SIRADIN RAYUWA CHAPTER 5 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 5 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

Babban club ne na masu aji da naira wanda yake hada manyan yara daga qasashe daban daban matasa masu jini a jiki,daga can wani kebantaccen waje zaka hangeshi zaune saman teburin daya qunshi kujerun zama guda biyar,kowacce kujera akwai mutum akwai,saishi cikon na biyar din dake zaune tsakiyarsu,ba abinda yake bankawa cikinsa hayaqi,wanda duk sanda yazuqa ya fesar sai kaga wani dunqulallen farin hayaqi yatashi sama yacure guri guda kai kace an hura wutar itace ne da

jiqaqqen itace ko wutar ta mutune tana neman agajin fifita,daga saman teburin akwai saura saura da burbushin wadanda yasha masu tarin yawa,bayaga kwalbar abunsha wanda babu ko kokwanton cewa ba zallar abunsha bane da baisa buguwa ba.

       “Kamal…..ka tsaida wannan hayaqin da kake bugawa cikinka kamar babur,tell us me yake faruwa,kasoma gaya mana kuma but u keep quite”.

        Sauran ta hannunsa yayiwa kyakkyawar zuqa sai gata ta qare,yadorata saman table din yakashe kamar yadda yayiwa sauran,kana yafeso dukka hayaqin waje ya qarawa sama hazo sosai sannan ya muskuta ya gyara zamanshi

“Kamar ni….ni prince AA zai kora daga gidanshi?” 

“What!” Suka fada kusan a tare kowa yana dubanshi,baqinciki yasake cika kamal yanajin takaicin yadda ya tozartashi cikin abokanshi dasuke sake ganin girma da qimarsa sakamakon cewa azeez din dan uwanshi ne na jini

“Amma baaabaa….ba cousin dinka bane?” Kai ya gyada

“Cousing dina ne amma yayimin haka” ya qarasa fada cikin dacin rai,daya daga cikin matasan wanda shima yaciro tashi tabar yakunnata yasoma busawa sannan yace

“Ni dama guy din fa ya tsayemin a rai,kishi nake dashi wallahi yadda kasan nasa bakin bindiha na harbeshi,kwarjininsa yayi yawa,kamar komai an bashi a rayuwa,amma….yakamata kamal kadauki mataki,dont let it to be in vain” kai yake jinjinawa,abinda yakwana biyu yana kitsama ranshi kenan yadda zai jawo abdul’azeez ruwa,ya tabbatar idan hakan tafaru zasufi samun sakewa suyi duka yadda sukeso cikin walwala tunda shima yazama dan hannu

“I know his week point,na rantse da Allah saina rama,saina dauki fansa….ba lalacewa yake gudu ba?….” Saiya saki murmushin jin dadi kana yasanya hannunsa yadaki table din dake gabanshi,dukkaninsu sun fahimci me yake nufi,don haka dariya ta gauraye wajen,daya daga ciki yasake cewa

“Maan…kace kwanan nan muma kuttun farinjininmu zai fashe if he join us,zamu sake zama big boys fa”

“Qwarai kuwa”

“Amma kunyi suya kun mance da albasa,banji kunyi magana kan hanyar da zaku jawoshin ba,aikine mai wahala idan kun manta na tuna muku,kai kamal kafi kowa sanin waye prince azeez”.

      Kai ya jinjina idanunsa akan matashin

“Nafi kowa cikinku sanin wannan….nakuma tsara yadda zamu gudanar da komai,kamar yadda nasan yanayinsa zamu hilaceshi da mace,amma mace wadda tacika ta isa mace,anan matsalar take,ban gano wata mace wadda zata dace da plan din ba,takuma jure shi” shuru ne ya ratsa tsakani,kowa na nazarin maganar kamal din,don a nan gizo yake saqar

“Wow!…..na tuna….minal” daya daga ciki yafada da sauri har yana zunkudawa gaba kan kujerar da yake kai,da alama abinda yatuna din yayi mishi dadi

“Wace minal?” Kamal ya jefa masa tambayar

“Itace yarinyar da take da interest akan prince harta kasa boyewa ta bayyana mishi,amma ya tozartata cikin jama’a,na tabbata ina da yaqinin idan mukaje mata da wannan maganar komai zai tafi”

“Ya take?” Kamal yasake tambayarsa,gira ya dage masa yana sheqewa da dariya

“Minal ta hadu,idan nace maka haduwa ina nufin ta hadun din”

“Good” kamal yafada yana murmushi,yabude baki zaiyi magana wayarshi tadauki kida,yaja dan tsaki kana yacirota  yana duba mai kiran,mahaifiyarsa ce,saboda haka ya daga.

        “Nayi qoqarin kiran me martaba na shaida mishi abinda ke faruwa,saidai kuma yayi tafiya baya qasar kaisa,amma gobe xai dawo,dole yaji wannan maganar,tunda shi bashi da mutunci,baya ganin kowa da gashi,kana dan uwanshi har zai iya korarka daga gidan saboda yasamu daurin gindi daga mahaifiyarsa?,na shaida mata abinda ke faruwa tacemin wani wai zata bincika?,bincike na meye?”

“Rabu dasu mom,na rantse saina dauki fansa kan abinda yayimin din,karki damu na gana tsars yadda komai xai gudana”

“Kome zakayi kayi,amma karka sake kayi abinda zai nakasta shi ko illatashi”

“Baki da damuwa,sai munyi waya” yafada yana katse kiran yakoma wajen abokan nashi sukaci gaba da tsara yadda komai zai gudana.

☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️

      A washegari cikin gidan nasu akayi ɗan ƙwarya ƙwaryar wuni,itadai bilkisu bata fasa zuwa makaranta ba bare wajen aikinta,don bataga wani sabon abu ba game da lamarin,hakanan batasan zaman me zatayi cikin gidan ba.

       Sanda tadawo kuwa kusan babu kowa sai ‘yan kawo amarya,tadinga bin tsakar gidan da kallo yadda akayi kaca kaca da abinci,ta dinga jin ciwon hakan cikin ranta,don a qalla abincin idan aka tattara yakai abincinsu na kwana da kwanaki wanda mahaifin nasu bai iya cida su,amma saboda aure yau gashi abinci a gidansu har soro,haka ta tsallake tawuce cikin gidan.

       Taji dadin yadda tasamu hannatu ta killace qannen nata duka a daki,data shigan sai tayi qoqarin sakin fuskarta,har zuwa lokacin data gama duk abinda zatayi,tasa kowannensu yasamu guri ya kwanta,ba jimawa kuwa Allah ya taimaketa dukka sukayi bacci,don haka ba’a kunnensu akayi badaqalar shigowar malam bilya da kazar amarya babu ta umma katti ba,da qyar su batulu suka shiga fadan suka sasanta yawuce abinsa dakin amaryarsa yana rawar qafa kai kace a ranar yasoma aure.

          Sati guda amarya tayi tana cin amarci kai kace budurwa ce a maimakon kwanaki uku,cikin kwana bakwai din gidan babu yunwa babu qishirwa,girki ake kamar kowanne gida sau uku kuma aci a qoshi,duk da cewa ita amarya ta tsaya kai da fata kan girkinta zatayi daban,bazatayi girkin hadaka ba,hakan kuwa babu musu tasoma dora tukunyarta,wanda kullum ta Allah sai anyi tashin hankali tsakanin malam bilya da umma katti,saboda banbanci cefane da yakeyi qiri qiri,miyarta tafi takowa maiqo da zaqi.

       To sannu sannu dai a haka rayuwar cikin gidan taci gaba da garawa,babu wani abu daya sauya,kullum sai qarin tsanani da nauyi dayake dake hawa a kafadar bilkisu,don bayan wasu kwanaki ya watsar dayi musu cefane ya kama na amarya ita kadai,ungulu takoma gidanta na tsamiya.

☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️

      Sati guda rak kamal yayi maimartaba yayi magana da abdul’azeez tilas yace dawo gidan,hakanan ya sake tattarawa yadawo saidai bai fasa aiwatar da qudurinsa ba.

       Saidai kuma duk yadda minal taso janyo abdul’azeez jikinta ta jefashi cikin sabgarsu kamar yadda kamal yabuqata abun yaci tura,haqarsu ta gaza cimma ruwa,wanda har tasoma sarewa takuma baiwa kanta amsar lallai abdul’azeez din bazai jawu ba,don ta gwada dukkan wata fikira da basira tata amma abun yaqi ci yaqi cinyewa,wanda daga qarshe tasamu kamal ta shaida masa.

      “Kayi haquri kawai,don yariman yawuce dukka tunaninmu,ina ganin ka ajeshi gefe kawai ka kama wata sabgar taka” cikin fusata yadaki bencin dake gabansu

“Ba zaki gane bane,bazaki fahimta ba,idan har abdul’azeez yazama dan hannu inajin kaf makaranta ba za’a samu wadanda suka kafa tarihi cikin rayuwar bariki ba irinmu,zamuyi komai cikin wadata da qasaita ne….amma indai wannan bata samu ba,ina da wani plan din,tunda taurin kai gareshi,zan masa mai gaba daya,sai nayi tarnishing image dinshi a idanun kowa idan ma yanajin shi wani ne,sainasa kunya ta hanashi shiga cikin al’umma,atlast zanyi amfani da wannan hanyar nayi destroying duk wani tanadi da suke da batar da sunanshi da yarima a masarautarsu,kin shirya aiwatar da wannan aikin?,idan kin shirya ki fadi ko nawa ne farashin aikin ki,zan biya”.

      Shuru minal tayi tazubawa kamal idanu,a mamakance take kallonshi,jiki da zuciyarta sun bata cewa lallai akwai wata a qasa,bawai a dalilin korarshi a gidan yasa zai aikata dukkan wannan abun ba,ba shakka akwai dama wani qulli duk yadda akayi tsakaninsa da yariman tun bayau ba,dan gyara zamanta tayi still tana kallonsa

“But….amma kamar kana da wani plan ne apart from dalilin da nasan ya sanyaka zaka mishi wannan abun” hannu ya daga mata alamun dakatarwa

“Wannan duka ba huruminki bane…just idan zakiyi ki fadi price” murmushi tasaka tana qarewa kamal kallo,a ajinta tana ganin kamal yayi qanqanta ya gaya mata magana haka,don haka tace dashi

“Ban amshi contract dinka don kudi ba,don basu na rasa ba,na amsa ne saboda nawa interest din,saboda haka,bani da sha’awar yin aikinka,inaga abinda zaifi kanemi wata” takai qarshe tans miqewa tsaye gamida qoqarin saba jakarta a kafada.

        Kallonta yake ganin da gaske tafiyar zatayi,idan tatafin kuma baisan inda zasu samu wata kamarta ba,bugu da qari yana buqatar privacy,baisan mutane da yawa susan maganar ta yadda zaya zamana babu wani sirri kenan

“Wait minal pls…..zauna kiji wani abu daya kafin kiwuce” sai data juyo ta kalleshi sosai,kana kuma a hankali takoma gurbin data tashi tazauna,ta zuba masa dukkanin idanunta alamun tana saurarenshi.

       Sai da yayi gyaran murya kadan gamida gyara zamanshi,yasake matsowa kusa da ita yadda zata jishi sosai

“Koda baki da buqatar kudi amma kina buqatar yarima ko?” Kaita gyada

“Of course..”

“Good,bari to na gaya miki abinda zai iya faruwa,wanda inada yaqinin koda ba hundred parcent bane to 99.9 parcent hakane” shuru sukayi dukkaninsu kafin yadora

“Duk wadda tasoma cikin galaba kan azeez takaishi wannan dunuyar ina mai tabbatar miki itave zataci gaba da kasancewa dashi,koda azeez zaiyi bariki,zaiyi bariki ne ta musamman ba irin ta kowa ba,kinsan dalili?”kai ta girgixa tana sake bashi dukka hankalinta

“He is arrogant kinsan da wannan,and he prides him self cewa babu wata mace data isa tayi dauke hankalinsa zuwa wannan hanyar,babu soyayya a ranshi bare a samu damar kaishi hanyar da muke kai,kinga,zai zamana yana boye sabon halinsa don kar asani a masa dariya,zai dinga qoqarin samun sirri ta hanyar yin mu’amala da mace guda,duka bayan wadan nan kuma….azeez yana da qyama da qyanqyami,so dat,kiyi tunani kigani,idan xaki iya barwa wata wannan opportunity din da kika samu….fine” yana gama gaya matan yamaida bayansa makarin kujerar yajingina yana dubanta,yana fatan maganganunsa su shigeta,ya tabbata matuqa sukayi nasarar bata azeez,babu makawa sune zasu shiga takarar neman zama sarkin kaisa,kamar yadda dokar qasar ta tanadar matuqar an samu yariman dake da damar hawa mulki da wani babban alfasha.

        A hankali take jujjuya maganganunsa,wanda fiye da rabin zuciyarta tatafi kan cewa ta karba tayi koda babu ko sisi,saboda samun yarima azeez a wajenta shine babban biyan da za’ayi mata

“I can do it” ta amsa mishi,saiya saki murmushi kana yace

“Well,yayi kyau,shikenan zamuyi magana,zan gaya miki yadda komai zai kasance,rana dakuma lokaci” daga hakan sukayi sallama tadauki qaramar jakar hannunta tafice daga wajen.

       ☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️

       Sassanyar safiya ce wadda ke cike da lullumi da wani irin yanayi me dadi a qasar ta mexico,daidai lokacin da yarima ke fitowa daga bandakinsa dake manne a cikin dakin baccinsa,agogo yasoma dubawa lokacin daya fito don yaga lokacin daya rage mishi kafin shigarsu lacture,saiya dauke kanshi yana ci gaba da goge jikinsa dake cike da gargasa da qaramin towel din dake hannunshi bayan wanda ke daure a qungunshi.

       Dan tsayawa yayi yana duban dakin,sai yaga kamar ba yadda yabarshi ba a sanda yashiga yashiga toilet,kamar wani abu ya canza,a nutse yasoma tattakawa yana sake qarewa dakin kallo dakyau,saidai bai sake ganin komai ba don haka yanufi gaban mudubi yadauki manshi mai taushi da qamshi yasoma shafawa yana sakin tsaki bayan yatuna cewa yau su ukune ma kawai suka kwana cikin gidan,tunda safe kuma daya shiga kitchen zaisha ruwan dumi yatarar duka sun fice,da alama kowanne cikinsu yana da lactures din safe.

       Sai daya gama shafa man,ya gyara sumarshi dakyau bayan yashafe ta da mayukan gyara gashi kala kala kai kace macace,sannan ya isa gaban ma’ajiyar kayanshi yasoma duba kayan da zai sanya.

       Gaba daya shigar fari yayi hatta da agogon hannunshi,yakoma gaban mudubin yayiwa kanshi ruwan turaruka masu sanyin qamshi da kwantar da rai,bedsite dinshi yajawo yadauki abinda zai dauka da wasu takardu daya gama dubawa daren jiya dake gefan madubin nashi kana yafito bayan ya murzawa dakin nashi key,don ba kasafai yake barin dakin nashi a bude ba,musamman idan yasan zaiyi nisan kiwo,mutum ne mai tsari da doka,sam bai yadda ana shiga mishi daki barkatai,shi yasa ko yana ciki to zaka samu qofarshi ya turota badai ka sameta a bude ba.

     Kafin yafita daga corridor dinsa kira yashigo wayarshi,dan qaramin murmushi yafidda ganin me kiran,saif ne,amininsa dan wazirin mai martaba,waziri musa adamu,cikin yanayin dake nuna akwai sabo da shaquwa tsakaninsu yadaga wayar soma magana,daidai nan ya qaraso falon gidan.

      Babu kowa cikinsa kamar yadda ya zata,sai yayi tsaye yana ci gaba da amsa wayar harya gama,motsin daya jiyo daga kitchen shi yaja hankalinsa yamaida dubanshi can,sakan talatin saiga kamal na fitowa daga kitchen din,dauke da madaidaicin plate wanda akai cups ne guda biyu da plates guda biyu wanda ke dauke da soyayyen plaintain.

       Da murmushi kan fuskar kamal din ya qaraso yana cewa

“Na tsammaci kafita ai”

“Ina dai niyya,kai kadai ka rage a gidan”

“Eh,nima nagama shiryawar break kawai zanyi nafita….bismillah zo muyi break din” yafadi yana aje farantin,kallon tea da plaintain din yayi cikin mamaki,don yasan kamal din mugun lazy ne,yawanci a kitchen yake karyawa a gurguje yafice,amma yau sai gashi da kinkimo faranti,kamar zaiyi magana sai kuma yafasa,ya qarasa gaban farantin yadauki cup daya daya rage a saman farantin don kamal din yadauki dayan,yasoma kurban tea din,saiya samu hannun kujera yazauna don yasan haramcin shan abu a tsaye.

      “Ohk,on my way” yaji kamal din yafada cikin hanzari ya aje cup din hannunsa,ya debi plaitain din yawatsa a bakinsa a gurguje yadubi yarima azeez

“Prince nawuce” kai ya kada mishi kawai ba tare da yace komai ba,yana qoqarin shanye sauran tea din hannunshi shima yafice.

      A nutse ya isa inda ‘yar qaramar motarsa mai azabar kyau ke aje,wadda take da budadden sam,yabudeta kana yashiga yazauna

“Oh my god,whats happening?” Ya fada sanda yake da niyyar tada motar,saboda wani irin feelings da bai taba jin makamancinsa ba dake taso masa yana ratsa sassan jikinsa,har tsigar jikinsa tana tashi,uwa uba kuma uban kasala yakeji kamar wanda ya shekara yana aiki.

       A qalla yakashe minti biyar yana jira ko mode dinsa zai daidaita,saidai sam babu wani sauyi tattare da yanayin da yake ciki,saima uzzura da lamarin yake,abun saiya soma bashi tsoro bayan mamaki,a kasalance yakashe motar yazare muqullin yafita daga ciki yasoma takawa zuwa cikin gidan,har wani jiri jiri yakeji,yana dafe da jikinsa yasanya muqulli ya bude gidan yashiga,da qyar ya iya kai kansa dakinsa yazube saman gado yana sake jin kowacce gaba ta jikinsa na sake mutuwa,yana kuma sake fita daga hayyacinsa,feelings din dake tare dashi yana sake ta’azzara kamar zai zauce.

        Daidai lokacin kamal yafito daga maboyarsa,yaisa varender gidan wadda daga ita sai ainihin falon gidan,yatura qofar falon dako samun damar rufeta abdul’azeez bai samu ba,kamal dinne ya qarasa rufeta,kai tsaye yashige kitchen.

      Tana zaune kan daya daga cikin kujeru ukun dake kitchen din,hannunta riqe da wayarta da alama charting take,cikin wata iriyar shiga wadda bata da maraba da tsirara,komai na jikinta ya bayyana,qamshinta kuma ya gauraye ilahirin kitchen din.

       Tsaiwa kamal yayi yana qare mata kallo gamida hadiyar yawu da lashe baki,ji yake inama ace shine zata jewa a wannan siffar tata,alamun motsin mutum ya sanyata hanzarin dago da kanta,suka hada idanu da kamal saita zabga mishi harara,ta tsani yadda yake da shegen kallo da yadda yake yawan bibiyarta da idanunshi,ta riga data gama karantarshi tun ba yau din ba,saidai ita sam bai mata ba,hasalima baikai ajinta ba ko kusa ko alama a yadda takejin kanta a matsayin babbar yarinyar dake harka da ‘ya’yan wasu,ko wasun kansu a baya,bare a yanzun da babu wani da namiji dake burgeta ko take gani sai abdul’azeez din,yashafe tauraruwar kowanne namiji a idanunta.

      Basarwa yayi yaqaraso kitchen din kamar mai rada yace

“Komai yazama ready,ki sameshi a bedroom dinsa,a yanayin da naga yake ciki bazai iya tsallakewa trap dinmu ba,i wish u all d best” yana gama fada yajuya yafice daga kitchen din,batayi jinkiri ba itama tabiyo bayanshi,saiya dakatar da ita,yadauko laptop dinsa wadda ya saitata da camerar da zai nadi komai,wadda ke maqale jikin qarfen da aka sanyawa net aka lullube gadon azeez din dashi,yakunnata ta kama,saiga hoton abdul’azeez din zaune saman gadonshi,qanqame da jikinsa,idanunshi a runtse gam,babu abinda yake fiddawa sai gumi.

      Qaramar dariya yasaki mara sauti kana yace

“Uhmmm,lokacinki yafara” batace komai ba tajuya zuwa sashen daya nuna mata,saiya zaro wayarshi ya danna lambobin wayar mahaifiyarsa,bugu uku ta daga

“Mom,komai ya kammala,yanzu haka za’a fara aiki,saiki addu’an samun nasara”

“Allah ya bada sa’a son,wannan nasarar idan ta tabbata ba shakka dukkan abinda zai biyo baya mai sauqine,rushe aysha da abunda tafi tutiya dashi duk duniya shine babban aikin,Allah yabada nasara,sai naji feedback”

“Ok mom” ya fada yana kashe wayar,kana yamaida dukka hankalinsa kan laptop din yana jira yaga shigar minal dakin azeez,har wani lumshe idanu yake yana sake relaxing cikin kujerun,ko banza shima zai more da kallon yadda komai zai wakana,yakuna sakin murmushi yana hango yadda vedion da hotunan zasuyi destroying azeez da mahaifiyarsa cikin masarautar kaisa…….

      Duk taku daya da zatayi na kusantar dakinsa sai taji wani matsananciyar faduwar gaba ta sameta,karon farko a rayuwarta tunda tafara irin wannan harkar data taba samun haka,sanda ta isa qofar dakin tsaiwa tayi cak bayan ta dora hannunta a handle na qofar,tanajin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,ta lumshe idanunta tana son baiwa kanta qwarin gwiwa gamida hasashen nasara,kana tatura qofar cikin sauri kawai tashige.
      Daga can sashen kamal yasaki ajiyar zuciya sanda minal ta bayyana cikin dakin,yana sake gyara zamanshi sosai tare da sake saita komai tare da bada hankalinsa gaba daya.
        Yaji bude qofar amma bai damu yadago ba,saboda yana zato da tsammanin daya daga cikinsu mustpha ne yadawo,baiso kuma kowa ya fahimci yanayin da yake ciki,infact ma baison takura,baisan ya akayi ya manya bai rufe dakin da muqulli ba.
      Tsaiwa tayi tana dan qarewa dakin kallo,yadda ya hadu haka komai nashi yake hadadde,yadda ya tsaru haka komai nashi yaje a tsare,yadda yake maikyau haka komai nashi yake me kyau,ta sake gasgata yarima azeez din na dabanne,saita sauya shawara,gwara tayi maaa shigar gaba daya,tana da yaqinin a yadda taga jikinsa na wani irin rawa bazaiqi karbarta ba,hakan shiya baiwa minal damar soma raba jikinta da duk wata sutura data shigo da ita,kana ahankali tasoma takawa zuwa gadon da yake zaune akai.
      Kamar a mafarki yasoma yin wasu abubuwa da suka sake birkitashi,cikin qanqanin lokaci tasoma cin galaba akanshi,wani irin bugu zuciyarsa take masa kamar zata tsaga qirjinsa tafito,yana kallonta,yana kuma son hanata amma ya gaza,abinda yake ji cikin jikinsa yanason yafi qarfinsa,tsahon wasu mintuna tana neman qarasa gusar mishi da hankali don tacimma burinta dana kamal,tamkar qiftawar idanu taji an harbota daga saman gadon zuwa tiles din dake shimfide qasan dakin
“Hasbiyallahu la’ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim” daya soma fadi tundaga zuciyarsa harta fito saman bakinsa yaci gaba da maimaitawa muraran a fili,ya rarrafa yasauko daga saman gadon yanaci gaba da maimaita addu’ar.
     “Kut!” Kamal dake jiran komai yasoma wakana yafara recording yafada yana miqewa zumbur daga kashingidar da yayi zuwa zama dafa’an,cike da mamakin ta yaya yayi escaping?,duk wata jijiya ta jikinsa sai data tsinke,ya hade hannayensa yana murza tafin hannayen nasa waje daya.
     zuciyarsa na wani irin tafasa,bacin rai yafito mishi muraran saman fuskarshi,kauda kanshi yayi sam ba tare daya dubeta ba tunda ya fuskanci babu suttura a jikinta,saiya sanya qafa ya tura mata kayanta,cikin rawar jiki dakuma tsoron yanayin da taga fuskarshi ta koma tasoma maida sutturarta,tana gamawa tasoma laluben qofar fita,tsawa ya daka mata mai qarfi
“Wacece ke?,daga ina kike?,ta yaya kika iya shigowa har inda nake?” Cak ta tsaya numfashin tsoro na fita da gudu daga qirjinta,lallai duk a baya yunqurin banza tayi tunda baima gane wacece ita ba,wani gumi ya karyo mata sanda taji yana takowa inda take tsaye saita kasa waiwayowa.
      Hannu ya sanya kamar zai shaqeta saiya fasa,yakuma fasa mata wata tsawar data sanya gumi yanko mata,daidai lokacin da mararsa tariqe saiya duqa riqe da marar tasa,da wannan damar tayi amfani tayi wuf ta bude qofar tafice kamar zataci da baka.
       Bai kuma bi ta kanta ba saboda yanayin dayake ciki,yaja jikinsa daqyar yaisa inda yake aje magungunanshi ya lalubosu,qara yawansu yayi akan qa’idar yadda akesha,saboda a yanayin da yake ciki baya jin idan yabi qa’idarsu ba zasuyi masa aiki ba.
       Minti biyu yaji kamar baisha komai ba,saiya sake jawo satches din yakuma ballan adadin na dazu yasake sha,cikin gaggawa dason tsaida halin da yake ciki ba tare da yasan silar shan wani abu bane yasa yatsinci kansa a yanayin ba,yadinga ballar maganin cikin fitar hayyaci yana sha har suka danganashi da ficewa daga hayyacinsa gaba daya,bai iya gane waye kusa dashi ko abinda ke faruwa a inda yake ba.
      Tun lokacin da kamal ya fuskanci abu ya kwabe yayi hanzarin tattara laptop dinsa yafice daga falon kada azeez yafito ya taddashi,don haka sanda minal tafito bata taddashi ba,itama bata wannan take ba,don haka bata tsaya nemanshi ba tafice itama tatari taxi tafada sai gida.
       Sai daya bada minti ashirin qwarara yasake dawowa cikin gidan,jin shuru babu alamu ko motsin azeez yasa yanufi dakinsa,sosai ya rikice ganinsa cikin wannan yanayin,ba ranshi suke so ba,sunanshi suke so su bata,darajarshi da matsayinsa kadai sukeso su amsa,cikin rudewa yakira number asibiti mafi kusa dasu,babu bata lokaci suka iso da motar asibiti suka daukeshi.
*****************
        Madaidaicin filine na musamman daga wanu sashe na sasasanta wanda aka qawatashi da abubuwan daukan hankali da more rayuwa iri daban daban saboda hutawar fulani aisha.
      Kamar yawanci lokuta haka yauma,tana kashingide cikin filin saman wani tattausan kilishi wanda aka zagayeshi aka kuma qawatashi da wasu irin manya da qananun filalluka wadanda ke dauke da zane da tambarin gidan sarautar kaisa,daga dama da hagunta kuwa barorinta ne wadanda suke amintattu a wajenta,wanda sukan zauna lokaci lokaci ayi hira sukuma bata labarai dakan debe mata kewa.
       Yauma hakance ta kasance,shugabar zaman wadda koda yaushe baka rabata da labarai a bakinta umma luba ce,murmushi kawai fulani aisha ke fitarwa,da alamu labarin da umma lubar take bata ya qayatar da ita matuqa.
      Daya daga cikin wayoyinta dake aje gabanta suka dauki qara,daya daga cikin barorinta data fi kusa da ita ta miqa hannu ta dauko kana ta rusuna cikin girmamawa tamiqa mata,hannu tasaka ta amsa tana duba mai kiran,abdulrashid ne,dan waziri musa adamu,hakanan tasamu kanta da miqewa tazauna sosai,barorinta suka dau kirari
“Allah ya taimaki uwar yarima,magajin maimartaba qwaya daya tilo” hannu ta daga musu alamun tana buqatar shirunsu,ta kara wayar a kunnenta bayan ta daga.
       “La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” fulani aysha tafada tana miqewa tsaye kamar wadda aka tsirawa allura,take suma dukka sauran barorin suka miqe suka tsaitsaya,donsu tabbatar tunda sukaga haka sun tabbata babu lafiya
“Allah yayi miki jagora yakula da lamarinki” umma luba tafada cikin nuna tsantsar kulawa da damuwa,saita sauke wayar daga kunneta tanajin zafi yana ratsata duk da iskar dake kadawa a wajen,a hankali takoma tana zama a inda tatashi bakinta yana furta
“Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagisu”
“Amin ya Allah…..amin” suka kusan hada baki wajen fadar haka.
       Shuru ya ratsa wajen na wasu mintuna kanta a qasa tana maimaita maganar da abdulrashid ya gaya mata,shudewar wasu mintuna kana ta daga kanta a hankali tace
“Ina laure?….” Da hanzari ta matso tana zubewa a gabanta
“Gani ranki shi dade…”
“Ki gaggauta zuwa ki shaidawa jakadiyar mai martaba,a shaidawa maimartaba,akuma yimin iso inason ganinsa da gaggawa yanxu yanzu”
“An gama ranki ya dade….Allah ya huci zuciyarki” tafada tana miqewa da matuqar hanzari tasauka daga wajen tayi dan nesa kadan tadauki takalmanta tabace daga filin.
      Shurune yaci gaba da wanzuwa a wajen,kowa yashiga cikin nutsuwa da taitayinsa,umma luba ta matso gefanta,cikin salo da dabara tasoma magana cikin kalaman kwantar da hankali da sanya nutsuwa
“Na gode” fulani ta ambata tana dagawa umma luba hannu,da alamu taji dadin furucinta,saidai a yanayin datake ciki bata buqatar dogon xance.
      *_fulani adama_*
      A daidai wannan lokacin daga can cikin quryar dakin gadon wanda babu mai shiga ciki sai ahalinta ko yaran cikinta,a lokacin da take yunqurin amsa kiran koda gittawar tsuntsu bata amincewa barorinta abarshi yawuce ba bare bil’adama.
       Kirane daga qanwar maimartaba mahaifiyar kamal fauziyya mu’az kaisa,qaramin murmushi fulani adama tasaki,tun jiya taje jira taji daga gareta,kuma jikinta yana bata aiki yayi nasara,wanda indai hakan tafaru rabi cikin burinkanta sun soma cika,a duniya babu wadda ta tsare mata gaba da baya irin aisha da dukka abinda suka fito daga tsatsonta,har yaranta mata gani take suna samun soyayya daga wajen maimartaba fiye da nasu yaran
“Ya ake ciki?,ina fatan komai ya kammala” ta tambaya muryarta na nuna tsantsar jin dadi
“Inafa!,komai yana shirin kwabewa,yanzu haka yarima yana kwance gadon asibiti unconsciouse” tsaki taja tana jin sam wannan bai dameta ba,inda zai mutu ma salin alin da tafi kowa farinciki a duniya
“Ba wannan bane ya dameni,an samu nasara?”
“Ta ina fulani?,ya tsallake duk wani tarko” take fuskarta ta sauya,bacin rai ya mamaye zuciyarta,ta yaya?,wannan wanne irin yaro ne,dogon tsaki taja takatse wayar kawai ba tare data iya sake furta komai ba,saita kasa zama,tahau safa da marwa cikin dakin tanason baiwa kanta damar yin tunanin abinda yadace tayi.
      “Allah ya taimakeki,Allah yabaki yawan rai,zaishiga sallar la’asar,idan yafito ki taddashi a sassansa” miqewa tayi ba tare data ce komai ba,tanajin ba zata iya zama a nata sassan ba har zuwa sanda zaiyi sallar yafito.
       Daga nan bata sake tsayawa ba saidata dangana da ainihin bedroom dinta,ta canza shigarta,cikin qaramin lokaci tafito a fulaninta sak,ta wani sashen kuma gimbiya diya ga sarkin mali,a gaggauce tafito tabaro sashen nata zuwa sassan maimartaba qarqashin rakiyar mutum uku rak,suma suna zuwa wani shinge da babu mai shiga sai iyalan nasa suka juya suka koma suka barta.
       Kasa zama tayi cikin tashin hankali take kaiwa tana kawowa,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta qasar mexico,hankalinta a tashe yake qwarai,tana tsoron wani mummunan abun yasamu abdul’azeez din,abdulrashid yaqi mata cikakken bayani bare ta fahimci silar ciwon nashi.
      Tana jin takun shigowar maimartaba tayi hanzarin juyowa tana dubanshi,itama shi take kallo,dukkanin rauninta ya bayyana,har kamar idanunta ma sun tara ruwan hawaye,duk da basu kai ga zubowa ba.
       Yasan meke faruwa,hakanan yasan rauninta,dukkanin rauninta abdul’azeez ne,bata iya jurewa idan wani abu ya sameshi,saita nufeshi da sassarfa kuka yanason qwace mata,ganin haka shima yaqara sauri yatareta,tafada jikinsa saita saki kuka mara sauti,bayanta yake shafawa a hankali cikin sigar lallashi ba tare da yace komai ba,tsawon wasu daqiqu sannan yace
“Duka ina jarumatar dana sanki da ita ayusher?,ummm…” Muryarta can qasa saidai duk da haka zaka fuskanci tana kuka ne tace
“Ina tsoron ko wani keson cutar min dashi ranka yadade,bisa alamu azeez baida lafiya sosai” saiya dagata daga jikinsa yana duban fuskarta gamida girgixa mata kai
“Um um,ko kadan aysha,nace kidaina kawo ire iren wadan nan tunanin a ranki kan abdul’azeez,yanzu dubi fuskarki….sam.hawaye bai dace da fuskar saraki irinki ba” dole yanayin yadda yayi maganar ya sanya murmushi yakubce mata,kai kace ba shine qasaitaccen sarkin nan bane ma’abocin kwarjini da izza,sai tasa tafin hannunta tana share hawayen daya bata mata fuskar,kana yajata saman daya daga cikin kujerun ya zaunar da ita
“Yanzu me kikeso ayi uwar abdul’azeez?”murmushin yasake kubce mata karo na biyu,yasan takanta sosai,saita duqar da kanta tana murmushi ba tare datace komai ba
“Anaso aje wajen yarima azeez aga halin da yake ciki ko?” Ya bata amsar tambayar da kanshi yana dage gira,kaita jijjiga da hanzari harsai da murmushin shima yakubce masa
“Ki shirya gobe ku wuce keda duk wanda kika zaba” hannayensa ta kama cikin murna tariqe qam
“Na gode your royal highness….Allah yaqara girma,yajiqan magabata” cikin lumshe idanu dajin dadin addu’arta yace
“Ameen”
“Sai alfarma daya da nakeso ayimin” tafada tana wasa da hannunshi da har yanzu bata saka ba
“Uhmm,inajinki” shuru tadanyi na wasu sakanni sannan tace
“Inason maganar rashin lafiyan azeez yazama asirtaccen zance Allah ya taimakeka ina neman alfarma” shuru yayi nawasu sakkani yana kallonta murmushi nafita saman fuskarshi ba tare data sani ba saboda idanunta suna qasa,yadade da sanin nata yarda da kowa ba indai akan Abdul’azeez ne
“Wai…dani da abdul’azeez wa akafi sone” da sauri ta daga kai tana ware idanu,dariya nason qwace mata,saiya ci gaba da kallonta yana cewa
“Yes,inaso inji” hannu tasa kamar zata rufe bakinta saita fasa tasoma magana
“Kaine maqyanqyshin abdul’azeez fa,kaga dole taka soyayyar ta dara tashi,albarkacin soyayyarka shi kansa yake ci” murmushi ya fidda,aysha badai iya nunawa miji qauna ba
“Um um….kadda nasaki jiki fa,ki gadi gaskiya anya abun cikin qwai baifi qwan dadi ba” kanta tadora saman kafadarsa tana dariya
“Ko kadan qwan gaba dayanshi yafi dadi” ana tsaka da wannan aka nemi izinin shigowa falon da suke,yasan koma waye wanda yashafi iyalinsa ne don haka yabada izinin shigowar.
       Fulani saratu ce,cikin shiga ta alfarma ita dinma,amma haske aysha saiya dusashe fiye da nata rabin adon,ganin aysha a wajen saita tsuke fuska ta qarasa shigowa da sallama,daga shi har ayshan kowa na mazauninsa daban saboda jin anason shigowa,ya amsa sallamar yana marabtarta kamar yadda yasaba yima matanshi,ta amsa masa amma sam fuskarta babu wani walwala ko fara’a,abu daya ne dataji dadi shine tadda aishan datayi a wajen,hakan yayi mata daidai,zatayi maganganunta son ranta,tunda dama ganawar ta nemi yinta ne saboda yaron aishan
“Magana nazo muyi dakai Allah ya taimakeka”
“Ina saurarenki saratu,Allah yasa lafiya”.
       Gyara zamanta tayi tana sake hade fuskarta,kana a fakaice ta watsawa aisha harara wadda batama san tanayi ba
“A gafarceni ranka yadade,magana ta gaskiya ce nazo na gaya maka,duk da hausawa sunce daci gareta,tuba nake ranka ya dade kan maganar walida ce…” Saita danyi shuru tana maida numfashi,yayin dashi kuma yaci gaba da kallonta dakuma saurarenta ba tare daya ce komai ba
“Da yarana,dana adama dana aisha ina tsammani dukkansu ƴaƴanka ne,hakanan kowanne yana da haqqi akanka,koda wanne irin jinsine,bayan haqqi da suke dashi suna buqatar a daidaita su dayi musu adalci kan komai a cikin gidan nan….zancan tafiyarta makaranta,ranka yadade da farko baka wani tsaurara ba kace zaka yi tunani da shawara,amma tunda abdul’azeez yazo yatafi kace fau fau babu wadda zatabar qasar kaisa da maqotanta tafita a nijeria zuwa baquwar qasa karatu,Allah yabaka yawan rai,caa nake shi wanda aka nema shawarar yabayar a yanzu haka zancan da mukeyi baya qasar nan,sai daya zaba qasar da yakeso sannan yatafi,a irin wannan ranka yadade yaran zasu dinga ganin kamar ba’a musu adalci saboda su yara matane,idan batun jinsine babu jinsin da bazai lalace ba idan yaso,shi kansa akasan me yakeyi a can din……” Da sauri aysha tamiqe jin tazo inda ba zata iya jurewa ba,kuma batason sanya baki cikin maganar ko digo saboda girmamawa gashi maimartaba,don haka tasoma takawa zata fice daidai sanda sarki abdallah ya dagawa saratu hannu yana dakatar da ita,bataji me yake ce mata ba itadai ta sanya kai tayi gaba abinta.
       Tana tafe a hanya tana mamakin abinda ta tsarema matan,ta tabbata banda kariyar Allah,da kaifin wayo da basira da Allah yabata da tuni sun gama batar da ita itada irinta a tarihin masarautar kaisa,tasan tana takatsantsan da bata duk wani shirinsu sun sani ko basu sani ba,amma ko sau daya bata taba yarda ta jefi yaransu da wata mummunar kalma ta batanci ba,tunda tasan duk inda za’aje azo yayyene ga nata yaran,kuma jinin abdallanta ne.
       A ranar tagama tsara komai na tafiyarta,takuma zabi mutanen da zatayi tafiyar  dasu,ta basu umarnin kowa yashirya,don a sassanta duk wanda zasuyi tafiyar zasu kwana,duk da amintattunta ne bata yarda su kwana akowanne guri ba sai a nan,cikin murna da zumudi kowanne yasoma shirinsa a sirrance ba tare da kowa yasan meke faruwa ba bare susan inda za’a din.
      **************
      “Alhamdulillah” bilkisu ta fada tana sauke ajiyar zuciya lokacin data shiga soron gidan nasu,don bata tsammaci zata ita kawo kanta gida ba daga makaranta,duba da irin doguwar tafiya da tazarar dake tsakanin gidan nasu da makarantar saboda azababbiyar yunwar dake sakadar cikinta,wanda rabonta da abinci tun daren jiya wanda shima wanda tasamo ne daga gidan umma luba suna yanyana sukaci ita da qannen nata.
       Sosai ta ware hancinta tashaqi qamshin soyayyar miyar dake tashi har soron gidan nasu,wanda kanaji ko ba’a gaya maka ba ta wadatu da nama,qamshin na shiga har cikin hanjinta taja qafafunta ta shige tsakar gidansu.
       Sauka idanunta sukayi kan varender dake qofar dakin amaryar baban nasu wadda ake kira da jummai,itace zaune kan kujera ‘yar tsuguno,tasha kwalliya da wata atamfa tata koriya shar,fuskar nan tasha jar hoda da jan jambaki wanda ada ake kira da kanta kile,idanun nan badau da kwalli ga jagira data ja layi daya a kan gashin girarta,idan gidan karuwai kashigo saika rantse magajiyar karuwai ce,gabanta rishonta ne tanata juya miyar data budade hancin kowa dake cikin gidan.
      Dagakai tayi tana duban bilkisu ba tare data amsa sallamar da takeyi ba,zata iya cewa tun zuwanta gidan babu wani abu qwaqwqwara daya taba hadata da ita,tundai ita bilkisun ba mazauniyar gida bace,koda ace mazauniyar ce sam bata da kwarafniya,saika wuni a gidan bakaji muryarta ba,koda kajinma to fada takewa qannenta kan wani abu da sukayi wanda ba dai dai ba,saika taka mata ka zubar mata bata daga kai ta kalleka ba bare ta nuna damuwarta,duk da ta tsani raini da wulaqanci abu biyu da ba kasafai take iya juresu ba,hakan yasa takan qauracewa sabgar jama’a ainun sai idan ta kama.
       Sai data leqa rumfar umma katti tashaida mata ta dawo yadda tasaba,duk da cewa ba wani magana mai dadi take gaya mata ba,wani lokacima takan hantareta ne kota jefeta da baqar magana
“Ke da’alla can,naji kin dawo saime?,wata uwar kike tsinanamin da zaki damweni dakin dawo?,’yar wahala wadda kullum take qarewa a gantalin neman boko,bokon da nake da yaqinin bazai tsinana miki komai ba,idan kinso in kika tafi makarantar karki dawo,amiki daki acan,ina nan ina fama da baqincikin ubanku daci dakai da tufatar dakai amma kin dameni da wani umma nadawo,mtseeww” haka take balbaleta da masifa dakuma mita duk sanda ‘yan wulaqancin ke kusa,ko kuma wani abu ya hadosu da babansu,itakam takan cika da mamaki a kullu yaumin,yau koda ace umma kattin bata zauna da mahaifiyarta sunsan juna ba bai kyautu tadinga mata haka ba,ta tsammaci yadda suka zauna da mahaifiyarta takuma yi haquri da ita itadin me riqeta ce?,bata mantawa sanda mahaifiyarta keda rai,yaran babansu da iyayensu suka fita suka barsu sun kusa biyar a sannan,mamanta itake musu komai cikin kudin da ake aiko mata daga gidansu,yadda take kula da bilkisu haka take kula dasu,bata barsu sunyi kukan rashin komai ba harsai data koma ga mahaliccinta,shi yasa har yanzu duk da basa zaune qarqashin mahaifinsu duk wanda Allah yakawo gidan zai mata alkhairi komai qanqantarsa,saboda tunawa da abinda mahaifiyarta maimunatu tayi musu.
      Babu wanda yatankawa wani tsakaninta da lami bayab sallamar datayi har bilkisun tawuce dakinsu,dakin babu kowa yadda ta tsammata sun wuce islamiyya,ta soma rarraba idanu tanason taga me sukaci,data daga kwanukansu saitaga burbushin garin kwaki,aje kwanukan tayi tasaki ajiyar zuciya,duk da tasan shita bar musu tayi tunanin basuci ba sun aje mata,tunda idan suka fuskanci bataci abinci ba saisuqi ci su aje mata su su haqura.
       Tana fidda kayan makarantar tana tunanin kudin extra lesson da za’a soma yi musu saboda shirye shiryen zana jarabawar waec da neco,komai da zata buqata an riga da an biya amma babu kudin extra lesson,wanda tasan cewa anty zuhriyya batasan zai taso ba,da babu shakka saita bayar,wasu qwalla masu dumi suka taru a idanunta,wanda bata iya dannesu kulli yaumin idan tatuna da qanwar mahaifiyartata wadda ita ta maye mata gurbin mahaifiya,kullum tatashi daga shimfidarta da safe tana tashi ne da begenta,haka nan tana kwanciya ne da tsananin kewarta da burin ganin shekarun sun cika ta dawo zuwa gareta.
       Hakanan jiki a sanyaye ta daura zani tafita ta watsa ruwa,tadawo ta shirya duk da yadda yunwa ke sassaqarta,amma dole taje gidan aikinta.
Har zata fice taga alamun baban nata yana dakin amaryartashi,wanda dama yawancin lokuta anan yake wuni abinsa akwance,sai yamma zuwa dare zai fita nemo mata na cefanen gobe,don sudin tamkar masu haya a gidan suke,wadanda babu wani haqqinsu dake rataye saman wuyanshi,bai damu da cinsu shansu suturarsu ko lafiyarsu ba,yabasu muhallin zama ne kawai,wanda shima yakan yanka lokaci zuwa lokaci duk sanda yatashi wani zarafi na aurensa.
       Shawartarta zuciyarta tayi,yaudau karon farko a rayuwarta,lokaci na farko tunda tayi wayo tsakaninta da mahaifinta,ta waiwaya ta duqa gabanshi ta roqeshi ya mata wata hidima qwaya daya cikin rayuwarta mana,takai minti goma tana shawara da zuciyarta daga qarshe tayi qundun bala takoma tataka zuwa varender da tunda aka ginata bata taba koda gogar gininta bare akai ga takawa.
       Bakin qofar dakin ta tsaya tayi sallama a nutse,yana daga ciki tajishi yana amsawa
“Waye ne?,waye a nan?” Yasake fada
“Bilkisu ce” ta amsa a sanyaye,tanajin alamun tashinsa daga kwanciya da alama akwance yake
“Mai gado,shigo mana,yaukin gama baqin ran naki kenan zaki shigo kiga dakin uwartaki” yafada yana kakkabe shimfidarsa,batabi ta wannan ba tacire takalmanta dasukayi qasa sosai saboda dadewa dakuma tafiya tasanya kai falon.
      Yana zaune saman kujerar da aka qarawa laushi da bargo,yayin da lami ke zaune gefansa tana kallon bilkisun harta shigo,kai tsaye ta isa gabanshi ta duqa tana gaidashi ya amsa yana jiran jin me zatace,cikin sanyinta da nutsuwarta tace
“Baba….zuwa nayi na roqi alfarma wajenka,karatunmu yazo gangara,zamu zana jarrabobi guda biyu,to kowacce tana da muhimmanci wajen dalibi,hakan yasanya aka ware mana lokaci daban wanda za’a dinga mana wani karatun bayan wanda muke a marantar,to akwai kudi da kowanne dalibi zai bada saboda malamai zasu dauko qwararru wadanda zasu dinga mana wannan karatun,za’a dinga biyansu ne….” Saita tsagaita tana tunanin qarasa gaya mishin,zamansa yagyara yana washe baki
“To yanzu cewa akayi nazo za’a daukeni kenan nima a dinga biyana?” Da mamaki ta daga kai ta dubeshi,amma saita sadda kai tana girgiza kai
“A’ah,cikin kudaden da anty zuhriyya tabiya babu kudin wannan,shine nace don Allah ko zaka taimaka ka biyamin”.
      Tsaf ya hade girarsa yana dubanta
“Kai,amma maigado bansan baki imani ba saiyau,yanzu don Allah keda kike fita aiki kullum yaumin nida kowa yasan kasuwanci yanzu ya durqushe sai lahaula wala qawwata illa billah nizaki duba kice nabaki wasu kudade?,yo aini da kikayi sallama na zaci anmiki albashi kika dubi halin da nake ciki kikazo kibani wani abu a ciki nima,gaskiya maigado kin bani mamaki,hankalinki ashe a qauri yake….to bari na gaya miki zance na gaskiya,ni yanzu bana maganin kome,kinganta nan lami baiwar Allah couse couse takeson ci amma haka na bata haquri shinkafa take dafawa yanzu….shawarar dazan baki idan kin samu ki biya,idan bakisamu ba ki tattara ki haqura da karatun,dama ni ya isheni” tabe baki lami tayi tana dora qafarta daya kan daya
“Uhmmm….ni bilya ma baikenka nagani,kana da zuqeqiyar yarinya kamar wannan amma ka sakata a gaba kanata ciyar da ita babu gaira babu dalili,tun farko aida kudin makarantar ka karba kayi mata kayan daki kasamu wani mai damshi damshin ka aurawa,qila da tuni yanzu yanzu ya biya maka hajji ana kiranka da alhaji” yatsanshi ya ciza yana kada kai
“Kumafa wallahi kin kawo shawara lami,dadina dake hankali,kinga waccar dosoruwar bata taba bani irin wannan shawarar ba wallahi,to amma yanzu ai tunda takusa gamawa kudin da sukayi sauran basu taka kara sun karya ba….”.
      Miqewa kawai bilkisu tayi ba tare data tsaya ta qarasa jin cecekucen dasuke ba,ta sanya takalmanta tafice daga gidan tanajin iska na yawo da ita.
      Tana tafe a hanya amma sam hankalinta baya tattare da abunda ke gudana kan hanyar,tayi matuqar nisa a duniyar tunani,wani irin quntata zuciyarta tayi,tanajin hucin hakan har saman fuskarta,kukan zuci take mai ciwo,wanda yafi na fili radadi da yankar zuciya,tana jajantawa yara da yawa cikin fadin duniya masu mahaifi irin nata,tayi amanna marayu da yawa sun fisu gata,marayu da yawa sun fisu daraja da kima,ya ilahi mahaifinsu meya hau kanshi haka?,Allah yayi masa daraja da baiwar ‘ya’ya amma shi baisan da hakan ba,meye marabarsa da matacce?,wanne abu zasu iya adarwa kan gata da wani abu mai muhimmanci da uba ya yiwa ‘ya’yansa,dame zasuyi tutiya?,da ire iren wadan nan tunanukan ta qarasa gidan umma luba.
      Taje ta sameta a hargitse da tulin hirarta,bakinta har kunne yau Allah ya yarda zata daga daga qasar nijeria masarautar kaisa zuwa mazako,duk da yanayin da take ciki hakan bai hana murmushi subucewa daga fuskar bilkisun ba,na yadda tafadi sunan qasar,dakuma yadda taketa lodar kaya kamar zata ta shekara a can
“Mexico ake cewa umma….sannan wadan na kayan da kika diba ai sunyi yawa,idan zaka wata qasar ba kaya kake loda ba,idan sati biyu zakuyi kala bakwai ma ya isheki” baki tasaki tana kallon bilkisu
“Ke ‘yar nan,tafiya cefa ta alfarma,ga qafata ga qafar fulani fa,a qalla muyi sati biyu ko uku” murmushi takuma yi
“Duk da haka umma”
“To yo ai gwara da kikazo,don ni niyyata iya adadin kwanakin zan diba harda qari ma,matso ki zabarmin” tafada tana bata waje.
       Anutse ta shirya mata komai,hakan kuma yayi mata dadi har tace
“Bude store dina ki daukar muku taliya goma,macaroni goma,shinkafa kwano biyu,samambita yakusa qarewa dauke ragowar kwa dafa kuci keda qannenki” sosai hakan yayiwa bilkisu dadi,tasan da yardar Allah bazasu galabaita ba sosai.
☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️
*_MEXICO CITY_*
      Tsaye takan gaba gadon da aka kwantar dashi,hannayenta saman kanshi idanunta qur akan fuskarsa,kana ganinsa kasan cewa lallai da gaske bashi da lafiya sosai,har cikin zuciyarta takejin ciwon nashi tamkar ita dince babu lafiya,sakin ajiyar zuciya tayi tana sauke hannun nata daga saman kanshi kana ta juya a hankali tafice daga dakin zuwa office din likitan don suyi magana,tana son jin cikakken bayanin abinda yake damun azeez din.
         Dukka hankalinta yana kan likitan lokacin dayake rubuce rubuce jikin file din azeez,harya gama kana ya daga kai cikin harshen mutanen qasar mexico yasoma mata magana,saita sauya harshe zuwa turanci
“Am sorry” ya fada yana murmushi,don shaf ya mance da cewa ba ‘yar qasar bace,saiya koma mata bayani zuwa yaren englishi
“A yanayin halittar yaronki a bincinkenmu mutum ne mai matuqar buqata,wanda baya biyan buqatarsa takowacce hanya dazai rage yawan ruwan halittar dake taruwar mishi,a maimakon hakan saiyake amfani da wasu qwayoyi da zasu gusar masa da dukkan wata sha’awa da zata taso mishi,wanda sannu a hankali suka zame mishi jiki suka bi jikinsa,har aka kai matakin da basa iya mishi aiki sosai a jikinsa,saiya koma yin allurar da ake ta jijiya,wadda tafi qwayoyin saurin isa inda akeso…..to,bayan hakan gaba daya,bamu sani ba tunda bama tare dashi,amma a shekaran jiya an kawoshi ranga ranga,mun karbeshi mun kuma bashi taimakon gaggawa,wanda daga qarshe bincikenmu ya tabbatar mana da cewa yasha maganin ne daya wuce qa’ida,wanda har hakan yanaso ya masa illar,illar da idan ba aure yayi ba to komai zai iya faruwa dashi”.
       Shuru yayi yana maida numfashi,cak tunanin fulani aysha ya tsaya,don ko kusa ko alama bata taba kawowa kanta wannan ba cikin jerin abubuwan daka iya zama sila ko sanadi na ciwon azeez din ba,mganar likita tasake katse mata tunaninta
“Saboda an kai matakin da magungunan sun daina aiki a jikinsa,banda ma yana da qarfin jini da tuni sun kashe masa sha’awarsa gaba daya,a yanzu kuwa idan yaci gaba da shansu komai yana faruwa dashi” saita lumshe idanunta tana jin maganganun likita na sauka ɗai ɗai cikin kwanyarta
“Godiya muke likita” ta fada a taqaice tana miqewa a nutse tabar office din.
       Duk da sunyi waya maimartaba amma bata shaida masa asalin ciwon dake damun azeez din ba,kamar yadda take da yaqinin daga ita sai abdulrashid suke da masaniyar haqiqanin abinda yake damunsa da abinda yayi silar shigarsa cikin ciwon,ta fannin abdulrashid sam baiyi mamaki ba,duk da cewa ba qasa daya suke karatu ba amma yasan azeez din na yawan ta’ammali da magungunan duk sanda lamura suka ci tura,don yana yawaita zuwa wajensa akai akai musamman qarshen mako,kamar yadda shima azeez din yakan ziyarceshi duk lokacin daya bushi iska.
       Duk da cewa su abdulrashid din suna tsaye a kanshi amma kasa tafiya tayi masauki anan dakin da aka kwantar da azeez din ta kwana,duk motsi ko wani juyi da zatayi idanunta na kanshi tana tunanin mafitar daya kamata ta sama mishi mafi sauqi kuma cikin sirri.
      Cikin dare yafarka sau daya,suka hada idanu yasaki murmushi,yana tason ya mata magana bacci yasake rinjayarsa,bai sake farkawa bai sai washegari da asuba.
       Sati guda cif ya kwashe cikin yanayi na jiyya kafin yasoma watstsakewa,a kwana na goma kuma ya watstsake sarai,har zuwa sannan bata nuna mishi tasan komai game da ciwon nashi ba,hakanan basuyi magana dashi ba,saima ticket data siya musu na tafiya qasar mali,wanda ta diba musu zasuje suyi sati biyu a can,badon komai tayi wannan tunanin ba,tayi hakanne don zuwa ta shawarta da makusanciyarta abokiyar shawararta kan lamarin azeez din,don batason ta koma kaisa ba tare da wata qwaqwqwarar mafita ba da zata zama maslaha ga rayuwarshi.
        A sannan saida ya kwana uku kamal yaje dubashi,da sunan cewa baya garin da suke makaranta sun turashi wani bincike kan course din da yake a wani gari daban,tunda yashigo azeez din ya kafeshi da ido,hakanan yaji ya dora alamun tambaya a kanshi,duk da cewa bai dora dukkanin zarginsa da zato akan kamal din ba,amma haka kawai yanayin daya nuna yakejin bai masa ba.
*****************
       Karfe goma da rabine na safiyar ranar talata,cikin falon alfarma dake babban sashe da aka tanadarwa fulani aisha cikin masarautar qasar malin wadda take qarqashin sarauta da jagorancin mahaifinta.
       Duk da cewa tayi rashi na uwa amma hakan sai bai sauya komai game da gata dakuma qimarta cikin gidan na,matan uban suna mata kallo ne irin wanda sukewa ‘ya’yansu.
       Su biyune tak cikin falon,tunda sukazo anan tasauka ita da azeez din,saidai akwai tazara sosai tsakanin dakinshi da nata,yayin da ‘yan rakiyarta suma suke wani sashe na musamman maicin gashin kanshi.
        A gaban fulani saratun yake zaune saman lallausan carfet da yayiwa falon qawanya,yana sanye da wando wanda yawuce qaurinsa da kadan bai kuma kai har can qasa ba,farine tas sai rigar jikinsa wadda ta kasance ruwan toka me haske.
      Farfesun kayan ciki yake sha a hankali da cokali,kana dubanshi kasan yasamu lafiya dakuma cikakken nutsuwa,yayin da fulani aysha ke jefa yankkiyar kankana a bakinta duk da cewa safiya ce.
        Duk wani motsinsa yana kan idanunta har zuwa sanda tagama shan tata kankanar ta aje cokalin da farantin,tazauna sosai cikin wani salo dake karantar damai kallo tsantsar izza da isar mulki dake yawo a jininta.
      Tafin hannayenta ta hade waje guda kamar yadda tashigar da yatsunta cikin na juna, anutse ta furta
“Me yasa ka yanke shan qwayoyin da zasu iya kassara maka rayuwarka ta d’a namiji har abada azeez?” A bazata tambayar tazo masa,don bai taba tsammanin maganar ta isa kunnenta ba,da yaji shuru yayi zaton likitan ya saya komai ne,saboda haka saiya nemi ya qware da da romon farfesun,har sai daya aje bowl din hannunshi,ya nemi ruwa ya kwankwada sarai sannan yaji dama dama,ya aje gorar ruwan yana maida numfashi,gami da tattaro irin amsar da zai bata saman harshensa.
      Ya daga idanunsa a hankali ya motsa bakinsa da zummar yin magana
“Dakata….bana buqatar kalaman kariya daga bakinka,ka kasa jurewa azeez,ka gaza ka daure ka isa ga matakin da nakeso ka isa a duniya…..,ba yadda zanyi dakai,nawa shine inyi iya abinda zan iya,sauran naka ne,tunda rayuwarka ne,dole saida gudunmawarka komai zai gudana yakuma tafi dai dai yadda ni da nake gefe na tsara maka” bashi data cewa sam,tunda komai yariga ya bayyanar mata,sai yayi shuru yana saurarenta kawai,idanunsa saman kofunan da suka yi amfani dasu yanzu.
      “A matsayin da kake kai yanzu,dole ne a matsayina na uwa na sama maka mafita ta dukkan hanyar da zata kasance mafitar ce a wajenka…..” Sai tayi shuru da alama magana mai muhimmanci zata fada,yayin da abdul’azeez yayi shuru yanajin wani sanyi yana ratsashi tun daga saman kanshi zuwa qafafunsa,wani nauyi na raguwa daga qirjinsa,fata sa kawai shine kunnuwansa su jiye masa kalaman amincewar ammi na yarjewarta kan yaje yayi aure
“Zakayi aure abdul’azeez” shuru tasake tana qara tariyo dukkan abinda suka tattauna da shawarar data bata cikin daren jiya,wanda taji ta gamsu da shawarar dari bisa dari,wata qaqqarfar ajiyar zuciya yasauke,wani munafukin qaramin murmushi nasan ratsowa ta saman miskilar fuskarsa ya bayyana kansa,saidai ya hana hakan faruwa,sai taci gaba da cewa
“Zakayi aure amma ba irin auren dana tanadar maka ba,zakayi aure amma AUREN KASHE GOBARA”.
        Da sauri yabude idanunsa fes kan ammin don bai fahimci abinda take fada ba,sam bai fahimci hausarta ta qarshe ba,yaci gaba da kallonta kamar yadda itama take kallonshi,tasan cewa yashiga duhu ne kuma yake da buqatar qarin bayani,tasan kuma dama zai buqaci hakan.
      Sake gyara zamanta tayi tana sakin ajiyar zuciya,itama idanunta a kanshi tace
“Zakayi aure abdul’azeez kamar yadda buqatar hakan tataso,saidai ba safwa zaka aura ba a halin yanzu ba” kadan fuskarsa tasauya saboda ta sake jefashi cikin duhune,maimakon yafita zuwa haske saiya sake shigewa cikin duhun
“Eh,a yanzun zan aura maka yarinyar da xaka zauna da itane iya tsahon adadin zaman rayuwar karatunka harka kammala,sannan daga bisani zaka auri safwa a lokacin da muka tsara ni da mahaifiyarta,irin auren da nake buqata,irin auren da mukayi tanadi dakuma buri,ina fatan ka fahimci abinda nake nufi?”.
      Gaba daya sai komai yazo mishi a baibai,dukka bayananta suka cunkushe mishi waje daya,kamar ya fahimta abinda take fada wani sashe kuma sai yakejin kamar bai fahimta ba,ya hadiye yawun bakinsa da qyar yana duban ammin,yamotsa bakinsa zaiyi magana ta daga mishi hannu tana miqewa
“Ba shawararka nake nema ba,wannan shine kawai mafita azeez,no way face mubi wannan,so kawai abinda yarage shine kajira,zan shiga ciki wajen maimartaba…” Daga haka tasoma takawa tafice daga falon.
       Wani zazzafar iska yafitar daga bakinsa ya nutsa dukka yatsunsa cikin sumar kanshi yana yamutsawa,kanshi na wani irin yamutsawa.
       Me yake shirin faruwa ne?,saiya miqe ya koma saman kujera yakwantar da bayansa sosai a makarar kujerar yana ci gaba da barin idanunshi a rufe,sarrafa maganganun ammi yake yadda zasuyi daidai da qwaqwalwarsa da kuma tunaninsa
“Auren kwangila?,ko auren yarjejeniya?,ko kuma me?” Yadinga maimaita tambayar kansa shi daya cikin makeken falon.
      Kusan ranar wuni yayi shi kadai a sashen da aka saukeshi yana son daidaita tunaninsa da maganar,yanason aunata kan ma’auni da mizanin dacewar hakan ko rashin dacewar hakan,dukkan wasu ‘yan uwa dakeson ganinsa dayi masa sannu babu wanda ya baiwa damar ganinsa,ya zabi zaman shi kadai wuni guda sur.
       Sai daga bisani ys tabbatar da cewa yana buqatar abokin shawara,waye a ciki?,sufyan ko abdulrashid?,daga qarshe yaji zuciyarsa tafi amincewa da kiran abdulrashid din,shi tuni yakoma kwana biyu da zuwansu mali.
        A iyakacin abincin da aka jera masa babu abinda ya iya sha sai tattacen gamayyar ruwan kayan marmari,bayan sallar isha’i yasamu yakira abdulrashid din.
     Cikin nutsuwa da aminci ya fayyace masa duk abinda ake ciki,bayan shuru na wasu ‘yan mintina kana yace
“Abdul’azeez,a rashin uwa akanyi uwar daki,babu wata hanya ko mafita data rage banda ka karbi wannan tsarin,tunda kana da yaqinin cewa matuqar akaci gaba da tafiya kan wannan tafarkin komai zai iya faruwa,ina ganin kawai ka bada dama shine”
“Amma….abdulrashid,mai martaba fa baisani ba bazai kuma sani ba a tsari na ammi” shuru yasake yi yana jinjina kai
“Matuqar yasani din kaima kasan dukka hakan ba zata taba faruwa da amincewarsa ba” shuuru kowannensu yasake yi kana daga bisani yayiwa abdulrashid din sallama saboda har yanzu yana da buqatar kadaici har zuwa yanzu.
***************
      Ko cikin gidan kebantaccen wajene da babu wanda ke shigarsa sai an lamunce maka.
         Fulani aysha ce zaune saman daya daga cikin kujerun dake wajen,hannunta riqe da wayarta,da alamu magana take mai matuqar muhimmanci,don ta bada dukkan hankalinta ga wayar.
      Bayan tagama sauraran dukkanin bayanin aminiyartata saita sauke ajiyar zuciya
“Amma inda nake ganin matsalar take saudat…..inda zan samu yarinyar da zata dace da ra’ayin azeez,kinfi kowa sanin halayyar yaronki,donko safwa ma ke zaki bawa wani labarin yadda aka qarke,inason komai yazama cikin sirri,inason yazama tamkar auren sirri tun daga qullashi har zuwa sanda zai qare,kin sani sarai muna tsakiyar magauta da abokan adawa,kowanne yazuba idanu yana son ganin bullar wani abu da zai riqa wajen bata rayuwa da duk wani ci gaba da daukakarmu”.
       Shuru hajiya saudat tayi tana dan tunani kana ta amsa
“Haka zancenki yake,saidai ni a anawa ganin samun yarinyar bazai zama wani abu mai wahala ba,ta fanni daya ne za’a samu yarinyar da komai zai tafi mana dai dai,ba tare da an samu wata matsala ba,ko daga baya aje ana jeka ka dawo,za’ayi mai gaba daya ne,kuma komai bisa yarjejeniya da amincewar iyayen kansu da ita yarinyar…” Sai tayi shuru tana sauraren fulani aisha,wadda dukka ta qagu taji ya abun yake
“Ke nake saurare saudat,idan na fahimceki kamar kinason kice da farko dole yarinyar tazama diyar masu qaramin qarfi kenan marasa hali?” Kai ta gyada kamar tana kallonta
“Tabbas haka nake nufi”
“To amma ta ina zamu samu kenan?”
“Kina da amintattu aisha,wadanda suke kusa kuma suke rayuwa tare da talakawan qasar kaisa,a nawa tunanin….a cikinsu idan kika basu asirtacciyar cigiya to ba shakka za’a dace” murmushi ne ya kufcewa fulani aisha jin duk wani qulli ya kwance,har farincikin hakan ya bayyana saman fuskarta
“Qwarai qwarai aminiyata,wannan tsarin yayi,hakan kuma za’a zartar…..zan kiraki”
“Ohk….sai munyi waya”
“Ma sha Allah” ta fada tana sauke wayar daga kunnenta murmushi na shimfide saman fuskarta.
      Tabbas idan tabi wannan tsarin komai zaiyi dai dai,hakanan komai zai tafi yadda ya kamata,saita miqe tana takawa cikin wajen a hankali tana sake zurfafa tunaninta kan yadda zata tsara komai bisa basira da fikra gamida kaucewa idanun ‘yan adawa,yayin da wani sashe na qwaqwalwarta yasoma lissafo mata mutanen da zata tuntuba cikin amintattun nata wanda tasan ba zata samu matsala ba haihata haihata…….
_tofa masu karatu,ba’a fara wasan ba,muje zuwa_.
****************
       Satinsu uku a mali azeez yakoma bakin karatunshi,yayin da fulani ayshan itama ta tattara tadawo nigeria.
        Sai data huta sosai sa’annan ta buqaci ganawa da barorin nata,cikin matuqar sirri da takatsantsan,mutum uku ta kira a cikinsu harda umma luba,da zummar idan bata samu yadda takeso ba saita sake kebe wasu ukun ta sanyasu cigiyar da neman.
       A nutse tayi musu cikakken bayani dazai gamsar dasu,bisa sharudda da dokokin irin yarinyar da take da buqatar a sama mata,shuru sukayi kowanne cike da fata da burin cewa asamu dacewa ta bangarensa,domin tabbas indai hakan ta tabbata ta bangaren mutum sun sani cewa kakarshi ta yanke saqa,basu bar wajen ba saida kowacce ta tabbatar wa da fulani aisha cewa zatayi iyakar qoqarinta wajen samo yarinyar data dace.
****************
      Tunda fulani aishan tayi maganar umma luba tashiga dogon tunani da nazarin wadda zata kaiwa fulanin,zataso ace cikin jininta zata samo mata yarinyar,saboda romon domokaradiyyar da take da yaqinin yarinyar ita da danginta zasu kwankwada,bugu da qari ba qaramar daraja bace wajen mace auren yarima azeez koda kuwa cikin mafarki ne,koda cikin sirri ne kamar yadda xai faru a yanzu,ba shakka madaukakiyar daraja ce cikin kundin tarihin rayuwar diya mace hada auratayya da jinin gidan sarautar KAISA koda kuwa hada jinin na minti daya ne.
        Washegari ba zata shiga gidan maimartaba ba,don fulani ta basu hutu na sati guda,kowacce taje tayi bincike takuma zo mata da labari mai dadi kafin zagayowar satin.
        Tana zaune a faffadan tsakar gidanta tana ninke kayanta da jiya bilkisu ta wanke mata su tas,kamar yadda yake yanzu bata da matsalar mai wanki,saboda bilkisun duka ta hada harda wankin nata saboda kudin aikinta ya qara auki.
      Sallamar bilkisun ita ta sanya daga kai tana duban qofar gamida amsa mata,fuskarta a washe kamar koda yaushe tana fadin
“Me gado,yana ganki haka dawuri” dan qaramin murmushinta tasaki tana isa gefan tabarmar umma uwalen tadan dosana,duk da sun debi shekara kusan uku tare amma kullum bilkisun kamar baquwa take a gidan,kasancewarta mutum bamai saurin sabo ba,umma luban tayi mitar tayi qorafi kan tadinga sakewa amma har yanzu jiya iyau.
      “Yana ganki tun lokaci bai qarasa ba?” Tasake tambayarta
“Yau banje makaranta bane”
“Aiho,to,koda naji” saita miqe cikin qarfin hali tana qoqarin kama aikinta,duk da cewa sam yaudin bata jin dadin jikinta,kusan shine ma silar data sanya bataje makarantar ba yau,amma tadaure tazo aikin saboda batason tayiwa albashinta gibi,umma luba akwai kirki idan taso,amma fa tana da qaunar dukiyarta.
        Jifa jifa tana ninkin tana duban bilkisun,yau shurun nata sai taga yasake yawa,amma tasan koda ta tambayeta ba gaya mata komai zatayi ba,mutum ce ita wadda bata iya bude baki ta fadi matsalarta ba,duk da tana tsammanin koma meye baya rasa matsala da yanayin da suke ciki a gidansu ba,tunda kusan umma luban tasan komai,duk da bilkisun bata taba bude bakinta ta gaya mata ba,kasancewar umma luban mutum ce mai dan shige shige da kuma jama’a yasa tasan komai.
        Tana zaune dai a wajen tana karantar bikisun,gabanta yafadi sanda bilkisun ke rataye hijabinta saman igiyar shanyar dake tsakar gidan da niyyar daura alwala,gashinta mai tsaho santsi da sulbi ya bayyana tun daga gaban goshinta zuwa gadon bayanta,kamar tasan tana kallonta tayi hanzarin janyo dankwalinta mai santsi dake niyyar zamewa ta sake daureshi saman kanta,hakanan umma luban tasamu kanta da qarewa halittar bilkisun kallo.
       “Tabbas wannan duk inda ake neman mace tacika mace,kuma koda fulani aisha nakaiwa ita na tabbatar zatayi mata dari bisa dari,banda rama dake jikinta ma da Allah ne yasan yadda za’a ga cikarta,wannan tayi kuma nasan zataja hankalin yarima azeez” haka umma luban tasamu kanta da nazartar yanayi halitta dakuma halayyar bilkisun harta kammala dukka ayyukanta tayimata sallama zata wuce,saita diba kusan rabin abincin data dafa tace tatafi dashi suci ita da qannenta,bataqi ba,don bata da tabbaci ko yaqinin abinda zasuci idan takoma,don hatta da amaryar gidan mai qyallin goshi yau sai da suka haura da baban nasu,da alama hantsi yasoma duban ludayi,sa’annan zani yasoma sanin mazaunai,saura kadan itama bisa dukkan alamu tabi sahu ,hannu bibbiyu ta saka ta amsa tayi mata godiya kana tawuce.
         Tana jin hamza yana kiranta amma taqi ta tsaya,bakinta cike da addu’ar kada Allah yasa ta cimma babanta bare yaji aiken da zai jero ya tilasta mata tafita ta saurareshi ba,don a yadda take jin kanta din nan a yanzun kwanciya kawai buqata ko abincin bai gabanta.
       Tana basu flask din kuwa tamaida haqarqarinta ta kwanta,duka sai yaran suka damu suka dinga tambayarta abinda ke damunta,cikin qarfin hali tayi musu dabara tace gajiya tayi,suci abinci maza suma su kwanta.
       Ranar kusan kwana umma luba tayi tana auna dukkan matakai da sharuddan amsar macen da zasu kawo da fulani aysha ta gindaya musu da yanayin halin rayuwar da bilkisu take ciki,duk ta inda ta auna sai taga bilkisun tahau ma’aunin,cif da cif,bataga gibi tako ina ba,can qarshen dare daga qarshe ta yanke shawarar fara tunkarar bilkisun da maganar,don harkar zatafi kyau ace yarinyar tasan komai,kuma tayi amannar babu yarinyar da za’ayi wannan tayin tana cikin halin rayuwa irin na bilkisun da zataqi amsar wannan gwaggwaban tayin.
☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️
Duk yadda taso tayiwa bilkisun maganar amma dole ta haqura har tsawon kwana biyu,saboda ciwon dai saida yasanya bilkisun takwana biyun bata fita,duk qaunarta da aikinta dakuma makaranta amma dole haka ta haqura,sai qannenta ta turawa umma luban suka shaida mata bata da lafiya. A wakankin kuwa taji jiki sosai,rama tayi qwarai. Umma luban tayi amfani da wannan damar ta dinga aiko mata da dafaffen abinci mai yawa wanda tasan zai ishesu ita da qannenta.
       Sosai hakan yayiwa bilkisun dadi,yakuma rage mata radadin ciwon,koba komai tana samun salama cikin ranta idan ta daga idanu taga qannenta suna da abincin da zasuci.
       A kwana na uku ta sake qwarara jikinta don zuwa taci gaba da aikinta,don tana lissafe da kwanakin da bataje na,hakanan ta shirya tafito,tasamu babanta a tsakar gida ta gaidashi tawuce. Ajiyar zuciya tasaki,tsawon kwanakin bata samu arziqin paracetamol ko na naira biyar ba daga wajen mahaifinta,hasalima ciwo kanshi baisan tanayi ba,wannan kuwa bawai wani baqon abu bane a wajenta,kusan haka tasu rayuwar take.
       “A’ah,mai gado,kin warke ne da kika iya fitowa?” Umma luba ta fada cikin nuna tsantsar kulawa,duk da babu wata matsala data taba ratsa tsakaninta da umma luban saboda tsantseninta da kiyayewarta da takeyi amma tayi mamakin yadda yau kulawar ta ninka ta baya tazama ta musamman
“Eh,naji qarfin jikina ne shi yasa nafito”
“Ai da kin bari kin sake jin dama dama”
“Babu komai umma”
“Allah to ya qara sauqi ya qara lafiya”
“Amin amin”
“Amma dai kinje asibiti ne ko?” Murmushi kawai tayi mata ba tare data amsa ta ba,hakan ya baiwa umma luban amsarta,saita kama haba tana dubanta
“Kai,maigado Allah ya fidda ku cikin wannan halin rayuwar,Allah ya kawo miki agaji ya dandasheki da miji da zai zama silar fitarki daga quncin da kike ciki keda ‘yan uwanki,ki huta suma su huta…kiyi aikin daidai gwargwado yadda zaki iya kinji,Allah yabaki lafiya,ke abar tausayi ce bilkisu” ta qarashe fada cikin nuna jajjabi. Ita kanta bilkisun taji maganganun har tsakiyar zuciyarta,taji zuciyarta ta karye sosai har hawaye yana shirin zubo mata,ta danne zuciyarta ta soma aikinta a hankali kuma a nutse yadda ba zata jigata ba.
       Kamar kowanne lokaci duk sanda tagama aikinta gida take tafiya koda qarfe nawa ne,ta qaraso tasamu umma luban cikin falonta tana zaune ta qurqurar tv dinta a gaba tana kallo,a zahiri kallo take amma a badani tana tsara yadda zata tunkari bilkisu da maganar ne,harta fahimta takuma amince.
      “Au….kin gama kenan?,aida kin tsaya,albashinki nakeson biyanki,kuma inaso muyi magana dake” tafada tana miqewa daga kwanciyar datake,ta janyo jakarta wadda bata rabo da ita a qugunta tazuge,tamkar an yiwa bikisun rahama haka taji,don sam bata tsammaci samun albashinta a yanzu ba,idan tasamu ma to nan sa kwanaki bakwai ko goma masu zuwa ne a lissafinta.
       Kudade ta lissafo ta miqa mata,saidai tun kafin takai ga karba tasan cewa kudin kamar sunfi adadin albashinta,karba tayi ta cire kudinta kana ta miqawa umma luba sauran
“Kudin sun haura,na dauki nawa” kai ta girgixa
“Babu komai bilkisu,ki riqe duka” juya kudin tayi fuskarta cike fal da mamaki,a qalla kudin sun doshi dubu goma harda albashinta,mamakinta ya kasa boyuwa,ta daga idanu tana duban umma luban,sai tayi mata murmushi kana ta gyara zama
“Wannan ba komai bane maigado,nan gaba kadan wala’alla ke zaki dinga kyautar kamarsu koma sama dasu,wataqil nan da wani dan lokaci kadan ire iren wadan nan kudaden canji ne a wajenki ba wai kudi ba,amma dukka hakan zata farune idan da amincewarki da kuma yardarki”.
      Gaba daya kamar ta sanya zare da allura ta dinke qwaqwalwar bilkisun tsaf haka taji,bata gane komai daga cikin maganar da take gaya mata ba,saita samu kanta da zubawa umma luban idanu qur kamar zata samu amsar tambayarta ne saman fuskarta,karo na farko kenan tun sanda suke tare.
      “karki damu maigado,yanzu zan miki bayani” cewar umma luban tana sake matsowa daura da bilkisun gamida tattara hankalinta waje guda
“Maigado,wata dama ce tasamu,wanda iya hangena da hasashena babu wadda ta dace da samun wannan damar saike,saboda dama ce dazata fidda ki daga qangin da kike ciki ke daduk wani wanda ya jibanceki,zaki rayu irin rayuwa ta gata keda ‘yan uwanki hadda mahaifinki,zakiyi arziqin da babu lallai talauci yasake rabarki…maigado….ana nemawa yarima d’an sarki Abdallah mu’az sarkin kaisa yarinyar da zai aura”. Hakanan gabanta yayi wani mummunar faduwa,ta dubi umma luba kafin ta dauke kai,cikin zuciyarta tana mamakin to ita din meye nata a ciki?,wannan ai sam ba maganarta bace,bama abinda ya shafeta bane bare tashiga ciki,meye ma alaqarta da maganar da har zata zama sikar samun sassauci cikin rayuwarta,a hankali cikin sassanyar muryarta tace
“Allah yabashi,yakuma tabbatar da alkhairi” saita motsa da alamun tashi zatayi,da hanzari ta tsaidata
“Ai dukka maganar taki ce” saita kuma dubanta cikin rashin fahimta
“Eh bilkisu,don babu wadda ta dace ta cancanta tasamu wannan damar kamar ke,zaki auri abdul’azeez abdalllah na tsahon shekarun dazaiyi a qasar da yake karatu,aure ne wanda za’a yishi bisa amincewarki data mahaifanki,kuma za’a daura auren ne da sanayyar qididdigaggun mutane,yayi shige da auren sirri saboda ba kowa akeson yasani ba,fadin irin alkhairin da zaki samu daga lokacin da kika amince zuwa rabuwarku,irin sallamar za’a miki ma bata baki ne,ina da imani da yaqinin zaki samu abinda zai sauya rayuwarku keda duka ‘yan uwanki mahaifinki dama wanda kikaso kika kuma zaba,ke hatta ni din nan na tabbatar da cewa na gama warkewa maigado ta silarki idan kinso”
*Tirqashi!,yaya zata kaya?!*🤏🏽🤏🏽

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *