SIRADIN RAYUWA CHAPTER 12
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Tsayin lokaci yana firfitar gamida mai maitaba innalillahi,ita kuma tana zaune tana kallonshi tare da mamakin rudewar tasa,shi duka baiyi wannan lissafin ba,ko tsabar rainin hankali ne kawai.
A hankali ya aje hularshi gefe sannan yace
“Yanzu meye abunyi?” Baki ta tabe
“Bansan muku ba,tunda badani aka qulla ba,abinda na sani kawai shine,ta inda aka hau tanan ake sauka,kasan dukka hanyar da zakabi ka sanarwa da uban cikin ajiyarsu dake jikin ‘yata,bama buqatar wani abu face su kwana da sanin akwai jininsu a jikinta” daga haka ta yunqura ta miqe,sai yayi saurin dakatar da ita
“Ya zaki tafi kuma?” Kallon banza tayi masa
“To ce maka akayi dama zama nazo yi?,saqo nazo isar maka,kuma tunda ya isa shikenan” daga haka ta juya tayi ficewarta daga falon,ta tsaya ta kirayi bilkisu suka wuce.
Tashin hankalin da bai tana zaton zaijishi ba shi yakeji,gumi ne kawai ke yanko masa ta kowanne sashe da loko na jikinsa,bai taba hasashe ko tsammanin faruwar hakan ba,bai taba kawo hakan zai iya faruwa ba,ko kallon mama ladi dake faman tambayarsa abinda yake faruwa cikin salon bugun ciki baiyi ba.
Zumbur ya miqe yana maida hularsa dake ajiye dafa’an a gefe saboda hasashen da qwaqwalwarsa ta bashi
“Ina zaka haka kuma malam?,wai wanne irin jarababben albishir wannan masifaffiyar matar tayi maka daya daga maka hankali haka,bayan nasan babu kalar abinda baka gani ba”
“Rayuwar ‘yata…..” Kawai ya fada yana yin gaba.
Yana tafe shi daya yana zancan zuci da qananun sumbatu,tabbas ta inda aka hau tanan ake sauka kamar yadda zuhriyya tace mishi,dole susan da zaman cikin,saidai bashi da wani yaqini ko tabbacin xasu amshi maganar,tunda sun riga tunda fari sunzo da dukkan sharudda nasu,shi kuma ya karba hannu bibbiyu ya amince musu,a lokacin da idanunsa suke a rufe,matsera yake nema kawai da hanyar da zai kubuta daka dukan da talaucin yake masa tako ina,bai tsaya wani dogon nazari ko tunani ba,sai gashi yau wannan al’amarin ya sameshi bagata tan.
Baiyi burki ko ina ba sai qofar gidan umma luba,wanda idan ka ganshi a yanzu ba zakace shi bane,saboda rushe mata shi akayi gaba daya aka sake mata sabon gini me bene,aka qawatashi da qaramin gate da fenti mai kyau harda shukoki,bayan umarar da sukaje tare da malam bilya din,da kuma kudade da aka danqa mata wanda suka isheta jari,bayan matsayi da fulani ta sake qara mata a masarautar kaisan.
Bakinsa cike fal da addu’ar Allah yasa tana nan ya sake gyara tsaiwarshi ga qofar gidan,ya kirayi wani yaro dake shirin giftawa,ba musu yaron ya qaraso da hanzari
“Shiga gidan nan maza kace ana sallama da luba” ya amsa mishi sannan ya tura gate din gidan ya shige,babu jimawa ya fito ya gaya masa tana zuwa.
Shudewar mintuna biyu aka taba qofar sannan aka budeta,umma luba ta bayyana,ganin malam bilya saita saki murmushi,har haqorin makkan data maqala yana bayyana
“A’ah,dama kaine…..aida ka shigo daga ciki ko?”
“Shigowar nan kuwa zata yiwu?,don gsky a gaggauce nake” cikin mamaki take dubanshi
“Koma meye ai shirin zaune yafi na tsaye ko?” Bai sake tankawa ba yabita a baya,basu tsaya ba har zuwa madaidaicin falon gidan,da aka qawata da kayan zamani.
Suna zama ta kira mai aikinta ta kawo masa lemo,don yanzun me aiki gareta,wadda take kula mata da gidan idan ya tafi gidan maimartaba
“Bar lemon nan luba…..babban tashin hankali ne ta tunkaroni ko ince ya tunkaromu” qirji ta dafe cikin razana ta fidda idanu
“Mun shiga uku!,wani abune ya faru?” Sai daya sanya gefan babban rigarsa ya sharce gumin fuskarsa,duk da sanyin acn dake falon wanda umma luba ta qure tana morewa jin dadin duniyarta,takan ce sai tayi qara’i yadda ya kamata,tunda hutun baizo mata a quruciya ba,yanzunma da yazo mata duk daya wai mamaci ya karye.
“Bilkisu ‘yar wajena,mai gado,juna biyu gareta….juna biyun yarima”
“Tashin hankali!” Umma luba ta furta tana zama sosai saman kujera gamida fidda idanunta waje sosai,kamar wadda bata gani,zallar tashin hankalin data furta a bakinta yana bayyana qarara saman fuskarta
“Wannan wanne irin bahagon lamari ne,ya akayi haka ta faru?,me yasa dukkanmu bamuyi tunanin yuwuwar afkuwar hakan ba?” Ta qarashe maganar tana kallon malam bilya,karon farko a bigiren farko da yaji kishin jininsa,don haka saiya hade rai tsam,shima yaso yadan motsa qwanjinsa wannan karon ko yaya ne,kamar yadda yaga zuhiryyar tayi
“Oho,wannan kuma bani zaki tambaya ba,abu daya ne,kawai ki shaida musu abinda ke faruwa,so ake su sani kawai,bawai wani abu ake bida daga wajensu ba” shuru tayi tana juya maganarsa cikin ranta,kowanne daya cikin biyun zai iya yiwuwa,imma dai idan tayi shuru nan gaba har aka haife abinda aka samu ta shiga sahun masu laifi wajen fulani,wanda hakan zai jawo mata matsala,inma kuma taje ta shaida mata hakan ya zama tashin hankali ko kuma ya ballo da wani ruwan,to kowanne tayi ciki tana zato da kokwanton babu mafita,amma kuma da ace shurun tayi wani abun ya bullo bayan watanni suyi kuka da ita,gwara ta shaida musu tun yanzun sunsan da maganar.
Shaidai malam bilya miqewa yayi ya kade babbar rigarsa ya qara gaba,saidai koda ya isa gida kasa shiga yayi,yayi zaune anan qofar gida lamarin na masa kai kawo,yana jujjuyashi cikin ransa tare da hasashen meke iya faruwa nan gaba,wala’alla hakan ya qara masa daukaka da girma na hada jini da masarauta,wala’alla kuma ya sake fadawa wata daban.
Dukkaninsu shi da umma luban a wannan daren basuyi wani isashen barci mai dadi ba,kowa da zancan ya kwana a ranshi yana juyashi tare da taraddadin meye zai biyo baya?.
Washegari sam bata da agender na shiga masarauta,a yadda ta tsara sai jibi,amma zuwan ya zame mata tilas don isar da wannan saqo zuwa kunnuwan fulani,don haka tun goma na safe ta gama shirinta ta doshi masarautar kaisa.
Sanda taje akwai baqin da fulanin ke ganawa dasu,tadai shaidawa jakadiya zuwanta,ita kuma ta shaidawa fulani,sai kuma tayi zaman jiran ayi mata iso.
Lokacin da aka bata izinin shiga ita kadai tasan yadda ta dinga ji,gumi ya dinga karyo mata,qafafunta babu qwari ta dinga kutsa kai falon,cike da taraddadin sakamakon da maganar zata bayar.
Sanda ta shiga tana zaune saman daya daga cikun kujerun alfarma dake wajen,fuskarta a sake take duban luba harta qaraso,ta zube cikin girmamawa a gabanta
“Allah ya taimakeki….ya baki yawan rai…Allah ya iya miki yakuma dafa miki,ya danqwafar da maqiyanki,ya qasqantasu a gabanki…..barka da warhaka ranki ya dade” murmushi tayi har cikin ranta tana jin dadin addu’ar da luba tayi mata
“Yauwa sannu luba,barkanmu….ya iyali”
“Kowa lafiya Allah ya baki yawan rai”
“To madalla,haka mukeso” shuru umma luba tayi tana jujjuya maganar,harsai da fulani ta fuskanci akwai magana bakinta,ta dago tana gyara zamanta sosai sannan tace
“Lafiya dai ko?” Kanta zuwa gefan fuskarta ta shafa,tana jin wani irin rashin sukuni
“Lafiya amma ba lau ba”
“Uhmm,gaggauta sanar dani,meye yake faruwa?” Zama tayi sosai dirshan,don a jikinta tana jin cewa maganar ba qarama bace
“Wato Allah ya baki yawan rai,jiya da daddare bayan sallar isha’i,mahaifin yarinyar nan da aka yiwa auren shekara daya da yarima Allah ya qara masa lafiya…..yazo ya taddani har cikin gida…” Saikuma tayi shuru,cikin sakanni da basu wuce biyu ba yanayin fuskar fulani ya sauya,ta zuba luba idanu tana kallonta
“Uhmmm,ina jinki,ina fatan jin badai wani abunne zai biyo baya ba,tunda mun riga da mun gama tsarawa da kuma qulla dukkan wata yarjejeniya dasu ko?”
“Allah ya taimakeki,tuba nake,amma kusan kamar baya ce ta haihu”
“Ki hanzarin fayyacemin komai,baya ce ta haihu kamar yaya?” Ta sake tambayar luba kamar mai shirin miqewa tsaye
“Yarinya dai juna biyu gareta” ta fada a hankali kamar batason fadar.
Wani irin rugugin aradu ne ya gifta saman kan fulani aisha,zuciyarta ta wani damqe waje guda na sakanni
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un?,garin yaya haka ta faru?,ya akayi haka?,ya akayi wannan kafar ce kawai.suka bari basu tosheta ba?,saboda tayi tunanin yariman zai kauce mata da.kanshi,tayi tunanin ko bata toshe ta ba shi xai toshe da kansa,tunda yasan irin auren da nau’insa,amma ya akayi basira ta bace mata bata jaddadawa sodangi ba?,me yasa basira ta bace mata bata gayawa ita kanta luba din ba?,ya akayi basira da wannan tunanin aka daukeshi cak daga kwanyarta?,me yake shirin faruwa?,tonuwar asirinsu?.
Batasan ta miqe tsaye har tana safa da marwa ba saida kalaman umma luba suka dawo da ita hayyacinta
“Allah ya huci zuciyarki,ki dade ki qarko,babu abinda zai faru fiye da abinda kike son ya farun”
“Kije zan nemeki” shine amsar kawai data iya baiwa umma luba,saboda ba al’amari bane da zata yanke hukunci da hanzari ba,akwai buqatar tayi zuzzurfan tunani akai,tunanin da ita daya take buqatar yinsa,ta kuma yanke shawarar abinda zai fishsheta,don wannan karon bata da buqatar kowa yaji ko yasan me ya kuma afkuwa.
Da hanzari umma luba ta miqe tana godiya,sallamar data mata a lokacin tayi mata dadi,don dama Allah Allah take ta matsa daga wajen,saboda kwarjinin fulanin dake sake sanyata cikin firgici da dimuwa.
Wunin ranar kaf cikin wani mawuyacin hali tayishi,maganar taketa maimaitawa tana dorata bisa mizani iri daban daban,duk hukuncin data bata sai taga batayi mata ba,tabbatuwar cikin da wanzuwarsa tamkar barazana ce ga duk wani sirri nata da kuma rayuwar azeez,zubewar mutuntakarta taba qima sa darajarta data ahalinta gaba daya.
Ranar kaf bata sake bari kowa ya ganta ba,har zuwa dare sanda take zaune gefan gadonta sanye da kayan bacci,hannunta dauke da cup tana kurbar tea wanda ta tilastawa kanta sha don kada ta kwanta da yunwa,maganar ce dai a ranta take sake juyata gami da yi mata fashin baqi.
Dire cup din tayi da sauri,saboda wata magana da tayi amsa kuwwa cikin kanta
“Karki zama shashasha mana…..daga sun fadi magana ki dauketa gaske…” Maganar ta shigeta sosai,sai tayi tsam da hankalinta tana dora maganar kan ma’auni
“Tabbas talakawa ne wadanda basu da komai,mahaifinta ma’abocin son abun duniya ne,babu wanda yake irin yanayin da suke ciki,wanda xai shiga daula irin haka kuma lokaci daya ayi handing over dashi ya yarda ya karba,ya kuma fita salin alin ba tare daya qirqira wasu abubuwa da zasu biyo baya ba,kudi qalilan sukan ruda irinsu,su kuma sauya musu hali da alqibla,ba shakka zasu iya komai saboda komai yaci gaba da tabbata tsakaninsu,waya sani ma ko sun qirqiro maganar ne don suyi blackmail dinsu.
Murmushi ya kubce mata,sanda ta tattara dukkan bayanan da kwanyarta ta bata na cewa qarya suke,babu wani ciki,sunaso ne kawai suyi amfani da wannan hanyar su dinga tatsar dukiya daga garesu
“Da sun sani bata haka suka biyo ba,tabbas basu san wace aisha ba,da sun fadi abinda sukeso kawai cikin girma da an basu,albarkacin igiyar auren data taba gittawa tsakanin d’ana da d’iyarsu” ta furta a sarari,tana miqewa,sai a sannan taji duk wani nauyi da kanta yayi,da cushewa da cikinta yayi ya warware,har taji wata yunwa,sannan taji tana buqatar abinci,don haka tamiqe ta fito don bada umarnin a gabatar mata da abinci.
¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
Hakanan cikin daren bacci suka qauracewa idanuwansa,ya takurawa kanshi da tuhuma da tambayar me yake damunshi ne haka a kanta,sau nawa ya ganta da zata zauna haka cikin zuciya ruhi da kuma gangar jikinsa,har yake jin kamar yabar wani abu nashi tattare da ita?,kodon itace mace ta farko daya soma sharing ainihin abinda ake kira da rayuwa da ita?.
A hankali ya dauko wayarshi dake dake aje a gefe,hakanan saiya samu kanshi da bude tsohon saqo,tsohon saqon da bai sake bi ta kansa ba tunda aka turo mishi,tsohon saqon da bai taba tunanin xai waiwayeshi ba,sai gashi yau ya samu kanshi da budewa,saqon da ammi ta tura masa na hotonta tun lokacin da ake zancan hada aurensu,yana tunanin idan ya gan hoton zai samu relief.
Saidai tunaninsa ya saba,wani irin abu yaji yana ratsa zuciyarsa,wani irin feeling mai kama da kayi kewa da abinda kayi matuqar sabawa dashi,hankalinsa ya sake tashi fiye da dazun,don haka ya aje wayar ba tare daya fita daga gun hoton ba ya miqe.
Bandaki ya fada kai tsaye,ya sakarwa kansa ruwa,wanka yayi cikin mintina ashirin,sannan ya fito ya soma shiryawa.
Cikin lokaci qanqani ya gama shirinsa cikin wani kyakkyawan yadi da yaji aikin sarauta,yayi masifar dacewa dashi hakanan ya fidda ainihin shi din waye,sai da yagama feshe jikinsa da turarukansa sa’annan ya duba agogo,ya tabbatar yanzun ammi batayi bacci ba,idan ma ba abincin dare take ci ba,to bata jima da gama ci din ba,mai yiwuwa suna falonta ita dasu afnan,kamar yadda takan zauna dasu a yawancin lokuta.