahaifinta da sukai zama tare a Saudiyya. Zuwan nasa ne ya faɗa masa RAHANATU ta koma Nijeriya gaba ɗaya sannan ya cigaba da bashi labarin abubuwan da suka faru.
Taha, Balaraben Saudiyya ne, zai yi kusan sa’ar IMRAN in bai girme shi ba. Dan sanda ne, masu bincike kasa kasa da ake kiransu da kanunil dauli a gargajiyance amma asali akan ce dasu MAHAIMINE ne sai dai shi nashi na bahsal amnil Dauli ne. Shi ke kai ma IMRAN labarin Sudan a wancan lokacin da yake Saudiyya in aiki ya biyo da shi Sudan.
Tun da ya kyalla ido ya ga Salmah, ya ji bai da wani buri da ya wuce ya mallake ta a matsayin matarsa. Bai bar ma cikin sa ba ya furta ma IMRAN, da fari yayi shiru ne amma tunawa da karamci irin na Taha da taimakon da ya masa zamanin da suke Yambus sana’iyya sai ya amince. Ya faɗa ma yan uwansa da iyayensa duk suka yi Na’am da shi…4
***
“kana ganin ba’a mata shigar sauri ba kuwa? Duka duka yaushe ta zo, bata san daɗin uba ba zaka aurar da ita ga wanda ya girmi ubanta, ni sai gaskiya ban ba da goyon baya ba” faɗin ummah (sunan da Salmah ke kiran matarsa kenan)
“kul! Ke shawara akai da ke kafin a aura min ke, ko bamu zame ma juna alkhairi ba. Ki faɗa mata Sudan ba Nijeriya bane da mace zata kaso aurenta ta samu matsuguni gidan ubanta saboda su har da Sakacin mazajen. Nan duk abin da ka riske zaka rufe ne ya gyara zamanka daidai da shi. Gara tun wuri ku kula” Ya faɗi yana kurban ruwan shayinsa da aka yi da ganyen soɓo.
Sai da ya dawo isha’i sannan ya faɗa ma Salmah abin da ake ciki. Da murmushin ta tace “Allah sa ina da rabon auren, Abba na a Nijeriya duk wanda ya zo da an fara zancen aure ake neman sa a rasa” take tausayin ta ya kama shi.
“saboda mijinki na kusa da abbunki ne, ai shi aure lokaci ne, duk yanda aka kai ga son ayi in lokacin be yi ba, toh baza’a yi ba. Amma in yayi nan zaki ga kamar anyi ruwa an ɗauke. Ke ma ranar Asabar za’a daura miki aure. Kinga nan da kwanaki huɗu kenan. Ki yi biyayya kin ji. Allah miki albarka” tare suka amsa Aameen ita da ummah.
STORY CONTINUES BELOW

Zuciyar Salmah cike da murna zata yi aure itama kamar su ummitr, rufaida jiddo da sauran kawayenta na marke. Itama dai zata ji daɗin da ake cewa akwai a aure, zata mallaki gado, kujeru da katifa duk mallakinta ba irin na Goggo mai mata gori ba. Da tunanin nan ta barci ya kwashe ta.
A bangaren ummah kuwa tausayin ta take, ta san yanda larabawa suke da son bakaken mata, balle kuma Salmah da take cike da sura son kowa ta san zai yi wuya in ba sha’awa ya dibi Taha ba. Addu’ar dacewa tayi mata kafin ta kwanta…
***
Tabouk, Saudi Arabia..
Washegari da safe ta tashi da karfin ta, ta haɗa duk wani abu da ya danganci wajen aiki ta damfari ofishin shugaban kamfanin da ya bata aiki ya tsaya mata wajen samun shedan zama da sauran abubuwa kamar yanda ake a Kasar.
Bayan sun gaisa take shaida masa ga abin da ta kawo saboda biyayya ga umurnin da aka bata.
“kina da sauran dama guda ɗaya, yanzu a janye duk wani doka da aka baki, sannan babu wanda zai sani don ba a rubuta shi a goshinki za’a yi ba” tsare shi da tayi da ido ne yasa yai tunanin ko zata ce wani abin ne. Amma ganin tai shiru ya cigaba
“awa biyu zaki bani a cikin lokutan ki. Ina son Na ɗanɗana ni’imar da Allah yai miki. Da kin yarda da tun tuni an wuce wajen, ga kuma karin albashi da zan sa a miki” Y karasa yana murmushi don a tunanin sa zata amince saboda tsaurin da aka sa mata. Ajiye masa abin da ta shigo da shi tayi ta juya ta wuce.
Samun dilallai tayi ta siyar da motar ta da gidan ta, sannan ta fara shirin samun tikiti jirgi mai zuwa Nijeriya kafin sauran awannin ta da Ka bata. Cikin ikon Allah ta samu mai tashi karfe biyar na maraicen washe gari.
***
Cikin dare jirgin su ya sauka a filin jirgin malam Aminu Kano, a nan ta kwana sai washe gari ta isa gidan kanwarta Amina. Bata faɗa mata ga abin da ya sa ta dawo ba amma ta ce da ita ta dawo gaba ɗaya kenan.
“kina kuwa ji daga yaran nan? ” RAHANATU ta tambaya suna zaune suna hira bayan sun gama cin abincin rana.
” Eh toh, kwanaki Abba ya ɗauko ta bayan sun samu matsala da Goggo, ni dai ban je gidan ba don Goggo tace bata yafe ba” Ta faɗi a sanyaye
“Aminatu ban san ko ni wace irin uwa bace, da sanda Imran ya juya min baya na Kwaso jiki na dawo da duk haka bai faru ba. Amma hangen abin duniya ya sa na turo su ni kuma na cigaba da nema, gashi dai na samu amma na rasa ya’ya na” Ta faɗa wani siririn hawaye na sauka mata.
“yanzu ko zaki leka gidan Abban ne, na san Suhayl ma kamar ya dawo nan ɗin saboda karatun sa, Salman kuma ai Sokoto yake karatun kamar aka ce” nan ma wani kunyar ne ya sake rufe ta, don sam bata taɓa tambayar komi game da su ba. A haka dai ta tsaida ra’ayin zuwa gidan dan kawunsu marikin ya’yanta.
***
A sanyaye ta shiga, ta iske inna da yan mazanta suna hira. Abin da ya ba ta tsoro shi ne gaisuwa ɗaya ta samu daga yaran tun daga ya’yan da ta haifa har ya’yan dan uwanta. Innace ma ta taso da murnar ta
“mutan Saudiyya ku ne a Kasar ” Ta faɗi tana Mikewa. Ganin yaran zaune ya sa ta ce
” baku gane ta bane? ” Ta karasa tana balla musu harara. Sum sum suka mike suna masu amsar kayanta da ta riko suka karasa cikin falon.
” aiko yanzu ya dawo, ya shiga ya watsa ruwa ne. Kin sha hanya, yaushe kika iso” Ta karasa tana tambaya yayin da ta ke sauke mata tiren abin tarbo.
“jiya cikin dare, daga gidan Aminatu nake, fatan na same ku lafiya” Ta ce tana murmushi
“lafiya lau, ya wajen su Aminan, ita sam kamar bata da kowa a garin nan. Ai duk mijin da ya ce zai yanke igiyar zumunci tsakanin ka da danginka ai ba miji bane. Ana ma miji biyayya matukar ba saɓon Allah bane. Annabi yace wanda ya yanke igiyar zumunta ba zai ji kamshin Aljanna ba. Allah dai ya kyauta” Ta karasa da karamar tsaki.
“Ai ita Goggo kamata yayi ta shiga halwa tayi ta rokon gafara, ba tayi ta yawon gidan boka tana haukatar da bayin Allah ba, Taɓ Allah ya bata ya’ya” faɗin Suhayl yana mai Mikewa.
“gidanku Suhayl, uwarka fa ce nan zaune, sannan Goggo ce mahaifiyar ta, ka iya bakinka in baka son ukuba daga Allah, iyaye ba abin wasa bane. “faɗin inna don sam bata ji daɗin abin da suka yi ba.
” Wacce suka ɗaura ma tsanar suke zuwa ga boka da malam don ta haukace ta haukacen, ta bi kwararo kamar yanda suka so. Sai da yarinya ta ɓata sannan zaki dawo RAHANATU. Wallahi ki ji tsoron gamuwar ki da Allah don zai miki hisabi tun daga irin uban da kika zaɓa musu mara gabas” faɗin abba sanda ya fito ya tsinkayi maganar. Kuka sosai ta saki tana faɗin
“sanda aka min fyade kuna ina? Da ciki ya bayyana a jiki na mai uwa ta tayi, mahaifi na ya rasu ba’a ji tausayi na ba aka kore ni, meye laifi na don na tsaya nai karatu kamar yanda mahaifi na ya so? Akwai wanda ya taɓa tambaya ta kalan Barcin da nake? Akwai wanda ya damu da ciwon da zuciyata take duk na tuna fyaɗen da aka min? Meye laifin mace a inda aka mata fin karfi aka kwace abin da yafi komi daraja a wajenta? An zage ni, an kore ni, Imran ya tsince ni a wacce bata da komi, ya aure ni bayan ya kwato ni daga gidan karuwai. Ta yaya ba zai wulakanta ni ba yana takamar ai shi ne kawai gata na.1
Da na turo su Nijeriya akwai wanda yayi yunkurin biyo ni, yai min faɗa irin wanda ake ma mai mafadi? Duk wannan saboda ni mace ce, bai isa ba sai da aka ma ya ta hakan6
Shike nan ita mace ba mutum bace? Shike nan namiji zai yi zunubi sannan a ɗaura shi ga mace? Shi ke nan ba ruwan iyaye da ciwo da damuwar yayansu mata su dai ko sa yaushe burin su kar ta jawo musu abin kunya.. ” Ta gagara karasawa nan ta sa kuka, sosai take yi gaba daya falon yai tsit, da allura zai faɗi tabbas za’a ji karar sa. Nan kuma sai yan maza suka fara Share kwalla a wayance…Assalamu Alaikum warahmatullah. Da fatan kuna lafiya. Am so sorry for the long break, exams plus fasting things. Ubangiji Allah ya sa muna cikin yantattun bayi a watan ramadan, ya yaye mana matsalolin mu ya kyautata rayuwar mu.5
Albishir din da zan muku shine nan da 2wks zan kammala Silar Ajali bi izni Rabbi. Sannan imidiately zan muku posting wani da already akwai shi a kasa ko a kammala gidan aurena.1
Anyways, thanks for sticking around. I love you all for the sake of Allah…
“Shin akwai abin da zai sosa maka fatar ka sama da faratanka?” Inna ta tambaya tana mai tsare ta da ido. Ganin bata da shirin magana kuma da alamun jikinta yayi sanyi sai ta cigaba da cewa
“kin sa kai kin tafi, yaranki kuma ko oho, haka ake yi? Ban san me yasa son duniya ya ke rufe ma iyayen zamanin nan da har sukan manta cewa yara amana ne a gare su, kina tinkaho Goggo salame kika bar ma ajiyar yaranki kin manta cewa ke ɗin da ta haifa ta gagara riko ta sake ki kika bi duniya. Wallahi in basu yafe miki ba tun wuri ki nemi wajen zaman ki a wuta, don amana ba zai barki ki tsallake siraɗi ba” Ta faɗi zuciyar ta na mata zafi. Ganin shirun yayi yawa sai ta cigaba1
“kar ku ga laifi na, kin san hadisi ingantacce ya zo cewa amana da zumunci zasu jira ɗan Adam a siraɗi kowanne a gefe da gefe sun saka siraɗi a tsakiya, duk wanda yaci amana ko ya yanke zumunci ba zasu bar mutum ya tsallake ba. Fisabilillahi RAHANATU Wanne ne baki taɓa ba. Ki ji tsoron Allah ki tuba ki nemi gafaran ya’yan ki” tana kaiwa nan ta mike ta bar su zaune jugum.2
***
An ɗaura auren Salmah da Taha , Wallima kawai IMRAN ya haɗa, sannan ya mika ta ga dakin mijinta yana mai mata nasiha. Farin ciki ne fal a zuciyar ta don itama dai gata yau a matsayin matar aure. Kallon ciki da falon da ya kama mata ya zuba katifa da abin da ba’a rasa ba take tana faɗin
“Happy independence Salmah” ta faɗi tana yin tsalle a kan gadon fuskanta cike da fara’a. Sam bata ji wani ɗar ko tashin hankali da amare ke ji ba, ita farin cikin ta yancin kan da ta samu.
***
Sai karfe ɗaya na dare ango ya shigo, bai yi yunkurin isa gareta ba don a tunanin sa ta daɗe da yin barci. Iyaka kwanciya yayi sai minsharin shi ta ji, dariya ta fara ciki ciki don aunowa tayi minsharin da yake ita da aminanta ne kewaye da shi da sun more dariya.2
Washe gari bayan sun idar da sallah asuba ya bata kudi ya bata yan jinai 5 guda ashirin, ya sa kai ya tafi. Murna ya cika ta don a zaton ta kyautar da ake cewa miji na ba amarya washegari biki. Barci tayi mai isar ta se kiran sallah azahar ya tada ita. Ta tashi tayi sallah ta fara neman abin da zata ci. Raguwar naman da suka ci da safe ne ta dauka ta ci, sannan ta koma barci, da la’asar ta sake tashi tayi, nan kuma sai ta fara tsorata ganin bai ko leqo ta ba. Kawar da tunanin tayi, ta cigaba da sabgoginta.
***
Tun tana kallon lokaci akayi karfe tara, goma, sha ɗaya, sha biyu babu shi babu alamun sa, nan ta kara tsurewa,
“ko dai yayi hatsari ya mutu ne” Ta ce da kanta, bata tsorata ba sai da ta tuna bata da waya, bata san hanyar da zai fitar da ita zuwa gidansu ba, ga miji bai dawo ba. Wani irin kuka ta saki tana mai tausayin kanta.
Tunanin su Rufaida, su ummitr take da rayuwar su, yan uwanta maza su Salman da Sulayl har ta kawo rayuwar ta a Kano, zamanta da mahaukata sai taga ai da a Aljanna take tunda ga wa’inda ta sani kuma suke sonta.
Barci ɓarawo ne ya sace ta, ta tashi tayi sallah tana kuka, ta idar kenan ta ji ana buga mata kofa, tsoro ya hana mata motsi don tunanin ta an zo a kashe ta ne itama.
“Salmah” muryar mahaifinta da taji ne ya sa ta sakin murmushi, ta je ta buɗe kofar, bata jira ya karasa shigowa ba ta rungume shi tana mai sakin kuka.
“kiyi hakuri, kiran gaggawa aka yi ma mai gidan ki a can Saudiyya, amma kwana bakwai kawai zai yi ya dawo” Ya faɗa cikin harshen Hausa da bai gama nuna ba.
“in Kwaso kayana mu tafi can gidan ko” Ta faɗi tana mai murna zata wajen matar babanta mai sonta
“Habibty Sudan ba Kano bane, anan in aka kai mace dakin mijinta mutuwa kaɗai ne ke sa ta fito, sai kuma saki wanda ba karamin abu ke sawa a yi ba. Ita mata zata tsaya komi wuya komi daɗi ta tsare dukiyar mijinta ta rike amanar kanta da ya bar mata, kin girma ne, zan dinga zuwa akai akai in duba ki, Allah yana tare da ke, ina rokonsa yayi miki albarka”.2
Haka yayi ta lallashinta da bata baki cikin lallausan lafuzza haɗe da kawata mata gidan aljanna da hakurin ta zai bata yasa taji ta wasai, har bata wani damu da tafiyar sa ba. Abinci kawai Taci ta fara kallo duk da ba wani fahimtar yaren take yi ba amma itace har da kyakyatawa.
***
Sati ɗaya, biyu, uku har aka shiga wata daya, biyu babu Taha ba alamun sa. Tun salma na damuwa har ta fara manta cewa da aure a kanta. Hidiman gabanta kawai take, tayi girka abin da take son ci, tayi barci tayi kallo. Kwanciyar hankali yasa tayi ja tayi ɓul-ɓul da ita, duk mahaifinta ya kawo mata ziyara da kalan hirar da zai mata, wanda da yawa akan sirrin zaman duniya ne da wasu kalubale da ya fuskanta a rayuwar shi. Ko kaɗan baya mata zancen Nijeriya don baya son abin da zai daga mata hankali, farin cikinshi ganin da yake mata yalwace da farin ciki.
Yau ma kamar kullum, zaune yake yana bata labarin yanda rabon su ya ja shi zuwa Nijeriya da yanda ya suka yi Rayuwar su a Kano kafin komawar su Nijeriya. Dariya take sosai don daga gani yana cikin shaukin kewar mahaifiyarta, kallon sa tayi tace
“ka je Saudiyya ka nemi sulhu da ummanmu don na ga kana ji da ita”
Shima dariya yayi sannan yace
“ai ina ga tun washegari zuwan ki Kasar nan mahaifiyarku ke Nijeriya, ban san me ya faru ba amma an ce min an kada ta ne” Ya karasa yana dariya
“Ko dai dama saboda ni ne taki dawowa? ” Ta faɗi ranta a ɗan bace.
” Toh ke dai ba gaki hankali kwance ba, kinyi kyau kin fito sak balarabiya…”
Sallamar da Taha ya doko ya katse masa hirar sa. Da murna ya tarbe shi suka gaisa, sai a lokacin Salmah ta kare masa kallo.
Kyakkyawa ne ajin farko, yana da tsawo da idanu da sau daya ta iya haɗa nata da shi saboda kwarjini. Askinsa da yanda yake Shirya gashinsa ya taimaka wajen kara ɓoye shekarunsa, take taji ta kamu da son wanda aka kira da mijinta.
Gaishe shi tayi sannan ta Mike zuwa kawo masa abin tanɗa. Nan suka gaisa da mahaifinta sannan ya tafi shima. Tun da ta shigo da faranti dauke da ruwa da kayan marmari yake binta da kallo, motsin kirki ya kasa don gaba daya ta tafi da imaninsa. Kasa ɓoye maitarsa yayi, chak ya dauke ta sai zuwa kan gadon su. Magana ya mata a kunne in da iya fahimtar ta a larabci ta gane abin da yake nufi duk da ba ta ji duk abin da ya ce bane.
“mijinki ne kar ki bari tsinuwar Allah ya hau kanki” Ta tuna karatunsu na islamiyya, duk da a tsorace take bata nuna ba balle tayi yunkurin hana shi.
Hanyar da ta ga ya bulla ne yasa tayi saurin hankade shi, ta mike da sunan guduwa.
“Haza Haramun” kawai take iya nanatawa don shine kawai larabcin da take iya tunawa.
“Taɓ, tsinuwar Allah fa, ai ko da aka ce ayi biyayya ga miji ba’a ce har a saɓon Allah ba, ta faɗi a tsiwace tana maida tufafi. Bata yi aune ba taji an dauke ta daga baya. Kan gadon ya maida ita duk yunkurin ta na son tsiratar da kanta. Dukkan karfin sa ya sa mata nan ta fara ambaton duk wani addu’a da ya zo kwanyarta. Ihu take da kuka har muryar ta ya dusashe, ta Sallamar don tana jin alamun zai samu nasara akan ta, kulle idanu tayi ta ce “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” , kamar ance ta waiga ta hango fitilar gefen gado, nan ta jawo da hannunta ta rutsa masa a kai, bai dago ba ta kara masa, nan kuma wani karfi ya zo mata ta hankade shi cikin jini ta ja hijjabin da tayi sallan la’asar tayi waje.5
***
Tun da ta fara gudu bata sanin in da take sauke kafafu ita de fatan tsira take. Hangen cincirindon mutane a inda ke nuni da bakin titi yasa ta fara tafiya tana haki har kai ga wani dogon gini ta jingina. Nan ta ankara ba takalmi a kafafun ta ga shi duk taji ciwo. Tashi tayi da niyar dumfarar mutanen ko za’a samu wanda zai taimaka mata. Duk da kasancewar zuciyar ta na kidan lugude bata fasa zuwa ba. Ɗaga kan da za ta yi bayan ta kawo karshen ginin kuma bakin titi sai ganin rubutun kofar gate din wajen yasa ta gane makaranta ce take ta karance su da boko da larabci duk a bayyane
” International University of Africa
(جامعة افريقيا العالمية) “
Hakan ya kara mata kwarin gwiwa har ta isa gare su.
” Ku taimaka min! Help me please! Agithnie!” Haka dai ta ke faɗa cikin shesshekan kuka tana hargitsa yaruka ukun, duk da bakin ta bai goge da larabci ba. Kallon sabon kamu ake mata har dai wani yayi kokarin tunkarar ta yace
“zo baiwar Allah ” Ya fadi yana yafito ta.+
Ta isa gareshi bakin ta na ambatar addu’a.
” Daga ina kike, me ya same ki?” Ya faɗi yana son tantance lafiyar ta.
“suna na Salmah, daga Kano nazo ganin mahaifi na sai wani ya sace ni shi ne na gudo na ɓullo ta nan” ta karasa cikin kuka.1
“bari na kaiki wajen shugaban daliban Najeriya, kinga bakano ne, kila da taimakon da zai miki. Share halayenki, nima dan Nijeriya ne, amma dan yobe ne” Ya karasa fuskansa yalwace da murmushi.
Wani ni’ima ya ziyarci zuciyar ta a hankali ya fara wanke tsoron da ya mamaye zuciyar. Binsa take cikin sauri har suka kawo wani gini da taga an rubuta “Nigerian students union secretariat” bayan sun yi sallama suka shiga ne mutumin da ta biyo ya kalli wani yace
“Ya Naqib, ga yar uwa na kawo maka, yar garinku ce ta ɓace”
“kace masu neman abin duniya, zaku haura Saudiyya ko, ke ma a dole se kin zama hajiya Kano to jidda ko” Ya fadi yana mai watsa mata wulakantaccen kallo. Hakan ya tsurar da ita, kuka ta saki tana fadin
“Wallahi na zo ganin mahaifi na ne shi ne aka sace ni, ka taimaka ka maida ni Kano mahaifiyata da yan uwa na duk suna can” Ta karasa tana kama kafafunsa. Janye wa yayi da sauri, waya ya dauko ya danna ya kara a kunne, bata ji abin da yace ba ta dai ga wata sa bata wuce sa’ar ta ba tazo.
“Zahra ki je da wannan, tayi wanka ta huta zuwa gobe Insha’Allah sai mu ji daga gareta. In muka same ta da karya mu mika ta da hukuma.
A tsorace take, haka suka fita zuciyar ta na bugawa har zuwa dakunan kwanan da Ɗalibai. Bayan tayi wanka suka zubo mata fara da mai haɗe da salak, Haba take ta manta wani tsoro ta far ma abincin.
STORY CONTINUES BELOW

“Allah sarki innata, har kun tuna min da ita, ta faɗi tana kallon su” kamar an mintsile ta zumbur Tashi tana nuna su da yatsa
“Ashe ku ne, kai Alhamdulillahi baku gane ni ba, zahra sa Rukayya ko? Mun haɗu a filin jirgin sama da nazo, ke ban ganki ba ya sunanki” Ta karasa cike da murna tana nuna ta ukun su
“ki kira ni da Yakasai kawai ko kice miss Yakasai, a ina kuka haɗu? ” itama ta karasa tana jifansu da tambaya
“ni Wallahi ban gane ki ba, kinyi kiba a Yan watannin nan, me ya faru? Ya akai kika ɓace” Rukayya ta faɗi cike da mamaki yayin da zahra sakin baki tayi tana kallon ta kamar ta ga uwayen gidanta zagezagi.
“Ku bani ruwa na sha,sai in baku labari. Har aure fa an min guduwa nayi, ai tsoron a maida ni ya sa na ce sace ni akai. Kun ga de ku aminai na ne ko, kar ku tona min asiri” Ta karasa cikin rana.2
Ruwa ta sha, tayi magrib, kamar yanda ta saba nan ta zauna tayi azkar dinta, sannan ta kwanta barci, cikin ikon Allah ba ɓata lokaci barci yayi awon gaba da ita. Ba ita ta tashi ba sai asuba. Nan ma sallah suka yi sannan ta fara basu labarin rayuwar ta, shaɓe shaɓe suke da hawaye, yayin da kaunar ta ke shiga jikin su har ɓargo.
“Ai gidanmu kawai zaki, bara na fada ma yayanmu zai san yanda za’a maida ki. Taɓ ai duk cikin su ba gwara, shi abbanki kamar bai ga gari ba, ita kuma ummanki rashin mafadi ke damunta” wacce ta kira kanta da Yakasai ta ke ta faɗa, su zahra na mintsilin ta amma masifa take. Haka dai har suka shirya suka tafi ɗaukan darasi.
***
Shi kuma Taha tun da ya samu Kanshi ya tashi yayi wanka ya kwanta yana jiranta da tunanin irin hukuncin da zai mata, shiru shiru dai har yaje isha’i ya dawo, tunani ya chanza nan ya sa hula ya nufi gidansu da guntun ledan tsarabarsa.
Da murna suka karbe shi, nan wani kakan salma ya ce
“kai ko ana angwancewa kana yawo, ko dai rago kake in karbe matata ” Nan suka sa dariya, godiya ya musu sannan ya sa kai ya koma.
***
Zagaye unguwar yayi duk a tunanin sa zai ganta a laɓe a wani wajen. Haka ya karaci yawon sa sannan ya sa kai ya koma gida da tunanin kila ta koma bayan fitarsa.
Ko da ya shiga ya iske gidan wayam, nan ne hankalinsa ya dan tashi har ya fara addu’ar Allah dawo da ita lafiya.
Daren ranar bai yi wani barcin kirki ba, da safe ya haɗa duk wani abin da ya mallaka a waje daya, sannan ya rufe kofa, gidan su salma ya koma ya samu waliy dinta ya kebe dashi sannan ya fara masa bayani.
“Tun da akayi auren mu Salmah bata amince da ni ba, jiya ma da na bukaci cin sadaki na wuka ta tashi ɓurma min a ciki na kauce, shine ta same ni a cinya, a dalilin haka na sauwake mata auren, ban daura mata iddah ba, Allah saka da alkhairi da karamcin ku gareni” yana kaiwa aya ya tasa kai gaba.
Waliy din Salmah ne ya faɗa, kafin a ce me zancen saki ya zagaye dangi kasancewar ba abu ne da ke yawan faruwa acikin su ba. Cike da jimami aka tura wasu dattawa mata su je don su ɗauko ta. Nan suka iske gidan wayam, ga alamun fashewar fitila a dakin kwanansu da sauran ababen da suka zubar yayin kokawa.2
“Anya ba ya gwada mata halin su bane? Don ga alamun kokuwa nan” faɗin daya daga cikin dattawan.2
“Gaskiya in ba haka ba, ina zata je yarinyar da bata san kowa ba, gaskiya a nemo shi ya nemo mana yar mu” faɗin kishiyar mahaifiyar Imran. Haka dai sukai ta maida magana da yawansu na tausayin salma yayin da kalilan cikinsu ke ganin ta zubar da matantakanta tun da har ta iya yin gardama da miji.
Jiki a sanyaye suka bar gidan bayan sun tabbatar da bata gidan. Nan suka koma gida da mummunar labarin cewa bata ba alamun ta a gidan, lokacin hankula suka tashi, babu ɓata lokaci aka kai kara wajen yan sanda, nan aka bazama neman ta tare da watsa hotunan ta a ko ina
***
MARKE, Nijeriya…
Tun dawowar RAHANATU Nijeriya bata taka MARKE ba sai da tayi wata uku. Lokacin da ta tabbatar da hankalinta ya ɗan kwanta sannan har an kira ta intabiyu na samun gurbin aiki a jami’ar Bayero sannan ta fara harama. Tare da Inna suka je, gidan Hakimi suka sauka.
“Kin gadama kin zo ne? Rahanatu kiyi ma Allah ki tuba ki dawo mu aurar da ke, in kuma wajen uban ya’yan ki zaki koma ku zo mu aura masa ke kamar kowace ya” Hakimi ya faɗi cikin lallashi amma da gani ransa a bace yace.
“kayi hakuri baba, na dawo kenan har abada, ina rokon alfarmanku ku, kuyi min aikin gafara. Da na samu miji kuma zanyi aure” Ta faɗa cikin hawaye. Hakan ya sanyaya masa jiki sai ya bi ta da lallashi da ban hakuri tare da karfafa mata gwiwa. Shi ya aika ma Goggo salame ta zo sannan ya haɗa su ya musu nasiha. Goggo na kuka wiwi tace
“Ga yar nan salma ba ta ba alamun ta, Shike nan na shiga uku na salwantar da rayuwar ta, sheɗan ne wallahi kun san ba hali na bane” Ta faɗi tana gun jin kuka. Nan kowa ya sa mata ido tayi ta tona abubuwan da tayi, wanda aka sani da wanda ba’a sani ba. Takaici ya cika hajiya Aziza nan take ta ce2
“wai wace Salmah? In dai jika ta kike nufi tana can zaune gidan mijinta, hankalin ta kwance, ko ina dai an san dangin uwa su ke iya rike ya’ya amma mu kam mun gaza” Ta karasa a kuntace ta bar musu ɗakin.
Ina rami Goggo ta saka kanta, da dai ta ga bazai fisshe ta ba ta zuri silipas ta yi waje. Tafiya take kai a sama bata ko kallon gabanta balle ta ji abin da ke tahowa bayanta, sai jinta tayi a sama tana yawo bata sake sanin inda kanta yake ba.
Da sauri mai bus dinnan ya fito yana INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN, mutane suka yo wajen, daɗin abin da yawa sun ga tahowanta tana sumbatu don har wasu na mata tsiya.
“Salmah ki yafe ni, na tuba ki zo in ganki” Ta sake faɗi yayin da ta ɗan farfado tana fisge fisge. Nan kuma ta shura sannan ta cika. Anan ne aka samu wa’inda suka je suka fada ma gidan Hakimi.
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun” kawai ke yawo, bakin su, imani da mamaki ya cika su don ganin yanzu ta bar su fa, amma kuma ba yanda Allah baya yi, shine daidai shi ya ke daidai.
***
Anyi ma Goggo sutura an kaita makwancinta mutane cike da alhini, Rahanatu komi ya dawo mata sabo, don tunawa tayi da rasuwan mahaifinta. Tashi tayi ta bar gida ranar da akayi sadakan uku. Bata tsaya ko ina na sai bishiyar da ta tsaya ranar da aka kai mahaifinta makwancinsa. Kuka take sosai don komi ya dawo mata sabo.
“a ko da yaushe ta inda aka hau tanan ake sauka, na san tabbas zan ganki a nan” muryar da ta kasa mantawa a duniya. Wani Sabon juriya ta ji ya zo mata, ta watsa masa harara
“Ban san ka san gaibu ba ai, bayan zaluncinka har gani har hanji kake”
“kinji na faɗi ranar tashin duniya? ” banza tayi da shi ta cigaba da hawayenta
” tunani na kike? Soyayyata ke sa ki zubda hawaye har haka” Ya faɗi a shakiyance yana dariya kasa kasa
“Tunanin ka? Inaga ni gaba daya ma ban da wani halitta wai zuciya balle har na samu lokacin batawa wajen tunani ka” Ta fada a kufale, ji tayi kamar ta shake shi ya margaya a huta.
“kar ki damu tawan, ni ina da, kuma ta ishe mu komai da ya shafi rayuwarmu, yanda nake ɓata lokaci wajen tunanin ki haka nake ɓata lokaci wajen tsara yanda dole zaki tuna komai a kaina, Rahanatu yanda na zama Silar Ajalin farin cikin ki haka zan zama Silar dauwamar sa” Ya faɗi yana mai murmushi..
“Nagode Allah ka san kai ne Silar duk wani ɓatanci da ya zo rayuwa ta, kayi min fyade duk da haka aka baka gaskiya, mahaifi na ya rasu baka tausaya min ba ka sake min wani fyaden sannan ka cika musu burin su na kora ta daga mahaifa ta. Duk don a wajen ku mace ba Mutum bace? Haadi ka cuce ni, ban san kalar addu’ar da zan maka ba” Ta karasa tana mai shessheka, amma amsar da ya bata ya sa ta tsaya chak don Tsabagen takaici tashi tayi ta kama hanyar gida shi kuma ya cigaba da nanata
“Addu’a zaki min na zama mijinki A Aljanna,”2Wancan da matsala, wasu sun yanke this is d corrected chapter
Kwance take kan gadon Rukayya, tun bayan da ta gama shan corn flakes barci ya kwashe ta. Dukan da Zahra ta sakan mata ya tashe ta a firgice.
“Tashi mun shiga uku” nan take barci ya watsake daga idanunta
“me ya fa… ? ” bata iya karasawa ba sakamakon ganin hotonta a jarida.
“Na shiga tara ni Salmah me kuma nayi?” Ta faɗi tana rushe wa da kuka. Nan su Rukayya suka shigo suna lallashin ta.
“Salmah satin ki biyu fa anan, duk da yaya Adam ya ce mu ɗan kara hakuri yana neman hanyar fita da ke ne, amma kuma kin san nan ba Nijeriya bace, ko ba komi bizanki ya kare tun da na wata biyu aka baki, sannan gashi kin ɓace, dole hukuma ta shiga ciki ka’in da na’in, yanzu duk ba kuka yakamace mu ba, mu nemi yaya Adam mu faɗa masa halin da ake ciki” faɗin Yakasai.
Hakan ne ya kara musu karfin gwiwa, suka kira shi. Bayan sun kora masa bayani ne yace musu
“Shi yasa nace kada ta fito babu niqab, ina nan ina neman hanya, kun san saboda boko haram sun kai hare hare kauyukan jihar Borno shi yasa aka rufe dukkan bodoji shi yasa ba’a samu shiga da ita ba. Amma bari mu gani, kun san dai in aka kama mu da ita za mu iya rasa gurbin karatun mu ko, don ba karamin criminal case bane, don haka ku yi takatsantsan” Ya gama sannan ya ce a mika ma Salmah wayar itama kwantar mata da hankali yayi sannan ya musu sallama.+
***
Murmushin Rashin dalili yake tun da ya ajiye wayar. Ɗaga hannu yayi ya ce
“Allahumma zawwijnie Salma bi fadlika ya Arhamar Rahimeen”
“Kai haka manzo SAW ya koyar, maimakon ka yi istikhara ka yi ma kanka zaɓi kenan, wai wace Salmah” Faɗin Ahmad abokin Adam
“Hmmmn Annabi SAW ya ce a ɓoye nema ka bari in na samu sai in bayyana ” Ya faɗa shima yana dariya.
” Toh Allah sa ba kaaba zamu je daurin aure ba don in ka ga kare na shinshinar takalmi” shima ya jefe shi da shi
“a’a Jerusalem zamu je” Ya maida masa da bakar magana. Tun daga haka Ahmad ya samu abin tsokana, karshe ma sai da Adam fita yayi ya bar masa dakin.
***
Kwanci Tashi sai da Salmah ta kara wani sati daya da su Zahrah kafin su kayi shahadar kuda suka damfari gidansu.
A sati ɗayan Adam ya maida hankali wajen binciken gidan su da kuma mahaifinta anan ya kara tabbatar da gaskiyar labarin da ta basu. Don duk hanyar da za’a bi waje fita da ita ya gagara.
Sai da suka yi sallah isha’i sannan suka tafi zuwa gidan su Salmah. Zaune suka iske dattawan gidan suna hira kamar yanda al’adar su take a gidan. Adam da Ahmad suka fara iske su, bayan sun gaisa ne Adam ya fara magana cikin harshen larabci.
“Ni ne shugaban Ɗaliban Nijeriya da ke jami’ar Afrikiyya. Kwanakin baya mun tsinci wata yarinya, ta kasance cikin rudu, sai jiya da na ga hotonta ana cigiya. A da ce mana tayi ita yar Nijeriya ce, sai a jiyan jiyan ne da muka tsare ta take ce mana dangin mahaifinta na nan, toh yau mun yini muna bincike kafin daga bisani muka gane nan ne. Kuyi hakuri ban bi ta hukuma saboda ba kasancewa na ɗalibi” kankan da kai da zaɓin kalamai da Adam yayi yasa ba wanda ya Musa masa, sai ma godiya da suka yi masa. Sannan aka kira su Salmah kowa sai murna yake, su Zahrah sun ga karamci haka su adam da ke waje. Hira sosai suke da iyayen salma da kakanninta. Garin tambaya da ake musu ne aka gano Adam da Zahra yaran Yayar Haroon Karima ce, yayin da Rukayya er Haroon ce Yakasai kuwa yar kanwar Haroon salima ce. Murna kamar IMRAN zai maida su ciki. Nan ya basu labarin zaman sa gidan su Haroon da kuma yanda Mahaifin Haroon ya tsaya masa har ya samu auren RAHANATU.
Sai faɗi yake
“Jinin Haroon sun min karamci a karo na biyu, ni kuma na damka ma Adam auren Salmah na har abada, don Allah kar ka ci amana kada kace a’a, sannan ka zama Silar dawowan farin cikin Salmah ko bayan bamu”
Gurfanawar da Adam yayi cike da farin ciki ya ba kowa mamaki, don mafi akasarin wa’inda ke wajen a tsorace suke kar ya ki karban tayin.
Basu rabu ba sai da Adam ya haɗa IMRAN da Haroon a waya nan abokan biyu suka cika da farin ciki don sun fi karfin shekaru goma sha biyar rabon su da juna, sannan ya faɗa masa alkhairin da yake son kullawa, farin cikin da Haroon yayi baya iya misaltuwa sannan sukayi sallama.
***
A sati ɗaya duk wani cukucuku da Grand khadi Haroon da wasu yan uwan Mahaifin su Adam sunyi don shigowa Kasar sudan. IMRAN na filin jirgin saman Khartoum don bai amince su Haroon su iso su jira ba.
Rungume juna su kayi suna hawayen farin ciki, tun daga filin jirgi har gida hira suke, a gidan ma da kyar suka rabu aka samu Haroon shima ya watsa ruwa kamar sauran abokan tafiyan sa.
“Wai ni ina RAHANATU ne, ko na ce Rayhan ɗinka tun da muka zo amarya kawai muka gani” Haroon ya tambaya bayan sun gama cin abinci.
Hakan yasa Imran ya kwashe duka abin da ya faru tun zuwa su Sudan har rabuwar su, da yanda Salmah ta dawo hannun shi har auren da ya mata da rabuwar duk bai ɓoye ba.
“lallai a rayuwar ku akwai darasi babba, ni daga kai har Rayhan din ban ga wanda yafi wani son kai ba, ita zan kara da cewa ilimin ta bai amfane ta ba don ko zamanin jahiliyyar farko ba’a yi abin da ta yi ba. Amma duk wanda ya ce duniya ne akan gaba, ko yace ba zai yafe laifin da aka masa ba, ko ya ce shi don wani abin da ba’a so ya same shi Shike nan ko oho ko da sauran mutane zasu mutu toh tabbas yana tare da wahala. Amma da yake haka kaddarar ku yazo, sai mu yi fatan Allah ya yafe muku da mu duka ya raya zuria”
“Aameen ya rabbi Haroon, Allah ya bar mu tare har gaban abada har a Aljanna “
” Aameen ya rabbi aboki na” Ya faɗi shima yana dariya.
***
“Kin san tun yaushe na ke son ki? Tun ranar da na fara kyalla ido a kan ki, kishin ki ya taso min don a tunani na kina cikin masu haurawa Saudiyya, Salmah ki amince da ni mu gina rayuwa mai inganci” Ya faɗi yana kallon ta so yake su haɗa ido amma taki, kunya duk ya rufe ta.
“Kinga in muka yi aure farkon abin da zan yi shi ne nema miki gurbin karatu ki karanci shari’a, ni kuma Kinga zuwa lokacin na ɗaura doctora (phd) zamu kammala a kusan tare, sai mu koma Nijeriya mu cigaba da rayuwa ” ita de kallon shi kawai take, chan dai ya sake cewa
” ni fa tun da na fara sonki na fara mana wannan Mafarkin “
Dariyar da Salmah ta saki ne ya tsaida masa zancen sa. Amma a hakikanin gaskiya jin zancen take kamar ana shuka irin sonsa ne a zuciyar ta. A take kuma yana tsirowa kuma yana rassa da yabanya ta ko ina.
” Kullum ki dinga mana addu’a kinji, Allah ya cigaba da haɗa zukatanmu yasa mu zama maaurata a gidan aljanna ” Ya faɗa mata cikin rada. Dariya kawai tayi haɗe da rufe idanu.Bayan shekaru Ashirin
Biki ake da gani bikin er gata ake, kwararriyar mai kwalliya aka gayyato don yi ma amarya kwalliya. Ana tsaka da yi ne wata mata ta shigo, kallo ɗaya zaka mata ka san jini ɗaya ne. Tsalle amaryar tayi ta nufe ta+
“Anty Salmah Oyoyo, wallahi jiya baki ga kukan da nayi ba, da aka ce wai ba zaki samu zuwa ba” Ta ce cikin harshen larabci.
“Haba Afaf ana bikin kanwata guda ɗaya tilo ba Nijeriya ba, ai ko Kasar Sin ce zan taho auranki. Shari’ar wata yarinya ya tsaida ni, sanata ya mata fyade aka kama shi, shi ne suke son a ɓatar da Shari’ar.” wacce ta kira da Anty Salmah ta bada amsa.
“Ai kina kokari sosai, su ummie na cikin gida ko kin gansu? “
” ina fa, su Salman sun iso kuwa? Jiya ya ce min zai baro Spain, wai bizar Rayhan ne ya dakatar da su” Ta amsa tana mai tafiya hanyar wajen su ummi.
***
Cikin shekaru ashirin anyi abubuwa ciki kuwa har da rashi na hajiya aziza da Hakimi da duk sauran matansa. Abba ma Allah ya masa rasuwa.
An kuma samu cigaba don kauyen MARKE a dalilin RAHANATU da jinin ta ya zama babban gari, Salman bayan kammala karatunsa ya samu aiki a jakadancin Nijeriya. Suhayl kuwa ya shiga makarantar horar da sojoji in da ya fita a muqamin 2nd lt, Salmah kuwa ta kammala karatunta na lauya a jami’ar ifriqiyya da aurenta daure a kanta, shi kuma Adam ya zama cikakken injiniya, kuma mijin da Hausawa ke kira da mijin marainiya. Duk abin da ta zama bata manta da kawayenta kuma aminanta na MARKE ba, jiddo, Rufy da ummitr. Rayuwa ya musu shar abin su don da su ake damawa saboda kasancewar su manyan yan kasuwa.
***
Nacin da Abdul Hadi ya nuna ya sa ya shawo kan RAHANATU har aka daura musu aure, Hakimi ya zame mata waliy kuma uba inda duk kuɗin ta sai da ya mata kayan ɗaki da gara da uba kanyi ma yarsa acewar sa amanar da malam Tanko mahaifinta ya bar masa ne ya sauke.
Tun kafin auren ta san son da Hadi ke mata ba ko kaɗan bane don Salman ya labarta mata yanda ya tsaya tsayin daka akan su a matsayin sa na malamin su a makaranta. Bata kara tabbatar da hakan ba sai da aka kaita gidan sa a matsayin matarsa, duk da kasancewar girma ya hau kansu bai hana masa sakin kwanji ya nuna mata soyayya ba.
Wata goma sha ɗaya bayan bikin su ta haifi yan uku, maza. Nan ya saka musu sunan annabi SAW da aminansa wato Muhammad, Abubakar da Umar.
Bayan shekara biyu, ta sake samun ciki, a lokacin aka tsaida auren Salmah inda suka dunguma zuwa Sudan don biki, a chan nakuda ya kamata ta haifi yan biyu maza, karamci irin na Abdul Hadi, bikin sunan gaba daya ya aminta ayi a chan, sannan ya ba IMRAN daman sanya ma yaran suna, nan ya sa musu Uthman da Aliyu, a Cewar sa A cikata Annabi SAW da surikansa kuma khulafaur rashidun.
***
A bangaren Imran kuwa tun da Aisha ta haifa masa Afaf haihuwa ya tsaya mata, hakan ya sa bayan su Aliyu sunyi shekara uku a duniya, Abdul Hadi ya dauke su ya damka ma IMRAN, yace
“ni ba zai iya baks Suhayl da Salman ba saboda sun zama sashi na jikinna, amma ga Aliyu da Uthman Uthman tun da sun zaɓi kasancewa da kai tun fitowar su duniya”
Farin cikin da IMRAN yayi baya misaltuwa, a dalilin haka zumunci tsakanin su ya fi na da kulluwa.
***
“Momma” faɗin yar budurwa da bazata wuce shekara goma sha biyar ba ya dawo da Salmah daga tunanin da ta ke a tsaye.
“Ummu abieha, ina su Yusra da sauran kannenki, da fatan kin kula min da su sosai” Ta ce da ita
“momma kin faye son ya’ya, ke da abba ban san wa ya fi son mu ba” Ta faɗi tana dariya
“Ja’ira ki jira ki haifi naki se ki banzantar da su” Ta faɗa tana jan kumatunta, nan ta lafe a jikinta itama wai kunya. A haka suka karasa wajen sauran, duk bakin Nijeriya ne, itama da sauri ta karasa wajen inna.
“Inna ta” Ta faɗi tana dariya
“kar ki karya min yar uwa” faɗin RAHANATU tana mai sha’awar shaquwar da ke tsakanin su.
“Kai Ummie, Inna ki gwasale ta ga amaryar Mahmoud na min dariya, se na sa ya auro biyu a tare” Ta karasa tana harar wacce ta kira amarya.
“Ai ya ce daga biyu ba kari” itama ta faɗi tana zumɓuro baki. Nan aka sa ta gaba da tsokana kasancewa kowa ya san ta da kishi.
***
Haka aka ci buki aka kare kowa na farin ciki yayin da alkhairi ke bin kowa.
ALHAMDULILLAH