SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Ajjiye wayar tayi tanajin wani daci da zallar rashin adalci cikin lamarin gaba daya,a iya sanin data yiwa fulani aishan macace mai tausayi jin qai da kuma kyan hali,batasan meya sauyata haka lokaci daya ba,tayi mamakin yadda tabari BURI gami da ALWASHIN watsa aniyar maqiya yakeson sauya halayya da dabi’arta,ta dauki buri mai tsaho da girma akan azeez fiye da yadda aka santa,duk da cewa dama can mutum ce mai son ‘ya’ya,amma duk da haka tana da kyakkyawar halayya da dabi’a wadda ta siya mata soyayya mai girma a zukatan al’umma,sai gashi yanzun tana wasu abubuwa da suke baiwa sodangi mamaki,halayyar da sam tasan ba tata bace,rashin adalci,rashin tausayi da kuma nuna halin ko in kula akan kowa face diyoyin cikinta,indai hakane kuwa maqiya sun cucuta,dafin magauta ya ratsata,ya mata kuma tasiri da har yafidda kyakkyawar halayya daga cikin jininta ya sauya mata wata.
Kamar yadda ta zata din kuwa babu wanda ya kalla abincin ma a cikinsu har ita kanta,kusan kowa zuciyarsa babu dadi,duk da cewa wani abu yau ya bata mamaki,ta gaza karantar yanayin da zuciyar bilkisu ke ciki a yau,farinciki ko akasin haka?,wani irin emotion take gani kwance saman fuskarta data gaza tantance a wanne bigire zata ajjiyeshi?.
Kamar kazar sa qwai ya fashewa a ciki take shiryawa,ita kanta batasan a wanne matsayi ruhi da zuciyarta suke ciki ba,abinda ta sani kawai shine,ta tashi da qwarin gwiwa bayan ta raba dare tana tunani tare da qoqarin samarwa kanta mafita,ta sanyawa kanta wani yaqini da jarumtar amsar duk wani nau’in rayuwa da zata tunkareta.
Tana shiryawa idanuwanta na sauka sashe bisa sashe na dakin,tana tuna dukkan yadda rayuwarta ta wakana cikin gidan tsahon shekara guda,ta runtse idonta lokacin da tunaninta yakawo ranar daya amshi mutuncinta,take dukkan wani qwarin gwiwa data tattarowa kanta ta tarwatse,saita sulale a wajen saman gwiwoyinta tana rufe fuskarta da tafukan hannunta,tana jin wani irin abu yana tasowa daga qirjinta can cikin zuciyarta,ambaton sunan Allah tasoma yi,wanda hakan ya taimaka mata ta daidaita tunaninta,saita miqe a hankali,tazauna gefan gadon,ta nutsu nadan wani lokaci sannan taci gaba da shirinta.
Sanda take sanya kaya take kuma agogo wanda yake nuna mata mintuna ashirin kacal suka rage su fita daga gidan zuwa filin sauka da tashin jiragen sama don konawarta tushenta,qarar qararrawa taji da alama akwai mai buqatar shigowa gidan,dukka saita tattara hankalinta,har zuwa sanda taji.mama sodangi ta bude qofar,muryar wata mata taji wadda bata santa ba,saidai tana iya jiyo kiran sunanta da mama sodangi tayi da ladingo,daga haka bata kuma jin komai ba saita qara hanzari ta kammala shirinta gaba daya.
Sake duban agogo tayi,minti goma ya rage musu,tana dauke idanunta ana turo qofar dakin,mama sodangi ce,idanunta kan bilkisu,cikin wani irin yanayi daya dasawa bilkisu fargaba da faduwar gaba,wadda ta sanya ta gaza ci gaba da kallon maman,ta sadda kanta qasa,har zuwa sanda ta qaraso inda bilkisun ke tsaye.
Kamar wadda batasan meya shigo da ita dakin ba ta tsaya tana duban bilkisu,a hankali ta lalubo hannunta ta sanya takardar,hakan ya sanya ta daga kai tana dubanta,kai mama sodangi tasoma girgixa mata,idan ta lura dakyau ma kamar qwalla ce cike a idanunta,dukkansu babu wanda ya iya cewa da dan uwanshi komai aka sake shigowa dakin,sallamar ladingo ta karade dakin,maimakon mama sodangin ta amsa,sai kawai tasaki hannun bilkisun ta juya da sauri tafice daga dakin,ita kuma ta rakata da ido har ta bacewa ganinta,sai a lokacin ta ankara magana ladingo ke mata,ganin alamun bata ji ba yasanyata maimaitawa
“Idan babu damuwa zan soma debe kayanki na fita dasu,driver yazo za’a saka cikin mota” bata iya cewa da ita komai ba,don ji take kamar bakinta bai taba magana ba bare tasan ta yaya zata amsa mata,qafafunta tamkar lawashi saboda rashin qwari,tana jinta kamar mai tafiya a wata duniya ta daban tasoma nufar qofa don barin dakin ba tare data waiwaya tasake duban dakin ba,ba tare data tsaya ta duba ko akwai abinda ya kamata ta dauka ba,babu komai cikin hannunta sai takardar datake da tabbacin ko ba’a gaya mata ta meye ba tasan ta meye,har takai falo sannan taji kamar qafafun nata ba zasu iya qarasawa da ita waje ba,don haka ta lalubi kujera tazauna donta ragewa kanta nauyin da taji dukka gabban jikinta sun mata.
Kamar a inuwa taga shigowar wasu matasa,wanda da alama ma’aikata ne,kamar a inuwar taga ana fidda dukka kayan gado da aka qawata dakin dasu,eh kamar inuwa zata ce,tunda hankalinta bai jikinta bare ta tantance inuwa ne ko zahiri ne.
Tamkar mutum mutimi haka take zaune cikin falon gidan,daga kunnuwanta har idanuwanta basa iya ganin komai,basa kuma gane kome face mai rayuwarta ta gaba zata haifar mata.
Hannunta na dama dunqule yake da takardar data zamto tamkar wani mubudi ne na rayuwarta ta gaba,takarda ce da saqon dake ciki take jinsa daidai da saqon ranar mutuwarta,riqonta kawai zafi yake mata tun daga tafin hannunta har zuwa qwaqwalwa da zuciyarta,yakuma zarce zuwa ilahirin jikinta gaba daya.
Duk da cewa tana tsammanin zuwan ranar,duk da cewa tasan cewa lallai lallai komai daren dadewa irin wannan ranar tana tafe,takuma shirya zuwanta tun daga ranar da aka soma lissafin kasantuwar kwanakin har zuwa randa zata risketa,saidai batasan me yasa ba,meye dalilin data tabata har haka ba,batasan meye dalilin da jikinta da zuciyarta suka girgiza har haka ba,sabone?,ko kuwa tunanin me gobenta zata haifar mata ne?,meye matsayinta meye sakamakon rayuwarta?,wanne sabon shafin zata bude?
Karo na qarshe ladingo tafito tafito da akwatinta da take jin shine abu na qarshe a cikin dakin data mallaka,ta qarasa inda take aje musu kayansu shima ta ajeshi,ta qarasa gaban bilkisu ta tsaya cikin rusunawa
“An gama fitar da komai,ance jirgin qarfe sha biyu zamu bi,yanzu haka mai motar dazai daukemu zuwa filin jirgin yana kan hanya….”
Qwaqwalwarta tajiyo wani sashe na maganarta,saidai bata fahinta duka ba,cikin jimla guda ta tattara maganartata,qwaqwalwarta ta sake aika mata da saqon
“Tafiya zakuyi,zaku koma nigeria,zaki kuma cikin gidanku”.
Tamkar wadda ake bawa umarni sai kawai tamiqe,cikin qarfin hali tasanya hannu tagyara zaman qaramin hijabinta,kana tasoma takawa a hankali kamar mai tafiya saman qayoyin da aka shimfidawa hanyarta tayi hanyar bedroom din daya zama shine matattarar dukka wani tarihi nata.
Idan ka kalleta a sannan zaka iya rantsewa tashigo dakinne tana son fayyace da ainihin qasar wanne waje aka gina dakin saboda yadda takebin kowacce kusurwa ta dakin da kallo sama zuwa qasa da kallo har na tsahon wasu daqiqu.
Sauke idanunta tayi awani sashe can na dakin,tasoma takawa a hankali kamar wadda maganadisu yake janta zuwa arean,tasa hannu tasoma shafa wajen,yana yawan tsaiwa a wajen duk da cewa cikin duhu take ganinsa,yana son wajen sosai duk da bata taba ganinsa muraran ba,saita sake matsawa da jikinta wajen,ta lumshe idanunta tana shaqar daddadan qamshin da wajen yake fitarwa,tabbas qamshinsa ne,abinda duk cikin rayuwar datayi mai kama da mafarki tafi riqewa,saikuma qaqqarfar ajiyar zuciya wadda tasaka dukkan gabbanta suka saki,hawayen da uta kanta batasan na meye ba suka ziraro daga idonta guda daya.
Kamar wadda aka tsikara tajuya da sauri tanufi qofar ficewa daga dakin,dakin da zuwa yanzu yakoma zallar kangonshi babu komai ciki tamkar wasu rayuka basu taba wanzuwa a ciki ba,batasan inda kayan suka koma ba tunda dama ba mallakinta bane.
Girgiza kanta take dasauri tana gayawa kanta,tabbas bata tsira da komai ba,babu abinda ta tsira dashi koda kuwa hoton fuskarsa ta zahiri ne face ragowar qamshinsa daya barwa hancinta da qwaqwalwarta tabonsa.
Cak ta tsaya tana duban gabanta,kana ta duqa a hankali takai hannunta tadauki zoben daya dauki hankalinta qwarai,zobene da tasha ganinsa a yatsunsa,abun guda daya tak datake iya banbance dangane da duk wani abu daya shafeshi,cikin sauri tadauki zoben ta damqe a hannunta kana cikin sassarfa tafice daga dakin ta zarce da ficewa daga gidanma gaba daya don tanaji cewa izuwa yanzu itama ya kamata ta yanke dukka sauran abinda yayi saura.
Tanajin ladingo na mata magana saidai bata ko tsaya ba bare ta waiwayo ta dubeta,fatanta shine ta raba kanta da komai daya wanzu a shekara guda,ta yanke dukkan wani abu dake da alaqa da shekarar……..
********** ***** ********
Tana zaune daga guri na musamman da aka tanada saboda xaman baqi,daga gefanta kuma maimartaba ne sarkin qasar kaisa,daga hannunshi da nata hannun yaransu kowanne zaune a mazauninsa,dukkaninsu sun bada hankalinsu dari bisa dari kan taron da ake gudanarwa,farinciki ya lullube zuciyar kowannensu na ganin yadda dansu kuma yayansu yaketa karbar lambobin yabo da girmamawa kala daban daban.
Kamar yadda a tsarin shiga kyan halitta,kwarjini da kuma wata irin ginshira tasa ya fita daban da sauran daliban,hakanan ma ta fannin hazaqarsa suna gamida shahararsa cikin makarantar,farinjininsa daga wajen malamai har zuwa dalibai.
Fuskar fulani aisha tamkar gonar auduga,zuciyarta fes kamar dutsen qanqara,har hakan ya gaza boyuwa ya bayyana saman fuskarta,jerarrun fararen haqoranta irin na azeez sun bayyana kansu saboda irin murmushin da takeyi,ko iya yanzu ta tabbatar da cewa azeez din yayi zarra,yakuma fara taka irin matakin da takeso ya taka,tauraruwarsa ta haska ta danne ta kowa,sunansa ya shahara yakuma fantsama ko ina,inama ace adama tazo wajen batayi qaryar bata jin dadi ba?,koda yake koda adama batazo ba,ta tabbatar afra zata bata labarin dukkan abinda ke faruwa,uwa uba akwai waya a hannunta tana nadar komai.
Wasu qwallar farinciki ne suka so fitowa daga idanuwanta a lokacin da aka buqaci mahaifinsa ya taso makaranta zata girmamashi saboda irin gudunmawar daya bayar,da kuma kyakyyawan misali daya baiwa dalibai,hakanan yasa makarantar tasake samun daukaka da suna,bayan maimartaba ya isa wajen sai azeez din ya nemi alfarmar mahaifiyarsa ta taso,sosai ta dinga jin farinciki,tana jin cewa taqi kadan ya rage burinta ya gama cika.
Awa biyu cur akayi kwashe ana gabatar da taron kafin a kammala,har yanzu farinciki yaqi barin zuciyarta,cikin sigar xolaya mai martaba ya dubi fulani aisha
“Ke ko ‘yar karan nan ma babu,kinga fuskarki kuwa kamar gonar qanqara?” Cikin dan jin nauyinsa tadan sunne kai kadan tana dariya qasa qasa kana tace
“Bazan iya boye farinciki na ba,don abdul’azeez bai bamu kunya ba,yayi dukkan abinda yakawoshi qasar nan,harma fiye da abinda muka zata” kai.ya jinjina shima yana sake jin dadi,alfahari da tilon dan nashi namiji yana ratsashi.
Daga mazaunin dalibai maza kuwa kamal ne zaune kamar ruwa ya cishi,duk wani motsi na azeez din yana kan idanunshi,jin zuciyarsa yake kamar zata babbake ganin yadda yaketa samun lambobin yabo daga bakunan malamai kala kala,ya tabbatar wannan labarin bamai dadi bane akunnen mahaifiyarsa,ya rasa kuma meye hana fulani adama zuwa wajen,bayan mom ta shaida mishi tana qasar,kuma zata zo.
Can wani sashen kuma daga rukunin mazaunin daliban dai minal ce zaune,ita dinma idanunta hankalinta da tuaninta yana ga azeez din,wani daci take ji cikin ranta da zuciyarta na yadda tayi loosing oppurtunity dinta,na yadda ta rasa azeez din,duk da ta taki babbar sa’a da bai sake tada case din ba,bai kuma sake nemanta kobi ta kanta ba,duk da cewa a hakan tana boye kanta daga gareshi,kada wataran su hadu ya tuna allura ta tono garma,wai shin me zatayi azeez ya sota kamar yadda take buri?.
“Guy din nan ya gama haduwa,komai yaji,Allah ya masa komai” ta tsincin furucin na fitowa daga bakin wasu ‘yammata dake zaune gefanta,saita waiwaya tana dubansu,ji tayi wani abu ya tokareta,kamar ta miqe ta shaqesu ganin yadda suke binsa da kallo duk inda ya motsa kamar wasu tsaffin mayu,dole ta janye idanunta daga kansu tana jan tsaki mai qarfi a fili,wanda sai daya sanya qawarta ta waiwayo tana dubanta gamida tambayarta,saidai bata bata amsar komai ba.
Lokacin tashi nayi kamar yadda aka tsara a rubuce aka qarqare komai,a nan dalibai suka soma musayar adress da lambobin waya gamida daukar hotuna a tsakaninsu.
Haka ce ta faru ga azeez,mutanen dake son daukar hoto dashi….musayar lambar waya da amsar adress suna da yawa,harda ‘yan shishshigi,harda wadanda shi bai taba hulda dasu ba,iya mutanen da suke selective a wajensa ya tsaya sukayi wadan nan abubuwan ya qara gaba wajen da motocinsu ke fake ya barsu a wajen.
Me martaba ne cikin motar,sai ammi a ciki,sauran duka suna wata mota ta daban,yana shiga maimartaba ya dubeshi cikin murmushi
“Wadan can mutanen da suka jiraka fa?” Sai daya waiwaya ya dubesu ta window sannan cikin girmamawa yace
“Allah ya taimakeka…..na gama sallamarsu” murmushi kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba,ya riga da yasan hali xanen dutse,har yanzu halayyarsa tana nan a jininsa,tun zamanin shekaru qananu har yanuzu da aka doshi shekara ta ashirin da shida.
Lokacin da drivern ya tada motar suka fara tafiya mai.martaba yayi gyaran murya,kana cikin sautin muryarshi dake nuna tsantsar hikima,dattijantaka da kuma kamala yace
“Babu shakka duk baiwar da dan adam yaga ubangijinsa yayi masa….yayi masa itane bawai don yafi kowa ba,a’ah,yayi masa itane saboda shi din mabuwayin sarki ne,yakanyi abinda yaso a sanda yaso a kuma lokacin da yaso,dukkan wata baiwa a rayuwa tamkar jarrabawa ce ga bawa,yakan iya cinyeta,yakan iya kuma afkawa zuwa ga halaka idan baiyi takatsantsan ba,abdul’azeez…,zuwa yanzu girma ya soma hawa kanka,tunda gashi har ka soma aje wani mataki na karatu,shekarunka kuma sun bar ashirin da biyar sun soma tsalle zuwa da shida,ina fatan zaka zama mai nutsuwa da nazari a duk yanayi matsayi ko matakin daka samu kanka,ka zama cikakken mutum mai kamala da adalci,sannan kuma adali a duk wani sha’aninsa,hakan zai baka dama ta gina inga tacciyar rayuwa,ka samu iyali na qwarai,ka auri matar da bazata zalunceka ba kamar yadda kaima ya haramta ka zalunceta,wannan shine matakin rayuwarka ta gaba” hakanan yaji wani irin yanayi ya shigeshi,cikin girmamawa ya furta
“In sha Allahu”.
Murmushi fulani aisha tayi tana qoqarin danne yanayin data shiga
“Allah ya taimakeka nasihar tun yanzu?,da ka bari ai mun qarasa gida kun huta tukunna sai kuyi xama na musamman” dubanta yayi shima yana murmushi
“Kinsan hausawa sukace da zafi zafi akan bugi qarfe,kuma kowacce magana akwai muhallin daya dace ayita” kai ta jinjina kawai tana kau da kanta gefe,sai takejin kamar wata qusa ya kafa mata.
Tans jinsu suna magana jifa jifa da azeez din har suka qaraso gidan,wanda babu kowa ciki sai fulani adama da fafur ya qirqiri ciwon qarya,saboda baqinciki da bacin rai mai martaban da kanshi ya tako zuwa bikin,saboda tsantsar soyayya d kulawar da yakewa azeez din kenan?.Sosai ta ware idanunta da sukayi nauyi tana kallon qasar datayi shekara guda cif ba tare data rayu a ciki ba,ta cikin motar take bin ko ina da kallo,motar da take ciki ita qwal daya,daga ita sai wannan matar da taji an kira da ladingo,tun sanda suka sauko daga jirgi ba zata iya cewa ga inda su mama sodangi da rakiya sukayi ba,ta lura da haka,amma batace komai ba,hakanan bata buda baki da niyyar tambaya ba,wataqila yana cikin tsarinsu,wataqila dukka cikin irin nasu adalcin kenan.
Kamar wadda ta warke daga makanta haka ta dinga bin qofar gidan nasu da kallo,gidan da shigarta daya kwanakinta biyu tal a ciki,gidan da take da tabbacin kowanne irin daukan hankali xaiyi an samar dashi ne bisa cinikin mutuncinta da akayi
“Mun iso” muryar driver dake gaban motar ta ratsa dodon kunnenta,ba tare data waiwaya ta dubi kowa cikinsu,ko tabi takan kayanta dake cikin motar ba ta,ta sanya hannunta ta bude motar ta xura qafafunta tafito.
Duk da cewa dare ne,duk da cewa bata gama sanin kan gidan nasu ba,amma hakan bai hanata gane qofar shiga gidan ba,ta tura ta cikin qarfin hali ta bude ta kutsa kanta ciki.
Bata manta hanyar falon nasu ba don haka taci gaba da kutsa kai,bata dakata ba sai data isa qofar shiga falon,sai a sannan taji duk wani rauni nata ya dawo,sai a sannan fargabar yadda zata tadda ‘yan uwanta ya fado mata,sai a sannan fargaba da tsoron irin rayuwar da zata gudanar ta dawo mata,ta sanya hannunta kamar wadda zata kama maciji ko qadangare ta yaye labulen nasu.
Hannatu tasoma hangowa zaune cikin falon qasan tiles din dake malale a falon,gefanta umaima ce da amina,hajara na kwance saman cinyar hannatun,da alamu kallo suke,don basu lura da labulen da aka daga ba.
Daga gefe saman kujera kuma wata matace zaune,itama.kallon take,a qalla zata doshi shekara talatin da takwas,qafarta daya saman daya,lokaci lokaci tana latsa wayar dake riqe a hannunta.
Wasu hawaye taji masu dumi sun ciko mata idanu,ko yaya suka rayu tsahon lokacin?,ko yaya sukaji lokacin da babu ita?,ko yaya rayuwa ta kasance musu?.
“Ta ina ake shiga?” Taji an fada daga bayanta,data waiwaya sai taga ladingo ce janye da akwatunanta,maida idanunta tayi cikin falon,ta qara taku ta saka qafafunta a ciki,bakinta dauke da sallama wadda take fitowa da qyar.
Dukkaninsu kamar an jona musu schoking suka daga kansu kusan lokaci guda,hakanan miqewarsu cikin tsananin mamaki wanda lokaci qanqani ya juye zuwa zallar farinciki,kana suka fara rige rigen isowa gareta,duqawa tayi a gabansu ta hadesu gaba daya zuwa jikinta,suka saki kuka kusan lokaci daya.
“Meye haka lafiya?” Matar dake zaune saman kujerar ta miqe tana tambaya gami da binsu da kallo,fuskarta akwai alamun rashin sanin wacece bilkisun,babu wanda ya iya tanka mata a cikinsu saboda kukan da sukeyi,ladingo ce ga dubeta ta soma gaidata,ta amsa tana son jin qarin bayani,kafin suce komai umma katti ta shigo falon
“Ke hannatu,kukan me kukeyi haka?,kuda waye kuma?” Cak ta tsaya ganin bilkisu duqe a gabansu,ta waro ido tana cewa
“Mai gado?,saukar yaushe?,yaushe kika zo?” Kai kawai ta daga ta kalli umma kattin,sai taga ta sauya sosai,ba kamar lokacin data barsu ba,maganar ladingo ce tayi kutse cikin tambayoyin da take jerowa bilkisun
“Ko xamu samu damar ganin mai gidan?” Tace da umma katti,don ta fuskanci kamar ita tafi wayewa da gidan akan wadda ta taras a falon.
Duban ladingo tayi ta gyada kai
“Eh bari ayi masa magana” daga haka ta juya zuwa wata qofa,tana tafe tana waiwayowa tana sake duban bilkisun harta shige.
A falonsa ta sameshi yana zaune yana zuba lomar tuwon shinkafar da ladi tayi da take girkinta ne umma kattin tashiga,har ladin ta daga kai xatayi masifa sai kuma saqon datazo dashi ya sanyata yin shuru
“Kazo ga maigado ta dawo” hakanan yaji wani faduwar gaba ta saukar masa,taste din abincin ya canza masa
“Na shiga uku,tofa” ya furta a sarari kuma a hankali,itadai umma kattin gaba tayi takoma zuwa falon don ta kashe qwarqwatar idanunta,taga meye zai faru,cikin yatsina fuska ladi tace
“Wai dama da gaske shekara dayar zatayi su dawo da ita?” Waiwayawa yayi.ya dubeta ba tare daya gane ma’anar tambayar tata ba,sannan ya miqe kawai yana goge hannunsa ya dauki hularsa dake gefe yadurfafi falon.
Yana shiga sautin kukansu yasoma sauka a kunnensa,saiya hada rai ya tsaya a kansu yana dubansu
“Wanne irin shashashanci ne wannan?,meye haka ke me gado?,ba zaku godewa Allah ba daya hada fuskokinku saiku xauna kuna kukan banxa dana wofi?” Janye jikinsu suka fara suna qoqarin tsaida kukan nasu,saidai ita bilkisun nata hawayen sunqi daina zuba.
Cikin girmamawa ladingo ta gaidashi sannan tasoma magana
“An umarceni dana danaganata da mahaifinta,kamar yadda akayi yarjejeniya bayan shekaru guda,to lokaci yayi,saboda haka gata nan kamar yadda fulani ta umarceni,shaidarta tana hannunta,dukkan abinda suka mallaka mata gasunan sun zama nata,tun daga lefe dukiyar aure dama komai da komai,hakanan sun bata dama,daga nan zuwa shekara guda duk abinda take da buqata a matsayin sallamarta ta qarshe ta fadi dukka adadin za’a bata….saidai fulani tace na tunasar daku yankewar alaqa ta har abada…..” Wani abu ya soki zuciyar bilkisun da har ta gaza daurewa ta dubi ladingo,duban da yasa bata iya qarashe bayaninta ba,har abada kuma komai lalacewa ubanta ubanta ne,wato xallar rashin adalci,wulaqanci da kuma qarfa qarfan har yakai matakin da za’a dinga aikama mahaifinta gargadi ta hanyar ‘yar aike kuma baiwa?,duk da cewa shiya siyama kansa koma meye,amma abun yasoma yiwa kunnuwanta muni.
Tsam ta miqe tana riqe da hannun aminatu da umaima,qasa qasa tace
“Kaini dakinku” da saurinsu sukayi gaba tana biye dasu,har zuwa dakin data zauna wancan karon lokacin da ake yinin bikinta,shine babu abinda ya sauya a ciki,saidai atsaftace yake hakanan komai yana shirye bisa tsari da doka,tasan za’a rina,dama bata taba tsammatar qazanta daga wajensu ba,saboda ta yadda da irin hoton data yi musu ma zallar tsafta da nutsuwa,saita qarasa zubewa anan tana sakin wani sabon kukan suna tayata,don suma bai ishesu ba,hannatu ce kawai bata biyi bayansu ba,wanda bata lura ba,har sai zuwa lokacin da zuciyarta ta gaya mata kukan ya isa haka,don bashi da wanu magani,face sake sanya qannan nata da zaiyi suma cikin wata damuwar,dole ta yiwa kanta waigi,ta goge nata hawayen ta lallashesu,kana ta shiga bandakinsu ta daura alwala ko zataji sanyi cikin zuciyarta.
Tana fitowa daga bandakin hannatun na shigowa janye da akwatunanta,saita dauke kanta don ko ganin akwatunan su kansu batason yi takoma kusa da amintu ta zauna tana kallon yarinyar tana dan murmushi duk cikin qarfin hali,tadan qara girma da wayo sabanin sanda ta tafi.
Hannatu ce ta qaraso ta dora mata wani abu dake nannade saman cinyarta tare da qaramar jakarta,saita kalli abun da alamun tambaya
“Kudinki ne da suka baki daga can,matar da kuka shigo tare ta baiwa baba,yace nakine bazai karba ba,baba ladi nata qoqarin sanyashi ya karba har tana yunqurin amsa nina karbo….karkiqi amsa don Allah yaaya,haqqinki ne,nakine bana wani ba,wanda akaci a baya ya isa,Allah ya amfana,idan ma kikace ba zaki karba ba babu abinda zai sauya,su zasu amsa su kuma murqushesu suci gaba da rayuwarsu ba tare da komai ya faru ba” idanunta taf da qwallar data samu ta tsayar take duban hannatun,tun daga yanayin jiki da kalamanta sun nuna hannatun bata da bace,hankali ya soma gameta,ba shakka ta sauya qwarai,ko nauyin daya hau wuyanta bayan tata tafiyar ne yasa hankalin yayi hanzarin zuwa mata haka lokaci guda?duk da dama tazarar shekara biyu rak ta bata,roqon datayi mata da qoqarin amso saqon da tayi tun daga falon,idan tace ba zata karba ba kamar ta watsa mata qasa a ido ne,don haka cikin hikima tace da ita
“Ganinsu ne banason yi hannatu” da sauri ta daukesu daga kan cinyarta
“Bazan takura miki ba yaaya,amma zanta ajjiye miki su har sanda kike da buqatarsu” ta qarashe maganar tana miqewa zuwa cupboard dinsu ta bude can sama ma’ajiyar kayanta ta cusa su sosai.
sai a sannan ta soma duban dakin loko da saqo,karon farko hauwa’u ta fado mata
“Ina kulu ta,ita kadai ce ban gani ba?” Ta ai qarshen tambayar tana maida idanunta ga hannatu,sai taga yanayin fuskarta ya sauya sanda take dawowa mazauninta data tashi,jin bata amsa mata ba saita sake duban sauran,suma dai kamar hannatun kowa fuskarsa ta nuna zallar damuwa,gabanta yayi mummunar faduwa,zuciyarta ta qiyasta mata wani mummunan abun ya samu hauwa’un suka boye basu gaya mata ba,cikin rawar murya tace da hannatu
“Hannatu,meya sameta baku gayamin ba?” Kai ta girgiza tana duban bilkisu
“Yan uwan mamanta sunxo sun tafi da ita”
“Ya Allahu” ta fada tana dafe kanta,wataqila rabuwarsu da hauwa’u kenan har abada taxo?,yan uwan mamanta?,yan uwan maman nata da sai afi shekara biyar ba’asan inda suke ba?
“Yaaya,hauwau na kuka tana cewa ba zata bisu ba sai yaaya maigado ta dawo,sai kin dawo kin sata a makaranta yadda kika ce,saikin dawo ta ganki amma haka suka dauketa,sunyi dauki ba dadi da baba,amma suka nuna mishi halinsu na fulani,saboda da zafinsu da shirinsu sukazo,tana kuka muna kuka haka suka jata suka tafi,kiran sunanki kawai take,munfi sati bama iya cin abinci,munfi sati muna mafarkinta,daga qarshe dole muka haqura saboda babu yadda zamuyi,amma kullum sai munyi zancanta,har yau muna kewarta,ko da kika ganmu xaune a falo ma zancanta muka gamayi kenan,sai gaki kin shigo”.
Wani sabon tashin hankalin taji ya rufto mata,ji take kamar jininta ya hau,hauwa’unta,yarinyar da duk cikin qannenta taficin buri akan tazo ta ganta,saboda tasan tafi kowa qulafucinta,kukan dai da bataso tayi shiya sake dawo mata,don bata da wata hanya ta huce takaicinta da baqinciki idan ba kukan ba.
***** ***** ****** *****
Tun a mexico ammi fulani aisha ta shirya masa walima ta musamman,wanda tasamu halartar familynshi na kusa sosai,musamman dangin mamamshi daga mali,har safwa ma wannan karon sai data zo,da tarin kyaututtukanta na murnar tayashi karatunsa,wanda ita saura shekara guda ta rage mata ta kammala nata karatun,walima me kyau da qayatarwa akayi,kusan kwanakin duka cikin sabga yake,sai washegarin randa aka kammala walimar sannan yasamu huta,ya kulle kanshi a daki ya kashe dukka wayoyinshi.
Saidai tun baccin baiyi nisa ba yasoma mafarkai,hakan ya tilasta masa tashi,yayi addu’a ya gyara kwanciyarsa,saidai baccin ya gaza sake samuwa kwata kwata,haka dole yanaji yana gani yaci gaba da juyo saman gadon,daga qarshe ma wanka yayi yasake ficewa,duk da hutun da yake da buqata.
****** ***** ***** *****
Tana zaune daga gefan gadon hauwa’u wanda a yanzu ya zama nata tun bayan dawowarta gidan,saboda taqi nata dakin kamar dai wancan karon,sanye take da rigar bacci doguwa mai dan kauri,sai wani qaramin dan kwali data rufe kanta dashi.
Misalin bakwai da rabi ne na safe,dukka yaran na zaune a gabanta sanye da unifoarm suna karyawa,wanda ruwan tea ne da bread,zata iya cewa a yadda tasan rayuwar gidansu a da,yaran sun samu ‘yanci da sauyi kaso sittin cikin dari maimakon daa,a yanzu akwai abinci a gidan dai dai gwargwado,safe rana da dare,babu zaman yunwa,hakanan baban nasu ya qoqarta sakasu a makarantar boko mai sauqin kudi,dama already ta barsu suna zuwa islamiyya,kuma basu fasa zuwa ba har kawo yau,basa yawo cikin tsumma kamar yadda sukeyi a baya,saidai kuma kusan babu mai kulawa da rayuwarsu,ba’a tsangwamesu ba tsangwama mai yawa kamar baya ba,hakanan babu mai tattalinsu kamar yadda suke dai a baya,umma katti ta kama yaranta sune a gabanta yadda dai rayuwar take a baya,mama ladi da amaryar da bilkisun tazo ta taras ya rangado wadda taji suna kira da anty sukam ta mijinsu suke ko ince ta kansu,domin a zahiri kowacce na nuna mishi tattali ne,yayin da kuma a badini kowaccen kanta da rayuwarta take qoqarin ginawa,suna hangen dan abun hannun malam bilyan,sannan kuma suna hasashe da lissafin basu haihu dashi ba,basu da kowa dashi,to ba shakka idan ta tashi barewa dasu zata bare.
Tana zaune tana dubansu suna ‘yan hayaniyarsu har suka gama,hannatu ta kada kansu don wucewa makaranta,ta laluba jakarta don basu dan abun kashewa saidai babu komai a ciki,saita buraci inama ace tana da wani abu da zata basun dazai sake yawan farincikinsu,hakanan ta musu fatan dawowa lafiya suka amsa cikin cikin walwala suka fice,don wannan rayuwar da suke ciki gani suke sun samu dukkan komai,tunda basu saba irinta ba,a baya sun rayu babi ci sha suttura ko muhalli mai kyau daga mahaifinsu,a yanzu kuwa dukka sun samu,don haka a nasu ganin basu rasa komai ba.