SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Zauna ki lissafa duka ƙannenki ki zabar musu kowa yasaka,yau fulani inajin juyen kayan drower ɗinsu sukayi….ki zaɓa na saida na saidawa,na bada na bayarwa,don ba shakka waɗan nan kaya yadda suke fes kamar ba’a sanyasu ba ƙaramin kuɗi zan samu dasu ba Allah mai gado” murmushi takuma saki wannan karon mai sauti,tana sake jinjina son kuɗi irin na umma luba,kayane masu asalin kyau daraja da tsada,wanda duk wanda ya kalla koda bakasan kuɗinsu ba amma kasani ba masu
ƙarami ko matsakaicin kuɗi bane,tanajin umma luba naci gaba da sambatu gami da bata labarai,ta tsugunna tana duba su hauwa’u tana zaɓarwa kowa,duk da sauran tasan sun musu yawa amma haka ta ɗauka musu,tana kintatar zata bayar a maida musu dai dai jikinsu.
“Ana abu a masarautar KAISA,wani abunma sai jibi idan Allah yakaimu” takai ƙarshe tana sakin guɗa,da alamu dai cikin nishadi take yadda ya kamata.
Sunan masarautar dataji ya fito daga bakin umma luba sai taji duka kayan sun fice mata arai,AFNAN itace abu na farko daya soma faɗo mata a rai,kenan kayan sjn fito ne daga gidansu?,wala’alla ba za’a rasa nata a ciki ba,sai taji kamar ta barwa umma luba kayan,amma hakan bazai yiwu ba,saboda niyyar alkhairi tayi a gareta,dole ya hade kansu ta bata leda babba ta saka ta mata godiya kana tafito.
Kamar yadda ta qudirta din bata koma gida ba sai data shiga makaranta ta bada haddar dake kanta,saboda bata son ta rasa rana daya cikin ranakun zuwanta makaranta,musamman da a yanzu suke gab da kammala haddace qananun litattafan addini su tafi zuwa manyan,ba qaramin dadin karatun takeji qwarai da gaske,koda yaushe takan godewa Allah wanda bayan ya hanata wasu abubuwa na rayuwa amma bai hanata hasken ilimi da qaunarsa ba,ba ita ba koda qannenta a yanzu ba zaka kirasu jahilai ba ta fannin addini,tunda alhmdlh dukkaninsu suna zuwa makarantar Allo da safe,suje ta magariba bayan sallar magariba.
A hanya take tunanin abinda zata siya musu suci,saboda tasan bata bar musu abincin dare ba,hakanan babu yaqinin za’a basu suci,taso siya musu wani abun amma duka abinda ta lissafa zaija kudine,sai taliyar hausa ta fado mata a rai,idan ta siya kuma akwai bata lokaci kafin dahuwarta,mai yiwuwa su qosa ko wasu daga cikinsu ma suyi bacci,saita wuce gida kawai tana fatan asamu sauran abincin sayarwa wajen umma katti,tunda ba’a rasata da saura.
Tun daga soron gidan mamaki yacikata fal jiyo muryar mahaifinsu yana hira cikin walwala da dariya
“Allah hakimu,yau kuma wanne manzan rahamar aka saukar mana?” Tayiwa kanta tambayar zuciyarta cike fal da taraddi,ba zata iya tuna lokaci na qarshe data jishi cikin irin wannan yanayin cikin tsakar gidansu ba,idanma zata tuna din zata iya cewa tun aurenshi na qarshe da yayi suka rabu,da wannan tunanin ta qarasa kutsa kai cikin gidan.
Bata sake daskarewa ba sai data ganshi tsakiyar yaran,ko ina farantai nashe nashe da shinkafa da miya kowa na kaiwa baka,data lura dakyau ma sai take ganin kamar tsokokin kaji saman abincin,a haka ta dinga takowa idanunta akai,tana jin tamkar mafarki take
“Ke meye hanka,kalli gabanki mana,idan kuma yunwa kikeji kije ki amshi naki abincin wajen kattime” muryar mahaifinta kenan dake magana yau cikin cikakkiyar isa sabida cikakken awo da cefanen da yake ganin yayi,maganar tashi taja hankalin ‘yan uwanta kan shigowarta,dukka suka bar abincin sukayi wajenta,wasu suna mata sannu da zuwa,yayin da wasu keta faman nuna mata rasha da gwabar da yau suka samu a gidan nasu,wanda sun manta rabonsu da samun koda arziqin fara damai da gishiri bare miyar kaji,wasu daga cikinsu ma namam suketa tura mata taci,saita maida hannayensu cikin sanyin jiki,don ita sam abun bai mata ba,hakanan bai burgeta ba,suma don basu gama sanin ciwon kawunansu bane,ta tabbatar da walakin,hakanan akwai wata a qasa,cikin tattausar muryarta da take tsarin halittarta tace
“Na gode,maza kuzauna kuci”
“Kujimin ja’iran yara,yo itama da nata kason ai,banson kilbibi idan zaku zauna kuci ku zauna” baban nata yakuma fada,duk sai suka zauna sukaci gaba da cin abincinsu.
Sai a sannan tadubi sashen da baban nata yake a ladabce tace
“Barka da wuni baba,an wuni lafiya”
“Lafiya lau,sai yanzu kike dawowa?” Ya fada kamar yana ganin takai dare da yawa,kai ta jijjiga kawai
“Eh….na tsaya makarantar dare ne”
“To madalla” ya amsa yana afa lomar shinkafa bakinsa,miqewa tayi zata wuce dakinsu,sai kuma ta fasa taga gwara tasoma sauke nauyin bashin kudin umma katti a kanta,saboda haka tasauya akalarta zuwa dakin nata,dai dai lokacin da baban nata ya qwalawa umman kira yana cewa
“Kattime….kinga…gwara ki fito ki sake abinki,kici kazarki kisha jar miya ki godewa Allah da budin daya kawo yau”
Wani mugun tsaki ta saki sanda bilkisu ke saka kai dakin
“Ka hutar da yawun bakinka,aiba saika fada ba abinci zancishi,tunda haƙƙina ne Allah ya ƙwata yabani yau,amma duk wani iyayinka da ɗigiminka na riga dana daɗe da haddacesu,jiya bayau bafa,nasan dai ƙarshen alawa qasa,to mu zuba mugani,Allah ya bada sa’a” ta qarashe zancan tana dukan cinya gamida zunkuda zamanta,da alama masifa tana cinta.
Sallamar bilkisun ma sama sama ta amsa mata,bata bata dukka hankalinta ba sai dataji da biyan bashi tazo mata,saita maida kai sukayi lissafi ta cire mata kuɗinta,tasa hannu kuwa ta amshe abinta ta linke kana ta tura mata kwanon abinci har guda biyu,daya shinkafa daya miya
“Ga naki kason nan,yau Allah yayi babu kwanan yunwa” umma kattin ta fada tana sake gyara boyon kudinta,da kallo tabi kwanukan,ita sam ko daya abincin bai bata wani sha’awa ko armashin ci ba,saboda ba umma katti ba,ko ita tasoma shanshano abinda ke shirin faruwa cikin gidan,wata ƙila ma nan da wasu ‘yan kwanaki masu zuwa
“Allah ya amfana” kawai ta fada tana ɗiban kwanukan tafice zuwa dakinsu,yaran na ganin fitowarta kuwa dukka suka bita daki sukabar baban anan,don dama ba wani sabo ko shaquwa bane tsakaninsa dasu.
Kaya tacanxa ta ninke wadancan don sune nadan fitar sannan taxauna sosai tajawo kanukan tasoma budewa,dai dai lokacin da amina wadda itace qarama a cikinsu tace
“Yaaya yau abincin yayi dadi wallahi,hadda naman zakara irin na gidansu hasana” ta qarashe maganar alamun walwala da annashuwa na bayyana muraran saman fuskarta,sai murmushi ya subewa bilkisun,yayin da hauwa hannatu da umaima suka sanya dariya
“Wai kice aikin babba ne aminatu,zakara ne bama kaxa ba”sai a sannan maganar ta bawa yarinyar dariya itama
“Ku matso maza musake ci” hannatu ta zaro ido tana sha cikinta
“Ai yaaya duk cikinmu yau ba wanda baiyi mugun qoshi ba,ni har amai nake ji wallahi,saboda nayita cine ina hutawa,don bansan yaushe zamu sake qoshi haka ba” da qaramin murmushi mai dauke da tausayi take dubansu sannan tace
“Bakin da Allah ya tsaga ai baya hanashi abinci hannatu” daga haka taja abincin tana ci,jifa jifa suna hira tana tattambayarsu abubuwan da suka faru bayan bata nan,da yake haka dabi’arta take,idan tadawo cikin hikima a cikin hira take bugar cikinsu wasu abubuwan,wanda anan ne idan taji wani kuskure da wani yayi ko ba daidai ba saita gyara mishi kota tsawatar masa.
“Ya akayi ne hauwa kuluwa?” Bilkisu tafada sanda take gama cin abincin da tsakurarsa kawai tayi ta ture,saita sauke hannun daga tagumin datayi tana murmushi
“Yaaya,duk kin fimu kyau,sai nadinga ji dama nice ke” murmushi mai sauti ya subuce mata,har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana
“Toh?,yau kuma hauwa’u”
“Nima yaaya,na dade ina gani,ko qawayena idan sukazo sai suyita kallonki,suce kamar ba gidanmu daya ba,waike kin fimu kyau,kalar ‘yan gayu dake” hannatu tayi nata sharhin daya sanya bilkisu dariya dole,sai data tsagaita sannan tace
“Kuma duka masu kyaune hauwa’u,bakigama ke ‘yar fillo bace,gashinki ma yafi nawa santsi dakyau,kema hannatu baki kallon mudubi?” Maganar saita dan jefa yarinyar cikin tunani
“Yaaya” takira sunan bilkisu a sanyaye wanda hakan yayi calling attention na bilkisun sosai
“Na’am” ta amsa mata da dukka hankalinta
“Da gaske ni ‘yar fulani ce?,amma ban taba ganin mamana ko ‘yan uwanmu ba,tunda mamana ta tafi ban sake ganinta ba,kodai bazan sake ganinta ba yaaya,ko itama mutuwa tayi kaman mamanki?” Shuru ya ratsa dakin,yarinyar na dubanta tana jiran amsa daga bakinta bilhaqqi,maganganun yarinyar sosai suka taba ranta,suka koma soso wani sashe maigirma na zuciyarta,tausayinta yasake ninkuwa a ranta.
Kama hannun yarinyar tayi a tausashe sannan tace
“Mamanki bata mutu ba tana nan da ranta,kullum tana tunaninki kuma tanason ta ganki,amma wataran saidai kawai ki ganta tazo ganin hauwanta” murmushi ya kubcewa yarinyar,cike da nuna zumudi da kuma fata mai tarin yawa tace
“Da gaske anty?”kai ta jinjina mata alamun tabbatarwa
“Da gaske jidda” sai farinciki ya mamaye fuskarta.
Da wannan hirar ranar suka kwanta,yayin da suka tadawa bilkisun tabo sosai cikin zuciyarta,don kowanne yanuna sha’awa dason ganin mahaifiyarsa,inama ace itama zata samu dama koda sau daya taga tata uwar,ta zanta da ita ko sau dayane kuwa?,tausayin yaran take wani lokaci fiye da kanta,don gwara ita tasan dukkan wanda yamutu haihata haihata shida dawowa doron duniya,amma sufa?,ta qyamaci halin mahaifinta dakan raba yaran da iyayensu yakuma kasa riqesu yadda yakamata,yayin da wasu daga cikinsu iyayen ne a karan kansu suke fushi saboda abinda mahaifinsu ya aikata su watsar da yaran.
A daren ranar sai datayi kuka sosai kafin bacci yayi awon gaba da ita.
☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️
*MASARAUTAR KAISA*
Kamar yadda muka fada a baya babbar masarauta ce mai cike da iko mulki da wata cikakkiyar izza,tun shekarun masu tsaho da suka shude a baya har kawo yau,wanda tana gogayya da dukkan masarautun da suke maqwabtanta dama na nesa da ita,masarauta ce data cika ta tumbatsa da wani irin salo na mulki mai cike da adalci da qasaita na daban uwa uba kwarjini da daukaka da Allah yayi mata.
Babbar masarauta ce wadda take da fadin qasa,tarin al’umma,kaisa garine da yayi iyaka da kano da jigawa,garine mai albarka noma da kiwo,hakanan al’ummar ciki na rayuwa ne qarqashin adalin sarkinsu maimartaba sarki Abdallah mu’az nuhu kaisa,wanda tun tale tale na kafuwar garin mulkin garin a hannunsu yake,shi kansa gadon gado yayi daga iyaye da kakanni.
Gidan sarautar kaisa babban gidane wanda zaka iya kiranshi kai tsaye da gari guda,mai dauke da sassa sassa bisa tsari da fasali tun daga farkon gidan, gidajen ƙananun bayi da manyansu,bayi,masu qananun muqami da matsaikaita,securities na gidan wasu daga cikin dogarawa da sauran hadimai na gidan,haka tsarin yake daki daki har zuwa ainihin unguwar da matan sarki suke da iyalanshi da sauran makusanta.
Sarki Abdallah adalin sarki ne wanda al’ummar garinsa kejin dadin mulkinsa qwarai da gaske,yana da tausayi ga talakawanshi,mutum ne mai sauqin kai duk da awasu al’amurran bashi da sauqi ko kadan,hakanan kaifi daya ne shi,magana daya yake babu canji,mutum ne mai qoqarin riqo da addini duk da cewa yayi karatun boko.mai zurfi,don kafin zamowarshi sarki ya riqe muqamai iri daban daban masu tarin yawa,tun daga qananu zuwa manya,don har ambassador ya tabayi,kafin daga bisani yadawo gida bayan Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa ya amshi sarautar garinsu.
Sarki Abdallah nada matan aure hudu,ta hudun da ya aura bayan zamowarshi sariki ta rasu bayan ta haifi yarinya daya dashi,matarshi ta farko hajiya saratu ya aureta ne tun kafin zamowarshi sarki,a lokacin yana ministern mai na qasa,wanda basu jima sosai da ita ba don haihuwarta biyu Allah yayi haduwarshi da mayarsa ta biyu haj adama,wanda sun dan zauna zaman kishi lokaci maidan tsaho kafin Allah yasake yin aurenshi da Aishatulhumaira,a lokacin yana ambassador a qasar mali,diyar sarautar qasar itama kamar yadda yake.
Tun haduwarshi da ita tashiga zuciyarsa qwarai da gaske takuma tafi dashi,saboda wani irin kyau da Allah yayiwa aishan,kowa yasan yadda kalar fatarsu da yanayin kyansu yake wanda yake dan zubi da na ethopian’s,uwa uba jan aji da shan qamshinta wanda ya amsheta qwarai yakuma dace da matsayinta,wata irin mace ce da Allah ya zuba mata kwarjini da farinjinin manema,don shi kansa a sannan sai daya danci wuya kafin yasameta.
Sai neman auren aishan yazama wani abu na daban wajen haj saratu da adama,tun daga sanda sukayi binciken kan wacece aishan hankalinsu yatashi qwarai da gaske,suka kasa sukuni saboda sunga cewa tako ina tafisu,sannan shi kansa mai gayya mai aikin sun fahimci kamar yana zumudin abun,duk da yadda yake qoqarin boyewa da dannewa,duk ta yadda zasu shiga a fasa abu ya faskara yaci tura,tilas daga qarshe dai suka shirya plan na tararshi gaba da gaba,suka sameshi a falo yana hutawa suka tada mishi maganar,yayi qoqarin fahimtar dasu da lallashinsu amma suka toge,daga qarshe ma suka sanya masa kuka hajiya saratu tace
“Kawai dai duka take takenka mun gane ,mun fahimci inda kasa gaba kuma mun fahimci me kake nufi,saboda Allah yabamu haihuwar ‘ya’ya mata bamu haifan maka maza saboda kana sakaran ka amshi sarauta kana neman magaji tun yanzu,to ai muma bamu muka baiwa kanmu ba,kuma cikin daya haifi ‘ya mace shi zai haifi da namiji” shuru yayi na mamakin kalamanta,sabodashi sam ko sau daya ma bai taba darsa wannan tunanin cikin ranshi ba,saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah,shi kanshi mai martaba a sannan yana nan da ranshi bai mutu ba bare yayi wani tunanin mulki.
Idanu kawai ya zuba musu,suka dinga tashin hankali kala kala har akayi auren,yabar aisha a qasarsu saboda shima a sannan yana can yana aikinsa,sam ita aishan bata damu dasu ba,duk da tana da kishi tana kishin mijinta saboda yadda take sonshi amma ko zancansu bata masa,taja mutuncinta sosai,tun bata fahimci yadda suke kishi da ita ba harta gane,saboda haka tasan halin kowacce cikinsu duk daba qasa daya suke ba,kuma abdallah baya mata zancan kowacce cikinsu amma ta fahimci kowa,macace mai matuqar saurin gano abu,kaifin basira da hangen nesa,yanayin yadda abubuwa ke gudana idan yakoma can wajensu kawai ya isa ya bayyana mata komai.
Basu sassauta kishinsu a kanta ba sai datayi haihuwar fari itama tasamu diya mace,kai kaga walwala da sakin jiki,harma suka yanke haj saratu zataje har can mali barka da taron suna,shi kansa yayi mamakin yadda suka sake din,amma bai kawo komai a ranshi ba donshi bai saka zancan haihuwar mata ko maza a wani babin ba,hasalima ya manta taqaddamar da sukayi dasu lokacin auren aishan,sai yayi murna sosai saboda yana tunanin sun sassauto ne saboda zuri’a da aka soma hadawa.
Haka kuwa akayi,ta shirya tsaf tayi siyayya ta alfarma suka tafi da duka yaran su hudu,nata biyu nimra da zunaira,sai na adama biyu Aafiya da afra.
Gidansu aisha gida ne na karamci suma,saboda haka tasamu saukar girma data sake sanyata ta bambance aya da tsakuwa,bugu da qari duka yadda suke hasashe ashe abun yawuce hasashen nasu,don yadda taga anata hidimar bikin sunan jaririyar cikin gidan nasu,aishan ‘yar gata ce gaba da baya.
Tunda tazo suka gaisa aka kai mata yarinyar bata kuma bari sun hadu ba,saidai duk wani abu daya kamata ayiwa baqo dama wanda bai zama dole ba duka an yiwa saratun,takuma aiko aka mata godiyar kayan barka,saidai a jikinta taji cewa ba zuwan Allah tayi ba,to koma mene batajin zata bari kota yarda a cutar mata da diya,don tun sanda ta haifeta take mata mugun so.
Yadda saratu tazo data tashi komawa saiya zaman gwiwa kusan a sanyaye,don ta ganewa kanta abubuwa masu yawa,ciki kuwa harda kyau da Allah ya yiwa yarinyar na daban,ga uwa uba gatan data gani ana nuna musu,koda ta dawo ta baiwa adama labari sai sukayi zugum,inda daga qarshe adaman ta katse tattaunawar tasu da cewa
“Koma meye dai mu godewa Allah data yiwo mu,don inda namijine kuma saita Allahu,sai abinda idanuwanmu suka gani kenan”.
Tafi tafi haka rayuwa ta dinga tafiya har zuwa sanda maimartaba ya kwanta ciwo,wanda ciwon nashi kusan shine silar daya sanya abdallah ajiye aikinsa na ambassador,yadawo gida gaba daya saboda shine babban danshi,wanda kuma sukagi shaquwa dashi fiye da kowa,wannan karon harda aisha itama tabiyo mijinta nigeria donta zauna dashi,a sannan dukka matan nashi ciki garesu,saidai akwai bambancin watanni,na saratu shine mai watanni bakwai,adama wata shida,yayin da aisha nata keda wata biyar,saboda tsayinta da yanayin shigarta yasama ba kowane ke lura dashi ba.
A wannan zaman da sukayi tare da sake karantar kowa tsaf ciki da bai,haka suma sun sake fahimtar tazarar data musu a zuciyar mijin,katsam saiga al’ummar gidanma kusan suna neman komawa qarqashinta,kasancewarta mai budadden hannu,ba baya bace wajen kyauta,duk da tarin izza da qasaitarta,duk da bata cika sakin fuska ko faran faran da jama’a ba,amma duka wannan bai damu mutane ba,da yake yanzun kusan kowa yafi ga abun hannun dan uwanshi.
A wannan lokacin tsakanin adama da da saratu kowa fafutukar ganin ya haifi da namiji yake a cikinsu,kudi suka dinga bararwa suna baiwa malamai na Allah daba na Allah ba ana abubuwa iri iri saboda su haifi namiji,gamida alqawura iri iri ga hadimansu na duk wanda yazama silar samun namiji a cikinsu zasu ‘yantashi,masu ‘yanci kuma zasu wadatashi,saboda kowacce tana ji a jikinta lokacine yayi da mijinsu zai karbi sarauta,wanda hakan ke nuna cewa abu na gab zuwa kansu.
Amma a zahiri idan sun hadu kowacce fata takewa ‘yar uwarta nako itace tasamu babu komai,saidai kowanne ta qarqashin qasa akwai hadimansa dake masa aiki a sashen kowaccensu ba tare da kowannensu yasani ba.
Ta fannin aysha kuwa hankalinta a kwance yake,sabgarta kawai take da kula da mijinta,da kuna tayashi kulawa kan lalurar mahifinsa,sun tuttura mata sabbin fuska don su shiga jikinta kamarsu amma basu samu wannan damar ba,saboda halinta na dabanne ita,tana da matuqar wayo da takatsantsan,don haka ita basu da wani labari daya danganceta ko sassanta sai dan abinda ba’a rasa ba.
Wata biyu da dawowarsu a safiyar wata asabar saratu ta haihu,tashiga tashin hankali da matuqar girgiza sanda unguwar zoman dake amsar haihuwarsu ta shaida mata diya mace tasamu,babu jimawa labari ya karade gidan,ranar sashin nata tamkar zaman makoki akeyi,saboda kowa yasan yadda ta qwallafa rai akan da miji kuma bata samu ba,dukkanin hadimanta ranar kaffa kaffa suka dinga yi,babu wani mai qwaqqwaran motsi ko dariyar kirki,a haka labari yasamu adama,tayi rawa tayi shewa tayi juyi gaban mutanen da take gani amintattun tane,wadanda sune suka kawo mata labarin,saidai batasan cewa sune makasan nata ba,kana ta umarci hadimanta maza su shirya abinci mai rai da motsi a kaiwa saratu,itama tana bisa hanya.
Isar abincin da isarta sassan saratun ba wani tazara mai yawa,donta qagauta taje ta ganema idanunta
“Haka Allah yashirya,qaddararsa kenan” adaman ta fada cikin fuskar jimami sanda take zaune kusa da saratu wanda ke kashingide saman wata kujerar hutawa dake wani daki na musamman da aka kebe saboda hutawar.
Nannauyar ajiyar zuciya saratun ta saki,kana a hankali ta dora idanunta kan adaman,tuni labarin abinda tayi ya rigata isowa,saboda haka tar take kallonta,saita miqe tazauna sosai sannan tace
“Qaddararmu ce gaba dayanmu halan” saita san dakata tana ci gaba da duban adama tana shaqar numfashi sannan ta dora
“kuma na rantse da sarkin da babu wani saishi,indai ni saratu uwar gida ga Abdallah bani nasoma haifa mishi ɗa namiji ba,babu matar da zata haifa ɗa namiji cikin gidan nan”.
Gaban adama yafadi tsoro yadan shigeta,kada fa yazamanto namiji ne a cikinta saratu ta aikata abinda zaisa yakoma mace,amma a zahiri saita dubeta duba na mamaki
“Tofa….kamar yaya,me kike nufi?” Sai data koma ta kashingida sannan ta bata amsa a taqaice
“Lokaci zai nuna” daga haka bata kuma tanka mata ba,saita aje mata yarinyar saitin qafafunta tamiqe tana cewa
“Lamarin ubangiji dai rubutacce ne,Allah ya qara lafiya,nina wuce” binta tayi da kallo,sai ta saki shu’umin murmushi
“Kinsan ubangiji ne adama?,muzuba mugani” ta fada cikin ranta,kana ta waiwaya tadubi yarinyar daketa bacci abinta batasan ma me ake ba,sai taji dama ta bude idanu ta ganta a matsayin d’a namiji ba mace ba,takirayi daya daga cikin barorinta tadauki ‘yar ta maidata cikin gadonta.