SIRADIN RAYUWA CHAPTER 11
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Sannu a hankali ta soma qoqarin bude idanuwanta da sukayi mata wani irin nauyi,a qalla ta dauki kusan minti daya tana wannan fafutukar sannan tasamu ta budesu tana warasu dakyau don su daina ganin dishi dishi,cikin ikon Allah ganinta ya daidaita,saita sake ware idanun nata tana kallon dakin da take ciki.
Da fari bai mata kama da dakin asibiti ba,sai data lura da wasu abubuwa da suke kamanceceniya dana asibiti sannan ta tabbatar tana cikin dakin asibiti ne.
Babu kowa cikin dakin,sai fanka da ac da suke aikinsu cikin madaidaitan sanyin da bazai takura ka koya hanaka sukuni ba.
Kallonta tayi qoqarin maidawa bakin qofa sanda taji an turo qofar,anty zuhriyya ce karo na biyu,qara saurinta tayi don ta iso gareta,fuskarta washe da fara’a sosai tana duban bilkisu,bata tsaya ko ina ba sai kujerar dake gaban gadon,wanda dama ita ta tashi daga kai,ta sanya hannunta ta kamo hannun bilkisu guda daya,murmushi da hawaye na qwace mata lokaci daya
“Yanzu ina ne yake miki ciwo?,mene ne yake damunki?”
“Babu komai anty” ta fada itama sabon hawaye yana balle mata,hannu tasa ta fara share mata tana cewa
“Daga yau ba zaki sake kukan baqinciki ba daughter tunda gani….bari naje na kira likita ya sake dubaki” kai ta gyada mata tana binta da kallo.
Tana dab da fita aka turo qofar dakin,babanta ne sanye da shadda da babbar riga,ya sake kutso kai dakin yana ta raba ido,murtuk anty zuhriyya ta hade fuskarta tsaf,maimakon ta fita saita fasa ta dawo cikin dakin.
Ko kallon malam bilyamin batayi ba harya shigo dakin,ya qaraso gaban gadon bilkisu yana yi mata sannu
“Me ya sameki mai gado?” Ya tambaya yana dubanta,kai ta kada
“Nima ban sani ba abba,kawai naji jiri ne saina fadi”
“Ashsha…Allah ya sawwaqe” ya fada yana maida dubanshi kan zuhriyya,tun ba yau ba yasan wacece zuhuriyyan,kuma kwanwarsu bata jiquwa sam
“Saukar yaushe?,ashe kin dawo” ya fada,batako dubeshi ba illa
“Eh” data fada albarkacin bilkisu dake wajen.
Turo qofar dakin da aka sakeyi ne ya katse shurun da yaso wanzuwa a dakin,mijin anty zuhriyya ne da suke kira da abbaaa shida yaransu gaba daua,wanda kafin ta tafin mutum biyu bilkisu ta sani,najwa da ateeq,yanzun kuwa sun zama su uku,an samu qaruwar da namiji haisam,su kansu su biyun data sani dukka sunyi wayau qwarai qwrai,kada ma najwa da take ‘yar budurwar taji labari,tana da tsaho wanda da alama tsahon babanta ta dauko.
Babansun na dauke da haisam,najwa da ateeq suna dauke da kwanukan abinci a kwanduna,bude hannunta tayi tana musu oyoyo,yayin da abbaaa ya tsaya gaisawa da malam.bilya,wanda babu jimawa yayi musu sallama ya wuce ganin kamar sun ma manta da wanzuwarsa a dakin.
Ranar kusan wuni sukayi tare,anty zuhriyya sai nan nan take da ita,abbaa mutum ne mai sauqin kai da jan mutane a jiki,bare bilkisun da take kamar diya a wajensa,dukkan yaran kansu sun sake da ita,musamman najwa ita tafi saurin tunota,ateeq sai a hankali a hankali ya dinga tunawa yana kuma sakewa,haisam kam dama sarkin qiwa ne yana kwance jikin mamarshi.
Ko da likita yazo ya dubata sai yace ko zuwa gobe ma zai iya sallamarsu,tunda babu wani abu dake damunta kuma,saidai sallamar washegari bata samu din ba,saboda a daren wani irin zazzabi ne mai azabar zafi ya rufeta,sosai hankalin anty zuhriyya ya tashi,ta kasa runtsawa itama daren gaba daya,sai gab da asuba aka samu ya sauka,bacci kuma ya dauketa.
Kwana biyu kenan tana fama da nataccen zazzabin,abinda ya hana sallamar kenan,sai a kwana na uku ne aka samu ta kwana lpy,washegari da safe kuwa ta tashi da dan qwarin jikinta,hakan ya yiwa anty zuhriyya dadi,da wuri ta sanyata tayi wanka,ta bare mata daya daga cikin sabbin kayan da tun tana kwance tahau siya mata,duk da tayi mamakin kyawawan sitturun data gani a jikinta,ta bata daya daga cikin wanda ta siyo mata ta shirya,tsaf kuwa tafito,ta hada mata tea da chips ta miqa mata tana dubanta
“Yau dai babu sauran ciwo,maza ki cinye wannan tas” murmushi bikisun tayi har fararen haqoranya na bayyana,hakan ya sanya anty zuhriyyan dan zuba mata idanu,saboda yadda kamarta da yayarta maimunatu ta fito sosai,sai taja kujera ta zauna a gabanta tana dubanta sanda take cin abincin,cikinsu babu wanda yace komai sai kallon juna da sukeyi lokaci zuwa lokaci,dakin babu kowa saisu biyun,don tunda safe da abbaa yazo da yaran ya kawo musu breakfast suka koma tare,dama ko sau daya basu yarda sun zauna tare da ita a asibitin ba,sunfi sabawa da abbaansu shi yasa suke maqale dashi,don haka ta barsu tare tunda akwai mai aikinsu a gidan dake kula dasu.
Sai data ci fin rabi sannan ta aje tana cewa
“Na qoshi anty” murmushi ta saki
“To ma sha Allah”
“Bilkisu….jikina ya bani cewa,bayan tafiyata,abubuwa da dama basu tafi dai dai yadda na tsara ko kuma yadda suka kamata ba,duk da nazo na tadda wasu sauye sauye,amma hakan bai kwantar min da hankalina ba….saura shekara biyu mu dawo amma naji dukka hankalina ya karkata nazo na ganki naga halin da kike ciki,ko bacci cikakke bana iyayi ba tare da nayi mafarkinki ba….sanar dani meke faruwa daughter ko kuma meya faru bayan bani nan”
Daga yanayin yadda fuskarta ta sauya tun kafin ta furta komai ya tabbatar mata da akwai gagarumar matsala,kawai kima abinda ya faru mai girma da rayuwarta.
Kasa cewa komai bilkisun tayi sai wani zazzafan kuka daya subuce mata,batasan cewa a baya kuka tayi mara ‘yanci ba sai yanzu,sai a wannan lokacin data samu kafadar da zata kwantar da kanta ta fidda duk wani zafi da radadi dake mintsinar zuciyarta,wasu irin hawaye masu dumi suka dinga kwaranya daga kuncinta,wanda ta tabbatar duminsu tun daga zuciyarta yake.
Shuru kawai anty zuhriyya tayi tana bubbuga bayan bilkisun ba tare data hanata kokawa ba,kuma ba tare data ce mata komai ba,zuciyarta cike fal da tsoro da taraddadin abinda kunnuwanta zasuji daga bakin bilkisun,babu abinda zuciyarta bata qiyasta mata ba,bata tsaida ita ba har zuwa wani lokaci da kukan yaja baya,ta miqe da kantabta bata ruwa mai maidaidaicin sanyi dake cikin fridge din dakin,tasha shi kuwa mai dama,sannan ta aje tana maida ajiyar zuciya.
Tiryan tiryan ta soma bawa anty zuhriyya labarin komai,babu abunda ta boye mata har zuwa ranar da antyn ta sanya qafarta a falon gidansu.
Tamkar wadda ta hadiyi tabarya haka ta kasa zama,idanunta tuni suka rine saboda kukan data dinga yi tun farkon labarin,har zuwa lokacin da hankalinta yayi mummunan tashi sanda taji irin auren da malam bilyan ya yiwa bilkisu,diya qwaya daya tilo da ‘yar uwarta ta jini ta tafi tabar musu,duk maganar data kwaso saita subuce mata saboda tsabar masifa da tashin hankalin dake cinta,a irin wannam yanayin abbaa ya dawo kawo mata hisham.
Shi kansa hankalinsa ya daga da yanayin daya taddasu,kasa ce ma abbaan komai tayi,sai sanya kanta itama a kafadarsa da tayi ta rushe da kuka kamar yadda bilkisun itama ke kukan,saboda labarin ya zame mata tamkar fami ne a ranta
“Bazan qyalesu ba abbaa,bazan rabu dasu ba,dukkansu kowa saiya dandana,kowa saiya debi sakamakon abinda ya aikata,har masarautar kaisan bazan qyaleta ba,koda dukkan abinda na mallaka zai qare sai nayi shari’a dasu” abinda take fada kenan,shidai baice komai ba face lallashinta da yake,yana rarrashin bilkisu kuma da baki,daga qarshe har bilkisun da share hawayenta amma kukan anty zuhuriyyan yaqi tsaiwa,daga qarshe janyeta yayi suka fice daga dakin.
Basu dawo ba sai bayan mintuna wajen arba’in,tsakanin miji da mata sai Allah,sanda suka dawo kukan ya tsaya,saidai fuskar nan tata a dinke take tsaf,bayansu likitane suka shigo tare dashi,yakuma dudduba bilkisu ta tabbatar masa batajin wani ciwo sannan ya rubuta mata sallama.
Cikin motar abbaan ma kusan shirune yayi musu rakiya,kowanne a cikinsu sai sauke ajiyar zuciya yake,bilkisu bata fuskanci inda suka nufa ba saida anty zuhriyya ta masa maganar titin da zaibi,wanda babu tantama titin gidansu ne
“Yanzu zuhriyya ba zaki bari ba zuwa gobe?” Ranta tasake batawa sosai tana dubanshi
“Abbaa,na riga dana maka bayanin komai,na rantse ko awa guda dukkan abinda ta mallaka bazai qara ba cikin gidan,kayi haquri bawai naqi bin umarninka bane,amma ta gama zama qarqashinsu har abada,koda bana raye na tabbatar dangina idan suka samu labarin komai ba zasu barta a qasar nan ba” shima bai sake cewa komai ba,saiya sauya akalar motar zuwa inda take kwatanta masa din.
Mintuna kadan suka isa qofar gidan nasu,ita da anty zuhriyyan ne suka fito,abbaa na xaune cikin motar suka shige ciki.
Tayi sallama saidai ciki cikin yadda ba kowa bane zaiji,anty ce zaune a falon ita da mama ladi,irin zaman da saikace dole aka musu,don kowacce tata ce ta zaunar da ita,don kusan rabin xaman kishi ne ke kawoshi,bata kalli kowacce cikinsu ba fuskarta kamar hadari tace da bilkisu
“Ki shiga ki tattaro duk abinda kikasan kina da buqatarsa kuma nakine kizo mu wuce” kai bilkisun ta gyada mata cike da taraddin anya idan mahaifinta yaji wannan zai yarda?,zata iya tuna kadan daga cikin dauki ba dadin da akayi tun tana mitsitsiyarta kan za’a dauketa ya hana,baya ga haka da wayonta ma ansha gwagwarmaya da duk wadanda suka zo daukan dansu da suka haifa cikin gidan,amma duk da haka bata tanka ba ta wuce ciki,saidai wani bari na zuciyarta ‘yan uwanta ne maqale a ranta.
“Waike wacece da zaki dinga shigowa mutane gida haka kai tsaye?,sannan kuma ki tsaya kina baiwa yarinyar mutane umarnin ta hada kayanta ku tafi,kuje ina?” Cewar mama ladi data miqe cikin son nuna ita din wata abace.
Wani mummunan kallo daya baiwa mama ladi mamaki ta jefeta dashi,qoqarin tausar zuciyarta take don kada ta kai mata mari,da qyar ta ragewa kalamanta zafi sannan tace
“Kije ki tambayi wanda ya ajeki wacece ni,sannan koshi din a yau bai isa ba yayi kadan ya hanani tafiya da bilkisu,idan kuma kuna musu bismillah” jin kalamanta ya bata mamaki,saita juya cikin rawar jiki tayi dakunan malam don ta kirashi.
Ba’a jima ba sai gasu tare yana qoqarin sanya hularshi aka,da alama tasowar gaggawa yayi
“Lafiya zuhriyya?” Shima din sai data soma watsa masa banzan kallo,tanajin kamar taje ta shaqeshi,banda maganganun da sukayi da abbaa da kuma yadda takejin kanta a yau ba shakka daga malam.bilyan har tarkacen matansa yau babu wanda xai tsira gurinta
“Au dataje ta taso ka bata gaya maka dalilin zuwa na ba?” Isowa yayi sosai tsakiyar falon
“Ta gayamin,kuma kinsan babu wannan maganar tun shekarun baya bare yanzu,bilkisu tana gidan ubanta,kuma nan ne ya dace taci gaba da zama kamar sauran ‘yan uwanta” wani tururi taji zuciyarta zuwa fuskarta sunayi,saita gyara tsaiwa sosai yadda zataji dadin fidda kalaman bakinta da suka cika qirjinta,dama neman rage wasu daga ciki takeyi
“Wanne uban?,ina uban yake?” Ta maimaita tambayarta tana kallon hagu da damarta alamun nemansa take,sai data gama waige waigenta sannan ta dawo da dubanta kanshi
“Wai kai ne?,to indai kanka kake kira da sunan uba ba shakka ka cuci iyayen qwarai,kuma kayi gaggawar cire kanka daga wannan sahun,don baka da wani abu daya da zaka iya bugar qirji dashi wanda zai sanya ka samun matsayin shiga sahun iyaye,sam halayya mu’amala da dabi’unka bana iyaye bane,kafi kama da wanda baisan ciwon haihuwa ba saboda bai taba yi ba,hakanan kafi kama da d’an kama karya kuma azzalumin uba,uban da baisan komai na diyoyin daya haifa ba,uban daya gwammace ya saida ‘yanci da mutuncin yarsa sabida abun duniya fararre qararre,uban daya baiwa zalunci sunan adalci,uban dake tarwatsa rayuwar ‘ya’yansa da hannunsa….tir da wannan uban daya manta cewa akwai hisabi tsakanin iyaye da ‘ya’ya,ya manta da hadisin da yace dukkaninku masu kiwo ne,kuma za’a tambayesu game da abinda aka basu kiwo,ya manta da zai tsaya gaban zatin Allah ya fadi yadda ya riqe ya kuma tarbiyyanci yaran da aka bashi,bana shakka bilyamin akwai tsantsar jahilcin ilimin addini bisa kanka,wanda hakan ya sanya tun karon farko da ‘yar uwata ta zabeshi xabin tumun dare tayi,ba shakka mummunar qaddara mai qarfi ya sanya ‘yaruwata saliha baiwar Allah,wadda bata zalunci ta hadu dakai harka shiga qaddararta ta hada zuri’a dakai,saidai duk hakan mu a matsayinmu na musulmai munsan cewa haka Allah ya qaddara”
“Hakanan barin bilkisu da nayi a baya babban kuskure na tafka,amma shima nasan cewa qaddarar saika aikata mata zaluncin daka yine,saidai a yanzu ina mai farincikin shaida maka,ka bude dukkanin kunnuwanka kaji,ni zuhiryya,indai an haifeni da jini kuma halastacciyar ‘ya ce,bilkisu tabar gidanka da sunan zama har abada,ina kuma mai jaddada maka cewa a yau,koda sama da qasa zasu hade,koda zan rasa lafiyata ko numfashina bazan fita daga gidan nan ba sai tare da bilkisu” sosai maganganunta suka tsumashi da kyau,saidai yaji kunyar yadda ta gaggaya masa maganganu gaban matanshi da yake cikawa baki,wanda tunda suka san juna da zuhriyyan duk da babu jituwa tsakaninsu amma bata taba gaya masa maganganu irin haka ba masu zafi.
Bilkisu dake daki tare da qannenta data samesu zaune waje daya cike da alhini suka ruqunqumeta cike da farincikin ganinta,don dama tun randa suka dawo basu sameta ba suka cika da zulumin inda taje,suka soma tunanin kodai ta sake tafiya ta barsu ne?,jin muryoyin mahaifinta dana anty zuhriyya ya sanyata fitowa,dukka yaran suka biyo bayanta.
Fitowarta taja hankalin anty zuhriyyan,ta dubeta da idanunta da suka sake birkicewa da bacin rai
“Waima kayan da zaki dauka ba daga azzaluman masarautar can kika samesu ba?” Kai ta gyada mata,cikin daga murya tace
“Bana buqatar ki dauki koda tsinke wanda ya fito daga hannunsu,ki tattarawa ki barwa masu zalama da son zuciya su qara kan yanke talaucin da suka basu,iya gyambon ma da suka barwa zukatanmu ya isa,wuce muje” a sanyaye bilkisun ke takowa zuwa qofar fita,tausayin ‘yan uwanta yana ratsata,tana son cewa wani abu amma tasan yanzun ba qadamin yin magana bane.
“Ke mai gado,karki kuskura fa ki fita” ya fada yana takowa,sai anty zuhriyya ta tsaya,ta waiwayo tana dubansa
“Kar kayi gaggawar kai kanka mana gidan yari tun lokacin shari’armu baiyi ba,ka bari har sai zuwa sanda na makaka a kotu kaida masarautar kaisa tukunna” daga haka taja hannun bilkisu suka fice.
Tana iya hango qannanen nata dakuma jiyo muryoyin kukansu,da alama baban nasu ke korasu ciki suna son ganin ‘yar uwarsu,hakan ya sanya ta fashewa da wani sabon kukan
“Kada ki damu,za’a kula dasu,tunda suma ‘ya’ya ne kamar yadda kike ‘ya,na miki alqawarin bazan qyalesu rayuwarsu ta tagayyara ba,zan basu dukkan wata gudunmawa da zata iya sanyasu kasancewa cikin farinciki saboda albarkacinki” anty zuhriyyan ta fada a tausashe,kai bilkisu take kadawa,tanason buda baki tayi mata godiya amma ta hanata,tadai buqaceta kawai data tsaida kukanta,tayi qoqarin yin hakan.
Sauke ajiyar zuciya sosai anty zuhriyya tayi tana sake rungume hisham daya soma bacci a qirjinta tana tsara yadda zata tafi da komai,abbaaa yayi murmushi
“Yaudai burin zuhra na shekara da shekaru sun cika” ya fada cikin salon tsokana,murmushinta jefeshi dashi kawai,don yau bata da bakin rama tsokanarshi,abinda aka yiwa bilkisun ke mata ciwo sosai a rai,tabbas ba zata bari ba,ba zata qyale ba kamar yadda taci alwashi……
A falo suka tadda najwa ateeq da mai aikin anty zuhriyya suna kallo,dukkansu suka taso suna rige rigen yi mata sannu da zuwa,ta amsa na mai aikin tana miqa mata hisham
“Jeki kwantar dashi a dakinsu,ki taho min da muqullan dakunan nan”
“To anty” ta fada cikin girmamawa tana daukar hisham daga kafadarta sannan ta wuce ciki.
Waiwayowa anty zuhriyya tayi tana duban bilkisu
“Dauhgter….ya haka,a gidanku fa kike” ta fada ganin yadda take tsaye tunda suka shigo,murmushi bilkisu tayi kana ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana dan qarewa falon kallo,wannan ba shine gidan anty zuhriyya data sani ba kafin suyi tafiya,wannan yafi wancan kyau da tsari,da alama sun sauya gida ne kafin dawowarsu,kuma wannan din na nuna cewa sabon gida ne kuma sabon gini ne,haka nan duk kayan dake cikinsa da alama sabbi ne.
Babu jimawa ta dawo da muqullan,anty zuhriyya ta karba tacewa bilkisu ta taso suje,miqewa tayi ta bita a baya tana sake duban hanyar da suke bi.
Wani corridor suka shiga,wanda ke dauke da dakuna guda hudu,bibbiyu suna kallon juna,sai babban window daga can qarshen corridor din,daya daga cikin dakunan ta bude ta shiga bilkisu na biye da ita.
Babban dakine wanda ke dauke da gado two bedside drower wardrobe sai kuma madubi,malale dakin yake da tiles kalar kayan gadon,sai wata qofa dake rufe cikin dakin wanda babu tantama bandaki ne.
Gefan gadon anty zuhriyya ta nuna mata,ta isa a hankali ta zauna,juyawa tayi ta soma qwalawa mai aikin nata kira,nan da nan ta qaraso
“Ina sabbin curtains din nan da aka kawo?”
“Suna inda kika ce na ajiye miki”
“Oya maza debosu kizo ki tayani sakawa”. To tace sannan ta juya ta fita,babu jimawa ta dawo dasu a hannunta,karba tayi tana nuna mata toilet
“Shiga ki dubashi da kyau ki wankeshi fes da Allah haula”
“To anty” ta sake cewa tana nufar bandakin.
Bilkisu dai na zaune antyn tasoma sanya labulayen da kanta,taso tayata amma ta dakatar da ita
“Kin manta daga gadon asibiti kike?,hutu yanzu shine abinda yafi dacewa dake” tana ji tana gani ta zauna ta barta da aikin,tana aikin tana janta da hira,tun bata sakewa harta soma sakin jiki tana bata amsa,wani abun kuma kawai tayi dariya,don har yanzu qannenta na maqale a ranta,tana tunanin halin data barsu.
Cikin qasa da awa guda dakin ya koma cikakken daki,haule ta qarasa gyarashi tas,tasa aka dauko spare plasma da sauran kayan kallo aka maqala,tunda dama already akwai gurbin sanyasu a dakin,sanyawar ne kawai ba’ayi ba,wala’alla saboda ba’a buqatar dakin babu mai zama a ciki.
Agogo anty zuhriyyan ta kalla
“Yanzu ki kwanta ki huta sosai,idan lokacin sallah yayi zan tasheki kiyi sallah” kai ta gyada mata,cikin sassanyar muryarta tace
“Na gode anty”
“Shshshsh!!,banason ki sake cewa komai,idan ba haka ba zanci qaniyarki,don na miki abu shine zaki godemin?” Murmushi ne ya subuce mata,itama saita sakar mata murmushin kana ta juya ta fice daga dakin tana sakin ajiyar zuciya.
Sai yanzu tadan samu nutsuwa kadan data soma yin abinda ya kamata akan bilkisun,saidai tana jin cikin wajiban da suka hau kanta batayi komai ba,so take ta taba rayuwar bilkisu sosai,ta goge duk wani bacin rai qunci da tabo data taba fuskanta,duk da tasan cewa duk.yadda kakai gason goge wani tabi a rayuwar mutum,yakan iya tafiya amma lallai zai bar maka burbushinsa,walau a zuciyarka ko rayuwarka.
Duk da taso tayi baccin amma hakan ya gagara,saboda tunane tunanen da suka cika mata qwaqwalwa,lissafe lissafe na rayuwa,kusan haka dai ta cinye lokacin da anty zuhriyyan ta dibar mata ba tare data iya runtsawa ba.
Sanda antyn ta shigi fes da ita,da alama tayi wanka ta canza kayan jikinta,baki ta kama
“Daughter,kada dai kicemin bakiyi baccin ba” murmushi kawai tayi
“Baccinne baizo ba”
“Ki tashi kiyi sallah to,saiki fito falo muci abincin rana”
“Toh” tace tana saukowa,ta shige bandakin ita kuma ta fita.
Dukkansu ta samesu saman dining,da alama ita kadai ake jira,cikinsu ta shige itama amma ta kasa sakewa saboda abbaa dake wajen,hakanan ta tsakuri abincin ta miqe,antyn ta karanceta,hakan ya sanya ta saka haule ta bita da wani daki.
Ranar gaba daya kusan wuni sukayi tare da ita,basu bata wata dama da zata kebe ba bare wani tunani ya dameta,saidai duk da haka lokaci lokaci qannenta suna fadowa a ranta.
Da daddare bayan tayi wanka tana shirin kwanciya anty zuhiryya ta shigo dakin dauke da leda,already ta riga data saba da yin wanka kafin ta kwanta tun xamanta a mexico
“Ga kayan bacci nan,da kuma wasu kala biyu spare,sai zuwa jibi idan kin huta sosai idan Allah ya kaimu zamu fita inyi miki siyayya,ki rubuta duk abinda kike buqata ki ajjiye,idan ba so kike ranki kuma ya baci ba kada ki soma cewa zaki muna alkunya,ki sanya a ranki kamar yaaya maimuna ce tace ki rubuta duk abinda kikeso” murmushi dai still tayi mata kamar yadda ta saba,sannan tayi mata godiyar data nuna mata sam bata so.
Kwanakinta biyar a gidan basu fita ko nan da can ba,antyn natason haifar da sabuwar shaquwa tsakaninsu,tana ta son bilkisun ta sake suma yaran duka su sake da ita sosai yadda ta kamata,cikin kwanakin sosai bilkisu taga kulawa da tattali,kullum cikin ina ka saka ina ka aje anty zuhriyya keyi da ita,bata fita ko ina duk da cewa ranar data diro qasar daga filin jirgi sai gidan malam bilya,tana da buqatar zuwa wasu gurare amma dukka ta soke tace saita gama settling din komai.
A kwana na shida ne da yamma tasa ta shirya ita da yaran duka suka fita a motarta,ita ke driving bilkisu na zaune gefanta riqe da hisham wanda yasoma sakin jiki da ita,ateeq da najwa suna baya.
Sai da suka hau titi sosai sannan anty zuhriyya tace da ita
“Wanne abu kike ganin ya kamata a yiwa ‘yan uwanki?” Duban anty zuhriyya tayi da sauri sannan tadan kautar da idanunta,bata zaci maganar nan kusa haka da wurwuri ba,idan ason ranta ne,kuma daso samu ne kowacce ta koma gaban mahaifiyarta ta kula da ita,saidai hakan kuma zai iya zama naqasu ga burinta nasin kasancewa tare dasu da kuma cikar burikansu,don babu lallai a inda zasu koma din su samu ingantacciyar rayuwa,wala’alla iyayen nasu sun jima dayin aure,babu tabbacin kuma wanda suka aura din zai riqe musu yaran nasu,dole sai hannun kakanni,wadanda suma wasunsu suna ta kansu ne bare su dauki wahalar riqe jikoki.
Maganar anty zuhriyya ta katse mata tunaninta
“Inaga a nawa ganin,kawai mu kula da iliminsu su samu ingantaccen ilimi a makaranta mai nagarta,da sutturar sawarsu zuwa walwalarsu cikin gidan,inaga wannan shine abinda sukafi buqata” kai take gyadawa tanajin wani sanyin dadi a ranta,ba shakka wadan nan kusan sune jigon komai,kuma tana fatan idan suka samu haka ka’in da na’in komai mai sauqi ne.
Godiya sosai ta yiwa antyn duk da ta nuna bataso,amma bata fasa ba,sai albishir na biyu daya sake faranta ran bilkisun,har ya sanya fuskarta ta washe qwarai
“Abu na gaba da nake tunani shine,zan daukeki muje ethopia,asalin danginmu dukka suna nan,jinin abbanmu can ne tushenmu” nannauyar ajiyar zuciya ta saki,karon farko da zata taka cikin ahalinta na uwa,zataga dangin mahaifiyarta wadanda kusan zata iya cewa tun tashinta bata sansu ba sai a yanzu,farincikinta ya kasa boyuwa,wanda hakan ya sake farantawa anty zuhuriyya.
Daya daga cikin manyan shagunan saida sutturu da dukka kayan qyale qyale na mata suka sauka,kaya sosai anty zuhriyya ta dinga lodar mata kai kace idanunta a rufe yake,kamar kuma batasan ciwon kudin ba,sannan ta koma bangaren mayuka zuwa turaruka suma ta musu diba son ranta,hakanan mayafai gyalulluka zuwa takalma,sarqoqi da kayan makeup,sai data ji a karan kanta ta gamsu da siyayyar data yi sannan taje aka mata total ta biya,babu abinda ta siyawa yaranta don bata su take ba,burinta kawai ta maida bilkisun asalim bilkisunta.
Cikin satittika qalilan ta soma komawa hayyacinta,sati hudu kacal tayi wani irin kyau,ta cika sosai fiye da yadda anty zuhriyya ta tsammata,kai kanka idan ka ganta sai kayi mamaki,dukkansu sun alaqanta hakan da nutsuwa da kwanciyar hankali data fara samu,don tuni antyn ta fara maganar yadda zata zana neco da waec,tunda lokacin zanawa ya sake zagayowa,wato shekara iwar haka akayi mata karen tsayen da yaso kassara rayuwarta,ta wani bangaren kuma tana shirin yadda zata maka masarautar kaisa da malam bilya a kotu.
Da qyar abba yasha kanta,a wani dare bayan ta gabatar masa da abinci yaci,ta kwashe kwanukan ta gyara wajen tsaf,saita dawo inda yake
“Abban najwa…..nace idan babu wani ni zanje nayi wani aiki?” Saiya daga kanshi yana dubanta cikin mamaki
“Wanne aiki ummin najwa zatayi da zaisa ta barni ni kadai?” Saita gyara tsaiwarta tana fata ya fahimceta
“Kasan na fara tsara yadda zan shigar da qarar bilkisu da masarauta da kuma mahaifinta,to so nake cikin satin nan na kammala komai a soma shari’ar,banason abun ya dauki dogon lokaci” ajjiye takaddun dake hannunsa da yake dubawa yayi,sannan ya gyara zamanshi sosai,saiya nuna mata gefanshi
“Zoki zauna muyi wata magana” a hankali cikin sanyin jiki ta tako ta zauna a inda ya nuna mata,kiran sunanta yayi cikin sautin dake nuna zancan da zaiyi mai muhimmanci ne
“Inda zakiji shawarata zuhra da kin ajjiye maganar shari’a a gefe,saboda wasu dalilai da nake ganin koda an soma shari’ar babu lallai a cimma nasara,dalili na farko shine,dukkan abinda ya faru ga bilkisu masarauta bawai gaban kansu ko qarfa qarfa sukayi suka dauke bilkisu suka aurarwa dansu ba,a’ah,sun nemi aurenta ta hannun mahaifinta wanda dama shine yafi cancanta daya aurar da ita,ya amince ya aura musu ita bisa sadaki da kuma amincewar dukkan waliyyan yaran,kinga ko a nan hujja ta qare,ba saceta akayi ba,ba’a daura auren ba saida amincewar waliyyi wakili kuma mahaifinta,abu na biyu wannan shari’ar zata zama tamkar tonon silili ne ga bilkisu,wanda baisan batun bama ya sani,ta zama abar nunawa aduk inda zata shiga,shi nasu dan namiji ne,wanda wala’alla ba kowa bane ma yake da matsayin ganinsa ba bare a nunashi,koda ana ganinsa wala’alla sau daya ne a shekara wajen hawan sallah,wannan zai zame mata qalubale wajen wanda zata aura a gaba,koshi ko ahalinsa,hakanan zai zama takura a rayuwarta,tunda shari’a ce da manyan mutane,dole zata shiga jaridu da mujallun qasar nan,hadi da gidajen tv dana redio,kuma hade da hotunanta da nashi,abu na uku,malam bilyaminu mahaifin bilkisu ne,mahaifi kuwa har abada yana nan a matsayinsa na mahaifi duk lalacewarsa,duk tarin zunubansa,ba’a sauyawa tuwo suna,hakanan zai.iya yiwuwa a sanda kotu ta yanke mishi hukunci hakan ya sosa ran bilkisu,ya kuma hanata sukuni da walwalar da kikeson sama mata…..zuhra….inason ki duba dukka wadan nan hujjojin nawa,bawai don bamu da kudin da zamu iya tsayawa bilkisu ba,saidai wasu abubuwan mukan dauke kai daga garesu,mu kuma yi kamar basu faru ba,kamata yayi yadda kika dauko hanya nason inganta rayuwarta ki dora daga nan,ki mance komai don kada ya hanaki yin abinda ya kamata” shuru tayi tana jujjuyawa gami da tattauna kalaman mijin nata,tabbas maganganunsa suna bisa hanya,saidai tanajin kamar shari’a dasu ce kawai hanyar da zata sanya ta huce,amma dole ta tsaya ta duba abinda ya kamata kamar yadda yace,da wadan nan kalaman ta haqura,ta kuma watsar da abunda daa ta qudurta aiwatarwa.
***** *****”””””***** ******
A hankali yake fidda kayan jikinsa bayan dawowarsa daga zaman fada na musamman da aka gudanar a yau,cike da gajiya da qosawa yake rage yawan kayan dake jikinsa,fuskarshi kamar kullum babu walwala babu annuri,komai ma baya masa armashi ko dadi,ji yake kamar wanda aka sanya qaton kwado aka qulle rayuwarsa.
Sai daya gama cire kayan duka sannan ya doshi bandaki,ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi wanda ya dinga ratsa sassan jikinsa,idanunsa a rufe amma qwaqwalwarsa ta tafi tunanin data saba,tunanin daya zame mata tamkar al’ada matuqar ya tashi daga gadon baccinsa har zuwa sanda zai koma ya kwanta zuwa wani daren,tunanin dake azabtar dashi qwarai,ya kuma dauke dukkan wata walwala tashi cak fiye da yadda aka sanshi a baya.
Yana dakinsa yana tsane lemar jikinsa,tare da ci gaba da tattaki zuwa bakin mudubi,kansa yake kalla yana kuma sake goge jikinsa,baisan me yasa ta zauna masa daram cikin kwanyarsa ba,baisan me yasa tunaninta ya zame masa jini da tsoka ba,yabi dukka wata jijiya ta jikinsa,yakeson hanashi zama lafiya ba,wannan wanne irin tunani ne mai naci?,wanne irin memory ne dayake kasa barin zuciya da tunani su huta?,a iya tunaninshi komai ya qare tsakaninsu,tunda igiyar alaqar data hadesu ta jima da warwarewa,yana ganin bai kamata komai yayi zurfi haka ba,tunda dama an shirya shine na taqaitaccen lokaci,amma me yasa?,me yasa komai yake zaune daram a kwanyarsa kamar a yanzun komai ke gudana?.
Tsaki yaja yana ja da baya daga gaban mudubin bayan ya dauki manshi da yake shafawa ya koma gefan gadon yazauna yasoma shafawa,yana kokawar kauda komai daga kansa kamar yadda kullum yake wannan yaqin,saidai kusan duka a banza ne.
Wayarsa dake gefe ta dauki tsuwwa,saiya waiwaya ya duba,ammi ce ke kira,ya sanya hannu ya amshi kiran ba tare daya dauki wayar a hannunsa ba,saidai ya sanyata a handsfree
“Kana sassanka ne?”
“Eh ammi”
“Ohkey,ka sameni a sassana,falo na uku,zamuci abincin dare tare anjima”
“To in sha Allah” ya amsa mata yana latse kiran.
Misalin takwas na dare ya shirya cikin qananun kaya,wadanda sukayi bala’in amsarsa,kyansa da kwajininsa dukka sun fito,ya dauki wayoyinsa sa’annan ya baro sashen nasa.
Hadiman dake sassansa sunso masa tattaki amma ya dakatar dasu,ya nuna musu bashi da buqata,don haka shi kadai ya dinga ratsa cikin gidan nasu da ya wadata da hasken fitilu tako ina saika rantse rana ce,yanayin iskar kadai ya dinga sanya zuciyarsa cikin yanayi na daban,yaci gaba da takawa a nutse zuwa sassan amminsa.
Daga nesa ya hangosu sun taho,sun jero da juna shi da ita,suna nufo sashen da yake shima,kanshi ya dauke kamar bai gansu ba,saidai kwarjininsa daya cika shi dashi tun daga nesa ya gaza wucewa shima,ya tako zuwa inda yake ya masa sallama yana miqa masa hannu.
Amsa mishi yayi ya bashi hannun shima ya soma gaidashi ya amsa yana duban walida,wadda baqinciki da takaici kamar ta mutu,ya jefa mata wani kallon gargadi sannan yajuya yaci gaba da takawa ya barsu a wajen.
Kitceh kitchen tayi da ranta,saiya saki murmushi
“No way idan ka ganshi dole ba zaka iya wucewa ba,ke kanki duk sanda kuka hadu laushi kike qara yi bare ni da nake a matsayin suruki,yana da kwarjini da cika ido” tasan da hakan sarai,amma saita tura baki
“Duk kwarjininsa amma dai qanina ne ko?,shi ya kamata idan ya ganka ya soma gaisheka” dariya yayi yana kada kai,ita kanta yasan ta fada ne kawai,amma ba abinda zai yiwu bane,haka ya lallabata sukaci gaba da takawa.
Har aka gama serving dinsu babu wanda yace uffan,sai data gama zubawa ta tafi sannan fulani taja nata abincin gabanta tasoma ci,maimakon taga yaja nashi abincin sai taga ya janyo babban jug din tangaran wanda yake cike da ruwan tattacen inibi yahau zubawa yana dirkawa cikinsa,bata ce masa komai ba har taci kusan rabin abincin
“Hala a qoshe kake kenan?” Kai ya jinjina
“Banajin yunwa ne…” Bata kuma cewa komai ba,amma tana karance dashi har ta kammala sannan ta dubeshi
“Batun ci gaba da karatunka….har yanxu baka kammala zabar universty din da zaka ba?” Kwata kwata a yanzun bashi da wata sha’awa ta tafiya wata qasar again,uwa uba ma dukka wani buri da shima ya ciwa karatunsa a yanzun babu shi,tamkar wanda aka zarewa dukkan wata sha’awa da burinsa,amma a yanzun yana da yaqinin furta hakan ga ammi ba qaramin qalubale bane,tunda ba abunda take son ji ba kenan.
Boyayyiyar ajiyar zuciya yasaki yana hade hannayensa waje guda
“Zan duba in sha Allahu”
“Baka kai ga soma dubawa ba kenan?”
“Sai nan gaba” ya fada don mutum ne shi da abune mawuyaci,ta riga data sanshi,don haka saita gyada kai kawai tana dubanshi tare da karantar sauyin yanayi muraran tattare dashi.
Zaune take tsakiya ateeq da najwa da suka baza litattafansu tana koya musu assigment,yayin da hisham yake zaune saman cinyarta yana wasa da wani abun wasan yara da ake daura musu a hannu,haule kuma na kitchen tana hada kayan girkin da anty zuhriyya ta sata ta hada din kafin ta sauko daga sama,saboda abune mawuyaci kaga ta sakarma haule dukka girkin gidan idan ba wani babban uzurine ya taso mata ba wanda bata kusa ko bazata dawo gida da wuri ba.
A hankali ta daga hannunta ya dafe bayan wuyanta dashi,saboda yadda takejin jikinta na wani irin ciwo,qashinta kamar ana sassara mata shi,yayin da takejin zazzabi nason kamata,saisai babu alamunsa saman fatarta,da alama zazzabin cikin qashine,daurewa ta dinga yi ganin sun kusa gama assigment din,a haka a anty zuhiryya da a yanzun take kiranta da mami kamar yadda yaranta ke kiranta ta sauko daga saman nata tana dubansu.
“Kinga ta kanki daughter,wai har yau ba’s gama aikin bane” idanunta ta daga cikin wata iriyar kasala da dandatsar da takeji a qashinta tace
“Eh….mun kusa amma” fuska anty zuhriyya tadan yamutsa tana kallon bilkisu
“Daughter….anya lafiya kuwa,kinga yadda idanunki suka sauya kala” itama yamutsa fuskar tayi
“Banajin dadi ne,kamar zazzabine yakeson kamani” da hanzari ta taho inda take tana dauke hisham daga saman cinyarta
“Ashsha…tun yaushe kuma amma kika tsaya kina wani aikin daban,maimakon ki samu waje ki kwanta,maza tashi ki dauko paracetamol guda biyu kisha ki kwanta,zuwa anjima kadan mu gani,idan baki samu relief ba ki shirya nasiru driver ya kaiki kiga likita” bata musa ba ta miqe,sai a sannan taji da gaske ashe jikin nata babu dadi,ta dinga takawa a hankali harta shige dakin da suke ajiyar magunguna,ta balli paracetamol din guda biyu tasha sannan ta wuce dakinta.
Kai tsaye gado ta fada taja duvet ta lulluba sosai tana sakin ajiyar zuciya saboda yadda taji qashinta na mutstsuka,tadan jima a haka sannan bacci yayi awon gaba da ita.
Sanda ta farka taji dama dama,don harma ta sake wanka don ta kuma jin dadin jikinta,takuma shirya ta sauko qasa akaci abincin dare da ita,lokacin kwanciya yayi ta dauke najwa tace tare zasu kwana suka wuce dakinta.
Saidai tsakiyar dare ciwon ya dawo mata sosai,harta kasa jurewa,ta dinga sakin nishi tana murqususu,ga wani dan banzan zazzabi mai kama da an kara mata wuta,hatta da numfashinta huci yake bayarwa,najwa nata bacci batasan me yake faruwa ba,sai gab da asuba da fitsari ya tasheta sannan ta gani,abinka da yarinta dakuma rashin sabo duk sai ya rude,ta juya da sauri ya fice daga dakin don sanarwa mamin nasu,duk da bilkisu tayi yunqurin tsaidata kada ta tashesu suna bacci.
Minti biyar yayi yawa suka dawo tare ita da anty zuhiryyan,sanye da hijabi da alamun bacci take ta tasota,a hanzarce ta isa inda bilkisun take tana riqeta,yadda taji zafin da jikin nata ya dauka ya daga mata hankali,saita saketa tana cewa
“Bari na yiwa abbaa magana,inaga gwara kawai mu wuce asibiti” bata da sauran qarfin da zatace komai saboda yadda taketa rawar dari,kai kace an sakata ne cikin kogin qanqara.
Cikin daren ya fidda mota suka wuce asibiti,sukabar yaran a gida su da haule,wanda suna zuwa cikin sauri aka karbeta,sannan aka bata dukkan taimakon daya kamata,cikin awa guda saiga bacci ya sureta,sai a sannan hankalin anty zuhriyya yadan kwanta.
Da safe likita ya bada test na malaria da typoid yace ayi mata bayan ya tambaya tana da aure antyn tace aah,baccin da take yasa aka jinkirta yin test din har zuwa sanda zata tashi.
Bacci tayi sosai saboda allurai da ruwan da aka saka mata,bata farka ba sai kusan azahar,anty ta taimaka mata saboda jirin da tace tana ji,ta shiga bandaki ta wanke bakinta,tayi alwala tazo ta rama sallar asuba data kubce mata,sannan ta dora da azahar,sai a sannan antyn ta zuba mata farfesun kifin da haule tayi da dankali jifa jifa a ciki,ya dahu sosai yadda zaiyi dadin ci,ta matso da kwanon kusa da ita
“Bismillah,ungo” ta fada tana miqa mata cup mai dauke da ruwan tea mai zafi bayan ta tura mata kwanon kifin gabanta,kanta ta dauke tana kada kai
“Bakina babu dadi ummee,kuma bana jin yunwa ma kwata kwata,cikina a cushe yake”
“Idan kika ci ko babu yawa zakiji dadin bakinki,sannan bazai yiwu ayita baki magani ba amma babu komai a cikinki,likitan dama yace idan kin tashi kici wani abu,kema.kya dan sake jin qwari,don lab zamuje yanzun za’a miki test”.
Batason mata musu,don haka ta saka hannu ta karbi ruwan tea din,kurba uku tayi mishi taji cikinta na juyawa,hakanan ba zata iya ci gaba da sha ba,saita dire tana cewa
“Ummi wallahi kaman xanyi amai,don Allah ki qyaleshi” yadda ta fara yunquri ya nuna mata da gaske take,don haka ta qyaleta,bata yi mata maganar test bama sai data kwanta tasake hutawa sannan sukaje lab din.
Washegari result ya fito,malaria din ne da typhoid,saidai malaria yafi yawa,nan anty zuhriyya ta dinga sababi
“Dama a wannan gidan kowacce irin cuta ma ba samunta za’ayi ba tunda babu mai kula dakai,mun godewa Allah daya sanya iya tsahon shekarun ciwon da kika samu kenan”.
Kulawa sosai ta samu a asibitin,satinta guda sa’annan ta samu sauqi suka bata sallama suka dawo gida.
*_BAYAN KWANA BIYU_*
Babu bata lokaci anyy zuhriyya tayi ma bilkisu registration na waec da neco,hakan ya sanya gaba daya bilkisu ta maida hankalinta kan karatu,duk wani buri nata ya sake dawowa sabo,kwadayin karatunta da karsashinta suka sake dawo mata,ta bude can wani saqo na zuciyarta data tattara dukkan burin karatunta ta cusashi a ciki ya zaqulo abinta ta sabunta shi,tunda a yanzun tana ganin ta samu dukkan wata dama data dace,hakanan babu wata sauran matsala da zata dakatar da ita.
Lafiya qalau ta zana waec dinta,cikin sauqi,don duk yadda ta zaci abun zaizo mata da wahala ta dinga jin tsoro duk da karatun da tayi sai taga duka ba haka bane,tazarar kwanaki suka soma neco.
Ranar farko lafiya lau taje itama ta dawo gida,saidai a komawa ta biyu ta soma jin jikinta babu dadi,kamar rashin lafiyar datayi a kwanakin baya tana son dawo mata,don haka ta fidda magungunanta da dama basu qare ba tun wancan lokacin ta sha,ta danji dama dama,sun kuma taimaka mata ta qarasa zana jarabawarta,har zuwa ranar da suke da paper qarshe.
Tun a makarantar da take zana jarrabawar ta soma jin kanta na juya mata,hakanan qafafunta basu da wani isasheshen qwari,a daddafe ta dinga amsa tambayoyin,tana yi tana dakatawa ta huta,a haka harta kammala,inda Allah ya taimaketa tuni drivern anty zuhriyya yana waje yana jiranta,don haka bata wani tsaya ba ta tattara ya nata ya nata ta fito,tunda dama babu wanda ta sani,kuma iya zuwanta bata bari tayi sabo da kowa ba,abinda ya kaita shi kadai takeyi,data gama take tafiyarta.
Tunda ta shiga motar take dafe da kanta,don tana daga zaunen amma jiri takeji,hakanan numfashinta na mata nauyi,Allah Allah take su isa gida ta samu waje ta kwanta sosai ko zata samu relief.
Suna isa ta bude motar ta fit,tana tafiya tana hada hanya,kallo daya zaka mata kasan ba lafiya qalau take ba,a haka ta isa falon gidan,anty zuhriyya ce kadai zaune tana kallo,duka yaran na makaranta lokacin tashinsu baiyi ba,sai hisham dake zaune a gefanta yana shan madara.
Yanayin sallamarta ya sanya anty zuhriyya dubanta tana amsa sallamar
“Yadai daughter?” Ta tambayeta tana qare mata kallo,ba zata iya wani dogon tsaiwa ba don kada ta fadi,saita doshi dakinta tana cewa
“Bab….ba komai ummi” saidai kafin takai ga isa tuni jiri ya debeta tayi luu zata fadi,cikin mugun hanzari anty zuhriyyan ta nufeta ta tallafota tana kiran sunanta,idanunta nakan fuskar antyn sanda numfashinta ke qoqarin daukewa,sannan a hankali dukka idanun nata suka lumshe.
Abinda yayi masifar daga hankalin antyn kenan,tasoma qwalawa drivern daya kawota kira ba tare da tayi la’akari da cewa babu lallai ya jita ba,ganin babu alamun yana jinta ya sanyata riqe bilkisun ta kwantar da ita saman kujera,sannan ta fita harabar gidan cikin hanzari tana sake qwala mishi kira,tunda babu kowa gidan ta aiki haule kasuwa.
Allah yasa yadan tsaya magana da me gadi a qofar gate din kafin ya fice yaje dauko su najwa,yanayin kiran ya alamta mishi ba lafiya,saiya taho da hanzarinsa
“Maza bude mota,daughter ya fadi” ta qarasa fada tana komawa cikin gidan cikin gudu gudu sauri sauri,sai data sake duba bilkisu cikin tsoro da firgici sannan ta haura dakinta ta yayibo hijabin sallarta tazo ta sake kamata zuwa cikin mota,sai data kwantar da ita sannan ta dawo ta dauki hisham daketa qwala kuka,ya zaci tafiya zatayi ta barshi,hankalinta a matuqar tashe,don ko abbaa batasamu damar gayawa ba saida suka isa asibitin aka karbeta sannan ta daga waya ta gaya mishi.
Jiki a sanyaye ta isa office din likitan tana fargabar wanne ciwo kuma keda bilkisun har haka,rabbi kada yasa wata mummunar cutar ce kuma ta daban ta kamata.
Cikin qwarara gwiwa abbaa da suka shigo tare ya dan taba kafadarta yana nuna mata wajen zama,don daya tashi daga office nan ya biyo,yaran kuwa tunda aka daukosu daga makaranta tasa aka wuce dasu gida wajen haule,ta isa inda ya nuna matan ta zauna abbaan yana binta da kallo,yasani cewa indai akan bilkisu ne raguwa ce,bata da wani jarumta ko qwarin gwiwa ko kadan,qaunar da takewa ‘yaruwarta ce gaba daya ta tattarata ta koma kan bilkisun,batason duk wani abu da zai sameta,ya dade da shaida hakan tun bilkisun batakai haka ba,shidin bai zauna ba,saiya tsaya kawai saman kan zuhriyyan suna sauraren bayanin likita.
Dukka test test din da akayi mata ya tattara ya zuba cikin file dinta sannan ya dubesu
“Mara lafiyarku tana da aure ne?” Cikin mamaki anty ta dubeshi
“Me yasa ka tambaya likita?” Kafadarshi ya daga sannan yace
“Eh,na ganta da unifoarm ne,sannan sakamakon gwaje gwajenta kamar bai dace da yanayinta ba” cikin daure kai ta sake amsa mishi
“Bata da aure” saiya dafe goshinsa sannan yace
“Ya salam” kusan abbaa yaso gano meke faruwa,don haka yayi gyaran murya
“Amm,likita ta taba aure,sannan bata jima da rabuwa da mijin ba” yanayin fuskarsa ya sassauta,saiya saki goshin nasa ya dago yana dubansu
“Good….to tana dauke da juna biyu na sati goma sha biyu”
“What!” Anty zuhriyya ta fada cikin wani irin tashin hankali,har tana miqewa idanunta dukka a waje tana duban likitan,duk da shima abbaa sakamakon ya bugeshi,amma sai yayi hanzari kama hannun zuhriyyan
“Relax zuhra….likita” ya kirashin yana dubanshi
“Bilkisu bilyamin muke magana fa?” Kai ya gyada
“Yes,ba wadda kuka kawo da azahar ba student?,shi yasa na soma tambayarki before na gaya muku sakamakon,ba typhoid yanzu a jikinta,sai malaria ‘yar kadan da kuma juna biyun da take dashi” ya sake karanto musu sakamakon bayan ya sake bude file dinta yana sake karanto bayanan da aka rattaba jikin takardar,sai daya qare sannan ya daga kai yana dubansu
“Bada ubanshi ba?” Yakuma tambayarsu cikin mamakin tashin hankalin daya gani saman fuskar anty zuhriyya,murmushi abbaa yayi
“Da ubansa,kasan shiriritar mata,saboda nasa tare da mijin kuma ga ciki shine abinda ya daga mata hankali” murmushi ya saki
“Hajiya qaddarar ubangiji ai tafi gaban haka,babban abun godiyar shine daya kasance ba shege bane”
“Hakane kam….mun gode likita” ya fada yana bashi hannu sukayi musabaha,sannan yaja hannun anty zuhriyya da tuni da daina ganewa ko jin abinda suka tattaunawa a kai.
Kuka ta fashe mishi dashi suna fita daga office din,ta dora kanta saman kafadarsa tana jin wani abu yana sukar zuciyarta,wannan zalunci ne,zalunci ne mai yawa,me yasa basuyi amfani da matakan kariya ba tunda sunsan ba zama zasuyi da ita ba donsu sauqaqe mata wahala,ta gama wancan zaman da yafi kama dana fursuna,sa’annan yanzu ga wata sabuwa ta bullo?
“Kiyi haquri zuhra hakanan don Allah,kaman yadda likita ya fada ne,mu godewa Allah daya kasance ba shege bane da ubansa”
“To meye marabar dambe da fada abbaa!” Ta fada a zafafe tana daga kanshi daga kafadarsa kai kace shine ya aikata dukkan komai,saiya saki murmushi,yasan kan kayarshi sarai,ya janyeta zuwa cikin motarsa yazaunar da ita seat din baya shima ya zauna gefanta,hannunshi ya saka cikin nata yana dubanta
“Nidai zuhrar dana sani jaruma ce gsky ba raguwa irin wannan ba,kin taba ganin bawa yayi kokawa da qaddararsa?,baki godewa Allah daya saka dan halas ne?,duk tsiya saida aka biya sadaki aka shafa fatiha sannan aka samar da cikin?,sannan wannan kukan da kike shi xaki ci gaba dayi har yarinyar ta farka ta gani,ki karya mata gwiwa kisake sata a zulumi,maimakon taga qarfafa gwiwa a fuskarki da rashin damuwa,wanda hakan shi xai qaranta tata damuwar da rungumae qaddararta,har a samu yadda akeso” cikin hikima da sanin makamar matarsa ya dinga gaya mata kalaman da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sanya mata kwanciyar hankali,sun jima cikin motar sai daya tabbatar yayi cooling temper dinta sannan ya qyaleta,saidai daga qarshe ta dubeshi
“Amma abbaa dole susan da zaman cikin nan” kai ya gyada
“Eh,wannan ya zama dole,kuma haqqinsu ne dama su sani saboda gaba” wannan din itama yayi mata,don haka ta gyada kai tana sauke ajiyar zuciya,saidai can qasan ranta tana jin zafi tare da baqincikin yadda suka sanya rayuwar ‘yarta cikin walagigi bisa tsarinsu da kuma son zuciyarsu.
Bata koma dakin ba sai data tabbatar zuciyarta cikin kaso dari kaso hamsin ya sanyaya,don ko abbaa bai amince ba batajin wannan karon za’a musu shuru,gwara susan da abinsu,kuma koda ta haihu su dauki abinsu ita kuma taji da rayuwar ‘yarta.
Tana tura qofar dakin idanunta akan bilkisu,ta waiwayo suka hada idanu,yadda ta kalletan sai taga kamar tasan yanayin data kuma fadawa,hakan ya karyar mata da zuciya,qwarin gwiwarta ya ragu,tausayinta ya kamata,ta fito daga wata jarrabawar yanzu gashi katsam ba zato ba tsammani ta fada wata,me yasa tun sanda ta dawo bata kawota an dubata an tabbatar babu ciki ba,da ta sani tun kafin abun yayi nisa da wala’alla an samu mafita akansa,qaddara ta tabbatar ita ta hana kawo bilkisun a bincikar mata lafiyarta da kyau.
Ta farka idinta biyu,saidai tana kwance a yadda take bata motsa ba,murmushi tayi mata sanda take tambayarta ya jikin nata
“Da sauqi ummi” yanda tayi.maganar sai ta sake ganin ta koma mata maimunatun ta,da sauri ta miqe daga kan kujerar da take kai jin qwalla na shirin zarto mata,ta isa ga drower din da abbaa yayi musu siyayyar kayan tea tana fito dasu,saida ta saisaita kanta sannan ta dawo.inda take tana duban ruwan da aka saka mata sannan ta maida kanta gareta
“Ya kusa qarewa,bari na musu magan suzo su cire miki ki samu wani abun kici” kai ta gyada mata ta juya ta fice ba jimawa suka dawo da wata nurse ta cire mata,ta taimakawa bilkisun ta tashi,duk da jirin da takeji ya ragu sosai.
Sai data kaita bandaki tayi alwala sannannta dawo ta shinfida mata abun sallah,yanayin anty zuhriyyan data canza ya bawa bilkisu mamaki,duk da batace komai ba amma ta lura komai da takeji jikinta a sanyaye yake,itadai bata tambayeta ba tahau abun sallar ta tada salla.
Sai data gama dukka sallolinta sannan ta zuba mata abinci tace ta matso taci,kaita soma kautarwa sabida wani tashin zuciya da amai data soma ji sanadin shaqar warin abincin,ta girgiza kai
“Bazan iya ci ba ummi” fuska ta bata
“Dole kici daughter,ta yaya zaki zauna ba abinci,kina so muyi fada kenan?” Kainta girgiza qwalla na cika mata idanu,tunda take bata taba jin irin wannan feeling din ba na batason ganin abinci kojin qamshinsa ba sai yanzu,kamar an nuna mata bindiga haka taji
“Kiyi haquri ummi,wallahi bazan iyac…..” Bata qarasa ba amai ya taso mata,tahau yunqurin aman da babu abinda ya fito saboda babu komai cikinta,sosai ta galabaita,don har sai da nurse din ta dawo,ta mata wata allura sannan aka sake maida mata ruwa,ta lumshen idonta tana sauke ajiyar zuciya sanda take akwancen,don babu abinda tafi buqata irin kwanciyar,gefe guda kuma tana mamakin wanne irin ciwo ne haka takeyi?,azaba da wahalar da takeji bata taba jin irinta ba,a haka bacci ya sake daukanta,anty zuhriyya na zaune gefanta tana ta qoqarin boye hawayenta.
Cikin sati guda rak wani irin laulayi mai azabatarwa ya rafeketa ba tare da ita kanta tasan laulayin take ba,don sam anty zuhriyya ta kasa gaya mata,gani take abun saiyayi mata yawa,babu abinda take iya ci ya zauna cikinta qalau,koda ruwa ne sai anci babbar sa’a bare akai ha abinci,hakan ya sanya koda yaushe cikin qarin ruwa take,ta zabge ta sake yin wani fari bau,gefe daya ga wata rama ta musamman datayi,dukka kayanta basa zaunar mata a jiki sun mata yawa,don wani lokaci rigunan najwa zuhriyya ke kawo mata ta saka,saboda tana da dan jiki,hakanan batanson hayaniya ko hasken rana mai yawa,wani irin azababben laulayi daya sanya anty zuhriyyan ta dinga mata kuka a boye,idan ka ganta saika zaci ba zatayi raiba saboda yadda take azabtuwa,itakam.har fatan cikin ya zube anty zuhriyya takeyi cikin ranta
“Wannan baqar qaddara taki Allah ya yanke miki ita bilkisu” haka take yawaita fada,saboda ganin irin yadda takeshan wahala da cikin da batasan ma yana maqale a jikinta ba.
Wata guda cur da satittika wajen uku sukayi a asibitin,sannan aka dan fara samun sauqi,har zuwa sannan batasan da wani ciki ba,saboda bata cikin nutsuwarta bare hankalinta da har zata lura da wani sauyi ko wata alama.
Da wani yammaci ta farka a bacci da wani irin fitsari daya matsota,a lokacin anty zuhriyya tana sallah,idan tana wajen duk sanda zata bandaki saita rakata,qaunar ummin na sake qaruwa cikin zuciyarta dakuma tausayinta,yadda take mata ko najwa ce iyaka abinda zatayi mata kenan a matsayinta na uwa,ta aje dukkan wasu harkokinta ta tattara a wajenta,hatta da gida saidai taje lokaci bayan lokaci ta dawo asibitin,duk hankalinta da kulawarta tana kanta.
Ganin yau jikin nata da qwari qwari ya sanya ta zuro qafafunta qasa a hankali,ta saka takalmanta ta miqe zuwa bandakin,don yau itama ta tabuka ta ragewa ummin aiki.
Tana zuwa fitsari sai taga jini,batayi wani mamaki ba,ta kawo a ranta period dinta ce tazo
“Dama naga kamar tayi jinkiri wannan karon bata zo akan kari ba,ko saboda ciwon nan ne” ta fada tana yin tsarki sannan ta miqe,amma sai taji mararta ta riqe,tadan cije bakinta,ikon Allah,tasan bata ciwon mara idan tana al’ada,amma yaya akayi yau mararta ke mata ciwo?,ta tambayi kanta tana fitowa daga bandakin a daddafe.
Sanda ta fito ummi zuhriyya ta gama sallar carbi take ja,ta zuba mata ido ganin yadda ta fito a duqe,da sauri ta tambayeta
“Lafiya daughter” saidata zauna gefan gadon sannan tace
“Marata ce take ciwo ummi,kamar period ne inaga”
“Periode?” Ta tambaya cikin fargana da faduwar gaba,saita gyada kanta
“Eh”
“Jini kika gani!” Ta fada tana miqewa a hanzarce har bilkisu na mamakin dalilin rudewarta haka,saita sake gyada mata kai
“La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” ta furta sannan ta durfafi qofa da hanzari,binta kawai tayi da kallo cike da mamaki,toko bai kamata ace tana period bane?,tayiwa kanta guntulalliyar tambayar da bata da amsa.
Sanda likita ya iso ya dubata saiya tabbatarwa da anty zuhriyya wahalar data sha ne bakin mahaifar ke niyyar budewa,saboda haka dole su bata bedrest again kona wata daya ne su gani.
Lokacin da suke bayanin kawai kallonsu take,kanta a daure tamau,ta kasa fahimtar komai,mahaifar waye zata bude?,waye keda ciki?,kuma wa za’a bawa bedrest?,duk da tambayoyin dake cin kanta bata iya furta ko guda daya ba,taci gaba da binsu da kallo ne harya gama abinda zaiyi ya fice,dakin ya rage daga ita sai anty zuhriyyan.
Ta lura da dimuwar da bilkisun ta shiga,da yadda take dan kallonta,da alamu tambaya ce fal kanta,tasan dama dole hakan zata kasance,tunda taji wasu magangun da bata gane kansu ba daga bakin likitan,don haka saita janho kujera zuwa bakin gadon da take kwance,ta zauna idanunta kan bilkisun,tana wassafa tare da tsara yadda zata mata bayanin da zai kwantar da hankalinta,duba da yanayin da take ciki,saboda rufewar ba zata amfana komai ba,face sanyata cikin tunani da kuma wani rudanin na daban.
“Daughter….nasan a rayuwa,daga sanda nake tare dake zuwa sanda bama tare,kin fuskanci abubuwa da dama arayuwarki,kin kuma rasa abubuwa da dama,kuma dukka kin juresu,rayuwa mataki mataki ce,kowanne mataki na jarrabawa idan yazo.maka kayi haquri kana iya cinyeshi yakuma wuce kamar ba’ayi ba,komai yayi farko tabbas yana da qarshe,kiyi haquri bilkisu….kina da juna biyu,wanda shine kusan silar ciwonki” wani irin abu taji yazo ya cake mata a maqoshi,ba don babu wasa tsakaninta da anty zuhiriyya ba da sai tace wasa antyn take mata,amma tasan babu wannan tsakaninsu,wani irin abu takeji yana mata yawo saman ka,kalaman antyn suna bangazar juna kamar xasu wargaza maya qwaqwalwa,saita rintse idanunta tana furta
“La haula wala quwwata illa billa” daga haka bata sake furta komai ba,bata sake cewa komai ba,saidai wani abu daya tsaya mata a wuya bata samu ya sauka ba har sai ranar da aka sallameta daga asibiti,sanda ta isa dakinta ta kwanta saman gadonta ita kadai,tana lissafin abinda yake cikinta,cikakken dan halas ne ko kuwa akasin haka?,ina ubansa?,tananda tutiya ko zarrar da xata nuna ubanshi harta furta shine yayi mata cikin da take dauke dashi a yanzu?.
Kuka ne mai wani irin nauyi a qirji da zuciya ya kubce mata,ashe haka matan dake yin cikin shege suke ji?,ashe haka suke tsintar kansu?,wanne irin bayani zata yiwa ‘ya ko dan cikinta a duk sanda ya girma ya nemi mahaifinsa,shin ta yiwa rayuwasa ko rayuwarta adalci?,ta hanyar data cancanci a samar dashi kenan?.
Wadanne irin mutanene wadan nan da babu halin girma ko dattako cikin jininsu?,wadanne irin azzalumai ne su da suka zabi rayuwarta cikin miliyoyi suka tarwatsa ta,meta musu ne haka suka hanata cimma dukkan wani buri na rayuwarta,matsalarsu dai a kullum ita ke dakatar da ita daga samun duk wani ci gaba,a duk lokacin data yunqura don ci gaban rayuwarta saisun daqileta,wancan karom sune silar karatunta,wannan karonma dukkan alamu sun nuna sune zasu zame mata tarnaqi.
Tayi kuka mai yawan gaske,irin kukan data kwana biyu bata yishi ba,har zuwa wayewar gari,yadda idanunta suka tasa ya sanya anty zuhriyya ta fahimci irin kukan data yi,fada sosai ta dinga yi tana bala’i,saboda har yanzun ranta a bace yake itama,wani da bilkisu take kan me yasa zata zauna tana kuka,yayin da mafi yawa kuma dukka kan masarautar kaisa ne,wanda basusan halin da ake ciki ba.
Sai data gama son ranta sannan ta sauko,taci gaba da lallashin bilkisun tare da kwatanta mata illar bacin rai da damuwarta ga lafiyarta.
Ba qaramin jajircewa anty zuhriyya tayi ba wajen ganin ta daidaita lamari da yanayin bilkisun,wanda sai bayan kwanaki data tabbatar ta sake warwarewa ta nemi abbaa ya bata izini zataje tayi magana da malam bilya,daga nan su sanar da masarauta,don ta inda aka hau ta nan ake sauka,bai musa ba mata ba ya amince mata,don haka ta sanya lokaci yammaci liqis sanda tasan za’a iya samunsa a gida ta sanya bilkisu ta shirya suka nufi gidan.
Cikin doguwar riga take purple,saqar qasar dubai,ta yafa mayafin doguwar rigar kawai saman kanta ba tare data nannadashi ba,mai kawai da turare ta sanyawa jikinta,amma idan ka kalleta sai kaga ta qara wani kyau na musamman,kai kace an mata amfani ne da wasu kayayyakin gyaran fata na musamman,saidai tana nan babu qiba ko kadan tattare da ita,plate din takalmi kawai ta zira,ko wayarta da anty zuhriyya ta sauya mata zuwanta gidan bata dauka ba ta fito suka wuce,daga ita sai antyn sai hisham wanda bilkisu ke riqe dashi saman cinyarta,antyn tana tuqi.
Sanda suka isa gidan ana kiraye kirayen sallar magariba,wasu da yawa sunata daura alwala suna tafiya zuwa masallaci don samun jam’i.
Suna shiga gidan bayan sun faka motarsu qofar gidan malam bilya yana fitowa daga cikin gidan,cikin hanzari jikinsa jiqe da ruwan alwala,yana ganin zuhriyyan gabanshinya fadi
“Jarababbiya masifaffiya,ko dame kuma tazo” ya fadi,amma gefan ranshi yana jin dadin yadda bikisun ta warware sarai fiye da sanda ya ganta a asibiti.
Itace ta soma magana
“Munzo ganinka,gashi kuma kana shirin fita” tayi maganar fuskarta a daure tamau,wannan furucin ya sake sanyawa gabanshi ya fadi
“Da wata aqasa kenan” ya fada a ranshi
“Ku shiga ku jirani,zanje nayi sallah na dawo” bata amsa mishi ba ta juya tayi ciki,tabar bilkisu na gaidashi kafin itama ta biyo bayanta.
Umaima da aminatu ne a falon da alama salla suma zasuyi,,suna ganinta kowacce tasoma rige rigen isa wajenta,suka rungumeta cikim jin dadi,itama rungumesun tayi tana jin dadi,don tayi kewarsu sosai,tunda tabar gidan anty zuhriyya bata sake barinta tazo gidan ba,saidai tayi musu dukkan abinda tace zata yi musun,kuma taga alamun sauyi da canji tattare dasu,bata taba kawowa cewa qaddara zata sake rabasu ba,ba zata sake barinsu su zauna tare ba.
Murnarsu ta fiddo da hannatu dake cikin bandakinsu tana musu wankin unifoarm,itama murna ce ta cikata,suka baibaye bilkisun kowa yana son bata labarai gami da tambayoyi,anty zuhriyya na zaune saman kujera tausayinta na ratsasu,ta wani fannin kuma suna bata matuqar sha’awa na yadda suke qaunar junansu da kuma yadda suka saba,bata ankara ba taga tuni sun janyeta zuwa dakinsu,saita saki murmushi kawai tana kada kai.
Murmushin nata ya katse sanda anty ta shigo falon,sai anty zuhriyyan ta hade ranta tsam,don ta gama karanatar kowaccensu,itama antyn bataga wajen wargi ba,don haka ta gama abinda ya shigo da ita kawai ta fita.
Babu jimawa umma katti ta shigo,saita soma washe baki ganin zuhriyya,ita kuwa babu abinda ya sauya dangane da yanayin fuskarta
“A’ah,zuhriyya ce a gidan namu?”
“Nice” ta bata amsa a taqaice
“Maraba lale,kyazo ki zauna shuru ke kadai,aiko bamu zauna da maimunatu ba kya nemeni” wani kallo tayi mata tana tabe baki,rainin hankalinta ma yaso zarta na kowa,saidai duka zataji dasu,sa’arsu daya ma yanzu bata tasu take ba,da kowacce saita kwashi kashinta a hannu,don tanajin ciwon riqon da sukewa diyoyin mijin nasu,riqo na zallar jahilci qauyanci da kuma son kai.
Banza ta baiwa ajiyarta harta gama sunadin surutunta,wanda yafi kama da tabarmar kunya tabata waje sanda malam.bilya yake shigowa ya umarci a bashi ruwa yasoma sha tukunna,mama ladi dake da girki ta nufi kitchen don kawo masa.
Tana daga zaune anan ta qwalawa bilkisu kira,ta kuma jiyota,sai gata ta fito,ta qaraso a hankali ta samu gefan anty zuhriyya ta zauna,kanta a qasa,batasan yaya baban nata zai amshi lamarin ba,kuma ta yaya za’a samu warwarar qullin.
Duban gefanta tayi ganin mama ladi xaune dafa’an,bisa dukkan alamu tana nufin gabanta za’ayi zancan kenan,don haka ta dubi malam bilya
“Kaman baka shirya zaman ba,don naga wadanda ba ahalin maganar ba zaune a wajen” ya gane sarai dawa take,don haka ya dubi ladi
“Ladi…bamu waje” haushi ne ya cikata,haushin zuhriyya take ji,don ta fuskanci bata daukar raini,hakanan bata daukesu a bakin komai ba
“Kome meye muna zaune zamuji” ta fada tana shirin fita
“Daga baya kenan,wai anyi sadaka da karuwa” anty zuhriyya ta bata amsa.
Sai data fice sannan ta dawo da dubanta kanshi,takaici yana cin ranta tace
“Malam bilya,shukar da kayine nazo shaida maka lokacin girbinta yayi,wala’alla babu wannan cikin tsari hasashe ko shirinka ko?” Dubanta yake cikin rashin fahimta,sai kuma ya hade rai wai karta kawo masa wargi ko raini
“Kamar yaya,me kike nufi?,kefa baki rabo da jarfa,idan zakimin bayani kiyimin” gyara zamanta tayi yana amsa mishi
“Shi zan maka yanzu” sai taga baima kamata aci gaba dayin maganar a gaban bilkisun ba,saboda haka tace tatashi ta koma,cikin matuqar mutuwa da sanyin jiki ta miqe ta fice daga falon.
“Diyarka kuma diyar maimunatu da ka bada hayarta…don haya shine sunan da yafi dacewa da aurenta,taje ta kuma dawo maka da tsarabar jika,in sauqaqe maka dogon nazari,yanzu haka juna biyu gareta” wani irin gumi ne me dumi ya karyo masa,idanunsa dukka a waje yace
“Kamar yaya zuriyya,me kike fada ne?”
“Abinda kunnuwanka suka jiye maka” ta maida masa cikin gatse da matuqar jin haushinsa. Baisan sanda ya zame hular kanaa ba yahau firfita gami da ambaton
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.⁴¹