SIRADIN RAYUWA CHAPTER 15 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 15

 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

       Mintina qalilan afnan ta dawo ta kammala,ta miqa masa plate din dake a rufe,da idanu ya mata alama takai mishi daki,saita juya zuwa dakin,cikin ranta tana mita da qunqunin rashin ganin amfanin matarsa,da ba zata iya tsaya masa kan cikinsa ba,da sun hada muhalli saidai su suyita hidima dashi,komai tafison a mata tana daga zaune yadda take tun daga gidansu.

        “Munyi waya da mai martaba,yace ya kamata mu dawo gida hakanan,saboda jama’ar dakeson yi muku gaisuwa” kai ya jinjina sannan yace

“Kamar yaushe ya kamata kenan mu tafi,tunda ticket kawai zamu siya” dan shuru tayi kadan sa’an nan ta dora

“Idan ba damuwa nan da jibi ya kamata mu wuce” ya sake jinjina kanshi

“Shikenan,babu damuwa,gobe zanje na karbo certificate din mutuwar suhaima,jibin saimu wuce in sha Alla” ajiyar zuciya fulani ta sauke mai nauyi sannan tace

“Allah yayi mata rahama”

“Ameen ameen ya Allah” ya fada yana sadda kanshi qasa,shuru ya ratsa falon na wasu mintuna,sa’annan ya miqe yana yiwa fulanin sallama ya wuce xuwa cikin dakin.

       Ya tars safwan tayi wankan tana zaune gefan kujera shuru ba tare da tana yin komai na,idanunta a kode suke sosai,ya qaraso ciki yana dauke idanunshi daga kanta,dab da ita ya zauna ya aje kwalin madarar saman wani dan qaramin tebur,sannan ya bude ya cika cup ya miqa mata,shuru tayi kamar ba zata amsa ba,amma ganin yadda ya tsareta da idanu ya sanyata tilas ta miqa hannu ta karba,ta soma kurba a hankali shi kuma yana ci gaba da kallonta,har sai data sha fiye da rabi sannan ta ajjiye masa tace ta qoshi.

       Baice komai ba shima ya bude kwali guda ya soma kurba shima a hankali,sai daya sha kusan rabi sa’annan ya lumshe idanu yana aje numfashi bayan ya jingina jikinsa da kujerar.

¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

    Fashin da tayi na kwana biyu saboda ciwon kan data dawo dashi tun ranar mutuwar suhaima ya sanya a ranar larabar ta shirya da wuri don tafiya asibitin,a kwanaki biyun tayita fama da wayar dr adam kamar zaya zo ya dauketa,yayi mita yayi qorafi kan rashin bashi adress na gidansu yafi sau shurin masaki,amma yaci mata alwashin kome zatayi bazaya janye ba,ta kuma rubuta ta jjiye,saiya lalubo gidansu duk inda yake,hakan daya fada ya bata dariya,don haka saita saki murmushi kawai ba tare data ce masa komai ba.

        Yau kam free take tasan amatu ba xata takurata kan zata bita asibiti ba,don anty zuhriyya ce zata biyo ta dauketa ita dasu amatun,zasuje bikin sunan wata matar abokin abbaa data haihu,to kasancewar suna garine da kowa baida wani nashi sai suka zama tamkar ‘yan uwan junansu.

         Tana gaban madubinta tana shafa tsadajjen manta saqo ya shigo wayarta dake aje gefanta tana chargy,saqo ne daga assadiq,ta sanya hannu ya shafa wayar kana ta bude saqon

_saqon fatan alkhairi gami da tashi lafiya zuwa ga sarauniyar kyawawan duniya,kuma mai mulkin zuciyata,da fatan kin wayi gari cikin qoshin lafiya,Allah yasa ana nan ana tunanin yiwa wannan zuciyar data kafu a donki adalcin da zai sanya ta dore ta kuma ci gaba da rayuwa,ki huta lafiya saraniya_

       Murmushi ta saki,ire iren saqonnin dr adam kenan dake cike fal cikin wayarta,saita maida idonta ga madubin tana duban kanta gami da tuna maganar da assadiq din yazo mata da ita ranar data bashi izinin zuwa gidansu,bayan ta fito da hijabi dogo har qasa mai hannu ta tarbeshi,suna zaune saman wasu kujeru dake jere a yalwataccen balcony na gidan.

       “Allah yasa sauyin rayuwa da tsahon xamani baisa kin manta cewa assadiq yana daya daga cikin tarin masoyanki ba,idan ma ke kin manta shi bai manta ba,kuma zai saki tuna miki da jaddada miki” saiya gyara zamanshi yana dubanta

“Kamar wancan karon ni assadiq naga bilkisu,kuma ina sonta,ina qaunarta har jinin jikina,hakanan inason na aureta ta zama matata ta sunna,ina buqatar hadin kanki qwarai da kuma soyayyarki,banason na sake rasaki kamar wancan karon,kimin alfarma don girman Allah” kalmarshi ta qarshe ta mata nauyi qwarai,saita sadda kanta qasa tana wasa da yatsunta,maza da dama sun sha neman soyayyarta,mutane iri daban daban,to amma tunda can tana jin wani nauyi na assadiq da qimarsa,don haka ta buda baki a hankali tace

“Na gode sosai da kaci gaba da daakon soyayyata tsahon wancan shekarun baka sauya ba har kawo yau,naji dadi sosai da soyayyarka gareni,idan so samu ne muci gaba da addu’a gaba daya nida kai,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi,yasa gobenmu ta haifar da kyakkyawar natija me kyau” duk da cewa bata fito kanta tsaye ta amsheshi kota koreshi ba,amma amsarta tafi masa kama da cewa yaci gaba da neman soyayyarta,duk da cewa ba’a bashi dama ta kai tsaye ba,amma hakanma yayi masa,yana fatan nan gaba ya samu amsa takai tsaye gamsashshiya.

        Dai dai nan ta sauke ajiyar zuciya,ta miqe tana isa ma’ajiyar kayanta dake shaqe da dumbin suturu kala kala,masu mabanbantan kudade,ta zabi ta shirya cikin daya,cikin qananun mintuna ta shirya kanta tsaf,ta kalli kanta a mudubi,sai taga kamar yau tafi kyau fiye da kullum,ayau saita hangi kyau tsari kwarjini da ajin da maza ke yawan gaya mata tana dashi,harda wasu daga cikin ‘yan uwanta mata.

        Sakin wannan tunanin tayi don bataga amfaninsa ba,ta dauki duk tarkacen da tasan zata tafi dashi,sannan ta zira takalminta da jakar hannu wadanda dukkaninsu duka dace da sutturar jikinta ta fito.

        Sanda ta gama parking motarta tana shirin kashewa ta hangi motar dr adam a gefenta,ta dauke kai da sauri tana addu’ar Allah yasa bai ganta ba,sai taci gaba da zama cikin motar tana so ya wuce ciki sannan itama ta shiga,don ta tabbatar idan ya ganta,zai tilastata saisun jera ne har ciki,ita kuma abinda bata so kenan.

        Saidai kuma addu’ar tata bataci ba,don tana tsaka da zaman taji ana knocking glass din motar,tun kafin ta bude taga shine,bata da sauran zabi illa ta fito kawai,don idan bata fito din ba shi shigowa ciki xaiyi abinsa,don haka ta dauki kayayyakinta ta bude ta fito.

       Fuskarsa cike da murmushi yake kallonta,ya bude baki cikin farinciki yace cikin harshen turanci

“Kyakkyawar laraba ce yau,naji dadi sosai da ganinki,yau inda bakizo ba,zansa mommy ne da kanta ta kiraki,ta kuma roqarmin alfarmar ki bawa danta adress din inda zaije ya ganki,tun kafin zuciyarsa ta buga” ya miqa hannu yana amsat kayayyakin hannunta,duk da bataso sakar masa ba,amma batason jan doguwar magana,dole murmushi ya subucewa fuskarta na furucin da yayi

“Bakajin kunyarta yanzu dr?” Idanu yadan fidda

“Au,ku a hausa fa abun kunya ne ko?” Sai ta soma takawa tana yin gaba ba tare data bashi amsa ba,tana bin kan tambayar tasa da gaisuwar ina kwana,ya biyota yana amsawa tare da qoqarin daidaita kafada da ita.

         Abinda take gudu dai shi yayi,dolen sai daya jera da itan,suna tafe suna haduwa da ma’aikata,suna gaidasu cikin girmamawa da mutuntawa,tun daga lokacin da kowa ya fahinci soyayyar da yake mata suke bata wani irin girma,tamkar itace dr adam din,wannan ya janyo mata hamayya daga wasu daga cikin likitoci mata dake nacin neman soyayyar dr adam din basu samu ba,saidai ita din ko a jikinta,dukansu basu dameta ba,don a rayuwarta ta yanzun ba komai take bari ya dameta ba,tace ta gama samun damuwa tun asubar fari ta rayuwarta,yanzu kuwa da komai ya warware mata bai kamata ta bari qananun abubuwa irin wadan nan nason dagula lissafinta ba.

        Bai barta ba kuwa sai da suka dangana da office dinta,don shi ya bude mata ma,yana aje mata kayan saman kyakkyawan table dinta ne yace

“Har yanzu mutanen nan basu karbi certificate na rasuwar yarinyarsu ba” ta daga kai ta dubeshi

“Na zaci tun ranar dana tafi ka sallamesu” kai ya girgiza

“Nima hankalina ba akwance yake ba,saboda yadda kika fita din na tabbatar ba lafiya ce ta kawo hakan ba” kafada ta gyada

“Ba damuwa,nan da awa daya komai xai kammala,koda sunzo zasu karba babu matsala” da qyar tasamu ya tafi nashi office din ya bata waje,bayan ya ritsata,ya kira mommynsa ya bata wayar suka gaisa.

        Batura sosai,babu ruwanta da wata kunya ko kwana kwana,hira take da ita kai tsaye,tana kuma sake roqarwa danta soyayyarta,sun dan jima kan wayar kafin suyi sallama ta bashi wayarsa ya tafi tana masa mita shi kuma yana dariya.

         Sai data gama rubuta certificate din,tayi waya daga dakin buga takardu na asibitin sukazo suka amsa sannan ta fita ita da nurses din dake team dinta,ta soma duba marasa lafiyanta,wadanda dr martin ne ya riqe mata su har zuwa yau data dawo.

         Ta shafe tsahon lokaci sosai tana duba komai,sai data tabbatar komai da kowa lafiya lau,kuma komai ya tafi daidai sannan ta nufi komawa office din ta duba sauran ayyukan dake gabanta.

        Tana shirin bude office dinnata taji ana dan kiranta da yanayi na girmamawa,ta waiwaya,daya daga cikin ma’aikatan dake buga takardunne riqe da certificate din,komai ya kammala kenan ya miqa mata,hannu tasa ta amsa tana masa godiya kamar yadda yake a al’adarta,ta tura qofar tana karanta rubutun jiki tare da lissafa adadin kwanakin da yarinyar tayi yau a qarqashin qasa

“Ranki ya dade akwai baqo” taji an fada da harshen qasar daga bayanta,ta waiwaya tana duban daya daga cikin ma’aikatansu ne

“Baqo daga ina?”

“Wai certificate xai karba” kai ta jinjina,mahaifin suhaima ne kenan,dama akwai maganar da takeson mishi,kan barin yarinyar da akayi babu uwa ko uba har wata uwa duniya,abun ya sosa mata rai,yana kuma ci gaba da sosa mata rai

“Ka bashi izini ya shigo” ta fada tana shigewa ciki shi kuma ya juya.

       Saman kujerarta ta koma ta zauna tana dan juyata kadan kadan hagu da dama tana dakon shigowarsa,ganin wasu mintuna sun shude bai shigo ba saita ciro eye glasses dinta ta sanya,ta janyo takardar wani patient dinta ta soma dubawa saboda rage lokaci.

      A hankali ya turo qofar office din bayan an bada izinin shigowa,sanye cikin trouser da shirt mai gajeran hannu,kalolin da suka masa kyau suka kuma bada ma’ana a jikinsa,qafarsa na saye da rufaffen takalmi,kanshi babu hula sai sumarshi da take zuba qyalli saboda kyau da tayi na gyaran da tasha,duk da ba mai yawa bace sosai,yanayin askin dake fuskarsa ya sake qawata zallar kyau da kwarjinin da Allah ya bashi,hannunshi daure da agogo rolex mai azabar tsada da kyau,sai gilashin idanu dake saman fuskarsa wanda ya kuma qarawa adonshi kyau da kwarjini,.

      Tunda ya shigo yake daukan hankulan mata kala daban daban cikin asibitin,musamman wadanda suka san nauyi da tsadar motar daya fito daga cikinta,takunshi kawai abun daukar hankula ne,duka wannan bai dameshi ba,baisan ma me ake ba,fuskarshin nan babu ko digon fara’a a cikinta,ba zakace ya taba dariya a duniyarshi ba.

        Maida qofar yayi yadda take saboda bin doka da qa’ida irin nashi,kana ya maido kansa cikin office din da niyyar yin salla.

       Cak kalaman bakinsa suka tsaya saman harshensa,maqogwaronsa ya kada fidda wani sauti bare harshensa ya motsa,tamkar an kafe dukkan ganinsa saman fuskar dake kallon takardar dake riqe a hannunta,kamanninta suka dinga bayyana cikin idanunsa a wancan shekarun da kuma yanzu.

       Sune dai,wadan nan kamannin daya jima da sani,wadan nan kamannin da suka hana rayuwarshi sukuni tsahon shekara bakwai da watanni,duk da cewa akwai bambamci mai tarin yawa,da suka bayyana qarara,tun daga yanayin fata,dressing da kuma yanayin ilimi gogewa da kuma wayewa.

       Amma bayajin koda shekaru dubu ne suka shude matuqar ruhinsa yana cikin gangar jikinsa wannan fuskar mai tarin daraja qima da martaba idanunsa ba zata taba bace masa ba,yanajin koda an mata sauyin fuska jikinsa zai gaya masa cewa tana tare dashi,ruhinsa xaici gaba da gaya masa cewa itace a tare dashi.

        Baisan ta yadda ya isa gaban table din nata ba,baisan yadda akayi yakai kanshi gabanta ba,yadai tsinceta tana daga fararen manyan qwayoyin idanunta dake ta walainiya kamar an diga musu mai ta dubeshi bayan qamshin turaren daya sanya mata matsananciyar faduwar gaba ya ziyarci hancinta,taso ta daure amma saita tsinci zuciyarta na gudu fiye da kima,bayan batasan daga inda qamshin ke kutso kai ba,hakan ya sabbaba mata dole ta daga kanta tana dubanshi,babban shahararren matashin attajirin dan kasuwar duniyar nan ta gani tsaye a gabanta,me ya kawoshi office dinta?,bata sani ba,saita tsuke fuskarta sosai tana ci gaba da kallonshi tanason jin me ha shigo dashi?.

       Kamanni na zahiri data sake gani saman fuskarshi irin da twince din ta yasa wani faduwar gaban ta daban ta sameta irin wadda bata taba jinta ba,dole badon taso ba taji idanunta na lumshewa,cikin zuciyarta ta ambata da sauri

“Subhanallah….ya ubangiji….ka sanya baida alaqa da mahaifinsu ko wani nashi,Allah ka sake nisanta tsakaninmu dasu” saita kuma bude idanun nata da sauri.

      Ta zaci zata sameshi a zaune ko kuma ya fita,saita sake ganinshi still dai a tsayen,hannayensa goye a qirjinsa,ya kafeta da idanunsa da takejinsu da wani irin nauyi a qirji da gangar jikinta,wani irin kallo da takejinsa ya bambamta da sauran kallo na kowa da kowa,qwayoyin idanuwa da bata taba ganin masu nauyi da kwarjini irinsu ba.

       Can daga wane sashe na zuciyarta ya zaburar da ita,tayi hanzarin maida hankalinta tana janye idanunta daga kanshi tana daukar takarda ta gaba dake gabanta,tana kuma sake tamqe fuska,tare dajin haushin yadda yazo ya tsaya mata akai,kamar wani bodey guard,ba kuma tare da taji sallamarsa ba har ya zuwa yanzu,da harshen turanci tace dashi

“Lafiya malam?,ka shigo wajen mutane babu sallama,kuma ka tsaya haka a kansu ba tare dayin bayani ko fadin dalilin shigowar taka ba” ta qarashe maganar tana duba takardar,saidai zallar mamakin kamanni da razana dake tattare da ita suna nan,kunnuwanta kuma na gareshi tana son taji me zayace,saidai tsayin wasu mintuna shuru,hakan yasa ta fusata,ta sake daga kanta cikin masifa tace

“Kaga….idan baka da abun fada kana iya fita ka tafi,akwai tarin ayyuka gaba na”.

       Ga dimbin mamakinta sai taji ya damqi hannunta dake riqe da takardar,wanda yayi hakanne don son tabbatarwa da kanshi ire iren mafarkan daya saba yine ko kuma zahiri ne wannan?.

       Cikin tashin hankali ta fincike hannunta tana dubanshi,kana ta miqe tsaye cikin fushi da fada

“Meye haka malam?,hankalinka daya kuwa?” Sakin hannun nata yayi,karo na farko daya buda bakinsa cikin tashin hankali bayan ya fahimci bilkisun nan dai daya shafe shekara da shekaru idanunsa na neman gani,zuciyarsa nason jinta kusa dashi,kunnuwansa na muradin jin duk wani abu daya shafeta itace dai,itace dai a gabanshi

“Am so sorry….kiyi haquri,wannan ce kalma ta farko da nake tunanin ya kamata na gaya miki”.

        Shuru tayi tana dubansa cikin mamakin kalaman da yake furtawa,me yayi mata,wayeshi?.

        Kallon rashin fahimta da take masa ya tunasar dashi cewa,bata taba ganin wayeshi ba,batasan shi din yanzu akan me yake magana ba,cikin wata iriyar murya mai sanyi yace

“Abdul’azeez abdallah mu’az kaisa,yariman qasar kais…….”

       Bai qarasa ba saboda yadda yaga da mugun hanzari ta nemi kujerar data tashi dazun akai ta zauna,wutace ta dauke tsaffff! Na tsahon wani lokaci,wani irin tashin hankali taji yana rufto mata,indai kunnuwanta sunji daidai,yana son gaya mata cewa shine mutumin da yayi silar zuwan amaturrahman da abdurrahman duniya?,mutumin da yayiwa rayuwarta karan tsaye?,mutumin daya sauya qaddararta shida ahalinsa?,tome yake nema yanzu a gareta?,me yazo yi?,ko yazo ne ya qarasa tarwatsa rayuwarta?,don bata taba tunanin yazo bane domin ‘ya’yansa,tunda tun suna tsiron da ba’asan ko meye ba a cikin cikinta suka nuna basu da buqatarsu,indai ko hakane yazo don ya tarwatsa sabuwar rayuwarta to qaryasa tasha qarya,ba zata taba bari suyi galaba ba koda waye gatanshi nan duniya.

       Cikin lokaci kadan ta maida hankalinta jikinta,ta tattara dukkan nutsuwarta,ta miqe a hankali saidai cike da karsashinta,jifansa tayi da wani irin kallo sa’annan tace

“And so what?…..don kaine yarima abdul’azeez kuma sai me?,ehemmm?” Ta qarasa fada tana harde hannunta itama a qirji,tana kuma jifansa da wani irin mugun kallo.

       Furucin nata ya dakeshi,bai taba zama ya tsara me zai iya biyo baya ba duk randa suka hadu,idanunshi a rufe suke,burinsa kawai ya ganta,yana tsammanin ganin nata shine abu mai wahala,idan ya gantan kome zai biyo baya sai yake ganin abune mai sauqi tattare dashi.

        Takawa ya soma yi yana nufarta,cikin wata iriyar murya da zaka gaza fasara yanayin da yake ciki yace

“Karki ce zaki fusata don Allah….ki bani dama ta yadda zamu zauna mu….”

“Dawa?…..kaga malam nifa banma ganeka ba,inajin kana da ciwon tabin hankaline ko dake tashi lokaci bayan lokaci,ya kamata kabar nan,idan kuma ba haka ba zan kira securities su fita dakai” duk da cewa yana cikin hali na dimuwa amma saida yaji maganar tata kamar wasan yara,saboda ya sani cewa koda duka securities din qasar zata kira babu wanda zai iya kama hannunshi ya fiddashi,saboda sun riga da sunsan wayeshi shi,ko baya ga haka ma bayajin akwai wanda ya isa ya fiddashi daga office din daidai wannan lokacin,zamanin daya dade yana hana idanunshi bacci kan fata da burin zuwanshi,yana addu’ar Allah ya nuna mishi shi.

       “Banajin ko duka duniya zasu taru sun isa su fiddani daga dakin nan bilƙess” cike da mamaki hakanan har tsakiyar kanta taji furta kalmar sunanta da yayi,saidai duka ba wannan ne a gabanta ba,yanayin yadda ya furta maganar ta tabbatar mata da cewa ainihin abinda yake cikin zuciyarsa kenan,magana ce data fito daga zuciyarsa,a bisa kuma saurin fahimta da gane halayyar mutane da Allah ya hore mata ta fuskanci  yana da wani confidence tattare dashi.

      Bata da buqatar ci gaba da tsaiwa dashi don haka bashi da wani amfani,hakanan tana jin zuciyarta na wani irin zafi duk sanda ta tuna waye tsaye a gabanta saman rufin daki guda daya,saboda haka ta soma tattara tarkacenta dake saman tebur din cikin hanzari da gaggawa.

        Saiya sake matsowa dab da ita hakan yasa ta dago da sauri cikin kaushin murya tace

“Ka dakata malam,kada ka sake aikata irin kuskuren daka aikata daxun,domin ban sanka ba,bansan daga wacce duniya kake ba,kanme zaka nemi shiga rayuwata”

“Bilqess!”

“Karka sake ambatar suna na,don babu wani abu daya hadani dakai”

“Igiyar aurena….don har yanzu ke matatace!” Furucin da yaso tarwatsa qwaqwalwarta fiye dana daxu,yakuma so sumar da ita a duqen da take,har sai da tayi taga taga zata fadi,tallafin da yaso kawo mata ne yasa tayi hanzari tallafar kanta,ta dafe kujerar daje gefanta

“Qarya kike,kin manta su din mayaudara ne,azzalumai,da basu damu da damuwar kowa ba sai tasu?,me yasa zaki gasgata kalamansa don kawai ya fada?” Xuciyarta ke ankarar da ita,wannan tunanin ya sanyata namijin qoqarin aro juriya da jarumta ta azawa kanta,sannan ta dubeshi sheqeqe

“Wannan kuma kaita shafa,kaika sani,bansanka ba bare wata kalmar aure ma ta gilma tsakaninmu” daga haka ta rataya jakarta a kafadarta,duk da bata gama diban abinda xata diba din ba,burinta kawai tayi nesa dashi,burinta kawai ta tserema ganinsa,cikin wani mugun sauri da batasan tana dashi ba ta soma dosar qofa,baiyi qasa a gwiwa ba ya rufa mata baya

“Na hadaki da girman Allah ki tsaya ki saurareni koda na minti biyar ne,koda ba zaki yarda da dukka kalaman bakina ba,ki daina pretending kamar baki sanni ba,bayan babu wannan maganar” a fusace tana bude qofar tace

“Bazan daina cewa ban sanka ba,saboda ban sanka ba din!,donme zaka dinga bibiyata ha’ab?!”da sauri ganin tana niyyar ficewa yace

“Idan ke baki sanni ba nina sanki,na sanki sanin da babu mahalukin daya taba miki shi duka fadin duniya….idan har baki sanni ba,ina cikina?,ina yaro ko yarinyata dana bari jikinki?”.

         Ji tayi jiri na neman kayar da ita,dr adam ne tsaye qofar office din yana duban fuskarta,hakanan kalaman azeez na qarshe na shiga kunnuwansa,batasan sa’adda da ta danqa masa katin rufe qofar tata a hannunsa ba,har hannuwansu na gogar na juna,tabbacin ba cikin hayyacinta take ba

” ka rufemin qofar,bani da lafiya”daga haka ta qara wuta cikin sauri gudu gudu duk don ta tsere masa.

      Bai tsaya bin takan dr adam.daya tsaidashi da tarin tambayoyinsa wadanda bai fahimtar ma me yake cewa ba,illa dai yaga bakinsa yana motsawa ba,ya rufawa bilkisu baya,yabar dr adam da binsu da kallo,baki sake,qwaqwalwarsa cike fal da tarin tambayoyi.

         Saidai qaura wambai ya rasa bilkisun cikin harabar asibitin,bayan ya tabbatarwa da kansa cewa bata bar cikin asibitin ba,yayin da take tsakankanin wasu shukoki tana hango gilmawarsa,tanajin wani tsoro da fargaba da nashigarta,me zayayi cikin rayuwarsu daya dawo yanzu?,dame suka zo musu a wannan karon kuma?”ta yiwa kanta tambayar yafi cikim carbi.

       Tayi dana sani mara iyaka kan rashin zuwanta yau da motarta,gashi anty zuhriyyan da zata dauketan har yanzu shuru basu qaraso ba,kafin wasu mintuna ta hada hawaye da gumi sharkaf saman fuskarta.

         Cikin jikinsa ya dinga jin tana cikin asibitin,hakan yasa ya kasa fita,ya dinga zirya yana duba loko da saqo na asibitin,yanaji cikin zuciyarsa zaya ganta,ya dinga yawo tsakanin cikij asibitin zuwa harabarsa.

        A karo na sau babu adadi yasake dawowa harabar asibitin,yanajin kamar zai zauce da bace masan da tayi,bayan ganinta da yayi karon farko na wasu ‘yan mintuna.

       Kamar ance masa ya juya ya hangeta cikin bala’e’en sauri tana nufar wata mota dake tsaye,wadda da alama ita suke jiran ta qaraso.

      Abubuwa guda biyu duka dakeshi lokaci daya,shirin bace masan da takeyi,da kuma yarinya da yake hangowa ‘yar kimanin shekara shida zuwa bakwai tana leqo da kanta ta window din motar,tana dubanta fuskarta cike da murmushi,tana zuro mata hannu gamida motsa bakinta da alama magana take mata.

       Idan ba qarya idanunshi ke masa ba,fuskarshi yake gani kan fuskar yarinyar,banbancin shekaru kawai da kuma kasancewarta diya mace,banda haka zai iya cewa tashi fuskarce,a gigice cikin rashin sanin abunyi ya dora tafin hannunshi saman tashi fuskar yana shafawa a hankali,kamar wanda ya rasa hankalinsa,kai kace yanason tabbatar da gaskiyar abinda idanunsa suka gane masa ne……….

        Bai ankara ya dawo hayyacinsa ba sai daya ga ta shige,an tashi motar ana shirin ficewa daga asibitin sa’annan ya zabura,cikin tsananin zafin nama da hanzari ya durfafi motar,sai ina tuni tayi masa nisa,har sun fice daga asibitin sun kuma harba kan titi.

       Da saurinsa ya dawo inda tashi motar take,ya budeta yashige ya tayar da ita sannan ya tasheta da wani irin gudu ya rufa musu baya.

        Da farko anty zuhriyya bata lura da yanayin da bilkisun ta shigo dashi ba,sai dataji yaran na mata surutu amma babu wanda ta kula a cikinsu,saita waiwaya tana dubanta

“Subhanallah!,daughter lafiya?,me haka?” Ta fada tana qoqarin sauka gefan titi,cikin muryar kuka tace

“Karki tsaya ummi muje don Allah” ganin yadda tayi maganar a gaggauce saita fasa tsaiwar,taci gaba da tuqin amma fiye da rabin hankalinta na kan bilkisun,tana karanto zallar tashin hankalin dake saman fuskarta.

        Motar saita dauki shuru,dukka yaran kowa ya kama bakinsa,abdurrahman da amaturrahman damuwa ta bayyana qarara saman fuskarsu,ganin yadda dukka yaran sukayi tsuru suna kallonta saita kifa fuskarta saman cinyarta,don ta tabbatar ba zata iya hana kanta kukan ba bare ta tsaidashi.

        Gudu yake zabgawa har ma ya wuce doka da qa’ida,saidai ko iri irin motar bai samu gani ba,haka ya dinga zagaye titunan dake daura da asibitin harma da maqwaftansa,shiga nan fita can,bayajin ko gajiya bata lokaci da kuma tsahon lokacin daya bata wannan aikin,tamkar wani zautacce,hatta da wayarshi dake aje gefan gear din motar daketa burari tana neman agaji bai jita ba bare ya saurareta,burinsa kawai yakai gareta,burinsa kawai ya cimmata,haka ya shafe lokaci mai tsaho yana zagaye saman titunan ba tare daya samu abinda yake nema ba,hakanan shima bai gaji da nema ba,yana fatan ko Allah zaisa ya ganta…..

        Yayi yawo mai tsahon dashi kansa baisan adadinsa ba,sai daya zagaye dukka area da asibitin yake da sauran maqwaftan unguwanni,saidai babu alamun zai ganta.

        Jikinsa ga soma mutuwa saboda yunwa da gajiya amma bai kulaa da wannan ba,zuciyarsa da qirjinsa ke masa wani irin zafi,roqon Allah yake tun qarfinsa ya tallafeshi,kada ya sanya ta subuce masa,kada ya qaddara masa wata doguwar wahalar kafin yasake ganinta,tilas daga qarshe ya gangara motarshi gefan titi,ya jingina bayansa da makarin kujerar yana lumshe idanunsa da suka sauya launi,yana fidda numfashi mai zafi,tun daga hunhunsa zuwa bakinsa da hancinsa,qwaqwalwarsa ta soma nisa cikin duniyar tunani tare da wassafa yadda al’amura zasu kaya anan gaba.

       Ƙarar wayarshi a karo na barkatai shi ya sanyashi bude idanunsa yana bin wayar da kallo kamar wata baquwarsa,yanajin ringing dinta kamar tsaga qwaqwalwarsa yake,saiya sanya hannu da nufin dauka ya kashe,saidai kafin yakai ga haka ma ta katse don kanta,yana shirin kashewar dai kiran ammi fulani ya shigo,bazai iya kashe mata waya ba,don haka ya daga,saidai bai iya karata a kunne ba ya sakata a handsfree

“Ba zakaci abinci tare damu bane yau?”

“Akwai wani uzuri daya riqeni,kada na tsaidaku” sauyi taji sosai cikin muryarsa,to amma ta sani ya sauya ya zama wani mutum na daban cikin shekarun,koda yaushe mode nashi na iya canzawa,don haka cewa kawai dashi tayi

“Allah ya tsare hanya”

“Amin” ya amsa suna aje wayar dukkaninsu.

       Tunanin daya fado mishi a rai ya sanyashi sake tada motar cikin hanzari,yana da hope da fatan xai samu cikakken adress dinta a a sibitin,adress din da zai zama silar kawo qarshen komai,ya kuma zama silar cimma burinsa na shekara da shekaru,don haka ya qarawa motar wuta yana burin isa asibitin cikin qananun mintoci.

*na yau da gobe ne sisters*🙏🏽🙏🏽🙏🏽__

… 55

*_IDAN kaji ƙi gudu sai in sa gudu bai shigo wajen ba. Ƴan uwa abokan tafiya, gafa magani A GONAR YARO. domin tabbas idan kaji gangami akwai labari_*.

*_Ina masu wahala kullum cikin neman maganin sanyi (imfection) amma babu biyan buƙata. Kinyi na asibiti har kin gaji babu canji, na gargajiyarma taɓawa kike babu wani ƙyaƙyƙyawan sakamakon. Tofa kakarku ta yanke saƙa. Domin kuwa ga dama a tafin hannunku. Munada maganin NI’IMA, maganin GYARAN HIPS (mai gida bye bye😉). Muna da maganin BOOBS (mai gida welcome🙈). Maganin BASIR mai hana sakewar zama. Duk ku garzayo domin samunsu akan farashi mai sauƙi da rahusa, ga kuma inganci domin an samosu ne daga tsaftatacciyar hanya mai nagarta._*👇🏻

         Hakanan fulani taji jikinta yayi sanyi bayan ta katse kiran data yiwa azeez kan zai qaraso suci abinci?,tayi shuru tana wani nazari,tare da karantar sake samun sauyi cikin muryarsa,jikinta ya bata tabbas akwai wani abu daya faru dashi,saidai batasan ko meye ba.

         Afnan wadda fitowarta kenan ta dubi fulanin tana bata fuska

“Nikam ammi gaskiya sai nakega kamar kinfi qaunar ya yarima akaina,shi kullum kamar wani qaramin yaro,bayan ya girma har iyali gareshi?” Qaramin murmushi ta saka,ta waiwayo tana duban afnan

“Ba wanda nafi qauna cikinku akan wani,saidai kawai kina kishi dashi ne,sannan bugu da qari yayanku akwai damuwa tattare dashi,dole sai ana ci gaba da bashi kulawa da kuma saita mishi hanya”

“Damuwar mefa ummi,ni kaina na karanci sake sauyawarsa sosai a shekara bakwai din nan” tayi maganar tana kallon fulanin sosai tare da son jin abinda ke damun nashi.

        Kai ta jinjina kawai tana gyara zamanta

“Kedai kiyi masa addu’a,Allah ya yaye masa”

“To ameen” tafada tana duban qasan tiles din falon,shuru ya ratsa wajen na wasu mintuna,kowa da abinda yake saqawa cikin ranshi,kafin daga bisani afnan tace

“Ina yaje ne yayan?,inata sauri na taddashi”

“Ya koma asibiti,karbo certificate of death na suhaima” ta bata amsa tana daddanna wayarta

“Allah sarki dota…” Afnan din ta fada cikin jimami,don sosai jininsu yazo daya da yarinyar,sai kuma ta sake cewa

“Kuma fa asibitin naso zuwa nima” bata amsata fulanin,da alama wani abune ya janye mata hankali cikin wayar,ganin haka yasa afnan din ta miqe,tana shawarin ko ta sami cave kawai taje ta duba asibitin,don tun randa taga wata kamar bilkisun hankalinta bai kwanta ba,jikinta yana bata itace,amma idan har ita din ce sai tafi kowa murna.

         Dakin da mama sodangi take ta tura ta shiga,da yake yawanci idan tana da buqatar hira da ita kadai take xama tayi hirarta hankali kwance,tasu tafi zuwa daya sosai,akwai sabo mai girma tsakaninsu da shaquwa mai qarfi.

        Samunta tayi xaune saman abun sallah tana jan carbi,saidai da alama tana azkar dinne kuma tunani yana fusgar hankalinta.

       Gefanta ta zauna tana dubanta

“Mama baki idar bane?” Murmushi tadan saki tana aje carbin,a duk sanda wani cikinsu ya kirata da mama saiya tuna mata da bilkisun,zamansu tare ya sanya koda suka dawo rakiya bata daina kiranta da maman ba kamar yadda suke kiranta dashi ita da bilkisun a zamansu na mexico

“Na gama ranki ya dade gimbiya,kina buqatar wani abunne?” Kai ta girgixa tana murmushi kana tadan kashingida saman gadon nata tana cewa

“Dawai asibitin nan zanje,ina buqatar dan rakiya” gaban mama sodangi yadan fadi,itama ta tuna mata da wadda ta gani din kamar bilkisu

“Me zakije yi acan gimbiya?” Ajiyar zuciya ta saki

“Wallahi mama wata na gani kamar tsohuwar qawata bilkisu,na jima inason Allah ya nuna mini ita,to amma ina shakka da kokwanton daqayar idan ita dince,saboda ita waccan iyayenta ba masu qarfi bane,sannan tun kafin mu gama secondry aka aurar da ita,auren dole ga wanda bata so,kinga ko idan hakane banga ta yadda za’ayi na ganta anan ba” shuru mama sodangi tayi gabanta yana faduwa,wani abu yana darsuwa a ranta,a yadda afnan ke wassafa bilkisu sai takega tana magana ne kan tata bilkisun sak,babu wani maraba ko kuwa banbamci,to amma indai hakane me zai faru?,tana da buqatar tabbatarwa,tana da buqatar sanin bilkisu ce ko ba ita bace?,wadda take tunani akai ita afnan ke magana akai itama?

“Shikenan,aisai ki shirya na rakaki ko?” Cikin jin dadi afnan din ta miqe tana cewa

“Yauwa mama,aiko na gode” ta fita da hanzari don shiryawa.

          Cikin qaramin lokaci dukansu suka gama shirinsu,suka cewa fulani zasu anguwa ne,ta musu Allah ya kiyaye suka fice suka tari taxi.

         Sanda suke shiga a lokacin motar azeez ke fita daga asibitin,saidai babu wanda ya kula da wani cikinsu,wani irin tuqi yake yana jin kamar bazai iya kai kanshi gida ba,dukkan wani kuzarinsa ya tsiyaye tas…..ya buga ya raya qaura wambai su bashi adress din dr bilqees amma sunce sam ba tsarin asibitin bane,yayi haquri,idan wani issue ne yakeso su tattauna ya sameta gobe a ofishibta dake cikin asibitin,idan da buqatar ta bashi adress din zata bashi da kanta ko tayi musu umarni a bashi,saboda suna da kiyaye duk wani abu daya shafi mara lafiyansu ma bare likitansu dake aiki a qarqashinsu.

       Ganin yadda ya kafe,hakanan suna ganin girmanshi da qimarshi a matsayinsa na wani babban mutum kuma sananne,sai suka danganashi da office din mamallakin asibitin gaba daya wato dr adam.

        Yaje ya sameshi cikin tunanin meye hadin bilkisun tashi,da kuma sananne kuma fitaccen dan kasuwar duniya Aa yarima?.

        Sanda ya iskeshi a office din ya tsammaci zai samu dukkan abinda yakeso,dr adam ya tsaya ya saurareshi,ya saki nannuyar ajiyar zuciya sanda yaji adress ma yake nema,baisan inda take ba kenan?,wannan shike nuna cewa ba wani abu bane mai girma tsakaninsu yadda yake tunani,koda yana cikin sahun ‘yan takarar neman bilkisun to hakan na nufin tabbas bata bashi wani matsayi mai girma ba bare hakan ya daga masa hankali kenan?,sai yaji sanyi cikin zuciyarsa,nauyin dake qirjinsa ya ragu,shima kuma ya gayawa azeez din kwatankwacin abinda sauran ma’aikatan suka gaya mishi.

        Yayi qoqarin nuna mishi muhimmancin adress din a gunshi,amma da gangan dr adam ya nuna bai fahimci komai ba,ganin xai bata mishi lokaci,kuma shi sam baida lokacin xama yayita roqonshi yasa ya tashi yabar mishi office din a fusace,ko a jikinsa don bazai taba yarda ya bayar din ba,babu abinda yafi tsana a duniya irin yaga wani na rabar bilkisu,burinsa a duniya a yanzu bai wuce ya aureta ta zama tashi shi kadai ba.

         Sanda su afnan suka isa asibitin basu samu wani information a kanta ba,hakan yasanya itama ta buqaci adress dinta,suma basu samu ba,saboda dr adam kafin ya fita daga asibitin ya jaddada cewa kada wanda yazo daga baya walau mace ko namiji a bashi adress din dr din,da qyar suka samu suka tsira da lambar waya,wanda iya hakanma ya yiwa afnan dadi,tayi serving number a wayarta da xummar idan ta koma gida zata kirata.

       Tana zaune daga gefan gadon,yayin da anty zuhriyya ke tsaye saman kanta tana sauraren abinda take gaya mata,tsayin mintuna da gama bata labarin anty zuhriyyan tana nazari,bilkisun ta buda baki a hankali muryarta tana rawa,alamun ko yaushe daga yanzu tana iya sakin kuka tace

“Ta yaya ma zai wani ce ni matarsa ce?,ta ina na zama matar tasa bayan ina da shaida ta takaddar saki da suka bani?” Ta qarashe fada,da alama abinda yafi damunta kenan cikin dukka batun.

     Nannauyar ajiyar zuciya anty zuhriyyan ta saki tana sauke hannayenta dake rungume a qirjinta,sannan ta koma dab da bilkisun ta zauna,ta kama hannayenta ta saka cikin nata,cikin tattausar murya tace

“Daughter….wannan dukka ba abun damuwa bane,dukkan abinda kike tsoro daya daga cikinsu bazan taba bari ya faru dake ba,wannan karon ko dame sukazo dai dai nake dasu,a wannan lokacin a shirye nake duniya tasan dukkan abinda ya faru,matuqar suka mana kan kara wannan karon sai mun musu na rodi,babu wanda ya isa ya rabaki da yaranki koda kuwa sarkin kaisa ne da kanshi bare danshi ko matarsa,banason kisa wata damuwa a ranki da zata hanaki walwala,kici gaba da rayuwarki kamar yadda kika saba,baki da wata matsala kisa hakan a ranki kinji?” Ta qarashe fada tana mata murmushin qara qarfin gwiwa,wanda sosai kalaman anty zuhriyyan suka bata qarfin gwiwa itama,suka kuma rage tsoron dake zuciyarta.

          A wani mugun hargitse ya koma gida,wanda kana kallon fuskarsa kasan akwai babban al’amari tattare dashi,mamaki kan meya sameshi daga futarshi zuwa dawowarshi safwa keyi,don daga dawowarsa yahau fidda kayansa gaba daya ya wuce direct zuwa toilet ya sakarwa kanshi sassanyan ruwa tsahon wasu mintuna kana ya fito.

       Duk da ruwan sanyin daya sakarwa jikinsa amma hakan bai sanya launin qwayar idanunsa komawa dai dai ba,daren gaba daya bai saurari abinci ba,bai kuma bari kowa ya dameshi da surutu ba,hasalima kebe kanshi yayi shi daya a farfajiyar gidan,yayi zurfin tunani wajen neman hanyar dazai dai daita komai.

      Wani irin dare ya gani mai tsaho baqi duhu da kuma fadi,wanda sam bai samu bacci ko daya a cikinsa ba.

     Washegari ticket nasu ya basu kawai su wuce su duka,yace musu wani aiki ya tsaidashi qasar,sam ba haka safwa taso ba,taso su tafi tare ko yaci gaba da debe mata kewa,amma hakanan tana ji tana gani tabi su fulani suka wuce.

          Suna zaune cikin airphort din afnan ta sake gwada lambar bilkisun karo na babu adadi,don tun jiya take faman kira amma sam bata shiga,harma ta soma fidda rai,ta kuma fara zargin lambar bogi suka bata saboda sunga ta matsa da son samun lambar.

        Ba zato ba tsammani taji ta shiga,fuskarta wadace da fara’a ta dubi mama sodangi

“Lah mama….kinga ta shiga” ta gaya mata ne saboda yadda taga itama ta damu ta son layin ya shiga,maganar tata ta janyo hankalin mama sodangi gaba daya kan wayar

“Ma sha Allah” ta fada amma idanunta akan wayar,itama tana dakon jin an daga kamar yadda afnan ke dako.

        Can qasa muryarta tayi sallama,saidai duk da hakan,haka bai hana mama sodangi gane muryarta ba,tabbas bilkisu ce,bilkisun ta,amma ga afnan data amsa sallamar donta tabbatar sai tace

“Don Allah ina magana ne da bikisu bilyamin?” Kai ta gyada daga bangarenta,tana aje mug dake cike da ruwan tea a gefanta

“Eh itace” murmushin jin dadi afnan ta saki tana gyara zamanta

“Ma sha Allah,kai amma gaskiya naji dadi sosai….nasan baki gane me magana ba ko?”

“Eh gaskiya….muryar ta dan kwanta min”

“No wonder…..sunana afnan abdallah mu’az kaisa,kin tunani?” Ta fada cike da confidence tana jiran amsar bilkisun.

       Mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,ba shakka afnan ce,afnan ce qanwar yarima,ina suka samu phone number dinta?,ta nan zaya bullo mata kenan ko kuwa me yake nufi?,koma meye yanzun ita din a shirye take,ta shirya musu,tana jin wata dakiya na ratsa zuciyarta,don haka ta sake dake zuciyarta itama tadan saki muryarta kadan

“Ya aiko ki kenan ko?,meye saqon nashi?” Cikin mamaki da rashin fahimtar zancan tace

“Waye ya aikoni?,baki ganeni bane?,afnan ce fa,afnan classmate dinki”

“Ina magana ne kan abdul’azeez” murmushi ta saki,tana raya wani abu a ranta,toko ya yarima ya santa dama?,akwai wani abune tsakaninsu take jiran aike daga gareshi?,to amma idan har ta sanshi ya akayi bata taba tambayarsa  ita ba?,ya akayi bata taba nemanta ba?,duk da cewa shidin tasan halinsa sarai ba lallai ya gaya mata ko ya bata labarin yasan wata class mate dinta ba

“Awwnnn…..kinsan yaa prince kenan?”.

       Gaba daya bilkisu ji tayi kamar tana shirin raina mata wayau ne kawai,don haka saita datse kiran tana jan dogon tsaki,ta kashe wayarma gaba dayanta ta aje gefanta.

       Duk da cewa afnan bata kai ga jiyo tsakin ba,amma mamaki ya cikata na yadda akayi bilkisun ta katse mata kira,hakanan bata nuna wani alamun jin dadin haduwarsu ba,bugu da qari kuma ta ambaci sunan yayanta kamar akwai wata sanayya sosai tsakaninsu.

       Da wannan daurewar tunanin ta waiwaya tana duban mama sodangi

“kinga mama,kodai bata gane ni bane?,na zaci zanji tayi murna”

“Ba zata taba murna ba tunda har tasan wacece ke,wace ke a wajenta” mama sodangi ta fada cikin ranta

“Bari na sake kira na qara mata bayani,nasan bilkisu ba haka take ba,hala ma ba itace ta daga wayar b…..” Dafe hannunta mama sodangi tayi wanda take qoqarin taga ta sake kiran bilkisun,zuwa yanzu maman tanajin ba zata iya ci gaba da boyewa afnan alaqar dake tsakaninsu da bilkisu ba,ya kamata ace ta sani

“Karki kirata gimbiya,saboda koda kin kirata ba zata daga ba” da mamaki saman fuskarta ta kalli maman

“Saboda me mama?”

“Kinsan DANGANTAKAR dake tsakaninku?” Saita girgiza kai da sauri.

        Bata boyewa afnan komai ba ta bata labari,tayi ne da yaqini da kuma zuciya daya,tayine bisa gaskiyarta koda fulani zata hukuntata,saboda ta tabbatar cewa kosu yaranta basu san tirka tirkar da aka tafka ba.

       Girgiza kai kawai afnan keyi cikin mamaki da girgiza matuqa,yaushe duka hakan ya faru?,yaushe amminsu ta aikata wannan danyan aikin babu shawara ko masaniyar daya daga cikinsu?,me yasa ammin tasu tayi sha’awar hada wannan danyan aikin?,ko tasan itace qawata da nake yawan yi mata maganarta shi yasa tun a wancan lokacin da nace za’a mata auren dole,masarauta ta taimaka ta shiga tace a’ah nabar maganar?,saita miqe tana duban mama sodangi

“Bilkisu rayuwarta abar tausayi ce a lokacin,nasan da haka a qurarren lokacin da babu abinda zan iya yi mata,wannan abu da akayi mata tamkar xalunci ne aka yiwa rayuwarta,bai kamata nabar ammi ba,ya kamata na tunkareta da maganar…”.

        Saurin riqo hannunta mama sodangi tayi tana girgiza mata kai

“A’ah,kinfi kowa sanin wacece fulani,bata haka ake bullo mata ba,ki sassauta zuciyarki ki kwantar da hankalinki,mu samu isashshen lokaci da zamuyi tunani akai” ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi bayan ta samu ta taushi kanta da qyar kana ta koma ta zauna,tayi shuru cikin zuzzurfan tunani tana sake tariyar labarin da mama sodangi ta bata,tsahon wani lokaci a hankali tace

“Ya akayi ya prince ya yarda da wannan aikin shi kansa?” Ta fada cikin salo na tuhuma,kai mama sodangi ta kada

“Bashi da laifi,saboda a lokacin yana kan qadamin neman mafita,hakanan uwa ce,umarni ya karba daga gareta”kanta itama ta girgiza

” a wajena shima mai laifi ne mama sodangi,kamar anyi amfani dashi ne an bata rayuwar wata baiwar Allah” ajiyar zuciya mama sodangi ta saki ba tare data sake iya cewa komai ba,daga haka shuru yaci gaba da wanzuwa tsakanin har zuwa sanda suka shige cikin jirgin,kana ya lula dasu duniyar sama don ya sadasu da qasata nigeria.

        Ta bangaren bilkisu kuwa tea dinta ta dauka taci gaba da sha hankalinta kwance,donta riga ta yiwa kanta da anty zuhriyya alqawarin lokacin tashin hankali ya dade da wucewa gurbin rayuwarta,tana shan tea din tana tuna wasu abubuwa,tun daga shigowarsa office dinta har zuwa kiranta yanzu da afnan tayi,sai data kammala sannan ta samu ruwa mai sanyi tasha,tabi lafiyar gadonta tana son rama bashin baccin da bata samu jiya tayi ba.

       Ta dade sosai tana baccinta kafin ta farka,ta shiga tayi wanka ta sauya kaya sannan ta dauki wayarta ta sauko qasa.

       Ta samu dukka yaran suna falo suna kallo,tabi kowannensu suka gaisa tadan tsokani na tsokana a cikinsu sannan ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana tambayar anty zuhriyya,najwa dake yunqurin shiga kitchen don duba abincin data dora musu tace

“Yanzun nan ta shiga daki,itama ta kwanta”

“Ok to” bilkisu ta amsa tana qoqarin kunna wayarta,donta tabbatar ba zata rasa saqonni ba ta watsapp da kuma sms.

       Tun kafin wayar ta gama saituwa kiran dr adam ya shigo,ta lumshe idanunta kana ta bude tanajin kamar karda ta daga,don batason qarin wata damuwar,amma ganin yadda yake kiran kawai ya shaida mata bazai daina kira ba harsai ta daga,don haka ta daga din.

       Ƙatuwar ajiyar zuciya ga sake sannan ta jishi yana cewa

“Mommy ta daga” idanu ta fiddo dukka waje,wato kusa da mommyn yake yake gaya mata ta daga,shi ko kunya baiji

“Ina ruwan bature da kunya” wata zuciyar ta gaya mata

“Kin bani wahala yau bilkis,kinsan ba zaki samu zuwa aiki ba sa’annan kuma ki kashemin waya?” Murmushi ne ya kubce mata na mamakinsa,jin yadda ya marairaice mata kamar zai saki kuka

“Au….kai na kashewa wayar ma?”

“Yes,eh mana,nasan nine babban dalilin kashe wayar,wato kada dan anacenki ya dameki ko?”

“A’ah,kawai dai banjin dadine yau din gaba daya,kuma idan nabar wayar a bude kira xaita shigowa,kuma ba lallai na samu damar dagawa ba”

“Mommy…kinji ashe bata da lafiya” ta jiyoshi adan rude yana gayawa mommyn,ta gwalalo idanu tana sake mamakin dr adam,wai me yasa ya fiya tabara ne haka?,kafin tayi wani tunani har taji muryar momyn,da alama zuwa tayi ta amshi wayar daga hannunta.

         A ladabce ta gaidata ita kuma tayi mata sannu da jiki,tana jiyo muryar dr adam sama sama saidai batajin me yake cewa,katsam ta tsincin mommyn na neman adress din gidan wai zata zo dubata,ba zata iya hanata ba,don uwa ta wuce wasa komai kashinta,saidai ta tabbatar da cewa plan ne na dr adam din,shi ya shirya hakan,kuma da tasan hakan zata faru da ba zata ce bata da lafiya ba,hakanan badon taso ba ta karanta mata adress din

“ai bamu da nisa ma sosai,nasan street din” ta gayawa bilkisun.

        Koda wayar ta koma hannunsa cikin shan kunu tayi masa magana,duk da baya ganinta amma zaka gane hakan kan muryarta

“Na gode daka hadani da mommy”

“Nifa babu ruwana,bama lallai nazo ba,ita keson zuwa ta miki sannu da jiki kuma ta ganki” tasan ya fada ne kawai,amma babu ta yadda za’ayi ace za’azo din bai biyota ba,shi me neman kuka an jefeshi da kashin awaki dama?.

        “Gashi kince baki da lafiya,kuma tafiyarku dubai larabar nan,ya za’ayi?” Mutum ce ita mai qwazo da neman sani koda yaushe kan abunda ya shafi aikinta,batason rasa tafiyar don tasan ba qaramin qaruwa zasuyi ba,don haka tace dashi

“Babu damuwa,ina saka ran kafin sannan na sake warwarewa,don yanzunma da sauqi sosai”

“To Allah ya qara sauqi ya nuna mana,sai munxo” ya fada cikin salon shauqi,da alama yana cike da farincikin samun adress dinta yau da yayi,da haka sukayi sallama.

         Tana shirin ajjiyewa wani kira data lura tun suna waya da dr adam ke shigo mata ya sake shigowa,lambar nigeria ce,kuma tana da yaqinin assadiq ne,hakanan badon taso ba shima ta daga ta saurareshi,saidai ta shaida mishi batajin dadi,hakan ya sanya hirar batayi tsaho ba yayi mata sallama,saita sake kashe wayar gaba daya donta samu ta huta sosai.

Washegari da yammaci suna zaune dukkansu a falon gidan,tana sanye da doguwar riga mai hade da hula tana yiwa yaran bitar karatun addini,kamar yadda ta maidashi wajibi kan wuyanta,dukka yaran gidan suna daukar karatun addini ne a wajenta,wanda bata sanya ta tsaya sosai kan hakan,tana soke duk wani uzuri da zai taso yaci karo da karatun yaran ya kawo musu cikas,shi yasa ko tafiye tafiye bata fiya son yi ba sabida hakan,don najwa ma tuni ta sauke a hannunta,yanzu haka hadda takeyi a wajen nata dai,yayin da yaran kowanne yayi nisa a biye,ateeq ma dan yake daya sauke,baifi sura biyu zuwa uku suka rage masa ba.
       Hatta su amatu dake da shekaru shida sun doshi izifi na goma sha shida a biye,wannan abun ba qaramin dadi yakewa anty zuhriyya da abbaa ba.
        Ƙaraurawar qofar gidance tayi qara,bilkisu ta dubi ateeq
“Ko baqin abbaa ne?” Kai ya girgiza
“Anya ko?,yace su sun fasa sai dare,ko naje na tambayoshi” kai ta girgiza
“Aah qyaleshi,jeka ka bude kaga waye” ya amsa mata da hanzarinsa yana miqewa,ita kuma taci gaba da sauraron haddar da najwa ke bata.
      Baquwar fuska ce ta shigo falon da sallama,wadda bata fita tar a bakinta,kana mata kallon farko zaka gane baturiya ce,hakanan ga kama nan sosai ta fuskar dr adam akan fuskarta,da alama kenan ita ya dauko,kalar fatar ne ya dauko mahaifinsa,shi yasa haskensa baiyi bauuuu ba kamar nasu,yadan russuna haka kadan.
      Idanunta kan bilkisu da alama ta ganeta kenan,tunda tana ganin hotunanta wayar dr adam wanda yakan dauketa ba tare ma da tasan yanayin hakan ba.
        Cikin girmamawa da fara’a ta tarbeta,ta shiga kitchen da kanta ta hado mata snacks da drink,ita kuma tana ta bin bilkisun da kallo bakinta yaqi rufuwa,da alama bilkisun ta kwanta mata sosai.
      Zama tayi a qasa tana gaidata,saidai sam matar tace saidai ta dawo kusa da ita su gaisa sosai,duk da yadda takejin kunya amma haka ta daure,ta dawo gefanta kadan ta gaidata tana sunkuyar dakai,dai dai lokacin da anty zuhriyya suka fito ita da abbaa,da alama tayo masa rakiya ne zai fita.
        Tsaiwa yayi suka gaisa cikin harshen mutan qasan brasil,sannan yafice,anty zuhriyya kuma ta dawo wajen baquwar tasu,itama suka soma gaisawa da harshen qasar.
       A wajenma tsayawa yayi suka gaisa da dr adam,duk da baisan waye ba amma yaga yabata bashi girma na musamman,hakan ya sanya ya saka ayar tambaya akansu,haka dai suka gama gaisawa ya shige motarshi ya wuce.
        Tana zaune tana sauraren hirar mommy da anty zuhriyyan ta soma ganin kiran dr adam a wayarta,saidai sarai tana sane taqi dagawa,tasan ba zaua wuce yace mata yana waje ba,ta fito ya ganta,qarshe daya gane ba dagawar zatayi ba saiga gajeran saqo
“Bazanyi zuciya ba,bazan kuma tafi ba har sai naga kyakkyawar fuskar nan taki” kamar kuwa anty anty zuhriyyan tasan meke faruwa tace ta dauki ruwa da lemo takai masa,bayan ta tambayi mommyn tace mata tare suke.
        Hakanan ta sanya dan madaidaicin hijabinta saman doguwar  rigarta,ta shiga kitchen ta diba ta fice.
      Already har ya zauna saman qananun kujerun dake ajjiye a qofar gidan saman grass carfet,bai lura da tahowarta ba har sai data iso saboda ciyayin dake wajen,ta ajjiye try din yayi da shi kuma yaci gaba da kallonta,ta masa kyau sosai a idanu,tamkar ya saceta haka yakeji.
         Kujera taja ta xauna,idan da sabo ta riga ta saba da irin wannan kallon,bama wajen dr adam kawai ba,har wajen sauran maza irinsa,tasha tsayawa gaban mirrow taga waishin me suke kallo?,ta tasa menene,sai daga baya anty zuhriyya ke gaya mata cewa
“Baiwar kyau bilkisu,ke ba zaki gani ba saidai a gane miki,kedin kamar yaya maimunatu sak kika dauko,sau nawa kike cewa ina da kyau?,to kowa ya shaida din itadin me kyauce fiye dani”.
       Ruwa da lemo duka ta tsiyaya masa tana miqa masa don ta katse kallon da yake matan,yasa hannu ya karba yana cewa
“Na gode sarauniyata,ashe cikin kowacce irin shiga kyau kike haka?” Murmushi kawai tayi tana kau da zancan ta hanyar gaidashi,saidai duk da haka bai haqura ba sai daya kodata son ranshi sannan suka shiga hira,wanda fiye da rabi yana sake yiwa kanshi campaign ne.
      Shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci,har ta tsammaci ko bashi da abun cewa,sai kuma yace
“Yarima AA yarima,ya dawo neman adress dinki ko phone number……,meye tsakaninku haka?” Bata rai tayi dajin abinda yace din,wato har ya soma bin qwaqwqwafinta kenan
“Ba abinda ke tsakanina dashi,hasalima ban sanshi ba” jim ya danyi,don zam zuciyarsa bata aminta da haka ba
“Amma daga yanda yake neman sanin wani abu daya danganceki cikin rudu da rudewa,sai nakega kamar akwai wani abu a qasa” sake hada rai tayi sosai
“Am telling you ban sanshi ha dr adam,pls mubar wannan maganar”
“Chapter closed” yace da ita yana aje cup din hannunshi.
       Sun dan jima harma ta qagu su tafi,kafin daga bisani mommy ta fito,ta taka musu har bakin motarsu kana suka wuce,duk kunya ta cikata na yadda baturiyar babar adam din ke dada campaign na danta da kanta.
        Sadda ta koma haka ta tadda kaya fal sun kawo mata wai duka da sunan dubiya,ta dauka iya wanda takeso ta rabe musu saura,anty zuhuriyya nata yaba sauqin kai da son jama’a irin na mamar adam.
 *****    ****   ******   ****
       Cikin kwanakin ya dinga jinsa tamkar ba’a duniya ba,baisan akwai kwanaki.mafiya tsauri sama da shekaru bakwai da yayi a rayuwarsa ba sai yanzu,babban tashin hankalinsa da dimuwarsa na bacewarta bat kamar walqiya,har yanzu ya gaza gano indo take.
       Inda a nigeria ce ko wasu qasashen da kakan iya biya ko bin wasu hanyoyi domin sanin inda mutum yake to daya tabbatar cewa a tafin hannunsa take,saidai su qasa ce mai doka da order da kuma tsari.
       Ganin qwaqwalwarsa na neman gazawa,ga wani dan banzan ciwon qirji da ya taba fuskanta a baya nason dawo masa yasa ya nemo abdulrashid.
       Yana bahrain amma haka ya saki abinda yakeyi ya taho din,saboda tunda yaga kiran nashi ya tabbatar akwai abu na gaggawa daya taso,yasan kuma halin aminin nasa sarai,ba kowa yake iya gayawa damuwarsa ba,hakanan bashi da wani abokin shawara ko sirri saishi.
      Kamar yadda ya zata din kuwa,ya tadda yariman a birkice gaba dayansa yana neman zaucewa wajen neman bilkisun
“Na ganta abdulrashid,na ganta harda yarinya da jikina yake bani tabbacin diyata ce,amma randa na ganta ranar ta bacemin,har yau kuma ban sake ganinta ba,duk kuwa da irin qoqarin da nake”
“Ka nutsu yarima,ka kwantar da hankalinka,i trust you,kana da fikira,hakanan kana da basirar da zaka iya nemota duk inda ta shiga,amma wannan rudanin rashin bacci da rashin nutsuwar shi zai sanya dukka basirar dake gareka ta subuce maka” haka ya dinga qoqarin kwantar masa da hankalin,wanda hakan yayi tasiri matuqa wajensa,don bayan ya sashi bacci a dakinsa yace idan ya tashi zasuyi maganar shima zaije ya huta kafin sannan,sai gashi ya tashi da cikakkiyar basirar hanyar farko da yake ganin zai cimmata.
         A lokacin abdulrashid na falon zaune yana cin takeaway din daya musu yana kuma dakon fitowar azeez din,ga tsammaninsa bai tashi ba,abinda bai sani ba tuni ya tashi harya shiga yayi wanka ya kuma shirya ya fito gaba daya yana qamshin turare,duk da babu koda rabin kwalliya irin tasa saboda yanayin da yake cikin.
        A tsaitsaye yake gayama abdulrashid din shawarar daya yanke din,ganin kamar a gaggauce yake yasa ya aje takeaway din yace suje ya masa bayani a hanya,ya mara mishi baya suka fice.
       Abdulrashid dinne ke tuqi,yayin da abdulazeez keta kiram wayoyi,da alama wadanda zasu hadu dasu ne yanzu,sai daya gama yana kashe wayar ya soma magana da abdulrashid
“Zanyi amfani da damata da mutanen dana sani cikin qasar,ina da abokan harka da kasuwanci wadanda suke manyan security a qasar,zan samesu na zauna na musu bayani,inason su bani mutane daga cikin mutanensu da zan basu picture dinta,zasu lalubomin duk inda take in sha Allah,zasu xamemin tamkar informers,duk wani motsinta zan dinga sani,bazan qyaleta ba abdulrashid,tunda har tana raye bazan iya rayuwa tana wani bigiren ina wani ba,ina buqatar ‘yata,inason inji duminta,inason dawowa da ita cikin rayuwata ko meye zaya faru a wannan karon a shirye nake da faruwar hakan” duk da maganarsa gasky ce amma saida abdulrashid yayi mamaki,don bai taba jin azeez din yayi kalamai kwatankwacin hakan kan wata diya mace ba tunda suke
“Hakan yayi….amma kasan cewa zaka kashe kudi” wani busashen murmushin gefan baki ya saki yana dan bubbuga wayar hannunshi cikin tafin hannunsa
“Kafi kowa sanin kudi ba matsalata bace,zan iya amincewa na rasa komai matuqar zan daidaita komai din” kai abdulrashid ya jinjina,kana yace
“Xaka iya yarima,fatan nasara”
“Na gode” ya amsa mishi yana dan zamewa ya jingina jikinsa da kujerar motar yana maida numfashi.
       ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶  ¶¶¶¶¶    ¶¶¶¶¶¶
       Maqale take da wayarta suna waya da hannatu bayan sun gama waya da mahaifinta malam bilyaminu,ta shaida mishi tafiyar da zatayi daga nan din zuwa dubai,don duk sanda zatayi tafiyar takan shaida mishi ya mata addu’a.
        Tana ankare da amatu dake zaune gefan gadonta sanye da kayan bacci,fuskarta a hade ta hade qafafunta tana cillasu kadan kadan,dukka tana fushi ne kan bilkisun tace ba zata je dasu ba,yayin da abdulrahman ke zaune qasan dakin shi kuma yana game da game dinshi,duk da cewa shima fuskanshi a hade yake,ta rasa me yasa suke da qulafucin uwa haka?,har gwara ma abdulrahman da sauqi akan amatu maqale mata.
      Sai data gama shirya kayan tsaf sannan ta isa gaban madubi ta shirya,don already tayi wankanta.
      Cikin wata tsadaddar turn down collar long coat me belt ta shirya,wadda tayi masifar mata kyau,gami da fidda sigar kyanta,tana tsaka da rolling babban dankwalinta da zai rufe mata abinda yayi saura daya fito na wuya zuwa qirjinta wayarta ta dauki qara,sunan dr adam ta gani
“Ohhh” ta fada tana jinjina naci da matsi irin nashi,saita daga ta sanyata a handsfree
“Gani na fito,ko na tsaya mu wuce tare?” Kaman yana ganinta ta girgiza kai
“A’ah na gode….ka wuce kawai,nima gani nan” langabe mata yayi
“Dama nasan hakan zakice,shikenan na gode” bata sake cewa komai ba ta katse kiran,saita dauki wayar ta turawa assadiq saqo,saboda tun jiya ya kirata miscal kusan uku bata samu dagawa ba,kuma yau ta tashi da shiri bata bi kiran ba.
        Saqon yana tafiya ta kashe wayar ta jefata cikin jakar hannunta,daidai lokacin da amatu ta kirayi sunanta,ta daga kai tana dubanta,sai kuma tayi shuru,tasan dai bazai wuce magiya da roqo ba.
        A hankali ta dauke idanunta daga fuskar yarinyar tana lumshe idanu,sai taga kamar fuskarshi aka dora kan fuskarta,komai nashi kamanninsa tsaf gasu nan,inama ace basu dauki kamarshi ko daya ba?,inama ace da ita sukayi kama,da ba shakka sai tafi kowa murna,amma ba’a isa a hana Allah yinsa ba,ta sauke qatuwar ajiyar zuciya tana kiran abdulrahman,sai sannan yabar game din da yake ya taso ya iso gabanta,saita duqa gabanshi ta rungumeshi tana cewa
“Me zan taho maka dashi?” Dan shuru yayi kadan sannan yace
“Ball” dariya tadan saki
“Kai baka gajiya da qwallo abdul?,bayan ita fa?”
“Ko meye ma mami inaso” kanshi ta shafa shima tana duban fuskarshi kamar babansu ne a gabanta,kamar tayi yawa,harma tana mamakin yadda akayi bata taba kula ba duk da hotunanshi da take gani a baya,ko don abun baya ranta ne?,bata taba kawowa ba?,ko don bata taba tsaiwa ta masa kallon tsaf ba
“Barakallahu fika,kayiwa mami addu’a ta dawo lafiya kaji?” Kai ya jinjina sannan yayi kissing nata a goshi kamar yadda ta sabar musu.
       Waiwayawa tayi ta kira amatu itama,ta taso ta taho tana tura baki,rungumeta itama tayi kamar yadda ta yiwa abdul din tana tambayarta me takeso
“Ko meye ma mami” kumatunta ta kama taja
“Nasan zabinki,amma sai kinyi dariya” murmushi ta saki wanda hakan yama bilkisu dadi sai tace
“Lets pray together….kowa ya hada hannunshi waje daya” take kuwa suka buda tafukan hannayensu tana karanto addu’a suna amin,harta gama suka shafa gaba daya,sannan ta karanta wasu addu’o’i ta shafa musu a kansu tana cewa
“Fi amanillah” ta miqe tana duba agogo kana ta janyo akwatinta suka sauko duka harda su amatun.
        Cikin cave din data tara zuwa airphort ta fidda glass din daya kusa mamaye rabin fuskarta,wanda ya mata masifar kyau ta saka,sannan ta ciro qaramar wayarta ta kira fadwa abokiyar tafiyarta,ta shaida mata tana can airphort din,itama tace gata nan tana hanya su hade a can.
         Daidai lokacin da yake cikin dakin motsa jikin wanda a yau ya tashi da sha’awar zuwa,saboda yadda gaba daya cikin kwanakin damuwar da yake ciki tasa ya manta da batunshi,a jiya da yakejin yayi abunda ya dace zuciyarshi tana ta gaya masa zaya ganta lokaci kusa,hakan yasa ya yanke shawarar zuwa ya motsa jikinsa ko kasalar da yake ciki zata ragu.
      Wayarshi dake aje gefe ta dauki tsuwwa,sunan daya gani saman screen din ya sanyashi gaggawar barin abinda yake ya nufeta.
        “Yanzu haka tana cikin passingers da zasu sauka qasar dubai” kalmar data rudashi,ta kuma sanyashi kashe wayar ba tare daya gama jin bayanan da yake mishi ba,hakan yana tabbatar masa da cewa sun ganta kenan,dubai….me kuma zataje yi a dubai again” cikin sassarfa da hanzari ya dauki qaramin towel da daya wayar tashi kamar zaya tashi sama ya fice daga dakin.
*_tofa ƙaƙa ƙara ƙaƙa_*
       Tun kafin ya qarasa gida ya kira dukka wayoyin da yakega ya dace ya kira din,ya riga ya gama yanke hukuncin cewa zaya bita,zai kasance da ita duk inda zata je a duniya,bazai sake yarda tayi masa nisa ba,ya samu information kan garin da zataje a dubai din,da kuma taron da zasuyi venue da time din,saidai kuma baisan masaukinta ba.
       Hakan yayi masa dadi,ya kuma isheshi,tare da zame masa haske na alamun nasara tattare dashi.
       Tuni ya yanki ticket cikin jirgi na biyu kuma na qarshe a ranar da xaije qasar,bai damu da tazarar yawan awannin da za’a shafe kafin tashin jirgin ba,yana shiga gida ya fada wanka ya soma shiri.
     ******    ****    ******
       Wannan shine xuwanta qasar na biyu,amma duk da haka sai takejin kamar zuwan farko,saboda yadda qasar ke qayatar da ita.
       Su uku cab ya dauko daga airphort din xuwa masaukinsu,dukkaninsu abokan aikine,kuma akwai sabo dai dai gwargwado a tsakaninsu,don haka suna tafe suna taba hira har suka qaraso masaukin.
       Kasancewar washegari itace ranar da zasu soma fita semina din,saiya kasance ranar kowacce kawai tayi wanka ta kintsa ne sun kuma zauna sun huta bayan sunci abinci,daga nan kowa ya kama sabgarsa.
       Ga bilkisu kuwa mutanen gida ta kira,anty zuhriyya ta hadata da dukka yaran suka gaisa,kafin ta kashe sa’annan tahau watsapp.
       Kamar wanda ke jiranta ashe assadiq na online,kusan shi ya riqeta lokaci mai tsaho suna hira,daqyar ya barta ta sauka,tana kashe data tana murmushi,assadiq mutum ne mai matuqar sauqin kai,hakanan ya iya hira wadda zaku kwashe awanni ba tare daka sani ba.
       Saita sauke ajiyar zuciya tana saukowa daga saman kujerar da take nade,ta taka a hankali zuwa bakin window din dakin da suke ciki,ta daga labulayen wanda hakan ya bata damar ganin cikin hotel din sosai,dama sauran gine gine da titunan dake daura da wajen,kasancewar suna bene ne hawa na uku.
        Shuru tayi na wani dan lokaci,tunaninta na daukarta zuwa rayuwarta ta baya yana tuna mata da wasu abubuwan da suka gabata na tsahon wni lokaci.
       Ajiyar zuciya ta kuma saki tana shafa dogon gashinta mai tsaho da sulbi,rayuwa ta mata kyau yadda take buqata,saidai har yanzu batasan ina ne makomar rayuwarta.
        Sakin window din data dafe tayi tana tunowa da hauwa’u,har yanzu bata samu nasarar samun yarinyar ba,yana daya daga cikin abubuwan da idan suka motsa mata takejin lallai tana da buqatar komawa nigeria a lokacin da anty zuhriyya tace,don taje ta matsa ta kuma nutsa da bincike ko Allah xaisa haqarsu zata cimma ruwa.
       “Tunanin me kike haka dr bilqess?” Ta jiyo muryar fadwa na ratsa dodon kunnenta,waiwayawa tayi inda dr fadwa ke tsaye,ta saki murmushi,kafin tace wani abu dr fadwan ta sake magana
“Kodai kina tunanin babban dr ne?,ai suna qasanmu ina tunanin,ba matsala sai a masa magana” dariya ma maganar tata ta bata,tadan dara kadan
“Manta da wannan batun dr….meke faruwa?” List da guraren da sukeson xuwa bayan gama semina din ta gaya mata ko tana da interest,ita dinma maison yawon bude idanu ce,don haka tace zataje,amma da fatan ba zasu wuce kwanaki uku ba
“In sha Allah” tace da ita.
         Tun bayan saukarshi qasar ya kasa zaune ya kasa tsaye a masaukinsa,yanata wassafa yadda haduwarsu zata kasance karo na biyu,ya sani cewa tilas ne ya fuskanci tirjiya da kafiya daga gareta,amma bai zaci zaikai har haka ba,bai zaci zata nuna bata taba saninshi kaf rayuwarta ba,bayajin yana da qarfin gwiwa dana qwanjin da zai iya jurewa wannan tarzoma tata,zuciyarsa bata da wannan jarumtar,indai har takai wani lokaci tana masa hakan tabbas komai zai iya faruwa.
      ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
       Cikin nutsuwa suke fitowa daga dakin taron bayan sun qare zamansu na yau,kallo daya zaka yiwa fuskarta kasan cike take da fara’a da alama taron ya mata dadi,rungume take da wasu takardu yayin da daya hannun nata take riqe da qaramar jakar hannunta.
       Idanuwansa qir saman fuskarta,yana jin wani irin abu mai qarfingana fusgarshi zuwa gareta,yanajin wasu yanayi yana dawo masa tar cikin kwanyarsa,zamanin da suka taba kasancewa tare da juna,lokacin da babu kowa cikin duniyarsu daga shi sai ita.
       Sam batasan da wanzuwarsa ba,saboda hankalinta kacokam nakan fadwa,da alama wani abun suke tattaunawa,bata ankara ba,bata kuma zata ko tsammata ba taga mutum ya sha gabanta kana ya tsaya cak a gaban nata yana dubanta da idanunsan nan masu cike da wani irin sirri da kuma kwarjini.
       Kallon second uku tayi masa idanunta suka dauki saqo suka aikawa qwaqwalwarta,take cikin sakannin dukka wata fara’a dake saman fuskarta ta dauke tsaf,kai kace bata taba dariya ba a duniyarta,saita kama hannun fadwa data fi kusa da ita wadda ta zuba ma azeez idanu tana dubansa cikin mamaki ta ja hannunta ta gewayeshi da zummat tafiya.
       Saidai bai bata wannan damar ba,gabanta ya sake sha,kana cikin harshen hausa wanda ya fuskanci duka abokan tafiyar nata guda biyu ba yarensu kenan ba yace
“Ki taimakeni ki bani dama komai qanqantarta da zamuyi magana mu fuskanci juna nida ke,na roqeki da girman Allah” ya qarasa fada cikin wata iriyar murya kana cikin sanyi yana hada hannayensa guda biyu.
         Cikin kalaman dake nuna zallar zafin da zuciyarta ke mata a sannan tace
“Ka sauraramin malam,ta yaya zanyi magana da mutumin da bansan wayeshi ba,na gaya maka bansanka ba,ban taba ganinka ko sanin waye kai ba,donme zaka damu rayuwata ka shugemin hanci da qudundune ne iyee?,mtsweew” ta qarasa maganar cikin jan tsaki kana cikin zafin nama ta kewayeshi ta wuce wannan karon ba tare data kama koda hannun fadwa din ba.
       Bai damu ba ya rufa mata baya,bai damu da yadda su fadwa ke binsa da kallo ba,bai damu da yadda masu fitowa jifa jifa daga dakin taron ke binsu da kallo ba yaci gaba da binta
“Wannan maganganun da kike fada kina fadarsu ne kawai saboda bacin rai,ke kanki kin tabbatar ba haka bane,kinfi kowa sanin waye azeez a duniya” tafiyar tasu batayi tsaho ba,bai kuma ankara ba yaga ta shige cab,kafin yayi wani yunqurin tsaidasu har sunja sun wuce.
        “Ya salam!” Ya fada cikin zafin rai da takaicin yadda idanunshi suka rufe bai kula da shammatar da tayi masa ba,saiya rintse idanunsa kana ya bude yana bin wajen da kallo tamkar zai sake ganinta,sai a sannan ya lura da yadda wasu ke kallon nasa,take qwaqwalwarsa ta tuna masa wayeshi?,wala’alla sun saba ganin hotonsa a mujallun qasarsu kenan
“Tur da rayuwar da zaka shahara kayi suna” ya fada cikin haushi takaici gami da jin zafi yana fadawa motarshi ya rufe bayan ya dage gilasan sama.
        Daga ranar da sunanka ya shiga cikin jama’a,labarinka ya fantsama a bakunansu,wata harka ta sanya sunanka yake shige da fice cikin bakunansu,to daga ranar idan bakayi babban nazari,dogon tsinkaye da sanya lura da takatsantsan a lamuranka ba,saiya zamana baka da wani sirri na rayuwarka,saikayi da gaske zaka zama me kulawa kamewa da kuma rufe sirrinka,kome kayi abun tattaunawa ne da bada labari a bakunan al’umma.
        Ya bude idanunsa bayan ya gama wannan gajeran tunanin,ya tashi motarsa kana ya fusgeta yana barin wajen.
         Tun cikin motar ta kifa fuskarta saman cinyarta ta soma kuka,kukane dake tuna mata rayuwar da tayi a baya,yadda ta rabu da danginta ‘yan uwanta,yadda aka tsareta a wani gida tamkar siyanta akayi,yadda ta rasa abu mafi qima tattare da ita wanda har yau bai dawo ba bazai kuma dawo ba,yadda ta samu rabon yaranta ta kuma rainesu cikin wahala har zuwa haihuwarsu.
         Kafin su isa tayi kuka sosai mai yawan gaske,don haka tana shiga dakinsu ta shiga bandaki ta watsa ruwa gaba daya,batason su fadwa su shigo su sameta cikin wannan yanayin bare su tambayeta,don sirrin rayuwarta ne,private life dinta ne da bai kamata wani yaji  koya sani ba.
        Rigar material ta saka mara nauyi sannan ta hada gashinta waje daya ta tufke,wanda harda shi ta jiqa tana fatan ruwan ya ratsa har saman qwalqwalwarta ko zata ji sanyi.
       Don ta hana kanta kowanne tunani saita janyo takardun data shigo dasu tahau dubawa,saidai ba gane komai dake ciki take ba,haka yaci gaba da kokawa da tunani da kuma yunqurin duba abubuwan dake jikin takardun.
       Bata jima da yawa ba su fadwa suka shigo,ta amsa sallamarsu tana qoqarin dora murmushi saman fuskarta,saidai ga duk wanda ya kalleta yasan akwai wani abu mai girma dake cin zuciyarta.
          Daga nasu bangaren duk da sun cika da mamakin hadin bilkisu da wannan babban dan kasuwar har kuma ta masa abinda ta masan wanda ya basu mamaki qwarai,su da sukasan cewa magana ma kadai dashi wani babban dama ne kuma abun alfahari ga mutum,saidai babu wanda ya tambayeta komai,suma sai kowacce ta kame bakinta,suka shiga sabgarsu data hada da wanka da cin abinci,abincin da bilkisu bata ma tuna dashi ba bare tabi ta kansa,hakanan tana zaune har suka kammala shirinsu sannan salwa daya abokiyar tafiyar tasu ta kalli bilkisun
“Mufa mun gama shiryawa” daga idanunta dakeson mata nauyi tayi ta dubesu,sam ta mance da agender zasu dan fita yau idan sun dawo daga taron,sai tasa hannunta ta dafe goshinta
“Banjin yau zan iya fita,kumin afuwa don Allah”
“Bb komai….saimun dawo to” salwan ta fada kana suka fice gaba daya abinsu.
        Fitar tasu sai taji kamar sun bata wani space ne,don haka ta watsar da takardun gefe,wadanda dama kamar dole aka mata karantasu,ta zame ta kwanta sosai zuciyarta da qwaqwalwarta na lulawa duniyar tunanin da taketa faman hana kanta,ta lura da alama tunanin kawai sukafi buqatar yi a wannan lokacin,ta yaya ya biyota dubai?”ya akayi yasan nan zata zo?,shine abunda yafi daure mata kai.
        Baiga laifi ko baiken kansa na sake barinta ta subuce masa ba sai daya koma masaukinsa,bacci ya qauracewa idanunsa,hankalinsa ya sake tashi da zuciyarsa ke raya masa idan chance dinsa na qarshe kenan fa daya bari ta subuce masa?,idan bazai sake ganinta ba kenan?,da qarfin tuwo ya samu da qyar ya cilla wannan tunanin gefe,yana fatan damarsa ba zata subuce masa ba.
       Ya kira abdulrashid ya shaida masa komai,ya danyi shuru yana nazari sai kuma yace
“Ina ganin ta dauki zafin da ba zata taba tsayawa ta saurareka ta hanyar lallashi da lallami ba….” Haka zuciyata ke gayamin abdul,inajin kamar saina dan saka tsauri da qarfi sannan zata yarda da cewar ta sanni ma totally,wannan shine mataki na farko”
“Haka nima nake tunani…..but kada ka saka tsaurin nan naka yayi yawa,saboda kada ya haifar mata da tsanarka fiye data baya” idanunsa ya lumshe yaba gyada kai,kalmar tsanar na neman masa barazana
“Na fahimta” ya fada in a low tune.
       Cikin daren ya gama tsarawa kanshi komai,ya gama tsarawa kansa komai ta fanjama fanjam,amma gobe dole ta tsaya ta saurareshi,dole ta yadda ta sanshi,dole yaji wani abu game da diyarshi jininshi.
       Tunda suka fita duk tsahon awannin tana nan kwance inda suka barta,kiran wayar da suka mata kan ta sauko qasa ta riqe musu leda daya dan Allah basason su shiga daki su sake fitowa ya sanyata tashi ta zauna dole,sai da tadan nutsu sannan tayi rolling mayafinta ta zura plate shoes dinta ta fito zuwa farfajiyar hotel din ta soma dube dube.
           Dai dai lokacin da KAMAL ke jingine jikin motar da suka shigo hotel din da ita,wayarshi riqe a hannunsa yana danne danne,yana tsaiwar jiran budurwarshi daya kawo hotel din,wadda ya daukota ne daga mazaunin dalibai dake cikin makarantarsu yarinyar ba tare da sanin iyayenta ba,suka kwashe sati suna sheqe ayarsu,yau kuma kwanakinsu ya cika zaya maidata.
       Kamar wanda akace daga kanka ya daga kanshi yana dan duban area din,yana son ganin ko samira ta fito?,saidai….maimakon yaga samira saiya hangi wata halitta daya jima yana neman inda take,wata halitta daya dade yana jin ita kadai ta dace da rayuwarsa,ita kadai ta dace ya aura,wanda a qalla shekara bakwai kenan da ganinta bai kuma sake sake ganin nata ba,shekaru bakwai baya a mexico.
       Ba tare da dogon nazari ko tsinkaye ba ya cusa wayarshi a aljihu ya kuma tunkareta,zuciyarsa fari tas yana jin wata annashuwa
“Hey baby” maganar data firgitata jin sautin namiji dab da ita,ta waiwaya a razane,sai kuma taja baya da hanzari tana binsa da wani irin kallo,yayin da yake qare mata kallo zuciyarsa na sake tabbatar masa da cewa eh tabbas itace,saidai wannan ta hadu sosai,ta hadu fiye da shekarun baya,ta sake zama babba kuma cikakkiyar mace fiye ma da yadda yakeso
“Ya kike baby?….sunana…..” Da sauri ta daga mishi hannu tana qarewa yanayinsa kallo dake nuna gogagge ne kuma mai budadden idanu
“Inajin kayi makuwa ne,bani kake nema ba” daga haka ta juya da hanzari,gabanta na faduwa tsoro na cikata ta wuce ciki.
      Baiyi qasa a gwiwa ba ya bita,saidai kafin yakai har ta shige elevator,nan ya tsaya ya saki baki cikin takaici.
       Ya sani koda yasan dakinta bashi da ikon zuwa har sai da ixininta,to amma babu wanda zai hanashi zaman jiran sake fitowarta,tunda dai yasan ba zata dawwama cikin dakin ba,daga nan zuwa safiya zuwa yammacin gobe dole ta sake fitowa,don haka saiya fita,ya samu samira na jiransa
“Munyi da wani abokina zaizo nan zamu tattauna kan business dinmu,don haka ga mota nan zata maidaki.makaranta zamuyi waya” tabe baki tayi tana dubanshi
“Amma dai ba haka mukayi dakai ba,sanda ka daukoni kana rawar qafa shine yanzu zakace na koma ni kadai?”tsawa ya daka mata wadda ta bata tsoro,dole ta rufe bakinta tayi shuru sannan tayi yadda yace din.
         Gabanta na wani irin faduwa ta isa dakin,ta samu waje ta zauna tana rufe idanunta tare da sauraren bugun zuciyarta,wannan wacce iriyar tafiyace mara sa’a?,da wadanne irin mutane take gamuwa ne tunda tazo garin?,me yasa?,su waye saisu dinga binta haka?,tana wannan tunanin kiransu salwa ya shigo wayarta wanda shi ya katseta,ta bude idon nata tana amsa kiran
“Mun iso amma bamu ganki ba”
“Na sauko naga baku qaraso ba,na riga dana koma daki,banajin dadi ne sosai”
“Ayya yi xamanki,zamu samu wani cikin ma’aikata ya taimaka mana”
“Ok” kawai tace tana aje wayar sannan ta koma ta kwanta rub da ciki tana kiran sunayen Allah don gaba daya tunaninta a birkice yake.⁵⁷

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *