SIRADIN RAYUWA CHAPTER 1 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
_akwai yiwuwar ganin sabbin qirqirarrun sunayen garuruwa da gurare_
1995
*Tushen Labarin*
Malam bilyaminu usman,haufaffen bafulatanin nijer a haihuwa da yare,ta wani fannin kuma d’an qasar *KAISA* kuma bahaushe magidanci mai halayya da dabi’u da al’adu irin na wasu daga bara gurbin hausawa,wadanda basu gama fahimtar abinda addini yayi magana akai ba kan iyali da haqqoqinsu dake bisa wuyan dukkan wani magidanci,walau saboda jahilci ko kuma sun take ne da
gangan bisa son zuciyarsu da soye soyen rayuka.
Haifaffen agadez iyayensa dukkaninsu suka kasance xallar fulanin niger,fatauci da neman kudi yakawoshi gasar kaisa,wanda a yanzun ita tazame masa mazauni
na dindin.
Shiga da saninki kusan shine laqabin da mutane suka yiwa gidansa bayan da halayyarsa tafito garara na auri saki,mutum ne ma‘abocin aure aure,wanda har hakan yazame masa jini da tsoka,bai kuma daukeshi a wani abun aibu ko abun Allah wadarai baya auri mata aqalla da suka doshi goma,wanda mafi yawa daga
cikinsu kowaccensu tana da yara a gidan,walau maza ko mata.
Yana da tarin yara da suka kusa su ashirin da biyarwanda dukkaninsu warin takalmi ne,mutum biyu uku uwarsu daban,harda masu mutun d‘ai d‘ai da uwarsu ta haifesu su daya tak cikin wannan gurguxu zuga da harqalla ta gidan,kamar
yadda BILKISU take ‘ya daya tilo da mahaifiyarta tahaifa cikin gidan.
Kusan dukka wadan nan tarin yara nashi yara mata sunfi yawa,saidai mazan da aka soma haifa masa na farko farko mutum uku daga ciki sun tasa,babu wani batun samun sauyi salama ko tallafi daga tasawar da sukayi,domin suma kowannensu takanshi yakeyi,ci sha sutura ko muhalli mai kyau bai cikin tsarinsa bare akai ga jigo kuma uwa uba ilimi,hasalima za’a iya cewa baisan kwana da
tashin wani cikin iyalinshi ba,kowa yana rige ne da kanshi. Saidai kash,dukka wadan nan halayen nasa hakan bai hana a bashi aure ba,a duk sanda tabusa mishi,ko ranshi ya raya masa,yayi katari da budurwa ko bazawarar da ranshi ya kwanta mai da ita,tofa bazaiyi qasa a gwiwa ba wajen zage qwanjinsa da qarfin aljihunsa koda qarfin aljihun wasunsa ta hanyar cin
basussuka yakashe mata kudi yakawota gidanshi.
Dukkan matar daya aura takan fantama a lokuttan da take cikin amarci,takanyi yadda takeso,takumayi yadda taga dama,saidai kuma da zarar wannan dama ta subuce daga hannunta shikenan itama zata shiga sahun ‘yan ci dakai da neman na wanki da wanka,wanda hakan kan sanya wasu kasa jurewa,wasunsu sukan kai harsu haihu,yayin da masu zuciya a kusa,masu qarancin haquri kan tafi da ciki su
haife a gida,bayan wani lokaci su dawo masa da yaro ko yarinyar da aka samu.
Cikin dukka matan daya aura mutum biyu ne tak suka iya jumurin xama dashi,mace tafarko itace kattume,wanda itace matarsa uku daya aura,tana da yara a gidan balaifi,jhakanan takama sana’a ka‘in da na‘in,tana daukan nauyin kanta dana yaranta,hakanan cikin yaran takan yiwa wanda taga dama,hatta shi kansa malam bilyamun wani lokaci yakanci cikin arziginta,jhakan yasanya babu ganin girma girmanawa ko ganin mutunci tsakaninsa da kattume,idan ta hadosu babu wanda bazaiji kansu ba,bata shakka ko shayin zazzaginsa,ko lafta mishi baqaqen maganganu, hakanan yake zaune da ita shima saboda wataran yakan jingina da ita,sa’annan tazama tamkar wata kujera a gidan,duk wani harqallarsa da auri sakinsa a gaban idanunta yakeyi,hakanan za‘ayi zaman a gama yasallami
mace yasake jajibo wata.
Mace ta biyu data juri zamanta a gidan kuwa itace maimunatu,maimunatu macen da bai taba auren matar dayaji sonta cikin jiki da zuciyarsa ba irinta,macen dayaso har zuwa randa tabar duniya,macen da haryau yake marmarinta duk da qasa tarufe idanunsa,macen da bata taba daga kai ta kalleshi ba duk da
mugunyar halayyarsa.
Yakance maimunatu tayi!,saboda ta soshi,ta qaunaceshi,takuma zauna dashi,duk da banbancin ahalin,daraja,nasaba,kyau arziqi da dukiya dake tsakaninsu,tazarace mai yawa tsakaninsa da maimunatu,amma duka bata duba wannan ba,a zamanin tanunashi takuma zabeshi cikin dubban samari masu kyau
dukiya da aji da take dasu a zamanin.
c
Mahaifinta dan kasuwane da yayi suna,hakanan ya shahara wajen arziqi,kamilin mutum mai managartan halaye,nagartarsa tasanya bai duba matakin arqizin bilyaminu ba a wancan lokacin yadauki maimunatu yabashi,duk da cewa su biyu
tak Allah ya azurtashi dasu a duniya.
Duk da tarin wahala da fama da take a cikin gidan bata taba fasa halin da take ciki bajtun mahaifanta suna da rai har Allah yadauki abinsa,hakanan taci gaba da zama dashi,sam babu jituwa tsakanin bilyaminu da qanwar maimunatu mai suna zuhriyya saboda yadda take ganin yana gasa ‘yaruwarta,ita kuma bata daga kai bare ta nuba mishi bacin ranta,tsabar sanyin halin maimunatu yakawo hakan,tun zuhriyya na budurwa idan tazo gidan bata kwana,iyakarta awa biyu uku tayi tafiyarta,don tace ba zata iya ganin baqinciki da takaici ba,kusan har tafi maimunatu jin zafin abun,don ko gaisuwa bata hadata da bilyaminu,hakan yasa
ya shina yake cike da haushinta,yakance “Duk abinki dai baki isa ki raba qaunata da maimunatu ba” “Dana isa din ai da tuni na raba wallahi da baka kai warhaka tare da ita ba”.
Haihuwarta tafari tasamu Bilkisu,yarinyar data fita daban cikin ahalin gidan da ‘yanuwanta gaba daya,hakan kuma baya rasa nasaba da dangin mahaifiyarta data dauko wadanda suke jinin fulani,kakarta mahaifiyar maimunatu kuma shuwa
ce.
Yadda komai na halittar bilkisu yake daban tun tana ganqanuwarta,saiya zamana komai nata ma daban yake,tsafta kwalliya da ado kullum cikinsu take,maimunatu tana da tsafta gason gayu da ado,uwa uba alokacin takan samu kudi cikin gadonta da mahaifinta yabari,na gidajen da ake mata haya da
sauransu.
Duk wanda yakalli bilkisu saiya kuma dubanta,komai nata tsaf gwanin birgewa,uwa uba ga kyau da Allah yayi mata,sai hakan yasake zame mata ado da
qawa.
Bilkisu nada shekara shida Allah yayiwa mahaifiyarta maimunatu rasuwa,duk dacewa a sannan tana da qarancin shekaru amma ta koka sosai,har hakan
yabaiwa mutane mamaki,kukan nata saiya zama wani gwanin tausayi.
Zuhriyya kusan tafi kowa jin mutuwar ba kadan ba,tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi, mutuwar ‘yaruwarta daya tilo datake gani taji dadi ta girgizata matuga,a lokacin saura watanni aurenta,amma babu yadda ta iya hakanan ta
dangana.
A sannan taso daukar rainon bilkisu,amma bilyaminu ya qeqashe qasa yace sam bazai bata ba,dama can shiri suke na,bata taba nadamar rashin jituwarsu ba irin wannan lokacin,sai taji dana sanin bata aikata dukkan abinda ta aikata din ba sabida rasa damar daukar bilkisu datayi,ta wani bangaren kuma saita sake qullatarsa dajin takaicinsa,saboda duk sanda tatuna rayuwar da ‘yar uwarta tayi
duk da wadatarsu wanda shine sila saita sakejin ginsa a zuciyarta.
Ta fannin dangi ma bata samu goyon baya ba,kasancewar bata da aure itama riqgonta ake, hakanan bikinta gab yake,tilas ta tattara ta haqura,duk da yadda taso daukar bilkisu kamar mutuwarta,saidai kullum tana hanya tana jelan ganin bilkisun,duk da tarin wulaganci da take gani daga wajen bilyaminu amma
tashanye,ita bilkisun kawai take kalla.
A sannan yarinyar bata gamu da wata matsala mai yawa ko.matsatsi ba,saboda zuhiryya kusan kwana a gidan ne kawai batayi,idan tayi nawar duniya ta tsallake kwana daya bata je ba,duk sanda taje zata mata wanka ta gyarata,ta siya mata duk abinda ranta yakeso,tawuni da ita,ta sanyata taci abinci sosai,a haka aurenta
yatashi.
To yanayin aure bazaiyiwu tadinga sakaraftu ba kullum tana kan hanya,saiya zamana duk sati take zuwa ganin bilkisun,a sannan ta fuskanci akwai ‘yan matsaloli na rashin kula daga matar uba dashi ubanma gaba daya,sai tasake
ninka kulawarta akanta.
Ganin haka yasanya mijin zuhriyya sake shiga maganar karbo bilkisu,nan
ma bilyamu yace Allah ya kasheshi shi bazai bada diyarsa ba,a sannan har duqawa zuhriyya tayi tana rogonsa kan hakan amma yace sam,haka tanaji tana gani ta haqura,saidai taci gaba da kulawa da bilkisun har zuwa tsahon wasu
shekaru,wanda a sannan bilkisun takai shekara goma sha biyar.
A lokacinne yanayin aiki yadauke anty zuhriyya da mijinta zuwa qasar
brazil,wanda zasu kashe shekara shida a can.
Ba qaramin tashi hankalinta dana bilkisun yayi na gaba dayansu,saida maigidanta ya kwantar mata da hankali,yakuma tayata shiryawa bilkisu duk abinda tasan
zata iya buqata na tsahon lokaci.
To,ta hadu da uba mai son abun duniya,kusan duk abinda aka aje matan shida matarsa akaci,hakan yasanya kayan basuyi wani tsahon rai ba suka taru suka qare,abinda yarage mata kawai school fees dinta,;wanda shima don anty zuhriyyan taje tabiya na shekarun da suka rage mata,hakanan islamiyya an mata
total ta biya na shekarun.
Asannam bilkisu ta sake tantance tsakanin aya da tsakuwa,tasake gane dacin maraici da rashin uwa,ta gane ranar anty zuhriyya,saboda cikin qanganin lokaci tasoma tagayyara,hatta da sitturunta zuwa wasu abubuwa nata masu daraja
tasoma adabo dasu saboda ba ita kadai ke amfana ba.
Dalili kuwa shine yarinyace da tunda tabudi idanu ta fahimci rayuwar gidan nasu Allah yazuba mata qauna da tausayin qannenta,kusan dukkaninsu suna qarqashin kulawarta ne,idan ka gansu saika rantse da Allah uwarsu daya ubansu daya,zata iya hana kanta tabasu,zata iya hana idanunta bacci su suyi,zata iya yadda ta wahala su su huta,saidai a wannan lokacin dukka wani qogarinta yagaza,saboda
bata da matallafi,sa’annan bata da wani sana‘a ko aiki da takeyi.
Kafin wani lokaci tsanani yayi tsanani;wanda yasa tasoma tunanin wacce sana’a zata kama?,duk da bata da komai bata da kowa,saita soma wankau,lokacin da malam bilyaminu ya fahimci haka nan yadinga surfa ruwan bala’in ba za’a maida masa gidansa gidan tsummokara ba,duk da gidan na wani kyaune dashi na azo a gani ba,hasalima yana buqatar gyare gyare saboda tsufa daya soma yi,tanaji tana
gani ta watsar.
Daga bisani tasamu aiki a maqotan unguwarsu,gidan wata mata da ake kira da
umma luba.
Takan fita wajen aikinta tun safe har dare,wani lokacima takan kai goma kota kwana a can,Idan tatashi a aikin saita biya gida wajenta ta amsa,duka duka albashin nata dubu biyu ne da dari biyar,jhakan yasa baya kaima tarin qannen
dake gareta ko ina bare tasamu ta tsinanawa kanta wani abu.
Babban tashin hankalinta a rayuwa taga qannenta cikin wani mayuwacin hali na bugqata,kuma bata da abinda zata basu ko tayi musu,wannan yasa tasake dagewa wajen daukarwa kattume tallan abinci ranakun da babu makarantar boko da safe kenan,kusan sana’arta kenan,wanda a ciki take ci tasha ta yiwa kanta da yaranta sutura,harma wani lokacin shi mai gayya mai aikin ya rabo yaci a jikinta randa
yatashi bashi dako asi.
Ko daya kattume bata da mutunci ko tausayi musamman akan kudi,akan kudinta zata iya yin komai,bata da lamuni bare daga qafa ko misaqala zarratin,tana iya dafa abinci ta hana dukkan wani yaro dake gidan sai wanda taga dama ko kuma
yaranta,takance “Ubanku mara zuciyar bai kawo ba,don haka bazaku karyani ba,duk maiso
yamiqo kudinsa yaci abinci” abun na matuqar baiwa bilkisu mamaki da daure mata kai,hakanan takan shiga tashin hankali duk lokacin da irin hakan tafaru babu kudin da zata baiwa kattumen ta bawa yaran abinci,idan ‘yan mutuncin na kusa duk sanda ta dawo daga talla zata zuba mata maidan dama,anan ne zasu hadu duka suci,idan wannan bata samu ba,saita karbi bashi idan aka bata albashinta tabiya ta,tana kuwa rubuce da adadin abincin nawa ta karba din, hakanan tana ankare da lokacin biyan bilkisun albashi,da zarar lokaci yayi
zata nemi kudinta.
_wannan itace BILKISU da salon nata rayuwar. Ko yaya nata SIRADIN RAYUWAR
YAKE?,ku biyo ‘yar mutan huguma,itake dauke da amsoshinku_
KEKE HRHKKHHE RHHHKKKEREEK
*2005*
K’arfe takwas na dare take takawa a hankali cikin layukan unguwar tasu,iskace
irin ta sanyi ke kadata hagu da dama,tana kuma kada dan yalolon hijabin dake
mannewa a jikinta kasancewarsa na roba,uwa uba tsufa da shan jikin da yayi
wanda ya rage kaso hamsin cikin dari na kaurin asalin yadin.
Kusan hankalinta bai jikinta,tayi nisa qwarai cikin tunani wanda har hakan yasa
ya bata damu da wanda ke gabanta ko bayanta ba bare gefanta,tunanin nata dukka yana kan qannenta data bari wuni guda sur yau a gida,batasab me sukaci ba yaudin,ko umna kattume ta basu abinci?,ko yauma tayi musu irin halin nata data saba,da yunwa suka kwanta ko kuwa sun goshi?,duka ire iren abinda yake damunta kenan tunda ta fito daga gidan umma luba takamo hanyar gidan nasu,wanda duk da yake cikin unguwa daya suke amma akwai ‘yar qaramar tazara
a tsakaninsu.
Hannu tasa tadan share kyakkyawar fuskarta da takejin qurar hazo samanta,wanda hakan ita bai dameta,takan dauki lokaci mai tsaho kafin ta sanya mudubi gaban idanunta takalli fuskarta,duk wata halitta takyau da Allah yayi mata baiwarsa saidai tajita daga bakin mutane,bata taba tsaiwa ta kalla ba bare
ta tantance,hasalima bata da wannan lokacin ko kadan a rayuwarta.
“Yammata daga ina haka?” Ta tsinci muryarshi daga bayanta,gabanta ne
yayi wani mummunar faduwa,tun kafin tajuya tasan waye,ko kusa ko alama
ta tsani duk wani abu da zaya hadata dashi,bata qaunar tarayyarsu ko alaga dashi,hakanan ta tsani irin abinda yake mata, ita kwata kwata bata sanya kanta cikin jinsin mata bare har wani yace zai damu da rayuwarta da sunan soyayya,a wannan halin da take ciki?,tana ganin babban zaluncine a gareta wani dan adam
ya takura mata da kalmar so ko qauna.
kalmace dako sau daya bata taba magana akanta ba walau a zuci ko a fili,a karan kanta ko ita da wani,towai dawa ma zatayi zancanta?,wa take dashi,bata da kowa bata da abokin magana shawara ko tattaunawa,bata da wanda zata gayawa
shawara ko damuwarta face ‘yan qannenta,wanda su kansu basu gama fuskantar
rayuwar ko matsalarsu ba bare su fuskanci ta wani.
Koda tana da wani gata ko wani tsayayye,tana ganin babban zunubine a
shekarunta qwalli goma sha biyar kacal ta jefa kanta a wannan layin.
Tana tsaka da wannan tufka da warwara yasha gabanta,yaja birki yana
kallonta,tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata ta bayyana tarwai a dan ragowar hasken farin wata wanda hazo yayi nasarar dakushe kaso mafi yawa
na hasken nashi,qare mata kallo yaci gaba dayi yana jin yadda yake sonta cikin zuciyarsa,bilkisu nada wani irin kyau mai sanyi da shiga zuciya,jhakanan komai nata mai kyaune,kama daga kallonta,tafiyarta da maganarta,hatta da shurunta ma,komai nata abun burgewa ne,duk da tarin talauci da fatara daya musu katutu kuwa,yasha rayawa a ranshi wannan da a gidan wadata take ba shakka ba qaramin haddasa fitina kyawun nata zaiyi ba,matuqar yasamu dukkan wani abun buqata da zai bayyana kanshi yadda ya kamata,ba kamar yanzu daya tabbatar da cewa duk da yadda yake ganin kyawun nata fatarar da suke ciki ta wawashi kaso
mai yawa ta boye ba.
Da wannan damar tayi amfani ta kewayeshi cikin matugar sauri da wani irin hanzari tawuce,to ba ma’abociyar iya saurin bace ita,jhakan yasa baiyi wani taku mai yawa ba ya cimmata,yayin da zuciyarta taci gaba da bugun uku uku,Allah
Allah kawai take takai gida wannan qaramar algar tasu ta yanke.
Dab da dakalin qofar gidansu yake a zaune,shi daya da alama yaudin babu ‘yan tayin hirar nashi duk dare da suka saba zaman kisan dabe,masu matattar zuciya kusan irin tashi,kuma ‘yan amshin shatar nashi,hakan yasanya tasu tazo daya
dasu sosai “Ke bilki,bilki!,zo nan” ta tsinci muryar mahaifin nata a sanda yana kwado mata
kira a sanda take gab da shigewa soron gidan nasu.
A matugar sanyi ta sauya akalar tata zuwa inda yake zaune,ta gefen idanu tana iya hango sabi’u wanda yasamu wani waje ya lafe bai qaraso inda suke ba
sakamakon ganin mahaifin nata da yayi zaune a qofar gidan nasu.
A ladabce ta isa gabanshi kana ta durqusa da dukkanin gwiwoyinta,kanta na
kallon rairayin dake shimfide gabanta “Gani baba” sai yatashi yazauna sosai daga kashingidar da yayi,ya gyara hularshi
dake niyyar zamewa tazauna sosai a kanshi “Yauwa” yafada yana sake gyara zaman rigar wuyanshi kamar wanda ya qwaci
kanshi daga hannun ‘yan dambe “Dama cewa nayi zan samu wani abune a wajenki?,yau natashi bani dako sisi
wallahi,waccar kafirar kuma yau tsiyarta ta motsa ganin na tada sabon ginin
dakuna,ta hanani abincin daren ma kwata kwata” wani dunqulailen abu mai tauri
garfin zuciya wajen iya shirya qarya tazauna yadda yadace,farad daya zai iya
ramfota,wanda ita kanta tasan hakan bazai mata dadi ba “Babu kowa’qur ya mata da idanu,yafi kowa sanin halin bilkisu cikin yaransa fiye
da kowayanayinta kawai ya karantar dashi komai,kamar zaice wani abu sai kuma
yafasa yamaida idanunshi ga inuwar da yake hangowa “Kailyakal,fito nan!” Ya qwalla kira wanda hakan ya tabbatarwa hamzan da cewa
yaganshi,saboda haka yafito sum sum kanshi a qasa.
Sam ba haka yaso ta kasance bayaso ace yajema mahaifinta tasigar data dace,ta sigar da addini ya shimfida,cikin girma mutunci da martabayanemi izinin zuwa
wajen bilkisun.
A ladabce ya tsugunna gabanshi kamar yadda bilkisu ke tsugunne,kanshi a qasa
yana shafa sumar kanshi cikin kunya yace “Gani baba,barka da warhaka” “Barka kadai” ya amsa mishi a gaggauce yana dan qare masa kallo ta hasken farin
wata “Da alama tare kuke da maigado,kaine surukin namu kenan?” Cikin kunya
yasaki murmushi kanshi har yanzu a qasa ba tare da yace komai ba,sai ya gyara zamanshi donya qagu yakai inda yakeson kaiwar yatashi yawuce wajen
lami,hankalinsa nacan wajen dare da dada yi
“To madalla,ai abu yayi kyau,Allah ya tabbatar da alheri”
“Amin baba,na gode,Allah yasaka da alheri”
“Amin yaro,ai babu komai,idan Allah yaso sai kaha bilkisu takace” sosai kalaman
sukayi nauyi a zuciya da qwaqwalwar bilkisu,wanne irin nau’in rayuwa ce wannan?,baida masaniya ko damuwa ma da sanin waye hamza a farkom fari kafin akai ga kowacce magana amma har wani abu mai kama da yanke hukunci na qogarin kunno kai ciki?,ama ture ta wannan da d’ai bata taba koda gwada yau gata a amatsayin ta wani ba,abu na qarshe a rayuwarta da bata taba tunashi bayayin da kalaman suka yiwa hamza dadi,don bai tsammaci komai zaizo da sauqi har haka ba,hakan yasanyashi ya karkata aljihun wandonshi na baya ganin baban yamige yanata karkade rigarsa wanda ba wani qura ta diba bayana yin
hakanne saboda yakawo tsaiko da jinkiri koda hamza zaiyi wani abu.
“Ga wannan baba babu yawa” yafada yana miga masa kudin daya zaro,babu wani
kara alkunya ko tayi yasanya hannu ya amshe caraf yana fadin “To Allah yayi albarka yaro kaji…ke maigado….zanje unguwa,idan kingama ki
sakaya qofar” kai kawai ta iya dagawa tanajin yadda kowacce gaba ta jikinta tayi
mata nauyi,daga haka ya juya yasoma bin layinsu yana qirga kudin bakinsa har
qarfin zuciya wajen iya shirya qarya tazauna yadda yadace,farad daya zai iya
ramfota,wanda ita kanta tasan hakan bazai mata dadi ba “Babu kowa’qur ya mata da idanu,yafi kowa sanin halin bilkisu cikin yaransa fiye
da kowa,yanayinta kawai ya karantar dashi komai,kamar zaice wani abu sai kuma
yafasa yamaida idanunshi ga inuwar da yake hangowa “Kail,yakal,fito nan!” Ya qwalla kira wanda hakan ya tabbatarwa hamzan da cewa
yaganshi,saboda haka yafito sum sum kanshi a qasa.
Sam ba haka yaso ta kasance ba,yaso ace yajema mahaifinta tasigar data dace,ta sigar da addini ya shimfida,cikin girma mutunci da martaba,yanemi izinin zuwa
wajen bilkisun.
A ladabce ya tsugunna gabanshi kamar yadda bilkisu ke tsugunne,kanshi a qasa
yana shafa sumar kanshi cikin kunya yace “Gani baba,barka da warhaka” “Barka kadai” ya amsa mishi a gaggauce yana dan gare masa kallo ta hasken farin
wata “Da alama tare kuke da maigado,kaine surukin namu kenan?” Cikin kunya
yasaki murmushi kanshi har yanzu a qasa ba tare da yace komai ba,sai ya gyara zamanshi donya qagu yakai inda yakeson kaiwar yatashi yawuce wajen
lami,hankalinsa nacan wajen dare da dada yi
“To madalla,ai abu yayi kyau,Allah ya tabbatar da alheri”
“Amin baba,na gode,Allah yasaka da alheri”
“Amin yaro,ai babu komai,idan Allah yaso sai kaha bilkisu takace” sosai kalaman
sukayi nauyi a zuciya da qwaqwalwar bilkisu,wanne irin nau’in rayuwa ce wannan?,baida masaniya ko damuwa ma da sanin waye hamza a farkom fari kafin akai ga kowacce magana amma har wani abu mai kama da yanke hukunci na qogarin kunno kai ciki?,ama ture ta wannan da d’ai bata taba koda gwada yau gata a amatsayin ta wani ba,abu na qarshe a rayuwarta da bata taba tunashi bayayin da kalaman suka yiwa hamza dadi,don bai tsammaci komai zaizo da sauqi har haka ba,hakan yasanyashi ya karkata aljihun wandonshi na baya ganin baban yamige yanata karkade rigarsa wanda ba wani qura ta diba bayana yin
hakanne saboda yakawo tsaiko da jinkiri koda hamza zaiyi wani abu.
“Ga wannan baba babu yawa” yafada yana miga masa kudin daya zaro,babu wani
kara alkunya ko tayi yasanya hannu ya amshe caraf yana fadin “To Allah yayi albarka yaro kaji….ke maigado….zanje unguwa,idan kingama ki
sakaya qofar” kai kawai ta iya dagawa tanajin yadda kowacce gaba ta jikinta tayi
mata nauyi,daga haka ya juya yasoma bin layinsu yana girga kudin bakinsa har
Zuciyarta cike fal da mamakin halayya da dabi’un mahaifinta da koda yaushe take kwana tatashi dashi,tabbas babu shakka banda wasu abubuwa da suka bayyana qarara cewa shine mahaifinsu,da babu abinda zai hana ta musanta cewa ta
tsatsonshi tarin yaran da yake dasu suka fito,ciki kuwa harda ita.
“Yi sauri ki migo min mana maigado,yunwa fa nakeji ba ‘yar kadan ba” yafada yana miqa mata hannayen nasa,sai data ja numfashi takaishi qasan hunhunta sannan ta daga oily eyes dake sheqi da walainiya kamar an diga musu mai,ga wanda bai sani ba kuma zaiyi tsammanin qwalla ta tara kuka take shirin yi,cikin sassanyar muryarta wadda ke bayyanar da yanayin nutsuwa da Allah yazuba a
halittarta tace “Bata biyani ba baba”.
Wani baci ranshi yayi,kai kace ajiya yabayar yazo karba kuma akace mishi an kashe,hura hanci yayi yafidda iska zazzafa daga dukkan hanci da bakinsa yana jin takaici,don harga Allah yasa rai sosai da kudin,don ya jima da haddace ranakun
da take karbar albashin nata,tamkar shike zuwa mata aikin “Oho,kicemin aikin banza kike zuwa yi,babu uwa babu riba,duk yadda nadauke
kai nayi haquri jumuri da juriyar barinki kina aikin ashe bazai iya kashemin takaicin komai ba,to gaskiya bazan lamunta ba” sosai gabanta yafadi,qafafunta sukayi sanyi harsai data kasa jurewa ta gyara durqusonta a gabanshi,tana tsoro,tana tsoron kada ya hanata zuwa aikin,wanda Allah da manzansane gatanta ita da qannenta sai aikin wanda bai kashe masu gishirwa koda cikin cokali cikin qishirwar abubuwan bugatun rayuwa da suke dashi,saidai duk da haka hausawa
kance da babu gwara babu dadi,hakanan yafi babu,da sassanyar muryarta tace “Ta yimin bayani baba,tace itama tana jira a biyata nata albashin ne saita
sallameni,kamar daga can inda za’a bada albashin dukka ma‘aikatan gidan ne basu nan” jim yayi yana tunanin ta inda zai wanye,idanunsa na hango masa inuwar hamza,kamar ya fahimci ya biyota ne yanason magana da ita,idan kuwa hakane yasamu inda zai samu kudin da yau zai siyawa bazawararsa tsire kamar
yadda yacika mata baki yakuma alqawarta mata.
“Shi kuma wancan da kuke tare fa?” Ya fada yana nuna saitin inda hamza ke labe,gabanta yasake faduwa karo nabiyu,idan akwai abinda ta tsana shine
babanta ya ganta da wani,akwai abubuwa masu tarin yawa da hakan zai iya faruwa da zubewar gima da mutunci da zai iya faruwa,kaita girgixa dasauri
ba tare da juya takalli inda yake nuna matan ba,saboda tana da rauni,bata da
c
kunne yana wassafa yawan bajintar da zaiwa lami dasu,wadanda yake fatan su
zama silar da tarkonsa zai kama kurciyarta tashigo gidansa.
Shurune ya ratsa wajen,yayin da bilkisu ta kasa koda qwaqqwaran motsi daga inda take duqen,ta gefan hamza kuwa ci gaba yayi da kallonta,yanajin qaunarta da wani farinciki na takar sa’ar samun karbuwa wajen mahaifinta karon farko tana ratsashi,shi kansa ya yabawa kansa kan namijin qogarin da yayi wajen tsallake matakai guda biyu masu matugar tsauri a wajensa kafin isa kan bigiren da yake kai yanzu,mataki na farko shine fitowa ya bayyanawa bilkisu soyayyarshi a gareta,duk da wani kwarjini da kamewa ta musamman da Allah yayi mata,duk kuwa da qarancin shekarunta,mataki nabiyu yadda ayau harya tsaya gaban
mahaifinta magana ta gudana a tsakaninsu.
A hankali tamiqe daga tsugunnon tasoma takawa zuwa shiyyar qofar shigewa gidansu,hakan shiya farkar da hamza daga duniyar tunanin daya tafi,cikin zafin
nama yayi dan tattaki ya cimmata “Bilkisuya zaki tafi ko gaisawa bamu….” A nutse ta daga idanunta ta kalleshi ba
tare data furta komai ba,sai yaji kwarjininta ya cikashi harya danja baya kadan yana dubanta,ta kalleshine kamar yadda tasaba kallon kowa amma sai yaji wani iri harya kasa sake ce mata komai har zuwa sanda ta tura qauren gidansu dake
dab da qarasa karyewa gaba daya su jingineshi tashige.
Ajiyar zuciya yasaki mai nauyiyana qaunar bilkisu irin qaunar da baisan adadinta ba,duk da cewa shi a karan kanshi yana ganin kamar tafi qarfinsa a zubi da
baiwar kyau da Allah yayi mata,kamar yadda abokanshi sukan sha gaya masa “Hamza,kabar ganin yarinyar nan tafito daga gidan masu qaramin garfi,ba tsarar
aurenka bace,irinsu kyawunsu shune jarinsu,duk talaucinsu baka rasa wani
hamshaqin mai kudin da zai qyallosu yayu wuf dasu,sannan uwa uba akwai qishin qishin din dangin babarta masu wadatane,ba’asan dai dalilin wanzuwarta a haka cikin wahala ba”. Wadan nan kalaman dama ire irensu yasha jinsu bakin abokansa
da yawa,amma yakan basu amsa da cewa “A rashin tayi akan bar araha,a rashin kira kuma karen bebe ya b’ata,hakanan
matsoraci baya zama gwani,kudai kubarni na gwada sa‘ata kawai” da wannan tunanin yasaki ajiyar zuciya kana yasoma takawa yana barin layin,cikin zuciyarsa yanajin ko iya haka yasoma taka matakin nasara kan bilkisu,kuma yana fatan nan
gaba nasarar tashi tafi haka.
Bagqiqgirin tsakar gidan nasu yake, babu hasken fitila ko kadan banda wadda ke fitowa ta tsakankanin labulen dakin umma katti kamar yadda sukan kirata,banda tallafi da rahamar ubangiji na hasken farin wata babu abinda zai hana mutum mai qarancin gani yazuba tuntube a tsakar gidan nasu dake warwatse da kwanukan da sauran tarkace nan dacan,wanda basu wuce na sana‘ar abincin daren umma katti ba,kusan haka al’adarta yake,duk sanda tagama sana‘arta ta dare tashi take tawuce daka abinta tashiga sabgoginta na irgen kudi dakuma wassafa abinda zata siya gobe bayan tatake cikinta dana yaranta,dana mai rabo cikin yaran mijin nata,tacusa kudinta qasan filo tamaida kanta takwanta tahau jan minshari,aikin kusan na bilkisu ne,wanda duk safiyar duniya bayan ta idar da sallar asuba bata maida kanta ta kwanta,saita kintsa gidan,kana tayiwa qannenta wanka itama tayi
tashirya cikin tsummokaran unifoarm dinta tawuce makaranta.
Ajiyar zuciya tasaki tadinga ratsa kwanukan tana wucewa zuwa dakinsu da take hango haske kadan kadan,wanda hasken take da yaqinin na acibal bal din data hada musu da kanta,amma tayi mamakin ina suka samu kudin kalanzir din suka
zuba,idanunta nakan dakin cike da tausayin yaran harta isa bakin qofar dakin.
Da sallama ta daga labulen tashiga,dukkaninsu suna zaune kusan su goma gaban tabarma qwaya daya da sukayi tarayya wajen kwana akai,tun daga jikkunansu basai ankai ga fuskokinsu ba ya isa ka gane tsantsar rashin gata da kulawa dake
tattare dasu,gamida buqatuwar tallafi cikin rayuwarsu.
A hankali take nazartarsu,fuskokinsu babu walwala sam,idanunta yasauka kan wacce ke kwance kan tabarmar,hauwa’u ce,da sauri ta cire takalmanta ta qara
hanzari zuwa cikin dakin a dan rude tana fadin “Subhanallahi, hauwa’u jikinne?” “Tunda kika tafi yaaya yau bata fito ba,zazzabi take tayi” cewar daya daga cikin
yaran,wadda tadan daresu duka a shekaru.
Saita waiwayo tana dubanta
“Baba yaga yadda take?” Ta tambayesu,sai kusan dukkansu suka kada kai “Kunci abincin dare?” Tasake tambayarsu
“A‘ah” suka bata amsa kusan a tare,don babu wanda cikinsu cikinsa baya kiran
ciroma,ciwon ‘yar uwar tasu ya sanya suka daina damuwa da yunwar sosai,don
dama kwana da yunwa ba wani sabon abu bane a wajensu.
Zallar mamaki yasake cikata,wacce iriyar rayuwa suke haka wadda bata da wani maraba da rayuwar marayu,marayunma marasa galihu,wadanda basusan uwa
uba ko wani dangi nasu ba,hauwa’u na daya daga cikin yaran da take matuqar tausayi cikin qannen nata,kasancewar taqamaimai a yanzu babu wani tartibin waje da za’a ce ga inda dangin mamanta suke,sakamakon fulani ne na tashi baban nasu ya aura,sadda xaman ya gagara sukazo suka mashi diyarsu suka bar
masa tashi gamida karba mata takardar sakinta “Ina hannatu?”ta tambayesu bayan ta lura da cewa bata dakin “Tafita roqo mata magani a chemist” sakin hauwa’u tayi tamiqe da hanzari,sam
bata qaunar idan dare yasoma yi taga daya daga cikinsu a waje,hannatu kusan itace babba a cikin yaran,saboda ta tasamma shekara sha hudu,shekara biyu
bilkisu ta bata “Ina zuwa'” ta fada da hanzari tana ficewa,dukka yunwa gajiya,damuwa dama
abinda ke damunta damuwar yaran saita murqushesu,tunaninta na farko inda zata sama musu abinda zasuci,na biyu maganin da hauwa’u zata sha kome qangantarsa,tana tsaka da wannan tunanin sukayi karo da hannatu wadda itama ke tafe cikin damuwa,kasancewar hauwa’u ce aminiyarta cikin yaran duka
gidan,duk da ta bata shekara biyu itama,amma tasu tafi zuwa kusa.
Sosai bilkisu ta hada rai tana dubanta “Daga ina kike?” Maimakon ta amsata sai hawaye yabiyo kuncinta,cikin muryar
kuka tace “Naje samowa hauwa magani a chemist din bala amma ya hana” kukan yarinyar
ya kashe mata jiki da zuciya sosai,maimakon fada dataso mata saita kasa,ta kama
hannun hundatun “Amma bana hanaku fita ba daga sanda akayi sallar magariba ba hindatu?ban isa
na gaya muku kujiba?” Kai tashiga girgizawa sosai,har yanzu tana hawayen tace “A‘ah wallahi yaaya kin isa,jikinta ne har huci yakeyi,tanata rawar sanyi,shi yasa
na kasa Zama,amma kiyi haquri” shuru tasakeyi tana hadiye wani abu mai daci da tauriyaran tamkar sun fahimci babban galubalen rayuwa,gibi gamida nakasa da rayuwarsu ke ciki,sai suke qaunar junansu sosai tamkar uwa daya uba daya
suke,tsahon wasu mintuna sannan ta iya bude bakinta “Ki daina kuka,zata samu lafiya,amma kada ki sake fita,banason fitar dare kwata
kwata” “To yaaya” “Muje ciki” tafada,hannatun tayi gaba tana biye da ita a baya har zuwa tsakar
gidan.
Dakinsu ta shige yayin da ita kuma ta durfafi dakin umma katti,bakinta dauke da addu‘a Allah ya dorata a kantayasa tasamu abinda zata baiwa yaran suci
sukwanta.
A hankali ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,tana kwance kamar yawancin daga ita sai daurin qirji da dankwali mai santsi wanda bai dauru sosai ba,saijsn gwarti take abinta,duka rumfar tata cike da tarkaceyaranta duka sunyi bacci sai
lariya dake zaune saman kan uwar tana cin abinci.
“Yaaya,kin dawo?” Tafada,kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu,duk da
yadda uwar kan kyaresu idan taga suna nunawa juna qauna “Nadawo lariya,umma tayi bacci?” “Eh amma bata dade ba” kan bilkisu tace komai lariya tasoma bubbuga saman
kan umma kattin tana cewa “Umma kitashi ga yaaya bilki tadawo” kafin takai ga hanata har umma kattin
tatashi,a fusace tazauna dungurgur tana gyara zaman dankwalinta dake shirin
zamewa tana duban lariyan “Me za‘a siya da saikin tasheni” sai datakai lomar shinkafar bakinta sannan tace “Ba abinda za’a siyayaaya bilki ce tazo nemanki” maficin da take firfita dashi
wanda garin bacci yazame yafadi ta jawo takai mata bugu “Shine don tsohonki zaki tasheni haka sai kace wata diyar gwamna,du randa kika
sakemin irin haka saina sassabar miki” itadai lariya cigaba tayi dacin abincinta,sai data gyara zamanta sosai fuska a dinke ta maida kanta ga bilkisu wadda ke
rakube kamar wadda ruwa yaciyo “Bashina kikazo biyana da kika saka aka tasheni sa tsohon daren nan?” Gabanta
ne ya yanke yafadi,babu alamun zata samu abinda tazo nema kenan da
alama,kaita kada a sanyaye “A‘ah,amma in sha Allahu zuwa jibi za’a biyani zan kawo miki”shuru tayi ranta a
bace na wasu sakanni sannan tace “To meye?”da qyar ta iya buda baki tace “zuwa nayi don Allah idan za’a samu sauran abinci wajenkiyarancan duka ba
wanda yaci abinci,ga hauwa na kwance ba lafiya” sake dinke ranta tayi “Ai kinsan rabon tsohonki da cefane a gidan nan ko kawo qwayar hatsi yau sati
guda cur ko?,kuma duk randa yakawo din idan na dafa ba wanda nake hanawa ai”
tasan magana ta yada mata amma saita shanye “Nufina abincin siyarwa,saimu saka a lissafi….” “Babu” ta fada da hanzari tana katsar numfashinta gamida juyawa da niyyar
komawa ta kwanta “Akwai wanda kika rufe da abun tatar taliya fa” raliya tafada,saita daga kai ta
watsa mata harara sannan tace “Tunda kece uwata aisaiki dauko ki bata ko?,zakici ganiyarki kema idan idan kika
qureni,xan barki da iya abincin da tsohon naku ke kawowa kiga idan zaki rayu”
daga haka ta maida kanta tayi kwanciyarta tana qananun mitoci “Yara sai shegen ci,na rana ma dana dubi Allah nabasu ashe basu gani ba zuba
idanun na dare sukeyi,sai kowa ya lashi walgiya ya kora da ruwa ai ya kwanta”.
A sanyaye ta juya tafuta daga dakin tana tunanin meye dabara ta gaba,a haka har takai soron gidan batama sani ba,tana yunqurin fita wani tunani yazo mata,saita
koma wajen tukwanen shinkafar umma katti dake jiqe.
Tsintsirar da ruwan dake ciki tayi a hankali har zuwa sanda ya qare,ya zamana saura qganzon shinkafa dake can gasan,cikin kwanukan dake wajen ta dauki guda daya ta wankeshi tas,sannan ta saka hannu ta dinga tsame qanzon tana zubawa a farantin,haka ta dinga yi harta tsame qanzon tas,ta sake wankeshi,ta tsaneshi dakyau,ta tsaya tana dubanshi sanda yake digar sauran ruwan da bai gama digewa ba tana wassafa yawanshi,duk da bashi da yawa,duk da bazai ishesu su qoshi ba,amma tasan a qalla zasu rage wata kafar,ba zasu kwanta da yunwa mai hana bacci ba,to amma inda gixon ke sagar inda zata sama musu mahadi,tasan cewa ba za’a rasa mai da yaji wajen umma kattin ba,amma tayi imanin koda ta roga maa yadda yau take kan tsininta ba zata bayar ba,tunda abun yau ba iyasu
kadai ya shafa ba,harda mai dugungurun gum dinma gaba daya wato babansu.
Ta dauki tsahon mintuna kana ta taka da kwanon a hankali zuwa dakin,tana shiga kowannensu yazubawa farantin idanu,da alama a zaqe suke,hakanan cikinsu
cike yake da yunwa,jira kawai suke su samu abun sawa a bakin salati,tausayinsu yasake cikata,inama ace wani abincine mai kyau da dadi a hannunta da zata ciyar dasu,wanda zasu kwanta suna murna cikinsu a qoshe taf kamar kowanne yaro
mai gata da ‘yanci?.
Saita isa tsakiyarsu ta aje farantin tana cewa “Bari na samo maku mai da maggi ko gishiri kunji?” Fuskarsu fadade da fara’a da
farinciki na qanzon da aka samu suka amsa da to,hannatu tace “Umma tabarki kin debo?,dazu dazan kankare mana muci hanani tayi ta sheqa
masa ruwa” tausayi yasake cikata har idanunta wannan karon ya hada quwalla,ba shakka duk yaron da aka haifeshi cikin gidan nasu ya fado cikin wata jarrabawa ne ta rayuwa,hakanan dukkaninsu ababen tausayi ne,duk da cewa gwara wasu da wasu a cikinsu,tunda akan samu wadanda iyayensu kan leqo da abun arziqi suga yaran nasu,Saidai kusan da zuwan nasu da babu duka sammakal,don da zarar uban ya qyallara idanu yaga abinda aka kawo din zai rage mishi wani nauyi zai dauke,ko yace ayi amfani dashi a gida,;wanda kwana daya ko biyu ya
qare,maimakon abarwa yaron da aka kawowa yamora.
Kasa bata amsa tayi saboda batason suga qwalla a idanunta ko raunintajtana