SIRADIN RAYUWA CHAPTER 14
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Ko sau daya bata taba tuhumarsa ko sake tunkararsa da maganar ba,domin yabar maganar tun daga ranar data bashi zabi,ya kuma zabi yi mata biyayya,ya zabi ya faranta mata,ya zabi yabi abinda ta shimfida ta kuma tsara.
Bata manta irin wahalar da yasha a sannan shekaru bakwai baya,har hakan yaso karya zuciyarta,yaso yasa ta karya tsarin nata da hannunta,ya kusan sanyata ta maida hannun agogo baya ta kuma sauka daga kujerar naqin data hau,saidai daga baya ta qarfafawa kanta gwiwa,taci gaba da zama kan matsayin da take kai,duba da abubuwan da zasu biyo baya idan har ta biyewa son ran abdul’azeez din,cikin abubuwan da zata iya fuskanta din kuwa harda kunyata gaban abokan xamanta,wanda ta dade da sanin cewa bata da abokan gaba sama dasu,suna daga cikin mutane dake sahun farko farko dakeson ganin kunyatarta da tozartarta cikin masarautar.
Abu mafi girma kuma dayafi wannan tsanani shine…..hukuncin da zata fuskanta daga hannun mai martaba,wanda wala’alla dukkan wani buri daya dorawa azeez din ya karye bazai kuma sake dawowa ba.
Ci gaba tayi da kallon fuskar tashi sanda yake kusantowa inda take,tana ci gaba da tuna wasu daga cikin abubuwan da suka faru ya yarda ya kawo kanshi zai mata biyayya a sannan,saidai taci wahala ita kanta kafin zuciyarsa ta samu dangana,inda ta masa tukuici da abinda take ganin zai sake sanyashi yayi laushi ya kuma haqura,wato auren SAFWA,anyi auren irin wanda take buri,auren da labarinsa ya fantsama lungu da saqo na qasar,ya kuma bawa maqiya haushi da takaici,hakanan ya tayar da tarxoma tsakaninta da kishiyoyinta,suka dinga duban cewa kome akayi a bikin mai martaba ne ya tsaya musu,ya kuma yi musu barin dukiya fiye da yadda yakeyi aduk sa’ilin daya tashi aurar da diyoyinsa.
Murmushi kawai yayi,ba tare daya biyewa lamari na kishinsu ba,don ya fuskanci duk yadda zai musu bayani ba zasu fuskanta ba,dukkan wata gudunmawa daya dace ya bada ya bayar bakin gwargwado,sauran kuwa ya sani dukka tsarin aisha ne.
Abu guda ɗaya daya fuskanci basu fuskanta ba daga wajen aisha ba wanda yake da yaqinin da sun karanceta da abubuwa da dama.basu gallabi kansu ba dashi,wani irin salon kishi ta iya wanda takan iya dugunzumasu tunani a lokuta da dama,ta manna musu hauka ta kuma nuna kamar batasan ana yi ba.
Ako yaushe takan yi qoqarin yin abunda xai alamta musu cewa ita ce ‘yar gaban goshinsa,koda a muhallin da ba hakan bane,aisha ce matarsa guda daya da bata taba yarda wani yagansu a rana shida ita,komai girman laifin da zai mata komai girman sabanin da zasu samu,zata fitowa ta nunawa duniya lau suke,basu da wata matsala,basu taba ma fuskantarta ba,yayin dasu kuma anasu bangaren basa iya haka,hatta da yaransu sukan samu masaniyar sabanin dake tsakaninsu,saboda qorafi rashin haquri da rashin iya yin shuru aduk sanda wani abu ya gitta tsakaninsu na rashin fahimtar juna,wanda ga aishan sam ba haka bane,bata iya yin haka,wannan yasa ta samu matsayi a wajensa da tazara mai girma tsakaninta da matansa,duk da cewa sun dan girme mata,sun kuma rigayeta kasancewa tare dashi.
Da fari ba safwa ba,ita kanta taci wuya da azeez din kafin a samu daidaito,su zauna zaman aure na haqiqa irin na kowanne ma’aurata,saboda canzawar hali da wasu daga cikin dabi’unsa,kafin daga bisani ta samu abubuwan su daidaita,saidai har a yanzun safwan bata samu kanshi dari bisa dari yadda taso ba,yadda kuma tasha qiyastawa zata samu,kamar bata gabanshi,kamar dole yake zaune da ita,kamar akwai dalilin da yasa yake zaune da ita,tayi dukkan abinda take ganin ya dace kuma zata iya amma har yau bata samu yadda takeso din ba,tayi haquri ta tattara ta zubawa sarautar Allah idanu,tana zaune dashi sabida darajar soyayyar da take masa wanda har yau bataga namiji kamarsa ba,hakanan babu wani haqqinta da bai saukewa,saidai akwai abubuwa da yawa da take da buqata daga gareshi fiye da wannan.
Kamar lokacinsa,kulawarsa tarairaya da soyayya ire iren wadda take gani ga turawa finafinai da litattafan turawa na soyayya,fara’arsa da walwalarsa ta zama wani abu mai tsada da wahalar samu a wajenta,amma dukka ta jure saboda soyayya.
Ajiyar zuciya fulani ta saki sanda yake isowa gabanta,ya qarasa a hankali yadan rungumeta ta gefab kafadarshi daya,tasa hannunta a bayanshi tadan bubbuga kamar qaramin yaro,tana jin babu dadi na yadda fuskarsa take a kullum babu walwala,ya saketa yana miqa mata gaisuwa cike da girmamawa,amsa mishi tayi cikin kulawa da fara’a,kafin daga bisani su wuce zuwa ciki daga ita saishi.
Katafaren teburin cin abinci ne da aka cikashi da kalolin abinci nau’i daban daban na alfarma,da kanta fulani take serving nashi duk kalar abincin dake wajen,harta kammala yana biye da ita da idanu baice komai ba,ta tura komai gabanshi taja kujera itama ta zauna bayan ta tsiyaya tataccen matsatstsen ruwan ‘ya’yan itatuwa tana kurba a hankali,idanunta akanshi.
Sam bata qaunar wannan shurun nasa daya sake zame masa dabi’arsa kuma jinin jikinsa,ta aje cup din tana sakin boyayyar ajiyar zuciya
“Sai yaushe ne su safwan zasu wuce?” Cikin mamaki ya daga kai yana dubanta,kana daga bisani ya cire farin eye glasess din dake idanunsa,yana jin ranshi na baci kadan kadan,kada dai ace wucewarta tayi ba tare da sanin ammin ba
“Tun inacan mukayi waya da ita cewa jiya zasu tafi,ban samu dawowa a jiyan ba shi yasa na gama musu komai daga can…..bata shaida miki ba kenan?” Murmushi kadan ammi tayi,tana jin ranta yana son ya soma baci kan wasu baqin halaye da bata so daga safwan,amma batason ran nata yakai ga baci har azeez din ya karanci hakan,tunda ko babu komai tafi kowa sanin cewa zabinta ce ita din
“Eh to….wala’alla don kada suyi missing flight ya sanya bata tsaya munyi sallama ba” sosai ranshi ya sake baci,koda bata zo ba ai a qalla ta kirata ta gaya mata ko?,baice komai ba ya ciro wayarshi daga aljihun gaba rigar suit din dake jikinsa ya soma neman layinta na brasil,dai dai sanda ammi tace
“Ba wani matsala bace,dama kawai naso na hadasu da sodangi ne,saboda yanayin kula da suhaima din,fata dai Allah yasa aje a sa’a kawai” bai tanka ba yaci gaba da neman layin,duk da yasan cewa ammin tanason dakatar dashi ne.
Qin shiga layin yayi,yayita qoqarin nema bai samu ba,ya tabbatar idan da sun isa ko bai shiga ba zai nuna masa alamun suna qasar,to babu wannan alamar,don haka saiya sauya akalar kiran nashi zuwa ga lambarta ta qasar nan.
Ga mamakinsa sai gashi kiran ya shiga,cikin mamakin ya kasa kunne yana jira yaji me zai faru,babu dadewa aka daga,muryar safwa ce tas tana fadin
“My prince….ka iso kenan?”
“Kina ina?” Ya jefa mata tambayar akwai alamu na bacin rai cikin sautin muryarsa,cike da rashin damuwa da nuna halin ko in kula tace
“Ina gida”
“Wanne gida?”
“Gidanmu wajen mom” idanunsa ya lumshe kana ya budesu,yana son yayi controlling fushinsa
“Ina suhaima?”
“Urppp…..sun wuce ita da mama rahama….zuwa jibi zanbi bayansu,idan ban samu jirgi ba kuma next week,kafin sannan sun gama settling na komai ko?” Kamar zuciyarshi zata fito haka ya dinga ji,magana da itama tamkar bata lokaci ne,don haka ya kashe wayar kawai ba tare daya ce mata komai ba,amma ya sani cewa saiya hukunta tata.
Ya rasa wacce irin uwace ita da har yau batasan cewa ita din uwa bace,har yau kallon kanta take a safwanta,shagwababbiya ‘yar lelen daddynta da mom dinta,bata iya raino nuna kulawa ko tattalin diyar da Allah ya bata ba,baya manta gwagwarmayar da aka sha kafin ta haife suhaima,kullum cikin kuka raki da tsoron ba zata iya haihuwa ba itakam,an gaya mata akwai wahala da ciwo,amma bai zaci wannan banzar halayyar shagwabar mara amfani zata ci gaba da bibiyarta ba,son jiki da rashin son yin komai,sai shegen son soyayya kamar wadda laila da majnun sukayi cikinta.
Duk idanunsa a lumshe yayi wannan tunanin,muryarshi can qasa yace
“Zan soke duk wani abu da nazo yi,zan bisu gobe in sha Allah”muryar ammi da tuni ta gama jin komai ta katseshi
“Ka qarasa dukkan aikinka….babu wata matsala,ka yankarwa kubra ticket zata bisu,bayan ta isa zan tura sodangi taci gaba da zama da ita,har sanda za’a sallamesu”, kai kawai ya kada baice komai ba,wannan bacin ran ya hanashi cin abinci,duk da dama cin abincin nasa ya zama sai a hankali tun lokuttan baya,amma saboda ammin ya daure yadan tsakuri wani abun.
Kiran wayarshi da abdulrashid yayi shiya tadashi,ya yiwa ammi nuni da yana zuwa,ya fice yana amsa wayar.
Bai gama ba har ya isa sashensa,wanda yake a gyare tsaf bayan gyara na musamman da aka masa,aka kuma sauya fasalin tsarinsa da gininsa,ya sake dacewa da zamani,wanda ba qaramin kudi aka narkar ba
“Ka jirani kawai,fitowa dama zanyi yanzun” azeez din ya fada yana katse kiran,lokaci guda kuma yana cire kayan jikinsa sannan ya shige bandaki.
Gaba daya ya baiwa business dinsa muhimmanci da lokaci fiye da komai cikin rayuwarsa,yana jin shine abu guda daya da zai dinga debe masa kewa da rage masa damuwa.
Minti talatin cikakku ya fito cikin rigar wanka,ya samu wata kujera dake daura da gadonshi ya zauna yana goge ruwan jikinsa,a hankali idanunsa suka sauka kan wani dan mitsitsin frame mai matuqar qanqanta dake maqale jikin drower gefan gadonshi,idanu sosai ya zubawa frame din,tsahon wasu sakanni sa’annan ya lumshe idanunsa yana jin yadda bugun zuciyarsa ke dada gudu,ya miqa hannunshi a hankali ya dauki frame din yana dubanta.
Tsahon wadan nan shekarun babu wani abu da ya ragu tattare da ita a zuciyarsa da rayuwarsa,saima qaruwa da yayi,ya sake habaka zuwa wani mataki na daban,kullum yanaji wani sashe na zuciyarsa na faduwa yana rugurgujewa idan ya tuna da ganin da yayi mata na qarshe,duk da yadda kullum kwanan duniya yake qoqarin danne zuciyarsa to amma yana ji a jikinsa,yana kuma tsoron ranar da zuciyar tasa zata bijire,ranar da zata bi karbar umarnin ammin,ranar da zata bijirema dukkan wani umarni.
Cikin jikinta fa?,tambayar da idan ya yiwa kansa yakejin kamar zuciya da qwaqwalwarsa zata fashe,yana jin kamar zuciyarsa zatayi bindiga,dukkan wani bin diddigi da binciken inda take har yanzu bai samu komai ba,bai samu wani qarin bayani ba da zai masa jagora ko ya bashi hasken ina take?.
Jin ya soma shiga wani yanayi wanda idan ya shiga din yakan kwana biyu a birkice ya sanyashi maida hoton ma’ajiyarsa kana ya miqe yahau shiryawa,saidai duk da hakan qwayar idanunsa tuni ta jirkice ta sauya kala,wannan dalilin ya sanya koda ya gama shiryawa ma baqin glass ya sanyawa idanunsa a maimakon fari yadda ya saba,yana ganin kiran safwa ya share,ya sani idan har ya sake ya daga to sakamakon da zai biyo baya bazaiyi musu dadi ba dukkaninsu daga shi har ita,ganin kiran nata ma sake qona masa rai da dugunxumashi yakeyi,don haka ya antayata a black list,wanda ba wannan ne karon farko da irin hakan ke faruwa ba dama,da zarar yaga alamun zata shiga rayuwarshi,abubuwa da dama tana cin daraja da mutuncin ammi ne,da tuni ya sanya kakkaifan gatari ya datse duk wata igiyar alaqa da tayi saura a tsakaninsu,wanda hakan da zai faru sai yafi kowa samun sukuni tare da ci gaba da fuskantar rayuwarsa.
Nannauyar ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar azeez daga falon,tana mamakin halayen safwan wanda ada bata santa dasu ba sai a yanzun,tana jin ba dadi da yadda ta zama wata rabin mutum,wadda tsabar gata da sangarta yasa bata iya tsinanawa diyarta ko mijinta komai,komai zatayi saida taimakon ma’aikata da barori,gaba daya yarinyar kamar ba jininta ba,kamar ba ita ta haifeta ba,bata fiya damuwa da matsaloli da sabgoginta ba sai idan abubuwa sunci tura,gaba daya safwan tazo mata ba’a yadda ta zaceta ba,duk wani data xata daga gareta babu shi,badan badan ba.
Bata jima da jin zancan cewa ta gama haihuwa da safwan tace tayi ba,don tana tsoron mutuwa,mutum biyu ne suka mutu ranar da taje naqudar suhaima a gaban idanunta,to ba zata sake ba bare a wuce da ita,tun tana daukan abun barazana da tsoro da wasu matan kan shiga a lokacin da suka haihu,harta fuskanci da gasken gaske take,tunda har zuwa yau da yarinyar keda shekara hudu bata sauka daga kan qudurinta ba,babban burinta na gaba a yanzu shine ayita haifawa a zeez din yara maza,ta yadda ko nan gaba kambun sarauta da gadon maimartaba bazai bar jikinta ba,ta lura mahaifiyar safwan itama sam bata iya tsaiwa tayi mata wani fada,data soma taga ran ya baci koya sakar mata kuka shikenan an wuce wajen,ba don tana duba wasu abubuwa ba da babu shakka ta sakewa azeez din aure,saidai akwai abubuwan da take dubayya dasu,shi kamsa azeez din tana da buqatar ganin dawowarsa cikin mode dinsa na baya.
Daya daga cikin katafaren kamfaninsa dake da mazauni cikin garin kaisa ya nufa,ziyara ta bazata don babu wanda yasan da zuwanshi,hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,saboda sun san cewa qaramin kuskure zakayi a yau din yayi maka sanadiyyar rasa aikinka.
Ba wanda baisan halinsa ba tun daga sanda ka soma aiki dashi kama yau,mutum mai zafi fushi fusata da tsautsarar ra’ayi,sau da yawa abdulrashid kanyi mamakin yadda ya koma ayau,saidai idan ya tuna girman abinda ke damunshi a rayuwa saiya bashi uzuri,sauda yawa shike qoqarin fahimtar da ma’aikatan kan cewa ba haka halayyar yariman take ba,akwai abinda ya sauyashi,sukan jishi ne kawai,don a haka suka sanshi,kuma a haka suke ci gaba da ganinsa har kwanan gobe basu ga wani abu daya sauyashi ba.
Ya jima sosai cikin kamfanin yana duba abubuwan da suka dace ace ya duba din,a ranar wadanda tsautsayi ya rutsa dasu da yawa sun rasa aikinsu,saidai abdulrashid daya dinga fansarsu kamar yadda ya saba,ya sallamesu da jarin da xai ishesu su kama sana’a.
Sai dare suka koma gida tare da abdulrashid din,don basu gama tattaunawa ba kan abinda ya hadasun,har yanzu ranshi a jagule yake,baya ga mode dinsa na yau da kullum kuma sai case din safwa,abun yana damunshi sau tari,amma a gaban ammin wasu lokuta yakan nuna bai damu,tunda yasan kome ma zatayi zabin ammin ne,abinda ta zaba mishi kenan,duk da cewa duk lokacin da tayi katari yana kan tsininsa baya daga mata qafa ko yi mata da sauqi.
A gaggauce take fitowa zuwa ainihin falon gidan don ta samu abinda zata sanyawa cikinta kafin takai ga fita zuwa asibiti,wanda ayau din tana da tarin ayyuka,ciki harda aiki da zata yiwa yara uku,ba sabonta bane makara sam shi yasa gaba daya hankalinta yayi gaba.
Duk inda ta motsa qamshi ne mai taushi da sanyi yake fita a jikinta,musamman idan kana daura da ita,duk shigar da tayi kyau take mata,musamman shigar da takanyi wadda ke killace komai na jikinta,ba zaka iya ganin komai na jikinta ba,daga fuskarta sai hannayenta,koda qafafunta ma tafi ta’ammali da irin takalman nan da ake kira da half cover,dr bilkess kenan,mace mai aji,wadda ba iya maza kawai take tafiya da imaninsu ba,hatta ‘yan uwanta mata takan burgesu qwarai,da yawa su buraci dama sune ita,ba tare da sunsan tsinin data taka ba kafin takai ga wannan bigiren da take kai.
Babu kowa a falon,dama ta zaci haka,saboda yayi safiya da yawa,don haka ta shiga kitchen ta samu ruwan zafi a kitchen,ta zuba mishi kayan qamshi,sannan ta bude fridge ta dauki samosa fresh one guda uku ta soya,tana daga tsaye ta soma gutsira tana ci,don idan ta fita din ba kasafai take cin abinci a waje ba,har sai ta dawo gida.
“Mamiiiii” taji an fada daga bayanta,ko bata juyawa ba tasan muryar amatu ce,ta waiwaya bayan ta gama wanke hannunta tana gogeshi da tissue tana dubanta,sanye da wani riga da wando pink,wanda yau tashin wurin data yi ya sanya tana gama wanka itama tayi mata ta shiryata,tace ne ta kwanta ta koma bacci abinta sai gashi ta sake biyota,tun daxun dama take nacin zata bita asibitin
“Ya kuma akayi?” Ta tambayeta tana tsareta da ido,saita langabe kai tana shirin sakin kuka
“Please mami,kinmin alqawari fa rannan….don Allah mami na rakaki don Allah” shuru ta danyi,sam batason fiya son zuwa dasu asibitin ba,wani irin farinjini yaran keda shi,wanda yawanci.idan taje dasu asibitin ma basa zama waje daya,daga wajen wannan sai wancan,shi yasa da wuya taje dasu din,saidai yanayin yadda amatun keta mata naci ya karyata,dole ta koma ta sauya mata kaya sannan suka fito tare suka fice.
Suna isa kuwa ta soma jawo mata idanun jama’a fiye da da,wadansun sun santa dama kuma suna son magana da bilkisun babu dama,wasu kuma ganin farko ne,da haka ta samu ta janyeta zuwa office dinta don karta bata mata lokaci.
Minti arba’in da wani abu ta gama shirin shiga surgery din,duk yadda dr adam yaso tabar amatu wajensa amma saita zame,ta hadata da wata nurse dinta mace,don ba zata iya barin mishi diyarta mace ba,duk da cewa bawai tana zarginsa bane,amma tarbiyya ba abar wasa bace,kuma sam bata taba wasa da tarbiyyar yaranta ko qanqani.
Cikin nasara kamar kowanne lokaci ta aiwatar da duka surgery din,bayan ta fito ta daura alwala cikin office dinta tayi sallar nafila raka’a biyu don nuna godiyarta ga Allah kamar yadda ta saba a duk sanda ta gama aiki haka successfully.
Bata jima da idarwa ba,amatu na gefanta tana wasa aka nemi izinin shigowa ta bayar,john ne,tunda ta ganshi tasan magana ce kan wani mara lafiyan,ta saki murmushi tana cewa
“Badai xaku barni na huta ba ko?” Shima martani ya mayar mata kana yace
“Naga kamar kin manta da patient din da kika ce idan sun iso a basu gado,kuma patient ce mai muhimmanci a wajenmu kamar yadda kika sani” baki tadan tabe kadan
“Wannan patient kuna ji da ita,ban manta ba,dole saina kammala komai kafin na ganta,yanzun haka ina dab da zuwa dakin,ba room 1 bane”
“Eh madam” ya amsa mata a ladabce,kai ta gyada yayin da shi kuma ya juya ya fice.
Sai data gama komai sannan ta maida kayanta,ta nada mayafinta da kyau ya zauna mata ta koma neat kamar yadda ta shigo asibitin sannan ta kama hannun amatu suka fito.
Dab da zata isa dakin wayarta ta dauki ruri,ta dakata tana duba mai kiran,nabila ce,qawa guda daya tilo aminiya datayi tsayin shekarun anan qasar brasil,wadda itama zuwau ce kamar ita,saidai Allah ya hada jininsu,ya saka qawance mai qarfi tsakaninsu
“Qawa kada dai ace ba zata kikamin kin dawo?” Inji bilkisu,daga can daya barin akayi dariya
“Kedai bari qawa,mamaki naso baki” daga haka suka soma hira wadda tadanja lokaci kafin suyi sallama,bilkisu ta aje wayar tana murmushi,a sannan ta lura da amatu bata wajen,tadan dudduba bata ganta ba,tasan wajen babu hanyar fita,tafi kyautata zaton ta shiga dakin da sukazo,don haka tayi gaba zuwa dakin,ta murda qofar ta bude kana ta tura kai ciki.
Tun kafin ta gama shiga ta jiyo muryar amatun rai rai,a hankali idanunta suka sauka kansu,su biyu ne zaune gefan gadon mara lafiyas,amatu da yarinyat da duka duka alamu ke nuna ba zata wuce shekara uku ba,sai nurse dinsu dake zaune gaban gadon saman kujera,riqe da cup da plate na abinci tana lallabar yarinyar ta karba,daga can wata kujerar kuma wata macace zaune tana fuskantarsu.
Duk da bata da tabbacin musuluncin matasa lafiyanta amma hakan baya hanata yin sallama a duk inda ta shiga,yanzun ma sallamarta ita taja hankalinsu,anyi katari dukkaninsu musulmai ne,don haka suka amsa mata,ta qaraso dakin hannayenta zube cikin aljihun labcoat dinta,idanunta saman fuskar yarinyar tana qare mata kallo,a haka ta iso gaban gadon tana ci gaba da nazarin kyakkyawar fuskar yarinyar.
“Kinga momy na….zatayi miki allura idan baki qarasa cinyewa ba….kuma ma na fasa qawancen dake idan bakici ba” cewar amatu tana karyar da wuya,da alamu ta damu sosai yarinyar taci abincin,kallon amatu bilkisu tayi,kafin ta maida dubanta ga nurse din dake tsaye bayanta kadan da farantan tana tambayarta meke faruwa
“Tunda suka zo taqi cin komai” hannu ta miqa mata
“Bani” ta amshi kwanukan,duk da cewa ba aikinta bane sai taja kujera ta zauna gaban gadon,cikin lokaci kadan abun mamaki yarinyar ta saki jiki da ita harta cinye abincin,abun daya bawa mutanen dakin mamaki,har amatu da bakinta ya kasa shuru,murna ta cikata na ganin yadda ta cinye abincin duka,itama matar dake zaune a can gefe wanda alamu ke nuna tare suka zo,ita ke jinyarta tace
“Lallai likita kinzo da farinjini,Allah ya qara basira” ta fada da harshen hausa,ba tare da tana da tabbacin bilkisun naji ba,don tunda ta shigo da yaran turanci dukkaninsu suke magana,sai data amsa mata da amin sannan tasan tana jin hausar,hakan kuwa yadan bata mamaki,don ta zaci wani jinsin yaren ce daban ba bahaushiya ba,duba da yanayin kalar fatarta na daban,da kuma qira takyau da Allah ya bata.
“Wanne likita ne yasoma dubata?” Bilkisu ta tambaya tana daukan file guda biyu na yarinyar dake gaban gadon,wanda ke dauke da qunshin dukkanin bayanan ciwon nata,daga dukkan asibitocin da suka taba dubata,nurse din ta bata sunan likitan,saita soma buda file din tana karanta kowanne rubutu dake jikin kowacce takarda tana daga tsaye.
Yanayin yadda taga bayanan ciwon yayi tasiri jikin yarinyar ya bata mamaki qwarai,jikinta yayi sanyi,don da alama ya tabata da yawa,saita soma laluben kujera,tana zama kai lokaci daya tana daga kanta ta dubi amatu data damesu da karadi,ta sanya patient din itama bakinta ya bude ta biye mata sunata zuba surutu,cikin harshen turanci ta mata umarni ta rage sautinta ta barta ta duba file din hannunta,da alama itama yarinyar tana ji,don sai taga itama ta qara nutsuwa ta rage hayaniya,bilkisu ta bita da kallo,tana mamakin yadda ta saki jiki sosai da amatu,kamar sun jima da sabawa,sai taji dadi,don haka zai taimaka wajen warkewa da sake gano wasu abubuwan dake damunta da suka gaza ganowa.
A qalla ta dauki mintuna ashirin kyawawa tana bitar files din kafin ta rufe tana sakin nannauyar ajiyar zuciya,a zahirin gaskiya tabata don yi mata aiki yanzu akwai babban hadari,tana da buqatar treatment sosai kafin akai ga batun aiki,don haka ta dubi matar
“Ina iyayenta?” Ta tambayeta tana kafeta da idanu
“Basu qaraso ba tukunna” cikin mamaki ta maimaita
“Basu qaraso ba kaman yaya?,kina nufin basu qasarma gaba daya?,ba tare kuka zo dasu ba?” Kai ta jinjina mata
“Mamarta dai na hanya,cikin satin xata iso”
“Tana hanya?” Ta maimaita tambayar cike da mamaki,wannan wanne irin careless ne?,wadanne irin iyaye ne haka?,yarsu ta cikinsu amma a rasa mai tattaki ya dafa mata baya neman magani?,saita maida dubanta ga yarinyar,take taji tausayinta mai girma ya kamata,verry innocent,bata san damuwa da matsalolin rayuwa ba banda wannan ciwon daya shigeta,hira take sosai da amatu kamar wadda suka jima ko suka saba,tana ta qyaqyata dariya,har hakan yaso baiwa ita kanta matar mamaki.
Dauke kanta bilkisu tayi tana jin wani abu bayan tausayi game da yarinyar me kama da qauna,ta kira dukka nurses din da tasan suna da alhaki wajen kula da yarinyar ta gana dasu,ta nuna musu duk abinda ya kamata ace sun sani,bata bar dakin ba sai da ta soma bata kulawa,tanayi tana jan yarinyar itama da wasa kamar yadda taga amatun tanayi,ta sake mata sosai kuwa itama kamar yadda ta sake da amatu.
Saida sukazo tafiya ta tubure saidai su tafi tare,matar tayi lallashin duniya amma ta kafe,hakanan bilkisu ta dinga qoqarin mata dabara nan ma taqi,itama amatun ranta a bace da alama batason su tafi,daga qarshe dole bilkisun taja kujera ta zauna,sukaci gaba da wasa har sanda bacci ya dauketa sannan suka samu damar tafiya,matar nata yiwa bilkisu godiya kan yadda ta nuna tsantsar kulawa da qauna.
Ko a hanya hirarta amatun ta dinga mata kamar tasanta,bilkisun na jinta,yayin data lula duniyar tunani,tausayin yarinyar da qaunarta take sosai,da alama bata rasa dukkan gata ba,saidai kamar ta rasa kulawa musamman ta uwa,duba da yadda taketa qanqame bilkisun tana kiranta da sunan momy,har suka je gida zancan amatu kenan,haka ta zauna tayita bawa su abdulrahman labarin.
A daren kasa bacci bilkisu tayi,tanata tunani tare da laluben hanyoyin da zasu bullowa ciwon bayan ta gama amsar treatment na sati guda kamar yadda ta tsara ko sati biyu,bata samu ta runtsa ba sai can tsakiyar dare.
Hakan ya saka washegari koda ta shirya fita aiki idanunta akwai bacci a ciki bai wani isheta ba,saiga amatu itama ta farka tangaran sanda take fitowa daga wanka,tana mutstsuka idanunta tana kallon mamin nata
“Mami…..” Saita langabe kai,bilkisu tadan bata rai
“Meye?”
“Mami yauma don Allah” sake bata fuska tayi
“Ba inda zakije,ki zauna a gida hakanan” daga haka taci gaba da shiryawarta,bata ankara ba taji ta sakar mata kuka,ita suhaima takeson zuwa ta gani,saita saki baki galala tana kallonta,sannan ta soma fada
“Wanne irin sakarcin banza ne da wofi wannan amatu?,da can dake nake zuwa?,kodon kinga kun samu hutu shine zaki tsiri bina?” Daidai lokacin da ummi zuhriyya tayi knocking qofar dakin ta shigo
“Yaya….yaya,waye ya tabamin mutuniyata?” Dauke kai bilkisu tayi daga wajen amatun tagayawa anty zuhriyya abinda ke faruwar
“Yaushe rabon da su biki banda abinki,shirya qawata kuje kinji” tsalle ta daka ta shige bandaki,ta samu abinda takeso,dama already ta iya wanka abinta sosai,murmushi anty zuhriyya tayi tana duban bikisu
“Da tayi zuwa uku zata gaji da kanta,yanzun ma rashin sabo ne”
“Ummi kawai dai kina daure mata qarqashine saboda ‘yar gaban goshinki ce bata laifi,idan hakane shima abdulrahman yace zashi mana” baki ta kyabe
“Ke rabani da wannan sarkin miskilancin tsiyar,duk randa yaji zashin ya magantu da bakinsa,amma nidai tunda yarinyata nason zuwa banga abinda xaisa a hanata zuwan ba” murmushi bilkisu tayi,bata da sauran ta cewa,daga haka suka shiga maganar data shigo da ita.
Bata lura amatu ta debo tarin choculets ba da sauran tarkacen su biscuit saida sukayi nisa,ta dubeta
“Wannan fa?”
“Suhaima zan kaiwa….Allah sarki tana ta cewa daddynta takeson gani,tafi sonshi,shi yake siya mata ya bude mata tasha” shuru bilkisun tayi,har yanzu tana mamakin abinda zai hana iyaye kasancewa da diyarsu,anya ma kuwa iyayenta basu rasu ba?,ba riqonta ake ba?,gaskiya tafi tunanin hakan,tausayin suhaiman ya sake shiga ranta sosai da raya hakan da tayi.
Cikin kwana biyu rak suka wani irin sabawa da amatun,kullum da safe kafin bilkisun ta tashi ma ita ta rigata tashi ta shirya ta zauna tana jiranta,tun tana dojewa ba zata je da ita ba harta haqura ta qyaleta,saiga abdulrahman shima yabi sahun ‘yan zuwa asibiti.
Ranar farko da yaje zama yayi abinshi daga nesa yanata kallonsu,kasancewarsa miskili bamai son surutu ba,duk hirar da suke nashi ido,gadon ya zama kamar wajen jinyar suhaima ne da amatu bawai na suhaima kadai ba,kwana biyar amma kamar sun shekara tare,har ya zamana bilkisun kan qara lokacin tashinta akan lokacin tashinta daga aiki na ainihi,john har tsokanarta yakanyi,yakance patient din da ake jama rai yanzu ta zama best a cikin patients dinki madam,dariya kawai takanyi,itama batasan ya akayi yarinyar ta shiga ranta ba,wala’alla sabon daya shiga tsakaninsu ne da yaranta ya jawo hakan.
****** ***** ******
Tsaye yake gaban ammin yana fuskantarta,sanye cikin wasu hadaddun suit masu bala’in kyau da tsada,wanda suka sake fidda kyakkyawar sura da cikar zatin da Allah ya huwace masa
“Zan wuce ammi,hankalina ya gaza kwanciya,gwara na wuce kawai,sodangin ta biyo ni zuwa jibi” sosai take sake danne bacin ranta kan lamarin safwa,ta fuskanci kwata kwata batasan abinda ya kamata ba,don gaba gadi taketa harkokinta kamar ba wani abu tayi ba,ko jiya da fulanin ta kira mom su gaisa ko hakan zai zame musu tuni game da suhaima safwan harda amsar wayar su gaisa tana sakalcin nan nata,ko cewa akayi kasancewarka d’a guda wajen iyayenka hauka ne?,ita kuma mom din harda cewa
“Wallahi kin ganni inata fama da ita ta tafi,wai sai zuwaira ta dawo su tafi tare,ita batasan ya ake treating mara lpy ba,sai aukin kiran yarinyar a waya ta mata hira,na rasa wanne irin sakarci ne ke damun safwa haka” takaici ya hana fulani cewa komai,sai kawai tace
“Allah ya kyauta”.
“Jibin zamu taho tare ne in sha Allah,kayi mata sannu da kyau kafin mu iso” daga haka sukayi sallama ya fito.
Sassan mai martaba aka masa iso,ya sameshi zaune tare da wasu hakimai,wanda da alama sun gama tattaunawar data hadasu a wajen,don wasu har sun miqe ma,cikin girmamawa ya isa gabansu ya duqa ya gaidasu,kowanne ya amsa cikin jin dadi da kulawa,saida suka fice sa’annan mai martaba ya maida hankalinsa kan azeez,yadan zuba mishi idanu yana kallonshi,shi kansa yadda yakanga sauyi tattare da dan nashi yana sashi a tunani,amma sai yake zaton girma ne da kuma tsabar kasuwanci babu hutu daya sanya a gabanshi
“Dan kasuwa” maimartaba ya dan tsokaneshi,Kasancewarsa mutum mai barkwanci ga jama’a,murmushi ua danyi yana dan saukar da kanshi qasa,yana qaunar maimartana qwarai kamar yadda yake qaunar amminsa,saidai akwai banbamcin halaye,wani sassauqan mutum mai sauqin hali da ra’ayi,mai saurin fahimta da bada uzuri,wanda bai dauki rayuwa da girma ko fadi ba
“Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana” ya amsa mishi cikin ladabi
“Lafiyar dai amin,amma nisan kwana iya abinda muka hadiyo shi zamuyi mu kauce muba wasu waje” ya amsa mishi kamar yadda yakan amsa mishin lokaci lokaci,kai azeez ya gyada kawai sannan yace
“Zan wuce wajen amaryarka brasil” fuskar mai martaba ta sauya
“Idanu dama kawai na zuba maka kaida uwarta ku gama dukka sakarcinku,da ita kanta aishan data zuba muku idanu,bansan rashin hankalin da kuka tafka ba sai a jiya” nan yahau mishi fadan barin suhaima da masu kula da ita kawai zuwa neman lafiya,fada ya dinga yi sosai,kamar yadda ya yuwa fulanin a jiya iya son ranshi,mutum ne shi mai son jikokinsa da basu kulawa,don haka azeez baiyi mamaki ba,yasan zaiyi fiye da hakan ma,ko baya ga haka ma ya tsani yaga an sarayar da haqqin wani ko wanene shi,kanshi a qasa ya bashi haquri sosai,sa’annan yayi masa sallama,bai barshi ya fita ba sai daya shiga ciki da kanshi,ya bada saqon kilishi mai yawa yace akaiwa amaryarsa,yasan yarinyar tana sonshi.
Sosai ya shiga zurfin tunani a mota,wannan karon yanajin indai safwa ba zata iya zama jarumar uwa kamar kowacce uwa ba,to ba shakka zaya dauke suhaima ne ya dinga tafiya da ita duk inda zashi,ko kuma ya karbi sodangi taci gaba da zama da ita a madadin uwarta tunda ita batasan meye ma’anar sunan uwa ba.
Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi yana ambaton sunan Allah sanda jirginsu ya daga daga qasa zuwa sararin subhana,hakanan yakejin wasu baqin abubuwa cikin gangar jikinsa da zuciyarsa,wala’alla doki dason ganin diyar tasa ne ya sanya haka,ya sake sakin ajiyar zuciya yana lumshe idanu,qaguwarsa dason ganin ya sauka a qasar brasil na sake daduwa,ya shiga irgen awanni ko mintunan da zasu sadashi da qasar.
*to me karatu?,shin ya zata kaya ne?,ku biyoni muje zuwa*🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️🏃🏾♀️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️
Duk wani nau’in abinda yasan suhaiman tana so sai daya siya mata kafin ya qarasa asibitin,a sannan babu kowa cikin dakin,daga ita sai mama rahama,wadda keta faman lallashinta kan ta karbi abinci taci,fir taqi yarda taci din,sai fushi da take,ta hade fuskarta tsam,sakamakon rashin zuwansu amatu yau asibitin gaba daya,wanda hakan ya faru ne saboda ba ranar aikin bilkisu bane,ranar hutu ne.
Ƙofar sukaji an turo,sannan lallausar muryarsa da yawancin lokutta take cike da sanyi da taushi tayi sallama cikin dakin,ya shigo idanunshi na akan suhaiman.
Kallo daya zakayi mata ya gaya maka zallar farincikin da tayi da ganin mahaifin nata,badon qarin ruwa dake hannunta ba,badon kuma riqeta da mama rahama tayi ba da tuni ta diro daga saman gadon zuwa wajenshi,hakan daya fuskanta shima saiya qara azama ya qaraso gareta,ya rungumeta tsam a jikinsa yana jin tausayinta,saidai kuma yaji dadi a yanayin daya ganta,wanda ya nuna mishi tana sakun kulawa dai dai gwargwado,don gashinan ta soma murmurewa,akwai alamun raguwar ciwon tattare da ita.
Sai da suka gama daukin ganin juna,ya baje mata dukkan wani abu da za’a iya ci saman gadon tahau hidimarta sannan mama rahama data koma can sashe daya na dakin ta zauna ta gaisheshi cikin ladabi,ya amsa mata sa’annan ya soma mata tambayoyi game da yadda ake kula da suhaiman.
Amsar data bashi ta masa dadi sosai,sai yaji ya qara nutsuwa da asitin da kuma likitar kanta dake dubata,mama rahama tayi murmushi
“Yanzun ma fushi take saboda likitar batazo ba yau tana hutu,bataga amatu diyar matar ba qawarta,taqi taci abinci yallabai” waiwayawa yayi ya dubi suhaima,duk sai ta langwabe,ya miqa hannu ya amshi abincin wajen mama rahaman,ya dubi suhaima ya tsatssareta da idanu sa’an nan yace
“Oya…..gyara ki karbi abinci” babu musu ta aje duk abin hannunta ta tattara hankalinta ga abincin,ya diba ya soma bata a baki.
Daga bangaren bilkisu kuwa ranar ta tashi kamar sauran ranakun hutu a wajenta,takan sake a gida saboda tasan bata da aiki,hakanan ba kasafai ya fiya fita ba,to yau dinma hakane,sunata sabgoginsu da yaran.
Saidai babu jimawa nabila tayi kiranta,wanda kiran nata yasa dole ta fita kenan,mamarta bata jin dadi,tasan kuwa idan bata yakice taje cikin ranakun hutunta ba,ba zata samu fitar ba,don babu inda take sake fita yawanci idan ta dawo daga aiki to tana gida,a yadda suke da nabila kuma bai kamata ba,shaquwarsu tafi gaban hakan,don hakan,bayan ta gama duk wasu ayyukan gida da takewa ummi duk lokuttan da take free,saita shiga bandaki tayi wanka,kana ta tsaya gaban mudubinta tayi shiri mai kyau cikin kayan da duka amsheta matuqa,suka fidda ainihin gayunta da ya riga yabi jikinta ya zame mata jiki.
Tun tana shiryawa ta lura amatu ta kasa sukuni,sarai tasan meke damunta,so take tace zata bita,hakan yasanya ta hade ranta itama tsam babu wasa,harta gama shiryawa ta yiwa ummi sallama ta fice.
Ta samu jikin mamar nata da sauqi,ta zauna cikinsu suka taba hira,bata kashe awa daya ba ta yiwa nabilan sallama tace zata wuce,amma koda zuwa jibi idan ta tashi daga aiki zata sake biyowa taga jikin nata.
A hanya harta dauki hanyar gida sai kuma suhaima ta fado mata a rai,hakanan taji tana da sha’awar shiga asibitin kodan ta dubata koda ita kadai ce cikin marasa lafiyanta,don haka saita sauya alakar motarta zuwa asibitin,cikin zuciyarta tana addu’ar Allah yasa dr adam baya nan.
Tana tsaka da parking wayarta ta dauki ruri,number din assadiq ce,bata daga ba sai daga gama daidaita parking din nata sannan ta sanya hannu ta dauka tana dab da tsinkewa tana yin sallama.
Idanunsa ya lumshe,yana jin sautin muryarta har tsakiyar zuciyarsa kana ya budesu yana amsa mata sallamar
“Nayi miki zuwan ba zata,kuma saina daki gurbi bakyanan” cikin mamakin yadda akayi ya sami adress dinta tace
“Kana nufin gidanmu?” Kai ya gyada
“Yes,kina mamaki ne?”
kanta ta mirgina,murmushi na qwace mata,wani irin qwaqwqwafi ne da assadiq haka?,anya shi din ba lauya bane ko dan jarida ba?,kafin tace komai ya sake magana
“Ayimin afuwa,so nayi na mamayeki,sai kuma gashi hakan bai samu ba….akwai wani batu mai muhimmanci da nakeso mu tattauna ne akai,idan babu damuwa a sake bani lokaci sai nazo mu gana,amma alfarma nake nema,kar a lulani da yawa zuwa wasu kwanaki,kinga nidin matafiyine kuma baqo,akan hanya nake,kwanaki kadan suka ragemin na tattara nabar muku qasarku” murmushi ya sake kubce mata saboda yadda yayi maganar kamar me neman agaji,idan ba gobe ko jibi ba bata da wani isashen lokaci
“Qasarsu dai,mu tamu qasar nigeria take….babu damuwa,kana iya samuna jibi a gidan in sha Allahu”
“Godiya nake qwarai da gaske” daga haka sukayi sallama,ta kashe wayar tana fitowa daga motar,ta kulleta kana ta nufi ainihin cikin ginin asibitin,cikin takunta dake nuna zallar aji kamun kai da isa cikakkiyar mace.
Bata nufi office dinta ba don bata tunanin ma zata shiga tunda ba aiki ne ya kawota ba,kai tsaye ta doshi sashen da dakin da suhaiman take.
Hakanan taji wani mummunan faduwar gaba sanda ta dora hannunta saman qofar da niyyar budewa,sai tsaya cak tana mamakin yadda bugun zuciyarta ya qara gudu.
,taja numfashi sosai cikin hunhunta ta sauke nannuyar ajiyar zuciya,ta bude idanunta dake lumshe kana ta tura qofar dakin a hankali,tamkar barawon dake shirin shiga wani gida yin sata,inda bashi da buqatar a kamashi.
Kadan qofar ta budu,amma tana iya hango wani sashe daga dakin,a hankali ta soma zagayawa da idanunta cikin dakin,mama rahama dake zaune gefe daya idanunta ga bango,da alama plasma din dake kafe take aiki ta tattarawa hankalinta,sai suhaima dake zaune gefan gado ta zuro qafafunta qasa,tana tauna a hankali da alama batason cin duk abinda take ci din.
A hankali idanun nata suka sauka a kanshi,kyakkyawar fuskarshin nan babu yabi ba fallasa,ya tsare diyar tashi da kyawawan idanunshi masu cike da wani irin sirri da kwarjini na musamman,fuskarshi babu yabo ba fallasa,saidai ga duk wanda ya sanshi zai iya cewa a hakan a sake fuskarshi take.
Dubanshi tayi na sakanni biyar tak taji bugun zuciyarta ya sake dawowa,idan idanunta suna gane mata dai dai,wannan business tycon dinne wanda hotunansa da labarinsa ya zagaye ko wanne lungu da saqo na duniya,saidai a yau tana ganin abu mafi mamaki wanda bata taba kula dashi ba tsahon ganin da takewa hotunanshi.
Kamanni na zahiri muraran,kamannin yaranta ‘yan biyunta saman fuskarshi,tamkar kaki yayi ya tofar,wani mugun bugun zuciya data ji fiye da wanda takeji ya sanyata sakin qofar ta koma da baya,ba tare data shirya ba ta tsinci kanta ta doshi qofar office dinta,ta bude kana ta shige zuwa ciki tana jinta cikin wani yanayi da bata tantance wanne iri bane.
“Wanne irin abu kike haka bilkisu?,me yake damunki haka?,daga ganin mutum saiki birkicen?,wala’alla ma babu wata kama da suke,idanuwanki ke nuna miki haka,meye hadinsu da zasuyi kama?” Kanta ta yiwa fada sosai,ita kanta sai taji haushin kanta da kanta,ta miqe ta tsaya gaban dan madaidaicin madubin dake office din ta gyara rollig dinta ya zauna sosai,kana ta dauki jakarta ta fice daga office din bayan ta rufeshi,ta sake durfafar dakin karo na biyu.
A hankali ta sake turawa kamar dazun,saidai a yanzu mama rahama ce kawai da suhaiman zaune,tayi sallama a nutse cikin sassanyar muryarta,cikin zumudi suhaima ke kallonta,bakinta har kunne
“Oyoyo momi…ina amatu na?” Murmushi tayi cikin tsantsar qarfin hali,saboda qamshin turaren da takeji cikin dakin,qamshine daya kama qwaqwalwa da zuciya gaba daya,qamshine daya zauna radama tunaninta tsahon shekaru bakwai,irin qamshin data sani jikin mutum daya,kuma tsahon shekarun bata sake jin qamshin jikin wani mutum na daban ba bayan shi,sai a yau daidai wannan lokacin,sa’an nan cikin dakin asibitin,wanda bata ha kowa a dakin ba face suhaima da mama rahama,don haka ta maida hankalinta kan suhaiman tana cire dukkan wani tunani daya bijiro mata.
Cikin kulawa take duddubata bayan ta tabbatar da cewa komai yana tafiya dai dai,daidai lokacin data gama dubatan ta saqala jakarta wayarta dake riqe a daya hannun nata ta dauki tsuwwa,data duba sai taga sunan anty zuhriyya,babu jinkiri ta daga,magana sukayi ta mintuna biyu sannan ta kashe ta dubi mama rahama
“Zan wuce mama,sai jibi idan Allah ya kaimu,an kirani daga gida ne nayi baqi”
“Babu komai likita,kedai sannunki da qoqari” qarasawa tayi gaban gadon suhaima,wadda tunda taga babu amatu,sannan bilkisun na maganar tafiya tayi kicin kicin,murmushi tayi tana shafa kanta
“Naso na dade kinji baby suhaima,amma jibi da wurwuri zanzo kinji”
“Amatu zatazo?” Sai ta danyi jim,batason mata alqawari kuma bata cika ba,to amma yarinyar ta damu dasu amatun da yawa,zatayi qoqari a kawosu,idan hakan bai samu ba jibi zata qoqarta taho mata da ita
“Idan na samu dama zaki gansu,idan ban samu ba kiyi haquri kinji diyata,jibi in sha Allahu xanzo miki da ita” saita gyada kai a sanyaye,har hakan yasa bilkisun taji babu dadi,yarinyar ta kafeta da ido tana ci gaba da kallonta,kana a hankali ta bude baki tace
“Kice to ina gaisheta” kaita jinjina tana fidda murmushin zallar wayo irin na suhaiman,kamarma wayonta yafi shekarunta yawa
“Zataji” ta sunkuya tayi kissing din goshinta.
Dai dai lokacin daya tura qofar toilet din ya fito,hannunsa riqe da handekherchief guda shida na suhaima daya tsaya wankewa tun dazun,wanda mama rahama tayi tayi ya bari ta wanke amma yace ta barshi zaiyi da kansa.
Yaga sanda aka gama kissing suhaima aka juya,yaga gefen fuskar matar saidai bai samu ganin fuskar gaba daya ba,wani mummunan faduwar gaba yaji ta ziyarceshi wanda baisan dalili ba,kamar wanda aka manne idanunshi a kanta haka ya zuba ma bayanta idanu saboda bashi da ikon ganin fuskarta,harta fice daga dakin cikin nutsatstsen takunta.
Hakanan cikin jikinsa yakejin kamar yasan halittar,kamar ya taba rayuwa da ita waje daya,kamar ya taba sanin wani abu nata.
Sam baisan ya bita da kallo ba,hakanan baisan yaci gaba da kallon hanyar data bi ta wuce ba duk data bacewa ganinsa ba,saida mama rahama tayi gyaran murya,wadda dukka nauyi ya cikata ganin yadda yakebin hanyar da kallo,hakanan suhaima nata masa magana amma sai baijin abinda take fada.
Sashen da mama rahama take ya kalla,kanta na duban qasa tace
“Itace likitar suhaima,itace wadda take magana akanta daxun ita da yaranta take fushi saboda rashin xuwansu” kai kawai ya gyada,sannan ya taka a hankali zuwa gefan gadon suhaima yazauna,yana jin wani mutuwar jiki da kasala,hakanan giftawarta ta kasa barin idanunsa,saiya sanya hannun suhaima cikin nashi yana dubanta,tare da tambayarta me take cewa?.
Washegarin bata samu kaisu ba,hakan ya sanya tayi aniyar tafiya da amatun gobe idan Allah ya kaimu.
***** ****** ****** *****
Tunda ta idar da sallar asuba take saman abun sallarta,hakanan baccin da takan samu ta koma ya qauracewa idanunta,sabanin daa da takan koma ta rintsa koda na minti talatinne zuwa awa daya kafin ta shirya,ya danganta da yanayin sammakon da zatayi,sabanin daa yau din ko kadan bata jin barcin,sai azabar mutuwar jiki gami da kasala da suka lullubeta,lokaci lokaci takanji fargaba da faduwar gaba,hakan ya sanyata ta qara yawa da tsahon azkar din da takanyi duk safiya.
Karfe bakwai ta tashi amatu ta mata wanka sannan itama ta shiga tayi nata wankan,bayan ta fito ta shiryasu duka ita da amatun,dukkaninsu cikin african abaya wadda aka musu dinkin iri daya sak komai da komai,tun wani zuwa da anty zuhriyya tayi nigeria tayi musu tsarabarta dukka matan har ita kanta.
A falo suka samu anty zuhriyya abeed ya tadata yunwa yakeji,ta dubesu tana murmushi
“Yau wace rana ba’a mana gori ba bamu roqa ba za’a asibiti damu” murmushi bilkisu tayi don har yanzu bata jinta dai dai
“Qawa tayi patient a asibitin,su suka uzzuramin zanje da ita na huta da tambayata amatu da takeyi”
“Ai ya kamata…..amma fa ba qaramin kyau kukayi ba,ni sai naga abayar nan tafi kyau da jikinku,kamar yaya da qanwarta” murmushi bilkisu ta sakeyi har haqoranta na bayyana
“Kai ummi…,ai dama tana da kyau baki taba kula bane,bare wannan atamfar da suka ratsa mata ta dace da jikin abayar sosai”
“Gaskiya kam ai sun iya dinkata,ba kamar wadanda na saba gani,inajin idan muka koma saina sake siyan wasu”
“Nima suna burgeni,zan qara wasu kodon fita aiki ma” suna wannan hirar suna karyawa ita da amatun,duk daba wani abun kari na azo a gani bane,saboda dama ba kasafai take jiran abincin break ba na duka gida duk randa zata aiki,musamman idan babu ‘yan makaranta ita kadai zatayi fitar sassafe.
Wayarta ce ta dauki tsuwwa,ta janyo ‘yar mitsitsiyar jakar hannunta me kyau ta fiddo wayar tana duba me kiran,sai taga daga asibiti ne,cikin yana dake nuna gaggawa ta gaske akace da ita
“Dr bilkees….kiyi hanzarin isowa asibiti,akwai matsala mai girma” maganar ta tada mata hankali sosai,tasan tunda aka gaya mata hakan akwai matsalar,don haka ta dire nata cup din ba tare data ida shanyewa ba,ta azalzali amatu ta wuce su tafi.
Gudu tayi sosai ba irin wanda ta saba ba,duk sanda take sake kusantar asibitin gabanta na qara faduwa,har gumi takejin yana tsatstsafowa a goshinta,idan matsala ce ya saba ganinta kala kala,amma batasan me yasa yau din take a birkice ba hankalinta a tashe fiye da yadda ta saba.
Tana aje motar a muhallin ajiyar motoci ta fito ba tare da bata lok
Uaci ba,ta kulle motar kana ta soma takawa zuwa cikin asibitin gabanta na dukan uku uku,sam batau lura da surutun da amatu keta faman zuba mata,data gajima saita dubeta cikin daurewar fuska
“Kimin shuru amatu,tun bansa an maidaki gida ba yanzun nan” gum tayi da bakin nata kuwa,saboda tasan kadan daga aikin ammin tata.
Tun daga nesa take iya hango dakin da suhaima ke kwance,kamar akwai mutanr dai daiku tsaye qofar dakin,sabanin da da bazaka samu kowa ba,data sake wasu taku zuwa wajen saitake jin sauti kamar na sheshsheqar kuka duk da batasan muryar wace ba hakanan batasan wace me kukan ba,amma hakan yayi matuqar fadar mata da gaba,sa’annan ya sake sanyata qara saurinta ta durfafi dakin kai tsaye saboda wani abu da zuciyarta ta soma raya mata,harta saki hannun amatu dake cikin nata ba tare data sani ba,burinta shine kawai ta isa dakin taga abinda yake faruwa.tare.___________
Babu inda idanunta ke kalla a dakin sai gadon da suhaima ke kwance,a miqe take sosai ba kamar yadda ta saba zuwa ta taddata yawancin lokuta tana zaune suna hira da wani ba,likitoci da nurses shida ta taras a kanta,saidai dukkaninsu suna tsaye ne,akwai alamun alhini saman fuskarsu.
Saita kutsa tsakiyarsu ba tare da tace da kowa komai ba,ta isa ga suhaima da idanunta na ke a rufe,jikinta ne gaba daya taji ya hau rawa,guri daya ta taba a jikinta gaba daya taji wani rauni yazo mata,ba wani ba wata yarinyar ta rasu,ta koma ga mahaliccinta,saitaji tana son daina gane komai,ba zata iya ci gaba da tsaiwa ba saboda yadda taji qafafunta na rawa,saita samu jikin bango ya jingina kawai tana son daidaita numfashinta,sai a sannan ta lura da wani mutum fuskarsa kife jikin gadon saitin kan suhaimar,kamar wanda bai dakin baisan me akeyi ba.
Idanunta ta runtse tana jiyo sautin koke koke daga wajen dakin,wanda ta tabbatar da cewa wasu ne da suka jibanci yarinyar,batasan ya zata iya buda baki ba tace musu ta mutu,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,sosai qirjinta yake suya,tana jin tunda ta kama aikinta bata taba mara lafiyar data shiga zuciyarta ba kamar suhaima,bata taba jin qaunar patient dinta ba kamar yadda taji tana son yarinyar sosai har cikin zuciyarta,amma sarkin dake da iko da kowa ya amshi abarsa,saita soma jan qafa ta durfafi qofar fita daga dakin.
Suna nan tsaitsaye kamar yadda ta barsu,saidai bata iya gane fuskar kowa a ciki saboda idanunta cike suke taf da qwalla,riqeta taji anyi
“Likita ke ake jira….bata mutu ba ko?” Dubanta ta maida kan matar dake riqe da ita tana kuka,kuma ita ta jefa mata tambayar
“Saidai muyi haquri,Allahnmu yafimu sonta” abinda ta iya gaya mata kenan matar ta zame a wajen tana sake fashewa da kuka,tabbas da zata iya data tsaya ta bata baki,saidai itama tata zuciyar cike take fak da rauni da kuma alhini,don haka ta wuce zuwa office dinta.
Dai dai lokacin da mama sodangi dake tsaye gefe guda tana matse hawaye tayi toxali da ita sanda take wucewa zuwa office din nata,daurewa kanta yayi,ta shi kokwanton bilkisu ce koba ita bace?,idan itace ya akayi tazo nan?,yaushe ta zama likita?,to amma bilkisu batakai cikar wannan ba,batakai wayewar wannan ba,bata kai gatan wannan ba……saidai kuma batajin akwai lokacin da xaixo ta kasa gane bilkisun,yarinyar da kullum take kwana da ita ta kuma tashi da ita,yarinyar da har yau ta kasa barin kwanyarta,ta kasa mancewa da ita,tausayinta yaqi raguwa daga ranta bare ta manta da ita,amma ga akayi tazo nan?.
Tunaninta yazo dai dai dana afnan,wadda tunda ta fito ta zuba mata idanu,duk da cewa tana cikin alhinin rasuwar yarinyar,amma sai zuciyarta ke gaya mata classmate dinta ce,qawarta ce kuma abokiyar fadanta,wato bilkisu bilyamin,amma ya akayi bilkisun ta zama likita?,bayan tafi kowa sanin auren dole akayi mata,auren dolen da yayi silar tsigeta daga karatun da tafiso fiye da komai,ya akayi ta tsinci kanta a brasil bayan tasan cewa basu da qarfin da zata iya zuwa wannan qasar?,anya ko bilkisu ce?,amma ta yaya zata mantata,bayan kullum saita tunata,kullum da tausayinta take kwana take tashi,da kuma burin son sanin ina take?,ya rayuwa ta kaya mata?,indai ko bilkisu ce to zataso tabbatar da hakan.
Tana isa office dinta ta zare rolling din kanta ta zauna saman kujerar hutawa dake office din,dafe da hannayenta guda biyu ta saki wani irin kuka,hakanan mutuwar ke ci mata rai,tana tuno yarinyar a sanda take raye,tana tuna hirarrakinsu da amatu,zancanta daya biyu abbinta,ba kasafai take maganar mahaifiyarta ba kamar mahaifinta,bata tsammanin kuma duk yadda yarinyar ta damu da iyayen nata sunzo sun ganta har ta koma ga Allah,ranta na mata suya idan ta tuna yadda tazo jiyya qasar babu dumin uwa ko uba a tare da ita,duk da cewa a sannan take da buqatarsu cikin rayuwarta fiye da kowanne lokaci,tunda duka duka shekarunta shekarune qanana qwarai,sosai tayi kuka wanda ta jima batayi irinsa ba,sai mutuwar ta tada mata tabon rasuwar mahaifiyarta.
Tunda ya kifa kanshi ko sau daya bai dago ba,shi ba qaramin yaro bane abinda tayi a gabanshi kadai ya tabbatar masa tun daxun suhaiman ta tafi,jarumi ne na gaske a zuci da fili,ganin kukansa ba kowanne mutum bane ya taba katari dashi ba,uwa uba kuma ya tabbatar hawayensa zai zama silar rasa jarumtar mutane da yawa,hakan ya sanya ya zabi kasancewa a haka har zuwa lokacin da yaji an taba kafadarsa.
Abdulrashid ne tsaye a kansa,ya daga kai ya dubeshi da idanunsa da suka kada sukayi jaa sosai,abdulrashid din yadan matsa kafadarsa alamun lallashi,saiya dauke idanunsa ya maida ga gawar suhaima dake lullube.
Addu’a yayi mata sosai wadda tadan saukar da nutsuwa a zuciyar yarima,kana ya juya ya fice ya sake barin azeez dake zaune a wajen,yana iya jiyo muryoyin ‘yan uwanshi daga waje,ciki harda sautin kukan safwa wadda aketa baiwa baki.
Tsahon wasu mintuna abdulrashid ya sake dawowa,still hannunshi saman kafadar azeez,muryarshi a tausashe yace
“Sunce mahaifi ko mahaifiya ake baiwa certificate of death….likitar kuma ita ke bayarwa,so saidai dana bincika likitar ta fita,saidai xuwa gobe idan Allah ya kaimu,sun rubuta duk wata takarda,ya kamata mu wuce da ita gida,idan anan za’a binneta to,idan ma saimun koma gidane ya kamata asan abunyi” kai kawai azeez ya iya gyadawa,ya miqe cikin qwararawa kanshi gwiwa ya isa inda gawar suhaima take.
Duk da nauyi irin na gawa haka ya dagata ya aza a kafadarshi,ba yadda abdulrashid baiyi ya ajeta a samo abun dauka su dauketa ba amma yaqi ya wuce gaba.
Fitowarsa ta sake rura koke koken da sukeyi,hakanan suka dunguma gaba daya suka wuce zuwa harabar asibitin don su wuce gida a motocin hayar qasar.
Fulani ce qarshe wadda take riqe da safwa tunda ta soma kuka,bata saketa ba kuma sai a yanzun data qara sauri tabi bayan azeez din,ita kanta cike take da alhini sosai,zuciyarta sam babu dadi,hakanan idanunta sun dan tasa saboda kukan datayi na rasuwar yarinyar.
Tayi nisa a tunani taji an bugi qafafunta,ta dawo da hankalinta da sauri gabanta taba furta
“Subha…..” Saidai batakai ga qarasa maganar tata ba ta tsaya saman harshenta,sakamakon ganin da idanunta suka mata na yarinyar da tunu ta miqe ta kwasa da gudu abinta cike da quruciya tayi cikin asibitin abinta,da alama babu abinda ya shalleta da bugewar da tayi dama wanda ta buge din.
Tamkar idanunta zasu fado haka ta bita da kallo,zuciyarta na wani irin bugawa,tunda take bata taba ganin kama ta zahiri ba irin yau,bata taba ganin,to amma shin idanunta ne da suka soma samun damuwa ko kuwa gaskene?,zahiri ne?.
Tana tsaye tana wannan saqa da warwarar har yarinyar ta gama bacewa idanunta gaba daya ba tare data sani ba
“Ammi….ke ake jira,zamu tafi” ta tsinci muryar afnan,wadda ke tsaye bayanta,cikin mamaki kuma tana bin inda taga fulani aishan nabi da kallo tana tunanin me take kallo haka?,me kuma ya tsaidata?,saidai bata ga komai ba.
Ajiyar zuciya fulanin ta saki kana ta soma takawa afnan na biye da ita,hakanan takejin fuskar yarinyar na mata yawo cikin idanu har suka isa bakin motar aka bude mata ta shige.
Hukumar asibitin tuni ta bada ambulance an dauki gawar suhaiman,wanda acikin ambulance din azeez ya tafi.
Mai martaba da yayo waya kawai ya bada umarnin a mata suttura abunneta a nan din,Allah yayi anan qasarta take,kuma akwai musulmai a qasar,hakan kuwa akayi,isu isu suka zauna zaman jimamin rashin yarinyar,saboda ta shiga ran da yawa daga cikinsu,musamman kasantuwarta ta fito daga tsatson mutum mafi soyuwa a zukatan al’umma cikin masarautar,sai waya da suke amsa daga ‘yan uwa da abokan arziqi dake nigeria ta tayasu ta’aziyya.
Ta bangaren bilkisu kuwa kukan data sha yasaukar mata da ciwon kai sosai,hakan ya sanya ta tattara ya nata ya nata ta wuce gida kawai,ba tare data tsaya cike takaddun da tasan dole zatayi ba saboda patient dinta ce ta rasu,amma tunda taga office din dr adam na nuna alamun yana nan,saita wuce din kawai,yasan zaiji da komai,a harabar asibitin ta samu amatu ita da wata nurse da tasu tazo daya,ta amsheta suka wuce zuwa gida.
A hanya amatun keta mata surutun ya zasu koma bata ga suhaima ba?,batace da ita komai ba,donta fuskanci batasan ta rasu ba,batasan kuma ta yadda zata gaya mata ta fahimta ba,haka yarinyar ta haqura tayi shuru,don tasan halin maman natasa sarai,aduk sanda suke mata surutu irin wannan indai sukaga shuru taqi amsasu to batason magana ne.
¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
Misalin qarfe tara ne na dare agogon qasar brasil din,dai dai lokacin da yarima ke fitowa daga wanka,jikinsa sanye da rigar wanka wadda iyakacinta qauri.
A hankali yake takowa tsakiyar dakin,jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarukan wankanshi,akwai qaramin towel a hannunshi yana goge ruwan jikinsa.
A yau yana jin sauqi cikin zuciyarsa fiye da kullum,yana jin haquri da danganar rashin tilon diyarsa yana shigarsa,saidai abune da yasan cewa bazai taba mantawa dashi ba.
Har ya isa gaban mudubi ya soma shafawa lallausar fatarshi mai saiya jiyo sheshsheqar kukanta,sam yama mance da ita cikin dakin,saboda yadda a kwanakin gaba daya ya sake dauke mata wuta fiye da yadda ta sanshi,saiya waiwaya sashen daya jiyo kukan yana kallonta.
Tana zaune takure waje daya,ta rungume gwiwoyinya a qirjinta,jikin gwiwar tata ta kifa hoton da yake da tabbacin na suhaima ne,saiya waiwayo gaba daya ya jingina da madubin gami da rungume hannayensa a qirjinsa gami da xuba mata idanu yana kallonta.
Cikin kwana uku ta fige ta rame,idan ka ganta saika zaci takaba take,zuciyarsa takanyi zafi a duk sa’ilin daya tuna yadda tayi watsi da rayuwar suhaima,tamkar bata damu da ita ba,koma na itace ta haifeta ba,hakanan yakanji zafi sosai idan ya tuna tahowar yarinyar wata qasa ba tare da mahaifiyarta ba,yaci alwashin hukuntata fiye da tunaninta kan abubuwan da take aikatawa harsai ta gane kuskurenta,to amma yanayin da yaga ta shiga yanzun yasa dukka wasu makamanshi suka zube,tausayinta ya soma kamashi,yasan cewa duk yadda uwa takai ga nuna halin ko in kula ga danta,ba qaramin dukanta zaiyi ba aduk randa akace yau babu shi a duniya,sai tafi kowa girgixa da jin xafi,kamar yadda a yanzun ya bayyana qarara kan safwa din,wannan dalilin ne kawai ya sanya yaji ya kamata yadan kawo sassauci cikin yadda yake matan,koda ba duka ba.
A hankali yake takawa har zuwa inda take zaunen,saiya zauna daga gefanta,ya saka hannunshi ya zare hoton ya aje gefe,sannan ya janyota zuwa cikin jikinsa.
Gaba daya ta shige ingarman qirjinsa tana sake sakin wani sabon kukan,wanda ke nuna dama tallafinsa take da buqata,ta cukuikuye gaban rigarshi sosai tana sakin kukan.
Baice mata komai ba sai hannunshi ɗaya daya saka yana shafan saman kanta,idanunshi na kallon wani waje daban,yayin da launin qwayar idanunsa ke soma canzawa,yana tuna abubuwa da yawa,wanda bai tsammaci zasu zo mishi ba a wannan lokacin.
Ya tuna sanda wata ke masa kuka mai bayyana pain da zuciya ke ciki shigen wannan,amma a lokacin bai tsaya ya mata wani dogon lallashi ba,hakanan yakan tuna wataqila har yanzu a doron duniya akwai wata halitta dake dauke da ciwo mai daci shigen wannan a zuciyarta tana rayuwa a haka,me yasa?,anya kuwa lokaci baizo ba da zaibi diddigin tsohuwar alaqa ba?,anya kuwa lokaci baiyi da zai bazama ya tono wannan alaqar da take da buqatar abincikata ba?,yana ji a jikinsa zuwa yanzun koda ya bijirema ammi baida laifi,Allah ba zaya kamashi ba,saboda ya cika mata dukkan wani burinta data qudirta akansa,ya cika mata dukkan wani qudirinta?,to me yayi saura?,ya nemota ya sauke haqqin dake wuyanshi,ya nemota duk inda take.
Tsahon wani lokaci kowannensu yana fama da tabo da ciwon dake cikin zuciyarsa kafin ya sauke ajiyar zuciya mai qarfi har qirjinsa yana dagawa,safwa dake kwance saman qirjin tayi luf bayan ta gama kukanta tana shaqar daddadan qamshin da jikinsa ke fiddawa duk da bai shafa kowanne turare ba,amma qamshi yabi jikinsa,ya kuma zauna masa sosai saboda tsabar yawan tu’ammali dashi da yakeyi kowanne lokaci
“Shikenan ta tafi my prince?,ta tafi ta barmu?” Saiya dagata daga qirjinsa,hannayenshi saman kafadunta yana kallonta
“Haka Allah ya tsara,kuma yadda yakeso haka za’ayi,koda mu ya kira dolenmu muje,bamu da wani sauran uzuri….idan bawa yayi haquri mai kyau sai hakan ya zame masa alkhairi nan gaba” kalamai ya gaya mata masu kwantar da hankali da sanya nutsuwa,sannan daga qarshe ya sanyata ta shiga tayi wanka ko zataji sanyi cikin ranta.
Shiryawa yayi shima ya sanya kaya sannan ya bude qofar dakin ya fita.
Falon gidan ya bulla,wanda yake dauke da dakunan da fulani mama sodangi,afnan da sauran barorinta suka sauka,don mom din safwa kwana biyu sukayi suka koma,don haka gidan saisu yasu.
Kitchen ya shiga da kanshi,yunwa yakeji amma kwana biyun nan baya iya cin wani abincin kirki,har ita safwan ya lura da haka,don kafin tafiyar mom dinta yasha jin tana artabu da ita.
Fresh milk mai sanyi ya ciro kwali biyu manya,saboda sosai yakejin cikinsa a fafake,mutumin daya saba baya wasa da cikinsa sam,ya dauki cups guda biyu sannan ya juya ya fice daga kitchen din.
Yana fitowa fulani itama na fitowa daga nata dakin sukayi kacibus,cikin kulawa take dubanshi da kwalin madarar hannunsa
“Da kayi magana idan kana da buqatar wani abun,basai ka shiga kitchen da kanka ba” duban kwalin madarar yayi shima sannan yace
“Ba wani abu,ita zan dauko kawai dama”
“Kana nufin madara kawai zakusha a abincin dare?” Tayi maganar tana juyawa gami da samawa kanta wajen zama,ganin haka shima saiya isa daura da ita ya zauna yana amsa mata
“Ta ishemu,ba wata babbar yunwa bace” kai ta girgiza
“Ban aminta ba,kwana nawa rabonka dakaci abinci,ina sane fa….” Kafin yace komai ta qwalawa afnan dake daki kira,a sannan tana waya ta sauko daga gadonta ta qaraso cikin falon da wayar a hannunta,don bata tsammaci harshi yana wajen ba.
Ganinsa awajen ya sanyata saurin katse wayar,ta soma qwaqule earpiece din dake kunnenta kana ta qaraso tana hardewa,saboda yadda ya kafeta da idanunsa masu dan banzan kwarjinin nan
“Gani ammi”
“Shiga kitchen ki samawa yayanku wani abuncin mara nauyi haka wanda bazai dauki lokaci ba” amsawa tayi da to sannan ta wuce ciki da sauri,ta sanya afnan ne saboda tasan duk wanda ta saka ya masa ba lallai yaci ba.
“A ina maganar yarinyar nan ta tsaya ammi?” Yarima yayi magana yana duban ammin tasu,fuskarta ta nuna alamun alhini kafin ta amsa mishi
“To….ana nan dai ana addu’a,ina kyautata zaton mijin auren ne har yanzu baizo ba,tunda koda yaushe addu’a ake,hakanan duk wanda yaxo ba korarsa take ba,ana bashi dama,Allah ne kawai baiyi ba” shuru yayi kawai yana dan tunani a ranshi,dukka yaran gidan banda ‘yar wajen fulanin masanawa afnan ce kawai ta rage gaban ammin,wani lokaci yakan qalubalanci mace ta zurfafa karatunta yayi zurfi da yawa ba tare da wani tsayayye ko gamsashshiyar magana a kanta ba,wasu mazan sai su dinga mata kallon tayi girman datafi qarfinsu koda ba yawan shekar gareta ba,misali ga afnan din da karatunta yake zurfi a yanzu,uwa uba kuma ta fito daga babban gidan sarauta dayake da dumbin arziqi tarihi da nasaba,ba kowane zai iya fuskantarta yace yana so ba,duk da bata rasa komai ba daya danganci kyau kyakkyawan hali nasaba da tarbiyya ba
“Allah ya zaba abunda yafi alkhairi”
“Ameen” ammin ta amsa tanajin babu dadi a ranta.
Dukkan abinda ta burata a duniya babu wanda Allah bai mata ba,amma saiya zamana afnan din ta zama ta takashin baya ta fannin aurarwa cikin gidan,wannan shine abu qwaya daya tilo dake damunta a yanzu,bata kuma ta hanyar da zata maganceshi kota kawo qarshensa,wanda har abokan zamanta manyan abokan adawarta ke samun abun goranta mata da yada mata magana a yawancin lokuta,sauqinta ma duka yayyenta aka aurar babu sa’anninta da aka aurar bare abun ya ta’azzara,itace auta.
Tunaninta ya sake nisa,fuskar yarinyar da yadda ta bugeta kana taci gaba da tafiya abinta cike da quruciya,abun yakan yi mata yawo aka,yana kuma dawo mata akai akai,saidai tunani guda daya dake sanya mata relief kan wani hasashe da zuciyarta ta soma mata,hasashen data kira da banzan hasashe mara tushe bare makama shine,bata ga hanya ba ko,hakanan bataga hadinsu da wannan qasar ba,bare tace hasashen da zuciyarta ke mata ne ya tabbata,babubta wata hanya da hasashenta zai iya zama gaskiya,saita saki ajiyar zuciya tana jin nutsuwa kadan kan tabbacin da daya sashen na zuciyarta ya bata.
*_da sannu sannu dai kunkuru zaije inda jirgin sama yaje wata rana,kada ku damu,ku zama masu bibiya cikin nutsuwa ba tare da gaggawa ba😊😊_*
⁵³