SIRADIN RAYUWA CHAPTER 20
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Tashi rago kawai” kalmar daya fada kenan,firgigit azeez ya bude idanunsa yana ambaton sunan Allah,saiya maida nutsuwarsa jikinsa cikin mamaki ganin me martaba zaune a gabanshi,kanshi ya sadda cikin jin nauyi,sannan a hankali cikin muryar marasa lafiya yace
“Barka da asuba” maimakon ya amsa mishi sai yace
“Ban taba tsammanin cewa kai din rago bane sai yanzu,shine ka zauna akan mace zaka mutu saboda tsabar ragwantaka?” Shuru azeez din yayi qirjinsa na bugawa,shi kadai yasan me yakeji,yana da tabbacin ba zasu gane ba,yayin da me martaba yaci gaba da kallonshi yana murmushi sannan ya kuma cewa
“Dago kanka ka kalleni”yayi maganar yana nade hannun rigar dake jikinsa me zubin alkyabba,dagowar yayi kamar yadda me martaba yace yana dubanshi
“ka ganni nan?” Ya fada yana nuna yatsarsa
“Ba’a tabani kasani akan mace ba,idan na qudirta a raina saina sameki saina samu…..ka tambayi mamarka….itace babbar shaida,mutum nawa na kasa a mali,na rabota dacan na kawota nan,amma kai mace daya ka kasa controlling tunaninta da soyayyarta zuwa kanka….koda yake,Allah baya goyon bayan zalunci” ya fada yana maida hannun rigarsa,wanda ya nadeta ne dama don ya nuna mishi qwanjinsa sanda yake masa misali da qarfin da yake dashi na qwatar soyayya.
“Tunda kai ka gaza yin komai mu munyi maka…..na maka bikon matarka amm….” Baiko jira yaji qarshen maganar ba gaba daya ya kama hannunshi ya riqe gam,bakinsa yana motsi ba tare da ya iya furta komai ba,dubanshi me martaba yake shima yana dariya
“Sakarmin hannu mana,yada saurin murna haka bakaji qarshen zancan ba” kunya ta kamashi,ya zame hannunsa daga cikin na me martaba
“Zata koma aduk sanda ta gamsu a karan kanta,wanda ni na bata wannan damar,saboda kada shiga haqqin nata yayi yawa” saiya sauya yanayin fuskarsa sannan ya koma sarki abdallahnsa sosai
“Abdul’azeez,abinda kuka shirya kuka aiwatar kaida mahaifiyarka yayi.masifar batamin rai da bani mamaki,ya nuna cewa bakusan daraja da qimata ba,hakanan baku daukeni a bakin komai ba,duk da cewa laifin mahaifiyarka shine kaso casa’in cikin dari,kai kuma kana da goma….”
“Abdul’azeez,nine uba kuma mahaifi a gareka,nine wanda nafi cancanta tun asali ka soma shaidawa cewa kana da buqatar aure,bawai mahaifiyarka kadai ba,dukkan wata dama ta sakin fuska da yadda zamu shaqu da juna na baku ita,sabida ire iren wadan nan abubuwan na rayuwa,bare kace babu fuskar da zaka shaidamin hakan,inda na godewa Allah ka shaida matan itama,baka shiga baragurbin rayuwa da matan bariki ba,irin yadda wasu daga cikin matasa da suka samu dama irin taku suke shiga ba,na godewa Allah daya zama kun hadune ta halastacciyar hanya,hakanan jikokina sun fito ya halastacciyar hanya”
“Abu na biyu shine,babu biyayya ga abun halitta wajen sabawa mahalicci,a duk sanda ka fuskanci mahaifiyarka takauce hanya,kayi qoqarin dawo da ita hanya ta mu’amala me kyau,da kuma tausasa lafazi,idan hakan bata samu ba kuma,itama tana dana gaba da ita,kayi qoqarin shaida musu saboda kauda ita daga fadawa halaka,wanda kai baka aikata hakan ba,sai kaci gaba da yi mata biyayya ba tare da kayi yunqurin shaida min ba”
“Na uku baka duba dukkan nauyin haqqin dan adam dake wuyanka ba,ka iya sakar musu yarinya don kawai mahaifiyarka ta baka umarni,wannan shine kuskure na qarshe mafi girma wanda ayanzu kaga ishara,saidai ka roqi Allah wannan jiyyar dakayi ya zame maka kaffarar zunubin dake tsakaninka da mahaliccinka,ita kuma yarinyar kayi qoqarin neman yafiya da afuwarta itama,ka kuma riqeta da kyau riqon tsauri,ka gyara duk wata baraka data taba giftawa tsakaninku,Allah ya gani,ni nayi iya nawa yin,sauran gyaran kuma ya rage naka”.
Kanshi a qas,cike da gamsuwa da kuma nadama yakewa mai martaba godiya,qauna da qimar mahaifin nashi na sake qaruwa cikin ranshi,bai wani jima sosai ba yayi mishi sallama ya tafi.
Sosai ya shiga zurfin tunani bayan fitar me martaba,can qasan ranshi yanajin wani dadi da farinciki na musamman yana ratsashi,ji yake kaman ya fice daga asibitin a yanxu ya tafi ganinta,saidai kuma babu wannan damar,saboda wani plan da ya tsara ma ranshi,wanda itace ha ya mafi sauqi da zata kawo masa bilkisun har dakin asibitin ba tare da anja wasu dogayen kwanaki ba.
Daga dakin da aka kwantar da azeez din likitan dake ganin azeez din me martaba ya nemi gani,yaci sa’s kuma aikij kwana yayi,kuma baikai ga tafiya ba.
Maganganu sukayi dashi har na wajen mintun ashirin,kana daga bisani yabar asibitin.
Cikin ‘yan rakiyarta hadimai ta shigo cikin asibitin,wanda tun kafin takai ga shiga dakin da azeez din ke kwance likitan ya nemi ganinta idan ta iso,bata jira ya isketa ba,ita ta iskeshi a office dinsa,don dama cike take da fargaba da taraddi kan bayanan da zataji kan sakamakon da gwaje gwajen azeez din.
“Ranki ya dade kamar dai yadda na taba gaya miki ne a baya,babu abinda ke shirin illatar masa da zuciya ta hanyar gagarumin hawan jini irin damuwa,damuwace a zuciyarsa wadda da alama ba tun yau ba yake fama da ita,wanda idan har ba’a dauki matakin yaye masa ko kawo masa qarshenta ba yaci gaba da kasancewa a halin da yake ciki nan da kowanne lokaci za’a iya rasashi,naso boye muku amma naga babu amfanin hakan,na riga dana shaidawa me martaba ma wannan bayanin,saboda haka inaga abinda yafi kawai shine,ayi qoqarin ganin an kauda masa da wannan damuwar,idan ba haka ba komai na iya faruwa”
Duk da acn dake karade office din,amma hakan bai hana gumi yankowa fulanin ba,ta kasa furta komai illa
“Na gode dr” daga haka ta miqe ta fice daga office din.
Duk wanda suka taho tare yasan cewa ta sake ficewa daga hayyacinta,dakin da azeez ke kwance ta tura ta shiga,idanunta a kanshi,saitaganshi kwance miqe kamar yadda ta barshi a jiya,babu wani alamun sauyi,kada dai ace tun jiyan ba wani ci gaba da aka samu?”tayiwa kanta wannan tambayar,sai taji hankalinta ya tashi,ta qarasa bakin gadon ta tsura mishi idanu,ramar da yayi ta bayyana muraran,saita dora hannunta saman sumarshi a hankali.
Karon farko taji wani abu mai kama da tausayi da nadama suna shigarta,abinda ta aikata din ya dinga dawo mata tiryan tiryan,ya akayi?,garin yaya ta fice haka a hayyancinta,idan hadin auren da rabasun da tayi tana sane kuma akwai.manufa daga baya hujjojin da suka dinga bayyana kansu meya hanata karbesu?,azeez ne fa,yaron daya fita daban cikin ‘ya’yanta,mutumin da tun daga quruciya zuwa girma bata bashi umarni ya tsallake ba,baisan cewa a’ah ba kan dukkan wani umarni nata ba,komai tace masa yakan ce to,komai tsananinsa ko rashin dacewarsa da nasa ra’ayin,me yasa zata katase masa farinciki cikin rayuwarsa?,me yasa ba zataso abinda yakeso ba?.
Saita tuna da twince dinsa,idan itace aka rabata dashi da afnan yaya zataji a ranta?,ta tuna dukkan wata gwagwarmaya da tayi cikin masarautar kaisa,wanda dukkanta ta yita ne saboda kare yaranta,saboda ta rayu dasu,amma shi me yasa ta zama silar rabuwarsu tsahon shekaru,amma duk da haka bai fasa mata biyayya ba,bai taba fasa kallonta a matsayin uwa ba,bai fasa mata biyayya ba,tabbas ya cika da na halas wanda ya cancanci samun aljanna,indai hakane….indai yayi dukka komai saboda ita itama ya kamata tayi komai saboda shi,idan tace komai din ciki harda dawo masa da bilkisun dama yaranshi cikin rayuwarsa gaba daya ba tare da jinkiri ba.
Tana kaiwa qarshen tunanin ta sauke hannunta daga kanshi,sannan ta juya da hanzari ta doshi qofar fita,abdul’azeez da tun tsayin tsaiwarta saman kanshi yana jinta,saiya bude idonsa guda daya a hankali ya bita da kallo,yana jin qamshin nasara cikin ranshi.
Ta bude handle din qofar ta jata baya ta zura jikinta zata fita suka kusa gware,safwa ce a gaba cikin yanayi na rudewa,mahaifiyarta na biye da ita,sai mai aikinsu wadda babba ce biye dasu da kwanduna na alfarma riqe a hannunta.
Kallo daya zaka yima fulanin kasan qasaitar ta motsa,san fuskarta babu wannan annurin da yanayin da takan tarbesu dashi,a tsaitsaye daga nan bakin qofar sukayi magana da bata wuce biyu ba da mmn safwa tayi gaba,tana kiran sunayen hadimanta da zata fita dasu din.
Yau din tun safe da suka tashi bilkisu ta hada kan matan zuwa kitso da gyaran gashi,anty zuhriyya kuma ta dauki samarin don su rakata siyayya kasuwa,saboda shiryen shiryen daukan azumin watan ramadan da akeyi a sati me zuwa,hakan ya sanya gidan babu kowa sai mai gadi da kuma me aikin anty zuhriyyar.
Tafiyar mintuna talatin fulani aisha ta yima gidan anty zuhriyyar tsinke,tun daga bakin gate me gadi ya gaya mata cikin girmamawa basunan saboda ya shaida wacece ita,amma saita zabi zama ta jira dawowarsu koda awanni nawa zasuyi.
A farfajiyar gidan ta umarci dukka hadiman nata su zauna su jirata,yayin data shiga gidan ita kadai.
Mamaki sosai ya kama mai aikin anty zuhriyya ganin wacece baquwar tasu,don wancan karan da tazo ita taje ganin gida batasan da zuwan nata ba,fuskar fulani aishan ba boyayya bace musamman ga ma’abota kallon tv ko yawaita karatun jarida,kasancewar tana da qungiyoyin tallafawa gajiyayyu da marasa qarfi,hakanan tana yawan bada tallafi a duk wani sha’ani da xai taso cikin qasar kaisa,hakan yasanya mai aikin yi mata tarba me kyau bayan ta shaida mata basu nan,amma sun jima da fitama,sunce kuma ba zasu dade ba,tace babu damuwa,zata jirayi dawowarsu.
Wayar dake cikin kitchen ta dauka ta kira anty zuhriyya don shaida mata tayi baquwa
“Wacece?” Ta tambayeta,cikin zumudi ta shaida mata
“Matar me martaba ce wallahi ummi”
“Matar me martaba?” Ta ambata cikin mamaki,tare da tunanin meye kuma ya sake dawowa da ita
“Eh wallahi,harma ta zauna tana jiran dawowarku”. Itama anty zuhriyyan sai abun ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,to meke tafe da ita?,koma meye batason haduwarsu da bilkisu,don hakan kamar zai sake tarwatsa duk wata ‘yar yarda da nutsuwa dake zuciyar bilkisun,don haka tace
“Ohk,shikenan muna hanya” daga haka ta katse kiran,saita lalubi sabuwar lambar bilkisun kan wayar data sauya.
Bugu biyu ta daga,tambaya ta soma jefo mata
“Kina ina?” Bata kawo komai a ranta ta amsa.mata
“An gama mana ummi,yanxu muka fito daga wajen,mun hau titi ma” ajiyar zuciya ta sauke,babu yadda zatayi ta maidata,hala yau din ya zama dole ne su hadu shi yasa Allah ya shirya hakan,jin tayi shuru yasa bilkisun cewa
“Lafiya ummi?”
“Babu komai,saikun iso,nima ina hanya” ta kashe wayar ta mayar jaka,saita haqura da sauran abubuwan da bata siya din ba,aka zuba mata sauran siyayyar a mota itama ta dauki hanyar gida.
A qofar gida me adaidaita ya saukesu bilkisun suka shigo gidan da qafa,amatu na shiga da gudu tana biye da ita tana qwala mata kira tare da matan fadan gudun banza.
Daidai lokacin da fulanin ke zaune a falon,jin sabbin muryoyi ya sanyata zubawa qofar shigowar ido bayan ta miqe ta sake matsowa tana jiran ganin masu shigowar cikin qaguwa.
Amatu ce first,don haka tayi caraf ta dauketa,wanda yarinyar bata zaci haka ba,hakan yadan bata tsoro,data kalli fuskarta kuma saita tuna lokacin data taba zuwa gidan,tayi wajensu,anty zuhriyya ta hanata tabasu,hakan ya sake bata tsoro,saita saki wani dan guntun ihu tana zillewa daga hannunta.
Tunda ta shigo farfajiyar tayi arba dasu jikinta taji sam bai bata ba,tunaninta daya daga ina suke?su waye su?,dan ihun amatun ya sanyata zabura itada najwa zuwa cikin falon gidan cikin gudu gudu sauri sauri.
Dai dai lokacin da me aikin anty zuhriyya ke dariya tana cewa
“Meye haka biyu?,baki santa ba ko?,ai dafa gareta dama,uwarta tafi ganewa fiye da kowa”.
Cak bilkisun ta tsaya ana kallon kallo tsakaninta da fulani,fulani na qare mata kallo zuciyarta na gaya mata tabbas itace bilkisun,don ta jima da haddace fuskarta a tarin tulin hotunan da aka dinga ruwansu cikin masarauta,yayin da bilkisu zuciyarta ke bugawa da wani irin sauri,idan har dai dai idanunta ke gane mata fulani aisha ce a gabanta,matar me martaba,mahaifiyar yarima azeez,matar da takan ci karo da hotunanta ko ganin fuskarta a akwatunan tv na qasar nan,mai tarin bada tallafi da taimako ga mabuqata,matar da take ga halinta ya saba da ayyukanta,matar da kullum taga ana yabonta mamaki kan cikata,taga zallar rashin sanin wacece ita yasa jama’a ke yabonta,matar data zama silar wanzuwar komai cikin rayuwarta.
Sallamar anty zuhriyya ta karade falon wanda itama ta fado ne da hanzarinta,a hankali ta waiwaya suka hada idanu da anty xuhriyyan,saita dauke kai a hankali ta soma takawa zuwa hanyar dakinta ba tare data furta wata kalma ba.
Babu wanda ya tsaidata cikinsu,hakanan ba wanda yace mata komai harta bacewa ganinsu,sai data bace din kana anty zuhriyya ta qaraso zuwa cikin falon,fuskarta a tamke,murya a kausashe ta soma magana
“Me kuma ya sake dawo dake cikin gidan n……”
“Sulhu,sulhu nake nema domin girman Allah da darajar manzonsa” tayi maganar cikin matuqar sanyi tana hade hannayenta biyu waje daya,domin a yanzun ta shirya yin komai don ta daidaita lamura,don ta wanke kanta,don kuma ta maida komai kan muhalli da mixaninsa
Tunda ta shiga hakanan taji zuciyarta na mata wani irin suya da suka,tsahon lokaci tana kaiwa da kawowa tsakanin bakin madubi bakin gado zuwa bakin qofa,kawai sai zuciyarta ta bata shawarar ta hada kayanta dana su amatu,idan da hali ta tafi jigawa tayi axumi da sallarta ma gaba daya,ba tare da takurar kowa ba,sai wanda taso gani ko yin magana dashi.
Tana tsaka da hada kayan babu ji babu gani tsayin wasu mintuna masu tsaho taji anyi knocking qofar sannan aka turo qofar a hankali gami da yin sallama.
Tana ci gaba da hada kayan ta daga kai ta dubi me shigowar,ba kowa bace face fulani aisha,idanuwanta akanta take takowa zuwa cikin dakin fuskarta akwai wani irin sanyi da laushi.
Duk da ganin shigowarta dakin hakan bai sanyata ta fasa aikin da takeyi ba,saita maida kanta taci gaba dayi kamar bata ga shigowar tata ba.
A qalla mintuna kusan biyar tana a tsaye a bayan bilkisun,tana tattauna duk wata kalma ko magana da xata gaya mata,yayin da ita kuma bilkisu ke ci gaba da aikin nata tuquru,ta cika wani akwatin ta bude wani tana sake zuba wasu kayan a ciki.
Caraf taji an riqe hannunta sanda take duqe tana saka wasu kayan sanyi nasu amatu cikin akwatin,saita tsaya din,hannayenta duka biyu fulani ta sanya a kafadan bilkisun kana ta dagota suna fuskantar juna.
“Kome kikayi kinyi dai dai,duk hukuncin da kika yanke wallahi bakiyi laifi ba,saboda na cancanci keda mamarki kuyimin koma meye,a hakanma adalci kuka yimin…..bilkisu…..bansan wacce kalma ce zata sanyaki jin salama a ranki ba,bansan kalmar da zan fada wadda zata shafe girman zunubina a wajenki ba,bansan kalmar da zatayi dai dai da laifina ba bare ta karkato dake wajen yimin afuwa…..amma duk da haka” sai tayi shuru tana jin qunci na cika zuciyarta,quncin cutar da rayuwar wani wanda baiji ba bai gani ba,shurunta ya sanua bilkisu daga idanunta dake cike taf da bacin rai ta dubeta,sai taga qwalla ce a cike taf
“Ina roqonki da girman Allah…..ina hadaki da darajar iyayenki da dukkan wani abu me daraja a wanjenki daki taimaka ki yafemin,kimin afuwa,ki tausaya ki yafemin ki kuma yafewa abdul’azeez,wanda dukkan abinda ya aikata ya aikata ne bisa umarnina,dukkan abinda ya faru babu shawarinsa…babu son ranshi….hakanan babu saka hannunshi face shawarata wdda ta zama gurguwa kuma mara amfani….” Hannunta ta hade dana bilkisun cikin sanyi tace
“Ki bani koda minti biyar ne na gaya miki dukkan dalilan da yasa nayi tunani kan wannan gurguwar shawarar…..hassadar mahassada da maqiya ta hankadani cikin babban kuskure dake dab da tarwatsa duk wata qima da darajar ahalina”.
Bata boyewa bilkisun komai ba ta zayyane mata yadda abun ya fara,sosai ta tsinkayi abubuwa masu yawa cikin labarin,kura kurai da kuma daidanta,da inda tayi saken da har hakan ta faru.
Wani abu ya sauka gefan zuciyarta,saidai har yanzu zafin da takeji cikin zuciyarta akwai sauranshi
“Ki duba dukkan hukuncin daya dace kiyimin na yiwa rayuwarki karan tsaye bilkisu…..amma kuma ki taimaka ki yafemin,kiyimin afuwa kan mummunan kuskuren da na aikatawa rayuwarki” saita soma tattare alkyabbarta tana shirin rusunawa a gabanta.
Cikin azama da sauri wanda batasan tana dashi ba ta tareta,tunda can itadin mutum ce mai matuqar girmama babba,duk yadda kakai ga lalacewar matuqar ka girmeta toba shakka zata martabaka,hakanne yasa hatta da umma katti,duk da irin xaman da sukayi dai dai da rana daya bata taba daga idanu ko ta kada baki tayi mata rashin kunya ba,hakanan bata fasa bata girmanta ba,bata iya gani babba ya tozarta ko yaji ya wulaqanta sanadinta.
Baya ta juya mata da sauri bayan ta tabbatar ta tsaya da qafafunta,tana qoqarin boye hawayen fuskarta saboda mahaifiyarta data tuna a lokacin
“Mahaifina” ta furta a hankali tana son saisaita muryarta
“Shine wanda yafi cancanta kiyi wannan tsaiwar a gabanshi….shine yake da iko da fada a kaina,shine mafi cancanta” daga haka tayi gaba da hanzari,ta fada toilet sannan ta sake rufewa kuka na qwace mata.
Tausayinta ya ratsa zuciyar fulani cike fiye da tsammani,ta girgixa kai kana cikin daga murya kadan yadda tasan bilkisun zata iya jinta tace
“Yanzu kuwa….na gode qwarai….na gode damar da kika bani” daga haka ta juya da sassarfa ta fice.
Azaune ta cimma anty zuhriyya a falon yadda ta barta,fuskarta qunshe da murmushi tace
“Haqiqa kun nuna min cewa kudin masu karamci ne,sannan na koya daga gareku abubuwa masu tarin yawa…..amma dai,ayimin alfarma bayan na dawo daga wajen baba,koda zaku riqe twince ku bani diyata na tafi da ita don Allah” murmushi kawai anty zuhriyya ta bita dashi har zuwa sanda tabar falon zuwa waje,sai sannan anty zuhriyyan ta miqe ta nufi dakin bilkisu.
A duqe ta sameta bakin gado tana kuka
“Kukan me zakiyi daughter…..bayan Allah ya gama yi miki komai,ubangiji ya dubeki ya amso miki darajarki da martabarki cikin sauqi?” Ta fada tana isa bakin gadon.
Maganganu tayi mata sosai masu kwantar da hankali da sanya rai nutsuwa,sannan taji yadda sukayi da fulanin,cikin gamsuwa take gyada kai
“Kin cika ‘ya ba shakka kin cika diyar arxiqi,kin kuma kuma fito da martaba da qimar mahaifinki,duk da kasancewarsa mai tarin laifi da zunubi a wajenki,Allah yayi miki albarka ya kuma zaba miki abinda yafi alkhairi.
¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
Daga nan inda take zaune tana iya jiyo sababinsa fes
“Me zanzo nayi musu?,cuta dai nida diyata an mana ita,sannan bamu sake tunanin mun hada komai dasu ba,kamar yadda a zahirin bamu hada ba bare suce sunzo amsa,don wallahi ko sama da qasa zata hadu wannan karon babu me kwashemin jikoki,ba sarauta ba Allah yasa tsinin mashi ne……ke ni wallahi banqi ayi mutuwar kasko ba,a fasa kowa yaji” kalaman malam bilya kenan dake zaune daga falonshi,bayan umma katti ta isar masa da saqon son ganinshi da fulani keda buqata,duk da yasan komai,anty zuhriyya ma ta sake masa bayani ta waya.
Juyin duniya ba wanda umma katti batayi dashi ba amma yace sam shi a yanzu bashi da magana dasu,duk yadda fulani taso hakanan ta haqura ta koma,amma duk da hakan bata fasa dawowa a washegari da safe ba.
Lokacin yana tsakiyar yan yaranshi da a yanzun suka zame masa sanyin idaniya suna breakfast tayi sallama ta shigo,take yayi wani kicin kicin kana ya soma yunqurin tashi yana cewa
“Duk son abun duniya yajamin,yake shirin hanani sukuni”
“Don darajar ma’aiki ka tsaya ka saurareni”
“Pls abba” cewar hannatu itama cikin marairaicewa,don ita kanta tana sha’awar ganin antyn nasu cikin dakin aurenta cikin yaranta kuma cikin farinciki.
Yana harhada rai ya koma ya zauna,sai duk yaran suka tattara kayan abincin suka fice dasu suka basu waje.
Cikin yanayin dake nuna zallar nadama da kuma laushinta ta soma magana
“Da farko ina me neman afuwa a gareka da bilkisu da kuma yaransu gaba daya bisa abinda na aikata,ina fata zaku yafemin don girman zatin Allah ba domin wani abu ba,tabbas nayi nadama bisa kuskure da kuma gangancin dana aikata,wanda bansan meya jagorance ni kan aikata wannan abun ba,sai yanzu Allah ya budemin idanuna nake ganin girma da xunubin dana aikata….ina me neman gafararka tare da neman afuwa,da kuma alfarmar komawar bilkisu taci gaba da rayuwa cikin iyali da ahalin kaisa a matsayin suruka kuma daya daga cikin ‘ya’yan masarauta,mata ga abdul’azeez,kamar yadda ta nema nazo na fara samun izini daga wajenka” shuru yayi yana sauraren kalamanta,tabbas idan bera nada sata to daddawa ma tana da warinta,idan tana da laifi shima akwai nashi,saidai suyi 50 50,don kusan komai ya faru ne bisa goyon bayanshi tallafawarshi amincewarsa dama yardarshi,a yanzun babban abinda xaiyi wanda zai hadu ya gyara dukka kurakurenshi shine amincewarsa ta koma gidanta,kamar yadda ya amincewa mai martaba,amma duk da haka bazaiyi saurin bawa matar kai ba,don haka yace
“Allah ya yafe mana gaba daya…..amma batun komawarta duk da cewa matarsa ce sai nayi nazari akai saboda gujewa afkuwar matsala,xan kuma sake jin ta bakin yarinyar da tabbatar da amincewarta” bata tsawwala ba,jikinta ya bata tunda anzo nan wajen to ba shakka komai yazo qarshe,saboda haka ta mishi godiya tafice suka bar gidan ita da tawagarta.
Washegari tana zaune tana yiwa amatu kitso bayan ta gama yiwa najwa kiran mahaifinta ya shiga wayarta,tabar abinda take ta soma daga wayar ta sanyata a handsfree sannan ta aje tana ci gaba da yiwa amatun kitso tana amsawa.
A ladabce ta gaidashi ya amsa mata kafin ya fara gaya mata dalilin kiran,nasiha ya soma mata mai dan tsaho sa’annan ya kuma neman gafararta da yafiya,wanda baya gajiya kullum da nemanta,kullum kwanan duniya yana ji ne kamar yacutar da maimunatu,ita kuma nauyin hakan takeji,sai daya gama sannan ya dora
“Jiya mahaifiyar mijinki tazo ta sameni ta nemi yafiya da gafarata kamar yadda mahaifinsa ya nema daga gareni,duk wani gata da xamu nuna miki baikai mu ganki dakin mijinki ba,saboda haka nake sake baki haquri da cewa komai ya wuce,kuma idan da hali duk sa’ad da suka nema toki koma dakinki ki riqe yaranki” cikin zuciya da mutuwar jiki tace
“In sha Allahu baba”
“Allah yayi miki albarka bilkisu yasa ki gama da duniya lafiya,yadda kika bini Allah yasa naki yaran su biki” addu’a ya mata sosai kafin suyi sallama su kashe wayar.
“Ah to,ya kamata ki soma shiri sosai” anty zuhriyya ta fada tana dubanta,haka nan takejin fargaba da faduwar gaba na ziyartarta,kamar cewa akayi gobe za’a daura mata aure karo na farko a rayuwarta,itadai bata iya cewa komai ba,cikin sanyin jiki taci gaba da yiwa amatu kitson.
A daren hakanan ta samu kanta da yiwa assadiq da dr adam saqo na taqaitaccen bayani,kana tayi blocking din duka numbers dinsu a watsapp da kuma kira.
Ta sani cewa koda assadiq zai dauki abun da sauqi tofa dr adam.ba haka bane daga wajensa,amma ta san dole daga qarshe yayi haquri,kamar yadda tayi haquri ta karbi qaddararta a yadda tazo mata.
Hakanan babu amfanin boye musu koci gaba da batawa juna lokaci,tunda dai mai afkuwa ta riga afku.
¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶
A hankali abdulrashid ya tura qofar dakin ya shiga,sai kuma ya tsaya yana kallon azeez wanda ke zaune saman gadon nashi,bayanshi jingine da bango yana kurbar tea a cup a nutse.
Da idanu azeez din ya tambayeshi kallon me yake masa haka?,saiya sako qofar ya qaraso ciki yana cewa
“Abunne to ai ya bani mamaki…..yadda fulani ta nunamin jikinka ya tsananta ne sosai,na tsammaci zanzo na ganka ne a kwance,saina sameka ma kana baiwa cikinka haqqinsa” bai cewa abdulrashid din komai ba illa idanu daya bishi dashi harya qaraso gabansa ya tsaya,sannan a hankali ya furta
“BASAJA mana” shuru abdulrashid yayi yana dubanshi,yanason fahintar abinda yake fada,ya gane me ya sanyashi tsaiwa haka,saiya dage masa gira
“Ka dauki haske mana haba” dariya sosai ta kubcewa abdul,saiya kaima azeez din duka da hannu ya kauce
“Allah ya isa….amma kai kam baka cika mutunci ba,ashe linqui kawai.kayi saman katifar asibiti ana jinyar banza da wofi?” Bai amsa mishi ba sai murmushi daya saki kawai ya aje cup din hannunsa,kana ya lumshe idanunsa yana jingine da bangon hadi da harde hannyensa a qirji,shi kansa baisan yaya akayi wannan idea din tazo masa ba,bai taba zaton zai iya aikata hakan ba
“To ai kuwa inajin basajarka ga cimma nasara” abdul ya fada yana zama gefansa.
Bude idanunsa yayi da sauri cikin mamaki,kamar xaice wani abun sai kuma ya fasa,ya zubawa abdul din idanu kawai yana jiran qarin bayani
“Tunda ba xaka iya buda baki ka tambaya ba shikenan” ya fadi yana dage kafadunsa,sai azeez din ya.maida idanunsa kawai ya kulle,cikin zuciyarsa yana addu’ar Allah yasa haqan tasa da gaske ta cimma ruwa
“Ga fulani nan isowa” abdul.ya fada da sauri yana hango tahowar tata ta qofar da bata gama rufuwa duka ba,cikin sauri azeez ya gyara kwancinyarsa,gami da sake rufe idanunsa kamar yadda yake daxun.
Hankalinta a kansa sanda ta shigo
“Yaya….lafiya abdulrashid?” Cikin fuska mai cike da alhini ya girgiza kai
“Jikinne yaketa motsawa,tunda na shigo sai yanzun ya samu ya koma barci” ya fada yana zagin azeez a xuciyarsa gamida danne dariyarsa,ya dade da sanin waye azeez din yasan takan tsiya sosai,hakanan tarin fikira gareshi da iya shirya abubuwa.
¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶¶
Fitowarta kenan daga wanka,tana gaban madubi tana shafa mai tana jin yadda jikinta ke fidda wani sirrin qamshi na daban,irin gyaran anty zuhriyya kenan,wanda sai data hadata da hajiyan ringim sannan takebin tsarin nata.
Muryar anty zuhiryya ta jiyo tana doso dakin,babu jimawa ta tura qofar dakin ta shigo,tana maqale da waya a kunnenta.
Kai tsaye ta cire wayar daga kunnenta ta miqa mata,tasa hannu ta karba duk da batasan waye ba,sai data saka a kunnenta sannan ta gane ashe abbaa ne.
Gaidashi ta soma yi duk da cewa sun gaisa daxun da safe kafin ya fita
“Ki shirya maigado keda umminki yanzu,ku shirya kuje ku gano yarima a asibiti” idanu ta zaro waje antyn na kallonta,akwai girmamawa mai dumbin yawa da biyayya tsakaninsu,don haka ta amsa mishi da to ta miqawa anty zuhriyya wayar tana dan kyabe fuska,ganin harta juya zata fita batace komai da ita va ya sanya tace
“Ummi….yanzu zuwa zamuyi?” Waiwayowa tayi tana dubanta
“Toko na kira miki shi ki masa bayani?” Ta fada tana danna wayar,da sauri ta daga hannu
“A’ah ummi…don Allah ki masa bayani mana da kanki”
“Nace masa me?” Ta tambayeta tana tsareta da ido,saita kasa amsa mata
“Nace masa maigado tace ba zataje duba uban yaranta ba da yake kwance rai a hannun Allah?”maganarta ta qarshe ta sanyayar mata da jiki,ta kuma sanyata yin shurun dole,har antyn ta fita batace komai ba,saita koma saman kujera ta zauna,tana tuna zuwanshi na qarshe,inda yake ce mata kishinta xai iya halakashi,idan zata iya tunawa tun ranar baida lafiya.
Tana nan tana laqai laqai dinta amatu da abdul duka shigo da hargowarsu,sunyi kyau cikin wasu sabbin kaya da batasan dasu ba,kamar ka sace yaran ka gudu,ba qaramin kyau sukayi ba
“Mami….baki shirya ba?,anty fa harta shirya tace unguwa zamuje,wajen wannan daddyn namu daya daina zuwa tun rannan” jin abinda yaran suka fada ya sanya ta tashi ta soma shiryawa kada antyn taga kamar ta raina maganarsu.
Tana gama shirin kuwa sai gata ta shigo,wani kallo ta bita dashi daga sama har qasa,sannan cikin matse gira tace
“Meye hakan?” Tayi maganar tana nuna shigar jikinta,bin jikin nata itama tayi da kallo,kamar batasan me ta sanya ba,bata kuma ce mata komai ba ta isa gaban closet din bilkisu ta bude ta.
Sai data birkiceta tsaf sannan ta zabo mata wani sassalkan material me azabar kyau da tsada,tafita sanin kudinsa sarai tunda ita ta siyo musu shi ita da najwa da antyn kanta,mai sulbi da taushi ne, ta aje mata,dinkin riga da skert ne,tana son material din sosai saboda yadda yake mata kyau idan ta sakashi,dole ta ajeshi kwana biyu saboda yadda yake bayyana kyanta idan ta saka yake kuma jan hankalin mutane kanta.
Uffan bata ce mata ba taja hannunta kamar qaramar yarinya ta gyara mata fuska da sassauqan kwalliya ta gyara mata gashinta tsaf sannan ta miqa mata kayan taja hannun su amatu suka fice,bayan ta cikata da qamshin turaruka masu sanyin dadi.
Ita kanta data kalli kanta sai taji ta burge kanta,to amma saidai ta kasa gane wannan shirin na musamman kuma na alfarma don kawai zuwa dubiya.
Ko a mota ma tunanin data dinga yi kenan,suna tafe tana kallon yadda su amatu suketa zuba surutu da zumudin zuwa ganinshi,kamar wanda suka shekara da saninsa.
Tafiyar mintina kadan suka iso katafaren asibitin,driver yana gama fakawa suka hangi tahowar fulani,fuskarta a sake da wani irin murmushi da kuma fara’a har ta qaraso bakin mota,tasaka hannu da kanta ta budewa bilkisu bangaren da take zaune tana cewa
“Barka da xuwa diyata” mamaki ya cika bilkisun,ta sanyo qafafunta a hankali ta fito,sai kawai fulanin ta rungumeta cikin jikinta tana cewa
“Oyoyo ‘yata” a karon farko kunya da nauyi irin na surukuta ya kama bilkisu,sai ta dan sunne kanta,yayin da fulani ta waiwaya tana vaiwa su amatu hannu,saidai dukansu sun noqe jikin anty zuhriyya kaman basu keta surutu da zumudi tafiyar ba.
Murmushi anty xuhriyyan ta saki kamar yadda fulanin tayi
“Kuje ku gaisheta mana amatu,grand ma ce fa” abdul ne a gaba amatu biye dashi,cikin yanayin dake nuna sun samu zallar tarbiyya suka dan rusuna suka gaidata,ta dora hannunta saman kansu tana shafawa sannan ta amsa,can wani saqo na zuciyarta tana istigfari,tare da fargabar kada dai ace abinda ta aikata yayi affecting nata tun suna ciki,shi yasa suka gaza sakin jiki da ita a yanxun.
Tana riqe da hannun bilkisun har suka isa dakin tana mata magana qasa qasa,wanda hatta da anty xuhriyya dake bayansu bata jin me take gaya mata.
Kamar ko yaushe,dakin shuru yake kuma luf luf,babu kowa ciki sai afnan dake zaune kan daya daga kujerun dakin,hannunta riqe da wani littafi kasancewarta mayyar karance karance.
Zaro idanu tayi sosai fuskarta washe da wata iriyar fara’a,zataso tadan saki ihun murnan ganinta amma fulani ta hanata da hanyar yi mata ishara da kai,bakinta sai motsi yake,ta kasa tsaiwa saida ta iso kusa da ita sanda fulani ke kaita gaban gadon da azeez ke kwance
“Barka da zuwa matar babban yaya anty billynmu” caraf xancan a kunnen azeez dake kwance,tsabar rudani da jin zancan babu zato saura kadan ya bude idanunshi,amma daya tuna hakan zai iya tarwatsa tsarinsa saiya fasa ya kanne,amma yanajin kamar ya fasa ihune kozai samu sasaaucin farincikin daya cika masa zuciya.
Tsahon wasu mintuna anty zuhriyya ta masa addu’ar samun sauqi ta fice,sai fulani ta yiwa afnan inkiya da su fice,afnan din ta dauki amatu a kafadarta ta kuma riqe hannun abdul suka fice,yana jin yaran kamar ita ta haifesu,qaunarsu take ji sosai.
Shuru dakin ya dauka bayan fitarsu,yaji a jikinsa sun fice,saidai baison nuna mata idonshi biyu yana son yava reaction dinta da abinda zatayin.
A hankali ta sake matsowa gaban gadon idanunta a kanshi,karon farko ta soma qare masa kallo,tun daga kyan kyawawan dogayen yatsun qafarsa,wanda tun daga nan zaka fuskanci mai yawan gashin jikine,faffadan qirjinsa duk dacewa a cikin riga yake zuwa kyawawan labbansa kamsu kalar pink,wanda ke kewaye da saje daya hade da habarsa,duk da bisa alamu qasumba ce ta fara taruwar masa sanadiyyar zaman asibitin.
Dukkan wani rukunin kyau mai.jan hankali da burgewa fuskarshi ta hadashi,wani sassanyan kyau da ke nuna zallar mazantaka da kuma cikar ingarman namiji.
Qaramin tsaki taja tana tuhumar kanta kan tsaiwar da tayi tana qare mishi kallo,tayi taku daya da baya tana shirin yin na biyun taji an fizgota,gaba daya cikin sakan daya ta yiwa kanta kyakkyawan masauki saman faffadan qirjinsa,wanda dumi da qamshin mayen turarensa suka mamayeta lokaci guda.
“Barka da xuwa duniyata gimbiyata” ya fada cikin wata iriyar murya tsakiyar kunneta,wanda sautin ya hadu da dumin numfashinsa ya shiga jikinta.
Wani mugun bugu taji zuciyarta ta soma yi,saboda bata taba zato ko tsammanin cewa idanunsa biyu ba,hakanan bata taba kawo cewa zata tsinci kanta haka a jikinsa ba,kafin ta sake cewa komai tuni ya sake gyara mata mazauni a jikinsa,yana sheqar daddadan qamshinta daya tayar masa da tsohon shauqi da kuma tsuminsa……
Dukkansu tsaye suke a harabar asibitin ana gyara tsaiwar motocin da zasu wuce gida a cikinsu bayan likita ya rubuta musu sallama.
Gaba daya ya kafa ya tsare,hakanan yana gadin duk wani motsinta da idanuwansa cikin wani zazzafan kallo,saita basar taqi dubar sashen da yake,duk da tanajin tasirin kallon har cikin bargonta.
Sau tari takanyi mamakin kanta,takanji cikin jiki da ruhinta kamar ta jima da saninsa ko sabawa dashi,takanji komai nashi daban a zuciyarta,ta gaza cankar meye wannan din.
Dai dai lokacin da wasu barori suka qaraso inda suke,cikin girmamawa suka rusuna
“Ranki ya dade,fulani tace ki qarasa mota ki shiga ku tafi” azeez dake tsaye ada yayi gyaran murya,duk sai suka shiga nutsuwarsu,cikin wasu sakanni suka bar wajen.
A hankali yataka zuwa inda fulanin ke tsaye,yadan shafo sumar kanshi kadan sannan yace
“Da wai na dauka zamu wuce ne”
“Ina?” Ta fada tana balla mishi harara,saiya kasa amsa mata
“Ka turomin ita mu wuce,lokaci na qurewa” ta fada tana shigewa mota,kamar ya saki kuka haka ya dinga ji,amma babu yadda ya iya,haka ya juya murya a cushe yace mata
“Ki qarasa ammi na jiranki” batace komai ba ta soma takawa inda fulanin take,saidai tana ta qumshe dariyarta ne,sannan bugu da qari ita kanta hakan ya mata.
Shuru ne ya ratsa cikin motar sanda suke keta titin zuwa masarautar kaisa,wanda ta fuskanci ba xasu maidata gida ba kenan?,don ko anty zuhriyya da sukayi waya daxun a wayar fulani kamar abinda ta nuna mata kenan
“Abdul’azeez ya shaida miki yana da wata iyalin bayanke?” Muryar fulani ta katse mata tunaninta.
Kaman daga sama taji xancan,amma zuciyarta data gaya mata mutum kamar abdul’azeez din,matsayi daraja da daukaka irin tashi ace ace daman tsayin wadan nan shekarun bashi da iyali,don haka ta aro nutsuwa ta sanyawa kanta,sannan ta girgixa kai a nutse
“Bai gaya min ba” sai fulanin ta saki ajiyar zuciya,a hankali ta soma warware ma bilkisun irin yanayin da azeez din ya shiga bayan rabuwarsu,ciwon da yayi bayan ya amince zai rabun da ita kamar bazaiyi rai ba,da kuma aurensa da safwa.
Can qasan zuciyarta ta saki wata sassanyar ajiyar zuciya,tana jin yadda zuciyarta ke sake nutsuwa dashi,amannar data gaza bashi sai taji a yanzun ta bashi,wani girma qima da darajarsa ta dagu cikin idanunta.
Laifinsa dan kadanne,amma saboda girma da qimar mahaifiyarsa ya gaza gaya mata ainihin waye me laifin har kawo yanxu,sai data ji daga bakinta tukunna,lallai ya cika da na halas,domin kuwa kowanne mutum yunquri yake ya kare martabar mahaifansa a idanin duniya,komai tarin zunubi laifi ko lalacewarsu
“Ina fatan wannan ya wanke dan abinda yayi saura a zuciyarki,naga har yanzu jama yaron nawa rai da aji akeyi” ta fada cikin tsokana da barkwanci,duka sai taji kunya ta kamata,ta sunne kai kawai tana murmushi.
¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶
Cikin hikimar nan tata ta gama tsara yadda zata bayyanawa duniya yarima azeez da iyalinsa boyayyu wadanda ba’a sansu ba.
Tunda ta tafi da bilkisun ta hana kowa ganinta,daga ita sai afnan sai mutum biyu na musamman data dauko masu gyara bilkisun suke ganinta,sai kuma amintattaun hadimanta dakewa bilkisun karatu kan yadda gidan sarauta yake,yayin da ita kuma a gefe daya da kanta take xama ta koyama bilkisun hanyoyin kama zuciyar miji da kuma mallakeshi babu boka ba malam.
Abun na saka bilkisu cikin kunya mai yawa,tun tana kunya harta sake saboda ta soma sabawa da jin kalaman bakin fulanin,a hankali saita fahimci ita din macace me hikima da fasaha,Allah ya hore mafa dabaran zaman duniya,wanda lallai dole tayi xarra tsakanin abokan zamanta.
Ita kanta a jikinta tasan cewa akwai sauyi mai yawa,gyara ne data sameshi ciki da waje wanda ya sake bayyana zallar baiwar kyau da Allah yayi mata,ya kuma maisheta wata jinsi daban.
¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶
Zazzafar iska ya fitar daga bakinsa yana sauke wayar daga kunnensa bayan ya gama sauraren kalaman safwa,kai yake gyadawa kawai,kana daga bisani ya nitsa yatsun hannunshi cikin sumarshi.
Wai me yasa mata aduk sanda suka sanyaka a tarakunansu idan bakayi wasa ba dukka lissafinka saiya tarwatse,ba dauki matsalar safwa wani abu ba,amma ayau tabbas banda tana cin albarkacin ammi ne da bata isa ta gaya mishi wadan nan kalaman data gaya masa a yanzun ba.
Gefe daya ga bilkisu,yarinyar da yakejin ta jima da zams mahadi na numfashinsa bama rayuwarsa ba,wadda yakeji a yanxun itace duniyarsa,idan babu ita tabbas duniyarsa zata tarwatse ne gaba daya,saidai itama a yanxun ta masa tsada,ko sau daya ammi taqi bari ya ganta tun randa ta daukota daga asibiti,ta kaita wani waje daban ga boyeta,duk wayo da dabararsa amma ya gaza ganinta,da qyar yake samun barci sau tari,ga uban ayyuka da suka shafi kasuwancinsa,wadanda a yanzun suna tafiya ne slow sabida rashinsa a gurare da dama,yaci burin ya ragesu gami da gyara wasu abubuwan ko daga gidane kafin komai ya daidaita ya koma kan harkokinsa amma hakan ya gagara,bilkisu ta hana ruwa gudu gaba daya.
A wajen twince dinshi kawai yake rage zafi,wadanda ammin taja mishi kunne kan ko sau daya kada ya shigo dasu masarautar,tana jiran lokacin shigo dasu yayine,sanda ta shaidawa maimartaba ta kuma yi shawara dashi kan abinda ta shirya murmushi kawai yayi
“Aisha….aisha sarkin dabara,Allah ya bamu aron rai da lafiya” ya fada kawai yana dubanta.
Sosai yaran ke debe masa kewa,yakan kwashesu ya kaisu gidansa na musamman wato village,su kwana biyu tare,shike musu wanka ya hada musu abinci,idan kuma suna da abinda sukeson ci xaisa a musu order a kawo masa har gidan.
Wannan ya haifar da shaquwa da kuma sabo mai yawa tsakaninsu,jini ya soma aikinsa,soyayyar uba da ‘ya’yansa ta soma zagayawa tsakaninsu,har wani lokacin sukan kwana su wuni basu tambayi mamarsu ba,sosai yake basu kulawa da dukka qarfinsa.
Miqewa yayi yana sanya hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sauke ajiyar zuciya,yanajin ayauma zai gwada sa’arsa ko xai samu damar ganinta,ya zura wasu lausasan rufaffun takalma na sarauta a kyakkyawar qafarsa,sannan ya isa gaban madubi yana sake kallon kyakkyawar fuskarshi,wadda kwanakin baya ba haka take ba,a yanxun ta sake kyau saboda aski da gyara data samu,gami da nutsuwar samun abinda ruhinsa keso kusa dashi,fuskar tashi ya shafa yana sakin murmushi shi kadai,duk sanda yako tunata takan sanya murmushi saman fuskarsa,shi kansa yana jinjinawa irin son da yake mata,duk wani bacin ran safwa sai yaji cikin kaso dari babu kaso tamanin,juyawa yayi ya taka a hankali ya fice daga katafaren dakin gadon nashi.
Duk wanda yayi yunqurin masa rakiya dakatar dashi yakeyi,shi sam baison irin wannan bibiyar ta gidan sarauta,shi yasa yake tsara yadda zai kwashe iyalinsa gaba daya suyi gaba,suje su bude rayuwarsu iyasu isu,babu takurawa bare sanya idanu ko matsi.
Tunda ya shiha sashen fulanin suke zubewa suna miqo gaisuwa har ya dangana da falonta na qarshe.
Babu kowa cikin falon sai afnan dake zaune tana kallo,ta daga kai a hankali tana amsa sallamar da yayi wadda take ciki ciki kamar wanda aka yiwa dole,dama tasan idan bashi ba babu me aikata hakan,yana daga tsayen ya tambayeta
“Ammi fa?”
“Bata nan,tadan fita”
“Ina princess?” Ya sake tambayarta yana kallonta kanshi tsaye,sarai tasan da wadda yake,amma saita dake ta kuma gimtse kamar bata gane ba,bayaga haka ammi ta ja mata kunne karta bar kowa ya ganta ma,yanzun nan ta shiga ciki daura alwala da wala’alla yadda basusan da shigowar nan tashi ba ya cimmasu tare
“Wa….?”
“Keep quit,ni abokin wasanki ne?” Ya fada a hankali yana fidda mata idanun nasa masu tsananin kwarjini,take ta shiga taitayinta,ya kuma tuna mata yariman na asali,qasa qasa cikin qunquni take fadi bayan ta nuna masa dakin da yatsanta
“Ni ina ruwana,ni nakar zomon?,ko ratayar ma ni ba’a bani ba” baijita ba,don tuni yasa kansa cikin dakin cikin sauri kamar wanda za’a kama.
Tana tsaye baki mirrow tana goge ruwan alwalar dake fuskarta,wanda saboda tsabar kyau da gyara da fatarta ta samu ruwanma bai zama sosai saman fatar tata,ta gama ta dauki comb ta gyara gashinta daya wargaje wajen shafar kai,tana qoqarin maidashi ta hadeshi waje guda ta hangeshi dab da bayanta ta cikin mudubin,saita zaro idanu tana niyyar juyowa,saidai tuni yayi caraf ya kama qugunta ya kuma mannata da jikinsa,cikin taushi da sanyi ya dora kanshi saman kafadarta,bakinsa da hancinsa duka suna sansanar wuyanta,wanda hakan ya sanya tsigar jikinta tashi lokaci daya,hakanan ya kashe dukka wata laka ta jikinta,saitayi collapes cikin jikinsa,tana tsintar kanta itama da kallonshi ta cikin mudubi kamar yadda yake duban qwayar idanunta shima.
Kamar masu kallon quda haka suka dinga kallon juna ta cikin madubi tsahon lokaci,kowannesu saida jikinsa ya gaya masa sannan ya juyo da ita suna fuskantar juna,still idanunsa cikin nata,ya sanya hannu ya gyara mata gashinta daya sauko gefan fuskarta,cikin sanyi ya sunkuya ya sumbaci tausasan labbanta kana yace
“Ko kadan baki kewata madam?,dake za’a hada kai a sake bani wahala ko?,kina so ne na sake komawa gadon asibiti karo na biyu?” Maganar tasa sai taso bata dariya,ta saki murmushi
“Gadon asibiti kuma?” Gira ya dage mata
“Eh yes,gadon asibiti” dan qwace jikinta tayi tana murmushi gami da bashi baya
“Nifa gaskiya ban shirya zama da ragon namiji ba” sake kamota yayi,don tsaiwarsu ta mishi dadi,baison ta raba jikinta da nashi,cikin zuciyarsa yasaki murmushi yana taune lips dinsa kadan na qasa,shi kadai yasan meya tuna sai yace
“Aiko ki shirya zama da raggo,don a kanki kam bani da wata juriya ko kadan….but saidai kinsan a inda ragwantaka take aiko….i mean ba ainihin ragon da kike magana bane,tunda kin dan shaida idan xaki iya tunawa….” Saiya duqa saitin kunnenta ya gaya mata wani abu daya sanyata qwace jikinta da sauri bayan ta saka hannuwanta ta rufe fuskarta,ta yaya zata manta wannan lokacin,lokacin da asannan takejin tafi kowacce halitta baqinciki a duniya,tafi kowacce halitta rashin sa’ar rayuwa,ta kuma fi kowacce halitta asara,saidai a yanzun tunaninta nata sauya mata dararen guda biyu zuwa darare masu tarihi arayuwarta,daren farkon daya bambanta da kowanne daren farko.na kowanne ma’aurata,tana danne kunyarta da boye dariyarta tace
“Lalala nifa ba haka nace ba,kuma ni ba haka nake nufi ba” wani murmushi yake jifanta dashi hade da wani kallo da zai gaya ma mutum cewa ya dade da narkewa cikin duniyar qaunarta
“Zoki gayamin to yaya ne?” Ya fada yana qoqarin kai mata cafka,saidai knocking din da akayi a bakin qofar ya tsaidashi,ya kalli qofar saiya basar kamar baiji ba,ya sake maida hankalinsa a kanta yana sake takawa zuwa inda da durqushe,bai qarasa ba aka sake qwanqwasawa,tsaiwa yayi cak,kana cikin qasaitacciyar muryar shin nan yace
“Afnan!….zaki bar wajen ko sai nazo na bata miki?”
“Ba afnan bace,uwar afnan dince” ya tsinkayi muryar fulani,saiya dafe goshinsa da tafin hannunsa,ya salam,asirinsa ya tonu?,bilkisu kuwa tuni ta miqe ta bude bandaki ta shige ta maida qofar ta rufe,da wanne ido zata iys kallon ammin idan fa shigo ta gansu tare.
Qofar ya nuna ya bude,tana tsaye tana kallonshi,ta tsareshi da ido.sosai,kunya ta kamashi amma saiya maze ya rabeta zai wuce
“Ina bilkisun?”
“Tana toilet” ya amsa mata yana wucewa
“Ka jirani anan” ta amsashi tana shiga ciki.
Dakin tadanbi da kallo har saman gadon,a gyare yake ba alamun wani ya hau,saita saki ajiyar zuciya,batason yakai ga tabata yazun,harsai ta gama shiryata tsaf ta yadda zai sake raina kanshi
“Idan kin gama.boyon ki sameni falo” ta fada tana dake dariyarta,don taga alamun jinta ne ya sanyata kulle kanta a bandakin,ta juya ta fice tana jin sanyi cikin ranta da Allah ya azurtata da suruka irin bilkisun,tana tuna abinda ya faru awa daya data shude tsakaninta da safwa da iyayenta.
Ta shirya ne da kanta zataje ta zayyane musu komai ta kuma kawo gyara kamar yadda tayi na bilkisu,tunda ita ta shirya komai,lokacin data iske mahaifiyar safwa suna tare da safwan,kanta na saman cinyarta uwar na shafa kan nata kamar wata jinjirar goye,da alamu ma kuka ta gama yi,shigowar fulanin ya sanyata yin zumbur ta miqe,bata ko tsaya gaidata ba ko mata magana ta haye sama abinta,inda katafaren sashinta yake kamar dama can a gidan take zaune,bawai aure take a wani waje ba.
Sama sama suka gaisa da mommyn safwan,itama tana ta wani cin magani,bata boye mata komai.ba ta fayyace mata tare da neman suyi haquri safwan ta koma dakinta ta zauna kamar kowacce mace,cikin daure fuska take amsa mata
“Amma dai wannan abun hajiya aisha ke kanki kinsan zallar cin amana ce da rashin gaskiya,ya za’ayi yana tare da yarinyarmu amma har a zagaye a aura masa wata?,kuma harda yara tsakaninsu,ace kuma waike bakisanma suna tare ba,hakanan bakisan da yara tsakani ba sai bayan wasu shekaru,ai hankali ma bazai kama ba,gaskiya bazan boye miki ba,naji zafin wannan abun sosai,kuma bawai ni kadai ba,hatta da daddynta yaji ciwo sosai,kuma ni bani data cewa sai abinda yarinya tace,saboda haka zan turota kuyi magana tsakaninku” daga haka ta miqe ta haura dakin safwa,wanda sai data kusa minti arba’in zaune tana jiransu,da alama bayan ta gama bata labarin komai sai data sha kanta da qyar kafin ta yarda ta fito,sai gata ta sauko tana wani kumbure kumbure.
Da harshe irin na uwa fulani aisha tayi magana da ita cikin lallashi da fahimtarwa,saidai tana bude bakinta cikin tsanar sakalci da sangarta tace
“Nifa yanzu na tsaneshi ma,saboda maci amana ne mayaudari,na bashi amana dari bisa dari amma yamin wannan yaudarar tsayin shekarun da muke tare dashi?,ni bazan koma gidansa ba saidai.idan har zai saketa ya rabu da ita,ni kadai na rayu a gidanmu kamar yadda momy na take ita kadai wajen daddy,so ni banga wani dalili da zai sani in zauna da wata ba” tadan murguda bakinta ta miqe ta koma inda ta fito,yayin da fulani ta bita da kallo cikin mamaki da takaici,saidai batason bacin rai ya kaita ga yanke hukunci da sauri,ko meye itace sila dole ta daure koma me zata gani ta kawo gyara iya iyawarta,haka ta miqe ta iske barorinta suka bar gidan.
Sai data iske mai martaba ta sanar mishi da komai,yayi shuru yana mamakin irin nasu dattakon su kuma a matsayinsu na iyaye,sai yayi ajiyar zuciya kana yace
“Zan samu lokaci nida kaina na iske ibrahim din,komai zai daidaita in sha Allah” da wannan ta baro wajensa,saidai ranta cike fal yake da mamakin abinda sukayi matan.
A falon ta iske azeez tsaye hannayensa zube a aljihu,idanunsa saman tv,saidai ba ita yake kallo ba,duka tunaninsa na ga bilkisu ne,zama tayi sannsn tace dashi
“Xauna” hannayen nasa ya cire kana ya zauna saman kujerar datafi kusa dashi,a nutse ta soma masa magana
“Inason kome safwa zata ce da kai,kayi haquri har sai al’amura sun daidaita” shuru yayi yana juya maganar aransa,hakanan jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa,amma dai saiya amsa mata dato,kana ya miqe ya nufi fita daga sassan.
Baiyi wani nisa ba yaji kamar muryar afnan na kiranshi,ya dakata ya waiwayo yana dubanta harta iso,sai data qaraso kuma sai tayi laushi kanta a qasa tace
“Yaa azeez….ammi ta boye maka ne,bata gaya maka komai ba” nan ta gaya masa dukkan abinda ya faru kamar yadda fulanin ta bata labari bayan ta dawo.
Wani irin bacin rai yaji yana hudashi,har wani tururi yakeji saman fuskarshi,idanunsa kafe jikin wata bishiya daura dasu,saidai a badini ba ita yake kallo ba.
Bazai taba lamunta wata halitta ta wulaqanta masa mahaifiya ba,bare mace macen ma matarsa,wadda a musulunce take a qarqashinsa,bayan ita din harda mahaifiyarta itama?,uban me suka musu?,duk iskanci da sakalcin da yarinyar takeyi bai taba daga kai ya duba koya dauki mataki mai tsauri ba duk sabida darajar ammin da takeci su basu gani ba?,bazai taba lamunta ba,koda da ruwan gold daka qerata kuwa bata isa ta taba mishi.mahaifiya ba,inda yasan ma inda ammin ta tafi da bai barta ba,don ko sabon aurene ya qara baida laifi a irin rayuwar d sukeyi da safwa din,wadda sam batasan muhimmancinsa ba bare auren dake kanta,tsabae sakacinta ya bada gudunmawa wajen mutuwar gudan jininsa suhaima,ko sun dauka ya manta ne?,ko zuba musu idanun da yayi suna zaton shi sauna ne ko baison ciwon kanshi ba?,kai kawai ya jinjina bai iya cewa afnan komai ba ya soma takawa yana barin wajen.
“Gwara a gaya masa gaskiya,kada ta dawo tazo taci gaba da wannan iskancin banzan kamar wadda aka yaye daga nono” afnan ta fada tana juyawa tana barin wajen.
Kiran da taji ana mata ya tsaidata,daya daga cikin barorin gidanne,ta qaraso da hanzari hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando da aka saqa da hannu da wata iriyar ciyawa
“Ranki ya dade,mangwaro na tsinko a lambun gidan nan,irin wanda kikeso,naga yafi dacewa dake” murmushi ta saki,ta saka hannu tana yaye dan qyallen da aka rufe kwandon dashi,ta dauki daya tana cewa
“Amma kuwa kin kyauta asiya,a wanke yake?” Tayi tambayar tana kaiwa bakinta
“Fes ma uwar dakina” ta bata amsa tana murmushi itama.
Kai ta jinjina bayan ta gutsira
“Yayi,irin nawa ne kuwa har dandanon,muje ki ajemin,kin cancanci a baki tukuici” cikin farincikin yadda ta amshi kyautar tata tadan rusuna kanta
“Kinfi gaban haka mai hannun alkhairi irin na uwarta,godiya nake” daga haka suka rankaya tare suna taba hira abinsu,kai bakace asiyan qasa da ita take ba.
¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶
Cikin satin kyakkawan saqon katin da aka qawata adonshi da ruwan gold ya zagaya lungu da saqo na masarauta kaisa dama qasar kaisa gaba dayanta,tare da wasu qasashe maqwabta dana nesa da suke wannan duniya dama garuruwa baki daya,katin daya daga hankalin maqiya da abokan adawa da yawa,katin daya faranta ran wasu,katin daya sanya ayoyin tambaya cikin ruhi da zukatan wasu,ya sanya wasu rayukan kuma cikun zumudi da son ganin zuwan wannan rana.
Katine dake dauke da gayyata ta musamman zuwa babban bikin taya yarima Abdul’azeez abdallah mu’az kaisa da mai dakinsa Bilkisu bilyamin murnar cika shekara takwas cif da auren wedding anniversary,sunan dake manne saman katin shi ya sanya al’umma da dama tambayar wacece?,tunda da yawansu sunsan safwa ne,babu wanda yasan da wanzuwar bilkisun.
Duk da cewa fulanin da fari ta dauka komai zai daidaita tsakaninsa da safwa ta hadasu dukka ta musu,rashin samuwar hakan da gudun bata lokaci yasata kawai aiwatarwa.
Sanda kyayykyawan katin daketa sheqi ya isa hannun safwan kamar tayi qaramin hauka haka taji,ta dinga koke koke kaman qaramar yarinya tana sake tabbatar da cewa azeez yaci amanarta,kuma babu ta yadda zata koma masa,babu bata lokaci ta dauki waya ta tura masa tex,ya gani ya karanta,ya kuma yi murmushi kawai sabida ya riga ya wuce wannan babin,yaci kuma da irgen kwanakin daya bata kawai,duk da bai fahimci wasu daga cikin kalamanta ba,don baisan me fulani ke shiryawa ba a lokacin.
Cak ta tashi fulani adama hajja fauxiyya da shalelenta kamal a tsaye,hankalinsu a matuqar tashe suka hadu domin tattaunawa kan lamarin,kowa ya kawo tashi shawarar,wanda suke hasashen cikin biyu abu daya ne zai faru,imma dai taron ya zamewa aishar abun kunya da tonuwar asiri gareta da iyalanta,ko kuma ya zama wankuwar laifi da fidda kai daga zargi a idanun al’umma,wanda daga qarshe sukaga babu wata mafita,illa dai kawai su zuba idanu suga yadda taron xai kaya,daba bisani sai susan matakin dauka na qarshe,don na zasu bata zuba idanu ko lamuntar wahalar da suke da fadi tashi na shekara da shekaru ya tashi a banza ba.
Ta fannin fulani saratu itadinma cikin dimuwa da tashin hankalin take,ya tabbata dai yana da wata matar kenan bayan safwa?,duk kudin data zuba kan amata aiki akansu ya tashi abanza kenan?,hakan bai sanya ta saduda ba,kudi ta sake zubawa masu ciwo duka akan azeez din,saidai kowa ya amshe kudinsa ya kuma kalmashe,sannan ya bita da qaryar ta zuba idanu daga nan zuwa bayan taron,zataga abinda zai faru,bayan kowa ya bincika yaga aikin yafi qarfinsa,amma babu wanda ya gaya mata,saboda yana tsoron rasa kwasar ganimar kudaden data je musu dashi.
Tayi imani dasu,ta kumayi imanin duk abinda suka fada haka yake,don haka tadan samu ‘yar nutsuwa kadan ta sama ranta zata jira din daganan zuwa ranar taron taga me zaya farun kamar yadda suka alqawarta mata,harta samu damar qarfafawa su walida gwiwar su halacci taron da suka shaida mata gayyatar da fulanin tayi musu,don tana ji a jikinta suke da nasara a ranar.
Abinda bata sani ba,tun farkon lamarin fulani aishan ta bada kudin sadaka masu tarin yawa kan ayi mata sauka babu adadi kamar yadda ta saba,wannan karon kan Allah ya daidaita komai cikin hikimarsa da ikonsa,ya kuma karesu ita da dukka ahalinta daga sharrin mai sharri mutum ko aljan.
Yadda al’amura ke gudana da shirye haiqan,kai kace auren afnan zatayi shi yake sake daga musu hankali,shiri take na qasaita isa ixxa da nuna zallar mulki da sarauta daga inda aka gajeta ba taka haye ba,hatta wasu sassan na gidan ta saka an sake gyaresu domin saukar baqi.
Duk abin nan azeez bai sani ba sai daga baya,shi daya ya dinga murmushi yana shafa kanshi,qaunar mahaifiyar tasa da tausayinta na sake ratsashi,farincikin da yaji a lokacin ba dan kadan bane,don haka shima saiya soma shirya nashi gagarumin walimar sanyawa auren albarka,ya kuma soma tura katin gayyata ga dukka wani abokin arziqi ko na huldar kasuwanci nashi dake fadin duniya,tare da shirya musu tafiya umara suyi azumin ramadan acan shi da ita dasu amatu,ba tare da sanin kowa ba banda anty zuhriyya.
Duk wani jini ko ahalin me martaba sai data tabbatar da goron gayyata ya isa gareshi,ciki harda yaran su fulani adaman da kanta ta aika musu ba tare data bi takan iyayen ba,hakanan nata yaran sumaira uswa da aafiya dukkansu kowacce ta dokantu tazo gidan,don basu taba haduwa da bilkisun ba.
Ga me martaba kuwa sanda ta miqa mishi katin ya gama karantawa saiya saki murmushi,yasani cewa tayine domin ta sake wanke kanta a idanunsa,tayi ne donta wanke yaronta daga zargin masu zargi,sannan tayine donta daga hankali ta dugunxuma hankalin abokan adawa yadda ta saba,hakanan tayine donta wanke kanta ta kuma bayyanawa duniya abinda ada ta boyeshi da hannunta,ta kuma qarasa aikinta,wanda takeji har jiki da zuciyarta shine abunda yayi saura da zatayi ta qarasa gyara dukkan alaqar data bata a baya,bawai kawai zallar manufar WEDDING ANNIVERSARY bace kawai,kamar zata jefi tsuntsaye da yawa ne da dutse daya
“Aishatunnabiyyi…..Allah ya nuna mana,ya bamu aron rai da lafiya” murmushi tayi tana amsa mishi.
Shi a karan kansa yakejin abun yayi dai dai,ya kuma burgeshi,shima saiya samu kansa da dokin zuwan wannan rana.
Bilkisun batasan dukan yadda aka shirya abun ba,duk da tasan da taron,harma ta gayyaci farida ita kadai,saidai yadda afnan ta kasa zaune ta kasa tsaye abun ke bata mamaki,a hankali kuma ta gano ba qaramin shiri sukema abun ba,ita abunma daure mata kai yake,yadda fulanin ke nuna mata qauna tare da qoqarin karbe fadar anty zuhriyya qarfi da yaji
“Alhamdulillahil lazi bi ni’imatihi tatimmussalihat” takan furta lokaci lokaci kawai,saboda tasan banda Allah babu wanda ya isa ya mata hakan.
Cikin dimuwa sukayi gware da juna lokacin da hajja fauxiyya ke kai kawo tana jiran shigowar fulani adama,dukkansu goshinsu ya bugu sosai,kowanne ya hau sosawa amma sam ba wannan bane damuwarsu ba,tsantsar tashin hankalin da suka gani yanzu a wajen gudanar da taron weddinga anniversary din ya shafe komai,ya shafe duk wani zafi da radadi da zasuji.
Cikin zallar tashin hankali adama ta kama hannun fauziyya
“Da gaskene wai fauxiyya abinda idanuna suka ganemin kuma naji ana fada?,abdulazeez keda wadan nan ‘yan biyun masu kama da juna?,don Allah kicemin mafarki nake” ta fada tana jijjiga hannun fauxiyya wadda itama gaba daya tashin hankalin da take ciki take jinta kamar ba cikin duniya ba
“Adama….adama na fiki shiga tashin hankali” ta fada tana buga cinyoyinta da hannu,duk yadda fulani adama taso daure kukanta wannan karon ta kasa,sai kawai ta dafe kanta da hannu biyu ta saki kuka tana fadin
“Wallahi aisha ta cucemu,ta shammacemu,tako ina tasha damu,ta zarcewa tunaninmu,aure tayi masa a boye da hadin bakin maimartaba,ta yadda ba zamu iya cutar dashi ko abinda suka samu ba,tanuna mana wannan kodaddiyar yarinyar a zuwan ita kadaice matarsa,Allah ya isa aisha,kin kadar da tunaninmu na tsahon shekaru,inda muka nufa daban kema inda kika nufa daban” saita sake kukanta sosai,saboda yadda abun yake mata ciwo a zuciya,duk wata hanya da take ganin ta dace tabi don tarwatsa matar da ahalinta amma ya gagara,tsayin shekaru aishan bata taba barin tunaninta ya huta ba da laluben hanyar daukar fansa mafi ciwo ba,sai gashi yanzu dukka dararen data bata a rayuwarta sun tashi a banza,hannun agogo ya sake komawa baya fiye da yadda yake ma a da.
Hajja fauxiyya sam ta kasa zama,sai kaiwa da kawowa takeyi kamar wanda ta hadiyi tabarya,gumi kawai ke yanko mata,tana jin abun kamar mafarki take wanda za’a iya tashinta kowanne lokaci.
Daga can dakin taron kuwa ‘yan qananun gulmarmaki ke tashi,mafi yawa daga bakin munafukai ne,kowa yana tattaunawa da abokin zamansa,yayin da mafi yawa mamaki yafi cika zukatansu,musamman wadan da zukatansu ke cike da alkhairi da kuma qaunar fulani aisha na yadda ta fita zakka cikin dukka matan me martaba wajen tausayawa da sauraren matsalolinsu,tunaninsu yafi karkata kan akwai babban dalili da yasa auren ya zama a rufe har zuwa yaran da suka samu,sun ta’allaqa hakanne saboda samun tsaro a rayuwarsa data yaran daya samun,wanda qilan sai yanzun ne suke ganin lokaci yayi da ya kamata a bayyanawa duniya su.
Tun tana zaune tana ganin zata jura,tana danne gudun da zuciyarta ke qarawa tare da ganin al’amarin kamar almara ce har juriyarta ta gaza,a hankali fulani saratun ta sulale daga inda take zaune ta zube a qas ba tare data shiryawa hakan ba,tsabar razana da ganin yaran da tayi baya ga matarshi bilkisu,hankalin yaranta yakai gareta,suka isa wajen da gaggawa suna girgizata,idanunta na kansu saidai babu baki ko damar motsa hannu,haka aka dauketa zuwa cikin gida cikin tashin hankali,yayin da yarima azeez da bilkisu harma da fulani aisha ke can suna gaisawa da jama’a cike da zallar farinciki,wanda hatta da bikisun a yau tana jin kanta ya daban kuma ta musamman.
Duk inda suka gitta sai idanun kamal ya musu rakiya,yana daga zaune a inda yake tunda yazo,zallar kishi wanda hassada tafi yawa a ciki ke cinsa,kanshi yakewa tambaya,waishin me yasa duk abinda ya burat a rayuwarsa saiya zama mallakin azeez dinne,yaso suna daukaka dukiya da uwa uba kudi,dukka ciki babu wanda ya samu,amma sai gashi azeez din ya mallaka,yaso bilkisu tun ranar daya soma ganinta,sai gashi ta zama matarsa harda kyawawan yara biyu.
Idanu ya lumshe yana gayawa kansa tabbas wannan karon bazaiyi faduwar baqar tasa ba,sai ya dasa baqinciki a rayuwarsu,wannan murmushin saiya juyashi ya koma kuka da alhini,saiya miqe da hanzari,cikin qarfi da zallar bacin rai yake takawa yana barin gurin,tare da ayyana da kuma tsara yadda zai gudanar da komai a daren yau basai gobe ba.
Sosai taro ya bada ma’ana,hakanan ya qawatar,ya kuma faranta ran zuciyar masoya masu qaunar fulani da ahalinta.
Gagarumin zaman cin abinci ta sake shiryawa tsakaninta da memartaba da duka iyalin nata a wani waje na musamman cikin gidan,saidai lalurar data samu fulani saratu bagatatan wadda ba’asan dalilin samuwarta ba ya sanya zaman ya kasance daga ita sai ‘ya’ya da jikokinta.
Karfe bakwai na dare aka sanya zaman zai kasance,kusan tunda aka tashi daga wajen taron tana tare da fulani,anty sumaira uswa da aafiya,wadanda sukejin kamar su hadiyeta ita da twince,abun mamaki yadda bata zata ba yaran sun sake sosai cikin gidan,kamar dama can sun saba dasu,sai wajen bayan la’asar sannan fulani ta hadata da zababbun barori masu mata hidima zuwa qawataccen sassan yarima azeez dake gidan bisa rakiyar afnan.
Tunda aka tashi shima bai samu zama ba,hakan ya sanya basu kuma haduwa da ita ba,yana can wajen baqinsa,wadanda wasunsu ke masa sallama suna komawa inda suka fito,tunda tafiya ce ta jirgi,wasunsu kuma zasu kwana ne a qasar kaisan,su jira walimar daya shiryawa a washegari.
Tamkar baquwa haka ta zauna a sassan,gashi afnan ta koma ta barta,daga ita sai yaran,wadanda suma baqunta bata gama sakinsu ba.
Ana magariba afnan da kanta tazo daukan amatu da abdul,tare da kayan da za’a sanya musu,iri dayane sak kayan,sai bambancin danki na mata dana maza,kaya ne dake nuna zallar sarauta da kuma tsadar da suke dashi,ita kanta da aka gama shiryasu kallonsu kawai take,saita lumshe idanu,ta tsinci kanta da godiyawa Allah daya bata su a matsayin yaranta na cikinta,wani lokaci sai taga kamar ba ita ta haifesu ba,kamar ba daga jikinta suka fita ba,ana gama shiryasun afnan ta kalleta
“Anty saidai fa ki taho donmu munyi gaba,kowa twince yake jira” murmushi tayi
“Wariyar launin fata zakimun?,kafin ki sansu wa kika fara sani?” Dariya ta saki
“Ke,amma yanzun gsky sun qwace fadar,saidai kiyi haquri daga ke har ya azeez din” dariya ma ta bata,saita tura qofar toilet kawai ta shiga don tara ruwan zafi su kuma suka fice.
Tana tsaka da shiryawa ya turo qofar,a raxane ta juya,don bata taba tunanin shigowarsa dakin ba a lokacin,saboda taga dakuna da yawa,bata kawo zai shigo nan din ba.
Idanunshi a kanta yake takowa inda take,yayin da ita kuma zuciyarta ke bugawa da sauri,tama rasa inda zata nufa don ta boye har ya cimmata,a bayanta ya tsaya a hankali ya kuma jawota jikinsa ya rumgumeta tsam yana sakin ajiyar zuciya
“Barka da warhaka gimbiya” ya fada a hankali kamar meyin rada,idanunta ta lumshe,tsigar jikinta na tashi,ta kasa amsa mishi harya sake cewa
“Maimakon ki jirani inxo muyi wankan tare?,tunda baki jirani ba dole ki sake wani kam” kafin ta ankara ya sunkuceta yayi bandakin da ita,saita kasa musa masa ko qwatar kanta.
Cikin bathtube din cike yake da ruwan data tara,don haka zare dan towel din jikinta kawai yayi ya tsullumata a ciki shima yabi bayanta,kamar xata narke saboda kunya haka taji,ta dinga qoqarin ya fita ya bata koda towel dinne ta daura amma sam yaqi,yayi mursisi abinsa,kamar ma baisan tana yi ba,daga qarshe ma saiya sanyata a jikinta ya soma aika mata saqonnin da suka mantar da ita akan me take magana.
Sai daya gama aika mata da saqonni son ranshi sannan ya barta ya soma wanke jikinsa,ta runtse idanunta don bata son ganinsa a haka,yana ganinta saiya tari ruwa mai sanyi ya watsawa fuskarta data yi wani kyau da haske saboda gyaran data sha
“Zakima sabane,sannu sannu wataran ma ke zaki min wanka,gwara ma ki shirya” tana jinsa harya gama bata bude idanunta ba,sai daya daura nashi towel din sannan ya miqa mata hannu
“Taso na sa miki muje mu shirya,mun wuce lokaci,nasan mu suke jira” kafada ta maqale,don ba zata iya tasowar yadda yakeso ba,murmushi kawai ya sakeyi saiya ciro towel din ya aje mata gefan bathtube din ya juya baya,da sauri ta dauka ta miqe ta daura,tazo ta rabeshi zata wuce,saiya kamo.hannunta yasake janta zuwa jikinsa,daurewa kawai yakeyi,yanaso ne ya nuna mata ainihin qauna da soyayya wadda yake ganin kamar tana doubting samunta ko tabbatuwarta daga wajenshi,hakan yasa ya yima ranshi alqawarin sai ya gamsar da ita cewa yana mata so guda daya tak ne.
Duk yadda take dojewa bai barta ba,don kusan tare suka shirya,cikin kayan da itama batasan da zamansu ba sai daya bata,wohoho,zo kaga zallar kyau iya kyau,kamar kwatankwacin wanda sukayi a taron daxun,wanda ita da kanta sai data tofa addu’a ta shafa a daxun saboda maganin baki,yana riqe da hannunta suka baro sashen zuwa sassan fulanin.
Yana labe a inda ya tanada sukazo suka giftashi,ya bisu da kallo ranshi na sake quntata,zuciyarsa da shaidan na sake ingizashi tare da bashin qwarin gwiwa na aikata abinda ya qudirta,saiya ciro wayarsa ya turawa fulani adama dan gajeran tex
_sun fita zuwa wajen,ina da tabbacin ba zasu wuce awa guda ba,dasun dawo zan shaida miki,kiyi qoqarin kiranshi zuwa sassanki_
Daga haka ya maida wayar aljihunsa yana jan qwafa qasa qasa,gamida sake cin buri kan abinda zai aikata din.
Lokacin da suka isa tuni suka samu kowa ya hallara su kadai ake jira,cikin qauna da kulawa kowa ya taresu,sannan suka fara gabatar da abinda ya tarasu a wajen.
Kallo daya zaka musu kasan cewa ahalin na cikin zallar farinciki qauna da kuma fahimtar juna,zuciyar fulani aisha a wanke fes haka yau takejin kanta,idan ta dubi iyalin nata sai taga kaman tafi kowa sa’ar rayuwa,hakanan qima da qaunar bilkisu kowanne lokaci sake yawa take a ranta,kunyarta kawaici da girmama na gaba da ita,bambanci take gani muraran tsakaninta da safwa,wanda ada bata bambance ba sai a yanxu.
Yadda suke ta janta a jiki da nuna mata kulawa yasanya dole tadan sake a cikinsu,don ma yarima ya hanata sakat da mayun idanuwan shin nan,duk.inda ta motsa yana biye da ita,batasan me yakeso ba hakanan,amma ita kanta zuwa yanzu tasan cewa mahaukaciyar qaunarshi ta mata mugun kamu,kamun da take zaton ba yau jiya ko shekaran jiya ya kamata ba,ta rasa yaushe ne?,a ina?,kuma a wanne lokaci?.
Sun dade sosai a wajen,don basu tashi ba sai sha daya saura,qiri qiri suka riqe twince suka ce wajensu zasu kwana,hakanan tana ji tana gani tana kuma jin nauyi tabi azeez din suka wuce sashensa,zuciyarta cike da fargabar wanne dare zata fuskanta a yau din?.
Tun daga farkon sassan ya baiwa duk barori dake hidimawa sashen hutu sannan suka wuce zuwa ciki,suna isa falon ya harde hannayensa yana dubanta da narkakkun idanunsa
“Zabi bedroom din da kikeso,wanda zaki kwanta ki huta sosai” maganar da yayi tadan kwantar mata da hankali,tadan dauke kai kamar ba zata nuna ba,murmushi ya saka,ya nufi wani wanda ke daura da nashi dakin
“Na zaba miki nan”
“Na gode” ta furta qasa qasa,ita gaba daya yadda yake kallonta yana sanyata cikin wani yanayi ne mai nauyi,gami da kunya,gabanshi gadi yake komai,dazun har gulmarsa uswa da afnan sukayi,saidaya jefesu da harara sannan suka guntse bakunansu.
Tana jiyo qarar wayarshi sanda take shiga dakin,duk da batasa dawa yake magana ba,amma taji takun fitarsa daga falon gaba daya,hakan ya bata sukunin sauya kayanta zuwa na bacci masu kauri yalwatattu,bata da sauran abunyi,saboda haka ta nade tsakiyar gado,ta jawo wuyarta daya mata kyautarta dazu me azabar kyau da tsada ta soma dudduba cikinta.
Cike da mamakin ha durfafi sashen fulani adama,yayi mamaki qwarai da yau ta daga waya ta kirashi da kanta wai tana son ganinsa,baya ga haka wai a daren,a daren ma qarfe shadaya da wani abu na dare?,abunda bazai iya tunawa sau nawa ya faru ba a rayuwarsa,hakanan ya danne mamakin har ya isa ainihin sassan nasa,ya kuma samu baiwa daya tana jiransa,tayi masa jagora har ainihin falon da fulani adama ke zaune tana jiransa.
Da mamakinsa da murmushi ta tarbeshi,harda miqewa tsaye tana fadin
“Maraba da yariman kaisa….sannu da zuwa” saiyadan dubeta kadan cikin mamaki sanda take nuna masa wajen zama
“Zauna mana,bari a kawo maka abunci da abunsha,na tabbata da qyar idan ka samu saka wani abu a cikinka saboda hidimar jama’a” kai ya girgiza yana soke hannayensa a aljihun wandonsa
“Bana buqatar komai,naci abincin dare tare da ammi na” cikin yaqe da boye takaici tace
“Ai amminka badai qoqari ba,duk damu an waremu ba’a gayyacemu ba” cikin zaquwa dason jin dalilin kiran yace
“Uhmmm” kawai,don dukka wadan nan maganganun nata baiga ma’anarsu ko muhallinsu ba face salo na batawa kai lokaci
“Ka zauna mana yarona,idan kaqi cin abinci ai bazaka qi shan komai ba” kafin yace komai ta kira daya daga cikin hadimanta,ta bata umarni ta kawo tatattaccen ruwan inibi kamar yadda tasan cewa azeez din yafi sonshi.
“Allah yasa lafiya dai ko?” Ya fada yana kafeta da idanu,saboda kame kame da yaga tanata yi
“Eh lafiya….amma saurin me kake ne,ka bari a kawo maka lemon mana”
“A qoshe nake,kiranki ne kawai ya fiddo ni”
“To…to ai shikenan…..dama akan abubuwan da suka faru ne wunin yau,yanzu ace shekaru har takwas abdul’azeez kana da mata harda yara biyu amma babu wanda ya sani a cikinmu?,aiko babu komai dai mudin kamar iyayenka muke,idam yau babu ranta mu xaka ci gaba da kallo a matsayin iyaye ko?,sam banji dadi ba,saiya zamana kenan bamu da maraba da sauran jama’ar waje dama talakawan gari ko?” Dan qaramin murmushi ya sake na gefan baki yana yada kanshi gefe kadan,sam baiga muhallin maganar ba,a yadda ma take magana kamar bata shirya yin maganar ba kawai yin kanta maganar take,ya jima da gama karantar halayyar matar tsaf,tun yana ganin kamar amminsa na daukan tsattsauran matakin nesantasu harya fahimci gaskiyar mahaifiyarsa,ya sani,makira ce ta gaske,maida dubansa gareta yayi
“Kinsan komai sai Allah ya nufa,to sai yanzu ya nufa ku sani”
“Eh hakane,amma duk da haka maganar gaskiya bamuji dadi ba,don innarka fauziyya ma don tabar nan wajen ne,amma fada ta dinga yi kamar zata ari baki,da qyar na tausheta” haka ta dinga soko maganganu marasa kan gado da sam bashi da alaqa dasu.
Bilkisu kuwa na tsaka da saita wayarta taji an turo qofar,da mamakinta tasa kai don taga waye,tasan cewa kamar ya mata sallama a fakaice ne sanda take shigowa dakin,to meye ya dawo dashi.
Saidai wanda ta gani din abun ya mugun kadata da razanata,wata fuska da batasan ga wacece ba tsaye gabanta tana qare mata kallo.
A hankali ta aje wayar gefe itama idanuwanta qur a kanshi tana son inda ta sanshi
“Malam lafiya?,waye kai,ta yaya zaka shigo dakin matar aure haka kai tsaye ba tare da neman izini ba?” Ba amsa illa ci gaba da qarewa surarta kallo da yake,wanda kallon ya bata tsoro sosai,saita soma sauka ta daya barin don ta dauko.mayafi ko hijabi ta qara suturta jikinta,Allah ya taimaketa ma kayan ba masu fidda tsiraici bane.
Tafiyarsa taji a bayanta sanda take sanya hijabin,tayi hanzarin juyawa tana daidaita shi a jikinta
“Ka fitar min a daki,baka da hankali ne?,ko kai mahaukaci ne?” Ta fada cikin qaraji da tsawa.
Wani shu’umin murmushi ya saki
“Dukka ina jinki,kuma ni ba tashin hankali ya kawoni ba,wala’alla ke bazaki gane ni ba,amma ni bazan taba iya mantaki ba,tun shekaru takwas dana taba ganinki zuwa watannin baya zuwa yau,na dade ina kishi da baqinciki da yarima,duk abinda nake buri a rayuwata sai naga shi ya samu ni kuma ban samu ba ciki kuwa harda ke,nayi burin aurenki,nayi burin samunki amma sai gashi lokaci daya yarima ya sameki,duk neman da nake shekara da shekaru ya tashi a banza,saboda haka nazo cikin salama ki bani na dandana yadda shima ya dandana,ko hakan zai ragemin zugin asarar rasaki da nayi,ki bani hadin kai,don har mu gama bazai dawo ba,idan kuma kinqi zan amsa ta qarfin tuwo,don naci alwashin bazan barshi wannan karon ya tsira dake ke daya ba”.
Batasan lokacin data daga hannu ta zabga mishi mari ba,tunda take a duniya bata taba jin tashin hankali irin wannan ba,tuni bacin rai zallah ya bayyana saman fuskarta
“Wanne irin jakin mutum ne kai?,wawa wanda baisan darajar aure ba,ko karuwa idan kana da kunya bai kamata ka gaya mata wannan maganar kai tsaye ba,bare matar aure mai mutunci,kayi gaggawar barin sassasan nan gaba daya,tun kafin na tara maka jama’a!” Murmushi ya saki yana shafa wajen yana sake matsowa inda take tsaye
“Naga alamar dai ba zaki bani hadin kai ba,saidai na yimiki fyade na karba ta qarfi” yana gama fadar haka ya danqi.hijabinta cikin zafin nama yana neman rabata dashi,kafin kace meye wannan kokawa ta kaure tsakaninsu,bilhaqqi ya sakar mata dukka qarfinsa da mazantakarsa kan sai ya keta haddinta,yayin da take dukka qoqarinta wajen ganin ta kare kanta ta tsira da mutuncinta.⁷⁷