SIRADIN RAYUWA CHAPTER 7 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 7 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 Baƙiƙƙirin ranta yakekamar yadda fuskarta take a murtuke kai kace saqaon mutuwa aka aiko mata dashi,idanunta na kafe waje daya ranta yana suya,babu wata sauran daraja itakam data rage mata,hotunanta sune abun dauka da turawa wani da namiji?,hawaye taji masu dumi sun taho daidai lokacin dame hoton yagama saisaita komai yafara daukan hotunan.

      Ji tayi zuciyarta ba zata iya dauka ba,saboda haka tamiqe ana tsaka da dakn hotunan tawuce zuwa dakin da shine masaukinta,sai data tabbatar data kulle qofa sannan ta sanya kanta jikin qofar tasaki kuka mai ciwo.

     Ta jima a haka tana kukanta,wanda ba kowa take kokawa ba wannan karon sai kanta da rayuwarta,sai data gaji don kanta kana taja jikinta zuwa cikin dakin tana fidda kayan jikinta wadanda take jinsu tamkar qaya.

**************

      Batasan murmushi take ba a sanda take kallon hotunan har rakai qarshensu,lallai lubabatu ta cancanci a qara mata wani abu kan tagomashin da akayi mata,don ta iya zabe,zabe kuwa na haqiqa,tasan cewa azeez bazai taba kushe wannan yarinyar ba,zata dace da ra’ayinsa qwarai.

       Sauka tayi ta kunna data dinta da kanta,kana tashiga email dinta ta tura mishi dukka hotunan,sannan takashe datar tasoma laluben wayarsa.

       Daidai lokacin da yake sanye da dogon wando da rigarsa mai dogon hannu irin ta sport,qafarsa sanye da rufaffen takalmi wanda zaiyi dai dai da jogging din da yakeyi cikin hasken rana a wanda baiyi zafi da yawa ba,hakanan a layin unguwannin nasu dayafi kama da titi saboda kwalta dake shimfide akan kowanne layi.

     P_cap ce a kansa,kansa saye da headphone wanda idan bakasan me yake yi ba,zaka zaci waqa ko kade kade yake ji,kamar yadda yawancin samarin yanzu suka maida wannan dabi’arsu,a maimakon wannan yanajin tafsir ne na daya daga cikin malamanmu.

      Baisan da tahowarta hakanan baisan ta iso kusa dashi ba sai datayi wave din hannunta a gaban fuskarsa kana ya lura,a nutse ya waiwaya yana dubanta bai fasa tattakinsa ba,itama shi take duba fuskarta qunshe da murmushi har haqoranta suna bayyana,sanye da kayan motsa jiki irin na mata a jikinta,tana ta qoqarin daidaita kafada dashi don kar yawuceta

“Hey!” Tasake fada duk da bata da tabbacin xai jita saboda abinda ke kunnenshi,ya ganta sarai yakuma gane me tace,amma sai yadauke kai kamar bai gani ba ko babu wani mutum a wajen,gamida dan qara hanzari wajen sassarfar da yakeyi,take kuma ya zarce mata,yana kuma kaiwa qarshen layin saiya karya kwana ta yadda yasan zai bace mata.

     Tsaki yaja bayan yadanyi nisa,yanajin haushin yadda bata da zuciya,hakanan yanajin haushin yadda take shige masa hanci da qudundune da yawa,farar fata ce wadda duk da baisan yaren ta ba amma  yanayinta ya nuna masa tabbas baturiya ce wadda baisan daga wacce qasa tafito ba.

      Qarar wayarsa ta dakatar dashi,yatsaya yana qoqarin ciro wayar daga aljihunsa hadi da neman daya daga cikin kujerun da akan ajiyesu haka siddan qasan bishiyoyin dake jere a layin haka siddan saboda hutawar masu wucewa,yadan lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya ganin ammi ce,yazauna sosai yana daga kiran ya kara akunneshi,bayan gaisuwa da suka saba kamar kullum tashaida masa tatura masa saqo na hoton yarinyar,yaduba idan batayi masa ba ayi gaggawar canza masa. Da to kawai ya amsa mata,yana shirin aje wayar takira sunanshi

“Kome kake,koda bata maka ba ba za’a daga abun nan nan da kwana goma ba,already nayi magana da mr james,an gama shirya wannan gidan dana shaida maka,acan nakeso kazauna,ka sameshi ka amshi keys din gidan a hannunsa,kaduba kaga idan akwai abinda baiyi maka ba kobai dace da tsarinka ba,karka manta….bana buqatar kowa yasan dalilinka na barin wannan gidan,hakanan banason kowa yasan inda zaka koma din,dole rayuwarka ta zama cikin privateness,ina fatan ka fahimta?” Kai ya gyada,sai kuma yatuna ba’a gabanta yake ba,dole yabude baki yayi magana don haka yace

“Naji ammi,godiya nake”

“Ohk” ta amsa a taqaice tana datse layin.

     Aje wayar yayi a gefansa,kana ya finciki water bottle dinshi yabude yahau daddakar ruwan,sai dayasha sosai kana ya bame murfin yana sauke qaqqarfar ajiya zuciya,koda yaushe yana kwana ya tashi da mamakin tsarin amminsa,why me yasa ba zata bari yayi aurenshi da safwa ba kamar yadda aka tsara,dama aure yana hana karatu?,dama ana gindayawa namiji lokacin da zaiyi aure ne?,daidai ne hakan ka hana danka ko ‘yarka aure harsai zuwa wani lokaci da suka cika maka qudurinka?,dole a haka zai bita har takai ga gacin tsarinta,amma bayajin zai iya hada jiki ko shinfida da kowacce mace bayan safwa har qarshen rayuwarsa.

      Yana gama wannan tunanin ya dauki wayarta tasa da bottle dinsa yaci gaba da tafiya don ya isa gida ba tare da yayi koda sha’awar yabuda hotunan yarinyar ba bare ya ganta,don baya sha’awar yaga ko wacece,don yasan ko wacece itan ba zata taba kama qafar safwa ba,daga inda yake yana iya hangen gida,don haka yaci gaba da takawa a hakali tunani iri iri yana bijiro masa.

       Yana taka qafarsa a qofar gidan wani kiran yasake shigo masa,daya duba yaga safwa ce,kamar tasan ita yake tunani,sai fuskarsa tadan washe,wanda yawanci idan kaga irin hakan saman fuskarsa to yana nuna maka murmushi yayi a sannan,bai jinkiri ba ya amsa kiran kana ya maqaleta a kafadarshi yana saka key don bude qofar gidan.

      “Kamar kinsan tunaninki nake?” Ya fada cikin sassanyar muryarsa,safwa dake kwance saman gado idanunta a rufe batasan sanda tabudesu tarwai ba,fuskarta cike da murmushi,bakinta yakasa rufuwa har sai datace

“What?,are u kidding me?” Murmushi yasaka mai sauti

“Ina miki qarya?”

“No my prince,it was just amazing” ta amsa masa tana zama sosai saman gadon,farinciki yana lullubeta

“Ohkey,let me repeat my self,tunaninki nake sanda kika kirani” farincikinta ya kasa boyuwa harsai data saki qaramar qara,tana bala’inson azeez ya nuna mata ko yaya ita din wani bangarene na musamman a rayuwarshi,hakan ba qaramin faranta mata rai yake ba

“Yau duka wannan kalamin naka shine babbar kyautar dana samu wadda babu wani abu da zai iya siyanta,thank you for making my day sweetheart” murmushi yasakeyi yana shiga falon sosai.

      A falo yacire takalmanshi yana ci gaba da amsa wayar sannan yawuce kitchen don yasamu abu mai zafi ya qarawa cikinsa,ya hada coffe mai yawa har a sannan yana amsa kiran safwan kana yasake dawowa falo.

      Sak ya tsaya yana dubanshi fuskarsa cike da mamaki sanda yaganshi yafito daga corridor din da babu wani daki sai nashi dakin,kamal ne,shima azeez din yake kallo

“Ina zuwa baby” azeez ya fada yana zame wayar daga kunneshi yana ci gaba da duban kamal dake tsaye.

       Ko a karon banza nauyi idanun azeez din kewa mutum bare a wannan karon da akwai qamshin rashin gaskiya tattare dashi,don haka yasoma kame kame da kanshi

“Oh…ashe sai yanzu kake shigowa,no wonder  naje inata knocking amma naji shuru”

“Really?,ina cewa munyi sallama dakai harka amshi aron mota ko?”

“Yeah,na dawo ne saina bawa su jabir suna da lacture sun kusa makara kuma shida mustapha” shuru yadan ratsa,abdul’azeez najin kamar ba gaskiyar ya fada masa ba,amma saiya share kawai,yazauna yaja coffe dinsa yasoma sha,yayin da kamal yayi gaba da sauri yana jin kamar wanda aka sunceshi daga wani tarko.

*******   ********   ******

     “Har yanzu na kasa gano meye abinda suke shiryawa,na kasa karantar da gano meye ne taketa jaddadawa yaron ya kiyaye,batason kowa yasani,taqi yarda ko bada fuskar da za’a shiga jikinta,amintattunta dukka sun kasa siyuwa,wai garin yaya aisha keson zamar mana gagara gwari?” Ta qarashe tambayar tana duban saudatu qanwa ga maimartaba abdallah sarkin kaisa,hakanan mahaifiya ga kamal.

      Nannauyar ajiyar zuciya tasauke

“Aisha wata irin macace ta daban mai wayo basira dakuma fikra,babban matakin nasararta shine rashin saurin yarda da sakin jiki wa mutane,amma koma meye wannan karon bazamuyi sanya ba,zamu durfafeta ita da dukkan shirinta tuquru,sai munga abinda ya turewa buzu nadinsa….yanzu haka na tura kamal dakinsa bincike koda zamu samu wata makama na abinda ke wakana,kiranshi kawai nake jira,shi yasa na hanashi yin nesa dashi,dakuma hanashi rabuwa dashi,zamansu tare dole zaici gaba dayi mana amfani,hakanan dukkan wani shirinmu xai dinga saurin samun nasara fiye da ace suna nesa da juna” kai fulani adama ke kadawa cike da qaguwa,yayin da saudatun ke kallonta can qasan ranta itama tana shirya nata qudurin daban wanda fulani adaman batasan da zamansa ba.

        Kiran kamal ne yashigo wayar mahaifiyarsa,dukkansu kiran yaja hankulansu,ta daga kana ta sanya handsfree,muryar kamal tafito tangaran

“Mom….babu abinda na iya samu ko ganin cikin dakinsa,ba wata shaida ko alama da zata bamu hasken komai fa” dukkaninsu gabansu ya fadi,ransu yabaci,cikin hasala hajiya saudatu tace

“Kamal…ka duba kuwa dakyau?” Hannu ya yarfar

“Haba mom,ke bakisan masifar da naso fadawa ba ne saboda yadda na tsaya bincikawa ko ina,saura kadan yakamani fa,daya kamanin kinsan me zai iya faruwa?,baida sauqi gayen nan fa ko kadan” 

“Shikenan,zan nemeka” ta fada tana yanke kiran gamida maida hankalinta ga fulani adama da hankalinta yayi masifar tashi,ji take kamar ta kurma ihu,kenan saidai su sake sabon lale?,dukka hope din da suke dashi ya rushe?,ita a jikinta tana jin tabbas akwai abinda yake faruwa,abinda idan ya bayyana zai sama musu hanya mafi sauqi da zasu tarwatsa yarima azeez da mahaifiyarsa dama ‘yan uwansa,su rusa dukka wata martaba tashi datake idanun al’ummar qasar kaisa.

      “Sun binne kuma sun boye komai,amma inaga…muci gaba da namu shirin,babu abinda zai dakatar damu” saudat ta fada tanason qara musu qwarin gwiwa.

*********    *****   *******

    Cikin kwanaki qalilan dukkan wani shiri ya kammala,fulani tagama shirya komai,takuma sanar a can mali kan daurin auren azeez din,saidai ko a can dinma sanarwar ta bulla ne a iyakacin mutanen da tasan ba zata samu matsala ba,hakanan labarin bazai taba zuwa kunnen maimartaba ko wani da bataso ba.

       Fannin gidan malam bilya daya zama alhaji bilya saboda umra da yaje ta sati biyu a tsukin da ake masa ginin gidan kuwa gini ya kammala,ginin da ko a mafarki bai tana zaton zai mallaki gida kamarsa ba,kowa yasan ginin daa dana yanzu ba daya bane,don duk sanda aka tashi rushe tsahon gini za’a maida na zamani akan samu ashe babban fili ne,to shima kusan hakanne,gidane babba ba’a gane hakan ba sai da aka rushe aka mayar na zamani,babban falo da dakuna harda bene na maigida alhj bilyaminu.

      Umma katti tadauki ciki da falo haka mama ladi,sai yaran suma aka ware musu babban daki mai hade da bandaki da aka zuba dukkan furniture da suturar sawa dai dai da kowa.

       Kafin kace meye tuni alhj bilya ya shaidawa danginsa abun arziqin daya sameshi dakuma bikin diyarsa,nan da nan saiga dangi sun fara zuwa,wasu suga gida susa albarka su tafi,wasu kuma su zauna zaman jiran biki,ko a jikinsa sai dadi da hakanma yamasa,don bashi da matsalar abinci,duk kuma wanda yazo sai yace masa sirikinsa wanda zai auri bilkisune ya masa wannan hidimar,kamar yadda yake cikin sharadinsu ko sau daya bai ambaci sunan angon ba.

      *******   ******  *******

      Duk da motar baqaqen glass ne da ita hakan bai hanata ganin irin sauyin da gidan yasamu ba muraran,ci gaba tayi da duban gidan har sanda motar tasu ta cusa kai ciki,kana aka zagaya sashen da take zaune aka bude mata,ta zuro qafafunta dake sanye da half cover takalmi da yafi kama dana sarauta.

      Bata lura dasu ba saiji tayi gaba daya an taho da gudu an qanqameta,ta daga kai tana dubansu,amina ce hauwa’u sai umaima,yayin da hannatu take qarasowa cikin hanzari da sassarfa

“Yaaya…kin dawo?” Suke jero mata tambayar kusan a tare,sai taji idanunta sun soma tara qwalla kamar yadda yazame mata jiki,ta tsugunna ta rungumesu gaba daya cikin jikinta,inama ace tadawo cikinsu xasu zauna ne din din din kamar yadda suke a baya,abinda basu sani ba shine kwanaki biuu kacal xata qara tare dasu tasake musu nisan dayafi wanda tayi musu a yanzu

     Sun jima a haka ba tare data iya ce musu komai ba,sannan daga bisani tace da hannatu

“Kaini ciki” da murnarta tayi gaba suna biye da ita,kowa yana qoqarin bata labarin irin sauyin da suka soma samu,kunnuwanta kawai ta iya basu tana saurarensu,ba shakka ko makaho yasan cewa sun sami canji,tun daga muhalli dama yanayin sutturar dake jikinsu,saidai ko sau daya zuciyarta taqi maraba da wannan sauyin wanda yake kamar fansa ne na mutuncinta,ko madadine na darajarta wadda nan bada jimawa ba za’a watsata.

        Umma katti tasoma arba da ita a babban falon gidan,tayi darashe darashe saman luntsuma luntsuman kujeru tasanya tv a gaba tana kallo,gefe kuma mutum ukune cikin dangin abbanta wanda suke zaman jiran biki,bikin da takejin za’ayi bikine na saidata ko miqata a mazaunin baiwa.

      Bakin umma katti har kunne tamiqe cikin bada wani irin girma da karramawa tana mata sannu da zuwa,hakama sauran wadanda ta taras,nan aka shiga ana akasa ina aka aje da ita,abun har mamaki yadinga bata da daure mata kai,bata jima a falon ba tawuce tabi qannenta zuwa daki,don tanason taji yadda suka rayu sati biyun da basu tare.

         Shuru tayi tana jin wani sashe na zuciyarta nayin sanyi bayan ta gama sauraren dukka labaransu,babu takura,sun rayu cikin kulawa ci sha da sutura mai kyau,hakanan babu wanda yake tsangwamarsu tsakanin umma katti da mama ladi,hasalima mama ladin na jansu a jiki sosai,tana cewa sune ‘ya’yanta yanzu tunda bata da ɗa cikin gidan.

       “Ya Allah,ka sake sanya tausayin wadan nan bayi naka cikin zukatansu,kasa suyi musu riqo nagartacce fiye da yadda sukayi niyyar yi” tasamu kanta dayin wannan addu’ar cikin zuciyarta.

      Tunda tazo ta fuskanci ta zama ta musamman cikin gidan,kowa kaf kaf yakeyi da ita,kwananta biyu ana uku suka tashi gagarumin yinin biki cikin gidan,wanda kaf dinsa babu dangin mahaifiyarta ko qwalli daya,basu san ma wainar da ake toyawa ba,daga dangin uba maqota sai dangin kishiyoyin uwa,wanda sukayi farin fitar dango suka cika gidan don kada aci arziqi suma babu su,zuciyarta tacika fal da mamaki dakuma tunani,wasuma mutanen sam ta manta dasu cikin babin rayuwarsu saboda halin qaqa nikayin talauci da suke fama dashi,amma ayanzu kowa ya dungumo yace shidin nasu ne,kuma lallai lallai dashi za’ayi.

      Duk wannan abun da akeyi su kadai suke kidansu suyi rawarsu,don ita wadda ake kira da amaryar batasanma anayi ba,tana daki liqe da ‘yan qannenta tana morewa sauran awannin da suka rage musu tare,hatta da dakin da aka ware mata cikin gidan cike fal da sutturu na alfarma wanda zatayi fitar yinin biki dasu nata kalla na bare ta bude tashiga,hatta da barorin da suka taho tare ta sanyasu sun koma gida,don bata da buqatarsu,batason ma ganin wani abu daya danganci masarautar dazai dinga tuna mata da al’amarin dake gabanta na tsahon kwanakin.

      Su dinma hakan baidamesu ba,tunda dai sun samu dukka abinda sukeso,abinci da abubuwan sha na kwali dana roba gasunan birjik sai wanda ka zaba.

      Darensu na qarshe tare tajima dasu tana musu karatun rayuwa wanda ba lallaine su fahimta ba,koda zasi fahimta dimma to hannatu itada umaima ne kawai zasu gane me take nufi,saiko hauwa ba’a batun su amina dama da basu ma gama sanin kansu ba bare su fahimci maganganu irin wannan.

      Sun jima sosai a hakan,wanda daga bisani har bacci yadaukesu itan tana zaune tana tufka da warwara.

*****    *****    *****  ******

      Cikin qasar da take mallakin mahaifi ga fulani aisha aka daura wannan sirritaccen aure,tayi matuqar mamakin ganin yayunta maza har qasar ta mali bayan mahaifinta.

       Duk da cewa yarima azeez din yana qasar a sanda aka daura auren amma koda gilmawarsa bata gani ba da sunan mijin da zata aura ba,hasalima da zaka ritsata kan waye mijin nata?,koda za’a jera mata maza cikinsu hardashi bazata iya tantanceshi ba,hatta da fulani aishan bata samu ganinta ba bare mai gaba dayan,wanda hakan yasake tabbatar mata lallai ta durfafi wani bigire na rayuwa na daban,saidai batasan ya tafiyar zata kaya mata ba….A hankali ta daga rinannun idanuwanta da suka jima da sauya kala tun daren jiya har zuwa wannan lokaci da awanni kadanne suka wuce da daura aurenta tana duban wanda ke shigowa katafaren dakin da aka ajeta,aka kuma wadata da dukkan wani nau’in abubuwa na more rayuwa.

       Macace mai cikar haiba gamida kamala,a shekaru ba zata haura shekara arba’in da takwas ba,tana da dan jiki kadan,ba zaka kirata da mai qiba ba,tana da tsaho saidai ba wani can ba,wanda bisa dukkan alamu ma qibar murjewar jikinta ne ya sake boye tsahonta,kallo daya ta fahimci itama tana daha cikin hadiman gidan sarautar kaisa,duk da cewa bata taba ganinta ba sai yau.

     Karon farko kuma a ganin farko data yi mata,taji tadanyi mata kwarjini,hakanan bataji irin abinda ta saba ji dangane da sauran matan da suke hidima da ita ba wadanda suka fito daga gidan

“Assalamu alaikum” tayi sallama matar hannunta riqe da kaya,wanda hakan yasaukar wa da bilkisu wata iriyar nutsuwa data jima rabon data ji irinta,ta motsa labbanta,karon farko tunda tazo qasar mali ta amsa mata itama cikin nutsuwa

“Wa’alaikumussalam warahmatullah” yadda yanayinta yake nuna nutsatstsiyar macace ita haka ya qaraso wajenta a nutse,ta ajjiye kayan kusa da bilkisu,sannan tazauna daga wata kujera da take fuskantarta

“Bilkisu ko?” Ta tambayi bilkisu tana dubanta,sai data daga kai ta kalleta,ason ranta ba zata amsa mata ba,don bata tsammanin akwai wanda baisan sunanta ba cikin gurguxunsu,amma sai taji tayi qimar da ba zata iya shareta ba,don a qalla ta haifeta,don haka ta gyada mata kai,itama kai ta girgiza

“Ma sha Allah,bilkisu…kowanne bawa tun yana cikin mahaifiyarsa da watanni hudu ake rubuta masa dukkanin qaddararsa,Allah S W T yakan umarci mala’ika yaje ya busa masa rai,kana ya rubuta masa dukkan qaddararsa har makomarsa bayan ya mutu,ita rayuwarmu mallakin mahaliccinmu ne,kowanne bawa da kika gani bakya rasa wani abu daya zuwa biyu cikin rayuwarsa da bayasonshi,amma kasancewarsa cikin littafin qaddararsa hakanan yake karbansa hannu bibbiyu yakuma godewa mahaliccinsa kan hakan,harma wataran kiga yana rayuwa kamar babu wannan damuwar a tattare dashi,kamar mu dai…..” Ta furta tana nuna kanta

“Allah daya haliccemu a matsayin bayinsa dukka daya muke a wajensa,amma daya tashi…..ya qaddara cikin bayinsa akwai bayin bayinsa,mu saiya sanya salsala da zuri’armu cikin tsatson bauta iyaye da kakanni,bakuma wai don baya sonmu ba,aah yana qaunarmu kamar kowanne mutum,don ya hanemu sabawa ko guduwa daga wajen iyayen gidajenmu,aikata hakan haramunne akan dukkan wani bawa abun mallaka wa uban gidansa”

“Subhanallah” bilkisu ta fada cikin ranta,kana ta daga kai tana kallon matat,macace cikakkiya kamar kallon data mata dazu,mai cikar haiba da kamala,amma tatashi a sahun bayi?,bayi da takanji ana maganarsu cikin littafin hadisi kona fiqhu,yau ga burbushinsu a wannan zamanin?.

     Kamar tasan me bilkisun ke kitsawa saitayi murmushi

“Baki godewa Allah dabai  sanyaki a sahun bayi kamarmu ba?,duk da muma babu abinda aka tauyemu dashi,saidai har abada bawa bawa ne,harsai sanda yasami ‘yanci,koda yasamu ‘yanci ma cikin tarihin rayuwarsa sunan ya taba BAUTAR abun halitta bazai taba gogewa ba” saita sake matsowa kusa da bilkisu sannan tace

“Sunana hafsa,amma kusan dukkan masarautar kaisa suna kirana da sodangi,nidin jakadiya ce ta yarima azeez,saidai ‘yantacciya ce kamar yadda aka ‘yanta iyaye da kakanni na,kamar yadda kowanne yarima da ake saka ran zamantowarshi sarki yake da jakadiya wadda kusan ita zatayi rainonsa har yagirma,bayan yazama sarki kuma zai riqeta ne a makwafin uwa,na gaji jakadanci daga wajen kakata,ita tayiwa sarki mu’az jakadanci,mahaifiyata kuma Allah ya jiqanta ita tayiwa sarki abdallah mahaifin azeez,ni kuma a yanzu ni nake masa…..an umarceni dana tafi tare daku zuwa mexico,nazauna daku har zuwa lokacin da aka dibawa zamanku ya qare,bilkisu…..nasan an shiga haqqinki an kuma shiga hurumin rayuwarki,hukuncine da fulani aysha ta yanke a lokacin da bana kusa da ita,duk da cewa ta quduri niyyar yin hakan ban isa na hanata ba,amma a qalla inada yaqinin bisa shawarata wasu abubuwan za’a samu sauyi da sauqi,duk da cewa ba hurumina bane,ina mata tsoron ranar da komai zai bayyana a fili…..” Ta fada tana kada kai sannan tadora

“kiyi haquri ki amshi jarrabawarki,ki kusanta kanki da ubangiji,komai zaizo miki da sauqi….sai kuma alfarma daya da nake nema ki taimakeni kiyimin” hakanan taji maganganun jakadiya sodangi yana shigarta,ta iya kalamai masu cike da hikima taushi da kwantar da zuciya,hakanan sai ta dinga ganin girma martabarta cikin idonta sosai

“An doramin dukkanin nauyi da alhakin kula daku,an jaddadamin ns tabbata komai yana tafiya yadda ya kamata har zuwa qarshen lamarin,ki taimakeni kibi duk umarnin da aka bani nabaki don girman Allah na roqeki” ta fada tana hade hannayenta waje daya,nauyin roqon datake mata takeyi,don haka da sauri ba tare data shirya ba tace

“In sha Allahu mama”

“A’ah,taimakeni ki kirani da sunan da kowa yake kirana,saboda ke a yanzu matsayinki sama yake da nawa,kusan dai dai yake da akiraki matar magajin sarki koda ta wucin gadice kuwa” kai ta kada

“Bazan iya ba,zanyita kiranki da maman indai ba zunubi na aikata ba” murmushi kawai tayi tajawo kayan data shigo dasu ta miqa mata tana cewa

“Ina fatan zaki saki jiki dani,ki daukeni kamar wata taki” karon farko murmushin da batasan ya akayi yazo ba ya subuce mata,duk da cewa iyakacinsa saman labbanta

“Ki sanya wadan nan kayan zamu wuce mexico yanzun nan,kafin nan mahaifinki zai soma magana dake,idan kin gama ina falo saiki sameni in miki jagora,idan kuma kina da buqatar wani taimakon yayin shiryawar taki ki shaidamin nashigo na taimaka” daga haka tamiqe tafice,bilkisu tabita da kallo kafin tadawo da kallonta kan kayan,haka kawai taji cikin kaso dari tasake da matar kaso goma,wanda ita kanta batasan dalili ba.

      Durqushe take gaban mahaifin nata kamar yadda kowacce amarya kan tsaya gaban mahaifinta don amsar nasihar ban kwana,cikin wata iriyar shadda da aka yiwa dinkin babbar riga ta alfarma yake,yacika kujerar yanata baza rigarsa,jinsa yake kansa daya da shugaban qasa,gyaran murya yayi sa’an nan yasoma magana 

“Amm….dafarko maigado babu abinda zance dake saidai nace Allah ubangiji yayi miki albarka,yadda kika min biyayya kema Allah yasa ki dace haka,Allah yajiqan maimunatu,yasa ta huta,wanda ba shakka naso ace tana raye taga wannan lokaci” ya fada yana share qwalla wadda ko digon danshi babu a idanun nashi bare kuka

“Abinda nakeso dake bilkisu kiyi biyayya,ban yafe miki ba idan kika saba kan dukkan abinda aka umarceki dashi,kibi duk umarnin da kowaye cikinsu zai baki,Allah yayi miki albarka,ya qaddaea saduwarmu”. Wannan kusan itace sallama ta qarshe data dimga tunawa tsakaninta da mahaifinta sanda take zaune cikin jirgi tana qoqarin maida qwallarta,a maimakon tsoro da zullumi dakan cika dukkan wanda yasoma shiga jirgi karon farko yake tsintar kansa a ciki a’ah,maganganun mahaifinta ne kadai ke bitar kansu cikin kwanyarta.

      Su uku rak ne taga sun shiga cikin jirgin wanda suke tafiyarsu daya,daga ita sai mama sodangi,sai wata matashiya wadda a qalla zasuyi sa’annin juna da ita wanda taji mama sodangi tana kira da rakiya.

      Tafiyar awanni suka sauka a qasar mexico,mexico city,tuni motar da zata daukesu ta iso,da alama ma tun kafin isowar jirgin nasu take dakonsu.

     Motace maikyau ta alfarma,aka zuba kayansu sa’annan suka fice daga babban filin sauka da tashin jiragen sama na garin.

     Duk da yadda zuciyarta take a cunkushe amma hakan bai hana idanunta wulqawa bisa titina da kyawawan gine ginen da suka qawata garin ba,shuru ne ya biyo baya cikin motar,sai mama sodangi da drivern da yake baqar fata wanda da alamu ma dan qasa nijeria ne suke taba hira jifa jifa,da alamu ba yaune karon farko da suka san juna ba.

       Shudewar wasu mintunan na daban suka isa unguwar,wadda tsarinta dakyanta ya fita daban,bata sake gasgata hakan ba saida suka sanya kai cikin gidan,tana biye da mama sodangi wadda take kamar ‘yar jagora a wajensu,yadda take saka kai cikin gidan ya isa ya shaida maka ba baquwa bace cikin gidan,ta sanshi sosai.

      Sai data soma sada bilkisu da wani daki daya sanya bilkisun tsaiwa cak cikin ‘yar fargaba tana dubanshi,komai na dakin fari ne da gold,an tsara dakin ne dai dai da ra’ayin tsari da colours din da azeez yakeso,kusan wannan shine favourite colour na bilkisun,ba wani tarkace bane a dakin amma komai na cikinsa mai aji da kyau ne,yana da fadi sosai,akwai cupboard dressing mirrow sai wani lafiyayyen dunqulallen gado da aka lullubeshi da wani ni’imtaccen farin net,akwai bedside lockers hagu da dama na gadon,wanda akan kowacce akwai fitila akai,sai wata corner daga can hannun hagu na dakin da aka dan mata ado aka aje litattafai na karatu na turanci,da fitila wadda take shige data gefan gadon,saidai tafi ta gefan gadon girma da dan haske,gaba kadan da wajen sofa ce qwaya daya iyama fara qal da ratsin gold,daga gaban gadon lallausan carfet ne madaidaici da wani dan qaramin table mahadin gadon,qasan dakin ba tiles bane hakanan ba carfet bane,wani shimfidadden abune mai kyau da ita kanta batasan sunanshi ba,labulaye ne masu kyau tsari dakuma kauri zagaye da dakin,farare ne da akayi musu adon wata rumfa daga saman kowanne golding colour haka madauran labulen suma duka kalarsu kenan,dakin bai cika haske sosai ba,saidai bashi da duhu kuma,amma luf luf yake,wanda akwai yiwuwar idan yamma tayi lis babu hasken qwan lantarki to babu shakka zai iya yin duhun.

      Qaqqarfar ajiyar zuciya tasauke tana ambaton sunan Allah,kana ya dosana mazaunanta a gefan gadon,tunanin gida yana bijiro mata,tana shanshano irin nisan tazara data yiwa gida,bama gida kawai ba qasarta ta haihuwa gaba daya,wanda tunda take wannan shine karo na farko data taba barin qasarta zuwa wata qasar.

       Tana nan zaune bayan awa guda aka mata knocking,rakiya ce,ta nemi izinin shigowa ta bata,cikin girmamawa ta neme izinin gyara mata kayan sawarta da sake karkade mata dakin,duk da bawani qura yayi ba bare datti,bata hanata ba ta bata dama,tana nan zaune a inda take tana kallonta lokaci lokaci,harta gama kana tashiha bandakin na wasu mintuna tafito,da alama sake wankeshi tayi.

Mintina ashirin tsakani mama uwani tashigo dakin,fuskarta dauke da murmushi tadubi bilkisu
“Lokacin wanka yayi,sai kuma abinci idan kina da sha’awar ci” kai ta girgiza don ita babu wata yunwa da takeji,wanka kuwa harya soma zame mata jiki,wasu irin mayun sabulai man shafawa da turarukan wanka suke bata take amfani dasu,bata taba ganin set irimsu ba tunda take,sun sake fidda ainihin kalarta,sun kuma qarawa fatarta kyau sheqi dakuma santsi,kamar wadda akewa wankan inji,saita miqe ta durfafi bandakin.
*******    ******    ********
      Satinta guda cas a gidan ba tare da taga wani da za’a iya kira da sunan mai gidan ba,hakanan ita kanta mama sodangi bata taba yi mata wata magana data danganci aurenta ba,a satin gaba daya zaman daki tadinga yi safe da yamma har zuwa dare kwanciyar bacci,bata aikin komai a gidan,daga wanka sai bacci sai cin abinci,sai kuma idan ta gaji ta kwanta,don ko kallo batayi,daga bisani data gaji ne takan zauna tayi tilawar izifi hamsin data samu haddacewa,sannan tayi na sauran litattafan data haddace wanda suke kanta,idan tagaji tasake komawa ta kwanta,takuma fadawa tunanin duniya.
     Tunda mama sodangi ta mata tayin ko falo tasamu tadinga fitowa tana kallo ko hira dasu,ta nuna bata sha’awa bata sake takurata ba koyi mata maganar ba,sau tari takan jiyo hirarrakinsu ita da rakiya,kodai na cikin gidan sarautar kona duniya,wani lokaci kuma taji kwarafniyarsu a kitchen idan suna hada abinci.
      Dukkan wani abu na buqata a gidan babu abinda babu,hatta da tsinken sakace a ajjiye yake yana jiran ayi amfani dashi,hakanan duk abinda ta nuna tana da sha’awa ko tanaso saita sameshi,saidai ita sam bataga manufa ko amfanin zamanta cikin gidan ba,tasha yiwa kanta tambaya,waishin an daukota ke don a hanata yawo ko a hanata ganin jama’a?,an daukota ne don a killaceta ta rayu ita kadai?.
        Yanayin rayuwar data taso ya sanya cikin kwanaki takwas kacal kwanciyar taso sanya mata zazzabi da ciwon jiki,saboda ta riga data saba kullum cikin struggling take,tattakin zuwa makaranta da dawowa da qafafunta,aikin gidan umma luba har zuwa dare,wankin qannenta da nata wani lokaci harda na mahaifinta da hidimar kula da qannen nata,sai gashi yanzu shuru bata aikin komai,hakanan babu kowa kusa da ita.
       A kwana na goma ne takai maqurar takura,don haka bayan ta idar da sallar la’asar saita nemi medium mayafi tayi rolling dashi,ta zura slippers dinta tana niyyar fita,sai kuma taji ta kasa fitar,don haka takoma gefan sofa tazauna hannayenta dafe da saman sofa din tana dan tura qafarta gaba da baya tana tunanin yadda zata fita din.
       ‘Yan maganganu taji daga falon,muryar mama sodangi ce,sai daga baya kuma tadaina jin motsinta,bayan kamar minti goma sai gata ta turo qofar dakin tashigo.
     Kamar koyaushe da murmushi saman fuskarta,wanda shike sanya bilkisu jin nauyinta,bai kamata koda yaushe tana kallonta da fuskar murmushi ba,ita kuma ta dinga maida mata da daurarriyar fuska,dole takan sanya itama tasake mata murmushin a yawancin lokutta.
      “Ranki ya dade yau za’a leqamu kenan?,aiya kamata,kinma yi qoqarin zaman,gwara ki fita kiga gidan,bakiga ma gidan ba bare akai ga fita kiga gari” murmushi tasake yi mata,yadda take maganar kamar tanayi da sa’arta ne,sam babu ruwan sodangi,tana da sakin jiki da haba haba da jama’a,yadda takejin hirarrkinsu da rakiya kawai ya isa ya gaya maka haka.
      Juyawa tayi zata fita don haka tamiqe tabita a baya har suka iso falon,babu kowa sai rakiya dake xaune qasar carfet ta zubawa tv idanu,da alama tana dason kallo,ganin fitowar bilkisun ya sanyata miqewa zumbur tana cewa
“Barka da fitowa ranki ya dade” cikin girmamawa,abun saiya mata banbarakwai
“Yauwa rakiya” ta amsa mata fuska a sake duk don tasaki jikinta,don ita bata ga wani bambanci ba tsakaninta da rakiyan,zata iya cewa tama fita ita a wajenta.
     Saman carfet din itama tazauna yadda tagansu zaune maimakon kan kujera
“Subhanallah,ya zaki zauna a qasa Allah ya taimakeki?” Kai ta gyada
“Nafison nan din” jin ta fadi hakan yasa ta qyaleta.
       Kamar falon zai dauki shuru sai kuma mama sodangi ta soma sako hira,ba dadewa rakiya ta biye mata sukaci gaba da hirarsu yadda suka saba,basu saka bilkisun ba,hakanan itama bata sanya musu baki ba don bata da abun cewa,bata da ilimi kan hirar tasu,saidai tana saurarensu,rabi kuma idanunta nakan tv tana kallon wani film da ake haskawa a daya daga cikin tashoshin talabijin na qasar mexico.
      Kusan awa daya da rabi wayar mama sodangi tadauki kida,da hanzari ta daga kana cikin girmamawa tasoma gaida me kiran
“Allah ya taimakeki kowa da komai lafiya qalau…..gata yauta fito muna tare da ita” shiru tayi nadan lokaci sannan tace
“Yau muna tare da yarima,yashigo gidan dazu awa daya data shude,ya bada uzurinsa Allah ya taimakeki ayi masa afuwa,yanzu haka yana dakinsa a sama yana hutawa”.
       Sai a sannan bilkisu ta fahimci dawa ake magana,takuma fahimci dalilin da yasa tun sanda tashigo falon tadinga jin wani baqon lallausan qamshin turare,ashe shine yashigo gidan?,tayiwa kanta tambayar,sai taji wata matsananciyar faduwar gaba,tamkar wadda aka tsikara tamiqe zumbur ta nufi hanyar dakinta don komawa,mama sodangi dake amsa waya tabita da kallo tana mamakin abinda ya tasheta.
       Har zuwa dare bata sake ba bata kuma saki jikinta ba,gani take kamar zuwa kowanne lokaci zai iya neman yin magana da ita koya nemi ganinta,gefe guda kuma tana taraddin wayeshi?,mutumin qwarai ne ko na banza?,yarone ko tsoho?,managarcin mutum ne ko akasin haka?,kai tana tsammanin ma mawuyacine ya zama nagartaccen,saboda tana hasashen babu ta yadda za’ayi nagartaccen mutum ya yarda yayi irin wannan auren,daga qarshe ma taga baiken kanta na takurawa kanta da tayi da ire iren wadan nan tunanukan,tunda koma meye halinsa koma yaya yake bazata iya canza qaddararta ba,hakanan ba zata sauya abinda yariga daya faru ba.
       Qarfe bakwai na dare yasauko daga saman nashi,ya tsuke cikin qananun kaya da suke sake fidda zallar quruciyarsa muraran,hakanan shigar tasake yi masa kyau ainun,ba abinda jikinsa yake sai fidda sassanyan qamshin turarensa wanda yake iske mutum tun kafin shi din ya qaraso wajen.
      Da dan sassarfa yake saukowa yana duba agogon dake daure a hannunsa,da alama sauri yake zai fita,mama sodangi dake zaune bayan ta idar da sallar isha’i ta waiwaya jin takun saukowarsa
“Ranka ya dade kafito kenan?” Ayagance cikin nuna aji na masu ajin yace
“Eh….zan danje wani guri,zan dan jima amma acan,so koda ban shigo da wuri ba babu wani damuwa”
“Amma baka tsaya kaci abincinka ba,sannan…..” Saikuma tadan sadda kai alamun girmamawa
“Baka nemi ganinta ba ita kanta,fulani takirani daxun,na baka dukkan kariyar data dace….” Labbansa ne suka dan motsa da alamu murmushi yake sonyi,mama sodangin kamar uwa ce a gareshi,banda haka babu mahalukin da zai tsaya yayi masa wannan maganar ko suyita dashi
“Karki damu da dukka wannan….tace na karba plan dinta na karba,nayi mai wuyar aiko?” Shuru mama sodangin tayi bata sake cewa komai ba,don bayaga mahaifiyarsa itace mutum ta biyu data san halinsa fiye da kowa,sai yayi gaba kawai,harya kusa kuma sai yace
“A hadamin salad kafin ku kwanta,idan nadawo zanci” ya qarashe maganar yana ficewa daga gidan.
     Ajiyar zuciya mama sodangi tasaki,itadai taga yadda za’ayi wannan auren,amma ta wani fannin tana ganin qoqarin azeez da tsananin biyayyarsa ga mahaifiyarsa,tunda bai nuna rashin amincewarsa ba ko kadan,ya amshi dukkan wani tsari na fulanin yadda takeso.
      Kusan raba dare tayi zaune tsuru cikin duhun dakin,ta kasa samun nutsuwar da zatayi bacci,duk wani motsi da ake cikin gidan kan kunennta,mama sodangi itace mutum ta qarshe data kwanta bayan tagama hada mishi salad din ta aje masa tare da sauran dukkan abinda zaya buqata,don tasan bazai tana yarda yaci girkin rakiya ba,hasalima bataga wannan fuskar da zata dafa mishi wani abu ba,zata iya cewa batama taba ganin yana magana da ita ba,duk da tana hidima ne a qarqashin sassan mahaifiyarsa.
      Sai data daina jin motsin kowa da komai kafin daga bisani bacci yayi awon gaba da ita.
*******   *****    ********
      Duk da yadda ta matsu takuma gaji da zaman dakin amma hakanan a kwankin taci gaba da zaman,tun randa tafito falon bata sake fitowa ba,tunda taji yashigo gidan zuciyarta ta bata tabbacin yadawo kenan,kuma koda yaushe za’a iya samunshi cikin gidan,ba tare da tasan bai fiya zama a gidan ba,yawanci idan yafice tun safe sai dare,da darenma idan yadawo yagama abinda yake sake fita yake,bacci ne kawai ke dawo dashi gidan.
       Wata guda ta kwashe a haka,saboda tsabar zaman waje daya fatarta tayi wani mugun murjewa ta qara haske kamar wadda ke shafa wani mai,saidai takura dakuma yawan tunanin gida data sanya a ranta ya sanya ko qanqani batayi wata qiba ba.
       Wata guda da kwanaki uku a wani dare tana tsaye bakin window tajiyo satar amsar lokuttan da yake dawowa gidan cikin hirar mama sodangi da rakiya,saita saki ajiyar zuciya,takoma tazauna tana qiyasta da lissafa yadda zata dinga tsara fitarta falo da dawowarta dakinta,qaramin murmushi ya kubce mata,sai takejin kamar tasamu wani qaramin ‘yanci,kamar fursunar da aka kwance daga kurkuku.
      ******    *****    *******
       Washegari tsaf ta shirya abunta da wuri,sai daukin lokacin dataji yana fita takeyi yayi tafito daga dakin,kamar wadda zata wata qasa zuwa wata,tana zaune gefan gado,lokaci lokaci tana duba agogo har lokacin yacika,saita sake gyara zamanta ta qara mintina ashirin qwarara akai sannan tamiqe tana gyara rufin kanta,ta murda qofar dakin a hankali ta fito.
      Babu kowa a falon,amma tana iya jiyo motsinsu da ‘yar hirarsu sama sama cikin kitchen,batayi qasa a gwiwa ba tasauya akalar tafiyar tata zuwa kitchen din,lokaci lokaci tana bin duk inda tawuce da kallo,ko ba’a gaya maka ba kasan gini da tsarin gidan dukka turawane suka yishi.
      Sallamarta tasa suka waiwayo da hanzari,nan suka marabceta dakyau,dukkansu suna mamakin ganinta yau har cikin kitchen din. Mama sodangi ce ta miqa mata kujera cikin nuna farinciki tace
“Zauna mana,ai bakya tsaya ba ranki ya dade” murmushi kawai bilkisun tayi,taja kujerar tana zama a lokaci guda kuma tana gaida mama sodangin,ta amsa cikin kulawa da jin dadi,hakanan Allah ya daura mata qaunar bilkisu da damuwa da halin da take ciki,sam batajin dadin yadda ta matsawa kanta ta tattare kanta a waje daya,don dai bata da yadda zatayi ne,hakanan batason wuce gona da iri da kuma shige hurumin aikinta,shi yasa kawai tayi shuru,tana addu’ar Allah ya daidaita lamarin,wanda ta lurama tanayi ne dominsa sam kamar bata gabanshi,hasalima naya wunin gidan ballantana tace.
       “Kiyi haquri,kinji abun breakfast shuru ko?,na tsaya na soma hadawa yarima ne kafin namu,saboda zai fita,yau naji dadi sosai daya nemi abinci,don ba kasafai yafiya neman abinci ba cikin gida” ta tafas batace ba,don sai take ga kamar bada ita ya dace mama sodangi tayi wannan maganar ba,domin itan kamar baquwa ce.
       Taji dadin xaman kitchen din sosai,bata dai cewa komai a maganarsu amma tana sauraren hirarrakinsu da kuma motsinsu sanda suke hada hadar hada abun karin safe,sanda aka gama mama sodangin ta ware mata nata,sai taji sha’awar tazauna taci a cikinsu,don ta manta rabon data ci abinci da wani,tun sanda tabaro gida cikin qannenta.
       Da farko sunqi sun soma dari dari,daga baya da sukaga ta saki sai suma suka sake,sosai taci abincin har tayi mamakin kanta,don rabonta dacin abinci mai yawa kamar wannan harta manta,lallai ba shakka mutum rahama ne,yayin dasu mama sodangi ke mamakin yadda ta tsame hannunta haka da wuri,don su a ganinsu abincin da taci bai wani kai yakawo ba,murmushi kawai tayi,su a wajensu ne haka,amma ita a wajenta abinci taci mai yawa,ta riga data saba kusan dukkansu har qannenta cikinsu ya riga ya kanannade da yunwa,shi yasa komai yunwar da sukeji kuma komai yawan abinci basa masa ci mai yawa.
      Dadin da xaman yayi mata yasa bata koma daki ba,kusan tare suka yini anan falo,tun bata biyewa hirarsu har tasoma murmushi kawai,ta lura ko tsakanin rakiya da mama sodangin akwai shaquwa sosai da sabo,wala’alla shi yasa aka hada tafiyar tasu tare.
     Bata koma daki ba sai data kintaci cewa kowanne lokaci daga yanzu zai iya dawowa,saita musu sallama tawuce ciki.
         Tun daga lokacin saiya zame mata jiki,daga zarar ta fuskanci yafita saita fito su wuni tare da mama sodangi da rakiya,tsahon zamanta bata taba jin muryarsa ko ganin gilmawarsa ba,hakan kuma baya rasa nasaba da yadda take takatsantsan da komai nata.
       Lokaci yaci gaba da garawa a haka,sannu sannu tasoma sakin jiki dasu mama sodangi,sai gashi takan dan buda baki ta amsa hirarsu daya biyu,daga baya sai ya zamto dukkan abinda za’a girka tana sanya hannu ta tayasu da wasu abubuwan,kamar blending kayan miya,yankan salad,gyara kifi ko nama da sauransu,tunda dama mama sodangi itake girkin gidan.
        Tafi tafi sai sabo yasoma shiga tsakaninsu,ta fara fahimtar halayyarsu kamar yadda suma suka soma fahimtar nata halin,tasoma jin mama sodangi kamar mahaifiya a gareta,saboda yadda kalaman bakinta ke fita kullum irin na uwa ne,hakanan kulawar da take bata itama irin ta uwa ce,tasoma jin rakiya kuma kamar ta samu sabuwar ‘yar uwa,wadda zata rage mata kewa da radadin ‘yan uwanta data baro,abinda bata taba sanin tana dasu ba a halayenta sai suka soma raguwa,kamar miskilanci,zaman shuru da sauransu,a gidansu da makaranta idan bada qannenta ba bata sakewa tayi hira da kowa,sai gashi a yanzun tana iya hira da mama sodangi da kuma rakiya kanta,don sun san yadda zasu ja hankalinta suyi hira da ita,duk da cewa ko sau daya bata taba gaya musu ko basu labarin abinda ya shafi kanta ko ahalinta ba,saidai tana yawan ambatar qannenta da basu labarinsu,da kuma fadin yadda tayi kewarsu,hakan da mama sodangi ta fahimta yasa taga bari tayi wani abu,me zai hana ba zata qara fadin sakewar datayi ba ta amintar da ita?,saita shaidawa fulani cewa ya kamata a siyawa bilkisun waya,saboda bata da ita,kuma tana da buqatar jin mahaifinta.
        Ita ta sanya azeez ya siya wayar ya kaiwa mama sodangi,ita kuma ta kaiwa bilkisu da kanta,saidai tace mata jiya data fita yi musu cefane ne tabiya tasiya mata saboda qannenta,bata shaida mata daga hannun data fito ba,don yadda ta karanci bilkisun idan taji wala’alla ba zata taba yarda ta amsa ba.
        Farinciki tare da qaunar mama sodangi ya cikata,sanda ta riqe wayar a hannunta anty zuhriyya ce kawai tasoma fado mata,sai taji idanunta sun tara qwalla,ta tuna sanda tayi mata alqawarin waya a randa ta kammala secondry school,tace itace gift dinta,ashe qaddara zata zo ta ra ganawarsu,ashe qaddara batayi mata tanadin gama makaranta ba,babban burin rayuwarta,ashe dukka ba zata gani ba.
      Data kalli wayar dakyau sai taga ta mata girma,kamar ta girmi girma da matsayinta,kamar tayi zari idan ta riqe waya kamar wannan,saita maidawa mama sodangi ta mata bayani a sama mata wadda bata kai wannan ba,murmushi kawai mama sodangi tayi,can qasan ranta tana fadin da tasan su waye ahalin sarautar gidan kaisa da batace wannan wayar tamata girma ba,amma saita lallabata cikin dabara harta amintar da ita riqe wayar.
        Kusan wayar saita tashi bata da amfani a wajenta,tunda bata da lambar kowa da zata kira ya sadata da mahaifinta shi kuma ya bata qannenta,taji muryarsu,hakan yasa ranta yadan sosu,saita aje wayar gefanta,taja filo ta dora kanta kana tayi rub da ciki.
       A irin haka mama sodangi ta shigo ta sameta,tazo dubata ne ganin shuru bata fito ba
“Na tsammaci kina nan kina waya da gida?” Saita miqe ta zauna sosai tana dubanta,don ta sosa mata inda yake mata qaiqayi
“Mama ban riqe lambar kowa ba cikin gidan” Dan shuru tayi maman tana nazari,sai kuma tace cikin hanzari
“Lubabatu fa?” Maimaita sunan bilkisu tayi a ranta,ko itadinma bata da lambarta,koda tana da lambarta ma bata jin xata iya kiranta,maganar mama sodangi ta katse mata tunaninta
“Inada lambarta,bari na kira ta idan tana da lambar ta bayar,idan kuma babu taje ta amso miki ko?” Kai ta gyada tana jin sanyi cikin ranta,qaunar mama sodangi na sake yawa cikin ranta
“Na gode” ta furta sanda take shirin fita a dakin,da murmushi ta juyo
“Babu godiya a tsakaninmu,don kedin uwar dakina ce,dole nayi duk mai yiwuwa don in faranta miki” daga haka tafice.
      Ba’a rufa awa guda ba mama sodangi tadawo da lambar mahaifin bilkisu,kasa zama tayi sanda taji tashiga tana ringing,sai tayi tsaye gaban mudubi tana kallon kanta da kanta,wayar kange akunnenta cikin zumudin son jin an daga.
Daf da zata tsinke kamar ba za’a daga ba taji sallamar mahaifinta na ratsa dodon kunnuwanta
“Wake magana?” Ya tambaya
“Baba….bilkisu ce” ta fada bakinta yana dan rawa
“Bilkisu?!….wace bilkisun?”
“Mai gado baba”
“Ke!….mai gado?,ince dai lafiya ko?” Ya tambayeta,saita sauke ajiyar zuciya
“Lafiya qalau baba”. Daga haka tasoma gaidashi ya amsa mata sannan tace
“Baba…su hannatu nakeso ka bani zamuyi magana dasu”
“Kina tantama ne kan lafiyarsu ko.maigado?” Ya jefa mata tambayar,da sauri tasoma girgiza kai kamar yana kallonta
“Ba haka bane baba,kawai najima bangansu ba banji muryarsu ba,shine kawai dalili” ta qarashe fada tana fatar kada ya hutsance mata ya hanata magana dasu
“Keda ganinsu kam ai sai bayan shekara daya….yanzu dai ina kasuwa,amma idan nakoma zan hadaki dasu,shikenan dai ko?” Kai ta gyada a sanyaye,badon taso ba,don tasone a yanxu yanzu suyi magana,amma babu yadda ta iya.
       Haka tazauna zaman jira,duk bayan minti daya saita irga mintunan da suka rage yakoma yakirata yabasu,rakiya tadinga mata dariyar ta qosa da yawa,yayin da mama sodangi take kallon ta cike da tausayi,don tasan ita kadai tasan ciwon da taji na rabuwa da qannenta da tayi.
        Murmushi tayi sanda rakiya ke ci gaba da yi mata dariya
“Rakiya kowa fa yabar gida gida ya barshi,dan uwa dadine dashi” sai taga ta kauda kai tana murmushi
“Mu duk bamusan wannan ba ko mama sodangi?” Da yake ta koyi cewa mama a wajen bilkisu,murmushin maman tayi kawai ba tare da tace komai ba.
       Sai bayan wajen awanni takwas sannan baban nata yakira,a sannan har tayi laushi,ta sanya wayar a gaba kawai da tugumi,ta yanke tsammanin zaya kira,tana dagawa muryar hannatu tasoma ji,wayyo Allah,farinciki kamar su faso wayoyin suga junansu,tana iya jiyo muryoyinsu dukkanin yaran a rude,kowa so yake ya ganta kuma yayi.magana da ita,da qyar tayi controlling kukanta don kada ta karya musu gwiwa,tasa hannatu ta sanya wayar a handsfree,sannan tace da daya da daya kowa yayi.magana da ita.
        Haka aka dinga bin layi,kowa tana biye masa tare da bashi lokacinta sosai,sam.ta manta a agaban mama sodangi take,saita dinga jinta kamar gata a gida a gaban qannan nata,duka saida suka gama gaisawa da kowa sannan tasoma tambayarsu kan abinda ya dameta
“Kuna cin abinci?,kuna zuwa makaranta?” Hannatu ta amsa mata
“Kullum yaaya sai munci har sai munce mun qoshi,dakinmu mu kadai babu mai takura mana,an kawo.mana kaya masu yawa dakyau,duka mun bada wadan can,kuma baba ya sanyamu a makaranta islamiyya harda ta bokon da kikace zaki sakamu,kinga ya hutashsheko” wata nannauyar ajiyar zuciya tasaki tana godewa Allah,wannan labarin data ji shi ya rage mata damuwarta kaso hamsin cikin dari,yakuma haifar mata da wata ‘yar qaramar nutsuwa da a baya bata sameta ba,lallai addu’a bata faduwa qasa banza.
        Tun daga ranar tasamu abunyi,kullum ta Allah saita kirasu da daddare taji ya suka wuni?,me sukeyi yanzu?,tun tana dari dari da tunanin baban zaiyi fada,koya hanasu wayar harta saki jiki,ganin bai sake cewa komai ba,ga mamakinta harda mama ladi wataran saita amshi wayar sun gaisa,wannan yasake haifar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali.
       Uwa uba kuma ganin babu wani abu daya biyo bayan auren nata,rayuwarta take cikin gidan daga mama sodangi sai rakiya kadai take gani,wanda take zaman dominsa bata taba ganin gilmawar koda mai kama dashi ba bare shi,koda sautin muryarsa bata taba ji ba,saidai taji mama sodangi lokaci bayan lokaci takan jefa zancansa tsakaninta da rakiya,yarima yace in masa kaza,ko dauke abu kaza saboda yarima yakusa shigowa,hakan yasa wasu lokuttan da yawa take manta meya kawota qasar?,take manta cewa ma tana da wani abu waishi aure,saita sake sakewa,batasan cewa BABBAN QALUBALE NA BIYE DA RAYUWARTA A GABA BA.
      Zamansu da rakiya yasa ta fuskanci tana da rauni wajen karatun addini dana boko ma,hakan yasanya ta dorawa kanta nauyin karantar da ita daga ilimin da Allah ya bata bayan kowacce sallar la’asar,tashiga internet tayi browsing duka litattafan da zata fara koya matan,suka baiwa mama sodangi ta nemi inda ake printing akayi musu,saboda ita din kamar ‘yar garice a qasar,tasan kan qasar sosai,kuma hakan baya rasa nasaba da yawan zuwa da fulani aisha keyi tare da abdul’azeez tun bai fara ma karatu anan ba.
        Yanayin qwarewar bilkisu yasa mama sodangi itama taji sha’awar zama ayi karatun harda ita,sai daliban nata suka zama biyu,anan falo suke zama ta karantar dasu,a sake suke tambayar dukkan abinda basu sani ba,ita kuma ta basu amsa daidai gwargwadon saninta dakuma yadda hukuncin yake a alqur’ani ko hadisi,sosai karatun yake musu dadi har ita bilkisun,don ya sake taimaka mata wajen debe mata kewa,tare da tuno mata wasu karatuttukan data manta.
       Wannan zaman yasake haifar da sabo sosai a tsakaninsu gamida fahimtar juna da qauna.
      ****    *****    ****    *****
      Ƙarfe hudu harda wani abune na yammaci,dai dai lokacin bilkisu na zaune a falon gidan,cikin doguwar riga data nada mayafinta a kanta,duk da cewa ba wani zama yayi sosai ba amma ya mata kyau sosai.
      Gefanta rakiya ce itama,wani series suke kalla,su duka sun bada hankalinsu kai,duk da cewa rakiyan ba fahimta take ba,bilkisu ce ke gaya mata duk abinda yake faruwa ta hanyar subtitile,don ba yaren turanci suke ba,harshen qasar mexico ne.
      Mama sodangi ce tafito cikin doguwar riga da wadataccen mayafi,hannunta riqe da wayarta dakuma atm card,idanunta a kansu ta qaraso falon
“Tashi rakiya muyi sauri mu dawo,yau siyayyar da yawa”
“Toh” ta fada tana miqewa da hanzari,sai bilkisu ta bisu da kallo
“Mama yau kuma ni kadai za’a bari kenan a gidan” dubanta tayi
“Ranki ya dade siyayyar tana da dan yawa ne,shi yasa na gayyaci rakiya muje tare,nasan koda na gayyaceki ba lallai ki amsa” ta qarashe tana murmushi,don tasha yiwa bilkisun tayin tazo suje din kodan ta miqe qafarta amma bata taba zuwa ba.
     Ga mamakinta sai taga tamiqe tana cewa
“Xanje” tayi hakanne don kawai tana tsoron gidan,tana tsoron xama ita kadai,uwa uba data duba time ma dawowarsa sai taga mintuna kadan suka rage,tana tsoron yadawo ya taddata ita kadai ya zatayi?.
      Fidda wayarta maman tayi tana cewa
“Ta kwana gidan sauqi ai,amma bari mu tambaya maigidan tukunna” jin ta ambaceshi sai bilkisun ta qara sauri tawuce daki,don kada ma tace mata ta tambaya da kanta.
     Mintuna qalilan tasake shiri tafito,tayi tsaf da ita,hakanan ta aje wani kyau mai daukan hankali,duk wani sirrin kyau nata da wahala da talauci suka boyeshi yanzun ya bayyana sanadin hutun data samu,qiba ce har yau babu abinda ta qara,tana nan ‘yar firit dinta.
      Taji dadin fitar sosai,taga gari yadda ya kamata,tsari da yanayin garin yayi matuqar burgeta,tun daga ranar saiya zamana sukan fita tare lokaci bayan lokaci,cefane ko wankin kai ku kuma shan iska kawai.
      A haka rayuwa taci gaba da garawa,bata sanshi sanshi ba,bai santa ba,bata taba ganinsa ba bai taba ganinta ba,bata taba nemansa ba,bai taba nemanta ba,tamkar kowa zaman kanshi yake ba tare da wata alaqa ta hada dayansu da dayan ba.
*_BAYAN WATA BIYAR_*
      Duk ranar Allah da zata fito ta fadi saita lissafa adadin kwanakin da suka rage mata cikin gidan da garin gaba daya,kwanakin da suka rage mata takoma qasarta kuma cikin ahalinta.
      Ayanzun watanni biyar data shafe gani take taci nisan zango mai yawa a tarin tafiyar dake gabanta,hankalinta akwance yake sosai fiye da baya,sai taga ashe dukkan yadda ta tsammaci abun ba haka bane,ashe da tasan haka tafiyar zata kasance da babu damuwa ko kukan da zatayi,idanma zata koka din…..zata koka ne kadai saboda rabuwa da zatayi da ‘yan uwanta na tsahon lokaci….
_tofa masu karatu,yanzu wasan zai fara_
      *****   *****   ******
      Kamar kowanne yammacin rana ta Allah buwayi da sukan zauna bilkisun ta dora musu karatu,yauma suna zaune a falon gidan bayan gama sallar la’asar da mintuna qalilan,ayau mama sodangi tana kitchen tanason kammala abincin darensu,kafin tazo sai bilkisu tasoma yiwa rakiya nata qarin karatun don kada a bata lokaci.
     Tana sanye da wani skert ne dogo wanda yafi zubi da buje,mahadi da hijabin jikinta wanda dukka tsahonshi bai zarta qugu ba,yadine mai taushi ruwan madara da aka yiwa dige dige dakuma adon furanni da dark pink,fuskarta tafito sosai tayi kyau kaman wata baby,hakanan kayan sun haskata qwarai,ta baiwa qofa baya,yayin da rakiya ke kallon qofar.
      Da fari sunji qarar tsaiwar mota a qofar gidan,basu kula ba,don sunyi tsammani maqotansu ne sukayi baqi,don sunsan su din babu mai zuwa wajensu a irin wannan lokacin,tunda dai lokacin dawowar azeez baiyi ba a yadda aka saba bare suce shine.
       Mintina kadan bayan nan sukaji ana taba qofar parlour dinsu,kafin suyi wani yunquri an bude qofar,da alama wanda yabude din yana da muqullin falon.
        Tare suka daga kai gaba dayansu,saidai yadda bilkisu taga rakiya ta miqe cikin girmamawa da tsananin nutsuwa yasa bilkisun kasa juyawa,wata matsananciyar faduwar gaba da bata taba jin irinta ba kaf rayuwarta ta ziyarceta lokacin da sassanyar muryarsa ke furta sallama afalon,muryar data karade dukkan kunnuwanta suka zarce zuwa ga qwaqwalwarta,tsintar muryar rakiya tayi tana fadin
“Barka da warka Allah ya baka yawan rai,barka da isowa” kanta a qasa,bisa dukkan alamu dokarsa ce baya son ana kallonsa,itadai bata sake jin muryarsa waida zummar amsa gaisuwar da rakiya ke kwarorowa ba,tamkar mutum mutumi haka bilkisu taci gaba da zamana wajen a daskare,zuciyarta tana wani irin gudu kamar zata fasa qirjinta,yayin da gumi yajiqe mata fuska zuwa wuyanta,bata motsa ba sai dataji ya kammala.takunsa gaba daya da alama ya gama hawa saman,sannan tayi wani irin yunqurawa ta kwasa da wani azababben sauri tawuce dakinta.
      Da kallo rakiya ta bita harta qulle,saita maido dubanta ga littafin da suke karantawa tana danne dariyar dake taso mata,tabbas batasan waye azeez ba,inda tasan wayeshin da bata damu kanta kan boye kanta haka ba,ko yanzun ma kallo guda tak yayiwa muhallin da suke zaune bai qara na biyu ba ya qara gaba,bai damu daya duba baquwar daya gani xaune a wajen ba sam,sai wani murmushin yasake kubce mata sanda take hango fuskokinsu a tare
“Zasu fa dace da juna” ta fadawa kanta da kanta a fili,sai kuma ta damqe bakinta tana zare idanuwa tana duban falon,Allah yasa babu kowa,litattafan nasu tahau tattarewa kawai tabi mama sodangi kitchen.
        “Wai kaddai ace harkun gama karatun,duk saurin da nake nagama na cimmaku” sai data aje litattafan saman freezer tana danne dariyarta sannan tace
“Inafa aka gama mama,yarima ne yashigo muna tsaka da karatun,tana ganin yashigo ta kwasa tawuce daki shikenan karatun ya qare” murmushin itama mama sodangi tayi tana kashe gas din,itakam wannan abun nasu batasan farko tsakiya ko qarshensa ba,fata dai Allah ya zabama rayuwarsu abinda yafi zama alkhairi tayi addu’ar cikin ranta.
       A mugun gajiye yashigo gidan,don asubancin da yayi yau yafita a gidan yajima baiyi irinsa ba,wanka kawai yayi yadawo yaxube a katafaren falonshi,kwanciyar rub da ciki yayi bayan ya tasa ruwan cikinsa da filo yana lumshe idanuwa,sanyin ac dana sauran ruwan jikinsa yana ratsashi.
       A hankali yasoma jin tsohon feeling dinshi da yaketa qoqarin adanawa yanason taso mishi,don haka saiya mirgina yakoma kwanciyar rigingine,kana ya jawo wayarshi yayi kiran abdulrashid,saboda kwana biyu basuyi waya ba.
     “Mr ango,yanzun nake cigiyarka a raina,ina tunanin idan nakoma gida na kiraka,tunda kai angonci ya boyeka” idanunsa ya lumshe kana yabude yana dan dukan tsakiyar kanshi,don sam bai gane angoncin da abdulrashid din ke magana akai ba
“Angonci ne mefa?” Dariya abdulrashid yasaka
“Karka rainawa kanka hankali….bansani ba nima” sai a sannan yatuna cewa shidin fa andaura mishi aure watanni kusan hudu ko biyar da suka shude
“Allah ya shiryeka abdulrashid…”
“Kaidai zance Allah ya shiryeka azeez,wannan attitude din naka bansan sai yaushe zaka rabu dashi ba” murmushi yasaka mai dan sauti
“Wanne attitude gareni?,wai har na kaika?,kaga kira nayi mu gaisa ba fada ba” ya fadi yana dakatar dashi.
      Hira sukayi mai dan tsaho sosai,wanda ta jawa abdul’azeez din lokaci,har lokacin magariba yakusa sannan ya aje wayar,yashiga bandaki ya sake watsawa jikinsa ruwa,don shi wani irin mutum ne mai mugun tsafta da qyanqyami,hakanan wanka baya isarshi.
      A gurguje yake shiryawa din yanason fita kamar kullum wayarshi tasake daukan ruri,safwa ce,saiya yarfar da hannu
“Safwa!” Kana ya daga wayar
“Its time for prayer fa” ya gaya mata a taqaice,saboda qa’idarshi ce bayason kiran waya lokacin sallah.
     Kamar yana gabanta ta murguda baki kana ga juya idanu
“U r in mexico and am in nigeria mr man,ko ka manta ne?” Qaramar dariya yayi
“Yes maaaa”
“Ohk,no more excuse da zaka bani,yanzun lokacinane gaba daya”
“Bance a’ah ba,but…yanzun lokacin sallah ne,and i have visitors,friends dina ne daga wata qasar….nayi alqawari i wil cal you” shagwabe mishi tayi yadda ta saba,wanda hakan ya sanya yaji tsigar jikinsa na wani xubawa yarrrr,ya lumshe idanunsa yana sauraren kukanta,a hankali yabude bakinsa
“Stop it please safwa,i said i promise” ajiyar zuciya tasauke
“Na yarda,amma vedio call?”
“Yes” ya amsa mata a taqaice,hakan ya mata daidai,saita saki murmushi tana masa sallama,yau rana ce ta musamman a wajenta,don ba kasafai yafiya yarda suyi vedio call ba,yakance mata tsarinsa kenan,don haka tana aje wayar ta dira daga kan gadonta cikin sauri,tahau hargitsa cupboard dinta,ta ciro wani riga da skert ta watsa saman gadon tawuce toilet cikin sauri kamar wadda ake jira,tanaso ayi mata gyaran gashi na garari,don tasan azeez din yana matuqar son suma,tun ranar data sani din kuwa duk randa zayazo sai taje an mata gyaran gashi an mishi ado mai kyau azubo dashi yadda zaike gani,saidai kosau daya bai taba tankawa ba,saidai ya kalla yadauke idanunshi,hakan bai dameta ba,saboda tasan halin miskilancinsa,ko iya kallon da zaiyi ita ya gamsar da ita.
      Wanka tayi sharp sharp sannan tafito ta shirya,kana ta zari muqullin motarta tafito.
        Saman daya daga cikin kujerun alfarma dake katafaren falonsu na farko tasamu mahaifiyarta zaune akai,yayin da wata mace ke durqushe gabanta riqe da qafarta,da alama pedicure take mata,itan kuma tana riqe da wayarta tana latsawa,kallo daya zaka mata kasan hamshaqiyar hajiya ce data jiqu da naira.
       Dago kai tayi da sauri tana duban safwa data rungumota ta baya
“Fita zakiyi?” Ta jefa mata tambayar tana karantar zallar farincikin dake shinfide kan fuskarta,kai ta gyada
“Zanje retouching ne amma,yau azeez ya yarda zamuga juna” saita saketa cikin sauri tanufi qofa,baki wangale ta bita da kallo,xasuga juna kamar yaya?,qasar zaizo?,bata samu damar mata tambayar ba don tuni takusa kaiwa ga qofa,saita daga murya kawai tace
(²⁵)
“Banda tuqin ganganci,ki dawo kuma dawuri tun babanki baizo yaga ke daya kika fita ba”
“Ohkey mom!” Ta fada yadda zata jiyota,saita girgiza kai kawai ta maida kan wayarta,ita kanta tana jinjina yadda diyar tata take bala’inson abdul’azeez din,tamkar babu wani namiji da yayi saura a duniya saishi,saidai tana godewa Allah daya sanya wanda takeso din ya cancanci a soshi,ba gama garin mutane bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *