SIRADIN RAYUWA CHAPTER 16 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 16

 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

   Kusan awa guda kenan yana tsaye qofar shiga da fita na hotel din yana jiran ganinta,wayarshi na hannunsa,lokaci lokaci yakan maida kanshi ya danna na wasu sakanni sannan ya sake daga kanshi idan yaji qarar fita ko shigar wani abun hawan.

      A irin hakanne motar da suke ciki ta durfafi gate din,yayi jinkirin daga kanshi wannan karon sai da suka kusa giftashi,a sannan idanunsa suka sauka kanta daga,tana zaune daga gefan hannun hagus saitin da yake,kafin yayi wani yunquri tuni sun harba titi,hakan ya sanya baiyi qasa a gwiwa ba shima ya tsaida taxi ya rufa musu baya don yana son cimmata a duk inda zata je.

     A qalla azeez ya kusa shafe rabin sa’a a bakin dakin taron,duk bayan wasu mintuna saiya duba agogon hannunsa yana jiran lokacin zuwan nasu ya cika,dubawa ta qarshe agogon ya nuna masa nan da mintina biyar zasu iya isowa,hakan ya sakashi fitowa daga cikin hadaddiyar motar tasa,ya haye samanta ya zauna,ta saitin daya tabbaatr idan ta fito babu lallai ta ganshi,saidai shi yana iya ganinta.

       Dukkan wata mota da zata shiga kota fita tana kan idanunsa,sanye yake da wasu baqaqen qananun kaya wadanda aka yiwa rigar manyan rubutun manyan haruffa da launin jaa,hakanan rufaffen takalmin qafarsa adon jiki gami da zaren jiki duka jaa ne,hatta da fuskarshi ya toshe qwayar idanunsa da baqin sun glasses,hannayenshi harde a qirjinsa,fuskar nan babu walwala ko misqala zarratin,sak ya fito a babban boss.

    A hankali motar tayi parking daura sa tashi ba tare data kula da waye a wajen ba,itace qarshen fitowa saboda tsaiwa da tayi ta sallami me abun hawan,ta fito tana saqala jakarta kamar jiya hannunta riqe da takardu.

     Cikin taku na nutsuwa ya sauko daga baya motar ya dosheta

“Assalamu alaikum,da fatan kin wayi gari lafiya” kalmar daya fada kenan saitin kunneta,wanda hakan ya sanyata zabura har takardun hannunta suna watsewa a wajen,kana ta juyo suka hada idanu,duk da cewa ita din bata iya ganin qwayar idanunsa,amma shinyana iya ganin tata,qwayar idon data masa wani mugun kyau,ta kuma yi tasiri cikin gangar jiki da zuciyarsa.

   Baki ta bude da niyyar jefa masa magana amma sai ya rigata

“Kada kice komai,don tuni na soma haddace kalaman da kike jerantawa kullum kina bitar gayamin,idan kikace baki sanni ba inajin kamar kina kashene ni bilqees”.

      Lokacin da yakai qarshen kalamansa lokacin kamal ya iso,yasauka ya sallami mai motar kana ya juyo da niyyar tunkarar wajen,saidai me?,ga mamakinsa ita ya hango tsaye da yarima abdul’azeez din,abunda yaso yadan daure mishi kai,saidai kuma daya tuna saboda shi dama ya soma ganinta sai mamakin nasa ya ragu,amma abun tambayar dama har yanzu suna tare?,wacce irin alaqa ce haka mai girma tsakaninsu da tayi lasting har tsahon shekaru bakwai?,tambayar da yayiwa kansa kenan,yana dan sake matsawa kusa dasu gami da zuba musu idanu.

      Harara bilkisu ta balla masa,saiya sake matsawa dab da ita yana son kashe duk wanu karsashi nata da kaifin idanuwansa,bayan ya zare glass din fuskarshi,har tana jin qamshin mayen turarensa sosai fiye da da.

       Wannan matsawar ta darsa wani abu a zuciyar kamal,shawara ce kai tsaye daga wani sashe na zuciyarsa,wanda shawarar tayi masa dari bisa dari,tabbas idan ya aiwatar da abinda ranshi ke raya masa burinsu na shekara da shekaru zai cika cikin qanqanin lokaci,babu jinkiri ko kuma daga qafa cikin hanzari ya zaro wayarsa ya kuma shiga camera.

  

      Ga bilkisu kuwa ganin yadda ya matse tazarar dake tsakaninsu sai kawai ta juya da sauri da niyyar barinsa a wajen,don bata jin zata iya ci gaba da tsaiwa dashi yana mata famin wasu sabbin al’amura da suka riga suka shude mata,duk da akwai burbushi cikin ranta,wanda dama shi ciwo ko rauni koda ya warke yakan bar gurbinsa jikin dan adam.

     Caraf yayi yunqurin kama mayafinta,saidai maimakon haka sai yayi nasarar kama hannunta,tattausan singalalin hannunta ya ratsa tafin hannunsa,kamar yadda lallausan tafin hannunsa ta jiyo duminsa har cikin jijiyarta.

     A fusace ta waiwayo tana watsa masa wani irin kallo

“Ka sakeni malam”

“Kiyi haquri,cikin girmamawa da lallashi kije muyi magana ta fahimtar juna ni dake”

“Idan naqi kuma fa?” Bai barta kalmar ta gama fita daga bakinta ba ya sunkuceta gaba daya ya nufi motarsa,abinda zuciyarsa ta jima tana gaya mishi daya aikata,abinda ya jima yana tunanun shibe mafita guda daya da zai kebe da ita,ya kuma bi hanyar data kamata don ta saurareshi.

      Wannan daukar nata da yayi shinya qarawa kamal qaimin daukar hotunansu a hakan lokacin da take yunqurin kufcewa,saidai ingarman sadaukin yariman ya nuna mata qashun sam.ba daya bane,hakanan akwai banbanci mai girma tsakaninsu,yayin da su fadwa daje tsaye dan nesa kadan dasu suna kallonsu cike da sha’awa,saboda yadda sukaga sunyi matuqar yi musu kyau suka kidime gaba dayansu,ganin ya sanyata a mota gamida rufewa,ya kuma zagaya yana niyyar shiga sit dinsa,da sauri salwa tabar fadwa anan ta shuga ciki kiran dr adam,wanda ya rigasu yin gaba,hakanan babu yadda baiyi dasu su taho tare ba amma bilkisu taqi,ta gaya mishi ya riga yasan tsarinta ai tun bayau ba,tun a brasil.

     Saidai fa dr adam yazo a makare,don ko qyallin motar yarima basu samu ba sai sawun tayar motar,fadwa ke shaida musu tuni ya wuce.

    Tsaye sukayi cirko cirko cikin tashin hankali kowannensu,duk da cewa he’s familia amma kuma basusan ina zaya kaita ba,kuma kusan a gaban idanunsu ya dauketa cikin qarfin tuwo ya sanyata a motar,hakan ke nuna ba tafiyar dadi bace kenan bare suce dason ranta akayita.

    Hankalin dr adam ya sake tashi sanda fadwa ke gaya mishi daukanta yayi da hannunshi,tashin hankalinsa ya hadu ya cakudu da kishi mai tsanani,har baisan ya rufe su fadwan da fada ba kamar ma sune yariman,saiya fidda wayarshi ya soma jera mata kira babu qaqqautawa.

   Sosai take mishi hayaniya da masifa cikin motar,ranta a matuqar bace ganin yadda ya maidata kamar wata ‘yar tsana,hakanan ya zubda mata mutuncinta da qimarta a idanun mutanen da suke ganin girmanta.

     Idan set din da suke kai ya tanka to yarima ya tankata,yasan kome zata fada yana fita ne tare da zafi da qunar dake cikin ranta,maganganun da take fada tamkar tana samun wani dan qaramin sauqi ne cikin zuciyarta,shi yasa ya zabi yayi shuru,ta fadi dukkan abinda takeson fadar,matuqar hakan zai sama mata salama cikin ruhinta.

      Tafiyar minti arba’in har suka iso masaukinsa batayi shuru ba,iya gajiya bakinta ya gaji,wanda isowarsu wajen ya sanyata dole yin shuru.

    “Ranki ya dade sauka muje” ya fada a tausashe cikin nuna girmamawa,da idanu takebin wajen da kallo,akwai jama’a nata kai kawo kowa yana sabgar gabanshi,saita dauke kanta gami da jan wani dogon tsaki

“Ba zani ko ina ba….ka mayar dani inda ka daukoni”kai ya girgiza cikin matuqar rauni

“Kiyi haquri,amma bazan iya maidake ba,inason kasancewa dake,inason inasan ina diyata take,yaya ta rayu ke da ita tsahon wadan nan shekarun?”

“Zamu shekara anan kenan” ta sake fada a harzuqe,kai ya girgiza

“Ba zamu shekara ba,saidai xan daukeki da hannuwana kamar daxun zuwa ciki,inda zamufi tattaunawa cikin nutsuwa” ya fada yana cire sit belt din dake daure dashi,da alama yana shirin daukar nata kamar yadda yace kenan.

“Idan ka daukeni zan maka ihu,in kuma gayawa duniya satoni kayi” murmushin gefan baki da yayi masifar qara masa kyau da kwarjini yayi

“Ko zaki shekara kina fada babu mai yadda dake….”

“Saboda kana taqama kaidin me arziqi ne?,kana da madafan iko da sarauta,kana da dukiya,Ka siye kowa?….ni kuwa talaka ce ba diyar kowa ba?” Ta jefeshi da tambayar cikin katsar numfashinsa ba tare data bari yakai qarshen maganarsa ba.

      Qaramin murmushin ya kuma saki ba tare daya shirya ba,duk da kalamanta qona masa zuciyasa sukayi,yasan ta fadi daya daga cikin abinda ke damunta ne a zuciya,kai ya kada

“Ba wannan ba,ke zakiso duniya ta kira uban ‘yarki da barawon mutane?” Sai kalmar tayi mata gingirin aka,ta kuma sake maimaita cikin zuciyarta,take fuskar amatu ta dawo cikin idanunta,sai taga kamar amatun ce a gabanta sanda ta fuskarshi,bai sake cewa komai ba ya sanya kai ya fice.

     Har ya bude qofar tayi hanzarin ce masa

“Dakata!,kada ka soma tabani” saiya tsaya din kamar yadda tace ya goye hannuwansa a qirji yana kallonta,murmushi da baisan dashi ba yana subucewa daga fuskarshi.

   Banzar harara ta jefa masa,bayan tayi kamar ba zata fito din ba,sannna taja qafafunta ta fito tana jan dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta.

      Tunda ta shiga kanta yana a qasa,duk yadda yakai gason tayi magana amma bata daga kai ta dubeshi ba bare tace mishi uffan,tsahon wani lokaci haka ya tashi ya miqe ya barta,babu jimawa ya soma jere mata kayan motsa bakinkala daban daban.

    Wani irin bacin raine ya cikata,me yake nufi?,an gaya mishi yunwa ce ta kawota ko mene ne?,ji tayi ba zata iya shuru ba tare data tanka mishi ba

“Ka maidani inda ka daukoni,don bance maka yunwa nakeji ba bare ka jere min wadan nan kayan a gabana” ta fada cikin matuqar hade rai,murmushi ya sakar mata yana jifanta da wani irin kallo

“Baqonka abun girmamawa ne a wajenka,duk da cewa kinqi cewa komai dani kinqi bani hadin kai….ko meye nayi miki a rayuwa babu abinda zai sanya ki fahimceni,idan na miki dai dai ko akasin haka,da gangan na miki ko ba cikin sanina bane sai zama mu tattauna,karki manta zuri’a ta shiga tsakaninmu,dole mu nemi makomarta,wanda bazai taba yiwuwa ace mace tayi ciki ita kadai ta haifa ba ba tare da uba ba,kiyi tunani,akwai wata rana da zata zo zata buqaceni,zata buqaceni koda baki so,zata buqaci sanin waye ni,zan baki mintina kiyi tunani akai”saiya miqe yana juyawa

“Bana buqatar yin wani tunani akan komai,na jima ina tunani akai,hakanan qwaqwalwata ta dade tanayin tunanika wadanda suka jima da gajiyar da ita,ta nemi hutu hutu irin na har abada,don haka bata buqatar yin tunani kan ire irenku da matsalar daya shafeku” murmushi kawai ya juyo ya jefeta dashi kana yayi gaba zuwa uwar dakin dake manne da falon,yayin da ita kuma ya bishi da harara,tana ganin baiken kanta da bata gwada ma yi masa ihun ba tun a can,komai ta fanjama fanjam.

    Yana shiga dakin ya tura qofar yana dafe goshinsa gami da sauke numfashi,ba shakka ba qaramar badaqala bace a gabanshi,amma duk yana ganin komai zaizo masa da sauqi matuqar zata dinga tsaiwa tana saurarensa,koda ba zaga amsashi ba kamar yadda tayi masa yanzun.

       Numfashi ya furzar mai dumi daga bakinsa,ya soma takawa zuwa cikin dakin,dai dai nan wayarshi tayi tsuwwa,ya zarota a kasalance yana duba mai kiran,fulani ce,don haka cikin girmamawa ya daga wayar yana karawa a kunnanshi.

      A ladabce ya gaidata,sannan ta isar da saqon da takeson isarwa din

“Wai sai yaushe zaka dawo ne?,cikin satin sama upper week za’a gabatar da hawan daba na al’ada fa,kowa da kowa zaizo,dukkan wani wanda yake jinin masarautar kaisa ne wannan karon zai halatta,harda wadanda basa a qasar,kasan kuma kusan shekara biyu rabonka da zuwa,ya kamata a wannan karon ka halarta,saboda inason koda yaushe ka dinga zama a hannun daman mai martaba,saboda shekaru suna sake turawa,ya kamata ace ana ganinka a dukka al’amuransa,tunda bashi da kamar yakai”

“Inason nima na dawo,saidai uzurin da nakeyi din ne yanzu ma na fara bare ayi maganar kammalashi”

“Wanne irin uzurine haka?” Kanshi yadan shafa yana duban qofar falon daya barta

“Kidai tayani da addu’a ammi” ga zatonta sha’ani ne daya shafi harkar business dinsa,wanda indai ta fannin ci gaban da daukakar da yake samune kulli yaumin hakan na mata dadi,saidai kuma ta wani fannin tana da damuwa sosai akanshi yariman,akwai abubuwa da yawa na rayuwarshi da take ganin bai dace da ra’ayinta ba,kamar yadda yake wofintar da matarsa da lamuranta,bai fiya damuwa da sha’aninta sosai ba,yadda yake jimawa bai waiwayi masarauta ba,bare abokan adawa su dinga yawan ganinsa,suna kuma tunawa da matsayinsa tare da tunasar da kanau cewa wataran akwai mai amsar sarauta,wataran zata amsa sunan ‘yar sarki jikar sarki matar sarki kuma uwar sarki,amma tana ganin tunda har ya cika mata dukkan buri da wani sharadi data kafa masa,ya kamata ta qyaleshi hakanan kuma yayi rayuwarshi yadda yakeso shima,akwai lokacin da komai zai daidaita,akwai lokacin da zai canza wasu abubuwan a qashin kanshi

“Shikenan,Allah yayi jagora”

“Amin summa amin,godiya nake” daga haka ta sauke wayar tana sakin ajiyar zuciya.

      Tana daga kai suka hada idanu da afnan,saita dan tsareta da idanu kamar yadda ta fahimci itama tun dazun ita take kallo,ta rasa dalilin sauyawar afnan din tun dawowarsu daga brasil

“Lafiya kike?” Ammin ta tambayeta tana kallonta,saita dauke kanta ta maida kan wani qaramin littafi dake hannunta,a son ranta mama sodangi ta barta tayima ammin magana,kullum idan ta tuna da abun sai taji zuciyarta na azalzalarta ta tari ammi da maganar,amma mama sodangi ta gaya mata akwai lokaci,yin maganar a yanzun ta hangi babu abinda zai haifar sai tabarbarewar al’amuran da suke saka ran gyaruwarsu.

      “Babu komai….kawai,ina tunanin,anya ba wani abu wanda ba dai dai muka aikata ba Allah ya jinkirta min aure na?” Ta qarashe maganar tana zube idanunta kan ammi fulani.

       Hakanan taji maganar banbarakwai,ta kuma rasa muhallin da zata aje maganar,cikin rashin fahimta tace

“Kamar yaya afnan?,me kike nufi?” Wani murmushi mara ma’ana tayi tana kada kai

“Babu komai,kawai inajin hakanne cikin raina,ban sani ba koba dai dai bane” shuru ne ya ratsa tsakaninsu cikin falon,ta saka ammin cikin tunani,wanda kafin ta fita ita kuma ta miqe da litattafanta ta wuce ciki,hakanan sai ammin ta bita da kallo harta bacewa ganinta.

      Ita daya tasaki nannauyar ajiyar zuciya,sai mafarkin da tayi jiya ya fado mata,mafarkin yarinyar sosai,yadda ta bugeta a asibitin kuma taci gaba da tafiyarta,abinda ta sake gani kenan,saidai wannan karon ta tsaya ta kalleta sosai a cikin mafarkin kafin tayi gaban abinta,idanunta ta rufe tana girgiza kai,tafi zargin saka abun da tayi cikin ranta ne shi ya sanyata mafarkinta a jiyan,ko kuma kewar suhaima ce.

      *_KAMAL_*

       Saboda tsabar zumudi bai iya bari ya isa gida ba ya koma cikin motarshi ya zauna sosai,sannan ya bude data dinsa bayan yahau watsapp ya tura dukka hotunan wa hajiya fauziyya mahaifiyarsa,kana ya sauka ya lalubi lambarta ya kirata.

     Sai data kusa tsinkewa sannan ta daga,zuwa lokacin har ya qagu

“Wai ina kika shiga ne mom?”

“Baqi gareni ban lura da kiran naka ba,saida husna ta miqo min…..ya akayi?”

“Babbar jarida zan siyar miki…sa’annan babbar nasara dake alamta mana cikar burinmu nan da wasu ‘yan kwanaki” baki ta tabe

“Nina yanke qauna dakai kamal,tunda har yau burinmu na shekara bakwai ka kasa cika mana shi,bayan mun sanya dukka burinmu da fatanmu saman wuyanka” wata banzar dariya ya saki sa’anan yace

“Idan nace miki nan da sati daya burinki na farko zai soma cika kafin zuwan na biyu zaki yarda?” Kai ta girgiza cikin nuna rashin tabbas

“Wai kana nufin bacin sunan yarima a duniya da kuma masarauta gaba daya?,kai anya kuwa,abun da kamar wuya,mutumin daya wuce saninmu a yanzu,ka kasa komai a sanda yake da qananun shekaru kuma shidin ba kowa bane a idanun duniya bare yanzu?”

“Wait mom….jeki watsapp dinki,amma da zarar kin kammala duban saqon…ina da buqatar jin alert na kudade masu nauyi a accnt dina kafin mu dora daga inda muka tsaya” tsaki taja

“Da gaske kamal lalacewa kakeson yi,banda haka duka duka yaushe mahaifinka ya tura maka kudade masu yawa?”

“Mom…wai kamata ta yaya bazan buqaci kudi ba,komai nawa fa saida kudi nake iya tafiyar dashi”

“Kamar wani ya hanaka tsaida hankalinka ka kammala karatunka,koka kama kasuwancin babanka da kyau,ba irin yadda kake riqon sakainar kashi dashi ba a yanzu”

“Yanzu mom na faranta miki amma zaki sakamin da haka?” Tuna batun da sukeyi ne ya sanyata cewa

“Sorry son,bari na duba” daga haka ta katse wayar,sai shima ya kashe tashi yana qunquni gami da kumbura,ya aje wayar gefe yana zaman jiran ji daga gareta.

     A hankali sai kuma yaji kamar bai kyautawa bilkisu ba idan ya bari fuskarta ta bayyana a idanun jama’ar masarautar a matsayin wata lalatacciya mai mummunan aiki,amma saidai kuma…..babu wata hanya data rage masa wadda zai iya samunta ta ruwan sanyi a amatsayin matarsa saita hakan,saboda kallo daya ya yiwa idanun yarima ya karanci wata iriyar soyayya mai kaifi da yakewa yarinyar,wanda da alama shidin baisan tana fita daga idanun nashi ba….da wannan tunanin ya kwantar da kujerarsa yana jiran kira ko saqon kudi daga mom din tasa haj fauziyya..

       Tun kafin ta gama ganin hotunan ta miqe tsaye cike da zallar farinciki,haqiqa ba shakka lokaci yayi,lakaci yayi na tarwatsa fulani da iyalanta,lokacin da zasu soma cimma burinsu kan sarautar qasar kaisa yazo,irin hotunan da sukeso,irin hotunan da suke da buqata,wadanda komai bincike idan za’ayi zai tabbatar da cewa na gaske ne,ba hadin computer ba.

       Batayi wani jinkiri ba bayan ta gama bin hotunan daya bayan daya da gaggawa ta kira kamal,shima baiyi jinkirin dagawa ba,tunda abinda yake jira dama kenan

“Haqiqa lokaci yayi,kayi qoqari sosai kamal,kayi qoqari ba kadan ba,duk da naso ace sunfi haka muni amma hakanma babu laifi,yanzu meye abu na gaba?,ta yaya za’ayi hotunan su shigo masarauta?”

“Kudina tukunna mom”

“Dalla can mayen kudi kawai,dan banzan yaro mai idanun cin naira,zan tura maka 100k”

“Kacal?”

“Au kacal ne ma?,kana zaune babu cas babu as ka samu 100k amma ka raina”

“Amma mom wannan ba aiki nayi ba?”

“Aikin da zaka fi kowa farinciki dashi ba,duk badon kai nake komai ba?,idan komai yayi daidai waye zai haye karagar?”

“Oh yeah,naji shikenan”

“Yauwa”

“Yanzu mom,hotunan ya kamata ne ace an wankosu da yawa,an kuma zuzzubar ko ina lungu da saqo na masarautar,yadda kowa zai samu gani”

“Hakane….amma so muke su isa gaban idanun ubanshi,kasan yadda jamar masarautar ke qaunar abdallah,za’a iya qin kai masa saboda kada ranshi ya baci….amma na tuna wata dabara….adama,ita ya kamata ta miqa hotunan zuwa gareshi,don banason aga fuskarsa a wajen,bare sunanka ya baci nan gaba,kafin lokacin da itama adaman aiki zai biyo ta kanta”

“Good,saiku qarasa tsara yadda za’ayi,nidai naji alert”

“Naji ubana…..inajin aikin nan lokaci mafi dacewa da farashi shine,lokacin babban hawan daba na qasar kaisa,lokacin da baqi zasu cika gidan,yadda maganar zatafi fantsama lungu da saqo na qasar kaisan…..inason ka halarci hawan kaima”

“Zanzo” ya bata amsa don akwai sabuwar yarinyarshi da yayi a katsina,dama yanason zuwa su hadu,da wannan mummunan shiri da qullin sukayi sallama kowa ya aje wayarsa cike da farinciki,saidai haj fauziyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,sai data lalubi adama don ta mata albishir.

     Duk da ba cikin yanayin take ba amma hakan bai hana idanunta bin falon da take a zaune da kallo ba,tunda take bata taba ganin dakin hotel mai kyau da tsaruwa irin wannan ba,idan kana ciki ba zaka tsammaci cewa a hotel kake ba,saidai daga ganin yanayin yadda yake sake sosai a wajen dakin ya zamar masa kamar nasa ne,irin abin nan da masu hannu da shuni kanyi,su riqe daki ya zama na saukarsu ne duk sanda suka sauka a qasar,koda basu nan ba za’a sanya musu kowa ciki ba,saidai fa suma zasu dinga biyan kudi kamar suna kwana.

      Abinda yasa ta gane hakan,qananun frames frames dake maqale a bango,wadanda sukafi kama da abun award,shaidar girmamawa da akan baiwa mutum sun kusa guda goma.

       Janye idanunta tayi a hankali tana jan tsaki,wanda yayi dai dai da fitowar yariman daga daki,sarai yaji tsakin amma sai yayi kamar baiji din ba.

      Wannan karon sanye yake jallabiyya mai azabar kyau da taushi,wadda duba daya zaka mata kasan kudinta ba kadan bane,yadda take da kyau haka tayi masa wani azababben kyau,ta fidda kyanshi mai sanyin nan da tafi da zukatan mata da yawa.

      Ganin ya nufi qofa yana shirin fita ya sanyata miqewa da hanzari tana fadin

“Malam dakata…bafa kaya ka ajjiye ba”

“Tunda muka hadu dake bilqees kike kirana da malam,kin manta sunan mijinki kuma uban ‘ya’yanki?,abdul’azeez abdallah,idan kin manta kuma ba laifi kina iya kirana da abban baby” ya bata amsa yana riqe da handle din qofar,yayin da take nufo qofar da sauri tana son cimmasa ta samu nasarar fita,saidai kafin ta qaraso yaja qofar ya rufe.

       Koda ta isa taja sosai taqi koda motsi bare batun buduwa,hakan na nufin kulleta yayi kenan?,bacin rai goma da ashirin,saita dafe goshinta da tafin hannunta tana jin kamar kuka zai qwace mata,babban takaicinta batasan yadda akayi ta manta wayarta a motarshi ba,da kira daya zata yiwa adam ta tabbatar babu bata lokaci zai bayyana a wajen,dolenta ta koma da baya ta zauna,tana wassafa irin babban abunda zata masa wanda zai tursashi barinta ta tafi,bayan yayi zuciya gaba daya ya bar bibiyar rayuwarta ita da yaranta.

       Minti a qalla takwas ya bude qofar ya shigo,yana dauke da jakar tata,saidai daya hannun nashi wayarta ce,yake riqe da ita,wadda yana shirin maida qofar ya rufe ta dauki tsuwwa.

     Ita dake zaune da shi da wayar ke hannunsa dukka hankulansu ya karka ga wayar,sunan Dr adams daya gani na yawo saman screen din nata shi shi ya sanya qwayar idanunsa soma sauya launi nan take,saboda sanda yake qoqarin dauko wayar ya lura da tarin miscal da irin wannan sunan,wane kishi na masifa yaji ya motsa masa,saiya bar abinda yakeyi din ya daga wayar ya kara a kunnenshi

“Sweet angel…..ina kika shiga haka?,ina ya kaiki,kin barmu hankali tashe munata nemanki” kalaman da suka soma dukan kunnenshi kenan,cikin wata iriyar kakkausar murya fuska kamar hadarin gabas,ya dawo da wannan kamar tashi,kamar bashine ke magana cikin taushi ba a dazun yace

“Kada ka sake kiranta,domin tana tare da mijinta,idan kuma ka qiya,ba shakka tsautsatsauran hukunci zai hau wuyanka,qaton banza kawai” ya cikashe da tsaki yana sauke wayar daga kunnenshi kana ya datse kiran.

       Niyyarsa ya shiga cikin wayar ya sanyata a flight mode,saida me?,hoton amaturrahman da abdurrahman dake saman wayar a matsayin homescreen walpaper dinta yaso tafiya da numfashinsa,iskar dake fita ta kafofin hancinsa ta masa qaura na wucin gadi,har ya dinga kokawar nemota saboda barazanar tafiya da take gaba daya.

     Bai ankara ba yaji am wafce wayar,kana muryarta ta maye gurbi

“Wai waye kai da zaka dinga gayawa mutane cewa kaidin mijina ne?,wanne irin mutum ne wai kai ehenn?” Ta fada tana tsaye a gabanshi.

       Sam bai fahimtar me take fada,tunaninsa ba’a kan wanann yake ba,tuni qwaqwalwarsa tayi nisa wajen gaya masa

“Yaranka biyu ne,tabbas ‘yan biyu ta haifa maka” baisan lokacin daya rarumota gaba daya ita da wayar ba ya sanyata cikin jikinsa ya matseta gam,bai damu ba,hakanan bai kulaa da yadda take kai mishi duka tako ina ba gamida yi masa gargadin ya saketa.

      “Alhmdlh,alhmdlh” shine abinda yaji bakinsa yana maimaitawa,kafin daga bisani yace

“Na godewa Allah da bai qyaleni na tafi a yadda tsarin yazo ba,na godewa Allah daya sanya wani lamari mai girma a zuciyata game dake,na godewa daya hukunta min haka cikin rayuwata,cikin sati guda kacal da nisantarki da rayuwarmu….ashe ke din wata alkhairi ce da kika shigo rayuwata,wanda dukkaninmu bamusan da haka ba?,ashe har yara biyu na bari a jikinki ba yare dana sani ba?” Ya fada yana dora hannunshi saman cikinta yana shafawa,wanda cikin hanzari ta buge hannun nasa qwalla na sauka saman kuncinta,saboda yadda ya riqeta tsam,kuma babu alamun zai saketa,ga kalamanshi dakeson dawo da komai sabo cikin rayuwarta.

     Birkitota yayi suna fuskantar juna,yana duban tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka dade da sauya launi,wannan karon dukka kafadunta ya kama ya riqe sosai yana ci gaba da maganarsa

“Ashe har yara biyu Allah yayimin kyautarsu ba tare dana sani ba,suna rayuwa a wata duniyar ina rayuwa a tawa duniyar daban?” Bata ankara ba ya zube gaba daya a gabanta saman gwiwoyinsa yana riqe da dukka qafafunta

“Kimin alfarma ki bayyana min ‘ya’yana,koda zakimin wani hukuncin na yarda zan karba….” Da qarfin tsiya cikin kuma sauri ta janye qafafunta daga gareshi,duk yadda taso nuna juriya da jarumtarta amma ta gaza,don tuni kuka mai nauyi da qarfinya qwace mata

“Wadanne ‘ya’yan?,ai kai da dui wani makusanci naka ku saka a ranku cewa baku da wasu yara a duniya sama da wadanda ke gabanku,yaran da tun a ciki kuka baiwa banza a jiyarsu?,kuka yiwa duniya kyautarsu?,dasu rayu da kada su rayu ba damuwarku bace,kuka qaryata wanzuwa da samuwarsu,to kamar yadda kuka qaryata samuwarsu,inason har duniya ta nade kuci gaba da raya wannan cikin ranku,don har abada ba zasu taba zamowa naku ba”.

     Ta soma yunqurin zame kafadunta daga hannunshi,tayi nasara saidai kuma ya kama hannayenta da sauri ya saka cikin nashi

“Ba laifina bane bilqess,anfi qarfina ta hanyar da sabawata zai iya zama babbar illa ga rayuwata….”

“Da bai zama illa ga rayuwarka ba yanzun ka gani ya zama illa ga jininka ko?….” Kai ya gyada

“Tabbas hakane….amma ki yarda dani….bani da laifi,koda ina dashi laifin nawa kadanne,nasan zakimin uzuri matuqar kika zauna kika saurareni….” Hannayenta ta zame ta qarfin tuow,ta cimma nasara kuwa saboda jikinsa dake a mace laqwas,yana jin zuciyarsa na masa wani irin zafi zugi da kuma quna

“Kada ka sake tabani,ka matsa daga kusa dani,sannan ka budemin qofa na koma inda na fito,idan kai bakasan illa da zunubin haka ba ni na sani”

“Babu wata illa,hakanan babu zunubi a kanmu,DOMIN KUWA KE MATATA CE” Idanu dukka ta zaro,don ga zatonta yabar wannan maganar ne,ya kuma fadeta ne a baya saboda kawai ya samu damar tsaidata.

     Idanunsa cikin tsakiyar nata qwayar idanun,kai ya gyada mata yana mai sake son tabbatar mata

“Yes…har yanzu ke matatace” nata idanun ta janye saboda yadda yake kallontan ya mata nauyi da yawa,ta saki wani malalacin murmushi da batasan yadda akayi ta qwaqwaloshi bama,ba tare da tace komai ba ta soma takawa zuwa bakin qofa kana ta soma bashi amsa

“Kabar wannan tatsuniyar kazo ka budemin qofa,domin koda jikina dukka kunne ne bazan taba yarda da wanna tazo mu jita din ba,koda zan yadda da kowacce ta tsuniya takan wannan kam bata da gurbi ko kuma muhalli” takowa yayi zuwa dab da bayanta ya tsaya

“Ba tatsuniya bace…hakanan yadda na fadi haka maganar take,inda shaidu har guda uku,wadanda na tabbatar koda a gaban alqali sun isa su zama shaida” saiya kewayeta ya bude qofar,ba tare daya dawo ba yayi gaba.

     Jinta take kamar mutum mutumi,jinta take kamar ba’a duniya ba,qafafunta kamar ansa wani abu mai qarfi an bubbuge mata su,babu qwari sam tattare da ita haka itama ta taka ta fice.

        Tun daga wannana rana ba ta sake fita wajen taron ba,wuni take kwance a gida,tana jin tamkar bata da lafiya,inda Allah ya taimaketa dr adam yana tsaye akan komai,rashin zuwan nata na sauran kwanakin bai zame mata wata illa ko asara ba,kusan duk abinda aka gudanar zata ji daga wajensu tare da gamsashen qarin bayani da ‘yan qananun jotting dake sake bata haske.

       Zamanta a dakinsun sai yafi mata kwanciyar hankali,saboda tasan babu ta yadda za’ayi ya iya ganinta ba tare data fita ba,tana kuma da yaqinin yana can yana fama da zirga zirgar neman ganinta,don ta fuskanci halayyarsa cikin wani qanqanin lokaci.

        Saidai wani abu dake bata mamaki saqonnin gaisuwa dake tafe a jejjere a wayarta da wata baquwar number da batasan ta waye ba,saqonni ne dake nuna zallar kulawa da kuma bege,bata taba damuwa tasan lambar waye ba,iyaka idan ta karanta ta goge taci gaba da sabgarta.

       Ta fannin yarima bai boyewa azeez komai ba ya shaida masa,ya sake qarfafa masa gwiwa tare da fatan nasara.

       Tabbas rashin ganinta ya sanyashi a damuwa qwarai,har yanzu baikai ga ji ko samun dukka abunda yake da buqata ba,saidai abu biyu na debe masa kewa da kwantar masa da hankali.

     Abu na farko ya riga da yayi connecting wayarta da nashi,duk sanda ta tashi barin wani gari ko wata qasa zuwa wata zai sani,hakanan da zarar ta koma brasil a sauqaqe zai ga adress din inda take zaune,ta wannan fasahar kuma ya samu damar shiga gallery dinta,ya debi dukka hotunanta wadanda sukayi masa,nata dana amaturrahman da abdurrahman.

       Ranar kwana yayi yana kallonsu,ya kalli hotunan kamar zasu gudu su barshi,ya kallesu kamar ba gobe,ya kallesu kamar mai shirin yin sallama da duniya,hakanan duk tsananin jarumtarsa dakiya gami da juriya amma ya gaza daurewa wannan karon sai daya zubda qwalla sanda yake kallon hotunan yaran,yake kallon tsantsar kama ta ban mamaki dake tsakaninsu,babu wanda yake hangowa a wannan lokacin sai fulani,ko yaya zata karbi lamarin?,ya zata kaeshi?,da wanne irin ido ko zuciya zata amshi yaran,tabbas ba shakka a wannan karon ya shirya tara dama qalubalantar ko meye zai faru,ko meye zai biyo baya.

¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

     Safiya ce mai cike da wani irin ni’ima da lullumi,shi daya qwal cikin dakin yana maqale da waya a kunnenshi yana amsa kiran da safwa tayi mishi,yayin da yake ta cike wasu takardun kwangiloli,ayyukane suka taru sukayi yawa kan harkar kasuwancinsa,amma ya tare komai ya kasa komai,bilkisu ta tsaida komai cak cikin rayuwarshi,yana lissafe da yau kwanaki bakwai rabon daya sanyata a idanunshi,yanajin matuqar wasu kwanakin suka sake biyo baya,tabbas zaiyi dukkan mai yiwuwa ya isa har dakin dake masaukinsu cikin hotel din,saboda zuciyarsa ta soma gazawa.

       Maganar da safwa tayi ne yasa yadan dakata da rubutun da yakeyi

“Ina saka ran ganinka a hawan daba na wannan shekarar…..kowa da kowa zaizo,nima wannan karon zanzo,inason ganinka don nayi kewarka”.

      Yasan cewa tana sonshi,hakanan tana da muradin kasancewa tare dashi,saidai wasu abubuwa da suka sanya sam zaman nasu bai fiya armashi ba,hakanan akwai tsarukansu da sam basuyi dai dai ba,bakuma su dace da ra’ayinsa ba,amma ko meye yasani cewa tarsa ce dai,hakanan tana da haqqi a wuyanshi,don haka cikin yanayi na kwantar da hankali yace

“Kada ki damu,wani babban aiki ne ya tsareni anan din,wanda bani da tabbacin zuwa din,saidai da zarar komai ya kammala zan taho ayi komai dani in sha Allahu” murya ta kwabe sosai tana jin babu dadi

“Kace kawai ba xakazo ba” kai ya girgiza

“Ba haka bane,babu tabbacin rashin zuwa kamar yadda babu tabbacin zuwan” xatayi magana ya dakatar da ita,sakamakin wani haske da sauti d wayarshi daya ware ta musamman tayi,yace zai kirata yana zuwa.

       Alama ce dake nuna mishi cewa bilkisu ta isa filin tashi da saukar jirage,hakan na nufin zata sake barin qasar,baida matsala yana da jama’a dake aiki a filin jirgin,don haka yasa aka laluba mishi inda jirgin da zai tashi yanzu ya nufa,aka tabbatar masa brasil ne.

      Already yana da visa dinsa,saboda haka yasa aka duba mishi jirgin da zai sake tashi zuwa qasar,aka tabbatar masa saidai gobe da yammaci,duk da ba haka yaso ba amma dole haka ya haqura,ya shiga shiri cikin zafin nama gamida shirya dukkan abinda yake saka ran zai wanzar idan ya isa brasil din.

      Cikin shiga dake nuna tsantsar alfarma isa mulki da kuma qasaita take nufar sassan mai martaba,wanda ta samu kira ne na musamman daga gareshi.

        Daga ita sai manyan hadimanta guda biyu,kubra da yaha,wadanda suta zaba suyi mata rakiya.

       Sau uku tana wuce gungun mutane wadanda dasun hangota suke zubewa su miqa mata gaisuwa,ta amsa musu cikin nuna zallar sarauta kana ta wuce.

      Gungu na uku da suka tadda bayan sun dan gota su ne ta tsinci muryar kubra

“Ranki ya dade,Allah ya taimakeki”

“Uhmmm,ya akayi kubra?” Dan jim tayi har sai da fulanin tace da ita

“Ina saurarenki mana,fadi buqatarki”

“Allah ya baki yawan rai….shin kin lura da yadda gungun dukka jama’ar da muka wuce ke boye wani abu da zarar sun ganki?” Cak ta tsaya da tafiyar da takeyi,tsahon sakan uku kana ta waiwayo tana duban kubra,wadda tuni suka sadda kai qasa ita da yaha cike da girmamawa

“Kamar yaya kenan?” A ladabce ta amsa

“Kamar akwai abinda suke gani,wanda ganin giftawarki ba zato wala’alla yasa suke boye abun….kin kula da haka yaha?” Kai ta gyada

“Qwarai kuwa,nima na gani har karo biyu kafin isowarmu nan”.

      Dogon tunani maganar tasu ta sanya fulanin,tayi shuru na wasu mintuna ba tare da tace komai ba,kalaman kubra suka dawo da ita daga duniyar tunanin data fada

“Amma uwar gijiyata,kina iya sanya idanu a gaba koda zamu sake ganin wasu mutanen” kai ta jinjina cikin gamsuwa,kana ta juya taci gaba da tafiya tana sake nutsuwa da sanya idanu ga hanya koda zata ga abinda su kubran ke fada.

      Ilai kuwa idanunta suka gane mata,cikin barorin gidanne kimanin su hudu,maza biyu mata biyu,idan ta lura ma da kyau kama sun razana ne da ganin nata,daya daga cikinsu dake can baya kuma hannayensa na boye a bayansa suka zube suna miqa mata gaisuwa.

      Bata amsa ba,saita soma takawa zuwa inda suke zuben,babu wanda ya motsa a cikinsu jin bata amsa ba hakanan bata tafi ba,saita isa gabansu tana qare musu kallo,idanunta ya sauka akan na bayan dake goye da hannayensa a baya…..

Har ta bude baki da zummar yin magana,sai kuma ta tuna ba girmanta bane,don haka ta juya taci gaba da tafiya ba tare data ce da kowa komai ba,sai su kubra suka rufa mata baya suma ba tare da sun tanka ba,jin batace komai din ba.

      Zuzzurfan tunani ta shiga,ba shakka akwai abinda ke faruwa,akwai abinda ke faruwa wanda ita din bata sani ba,kuma koma meye yana da alaqa da ita,lallai abun ya shafeta,amma zata bincika cikin hikimarta kamar tadda ta saba.

       Saida sukazo iyaka,wanda su kubra basu da izini ko ikon darawa daga nan din sannan tayi magana a sanda suke juyawa

“Na lura da abinda ke faruwa,kuma ba shakka abun bisa dukkan alamu ya jibanceni ne…..ku isa sassana ku jirani,kada ku tafi,ku kuma kira sodangi da lubabatu suma suyi dakona,zamu tattauna bayan na fito”

“An gama uwar gijiyarmu” suka amsa mata a kusan tare,ba tare data waiwayo ba ta saka kai zuwa ainihin sassan mai martaba.

      Cikin qasaita da nutsuwa tayi sallama a katafaren falon daya kasance yana ganawa da iya iyalinshi kawai,ba’a amsa mata ba,hakan ya bata mamaki,saita ware idanu tana kallon wadanda ke zaune cikin falon.

       Uwar gida sarautar mata ce fulani saratu,saman cinyarta daya daga cikin jikokinta ne maza,hakama gefanta jikan nata ne wanda dukkansu ba zasu haura shekara hudu da biyar ba.

       A daya kujerar kuma maibi mata ce wato fulani adama,itama tana zaune da nata jikan guda daya a gafanta tana tsinke mishi inibi cikin kayan marmarin dake jibge a falon tana bashi yana ci,shima bazai wuce shekara shida ba.

       Batayi mamaki ba don saratu bata amsa mata ba,adama ce cikin salo na kissa tadan tada kai ta amsa mata babu yabo ba fallasa.

      Ganin kamar yau din kowa akwai abinda ke cikin ranshi sai itama ta nemi tata kujerar cikin hakimcewa ta zauna,ta kuma kama kanta da kyau ba tare da tabi takan kowaccensu ba.

      Tsahon mintuna falon ya dauki shuru,bakajin komai sai darar su fulani saratu kowacce da jikanta.

      Abunda fulani aisha ta lura dashi da kyau shine,kamar abinda sukeyi din sunayi ne da biyu,don haka saita sake baiwa banza ajiyarsu.

      Jikan adama keta wasanshi cikin falon yana zagayewa,ya hau wanann kujerar ya fada kan waccan,yayin da fulani adaman ta shiga masa tafi tana masa waqa,kana ta dora da cewa

“Tattaka da kyau….yauwa,cikin ikon Allah wataran sai kaga kaine mamallakin wannan wajen….eh mana,tunda su magadan sun kasa kawo nasu magajin…duk inda aka kai magaryar tiqewa ai dole a miqo mana mu masu jikoki maza,ahaaann….ai wani hanin ga Allah baiwa ne”.

      Sosai maganar ta taba fulani dake danne dannen wayarta,ta taba ranta sosai,saboda tasan bada kowa suke ba sai ita,hakanan suna magana ne kai tsaye akan abdul’azeez dinta,harta daga kai zata magantu sai kuma taga ba girmanta bane,hakanan tafi kowa sanin ta yadda take maida musu amsar magangununsu irin wannan ta qona musu rai cikin ruwan sanyi fiye da yadda sudin sukayi mata,don haka saita share taci gaba da abinda take,duk da zancan ya tsaya mata sosai cikin ranta.

     Batasan me yasa fulani adaman ta sauya cikin shekarun nan ba,kishin nata da ada take dannewa ta cinye yanzun ga kasa,takan mata gugar zana a lokutta masu yawa,saidai abinda ta lura dashi sam bata kwatantawa gaban maimartaba,akasin fulani saratu da bata iya boyewa gaban kowa ma.

      Wannan bai bar kunnuwa da qirjinta ba fulani saratu ta daga qaramin jikanta dake kan cinyarta tahau masa rawa 

“Idan Allah ya baka babu me hanaka…..wani hanin ga Allah baiwa ne” sunan Allah ta ambata can qasan ranta,sa’annan taci gaba da danne dannen wayarta kamar basu dameta ba,daya daga cikin dabi’unta dake qona musu rai,na yadda bata taba buda baki ta nuna musu bacin ranta kan wani aiki nasu,saidai su gani a aikace.

       Allah ya taimaketa ba’a qara second goma ba maimartaba yayi sallama cikin falon ya bayyana,cikin shigar da yakanyi idan yana cikin iyalinsa yana kuma buqatar ya sake sosai.

       Fulani aishan ce ta soma amsawa,wanda hakan yaja hankalinsa matuqa a kanta,adonta ya qayatar dashi,don dama babu qarya,gwanace ta wannan fanni,tun yarinta zuwa girma yanzu daya cimmata.

      Ita ta soma miqewa ta aje wayar hannunta,ta isa inda yake tsaye,ta saka hannayenta ta soma karkade mishi kujerar da yake da niyyar zama a kai,duk da ba wani datti ko qura ko qanqani akai

“Barka da fitowa ranka ya dade” ta fada tana kallonshi cikin wani salon murmushi mai qayatarwa,dolenshi ya maida mata martani ba tare daya shirya ba,duk da yadda yaso ya daure kodon su saratu dake wajen

“Barka kadai aishatu…..da fatan kin wuni lafiya” murmushi ta sake masa tana duqawa gamida soma zuba mishi abun sanyi dake cikin jug jug na alfarma na tangaran dake jere a wajen

“Lafiyata tana tattare da yadda ka wuni lafiya yallabai” ta qarashe fada tana miqa masa kofin,fuskarsa dauke da murmushinya karba sannan yace

“Ma sha Allah,na gode qwarai aishatu”

“Babu godiya tsakaninmu,amfanina kenan” da haka ta juya tana sakin murmushi zuwa mazauninta,ko iya haka tasan ta rama wani sashe daga abinda sukayi mata.

       Sai data zauna sannan ya dubi saratu

“Sarautar mata…,kuna lafiya?” Ya tambayeta yana miqawa daya jikan nata dake zaune gefe hannu,saiya sauko da gudu ya nufi inda yake,da alamu akwai sabo da shaquwa tsakaninsu,bata iya danne bacin ranta ba,don gashinan saman fuska da muryarta haka ta amsa mishi,saiya waiwaya ga adama

“Ranki ya dade?,to kefa?” Tayi qoqari ita din tadan sakaya da murmushin yaqe,ta amsa mishi a taqaice

“Lafiya”.

      Sai daya gama shanye lemon da fulanin ta zuba mishi shi da jikokin nasa,yana yi yana jansu da wasa,wanda wannan shi yadan sauko dasu daga dokin da suka hau,sannan ya fara maganar data tarasu.

      Gida biyu hankalinta ya kasu,daya yana ga maganar da suke da mai gidan nasu,yayin da dayan ya lula zuwa ga tunanun abinda ya afku dazun,shin meke faruwa?.

       Awa daya da wasu motsi suka shafe sa’annan ya sallamesu,nan ma sai datayi abinda ta tabbatar zasuji ba dadi sannan ta fito abinta,tama rigasu barin wajen,don yanzun hankalinta ya tafi ga lalubo abinda ke shirin faruwa.

       Sanda take fitar da wani irin kallo adama ta bita,ta kuma saki shu’umin murmushi,duk da abinda tayin ya qona mata rai,saidai bacin ran nata ragagge ne,takan kuma cika da farinciki,idan tuna nan da wasu awanni da idan sunyi nauyi awa 78 rayuwarta ita da ahalinta zasu shiga cakwakiya,don tana da yaqinin saqon data bada ya soma bazama lunguna da saqunan masarautar,a iya yau kadai Allah ne kasai yasan adadin jama’ar  da suka gani.

     Kamar yadda ta buqata haka taje ta samesu suna jiranta,cikin girmamawa kowanne ya miqe tsaye harta samu waje ta xauna,kana suka gaisa da mama sodangi saboda yau din duka basu hadu ba.

     Shuru na dan mintuna sannan tace

“Nasan zakuyi mamakin taraku da nayi anan,duk da cewa yaha da kubra sunsan dalili,amma kudin nasan baku sani ba”

“Gaskiyane” suka amsa mata,saita gyara zamanta sosai sannan ta zayyane musu abinda ke faruwa.

       Shiru ne ya ratsa falon babu wanda yace wani abu,saita shiga nazartar fuskarsu tare da shiga nazarin amsa da mafita da kowanne zai bata.

      K’an kame hannunta umma luba tayi,wanda ke dauke da daya daga cikin hotunan data samu tsinta itama cikin masarautar tun gefin magariba,hotunan data fuskanci sun fara yawo cikin masarautar,don wannan shine na biyu data tsinta,tun dazun take ta tunanin hanyar da zatabi ta nunawa fulanin,ta kuma ankarar da ita abunda ta fuskanci ya soma wanzuwa,dalilin jimawarta kenan cikin gidan har kawo wannan lokacin ba tare data tafi gida ba.

       Sosai fulanin ta ankare da mutsu mutsun da umma luban keyi,hakan ya sanya ta zuba mata idanu,ta kuma gano yadda hannuwanta ke dunqule kamar yadda ta dinga ganin hannuwan dai daikun mutanen data wuce dazun.

   

     “Lafiya lubabatu?,ya akayi?” Ta tambayeta tana sake tsareta da kallo,ta dago da niyyar ce mata babu komai,to amma kwarjininta ya sanya ta kasa fadar hakan,saita soma inda inda irin ta marasa gaskiya,sa’anna daga bisani akan kanta dole ta fiddo hotunan guda uku ta miqa mata.

      Ji ta dinga yi kamar a mafarki sanda take kallon hotunan,yarimanta yaronta rungume da mace cikin jikinsa,har daya daga cikin hotunan ma yafi kama da kiss yake mata,don ya rufa fuskarshi ne saman tata sosai,babu wani batun almara ko zane,yariman qasar kaisa yarima abdul’azeez ne sosai.

      Wani mummunar faduwar gaba gamida fargaba ta rusketa sanda ta tuna fuskar yarinyar,qwaqwakwarta kuma tayi mata tariyar wacece ita,kaddai ace tsahon shekarun suna tare,kaddai ace data rabasun tsayin shekarun basu rabu ba suba tare da juna suna zaman haramc……

       Saita hana zuciyarta qarasa wannan mummunan tunanin,ta miqe tsaye qirjinta na suya,zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,a matuqar rude ta miqawa mama sodangi hotunan tana jifan umma luba da kallo bayan ta yiwa kubra da yaha nuni da hannu kansu fita hade da tambayar umma luban

“Wannan ba yarinyar nan bace da kika samo sukayi aure da yarima na shekara daya ba?” Kan umma luba a qasa ta gyadashi

“Tabbas itace uwar gijiyata”

“Ban fahimta ba,a ina suka hadu,ko dama suna tare basu rabu ba?” Tayi tambayar wannan karon tana maida dubanta ga mama sodangi tana jin duk wani dabara da hikimarta suna toshewa.

       Mama sodangi da tunda ta dora idanunta akan hotunan taji wani sanyi yana kwarara cikin ranta ta daga kai tana duban fulanin,kai tsaye tace da ita

“Tabbas basa tare,canzawar yanayin yarima kawai na tsahon shekarun ya isa ya shaida maka hakan”

“Ta yaya zan tabbatar da gaskiyar hakan,bawai pretending yake min ba?”.

       A wannan karon babu wanda ya bata amsa a cikinsu

“Tabbas indai abinda nake tunani ne abdul’azeez ya tafka babban kuskure,kuskure mafi girma a rayuwarsa” ta fada cikin gsananin bacin rai.

      A wannan karon kasa shuru mama sodangi tayi,cikin nuna girmamawa tace

“Ina ganin kibi komai sannu a hankali….abdulazeez yarone mai biyayya matuqa da gaske da duka duniya ta shaida,karki zafafa wannan karon,kada ki shiga raywarsa da yawa”

“Dakata sodangi!” Ta daga mata hannu cikin fushi

“Kina nufin na zura idanu?,kinaso ki cemin na qyaleshi yaci gaba da mu’amala da wannan ‘yar talakawar wdda ba sa’ar aurensa ba?,na qyale ya maido rayuwasa baya bayan andade da wuce wajen?” Ta fuskanci ta dauki zafi sosai,hakanan tayi nisan da bata ko jin kira bare ta amsa,don haka saitayi shuru ba tare data sake tankawa ba.

      Shuru ya sake ratsa falon,tsanar bilkisu da ada bata jita ba tana neman samun muhalli da gurbi cikin zuciyarta,qarin wasu mintuna suka sake shudewa kafin ta sake magana 

“A kowanne lokaci yarinyar nan itake shiga tskaiyar lamurana da tsarina ta nemi wargazashi,koda yauahe saita zama dalili na bacin raina,tun daga sanda na shigo da ita k

Lamurana kawo yau,yau gashi zata zama sila na tarwastewar qima daraja da martabata data yarona a idanun duniya,abdul’azeez bai taba bujirewa ko saba umarni na ba tunda na haifeshi,koda kuwa bayaso,koda bai dace da ra’ayi ko zabinsa ba sai data shiga rayuwarsa,ta yaya zan dubeta da idanun tausayi ko qauna?,sam sam….matuqar kuma ta zama sila na bacin martabarmu ba shakka sai tayi nadamar sanin fulani aisha da zuria’arta….ku kiramin yarima a waya,ina da buqatar magana dashi” ta bada umarni kai tsaye,ba tare data damu da wanda zai kirashin tsakanin umma luba da mama sodangi ba,burinta kawai ta sameshi a waya taji muryarsa.

    *YARIMA ABDUL’AZEEZ*

      Tun randa ya koma din ya tabbatarwa da ranshi bazai iya zama ba ba tare daya risketa gidansu ba,bisa adreshin da yake gani nata a wayarshi.

      Misalin bakwai na dare ya gama shirinsa cikin shigar sarauta dake nuna ainihin asali da tsatsonsa,dukkan wani cikar kwarjini haiba da kamala sun bayyana tattare dashi,ya dauki mota shi daya ya fita,bisa jagorancin wayarshi dake masa nuni da hanyoyi da kuma titunan da zaibi har ya sadashi da qofar gidan.

      Kyawawan tafiya ta minti talatin da biyu ya tuqe a qofar gidan,cikin nutsuwa ya samu wajen daya dace yayi parking,ya kashe motar ya fito yana kallon wayarshi dake nuno mishi arrow na saitin gidan.

     A hankali ya dauke fuskarshi da kan wayar,ya aza idanunsa ga qofar gidan da yake fuskanta.

      Sosai ya zubama qofar idanu,yana jin wani abu na yawo cikin zuciyarshi da ruhinsa

“Yanzu nan ne ‘ya’yanshi da matarsa suke?,yanzu haka suna ciki?” Saiya dinga jin kamar ya sanya kai kawai cikin gidan,ya shiga ya daukosu kana ya sakasu a mota suyi tafiyarsu,su tafi can da nisa inda zai koya musu sabo dashi,inda zai koya musu yadda zasu qaunaceshi,su rayu abunsu su kadai ba tare da kowa ya shiga ciki ko ya kawo musu cikas ba.

      Yanke tunanin yayi da hanzari yana maida wayar aljihunsa,kana ya soma takawa yana durfafar gidan.

     Dukkansu suna zaune a falo  suna kallo,yayin da najwa kecin abinci daga gefe guda ita da abdurrahman a kwano daya,anty zuhriyya da bilkisu kuma na zaune saman kujera,kusan anty zuhriyya ke kallon sosai fiye da bilkisu,wadda ta kasa hankalinta gida biyu,rabi yana ga tv,rabi kuma yana ga chart da suke da hannatu tana sake tambayarta lamuran gidan nasu,da sauran sabbin abubuwa da batasan dasu ba.

      Ajiyar zuciya ta saki,wadda ta saka anty zuhriyyan juyowa tana kallonta,suka hda idanu,sai bilkisun tace

“Hakanan zuciyata tayi nigeria ummi”

“Mun kusa in sha Allah,don ba lallai abba ya bari mu qara wata biyu bama…..amma tun jiya nakeson tambayarki…..wannan tafiyar nidai a idanuna sai naga sam bata amsheki ba,da kika dawo a birkice na ganki,kamar wadda taje jinya?” Shuru ta danyi zuciyarta tana raurawa,babu wanda ke saurin karantarta irin anty zuhriyyan,bata da wata uwa a yanzu sama da ita,don haka bata boye mata ba,ta karanta komai,duk wani abu daya faru daga zuwanta dubai zuwa dawowarta.

      Shuru itama antyn tayi cikin nazari da tsantsar mamaki,koda zata lamunci komai ita dinma ba zata yarda da tatsuniyarshi na cewa da yayi bilkisun har yanzun matarsa bace,wannan zallar rainin wayone da kuma rainin hankali.

      “Kamar yadda nace miki ne,banason ki sanya damuwa cikin ranki,babu wanda ya isa ya sake shiga rayuwarki kamar daa,babu kuma wanda a yanzu ya isa ya tilastaki ko yi miki dole a dukkan wani sha’ani daya shafi rayuwarki,ki rabu dashi yayita bibiyar,wala’alla lokacin sakayyarki ne ubangiji ya kawo miki,lokacin da zasu girba abinda suka shuka….”.

      Dire kalamanta na qarshe yayi dai dai da soma bugawa da qaraurawar ta somayi,da alama akwai mai neman shigowa ciki kenan.

       Najwa anty zuhriyya ta yiwa umarni taje ta duba,suna ci gaba da tattaunawa da bilkisu,babu jimawa ta dawo fuskarta dauke da murmushi,saboda kalaman da baqon ya gaya mata,kada tace me kama da amatu ne,idan ba haka ba tun daga yau ganin farko zasu fara fada dashi,don tana budewar abinda ta soma gani kenan,bata kuma yi qasa a gwiwa ba ta fada mishi kanta tsaye,yana da tabbacin indai ta fadi hakan ga bilkisi,babu abinda zai sanyata fitowa,daga nan kuma an samu matsala,shi yasa ya buqaci tayi shuru,saidai duk da haka bakinta motsi yakeyi,neman wanda zata gayawa taga mai kama dasu abdul takeyi.

     Cikin mamakin waye baqon nata ta ari hijabin anty zuhriyya da yafi kusa da ita ta saka bayan antyn tace mata

“Wataqila adam ne” sai ta gamsu da hakan,don tasan akwai maganganu masu yawa a bakinsa game da ita da kuma abinda ya faru a duba,saidai kuma ai bai gaya mata zaizo ba,duk da wannan bata fasa fita ba,saboda zarginta yafi qarfafa akan cewa shi dinne.

       Yana tsayr harde da hannayensa a qirjinsa,ya juyawa qofa baya,don haka bata yadda zataga fuskarshi har sai ta iso inda yake tsaye.

      Dab dashi ta soma jiyo qamshin nan da yake tambarinsa a wajenta,yayin da shi kuma jikinsa ya bashi tana dab dashi,ya waiwayo da hanzari lokacin da ita kuma zuciyarta ke gaya mata shine take shirin juyawa cikin gida cikin tsoro fargaba gami da mamakin ta yaya akayi yasan gidansu.

       Cike da kuzari gami da karsashi yayi hanzari shan gabanta kamar zai shigr jikinta yana jifanta da wani irin kalo mai nauyi,sai tayi hanzarin ja baya cikin fushin nan nata dakan taso mata duk sanda sukayi face to face dashi

“Janyemin a hanya zan wuce” sassanyar murmushi ya saki kamar babu wani abun dake damunsa sannan yace

“A fuska kamar baki zubin masu fada ba,amma ga mamakina sai.naji kin iya,a qalla kyadan dagamin qafa kwana da kwanaki bamu hadu ba,banga alamun kinyi kewar koda takurata a gareki ba,bayan ni kuma mahaliccina ne kadai yasan ya na kasance a kwanakin,kin hanamin ganin fuskarki,hakanan ko sau daya baki bari uban daya shekara bakwai baiga fuskokin kyautar da Allah yayi masa ba,hakanan baki barsu su kansu sunji dumin mahaifinsu ba”.

      Zallar rainin wayo qarara ta hango cikin kalamansa,kamar ma ba wani abu bane mai girma tsakaninsu ba,kamar ma ba wani abu ya aikata ma rayuwarta ba,yanason maida komai wasa,yana son maida komai ba komai ba,yanason kuma ya nuna kamar ya manta dukkan abinda ya farun,tunda har gashi yana so yana kuma shauqin ganin yaran da sun suna ciki suna a matsayin gudan jini basu zama mutane ba,to amma sai taga shurunta kamar ma ta bashi dama ne,don haka ta motsa bakinta bayan itama ta harde hannayenta a qirji,ta kuma yi jarumtar saka nata idanun cikin nashi,duk da yadda kaifin nashi idanun ke barazanar dakusar da nata

“Au…don Allah?,amma nayi mamaki da har kake da qarfin gwiwar kiran korarrun yaran da yaranka,ka manta wai kun dade da baiwa uwarsu su?,ya kamata kayi gaggawar ciresu daga sahun yayanka”.

      Yadda take maganar cike da qwarin gwiwa fushi fushi da kuma dakiya ya burgeshi,hakanan ya sake bashi damar qarewa kyakkyawar fuskarta dake samun kulawa ta musamman kallo,jajayen labbanta masu kyawun zubi,baisan yakai hannu ba zai shafi gefan fuskartata ba sai daya kusa sannan ya ankara,yayi hanzarin janye hannun nashi,cikin laushin murya yace

“Calm down baby….fushin bai miki wani kyau,haramunne kuma mace ta dinga dagawa mijinta murya haka,mala’iku suna jinki….” Sai ya matso dab da ita har suna musayar numfashi,muryarsa na sake yin laushi da taushin daka iya kashewa duk wata lafiyayyar mace jiki yace

“Ban fada ba,hakanan har abada bazan taba cewa na barwa duniya ko uwar d’ana ‘ya’yana ba….ni abdul azeez….ko cikin shege na yiwa mace bata isa na bar mata yarona ba,koda zuciyata bata taba sonta ba,mun hadune a rariya,bare ke da kike da wani babban matsayin da duk duniya babu meshi,bare yarana da suke na sunnnah,da kinsan waye azeez da bazaki fadi hakan bama,jinina yana da qima da martaba a idanuna,koda b’arin dana akayi zan girmama inda aka binneshi,pls,na roqeki da dukkan wani abu mai girma….ki barni naga yarana,ki barsu su rabeni,koda ke akaran kanki ba zaki saurareni ba,duk da koda baki saurarenin ba ina mai tabbatar miki da cewa azeez bazai taba qyaleki ko rabuwa dake ba,idan kinayin wadan nan abubuwan don na barki,ina mai farincikin shaida miki cewa….ban gaji ba,bazan kuma gaji ba….idan akwai wasu qarin hanyoyin ma ki dado dukka kiyimin,indai zaki huce,indai zaki sake bani chance na shiga rayuqarki karo na biyu”.

      Mamakin wanne irin mutum ne shi ta tsunduma,dukka kalamansa yanayinsa da yadda take furtasu kawai sun isa gaya maka da gasken gaske yake.

   Baya ta janye ta daga kai zata kalleshi ta gaya masa maganar da zata hanashi barci a yau,sai taga hankalinsa ya raja’a ga bakin qofar gidan.

     A hankali ta wawaya don ganin abunda yake kalla din,amatullah da abdurrahman ne ke kokawa akan bindigar ruwa ta wasa,kowa nason karba,saidai tuni abdur rahman din ya amshe da yake shi din namiji ne,amatu ta soma tattakowa cikin kuka ta nufota,da alamu qara zata kawo mata.

      Bata taba tunanin akwai wani abu da zai sake sanyata gudu ba bayan wanda tayi na quruciya ba sai yau,tuni ta riga azeez din isa ga yaran ta cafki hannayensu,kana cikin mugu sauri ta jasu zuwa cikin gidan ta banko qofa.

     Daidai lokacin da najwa ta kasa haquri take baiwa anty zuhriyya labarin mai kama sak dasu abdul ta gani,shiya aikota kiran anty bilkisu.

      Shuru anty zuhriyya tayi tana dan gajeran nazari,ranta na raya mata waye,duk da cewa tasan shi baisan gidan ba.

     Yanayin yadda bilkisu ta shigo da yaran yasanya ta fahimci inda amsarta take,ko ina na jikinta na rawa,hakanan kuka keson qwace mata

“Maza najwa ku wuce ciki gaba dayanku,oya” anty zuhriyya ta bata umarni,ba jinkiri ta kada kan dukka yaran suka wuce ciki,falon ya rage daga ita sai bilkisun,ta qarasa ta kama hannuwanta

“Meye?,meya faru?”

“Shine ummi,bansan ya akayi yasan gidan nan ba har yazo,yaga su abdul sanda suka fita,har ya taho wajensu,ummi banason ya shiga rayuwarsu,bana son ya qwacemin su,yanzu yasan inda nake zaune” tabe baki anty zuhriyya tayi

“Don yasan gidan nan shine me?,don yaga su abdul sai meye?,kefa bai isa yin komai cikin rayuwarki ba ina gaya miki sai idan kece kika bada qofa kika yarda kin fahimta,babu abinda zai faru kamar yadda na saba shaida miki”.

     

     Tana dire maganar taji ana bude qofar falon gidan,tasan kuma mutum dayane zai.haka wato abbaa,saidai kuma a yadda sukayi dashi zai dawo lokacin dawowarsa bai qarasa ba,don haka ta maida kallonta ga bakin qofar cikin mamaki harya gama budewa ya shigo.

       Da sallama a bakinsa yashigo din,saidai kuma ya karanci kamar akwai abinda ke faruwa saman fuskokinsu

“Lafiya abbaa naga ka dawo tun yanzun?” Anty zuhriyya ta tambayeshi sanda yake zama saman daya daga cikin kujerun fuskarsa na nuna alamun damuwa da kuma rashin walwala

“Wallahi jikin hajiya ne ga motsa sosai,ina can malam ke sanar min,sai naga kawai gwara na dawo mu fara shirin tafiyar nan,a haqura da qarshen watan,cikin satin nan kawai mu wuce mu sauka ringim din gaba daya” cikin yanayi na nuna alhini da kulawa tace

“Subhanallah,amma koda na kirata batace min komai ba,da sauqi kawai ta bini dashi”

“Eh ai batason a fada,haka take cewa kowa”

“Allah ya tashi kafadunta” ta amsa tana barin wajen da suke tsaye da bilkisu,itama bilkisun cikin sanyin jiki gami da sanyin murya tace

“Allah sarki hajiya,Allah ya tashi kafadunta,ya bata lafiya”

“Amin amin” ya amsa kana yace

“Meke faruwa?na shigo na sameku a tsayr carko carko,banji kuma motsin kowa a gidan ba ina duka yaran?” Yanayin damuwar lalurar mahaifiyarsa yasa taga bai kyautu ta sake qara masa damuwa ba,don haka tace

“Babu komai,kawai muna tattaunawa ne,sai kuma ka riskemu a haka” ta qarasa fada tana buda fridge don dauko masa abun sanyi,tana kuma qwalawa yaran kira tana shaida musu dawowar abban nasu,bilkisu kuma ta juya ta shige ciki tana qoqarin daidaita yanayinta.

    Mutuwar tsaye yayi na wucin gadi a wajen da suka shige gida suka barshi,yana jin wani abu yana zagaya qwaqwalwarsa yakuma tsaida tunaninsa na wasu mintuna.

    Ya jima a haka kafin yaji qafafunsa sun soma gardama da tawayen qin karbarsa,hakan yasa ya yiwa kanaa qiyamullaili ya isa ga motarshi ya shiga kana ya rufe.

      Kanshi kawai ya kifa saman sitiyari,fuskokin yaran na yawo cikin idanunsa,wata qauna mai tsanani tasu wadda ta nunka wadda yakeji a baya tana shiga zuciyarsa tana barazanar kekketata,tabbas banda uwa uwa ce,banda fulani mahaifiyarsa ce babu mahaluqin daya iaa yayi masa haka a duniya,saidai uwa ta zarta duk wani tunani dan adam,hakanan takanyi komai ne da sunan soyayya koda zai dawo daga baya ya cutar da rayuwar danta ba tare data ankara da hakan zai iya faruwa ba.

      Har uncle abbaa yazo ya wuce ciki bai sani ba,shima bai lura ba saboda yana cikin mota ne,ya tsammaci maqotansu ne suke da baqi.

¶¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶  ¶¶¶¶¶

     Kwanki uku ya kwashe yana jera zuwa gidan ya zauna bakin qofa,yayita jera mata kira ko saqo kan ta taimaka ta turo yaran ya gansu koda ba zasu iso inda yake ba,idan ba zata barsu ba to ita ta leqo ya ganta,baya damuwa da yawa ko adadin awannin da yake shafewa zaune a wajen ba,burinsa kawai taji tausayinsa ta kuma yi masa alfarma.

     Zuwan nasa tamkar takura yake a wajenta,duk da bata ganin koda qyallinsa,amma duk da haka bata qaunar taji saqonshi na cewa yana zaune a waje,saidai ta sharema zuciyarta,tunda babu abinda zai sanya ta fita bare ya ganta koya tareta,hatta da aiki ta dauki excuse,kuma dr adam baiqi ba ya bata.

    Tana ta kasa kunne ko dr adam din zaice wani abu?,baice ba,amma akwai sanyin jiki daga yadda ya saba waya da ita,saida aka kwana uku sannan yace ta gaya masa yaushe zaizo gida ya sameta,akwai muhimmar maganar da yakeso suyi.

      Ta riga data sani,tasan qarshen labarin,don haka tace dashi

“Zamuje nigeria mu dawo,kayi haquri idan na dawo saimu tattauna kome zamu tattauna din” bai musanta mata ba ya amsa da to.

     ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶

     Kamar kullum,yauma yayi parking motarshi daga gaban gidan kadan,duk da yasan cewa babu lallai ya samu ganinta ita ko yaran,amma a yau yana jin cewa bazai iya jura ba,don haka yana kashe motar ya fito sannan ya kulleta.

      Tsayin mintuna yana duban gidan kana ya durfafeshi kai tsaye cike da qwarin gwiwa da kuma tarin jarumta,ya gaji hakanan,koda zunubin na bisa wuyansa naqin amsar cikin aiya kamata a sassauta masa hakanan,a barshi yaga gudan jininsa.

       A lokacin bilkisu na kitchen ta dora sanwar abincin dare,sanye cikin doguwar riga mai yankakken hannu A shape na wani material mara nauyi,dankwalinsa baida fadi,hakan ya baiwa kwantaccen baqin gashinta dayasha gyara daman bayyana.

      Abdurrahman ne kawai a falon shi da ateeq,amaturrahman da najwa da abid suna backyard na gidan suna wankin undies dinsu,wanda tuni sun riga da sun saba,saidai najwan na tsayawa tare dasune tana gyara musu idan sunyi kuskure.

      Sosai.hankalinsu ya tafi kan cartoon da suke kalla,hakan ya sanya daya daga cikinsu ya kasa tashi yaga waye a bakin qofa,duk da qararrawar dake kadawa,dai dai lokacin anty zuhriyya ke fitowa daga dakinta sanye da hijabin data idar da sallar la’asar tana waya da hajiya.

      Ta gama wayar don haka ta sauketa daga kunnenta,tana qoqarin katsewa tace

“Saboda sakarci kuna jin ana magana a waje amma ku kasa tashi ku bude,koma waye kenan yayita tsaiwa ko?” Ta qarashe maganar tana dosar qofar don ta bude din

“Sorry mommy” a teeq ya fada yana sake gyara zamanshi,don shi kallon yayi masa suger.

     

     A hankali ta buda qofar,idanunta suka sauka kan azeez dake tsaye sosai,irin tsaiwar dake nuna kuzari da cikakken qoshin lafiya gami da cikar halitta.

      Bata buqatar neman qarin bayanin wayeshi,kallo daya zaka masa ka tabbatar da kamanni na zahiri tsakaninsa dasu amaturrahaman,iya kamar kawai ta isa ta gaya mata wayeshi.

       “Barka da yamma anty” ya fada yana dan rusunar da kanshi alamun girmamawa,sosai ta hade ranta,fada takeso da masifa tayi masa sosai,amma baya ga hade ran saita kasa komai,tana jin kwarjininsa yana cika wajen yana kuma cika idanunta

“Yauwa….lafiya?” Bai zaci zata tambaya ba,amma kuma yana tunanin qila bata sanshi ba,don haka cikin dakiya yace

“Nazo ganin twince ne,idan babu damuwa ayimin alfarma na gansu” ya fada yana kallon fuskarta,cikin ranshi yana addu’ar samun nasara.

      Shuru tayi tamkar mai wani tunanin,tana son tace masa aah ne,tana son gaya masa maganar dake yawo kan bakinta amma kwarjininsa nason rufeta,daga qarshe sai kawai ta samu kanta da juyawa zuwa ciki,muryarta ciki ciki tace

“Bismillah” kana ji kasan wani abu ya tilastata fadan haka din.

     Nannauyar ajiyar zuciya ya saki,a hankali yana shafa qirjinsa da hannu daya gami da lumshe kyawawan idanunsa yace

“Alhamdulillahi rabbil Aalamin” a nutse yabi bayan nata zuwa ciki.

       Tuni ita ta isa cikin falon,ta kuma aika ateeq ya kira amaturrahman,ya shiga kitchen ya samu lemo da ruwa ya kawo falon,daga haka tayi shigewarta ciki.

      Da abdurrahman ya soma tozali,kasa zama yayi yaji zuciyarsa na wani irin bugawa kamar yaga abun tsoro,ya zubawa yaron idanu,wanda sam shi baisan me ake bama,kamar kuma ance kalli bayanka,saiya waiwayo,take suka hada ido dashi,tsaiwa yaron yayi shima kamar mai tunani ya zubawa azeez idanu na wasu sakanni,hakanan kuma saiya saki murmushi yana cewa

“Ina wuni uncle” murmushin shima ya sake sama,kana ya miqa masa hannunsa alamun ya taho,kamar me tunanin wani abu ya tsaya yana dubanshi,sai kuma ya taso a hankali yana takowa inda yake.

      Yana zuwa azeez din ya janyoshi jikinsa,ya rungumeshi gam yana jin wani maganadisu cikin zuciyarsa,tarin qaunar yaron tana motsawa daga ainihin zuciyarsa,koda ba’a fada ba yasan photocopy dinsa ne sak!,kamar yayi kaki ya ajjiye.

 

      “Kaiiiii” yaji ance,sai a sannan hankalinsa yakai kai,amaturrahman ce tsaye daura dasu tana kallonsu,cikin mamakin ganin me kama da ya abdul dinta.

      Tattausan murmushi ya saka yanajin qwalla na shirin taho masa,ya miqa mata hannu itama,amma saita noqe,saboda tana sa wuyar sabo da rashin yarda,abdul dake zaune saman cinyarsa yace

“Kizo kiji amatu,yace waishine daddynmu”

“Daddy?” Ta maimaita cike da mamaki da zumudi,kalmar data dade tana son ji sakamakon yadda kullum ‘yan ajinsu kowa baida zance saina mom dinsa da dad dinsa,wannan ya sanyata tahowa itama harda saurinta,ya hadasu gaba daya ya sake rungumewa yana yiwa Allah kirari gami da shafar kawunansu,yana jin wani irin madaukakin farinciki yana ratsashi,wani abu daya qulle masa daga qirjinsa zuwa zuciya shekaru bakwai baya yaji yana raguwa gamida narkewa.

      Daga kitchen kuwa sanda ateeq ya shiga tana gyaran salad,ya isa ma’ajiyar farantai da kofuna ya soma hadosu hadin gambiza,saita kalleshi

“Me kuma zakayi dasu?”

“Baqi akayi ummi tace nakai musu ruwa” amshewa tayi tana maidasu inda suke tana sake zabo wasu

“Shine zaka dauki kofuna wari da wari haka?” Ita ta shirya masa komai saman farantin ta bashi,saidai kafin yakai ga fita santsin tiles ya kwasheshi ya watsar da wasu kayan,Allah yasa kofunan basu zubeba,ta qaraso da sauri ta amsa

“Allah ya shiryeka,banda abun ummi ta manta dama ba’a abun arziqi dakai?,bani nan suna can suna zaman jira” karbe tray din tayi tayi gaba zuwa falon da zummar takaiwa baqin ta dawo taci gaba da girkinta.

      Sam bata taba kawowa a ranta baqi maza bane,tunda tasan antyn babu wani namiji da take mu’amala dashi dahar zata kawoshi gida,abbaa kuma baya nan bare tayi tunanin mazanne,hakanan tunaninta ko mafarkinta bai taba kawo mata cewa wai abdul’azees bane cikin falon nasu.⁶¹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *